Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gefen gadon. Cikin qarfin hali irin nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa, ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance dukkansu. Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace “sauda.” tace Na’am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama. Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado. Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da naji ‘yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji. Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen, tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari, gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja Anjima. Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari koken Na’ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta soma kiran Na’iman. Cikin sauri Na’ima ta daga har lokacin kuka takeyi. Na’ima wai kkce Abbas ya mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah. Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya. Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na’ima tace to. Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp. Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya 6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa. Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar, sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana kallon su. Sannan tace musu, “sannunku da zuwa. Ku yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta harareta, cikin 6acin rai tace, “au dama in kinji a ta6a qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum kuzo mu shiga hajiya ladi. Suka shiga Na’ima ta zauna a gabansu tana cewa, kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace gidanki. Har Na’ima ta kawo musu abin sha da cincin, su diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum Na’ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba. Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi. Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace, hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa’ar sarakuwa ba, alamu sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka hajiya mairo gdn danta mansur? Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada, ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son jama’ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya kuma qanqame abin hannunsa. Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu! Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta da son jama’a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine gaba kura baya damisa. Na’imar da bata samu kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa. Haka kuwa washe gari sai Na’ima ta sake jin bugun qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil. Cikin ‘yar fara’a mai kama da yaqe tayi musu sannu da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki. Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa? Na’ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne, Na’ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya shigo kusan shida na yamma. Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace, an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata. Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar qannensa su fahimci wani abu. Ta tura qofar falon ta bude. Na’ima ta shiga cikin fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a fusace, “lafiya? ” A tsorace kuma cikin faduwar gaba tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan min anan! An dade ba’a gane cewa, Tsakanin mu akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko? Na’ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi. Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba. Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk lokacin da ‘yan uwana suka zo wani yayi kuka dake, na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai! Na’ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito, sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan. Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na’ima bata tanka ba har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce, mun wuce, Na’ima bata daina kuka ba bare ta amsa. Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na’imar kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace, sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a mata. Samira tace, mu ma da zamu taho ba tace mana komai ba. Aisha tace, ku dai kuna da matsala wlh, ba kuga tana ta kuka bane? Tayi tsaki, ta miqe ta nufi dakinta. Ita dai ko a cikin ranta, bata so Bros Abbas yaci zarafin matarsa ba. Domin ta ba ta tausayi lokacin da take ta kukan. Na’ima kuwa kiran layin momy nafisa tayi, amma bata daga ba. Don haka sai ta tura mata saqon waya kan cewa, ita fa ba zata iya wannan auren ba. Domin mimi ba qaramar sa’a tayi ba, da bata kasance matar Abbas ba. Don Allah ki ceci rayuwa ta. Sam ynxun na haqura da son Abbas. Saqon yaje sama da minti goma sannan kiran momy nafisa ya shigo. Na’ima ta tashi zaune, ta tallafe kanta mai matuqar sarawa, sannan ta daga wayar, momy tace, Na’ima yaya ne? Na’ima ta soma kuka. Momy tace kashh! Ke kullum Sallamar ki kenan kuka? Sake dukanki yayi? Na’ima ta sanar da momy zuwan mahaifiyar sa da qannensa. Momy tace, tirqashi! Abin harda danginsa? Na’ima tace, momy kizo ki daukeni don Allah. Momy tace gobe zamuzo da hajiya nana. Na’ima tace, don Allah mommy kuzo. Tace karki damu zamuzo. Kwanan Zainabu biyu a asibiti, amma babu labarin alhaji. Innar ta kuwa taci bashi yafi na dubu goma. Sawunta hudu a gidan Alhajin, amma bata samunsa. Don haka sukayi shawara da aminiyarta yalwa cewa, in an sallami Zainabu su wuce da ita gida kai tsaye, in yazo ya biya kudin saita koma. Baban su Zainabu kuwa yaje ya duba ta sau daya, bai kuma komawa ba. Zainabu kuwa kuka takeyi akan ba zata koma ba, domin kwanakin nan da bata gidan, duk da cewa a asibiti take yafi mata zaman gidansa. Hankalinta bai sake tashi ba, saida ‘yan gidan su Ismail suka zo duba ta, taji wannan fatu din tana cewa innar su wai sunzo duba matar Ismail ne tayi hatsari. Innar su Zainabu tace, ai yayi aure ne? Nan su fatu da sauran matan gidan suka soma ba innar su Zainabu labari. Ai maigidansa ne ya bashi ‘yarsa, ita kuma bataso, ta gudu shine tayi hatsari. Daga nan Zainabu bata iya ci gaba da saurarensu ba, ta shiga rera kuka. Daren ranar bata runtsa ba, kenan Ismail yananan asibitin yana jinyar matarsa. Ita dai zata so ta sake ganinsa a rayuwar ta ko da daga nesa ne. Ta san lallai ta rasa Ismail tunda har yayi aure. Ta yi ta tuno kalaman da yake fada mata na irin tsantsar son da yake mata. Washe gari da safe innar ta taje famfo inda zata wanko ‘yan kayan Zainabun, ita kuma zainabu ta sauko a hankali, ta dauki zani guda daya daga cikin zannuwanta ta yafa ta nufi fita. Matar kusa da gadonsu tace, ina zakije Zainabu, ko bandaki zaki shiga? Tace a’a zan dann tattaka ne, sbd jikina duk ciwo yake sbd zaman guri daya. Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu sannu tana ‘yan waige-waige. Daga baya ta yanke shawarar tambayar dakin ‘yan hadari. Dan haka sai ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa. Sannan tace, don Allah inane dakin ‘yan hadari? Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace “mata.” Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga, dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa bata ganota ba. Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin damuwa tayi shi, don ko ‘yar shinkafa da waken da innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito ta sake zuwa dakinnan na ‘yan hadari. Bata shiga ta qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan da tace mata kece matar malam Ismail? Kai kurum ta girgiza alamun a’a. Ita kuma sai take qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin da yasa tace a’a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar. Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin. Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi’a, budurwarsa, don ta san ta, itama ‘yar islamiyyarsu ce, sai dai ita, ‘yar babban aji ce, ajin da Ismail ke koyarwa. Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba. Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna. Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya har takai gurin da Nurses masu kula da wannan sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu ta daburce, ta soma inda-inda, “am zan..zanje can ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya zanyi. “ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace, daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a dakin ‘yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake, can dakin ‘yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail. Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko? Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke ajiyar zuciya. Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta, dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi’a kuma ta zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado. Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail data gani, hawaye suka soma sharara akan kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi’a ta tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin dake gurin. Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi mata, sai suce, “Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo asibiti ko sau daya bai leqo ba. Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona ma kanki asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun farko da kk qi nuna masa so. Zainabu tace, to ni bana sonshi, kuma bazan koma gidansa ba. Inna tace, sai kiyi tayi. Ga faten doya nan da mai wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace, bana ci. Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi da tuwon da wannan ta kusa damu din ta bani Zainabu ta zame ta kwanta, idanunta na qara hasko mata Ismail dinta ke baiwa matarsa abinci a baki. Ta tabbatar da irin son da Ismail yake yi mata, da ace ita ce, qila ma sai ya tauna a bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun rasa mai kawo musu, sai dai maqotansu na kwanciya su sam musu. Da wannan takaici Zainabu tayi varci mai cike da mafarkan masoyinta Ismail. Mahmoud ya kalli rabi’a kinyi qoqari domin mara lafiyar nan bata ci komai ba tunda tazo asibitinnan sai yau da kika kawo mata. Azaton Mahmud Ismail baijishi ba yanayin jinjina ne ga masoyiyarsa. Sai kurum yaji Ismail ya cafe da cewa, ni kaina na jinjina miki rabi’a domin a tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai abinda basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce, kuma farfesunshi rabi’a tayo da alayyahu. Haka nan ta dai yo ne don batasan me zata yi ta kawo ba. Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana saida ma masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam mata zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai data qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha sannan tace zata kwanta. Tun lokacin da likitan ya taimaka masa suka shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada masa cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan ruwa, kuma sun saka mata pampers ita da wata nurse. Harma mimin tace, su sake canza mata rigarta. Yaji dadin sannan ya dawo da murna sun samu admission islamic ya nema. Mahmud kuma sai suka bashi English baiso ba amma hakanan ya haqura. Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka fito, Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma wadannan Nurses din na gefensu da zai wuce, sai dayar take tambayarsa dazun wata ‘yaruwarka ta gane gurin ku ko? Ismail yace, da yau she kenan? Tace dazun nan kuma nice nayi mata kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru kodai rabi’a ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina dinnan ko? Nurse tace, a’a ita daya ce tace, tana nan asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai. Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace, naga lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton tana tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya sake dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take nema? Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira. Yace to gsky bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu dama munga har kwatancenka anyi mata tace kaine. Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi wata baquwa? Tace A’a sai dai ina neman wata alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta.”ina saauraronki” yadan rusuna sbd Mimi bayayin magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu. Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd suna ne mai dadi da ma’ana. Allah yasa halayenki su rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta farko data soma kar6ar musulunci a tarihi. Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci. Sa’annan itace ta haifawa ma’aiki ‘ya’ya guda shida. Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta. Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba musulmi ba yasan mai tsira da Aminci. Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za’a yi hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane. Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce masa qala ba. Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi. Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba. Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa. Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan ya nufi gadon mimi yayi mata addu’o’i ya shafa mata, sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado masa, to ko wacece? Ko kuma cikin ‘yan uwanta ne? Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane. Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba. Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo, kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo. Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau. Mimi tace, yaya don Allah za’a iya yimin wanka? Yaya Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, “yaya ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami. Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta sunsuna. Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija, don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta. Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? “Don Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai domin wani ciwon zai shigar ki. No related posts. POST COMMENT 22 Let God take the burden off your shoulders. Connect now. GodLife OPEN 22 Ismail ya miqe “yaya ni dai bari in barki da ‘yar rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi, zan koma gida da

Chapter 19 of 32