Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
sai hawaye kawai, gaskia ya tausayawa sumy ba kadan ba, duk laifin hajiya hadiza ne, da yanxu sumy na gida agabanshi hankalinta kwance. Yana taba sumy hakuri akan karta damu jarabawa ce ta ubangiji, komin wuya akwai dadi, ya ajiye masu shopping din daya masu sa’annan ya masu sallama zai koma kano, karshen shekara zai dawo ya dauketa, ya dauko makudan kudi yabasu suna ta godiya.. Daddy kam yayi niyyan kwana biyu, amma bazai iya jure ganin sumy halin da take ciki ba, shi kanshi daurewa kawai yake amma ranshi a bace yake, aka ya tattara ya koma kano, Hajiya hadiza na hakimce a parlour a zaune tana jiran shigowan daddy gidan, dan ta kwarara mai buhun bala’in data saba akan yaje ganin yar tsintuwo bada izinin taba…. Yana shigowa ta gane muryanshi da sallaman da yayi bata ma damu da yanayin shi ba, ta hau zaginshi damai rashin kunya ta ko ina, daddy kam kasa magana yayi ma saboda bakin ciki ta riga tamai yawa, nan take shikam ya yanki jiki ya fadi sai jin faduwan mutum tayi tim akasa…..:oops::oops: Ta kwallawa samira (yar aiki) kira maza ta fito Alhaji ba lafiya, samira ta fito da gudunta tana hajiya, alhaji ne ya fadi da alama ma rai yayi halinsa. Hajiya a rude tace “samira kiramin wayar shehu nasan baiyi nisa ba,kirashi mukai alhaji asibiti….. Baba shehu da sauri ya iso gida,suka sa alhaji a mota sai asibiti likitoci sun yi iya kokarinsu, amma rai yayi halinsa (kulli nafsin za’ikatul mauti), abun tausayi hajiya da baba shehu sai kuka suke yau sunyi babban rashi. Doctor yasamu baba shehu da hajiya ya tambaya su ya akayi suka bari har zuciyan alhaji ya buga alhalin sunsan yana da ciwon zuciya, hajiya tayi tsuru tsuru bata ce komai ba illa kukan da take tayi dan tasan tabbas itace silan ciwon zuciyan alhaji, yanxu gashi ya tafi ya barta, kuka kawai take tana nadaman abunbuwa data shuka mai…….. Nima kasa rubutu nayi saboda mutuwan daddy ba karamin girgizani yayi ba…… Rip *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By ~Xarah Bukar Page ~ *Kano* Mutuwa daddy ba karamin girgiza jama’a tayi ba, mutane da dama sun sanshi da halin kwarai da taimakawa talakawa, Sam ba ha’inci ko xalinci a lamarin sa……mutane sai shigowa ta’aziya suke, baba shehu na daga waje yana amsan gaisuwa… Hajiya kuka kawai take dakyar take ma iya amsa gaisuwan da ake mata, hajiya mario ce tadawo gefen ta tana kara bata baki akan tayi hakuri addu’a ya kamata tamai bawai kuka ba. Zainab ma tayi rashin daddy ba kadan, dan daddy ne kadai yake kwabarta da mata nasiha sosai game da yanda tadau rayuwa da zafi, yau gashi tayi babban rashi. Tana kaunar shi tamkar shiya haife ta.. Har gida yazid yaje yama xee ta’aziya, ya tausaya mata sosai dan yasan yadda suka shaku da daddy ba kadan ba, wani irin sonta ya karaji a zuciyan shi….har dakin hajiya yaje ya mata gaisuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa dan yanxu tadan rage kukan nata, dazai wuce ta bashi sako ya kaiwa mairo tare da shi mai Albarka. ……..yazid kam yana jin haushin yadda hajiya ke cewa umman sa mairo sai kace a kauye Ina laifin maryam ma…… Bauchi Yan makaranta kam sai shirye shiryen xana jarabawa shiga ajin karshe ake babu wasa kowa ya dukufa da karatu, sumy kam ciki ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe, “Sam bata da labarin mahaifinta ya rasu wata bakwai da suka wuce. Kursum da gimbiya kadai suka San da rasu war shi, sunki sanar matane akan lalular da take tare shi. Sun fiso saita haihu sannan su gaya mata….. Bayan kwana biyu, sumy ta tashi da nakuda mai tsanani, da gudu kursum ta kira gimbiya sukai rushing dinta zuwa hospital , Allah yasa haihuwan taxo mata da sauki ta haife kakkyawan baby gal wanda babu bambamci da ubanta kaman an tsaga kara an karya…washe gari likita ya sallamo su suka dawo… Ranan suna ba wani bidiri akai ba, duk da gimbiya ta gayyato mutanan ta, yarinya kam taci suna hanifa son kowa kin wanda ya rasa. Sumy kam sai murna take, ba karamin son hanifa take ba, dan yanxu tama daina jin haushi mijinta asalima ta yafe mai duk abunda ya mata…tana fatan Allah ya hada hanifa da ubanta wata ran. Kursum ce ta shigo daki ta kwantar da hanifa da tayi bacci, tace akwai abunda nakeson gayamaki sumy amma kiyi hakuri bamu gayamaki ba tun lokacin saboda cikin ki, Allah ya yayiwa daddy rasuwa tun wata takwas da suka wuce…. Innalillahi wai inna’ilaihi raji’un kawai sumy take furtawa, kuka take na tashin hankali shikenan daddy ya tafi ya barta yanxu bata da wani gata, yanxu ya zata koma gida da zama, dan bata manta da azabar da tsanar da hajiya ke mata ba tun tana karama, hawaye kawai take tana Allah yaji kanka da rahma daddy……Kursum kam tashi tayi tabar dakin dan bazata iya ganin kawarta cikin yanayin da takeba…….itama tasan tayi rashin daddy ba kadan ba, dan shine ya mamaye mata gurbin uban da bata dashi. *kano* Gaba daya family din daddy sun hallara a parlour din gidan tare da lawyer (alkali) sa dan karanto will (wasiha) da alhaji ya bari kafin ya rasu…… Baba shehu kam sai murna yake dan yasan dole yasamu abu mai tsoka, dan tun rasuwar daddy ya maida kanshi managing director din oil company dinsa. Mommy da xee suma suna zaune suna jiran barrister yafara bayani.. Barrister shu’aibu ya fara da addu’an sannan ya fara bayani yace tun lokacin da alhaji yakamu da ciwon zuciyan yasan bazai dade ba, shiyasa yazo ya sameni ya bani takardar nan, acewarsa duk ranar da baya duniya yanaso acika masa burinsa dake rubuce anan…… barrister ya Bude yafara bayani kaman haka Ni Alhaji Tanimu Bawa na damkawa ya’ta sumayya dukiyata kashi hamsin acikin kashi Dari, sannan na bata matsayin managing director na oil company dina da kuma gidan da muke ciki duk na mallaka mata su. Acikin kashi hamsin daya rage na bawa hajiya hadiza kashi ashiri, kashi goma na bawa Zainab, kashi goma na bawa shehu sai sauran kashi goma akai masallaci da gidan marayu. Ina fatan iyalaina zasu cikamin burina , sannan banyi haka danna matawa wani ko wata rai ba…..bissalam Barrister ya gama karantawa sannan ya mikawa mommy takardar, yace alhaji yamai xancen nan da shekera daya atura driver yaje ya yaje ya dauko sumy daga makaranta, mommy tace to insha Allahu xaai haka, barrister yamasu sallama yatashi ya tafi. Baba shehu kam fuskan nan babu annuri ko kadan, wato haka alhaji zai sakamai duk irin kokarin dayama company dinsa shine zai bashi 10% kawai acikin uban dukiya daya tare, kuma harda ba yar’sa director din company din, yarinya karama da komai bata sani ba, “Yayi murmushin mugunta da tunanin halaka yarinya kafin ma ta shigo gidan nan.. Hajiya kam bata damu da abunda tasamu ba asalima abun duniya bai dameta ba, takai cinta daya shine yadda alhaji ya bawa sumy komai daya mallaka alhalin bama yar’sa bace ta jini, zata bar sumy ta zauna a gidan amma tayi alkawarin making life dinta miserable. Zee sai murna take, dan batama yi expecting samun wani abu ba, tunanin ta daya shine Wacece sumy ya take, itadai tasan sumy diyar alhaji da mommy ce amma bata taba ganinta ba. *Bayan shekara daya* Sun gama exams sai shirye shiryen tafiya suke, kursum dake wasa da hanifa tace sis yanxu kina ganin idan nabi ki gidanku ba matsala , nidai ina tsoro kar hajiya tamin wulakanci ta kore ni, dan yanda kike ban labarin halinta na rashin kirki nasan tana iya wa. Sumy tace karki damu nasan yanxu ta canza tunda shekaru sun ja, kuma makauniya ce ba lailai bane tasan kina gidan ba…… An turo driver daga gida daukan su, sai sallama suke da kawayen su da sauran malaman makaranta , suka shiga har office din gimbiya hafsatu sukai mata sallama ta dauko wani dan karamin box ta bude taciro wani hadadden pink diamond da take ajiye dashi wajen shekaru goma sha takwas da suka wuce ta damka wa kursum a hannu, tace yaudai na cika alkawarin, kursum tace wanna na miye kuma, gimbiya tace matar data kowa kine tun kina jiririya tace in baki idan kin tashi tafiya kya iya siyarwa ki samu na rike kanki, Kursum tai mata godiya sosai suka fice, sun iske driver na jiran su, suka shiga mota… koda suka shigo cikin gari sun tsaya suka shiga gidan Inna sadiya (mai kitson su) suka gaishe ta sosai ta amsa da fara’arta dama tasan da zuwan su, sumy ta mika mata hanifa, Inna ta amshe ta sai wasa take mata tace karku damu zan rike muku ita har kudawo daukan ta dama nagaji da xaman kadaice. ….. Kursum tace Inna mungode sosai, da munyi settling zamu zo mu dauke ta yanxu ki rubuta mana number wayan ki yadda idan mun isa gida zamu kira, dan yanxu ba waya ahannun mu, “Suka bata kudi masu yawa wanda zai ishe su kafin su dawo, suka kama hanya sai kanon dabo… amota sumy sai kukan rabuwa take da hanifa, tabbas tasan barin hanifa wajan Inna shine daidai dan tasan hajiya bazata taba yadda da cewan tayi aure harta haihuwa ba, shiyasa ma tabar ta hannun Inna kafin tasamu yi mata bayani. …… Sun shigo kano kenan, sumy tace gaskia yaka mata kindan gyara fuskan ki kodan kwalli ne kisa a ido, kursum tace kinsan ni bana kwalliya asalima ko kayan kwalliya ban dashi, sumy ta mika mata handbag dinta tace bude kidau powder ki sha fa, Daidai lokacin da kursum ta amshi jakar sumy wata katuwar motar petur dake tafe ta bangaje motar su, kofan side din da kursum ke zauna ya Bude ta fado kan titi rike da jakar sumy, sai birgema take harta buge da wani katon dutse, sumy da driver kam suna cikin mota dake kamawa da wuta sai gangarawa motar take cikin daji harta bugu da wani katon bishiya tayi exploding baammm kawai kake ji. … :oops::oops::oops::oops: *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By ~Xarah Bukar Page ~ Kursum ta farka taganta a gadon asibiti, duk jikinta ya duk jikinta ya kurje ga farin bandage da aka daura mata a kai dan tsayar da jinin dake zuba, sai kuka da ihu take tana Kiran sunan sumy. Da gudu wanda ya tsince ta a hanya ya kawota asibiti yaje ya kira doctor malik yana gayamai patient din ta tashi amma kaman bata hayyacinta… Doctor ya shiga yana mata magana, amma ita kam ihu kawai take tana Kiran sumy, ya tsira mata allurar bacci ya fito. Yace Bala daka tsince ta babu waya ahannunta ko wani abu dazai sa musan family dinta ko inda take zama, Bala yace gaskia babu sai dai ko jakarta xaa duba, dan koda na ganta akwai karamar jaka tare da ita, ya mikawa doctor malik jakar, suka zazzage jakar daga kayan kwalliya sai wani wallet mai kyau suka bude, pictures din daddy kuda biyu Dana kursum ne aciki sai wani karamin littafi an rubuta sumayya tanimu bawa. Doctor malik yace ai wanan hoton alhaji ne, kuma ba shakka wanna yarinyar yar’sa ce amma to ina taje harta samu accident, ya kalli Bala yace mungode sosai da taimakon da kayi, nasan family din yarinyan kuma yanxu zan kirasu awaya suzo su dauketa, nine family doctor din su. Bala ma yamai godiya sannan ya wuce. Doctor malik ya kira mummy yamata bayanin komai, tace tabbas yar’ta ce dan dama tun wajen kwana biyu daya wuce akaje dauko ta daga makaranta, amma sukaji shiru basu iso gida ba, an duba hanya an gano motarsu tayi hatsari ta kone sai gawan mutum biyu akone kawai aka gani, kuma ance mana tare suke da kawarta daga makaranta, doctor yace kawar ce ta rasu da driver kenan, dan yanxu haka sumy na nan kuma jikinta yayi sauki sai dan ciwon da baza’a rasa ba, tayi mai godiya sosai tace zata turo baba shehu yaxo ya dawo da sumy gida.. Kursum ta tashi sai dai ba ihu yanxu sai kuka kawai take, doctor ya shigo yana gayamata ai kawarta da sukai accident tare ta rasu dan haka yanxu ta shirya kanta dan kanin mamanta yazo daukanta suje gida, ya dauko wallet da pictures din yabata hade da jakan gabadaya sannan ya bata magunguna wanda zata sha, yace sumy ki tabata kinsha maganin nan saboda your body is still weak, tace to nagode sosai doctor, Kursum kam hankalinta duk ya tashi shikenan sumy ta rasu yanxu ya zata yi , gashi kuma ana tunanin itace sumy alhalin kuma sumy ce ta rasu ba kursum ba, amma kuma dole ne ta tsaya a matsayin itace sumy kodan ta samo wa hanifa gata da yancin ta. Ta fito ta iske baba shehu na jiran ta, dukda batasan shi ba saida tace kawu ina wuni, ya bita da kallon banza sannan ya amsa a kwasale yayi gaba abunshi tana binshi a abaya, a zuciyan ta tace tab wato family dinnan babu sauki, lailai zata daura damara dasu dan kuwa baza tai tolerating ko wana nonsense ba. Suna isa gidan yayi parking mota suka fito, masha Allahu kawai take fada dan kuwa bata taba ganin katon gida mai kyau kaman wannan ba, wani tausayin sumy taji, Allah yaji kanki kawata kuma insha Allahu hanifa sai ta samu gatan xaman gidan nan Daram. … Hajiya da xee suna zaune a parlour suna jiran isowan su sumy, baba shehu yafara turo kofa sai kursum abaya, tana karasowa cikin palon xee da mum suka tashi tsaye afirgice suna kallon ta……. Nima afirgice nayar da biron rubutuna dan na tsorata da yanayin mom, ita da bata gani miyasata firgita haka..:oops::oops: *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ kursum 36 to 50 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 KURSUM By ~Xarah Bukar Page ~ Kursum ta dukusa har kasa ta gaishe su, hajiya kam hankalinta bai tare da ita, mamaki kawai take yadda sumy ta zama kekkyawan budurwa dan koda tasan ta abaya ba wani kyau garetaba sai fari kawai …….abangaren xee kuwa faduwan gabanta sai karuwa yake, yaudai duk takama da kyawuta taga Wace ta fita kyau da komai, wani irin tsanar kursum taji azuciyanta. …….:evil::evil: Hajiya amsa adakile, ta kwallawa samira kira, taxo da sauri tana gani hajiya, tace kikai sumy can gidan baya kusa da dakin masu aiki sai ta zabi dakin data ke so, samira tace toh. Kursum da haushi hajiya ya isheta ta, ta karaso cikin palon ta xauna tace tunda gidan ubana ne babu wanda ya isa yasani xama dakin masu aiki, dan haka nima a main house zan zauna, ta tambayi samira ina dakuna suke da kuma wana dakine yafi kyau da girma a gidan, tace antee dakuna asama suke kuma dakin daddy yafi kyau da girma tunda ya rasu babu wanda ya shiga, kursum ta mike tsaye ta karewa hajiya da xee kallon sannan tace samira kaini dakin daddy dan yanxu yaxama nawa in ga wanda ya isa ya hanani…:? Hajiya kaman tafasa ihu dan takaici, lailai yarinyan nan wato ba kyau kadai takara ba harda baki tayi, yazama dole insa mata ido saboda….. Da daddare Abba da umma ke zauna a parlour sai hira suke suna darawa, umma tace gaskia yakama in leka hajiya mun dade bamu haduba aiki yamin yawa. Abba ya kalleta yace wai ke bana hanaki shiga harkar hadiza ba, kinsan sarai banason matan nan saboda Sam bata da mutunci, kowa yasan itace sanadiya mutuwan mijinta , umma tace haba alhaji ya za ai kace haka, lokacin mijinta ne yayi……. bata ida magana na ba yazid ya shigo da sallaman sa, sanye yake da uniform dinsa na pilot wanda ya kara fito da ainuhin kyau shi, ya fada kan kujera yana wai na gaji, umma ta kalle shi tace my son hope dai you are okay, banason ganinka da stress , Abba yayi tsaki yace wlh maryam ke kike kara sangarta yaron nan, idan baije aiki ba so kike yana xaman gida ko me, shida wataran zaiyi aure ya kula da iyalansa……yauwa nama tuna shehu yazo min da batun diyar shi Zainab dinnan kwana kin baya, kun dade kuna soyyaya amma baka ma xancen aurenta kuma ma dai at your age ya kamata ace kafara tunanin fara iyali. Yazid ya tamke fuska, yace gaskia abba ni ban shirya aure ba dukda inason xee, koda zanyi aure sai nan da shekera daya, ya tashi a fusace ya wuce dakin shi. Abba ya kalli umma yace kinga halin son dinki ko , tace karka takura mai tunda yace ba yanxu ba, ni xee dince ma banaso ya aure Sam bata da kamun kai, yace to ina ruwanki bashi ya gani yanaso ba kuma ni banga rashin kumun kan taba, babanta abokina ne kuma yana da kirki sosai, umma dai shiru tayi bata ce komai. *************************** Bayan kwana biyu jikin kursum ya warware ta samu sauki sosai tayi fresh ta kara kyau, sai dai zaman kadaice da take babu mai shiga harkanta a gidan sai samira kawai dan ita ke kawo mata abinci har daki, tayi tsaki ta kwallawa samira kira, taxo da saurin ta tace antee kina bukatan wani abu ne, kursum tace babu komai tambayan ki zanyi wai babu masu shigowa gidan nan ne, naga tunda na zo banji an shigo ba, gida sai kace kurkuku……samira ta gyara zama tace antee ai indai gidan nan ne ana wata biyu babu wanda ya shigo, yaya yazid kadai ke xuwa wataran umman shi takan zo wajan hajiya dan kawarta ce sosai, kursum ta nisa tace Waye kuma yaya yazid wajan wa yake zuwa, samira tace ai saurayin antee Zee ne kuma suna son junan su sosai bare ma antee zee tana iya mutuwa akanshi, kursum ta bata rai tace tashi ki fita ban tambayi ki wannan ba, sumsum ta tashi ta fice da saurinta……ita ko wani farin ciki taji ta maimaita sunan yaya yazid, gaskia sunan ya mata dadi. .. :mrgreen::mrgreen: Da yamma barrister shu’aibu yazo har gidan ya damkawa kursum takardun gidan da komai data mallaka amatsayin itace sumy, sannan yace mata ta shirya gobe zata fara aiki acompany din babanta amatsayin managing director, tamai godiya sosai ya masu sallama ya fice. Hajiya dake gefe sai hararan kursum take ta eye glass dinta (oho dai batasan kina yiba)…… Baba shehu ma ya cika yayi fam , ya kalli kursum yace yanxu sumy abunda ya kamata shine kibarmin komai a hannun na tunda na dade in charge, xan naima maki admission ki shiga university tunda iya kacinki secondary skull kuma baki da experience na managing babban company, kursum shiru kawai tayi batace komai ba ta haura sama abunta. …. Baba shehu yayi murmushin samun nasara da alaman yarinyar ta yadda da Zancen shi….:mrgreen::mrgreen: Washe gari da safe kursum ta shirya cikin hadadden pink and white suit mai shegen kyau na kardashian collection tayi rolling kanta da karamin pink veil mai kyau, ta dauki handbag karamin mai kyan gaske mai tambari versace tarike a hannu, tabi stairs tana sauka atsanake hankalinta kwance, ji tayi an bangajeta har tana naima fadowa kasa, tana daga kai tayi ido hudu da xee, da ganinta kasan she is high danko kayan jikinta bana kirki bane, xee tace ke dabbar ina ce ko bakiga ina hawowa bane, banza bakauya taja tsaki ta wuce, kursum kasa cewa komai tayi ta wuce abunta tana mamakin hali irin na xee ta tabbata daga club take kuma till dawn tayi, dan samira ta taba gayamata xee bata fiya kwana agida ba, bata da aiki sai clubbing, kuma baba shehu da hajiya suna sane amma babu mai kwabarta…. Allah ya shiryeta kawai tace ta karasa waje ta shiga hadaddeyar motar ta kirar 2016 Buick Cascada……….driver yaja ta sai company. Babban Company ne mai huge twenty-story office building, all curved glass and steel, an architect’s utilitarian fantasy, with Tanimu bawa oil & investment written discreetly in steel over the glass front doors. Tana shiga officials din suka karaso suna gaishe ta tare da mata congrat as the new MD , ta amsa da fara’arta tana masu godiya, Mr dabo ya karaso gabanta yace madam am your PA let me excort u to ur office, ta bishi har office din amma sai tayi mamakin :oops::oops: ganin office karami kaman gidan kaji, ta juyo tace Mr dabo how comes ina MD zaa bani karamin office haka, yace madam kiyi hakuri ba laifin mu bane, kawunki yace abaki nan tunda ba wani sanin kan aikin kikayi ba, kursum tace lailai ma baba shehu wato itace ta dace danan, aikuwa zanyi maganin shi…. ..tace Mr dabo kaini office din baba shehu yace toh… Suna shiga taga office dinshi tankameme kaman aljarnar duniya komai na office din ya burgeta tace Mr dabo nan nake so as my office ka kwashe tarkacen kawo ka canza mai wani office sannan kuma ka kawo min file din ko wana employee zan fara aiki na, yace to angama madam Ya fice. … Kursum zauna kan office chair tana swivel din kanta, sumy kawai take tunanin, Allah sarki kawata da yanxu kice anan bani ba, Allah yaji kanki insha Allahu zan rike maki hanifa tamkar nina haifeta… Banko wan kofan da akayi ne ya firgita ta, baba shehu ne fuskar nan tamke, babu annuri ko kadan, yace “I won’t let you disrespect me, I’ve been working day, noon, and night for this company, busting my hump since before you were born.” who are you to throw me out of my office? Kursum ta mike tsaye ta karemai kallon sannan tace, the early bird doesn’t always catch the worm, Warming a seat in this company doesn’t mean you’re working, baba shehu daya gama kulewa ya nunata da yatsa yace, how dare you, you snot- nosed brat! Kinsan dawa kike magana kuwa, ta kara kare mai kallo tace, I dare because I’m the heir to my father’s company. From now on, I’m going to monitor the performance of every employee; including you. No, not including, but beginning with you. If you don’t like it, the door is wide open enough. Understand? or should I draw you a picture?” Baba shehu kasa cewa komai Cox kalamanta ba karamin girgiza shi yayi ba, sai yanxu ya tabbatar kawar da yarinyan nan will not b easy, amma dole ne ya naima mafita kafin taza ma doom dinshi Hmmmm *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By ~Xarah B Page ~ Zaune yake a office dinsa yana waya da xee tana ta zuba mai shagwaba kaman tana gabanshi, ta turo baki tace baby kace zaka zo Jiya baka zo ba I couldn’t sleep Cox I was thinking of u kuma your fone was off, ta kara shagwabe fuska, yace am sorry dear I was kinda busy ne xanzo anjima, kar kiyi fushi kinsan I love you alot……….Abba ne ya shigo office din yasamu kujera ya zauna jiran ya gama wayan, yazid yace baby xan kiraki later, tace toh my love, kisses & hugs dear …… Abba yace miye amfanin love dinnan da bai da future, ance kayi aure kace you are not ready, kudai yaran zamani halinku sai ku, yayi murmushi yace abba abar xancen auran nan plz, nace muku am not ready, abba yace kai ka sani yanxu dai ga document din shares din mu na Tanimu bawa oil & investment company, Ina so gobe ka kaiwa new MD na company din tasa hannu, ya dire mai document din ya fice abunshi , yazid ya bude yana dubawa yace abba kenan wato dan aikin nan ma bazai tura wani ba dole dai ni zai aika……..:evil::evil::evil: Hajiya ce zaune a falo rike da sandar ta, tasha bakin glass dinta, tunanin kawai take yadda za ta fidda sumy daga gidan dan Sam bata yarda da ita ba, tana suspecting akwai abunda take boye masu, tasha leka dan karamin ramin dake jikin kofan dakin ta, ta ganta rike da wani hoto tana kuka tana cewa ki yafeni hakan da nayi shine kadai mafita, hajiya ta tashi da saurin ta haura sama, ita dai tana son sanin wana mafita sumy take nufi, ta bude dakin kursum ta shiga ta fara bude bude da binciken amma bata ga komai ba, side drawer na gadon taxo budewo ta ji muryan samira abakin kofa tana cewa Antee kin dawo ne, da sauri ta maida glass dinta ta fito daga dakin, samira tace hajiya kece aciki ashe, ko kallonta bata yi ba ta bi gefe ta wuce tana dafa bango dan karta fadi…….. Samira mamaki ne ya cika ta, matar da bata gani miye na shiga dakin daba nata ba kuma da alama ma bincike take, ikon Allah kenan…..:oops::oops::oops: Kursum zaune a office tana hada files waje daya dan yamma tayi zata wuce gida, ta kira Mr dabo tace mai ya kwashe duka files din ta gama dubasu sannan tamai sallama ta wuce parking lot tasamu driver na jiranta a mota, ta shiga ya ja…. Sun hau kan babban titi driver ya hango hold up sosai, babu alaman motoci na motsi, yace madam hold up dinnan yayi yawa amma akwai wani one way gaba kadan, bari inbi damu tanan, kursum tace toh duk yadda kayi ta cigaba da kallon sabuwar wayar da ta siya dazu kirar iphone 3G king’s Button… Daidai lokacin da driver ya danno kan motar, dai dai lokacin da shima ya karyo kwana sai ji kake kiiiiiiiiiii……..ko wannan su yaja birki, kiris ya rage suyi accident.. Sanye yake da uniform dinsa na pilot yasha kyau da alama shima daga aiki yake ya fito fuska tamke, tun kafin ya karaso driver ya fito da sauri yazo yana bashi hakuri, amma ina shi kam baisan hakuri ba sai zazzaga masifa yake yace kai wawan ina ne, koka taba ganin inda akabi one way, hanyar da ake fita shine kake shirin shiga tunda baka da hankali, driver dai sa hakuri yake bashi…. Tana daga mota take jin hayaniyan su, wato driver na bashi hakuri shi ko guy din kara harzuka yake, lailai ko zata yi maganin shi, ta bude kofar motar ta fito da tafiyar ta mai daukan hankali ta karaso ta bayan shi tace Mr man ko Kaine devil himself sai haka, ana baka hakuri kana kara harzuka, toh karka hakura idan titin taka ce sai mu gani, taja uban tsaki, ya juyo a fusace fuskan nan ba annuri, ya kare mata kallo tas yace ni kike gayawa wai maganar banza , ita ko hankalinta bai ma jikinta dan ba karamin tsorata tayi ba, tabbas babu tantama wannan shine wanda sumy ta aura ya yaudare ta ya gudu, sau daya ta taba ganin shi amma bazata taba manta wa da fuskan shi ba, ba

Chapter 2 of 6