Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana zaune tana jiranta. Momy kinji abinda na sameshi yanayi? “me? ” inji momy. Na’ima ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi. Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace, da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake. Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole zaiji shakka. Ki barshi bari yazo. Na’ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy ta yi shiru tana ta kallon Na’ima cikin matuqar mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara mutunci kawai. Na’ima ta kalleta. Da kin barshi kawai momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara in taka masa birki. Ta tasa Na’ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai, yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace, bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida momy Nafisa ta zauna, sannan tace “lfy” shine wato Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to zaka iya bani ‘yan mintuna muyi magana? Ya hada tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to zuwa nayi inji laifin da Na’ima tayi maka da har zaka soma wulaqanta ta daga kawo ta. Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin. Ya kalli Na’ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta? Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason matsala. Tayi harkarta inyi tawa. Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye yana kallon momy tare da cewa, “au dama baku sani ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso. Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa, damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk nufi? Ya kalleta, ban gane ba. Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna Na’ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, inji masu magana. A gabana kk fadin bakason ‘yata? Yayi guntun murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane, saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba’a masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na farar mace nake so. Kinsan kowa da ra’ayinsa. Qila da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni, kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son takura. Ta kalli Na’ima, tashi muje. Na’ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai momy, ta dube shi a qufule. Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu, sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama irinki ce, tafi son ‘ya’yanta akan na kowa. Ni dai kunji ra’ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin Na’ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na’ima tana ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa, sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace yakeso ba? Na’ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da zaki ja ra’ayinsa. Na’ima ta dan ta6e baki tallafe kanta sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba, ma’ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata bilicin din ba. Momy ta dafa Na’ima, cikin sigar lallashi, karki damu Na’ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana, domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke saka fari. Na’ima tace, to kafin ta wuce saida ta tabbatar hankalin ‘yar tata ya kwanta, ta nuna mata cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana sai abin da tace masa zaiyi. Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na’ima cikin damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke. Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za’ayi da wannan dankalin? ‘Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi. Na’ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan yazo yai magana. Na’ima tace, ni bance sai kinyi min lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na’ima kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar, Na’ima ta kasa sukuni. Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa. Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi suke mata a wuya. Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta, don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa. Tana fadin, na yarda honey. Cikin matsanancin kuka, Na’ima ta kira layin momy, wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy. Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na’ima ba nace zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa?? Momy ta tambayi Na’ima. Ta rantse, sannan ta ci gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na’ima ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar auren Abbas. Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki, Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai? Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo ba, za’a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa kawai kuka yi. Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din, basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki shanye. Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata zage-zage, wai shi za’a kawo wa raini da rashin mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko wata daya ba’a yi ba za’a ce har tanada wani ciki? Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun, tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan al’amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje! In ba zakije ba, in tafi. Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha. Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi tunda fitar bana shiri bane. Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace, iroro kana ina ne ynxun? Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji. Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, “lafiya dai kazo nan? Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti. Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata. To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata. Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun daga ynxun. Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba, kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace 6era. Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, “kai kanaso ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane, Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai, shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi, Allah ya bata lfy. Ameen ya rabbi, ina fata ‘yan sandan sun baku jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud yace, ‘yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan rabin sa’a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba. Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan meye? Kaje ka samo wacce zatayi jinyar ta, domin kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina bane, nan ya sanar dashi komai, likitan yace, shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea gurin ta. Ina nufin ‘yan dubiya. Likitan ya sassauta murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole ne ta zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali. “Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun ta farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka saiku kula sosai. Tashi kuje, za’a zo a dabi jinin naka ynxun. Ismail yace, to nagode likita. Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud, yace vari ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a hankali ya tura dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta tana varci, ya juya ya koma kan kujera, zamansa keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli mai shigowar, Namiji ne da riga fara, irin wadda likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa. Yace. Kaine Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace, Na’am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi da wasu ‘yan qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin lokacin sallah. Bayan la’sar, sai ga babban wan su Ismail yazo, lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka shiga ya duba ta. Har lokacin bata farka ba, bayan sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari. Ismail Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In ta warke ka maida musu ‘yarsu, Ismail bayason doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da haka suka kai qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma ya koma ciki. Duk fargaban Ismail, in ta farka baisan dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai fuskanta ba. Kuma shi gaba daya ma zaman asibitin ya gundure shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account number da tace ya tura mata. Suka gaisa, bayan ya daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi. Yace, kiyi haquri hajiya, kaina ne yadau zafi. Ban tuna ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu na makaranta. Insha Allahu dana sanar da malam Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai gobe. Ynxun dai jini za’a qara mata. Tace, an samu jinin ne? Yace, eh, nawa ne za’a sa mata. Tace, Allah ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu. Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da zai koma dakinsu, sai kurum ya hango innarsu Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata takarda. Ya jira har saida suka iso gurinsa, sai dai da alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa, wannan maganin shi kadai dubu daya da dari bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa? Qawar tace dama nice ke, tunda ta samu dan qwarin jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai dai babu mai bashi amsa. Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama mahaifiyar tace take son in tura mata account number na, nace mata banida shi, amma zan turo mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai, Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi sallama. A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa hajiya Account number din, bada jimawa ba ta kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi sallar magriba, yanason sai yayi isha’i zai dawo don haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar isha’i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci. Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har zuwa shigowar wannan matsalar. Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace, nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take? Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa kacemin Mahmud? Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba, sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi. Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita? Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba. Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu’a, ki roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan. Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi. Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi. Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba. Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka hada da Addu’a. Zamu taya ka, wata rana sai labari, ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in tafi, gidansu rabi’a zanje. Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen. Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba? Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu goben.! Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala don yin shafa’i da wutirinsa tare da da addu’o’insa daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan saudatu bashir. Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace, kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen, inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya. Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin zamansa shiru ya isheshi. Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za’a yi mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace, naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace, haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa? Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya, hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan zuwa anjima. Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya. Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta turo kudi a account din makaranta zanje in cire. In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka kwantar da ita akan gadonta tare da maqale qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis, likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya doctor salis yace ma Ismael, “yar amanarka zata warware. ” Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka. Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula ‘yar fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce, daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun gode, Allah ya saka. Sukace Ameen. Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna. Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, “ina zan san abin da ya janyo. Kai sama’ila yaya abin ya faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan. Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja “Mtsss” sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne kaji cikinsa. Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa. Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da rabi’a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka akan wani super market. Yace ma dan acha6an don Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace, amma ba dadewa zakayi ba ko? Daidai lokacin da ya tsaya, A’a insha Allahu bazan jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga mashin din. Ya shiga tafkeken super market din tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci

Chapter 17 of 32