Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fatanmu allah yasa bai riga ya ba wai ba.rufe bakin mahmud ke nan,lsmail ya ce,amin...bai karasa ba,sai ga MIMI ta fito sanye da riga da wando damammu,sai dan mayafi da ta rataya shi kamar yadda take yi tana janye da dan akwatinta.da sauri ya nufo ta,ina za ki je?ta kalle shi sama da kasa,ta ja tsaki,ta tsallaka kwata.ya kalli gurin zaman yan majalisar kofar gidansu ba su fito ba rana.mahmud ya ce,bar ta mu bita a baya. haka kuwa tana tafe suna bin ta.sai ta tare dan acaba ta hau.su ma suka hau suna hangenta tana waya har zuwa garejin mota.tana tsayawa suka tsaya ta ciro kudi ta ba dan acaba,su ma haka.ta nufi wata mota.kafin su tsallaka su isa ga motar har sun tashe ta.lsmail ya shiga tashin hankali sosai.ya ce, mahmud barin ta za mu yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna. [01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi. CANJIN RAYUWA 3 Halima K mashi Littafi na Uku Hausaebooks Shuraih 99% Daga:- http://keffiansonline.cf Hankalin isma’il yayi mutukar tashi lokacin da aka juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan mahmud yazoya kama kafadun isma’il yana cewa karka damu isma’il mutafi asibiti sun nufi motar kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana cewa kaiba ni kayan nan konakane? Yace ammm dama inace za aje gurin yansadane mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada in anyi hadariko? Mutumin ya miko akwatin tare da cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan sannan ya shiga yana cewa “muje hamisu!” kuwwar motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso. Sannan suka nufi asibitin tare. Cikin sauri aka amshi su aka yi emergency dasu, musamman dayake angansu da yan sanda.isma’il yana tsaye cikin matsanancin hali.addu’o’in da isma’il yake yine sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya abin yafarune? Mahmud yakalli dan sandan gudu yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune? Sai wani ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne suke dauko mota suzo sunamugun godu atiti.mahmud yce, yarinyar da suke tare matar wannance, yanuna isma’il.jiya aka daura musu aure shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma’il batason kane? Lsma’il yace, babanta ne yahada nida ita ranka yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce, kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara. Sannan suka ce, allh yajikansa da gafara.isma’il yakama hannun likitan yana fadin”doctoh itafa? “yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu karaya guda biyu a kafarta, da kuma guda daya a hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta, saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda, kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka wadannan,yanxun kakawo mana. Isma’il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana. Daga nan sai mutan gadan su san halinda ake ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba agata mimi ba. hamisu yajasu, kai tsaye gidan suka koma, inda isma’il ya aje jakar mimi,sannan ya dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi. Ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai magungunan. lokacin ne ma dansandan yake fada musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki gawarsa.isma’il ya girgiza kai don jinjina yadda mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira hamisu don yaji ko ya kosa kaduna. Zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace xaiba shi,don shima yaji dadinsa. Hamisu yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba har yanxun.alhaji ya ce, meya faru kuma? Hamisu ya sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai yace ma hamisu,”kataho kawai!”yace,alhaji yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali sosai,don duk akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar. Babu abin da zan iya yi mata, kaima bbu abin daxaka iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace, shikenan,alhaji zan taho yanxun.”yace,” to, kana kusa dashi malam isma’il din ne? Yace, “eh ina kusa dashi.yace,toka bashi!”ya mikama isma’il wayar.sun gaisa,alhji yace,”ashe abinda yafaru kenan?”isma’il yace kwarai kuwa alhji.yace Allh yakyauta.”cikin tashin hankali isma’il y2e,alhji kayi mata duk abinda takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya rasuma.”duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar khalil a ransa,amma afili sai yace,”karka damu malam isma’il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar.”isma’il yace alhji kuzo ku taimaka mata.”alhji yace,isma’il inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu wayar!”cikin rawar hannu,isma’il ya mika ma hamisu wayar. (Za mu ci gaba)…. (Tare da Halima K Mashi) Canjin rayuwa A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya sauda. Ya kalli mahmud, “ya kamata in sanar da mahaifiyar yarinyarnan ko? ” Mahmud yace, “tabbas ya kamata ka sanar da ita” kan benci ya zauna, sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne? Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar zuciya, to da sauqin dai za’ace amma shi ya rasu… Ya rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,. Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe wayar. Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba, yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran ‘ya’yanki banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji? Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe wayarsa. Shi kansa Alhajin cikin damuwa yake, amma ya tsara ma kansa cewa, dole ya haqura don wani dalili nasa, sannan yasan cewa, abin Ya ta6a zuciyar hajiya sauda, sbd hk ya yanke Shawarar sake kiranta. Ta daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai nayi hakan. Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin wannan. Nasan zaki iya saka ‘ya’yanki su dangana da zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya, shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya kawo ka lfy. Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata. Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili. Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne? Tace a’a ba zan samu zuwa ba, in dai ta tashi kace ina gaisheta. Yace hajiya kema baki samun damar zuwa kenan? Ta soma shesshekar kuka, mahaifinta yayi mana iyaka da zuwa gurin ta, cikin sauri yace sbd me? Don Allah ku yafe mata, sbd tana cikin wani hali, wanda ba dole bane ta tashi. Hajiya tace na yafe ma ta duk abinda tayi min, wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma nima bansan dalilin sa nayin hkn ba, amma idn ya fadamun zan sanar dakai. Sannan kuma malam Ismail zan sake baka amanar mimi, ka qadd ara batada kowa, sai kai kadai mijinta. Lokaci zuwa lokaci zan dinga jin yadda jiki nta yake, amma ta waya daga bakinka. Ismail yace shikenan nayi miki alkawarin zanyi iyakar iyawata, sai Anjima. Ya kalli Mahmud, bayan ya kashe wayar, wannan wace irin qaddara ce ta hau kaina? Alhaji ya hana su zuwa ma. Mahmoud yace wanna n abin da Mamaki, amma tunda kai iyalinka ce, nauyinta ya rataya ne a wuyan ka. Kai ya cancanta kaci gaba da kula da lfyr ta har zuwa lokaci n da zasu huce. Nawa zaton sunji zafin guduwar data sake yi ne. Amma in sun huce zasu zo. Ismail yace Allah ya sani, tunani na dama banida qarfin dazan iya kula da lafiyarta. Mahmud yace, kar ka damu Allah zai duba maka. A sanyaye Ismail yace Allah ya duba mana, suka hada baki gurin cewa Ameen! Saida lokacin sallah yayi sannan suka miqe suka nufi masallaci. Daga masallaci ne Mahmud ya nufi gd don sanar wa malam Aminu. Ismail yace kabi ta gdn yaya Amina ka fada mata don bata sani ba, Mahmud yace zanbi insha Allahu. Kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu’a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen. Bayan la’asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu’ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a’a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a’a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a’a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s Canjin rayuwa Canjin rayuwa sun kai kusan minti goma, sannan wata nurse ta leqo, ta kalli Ismail, tace masa wanene khalil? Yace mata shine wanda sukai hadari tare ya mutu. Ta juya da sauri, Ismail dai yanata kai komo. Ya kai kusan rabi sa’a sannan likitan ya fito, ya kalli Ismail yace masa, zo muje! Ya bishi zuwa offishinsa, inda suka zauna, ya kalli Ismail, kai wanene dinta? Ismail yadan yi jim kadan don yana jinjina kalmar, duk lokacin da zai furta ta. Tsakanin jiya zuwa yau, ya lumshe ido, “ni mijinta ne” likitan yace ok to zamu kaita dakin jinya, domin ynxun ta farka, amma yanxu munyi mata allurar varci sakamakon tana ta kiran sunan marigayin. Ya ajiye biron daya dauka, sannan ya kalli Ismail yace, wazai zauna da ita? Ismail yace nine, likitan ya girgiza kai, babu dama ka zauna da ita, sbd kai namiji ne, kuma dakin akwai matan mutane, sai dai in zaka biya daki na musamm an, sannan za’a buqaci kudi sbd likitan da zai mata dorin zaizo ne da ga kano, kuma gashi dorin har guri uku ne, Ismail yace to likita kamar nawa ake nema? Yace kasan shi likita ne mai zaman kansa, dauko shi akeyi, qila yakai gurin dubu sittin, banda magani. Ismail yace insha Allahu za’a san yadda za’ayi, Amma likita bata samu matsalar da ake tunanin ta samu ba ko? Ya girgiza kai, bana zaton ta samu wata matsala, Ismail yace Allah yasa dai, zan biya kudin daki na musamman din. Likitan yayi masa kwatancen inda zai biy a kudin dakin. Har ya miqe sai likitan ya sake kallon sa, ba tada iyaye ne a garinnan? Eh, kawai yace, to ko cikin dangin ka ba wanda zai iya zama da ita? Cikin qosawa yace nima yayata ce guda daya, kuma tana da qananan yara. Baya son doguwar magana, shiyasa ya amsa a qagare, shikenan ka iya tfy, inji likitan, an kaita daki na musamman akan kudi naira dubu ashirin a sati biyu. Dakin akwai TV da dan fridge, sai na’urar sanyaya daki. Ismail yana tsaye yana kallon mimi, an manna mata bandeji a gurin da taji ciwo. Addu’o’i kawai yake yi mata, har lokacin da yaje yayi sallar magrib a bata farka ba. Yana shigowa yaci karo dasu yaya Amina, suna neman dakin da aka kaisu. Ya amshi kular hannunta sannan suka nufi dakin, suka gaisa da abbab saddam, yayi masa jaje. Basu jima ba suka ce zasu wuce. Yabi su don yadan taka musu, anan ne take tambayarsa ko ‘yan gdansu sunzo? Yace kinsan dai koda zuwan ne, sai dai in mazan, amma matan ban sa rai ba, mazan ma daqyar in sunji, tunda lokacin da naje gdn basa nan, tace to ba komai Allah ya bata lfy, yace Ameen, tace tuwo ne fa akular da muka zo da ita, naga kana son tuwo, yace nifa yau ko karyawa banyi ba, dama zan samu ruwan zafi, tace vari to inje in dafa maka, sai abban su saddam ya kawo maka, tunda ga mashi n ahannunsa. Ismail yace to na gode. Suna fita, wayar Ismail ta soma ringing, ya daga ashe Mahmud ne ya kawo innarsu zata duba ta, suna cikin gaisawa da innar sai ga kiran hajiya sauda. Bayan sun gaisa take tambayarsa jikin mimi, yace da sauqi, amma tana varci, bata farka ba, tace to zata kira zuwa gobe, sannan ya turo mata account number dinsa, yace to insha Allahu, sannan yayi mata godiya. Kusan qarfe goman dare, mimi ta farka, lokacin Ismail yana zaune kan sallaya, ya idar da sallar shafa’i da wutiri. Sai yaji tana cewa, “daddy na, daddy na!” cikin wani irin sauti mai ban tausayi. Da sauri ya miqe ya nufi gadon da take, ya kama hannunta yana “khadija, sannu kinji. Kin tashi ne? Bari in kira likita” ya miqe ya nufi qasa da sauri domin kiran likita. Ta soma kuka, ni fa taimako nayi sbd kar aji kunya, yace aikuwa zakiyi da kin sanin wannan taimakon. Inaso kisan wani abu, ni mutum ne wanda in naga abu inaso, to so ne na gske, kuma ba zanyi wasa da son ba. Haka nan kuma qi, don bana yin qi da wasa, mimi na gani nace inaso, tunda tace bata yi ai sai abarni inji da ciwon rashin ta, ba wai akwaso min ke ba, baqi qirin! Ni farar mace itace ra’ayina, kin gane? Na’ima ta soma kuka wiwi, tana cewa, toni ynxun ka fatamin matsayi na, ya miqe tare da nufar dakin varcin sa. Gashi na fada miki kuwa, banda wannan matsayin wanne kk son ji? Don Allah tashi ki fita a daki na, Na’ima ta miqe jiki babu qwari, ta nufi dakinta cikin kunya da kuka, ta kira momy nafisa a waya, momy tace lfy da wannan daren? Na’ima cikin kuka tace “momy Abbas baya so na, ya fadamun ” momy tace sakarya! Baki dai iya kissa ba kawai zaki ce. Har akawai namijin d zai raina mace? Bare ke da kyanki da komai, amma dai ki vari zamuyi magana dake zuwa da safe, na fada miki jikin dadynku ne ya motsa, gashi ma anyi masa waya mimi tayi hadari. Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci, bayan likita ya gama dubashi. Na’ima cikin sauri tace “sis mimi din ce tayi hadari momy? ” tace eh itace, sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu. Na’ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji’un! To ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace, dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin jiki. Na’ima tace Allah sarki sis mimi! To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra’ayin mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu, Na’ima tace a’a momy kar ta mutu, tunda dai mun samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min ba, tace shikenan zanzo da safe. Na’ima tace Yauwa gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai nazo din, sukayi saida safe. Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi, cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki? Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman, da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari. Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci, sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta, sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani ‘yan kudina. Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane farin ciki nake samu gurin ‘yarta da har zan dinga bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa uwata. Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba’ayi ba, tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji, sauri nake zan fita. Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al’amuransa bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka. Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya, shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa, amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta. Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da qyar ma tadan kur6i ruwan kunu. Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba. Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe rabonki da al’ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai. Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki cewa kina da ciki ne? Kice masa a’a shawara ke damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani, kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata. Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko, ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho’ to kina shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani kamar wani dodo? Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga

Chapter 15 of 32