Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
kusa da ita ta riko hannun ta , tana mamakin abunda ya firgita hajiya da jininta ya hau sosai, duk sai taji tausayin hajiya ya kamata, batasan lokaci da ta fara zubda hawaye ba , burinta kawai Allah ya sada ta da maihaifiyar ta wataran koda amafarki ne. Digan hawayen da hajiya taji ahannu ta yasa tafara motsi tana kokarin bude ido, ahankali harta bude idonta, ta kalli kursum dake kuka, afirgice ta tashi ta ruko hannun kursum tace “Kursum ashe baki mutu ba” Agigice kursum ta dago ta kalle ta………..:oops::oops::oops::oops: Rudani, tashin hankali, faduwar gaba, lokaci guda ta shiga:oops: *Xarah Bêê* KURSUM By ~ Xarah Bukar page Hankali tashe Tace “hajiya nice sumayya ba kursum ba, amma sam hajiya batasan inda kanta yake ba, ihu sunan kursum kawai take, doctor ne ya shigo dakin da sauri jin ihu ta, ya tsira mata allurar bacci. Ya kalli kursum yace”wace mai sunan da hajiya ke kira? “Tace nima dai doctor bansani ba,ko adangi banji mai sunan ba, “ya nisa yace tabbas mai sunan tana da alaka da shock din da hajiya tashiga, amma karki damu idan ta tashi she will be normal, “tace toh dr mungode, ya fice. Itama taja kujera ta zauna tayi tagumi, tunanin ta daya wace kursum din da hajiya ke ambata, dan tunda take da sumy bata taba mata xance wata kursum ba. Ranta abace ta iso gidan aminiyar ta tana kuka, meerah dake baje afalo daga ita sai bom short da bra ga uban giya agabanta, ” ta ajiye cigarette din hannunta, ta karasao wanjenta dasauri,”tace zee mi aka miki? Miya faru? Kukan mi kike? Zee takara fashewa da kuka tace “girlfriend wai yau ni ya yazid ya mara akan wata shegia yarinya, “meerah ta kwalala ido waje, tace babe gayamin wace yar iska ce yanxu in maki maganinta, “zee ta gyara zama ta zayyane mata komai akan sumy, “meerah tayi kwafa tace lailai galfrnd, akan small brat dinnan duk kika birkeci, yanxu abunda zamuyi shine gobe muje har school din da aka jefar da ita a bauchi mu binciki past dinta, dan na tabbata she will have some dirty secret da take boyewa,” zee tace nima dai I dnt trust her, dole mu samo abunda zamuyi using against her, “meerah ta zuba giya a cup ta mika mata,tace just drink diz banason ganinki haka plz, chill up babe akwai casu anjima, ” ta amsa tayi murmushi, ita dai tana son meerah sosai cox she is always there 4 her. *wace ce meerah* Asali sunanta Amirat oyekola, haifaffiyar garin lagos ce, sun hadu da zee a lagos state university inda department dinsu guda, ganin zee yar masu kudi ce marar wayo yasa ta shishige mata har suka zama best friends, duk wata harka ta shaye shaye da clubbing saida ta koya mata, taso tasa zee a harkar bin maza amma taki yadda. Sun kare degree ta tattara tabiyo zee kano har gidansu, acewarta ta gaji da talaucin iyayenta, “haka tayita harkar kawo samari gidan, daga karshe hajiya ta koreta tabar gidan, wani daga cikin samarinta suka kama mata gidan da take yanxu. *cigaban labari* suna zauna a parlour suna hira “yace umma barin leka huzaifa kwana biu bamu huda ba, tayi murmushi tace a daren nan, gayamin gaskia dai kodai gurin sumy zaka, dannan lura da kallon dakake mata dazu, ya sosa keya, “Allah umma wajen huzaifa zani kuma yarinyan nan babu komai tsakani na da ita,”tace to son saika dawo, “kaima dai yakamata kayi auren, ga abokinka ya dade da aure shiyasa ma ya rage zuwa nan,”yayi dariya yace umma karki damu very soon xanyi, ya fice. Zaune suke suna cin abinci sukaji knocking din kofa,ta tashi da sauri ta zura hijab taje ta bude,”tace ya yazid yau kaine a gidanmu sannanu da zuwa, “yayi dariya yace amarya bakya laifi, ya karasa ciki, huzaifa yace “aina dauka yauma baza ka zoba aiki yama yawa, yazid yace toh gashi nazo kuma dama yunwa nake ji, nazo adaidai, “huzaif yace to ai xama zakayi mu baje, “salma dai dariya kawai take dan tasan basa wasa da abinci. sun gama Ci suka hau hira, huzaifa ya yace “angon zee wai yaushe xamu kawo maka itane, yazid ya bata rai yace “zee ko matsala, banma gayama ba hajiyarsu ba lafiya tana asibiti, huzaifa yace kace suruka dai ba lafiya, “yazid ya kaimai duka yace nifa bance maka zan auri zee ba, “Salma tace gaskia ya yazid zamu biya gobe mu dubota duk da bana shiri da xee, “huzaifa yace kodan darajan amintakar su da umma yakamata muje, “yazid yace to Allah ya kaimu goben, xan biyo sai mu wuce, ya musu sallama dare yayi ya wuce. samira ta kawo masu komai da zasu bukata, wajen 10pm doctor mallik ya shigo dubata, “ta tashi jikin da sauki, ya kalli kursum yace,”data farka ba tace komai ba? “tace eh, ya mika mata magunguna, yace wanna joltan valsartan 160 mg na hawan jini ne, zata na sha sau daya a rana, Aspirin cardio 100mg zai taimaka wajen narkar da jini daya hau kanta shima sau daya zata sha, ku tabbata tasha su, “tace toh Dr nida kaina zanna bata, “yace jikin nata yayi sauki gobe xan sallame ku, “tace Allah kaimu ya fice. tashi tayi ta ninke kayan sallarta ta ejiye gefe, ta karaso gaban hajiya dake Zaune tayi tagumi, “tace hajiya sannu kina bukatan wani abu?? tace taimaka min in watsa ruwa kawai. “ta rike hajiya har toilet ta watsa ruwa tayi alwala ta fito tafara sallolin.. *washe gari* Duk sun hallara a asibiti umma na zaune kusa da hajiya suna xantawa kasa kasa, kursum na gefe tana hada musu kayansu waje daya, shi kuwa oga yazid ya kame kan kujera yana waya ya zuba mata idanu,”da sauri ya tashi yace umma barin je in shigo dasu huzaifa suna waje” tace to my son,” ta kalli hajiya tace bakwa hira da sumy ne ?? naga tunda mukazo tana gefe tayi shuru, hajiya taya tsine fuska tace “ina ruwana da ita” umma tace haba hadiza tunda kin rasa yarki Ai ya kamata kija sumy ajiki tamkar ke kika haifeta, tsaki hajiya tayi tace nifa banason ta, xan jata ajiki kawai dan inji labari kursum daga bakinta. yazid ya shigo tare da huzaifa da salma, suka gaishe da umma da hajiya, umma tace angama amarcin kenan tana zolayan salma amarya, huzaifa yana dariya yace kakus (sunan dayake Kiran hajiya) an tabo file kenan, ya jiki ? hajiya ta harare shi ta tace” nagaya ma ban tsufa ba har yanxu am 16 kana cemin kakus, gaba dayan su saida suka dara, sai sannan suka lura da kursum dake dariya daga gefe, huzaifa ya kalleta yace yammata daga ina ? tayi banza dashi, “yace umma ina kuka samo yarinya mai kama da kakus, yazid yayi caraf yace ai yarta ce, zai sake magana hajiya ta wullo mai harara, ba shiri yayi shuru, “salma tace nikam nasamu kawa, takarasa wajen kursum, tace kawata bakya magana ne? kursum tayi murmushi tace “inayi mana yakike ? ni sunana sumayya, “salma tace gaskia naji dadi saninki dama banda kowa agarin nan, kursum tace u are welcm nima am happy to meet u. ………huzaifa na gefe yana waya, yazid ya karaso wajen su ya zauna, ya kashewa kursum ido yace “my witch anyi sabuwar kawa an manta dani koh ?? ta bata rai ta murguda baki tace ina ruwana dakai, u are my enemy not a friend, yayi dariya yace bakisan enemies na zama best frnds ba, “salma dai bunsu tayi da Ido, “huzaifa ya gama yace”umma nizan wuce ana naima na a office, tace to son kayi kokari ma, ya kalli hajiya yace kakus get well soon, “salma ki zauna tare da kawarki later zanzo in dauke ki, tace toh , yabi kursum da kallo ya fice, yazid daya lura da abokin shi, yatashi fuska a daure yace umma sallaman sai yaushe ne? nafara gajiya da zaman asibiti, “hajiya tayi caraf tace kaga yaro da rigima, ai tunda bagaka zee ba dole ka damemu, idan ka gaji kaje waje ka zauna mana, “a fusace ya fice yayi waje dan yasan halin hajiya, “umma tace kwantar da hankalin ki, keda baki da lafiya miye na tada jijiyar wuya, ” kursum dake jinsu bata ji dadin abunda hajiya tace ba, kaman ta fita ta bishi amma ba dama… Baba shehu ne ya shigo da takardar sallaman hajiya, yace su zo su wuce ya sauke su gida, kursum da salma suka kwashi kaya, umma ta taimakawa hajiya ta mike suka fice, “yana zaune cikin mota, umma tashigo tace muje koh, yace su hajiya fa ? tace suna motan shehu, muje gidan “yace toh umma. sun iso gidan, samira ta fito da sauri ta gaishe su ta kwashi kaya tayi ciki dasu, kursum da salma suka shigar da hajiya, baba shehu ya juya ya koma office. “umma tace son bazaka shiga gidan bane, “yace umma barin jiraki anan kawai banason shiga ga mitar hajiya ga kuma zee da rigima nasan tana ciki, “tayi dariya tace yau kuma zee ake boyewa, to barin shiga agurguje in fito, ta wuce shi kuma ya karasa garden ya zauna. ……. Sauri suke ta karaso gida ta canxa kaya su wuce bauchi , tun sassafe su kayi niyya tafiya, till dawn party din da sukayi yasa su bacci har rana, meerah tace galfrnd kiyi parking a waje kawai ki shiga ki canxa kaya ki fito mu wuce kar muyi dare, ” zee tace karki damu babe bazan jima ma,” meerah tace yauwa karki manta da kudaden dazaki kwaso, tace toh hajiya da umma na sama adaki suna xantawa, kursum da salma suna parlour suna hira, “samira ta sauko tace antee sumy umma na Kiran ki, kursum ta tashi da sauri ta haura sama, ta shiga dakin da sallamanta, umma ta amsa da fara’arta tace yauwa sumy yayanku na waje ki kaimai ruwa yasha,”tace toh ta fice, taje kitchen ta dauko bottle water ta fita haraban gidan, can ta hango shi shinkide kan kujera, ta karaso, “idon shi rufe da alama bacci yake, tayi murmushin mugunta ta bude roban ruwa zata tsiyaya mai a fuska, “karaf taji ya rike mata hannu gam saida ta tsorata, ya mike tsaye yana kallonta,”tayi karfin halin cewa miye haka na rikemin hannu, yace ai yau bazan sake kiba saikin gayamin dalilin dayasa kike cemin am ur enemy, “tayi shuru batace komai ba. Agurguje tayi parking awaje, ta shigo gidan da saurin ta, gabanta saida ya fadi hangosu tare rike da hannu ta, wani irin bakin ciki ya mamaye zuciyan ta, wato yarinyan nan bazata fita harkar saurayina ba, lailai kuwa I have to destroy her once n 4 all, ta karasa parlour da sauri dan karsu ganta, bata ankara ba taji salma tace “zee daga ina haka ? saurin mi kike ?? “ta juyo a fusace tace I don’t owe u any explanation, dan kina matar abokin yazid dat doesn’t give u d right to interfere in my life, taja uban tsaki ta wuce, salma kam bataji haushi ba, tasa ba da cin mutuncin ta, dan farkon haduwan suma ce mata tayi she is 2 local tayi harka da ita. hmm ko dakin hajiya bata shiga ba ta wuce dakin baba shehu ta kwashi kudade masu yawa da papers na address din makarantar sumy, ta wuce dakinta tasa wasu matsatsun english wears marasa mutunci, ta sauko koh kallon salma batai ba ta fice, “salma tace Allah ya shirya, gaskia dai ya yazid baiyi saan mace ba. koda ta fito suna nan tare, saidai yanxu zaune suke da alama hira suke, tayi kwafa ta wuce waje, taja mota sai bauchi, meerah na magana ko kollanta batai ba, sharara gudu kawai take. kinyi shuru baki ce komai ba, tace to ya yazid me kakeso ince, nidai kawai I don’t like u datx all, yayi dariya yace karya kike nasan kina sona, ta bata rai ta tashi zata tafi, yace my witch karki tafi zauna in baki labarin rayuwata, “ta kara tamke fuska ta zauna tace ina jinka, “yace kinsan dai no one is perfect koh ? ta girgiza kai alaman eh ,”yace ni nan da kike ganina nayi making alot of mistakes arayuwana wanda har yau am still regretting, “akwai wata yarinya dukda na manta sunanta, but I will never forget her smiling face, ya gyara zama zai cigaba da magana umma ta fito tace mai su tafi , ya tashi ya killi kursum yace next time idan mun hadu zan karasa miki, “jikinta a sanyaye ta bishi da ido tace toh, ya wuce, tayi shiru tana tunanin, wato ya yazid bai manta da sumy ba, amma meyasa bai dawo gareta ba ko sau daya ba ?? jiki ba kwari ta shiga ciki, salma tace ke kuwa daga kai ruwa kin makale, kursum tace aiko ban dade ba, “muje dakina muyi hira zaman parlour ya isheni, suka wuce daki, salma ta dale gado tace “anya sumy ya yazid ba sonki yake ba, “kursum tace haba dai, aini ko sona yake bazan yadda ba, saboda he is really good at playing women’s heart, “salma ta kwalalo ido tace dama kinsan shine ,”da sauri tace a’a, salma tace au nayi mamaki ne, dan ya huzaifa ya taba gayamin ya yaudari mata ba kadan ba amma yanxu kam ya daina, mata basa gabanshi.”kursum ta sauke ajiyan zuciyan, aranta tace Allah yasa dagaske ya shiryu. Sun iso bauchi around 6pm direct makarantar suka wuce, suna zuwa har office din gimbiya Hafsatu aka gaisu, gimbiya na zaune rai abace sai hada tarkacen ta take waje daya, suka shigo da fara’arsu suka ja kujera suka zauna, ta kalle su tace kuna bukatan wani abune yan mata ? zee tayi shiru, meerah tace mu yan garin nan ne, dama cigiyar kawarmu muke, munaso kidan bamu details akanta na zamanta a makarantar nan. gimbiya ta nisa tace miye sunanta ? zee tace sumayya tanimu bawa, “gimbiya ta kare masu kallo aranta tace karya suke, dan sumy bata da wasu frnds sai kursum, kuma daga gani yan bariki ne, kila sunji labarin dukiyar da ubanta ya mutu ya bar mata shiyasa suke naiman ta suci arziki, toh Basu isa ba nice xanci arzikin nan. Tace yammata sai dai kuyi hakuri record dinmu confidential ne bama fitar dashi, “zee zata fara roko meerah ta tabo ta tayi shuru, meerah ta bude jakar xee ta fiddo da makudan kudi ta tura su gaban gimbiya tace ko nawa kike so zamu kara miki ki gayamana abu akanta kawai, “gimbiya tace lailai yau na hadu dayan duniya, ta masu kallon banxa tace ku fice mun daga office kafin insa ayi waje daku, Meerah tace toh xamu tafi, ta dauki paper ta rubuta mata contact dinsu incase in ta canxa mind din gayamasu wani abu, suka fice. gimbiya taja tsaki ta dauki paper tasa a dust bin, ta kwashe kudin tasa a jakar ta, “dama naiman kudi take ido rufe, saboda gwamnati tayi seizing licences dinta na makarantar akan zarginta da ake na saida dalibai,” tayi murmushi tace sumy amfanin ki yazo rayuwata, ta binciko file din sumy ta kwashe address din gidan su…….ta kyalkyale da dariya tace gobe sai Kanon Dabo :oops::oops::oops::oops:Hmmm tashin Hankali kursum get ready gimbiya na hanya. *Xarah Bêê* *Dedicated to bady social* ~Luv u all~ [05/09 12:52 pm] xarah bukar : KURSUM By ~Xarah Bukar Page Dadaddare huzaifa yazo daukan salma, har bakin mota kursum ta rokata,suna ta hira da dariya kaman dama sunsan juna”ta gaida shi ya amsa da fara’a sa yana tsokanar ta da autar kakus (hajiya),tayi dariya tamasu sallama ta koma ciki…….. Bayan kwana biyu jikin hajiya yayi sauki, “kursum ta shigo dakin rike da magani da ruwa, tace hajiya lokacin shan magani yayi “ta ya mutse fuska tace maganin sai dacin tsiya a dole kawai nake sha, tayi murmushi ta zauna tabata maganin da ruwa tasha sannan ta gyara mata kwanciya, zata fita hajiya tace Sumy kawarki da kukayi accident, ta rasu iyayanta sun sani kuwa? Dam gaban kursum ya fadi, ta dawo ta zaune tace Ai marainiya ce bata da kowa, dama gidannan zamu zo, “jikin hajiya yayi sanyi,da gangan dama ta tambaye ta Dan taji labarin yar’ta ,ta nisa tace Allah yaji kanta amma ya akai tayi surviving a skull din tunda kince bata da kowa “kursum dake sharar kwalla tace abun tausayi ko kayan sawa gimbiya bata siyamata saidai Sumy ta bata akayanta,excursion ma baa zuwa da ita,tunda bata da kudin biya,” hajiya tace wace Sumy CE ke bata kaya? Kursum data gano kuskuren magananta tace ni mana Nike bata kayan. Ran hajiya ya gama baci, aranta tace wato diamonds din da akaba gimbiya cinyesu tayi,alhalin ko wana diamond worth 2.5 million ne ,shine ko kayan sawa bata iya siyawa yar’ta, wani irin tsanar gimbiya taji……”ta kalli kursum tace ke tashi ki ficemin daga daki ,”kursum tace daga hira kuma sai kora kaman nayi laifi ,ta tashi sum sum ta fice, tana mamakin halin hajiya wataran ayi hirar arziki wata ran kuwa ba mutunci… Kina ganin akwai Hope kuwa,kwana biyu da dawowan mu amma shuru matan nan bata Kira ba, “meerah tace haba zee duk kin tada hankalin ki, idan ma bata kira ba zamu samo wani mafita, zee tace ai dole in damu dan yanda nake ganin taketaken ya yazid zai iya rabuwa dani ya komawa Sumy, meerah taja tsaki tace karfa ki manta tun farko dama baice yana sonki ba,kece kika makale mai, so don’t be surprise idan ya rabu dake, zee ta bata rai tace koda na makale mai aiya kulani, kuma yanxu Gidan su zani coz nasan he is still angry with me ko calls dina bai picking ,ko kallon meerah batai ba ta suri Jakarta ta fice……… Zaune suke a dinning suna lunch, Umma tace “son hurry up ka wuce airport saura 1hour flight din abbanka yayi landing, banaso ya jiraka, “yace toh umma ina gamawa xan wuce,” bugun kofa sukaji anayi da karfi, umma ta kwallawa hajara (mai aiki) kira taje ta bude,”tana budewa zee ta ban gajeta ta shigo ciki tana kwalla wa ya yazid kira batama lura dasu ba, umma ta bata rai, azuciyan ta tace dama nasan sai crazy girl dinnan, dan haushi fasa cin abinci tayi ta tashi zata wuce, “yazid yace umma baki ci komai ba ? Tayi banxa dashi, sai sannan zee ta lura dasu,ta karaso da sauri tace baby ashe kana nan shine kayi shuru,ta kalli umma tace sannu,” umma ta balla mata harara ta wuce. Taja kujera ta zauna ta tace “baby miyasa mom dinka ke treating dina lyk nobody kaman ba future in-law taba, “ya tamke fuska yace” Ai baki taba gaishe taba iyaka cinki sannu, sannu ko ba gaisuwa bace, ta turo baki tace “nifa ko babana bana gaisarwa balle ita, bata isa ba, yazid daya gama fusata ya mike tsaya yace uwartawa CE bata isa ba ? hankali kwance tace Yes, ” Rai abace yace ban taba sani u are crazy ba saiyau ya dauki car keys zai fice, tayi saurin riko hannun shi ta rungumo shi ta baya tace yes am crazing in love with you, “a fusace ya tureta,ya kalle ta yace diz is not love,u are only obsessed with me, infact nida ke it over……what ta fada a firgice tace are u breaking up wit me? Yace yes,ko juyowa baiba ya fice abunshi. Duniyar gaba daya tai mata zafi, kuka take rusawa ta shiga fasa plate da cups dake kan dinning ,tabbas tasan saboda Sumy ya rabu da ita,amma tayi alkawarin bazai taba samun taba cox sai tayi destroying life dinta, sai zage zage take kaman tababbiya. Umma dake daki ta fito da sauri jin fashe fashen yayi yawa, ganin zee na displaying madness yasa ta kira hajara tayi waje da ita…..zee tace basai anyi waje dani ba, nasan hanya, kuma nasan makircin kine yasa ya yazid ya rabu dani, “Allah ya shiryeki kawai umma ta iya ce mata, taja tsaki tabar gidan. Office din baba Shehu ta wuce, yana zaune yana waya ta banko kofa ta shigo tana kuka, ba shiri ya ajiye wayan ya karaso gabanta yace zainab kukan mi kike ? Ina kika shiga kwana biyu ban ganki ba ?” Cikin kuka ta tsara mai komai har zuwan su bauchi, baba Shehu yayi dariya yace halina dake u ar alwyz crazing bakya Abu da tunani, “ta bata rai tace Baba ka daina cemin am crazing ina da hankali, I don’t knw y mutane ke cemin banda hankali, yayi shuru yana tunani, koda ya auri jamila (maman zee) tana da mental illness harta rasu, shiyasa sumtymz zee take abu kaman mai hauka, ya nisa yace ,” am sorry auta ta….ta kyalkyale da dariya tace to baba yanxu miye mafita, yace karki damu zan tura private detective dazai binciko miki komai akan ta, tun daga ranar da aka kaita school din, abunda kikeso kenan koh ?da fara’arta tace eh, yace toh yanxu abu biu zakiyi idan kinaso komai ya tafi daidai, da sauri tace me ? Yace dole ki nunawa yazid kin hakura dashi sannan kuma kija Sumy ajiki yadda bazata gane abunda kike shirin yiba, ta kwalalo ido waje tace”gaskia baba bazan iya, yace toh ke kikasani tashi ki tafi,”ta ma rairace fuska tace na yadda xanyi, yace toh ki wuce gidan kafin in zo tace OK ta fice da murnan ta…… Shima sai murmushi yake dan perfect tym yake jira ya kawar da Sumy once n 4 all. Washe gari, hajiya na zaune a parlour tana cin abinci, zee na kallon TV, kursum ta sauko zata wuce office kusan kwana biu bata jeba, ta gaishe da hajiya ,”ta amsa a yatsine ne ,zee dake gefe tace my sis har zaki tafi,kursum da taji maganan bambarakwai,tace eh ta masu sallama ta fice. Zata shiga mota taji hayaniya abakin gate, ta karasa wajan da sauri, mai gadi daya hango tana zuwa, ya kalli matar dake tsaye da Da niki nikin akwatuna, yace yauwa ga madam Sumy nan zuwa kwayi magana dan bazan bari ki shiga gidan nan ba,”gimbiya tayi shewa tace gidan nan shiga daram. Tana leka waje sukayi ido hudu da gimbiya hafsatu,dam gabanta ya fadi ,gimbiya data gama tsorata tace baki mutu ba dama…….. Da sauri kursum taja ta gefe ta tace mi ya kawo ki gidan nan, gimbiya tace aike xan tambaya kin mutu miya kawoki nan,INA Sumy ? Kursum tace ai Sumy CE ta rasu bani ba, yanxu haka yan gidan sun dauka nice Sumy, long story ne idan mun zauna xan baki labari ,”ta bude Jakarta ta zaro makudan kudi ta mikawa gimbiya tace ga wannan ki koma bauchi yanxu nan, zamuyi waya……gimbiya ta kece da dariya tace Ai baki isa ba, babu inda zani, kursum tace koki tafi ko in kira securities su fitar dake daga nan, “ta kara kecewa da dariya tace ai ke zabi ya ragewa, ko ki barni in zauna a gidan ko kuma inje in tona miki asiri,kinga dagani harke mun rasa , balle ke da baki da wajan zuwa. Kursum data gama kulewa tace Baza ki zauna a gidan ba, kiyi abunda zakiyi. Gimbiya tace toh zakiga Abunda zanyi kuwa, ta bangaje maigadi ta shige gidan da gudunta, Agigice kursum ta bita tana cewa tsaya!! Tsaya!! Muyi magana, amma ina…..gimbiya tayi nisa batajin kira, harta karaso bankin parlour ta tura kofa ta shiga…….. Tashin sense :oops::oops: *Xarah Bukar* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ kursum 56 to 58 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 [06/09 10:53 AM] Xarah Bukar : KURSUM by ~ Xarah Bukar Page Hankali kwance ta tura kofan ta shiga da sallaman ta, hajiya ta amsa tace waye ? Zee ta juya taga gimbiya, tace baiwar Allah aida baki zoba kin kiramu ta waya, sai sannan gimbiya ta gane zee, itace marar kunyan nan da sukazo naiman labarin sumy, taja tsaki tace bansanki ba kuma ba wajan ki nazo ba, hajiya tace zee kinsanta tane ? Zee tayi shuru, hajiya tace bakuwa gurunwa kikazo ? Caraf kursum ta shigo tace gurina tazo, kuma a gidan nan zata zauna, hajiya tace bazata zauna ba, Ai nan ba hotel bane daza ki kawota, gimbiya tace haba hajiya nice fa gimbiya makarantar da Sumy tayi harta girma, yadda na kulan miki da ita bai kamata ki Kore niba, “ran hajiya ya gama bacci, wani irin tsanar gimbiya taji a zuciyar ta,aranta tace wato matar nan itace ta maida min kursum abun tausayi ko kaya bata siya mata. Ta nisa tace koda kike riketa aiba kyauta bane kudi aka baki, na baki minti biyar ki ficemin daga gida….. Gimbiya ta kalli kursum tamata signal kotasa baki ko kuma ta tona, ” kursum tayi Gyaran murya tace gaskia hajiya saidai kiyi hakuri, dole gimbiya ta zauna agidan nan, tunda gidana ne, “hajiya data gama fusata tace to na yadda ta zauna amma ba nan tare damu ba, ki kaita can bangaran masu aiki ta zauna, kursum zata kara magana hajiya ta daka mata hannu tace nagama magana, ta dogara Sandar ta tahau ra sama…….kursum tace nizan wuce office ta fice,da sauri gimbiya tabi ta tace amma dai hajiyar nan bata da mutunci, kursum tace karki CE haka dan kuwa bata da matsala, kiyi hakuri ki zauna a part din masu aiki kafin insamo mafita, idan kika Kama kanki zakiji dadin zama da ita, makauniya ce ba gani take ba,gimbiya tace kina nufin duk kwalliyan datayi da uban dauri da bakin glass din bata gani ? Tace kwarai kuwa,tun wajan shekaru 18 da suka wuce tasamu matsalan ido, gimbiya tace shikenan ki tura masu aikin su gyaramin dakin, kursum tace toh kayan ki ma xansa ashigo dasu, xan wuce aiki saina dawo. Gimbiya ta koma parlour ta zauna, zee ta kalle ta taja tsaki tace ashe bakin ku Da ita shiyasa kika ki bamu details akanta, gimbaya tace yarinya ni kike jawa tsaki ? Zee tace eh mana ke wace CE ? Gimbiya ta mike taje har gabanta ta kama mata kunne gam tace idan kina takama ke yar bariki toh ni sunana na biyu bariki, ki kiyaye ni danni ba tsarar wasanki bace,kina jina ? Zafin da taji yasa Ba shiri tace eh naji kisake mun kunne, saida taga kunnen yayi jajir sannan ta saki ta koma kan kujera ta baje, “da sauri zee ta tashi tace muguwa ta gudu sama……….. Agurguje plz…….. Kursum ta koma bakin aiki, takan kiran inna taji ya hanifa, tsakanin ta da yazid sai wasa buya bata barin su hadu dan ta tabbatar ta kamu da son shi. tsoranta daya bai wuce kar asirinta ya tonu ba. Hajiya ta warware sosai, bata shiga harkan kowa a gidan kullum tana makale adaki, kursum tana shigowa gaisheta ta bata magani. Yazid ya kanzo

Chapter 4 of 6