Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
shiri ta saita kanta, ta wurga mai harara tace kwarai kuwa dakai nake kai din banza Waye kai da bazaka hakura ba, Driver mu tafi plz karya hakura din yana iya kwana anan tunda hanyar tasa ce, ta juya ta barshi nan tsaya yana mamaki karfin hali irin nata, lailai ko sai ya koyawa mata hankali, ya ga ubanwa ya tsaya mata da har ta isa ta gayamai magana, yayi kwafa yaja motar sa yabar wajen. Suna cikin mota tana tunani iri iri, gaskia dole ta naimo Mr devil kodan ta koyamai hankali, wato hankalin shi kwance har wani kyau yakara, kibiyar tsanar shi ce ta soki zuciyar ta, tayi murmushin mugunta afili tace count down to my revenge has ended, it’s time for pay back Mr devil…… Driver yace madam mun iso fah naga kinata magana ke ka dai, tace ahh ba komai barin sauka saika gyara parking, yace toh. Ta turo kofar parlour da sallaman ta, hajiya da xee na zaune ko kallo bata ishe su ba, tana gaishe su ko amsawa basuyi ba suka bita da harara, ta haura sama abunta…. Xee da taci uban kwalliya da wasu matsasu kayan dake jikinta, ta kalli hajiya tace ni wlh na tsani yarinyan nan ga shegen kyau kamar aljana, ni wataran kina min kama da ita ma, hajiya taja tsaki tace ke daina hadani da mayya ni kaina na fiki tsanar ta, na gayamaki tsinto ta Alhaji yayi a titi, ko jini ban hada da ita ba……..zata kara magana hajiya ta tsayar da ita, tace surutun ki ya isheni haka, ba kince saurayin ki zai zo ba, toh sai kiyi zaman jiran shi ai, nikam na tafi daki……xee tace haba hajiya ki tsaya ku gaisa mana, tace nikam bacci zanyi ta haura sama abunta. Tun komawar shi gida, sallah kawai ya iya gabatarwa, ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi, abunda ya faru dazu gani yake tamkar a mafarki, wai yau shine little witch (sunan daya laka mata ) tama rashin M, lailai ko saiya making life dinta miserable sai tayi dana sanin cin zarafi da ta mai, wani irin tsanar ta yake ji, ya mike ya naushi bango a fili yace Game on little witch……….:evil::evil::evil: Hmmmm tashin hankali Masu karatu muje xuwa….. (Dedicated to Bady social KURSUM by ~ Xarah Bukar Page ~ Tana shiga dakin ta ganshi a hargitsi da alaman an shigo an mata bincike, ta kwallawa samira kira, taxo da saurinta tana antee har kin dawo kenan, kursum tace waya shigo min daki naga komai ba daidai ba, samira ta sosa keya tace Antee nima bansani ba amma dai naga hajiya ta fito daga dakin dazu…. Kursum tace hajiya kuma, ita da bata gani miya shigo da ita dakina, tayi shiru can dai tace tashi ki tafi zan naime ki anjima, samira ta tashi ta wuce….. Ta tashi ta gyara dakin ta kimtsa komai daidai , sannan ta bude side drawer ta dauko picture dinta ita da sumy da pink diamond dinta wanda su kadai ta tsira dasu ranar da sukayi accident da yake cikin aljihun trouser dinta tasa su, ta kalli pic din tana hawaye, rayuwarta da kawarta kawai take tunawa, tayi missing dinta sosai , yanxu tunanin ta daya shine yadda zata dauko hanifa daga Bauchi, ta tashi ta dauko wani karamin book din sumy inda Inna sadiya ta rubuta masu number ta akan in sun iso zasu kira ta, da sauri ta kwashe lambar tayi dialling………ringing daya biyu Inna sadiya ta dauka da sallaman ta, kursum tace Inna ina wuni ya gida, ya hanifa, nasan baki gane mai magana ba kursum ce…..Damm gaban Inna ya fadi gaba daya ta gigice dan bata taba tunanin kara jin muryar kursum ba, tace kursum dama baki mutu ba , aini dana je aiki makaranta gimbiya ke cemin ai kunyi hatsari kin rasu, kursum tace eh wlh munyi hatsari amma sumy ce ta rasu bani ba. Inna tace Allah yaji kanta, yanxu hanifa ta zama marainiya, kursum nace haba Inna kar kice haka, nice uwar hanifa yanxu bazan taba bari tayi maraici ba, insha Allahu dana samu lokaci xanzo in dauke ta, Inna tace to babu damuwa sai kinzo, gatanan kuwa tayi bubul da ita, kursum tayi murmushi tace Inna karki gayawa gimbiya ban mutu ba, kibarta amatsayin ni na rasu ba sumy ba, Inna tace toh duk yadda kikace, sukayi sallama ta ajiye wayan….. Driving yake hankali kwance, fuskar shi ba yabo ba fallasa, yasan rigimar zee idan baije wajen taba zai sha mita, ya iso gidan mai gadi ya bude mai gate ya shigo ciki…… xee data cika tayi fam a parlour, sai tsaki take ja, wajen awa hudu kenan tana jirashi ta kira layin shi switch off, ranta duk abace:evil::evil::evil: taji karar doorbell , ta kira samira taje ta duba waye, ta bude ta ganshi tsaye yana mata murmushin, tace yaya yazid sannu da zuwa ashe Kaine, yace yauwa samira ya karaso ciki, tana jin muryar shi ta tashi da sauri tana kukan shagwaba taje ta rungume shi. yace haba zee kukan mi kike haka, ta kara fashewa da kuka tace ba Kaine kaki zuwa ba tun dazu nake jiranka, yace baby kiyi hakuri yanxu nazo ai forgive me ? Kinji baby na yakara rungumeta tsam yana shafa bayanta, ita ko sai sauke ajiyar zuciya taje.. Basu ankara ba sai ji sukayi ana tafa masu lokacin guda suka saki juna suka juyo suna kallon ta, sanye take da black jeans da yellow top, sauko wanta kenan zata je kitchen ta naima wa kanta abun ci ta gansu makale da juna kaman ba gobe…. ta masu kallon up & down, tagane guy din sarai shine Mr devil wanda suka samu clash dazu, tace lovers of the year duk iskanci da kukeyi awaje bai ishe ku ba har sai anxo ana nuna hali a gida:?:?, shi kam yazid kasa magana yayi dan mamakin ganinta yake for d second time kuma a gidan nan, ta karaso gabanshi ta nuna shi da yatsa tace shameless man haka dai zaka kare da bin mata, dan iska kawai, xee data bata rai jin kalaman da kursum take gaya masu yasata karasowa da niyyan wanketa da mari amma ina kafin takai mata marin kursum ta rike mata hannu gam tace don’t you dare sis, jikina yafi karfin duka, kuma am advicing you to stay away from diz man cox he is just using you for his own selfish reasons, tayi tsaki ta wurgar mata da hannun ta wuce kitchen abunta….. yazid yace baby ina kuka samo witch dinnan ne, I hate her with passion, she is rude, zee tace diyar daddy da hajiya ce, shegiyar yarinya, mayya, Yar titi, agidan marayu daddy yasa mota, tana school ne sai yanxu ta dawo gida ……:? ya nisa yace baby barin wuce kawai, am not in a good mood, tace haba yaya daga zuwan ka zaka tafi, indai akan abunda ta fada ne kayi hakuri zan mata magana , yace sorry zee but I have to go, ya mata peck a cheeks ya wuce rai abace:evil: kursum da take hango su ta kitchen ta kara mata rai, ko miye na mata peck kuma in ba iskanci ba, zuciyar ta namata zafi …… (su kursum da karfin hali, mutum da budurwa shi karya soye ) *Xarah Bêê* kursum 51 to 52 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 KURSUM by ~ Xarah Bukar page Abincin ma kasa Ci tayi dan haushi, ta fito zata wuce dakinta zee ta finciko ta, tace ke yar titi ki fita daga ido na, ke har kina da bakin Kiran mutum dan iska, wayasan iskanci da kikayi a makarantar da aka jefar dake, ina baki last warning ki fita daga rayuwa ta…… kursum bata ce mata komai ba illa gyara rigarta da tayi ta wuce abunta, zee tayi kwafa tace lailai ma yarinyan nan, ya zama dole in binciki past dinta, xanje har makarantar da aka riketa in samu wani abu akan rayuwarta. … umma ce zaune a daki tana duba new designs dinta a laptop, yayi sallama ya karaso ya fada kan gado, tace my son daga ina haka a darennan, naga ma ranka abace, hop all is well ? yace ba komai dama wajan zee naje, nan take umma ta bata rai, ita dai bata kaunar zee ko kadan, dan farin cikin son dinta take nuna tana sonsu tare, ya nisa yace umma dama hajiya hadiza nada ya’ budurwa ?? Dam gaban umma yafadi dan tasan tabbas hadiza nada diya kuma yanxu ta isa zama budurwa, tace my son hajiya bata da diya tun wajan haihuwa yar’ta ta rasu, nasan dai alhaji yayi adopting yar yarinyar daga gidan marayu, zaman su yaki dadi da hajiya shine yakai ta wani boarding skull…. yazid yace ta dawo ai, ita nagani a gidan dazu, yarinyar sai rashin kunya da raina mutane, umma tayi dariya tace haba son daga ganin yarinya sai aibata ta, Allah umma dagaske nake sau biyu muna haduwa tana min fitsara, sam bana sonta:?:? umma dai dariya kawai take yadda ya dage shi baya sonta, sai kace ance ya so ta, tace son abbanka ya wuce England dazu, yayi trying line dinka switch off, yace eh wlh I was so busy ne, zan kira shi gobe, tace to yace dai karka manta gobe ka kai ayi signing document din daya baka dazu, yace toh umma barin je in kwanta good nyt, okay nyt my son. ******** sauri take ta wuce office dan yau ta makara kuma suna da meeting, harta fito daga daki ta kara komawa da sauri, ta bude side drawer ta dauko pink diamond dinta, tayi murmushi, ta san koba komai tana da abunda uwarta ta ajiye mata, ta saka pink diamond din jikin chain din wuyanta, ta fito tayi kicibis da hajiya abakin kofa amakale tace hajiya ina kwana, mai kikeyi abakin kofana ? kina son wani abune ?? lokaci guda take jero mata tambayoyi, hajiya data gigice ganin diamond din wuyanta yasata fara kame kame, tace daban kwana ba zaki ganin, shegiyar yarinya toh wuce wa xanyi ta wuce fuuuu har tana naiman faduwa, kursum dake tsaye tana mamakin hajiya, anya matan nan bata gani kuwa, ta rufo dakin ta wuce. hajiya ce a daki sai sake sake take da tunani iri iri, ina yarinyar nan tasamu diamond din nan, nasan ni kadai keda irinshi kuma na bayar dashi dadewa, wayarta ta dauko tayi dialling line din mairo dan tasan ita kadai ce zata bata amsar komai, ringing daya umma ta dauka, kafin ma su gaisa hajiya tace mairo kizo gida inason ganinki, ina son muyi magana akan abunda ya faru shekara goma sha takwas da suka wuce…… Dam gaban umma ya fadi, :oops::oops::oops:dama tasan zaa rina. *Xarah Bêê* *Dedicated to bady social* KURSUM by ~ Xarah Bukarêê page Tana isa boardroom ta wuce, “suka fara meeting, dama ita kawai ake jira, “baba shehu sai zuba bayani yake, ita dai bata gane komai ba har aka gama, ta koma office dinta. baba shehu ne yashigo office din, sai wani fara’a yake kaman dagaske, “kursum tace baba da kanka, ayda ka turo wani, yace “nida ya’ta ai dole inzo gaisheki da kaina, ya mika mata check din makudan kudi tayi signing, ta karba ta duba tace “baba kudin sunyi yawa, me xaai dasu ? “ya sosa keya yace dama wasu sabbin machines na company mukeso importing dan wanda muke dasu sun fara lalace wa. tace toh shikenan amma dai xan rage kudin sunyi yawa, tayi signing ta mika mai, bai ji dadin abunda tayi ba ya amsa ya fice rai abace, ita dai kursum bata yadda da fara’arsa ba kwanan nan sabanin da idan ta gaishe shi sai harara da zargi yake wurgo mata. zaune yake a office yana duba takardun dake gabanshi, can ya hango papers din shares dinsu da abba ya bashi yakai T. b oil & investment company asa hannu, da sauri ya mike ya kwashe papers din tare da car keys dinshi ya fice Da sauri yake driving har ya iso company din, ya tambayi daya daga cikin workers din inda office din MD yake, suka kai shi office din Mr dabo, da sauri mr dabo ya tashi ya gaishe shi dan yasan family dinsu ne major share holders din company din, “Yazid ya bashi hannu suka gaisa dan ya sanshi sosai mutumun abba ne, “yace mr dabo ashe kaine new MD din, dabo yayi dariya yace ai bankai matsayin nan ba, nine dai personal assistant din new MD din, barin gayamata tayi bako, da sauri ya fice ya dawo yace kana iya ganinta yanxu, “Yazid yace okay thanks….. Hankalin ta kwance sai buga game take abunta, yayi knocking kofa, ko dagowa batayi ba tace come in, yana karaso ciki ya ganta yaji mugun takaici, dama witch dinnan itace MD din, lailai ko yau idan tamai fitsara bazai barta ba, bai ankara ba yaji tace can I help you ? ya kara kallonta wato ko dagowa baza tai ba game dinta kawai take, lailai ko zanyi maganinta. …… Papers din hannun sa ya watso mata a fuska, da sauri ta dago suka ido, sai da gabanta ya fadi dan ba karamin kwarjini ya mata ba, ta harare shi, ta daure tace “miye haka zaka watso min papers, have u lost your manners ? ya bata rai, “yace aiki kika zoyi ko game, ko an gayamiki wasan yara ake anan, ta murguda baki tace “bansani ba ina ruwanka, dariya ma ta bashi, yace “signing zakiyi akan papers din” ta yamutsa fuska tace na miye , harara ya wurga mata yace baki iya karatu bane, “ta hada papers din waje daya ta karanta ta kalle shi tace “ashe kuna da shares a company dina” yayi banza da ita , tayi murmushi ta tashi ta karaso gaban shi ta ajiye mai papers din tace ” banda pen ( biro) balle inyi signing, kana iya komawa da papers din, next time idan xaka zo saika hado da pen ta zauna taci gaba da game dinta… Bai ji haushi abunda tace ba, ya tashi yadau papers din yai murmushi ya kalle ta yace” I have nothing to say amma keda kanki zaki ne me papers din, ya fice daga office din. Mr dabo ne yashigo office din da saurin sa yace madam lafiya dai koh, naga bakonki ya fita a fusace, ta yatsine fuska ta gayamai abunda ya faru, yace “madam ai kinyi kuskure babban saboda sune major share holders din company dinnan, idan suka kwashe shares dinsu company dinnan zai zama bankrupt kuma zaiyi affecting oda share holders, “kursum da hankalinta ya tashi tace mr dabo yanxu ya xaai kenan dan papers din na hannu shi, “yace abu mai sauki tashi zakiyi muje har office dinshi ki bashi hakuri ya baki papers din, “tace to muje ” handbag dinta ta dauka da sauri suka fice… umma ce ta shigo parlour gidan da sallaman ta, shiru babu wanda ya amsa “can ta hango zee zaune tana kallon tv da alama batasan ma ta shigo ba, ta karasa ciki tace baki ji ina sallama bane , ta juyo ta kalle ta aya tsine tace banji bane sorry, umma tare kuke da yaya yazid ? umma tayi banza da tambayan tace ina hajiya ? zee tace bansani ba amma ki dubata sama, ta cigaba da kallon tv abunta. …..Umma tayi kwafa ta haura sama, tana takaicin hali irin na zee, sam batayi sa’ar suruka ba. hajiya ce zaune a daki sai kuka take tana dana sanin jefar da yar’ta datayi, babban tashin hankalinta shine rashin gayawa daddy cewan yar’su bata mutu ba harya rasu, kuka kawai take tana dana sanin bakin halin data shuka a rayuwarta, “da sauri umma ta karaso wajanta tana hadiza lafiya, meke damunki ? hajiya tayi shiru tana tunanin yadda zata gayawa umma ta ga pink diamond dinta awuyan sumy, saboda kowa yasan makauniya ce, ta nisa tace “shekarun baya da suka wuce nayi niyyan jefar da ya’ta, amma kika dauketa kika kaita inda zaa raineta harta girma, “ta kara fashewa da kuka tace mairo ina ya’ta kursum take ? kina da labarinta kuwa ?? umma ta gyara zama tace “hadiza ni bansan inda yarki take ba, makarantar dana kaita munyi dasu idan takai shekara sha takwas zasu sallameta, kuma yanxu ko ta cika sha takwas dan gimbiyar makarantar ta kirani ta gayamin tacika alkawarin dake kanta na bawa yarinyar diamond din da kika ajiye mata. … agigice hajiya ta kalle ta, tace mairo ki taimakeni ki kiramin gimbiyar awaya, ko zata San inda ya’ta taje ranar da suka sallameta, umma tace to barin kirata muje, dan nima tunda nakai yarki makarantar ban yanke zumunci da gimbiyar ba, dan nasan wataran zaki nima yarki….. Tasa masu call din a speaker, ringing daya biyu Gimbaya hafsatu ta dauka da fara’arta, suka gaisa da umma, “umma tace dama zancen kursum ne, ko kina da labarin inda take yanxu, gimbiya ta nisa tace “ai kursum Allah yayi mata rasuwa tun lokacin da muka sallame ta, kawarta tabi suje gidansu a kano shine sukayi hatsari a hanya, ita ta rasu amma kawar bata rasuba, “Dam gaban hajiya ya fadi, shikenan yar’ta ta rasu” umma tace gimbaya ya sunan kawarta ? tace sumayya tanimu bawa sunan ta, umma tace nagode sosai gimbiya sukai sallama. Rudani, tashin hankali, lokaci guda hajiya ta shige su, ta kalli umma da jajayan idonta da suka rine tsaban kuka tace “babu tantama sumayya gidan nan ce kawarta, tare sukayi accident kursum ta rasu, kuka kawai take tana salati , taga samu taga rashi, “umma sai bata baki take tana kwantar mata da hankali, amma ina kuka take , bata ankara ba sai gani tayi hajiya ta fadi kasa sumammiya. :oops::oops::oops::oops::oops::oops: Xarah Bêê kursum 53 to 55 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 Kursum by ~ Xarah Bukar page Umma ta tashi ta dibo ruwa ta yayyafa mata, amma shiru hajiya bata tashi ba, a gigice ta fito ta kwalla wa zee kira, zee tazo da saurinta tana “umma lafiya kuwa?? tace ba lafiya ba maza kira doctor malik, hajiya ba lafiya, “da sauri zee tayi kiran layin doctor tana gayamai abunda ya faru, “doctor yace ni yanxu am very bixy , zan turo ambulance yanxu akawo ta asibiti, “zee tace toh dr. muna jira. Ba’a fi minti biyar ba, ambulance yazo suka wuce asibiti gaba daya, direct emergency aka wuce da ita, umma da zee na daga waje hankalinsu duk atashe, umma tace zainab kin gayawa shehu muna asibiti kuwa? , tace eh yanxu na kira shi yana hanya zuwa ma, “umma tace tun dazu nake trying line din yazid ban samu ba, gwada kira min shi ko zaki samu, “zee tace nima dai tun dazu nake trying line dinshi ban samu ba, amma barin je office dinshi inji ko lafiya, umma tace toh ki gayamai ina naiman sa yanxu nan, tace to ta wuce. Zaune yake a office yana sipping coffee, yana danna laptop dinshi hankali kwance, ya dauka papers din ya kare masu kallon, yayi murmushi ya ejiye su gefe, secretary dinshi suzzie ta shigo, “tace sir a lady is here to see you, “yace owkay tell her to come in” suzzie ta fita tace madam u can go in, kursum tace tnx, ta juyo ta kalli Mr dabo “tace karna batama lokaci, kana iya komawa office, idan nagama zan naimi taxi indawo, yace toh madam sai kinzo, ya wuce. Ta turo kofan tashigo, wani irin kamshi mai dadi da sanyi suka mamaye ta, offfice din mai girman gaske dan har yamafi nata, dago wa yayi ya kalleta yayi murmushi ya cigaba da abunda yakeyi, “ta karaso tace mai sannu taja kujera zata zauna, ya dakatar da ita yace “baa zaman min a kujera saida izini ni na, kuma miya kawo ki nan?? Tayi shiru ta koma gefe ta tsaya, “tace humm mm dama papers dinnan zaka bani inyi signing” yayi banza da ita kaman beji abunda tace ba. Har kusan minti biyar baice komai ba kuma bataga alaman zaice ba, ga tsayuwar ta isheta daurewa kawai take, “kashe laptop din yayi ya tashi ya dibi wasu files, ya kalleta yace kina iya zaman a couch din can kiyi game din da kikasaba, ni yanxu ina da important meeting da zanyi attending” bai jira abunda zata ceba ya fice. Ba yadda ta iya dole ta jira shi, ta bude jakanta ta dauko wayanta ta fara game, har kusan 30mins bai dawo ba, gashi ta gaji da game din, ta kwanta ta fara bacci abunta, “bayan awa daya ya shigo ya cigaba da aikin gaban shi, yama manta da wata a office din, can ya dago zai dauki wasu files ya hango ta kwance kan couch tana bacci da alama ma sanyi Ac yamata yawa dukta takure waje daya, ya dauki papers din ya taso zuwa wajenta da niyyan ya tashe ta, ya tsugunno setin fuskan ta yana kallonta, yaune na farko daya kare mata kallo, ya ciro wayan shi yayi snapping dinta, ta gyara kwanciya veil din kanta ya zamo kasa, gashin kanta ya zubo ya rufe mata kakkyawan fuskan ta, da sauri yasa hannu ya matsar da gashin gefe, karaf ta tashi sukayi ido hudu dashi, ya tsakar mata lausassar murmushi, “ta lumshe ido tana kallonsa wani irin sanyi take ji azuciyar ta, dakyar ta mike, ta Harare shi “tace miye haka zaka tabani? ? Dariya ma ta bashi, ya mika mata papers din yace kiyi abunda kika ga dama dasu, ta bata rai ta amsa ta ciro pen a jakarta tayi signing ta mika mai, ta tashi tace sai anjima, yace “babu ko godiya, tayi banzan dashi ta wuce zata fice, takasa bude kofa, ta danna lock din yaki budewa, ta juyo ta kalle shi a fusace tace “nakasa bude kofan, yayi dariya ya taso yace d door is open kece dai yar kauye baki iya budewa ba, yasa hannu xai bude kenan aka bango kofan daga waje kursum ta fada jikin shi a tsorace:oops::oops::oops: Zee dana gama kulewa ganin kursum jikin masoyinta yasan ta kara fusata:evil::evil:,tace yaya yazid dama shegian yarinyan nan ce a office dinka tun dazu, shine secretary dinka ta zauna dani office dinta tun dazu akan cewa kana da important visitor, gajiya nayi da jira shiyasa nayi deciding in shigo kawai, ta fashe da kuka Ya yazid kasa magana ma yayi dan haushi, dan dama haka take shigo mai office duk lokacin data ga dama,”kursum ta karaso wajenta da sauri tace “kiyi hakuri, wlh ba abunda kike tunani bane, aiki ne yakawo ni nan ba komai ba” zee ta Harare ta tace karya kike munafuka dama daga ganinki ke yar bariki ce, mayya yar titiiiii…….bata ida magana ba ya yazid ya wanketa da mari saida taga wuta , tace baby ni ka mara? Yace namareki din, ba sister dinki bace atleast respect her for once, “kursum dai tana gefe bata ce masu komai, zee tana kuka tace baby dan ina sonka dayawa shiyasa kakemin wulakanci, ta kalli kursum tace ke kuma hajiya na asibiti ba lafiya kinzo nan kina cin amana, toh baki isa ba kuma sai na koya miki hankali ta fice , da sauri itama kursum ta bita tana kwalla mata kira. Yana nan tsaya yaji wayar shi na ringing ya duba yaga umma,da sauri ya dauka suka gaisa, tace my son I hav been trying ur line bai xuwa, kana ina ne? “Yace ina office umma, tace to kazo ka sameni a asibitin dr malik yanxun nan, hajiya hadiza ce ba lafiya, yace toh ganinan umma, ya ajiye wayan da sauri yadau mukullin mota ya fice. Har bakin mota ta biyota tana zee kiyi hakuri mana, ki taimaka ki kaini asibitin banzo da mota ba, zee tayi banza da ita ta shige mota abunta taja a fusace:evil::evil: Haka ta karaso bakin titi kozata samu taxi, shiru dai bata samu ba ga wani irin ciwon kai dake damunta, tana tsaye wata hadaddiyar jeep kirar classic 2020 taxo gabanta, yayi wining glass din motan, yace little witch shigo in kaiki, tayi banza dashi, yayita mata horn taki kulashi, da daga dai zai kara mata ciwon kai tayuwo tace ya yazid miye haka, nace bazan shigo ba ka wuce kawai, “yace asibiti zani wajen hajiya kema nasan can zaki je, kizo in maki lift dan bazaki samu taxi anan ba, ta tsaya tunani, ita dai bataso zee ta kara ganin su tare, haka dai ta hakura ta shigan motan. Har suka iso asibitin babu wanda ya yiwa wani magana, ta fito da sauri zata wuce ciki, yace ke kinsan inda aka kwantar da ita ne? Tace a’a, “yace to saiki jirani ai tunda ni nasan wajen, duk sai taji kunya, haka suka jero har inda umma ke zaune, ya karaso gabanta yace umma lafiya dai ko? Tace eh hajiyan ta farfado, yanxu bacci take ma, shehu yana wajen doctor jin meke damunta, kursum dake bayanshi ta karaso ta gaida umma da mata godiya sosai akan kokarin datayi na kawo mamanta asibiti, umma dai sai kallonta take dan batasanta ba, tace my son ina kasamo pretty girl dinnan, yazid yayi dariya yace ai sumayya ce diyar hajiya, na rage mata hanya ne,”umma tace ikon Allah dama ni ban taba ganinta ba, ya kike sumayya? Kursum akunya ce ta amsa tace lafiya kalau, umma dai sai murmushi take, ji take kaman tasan ta, wani irin son yarinyan taji har cikin zuciyan ta.:mrgreen::mrgreen: Baba shehu ne ya fito yasame su yake gayamasu ai jinin hajiya ne yahau sosai dalilin firgeta da tayi, dan yanxu haka ta farfado amma har yanxu tana tare da shock,”ya kalli umma yace haijya mairo bata gayamaki abunda ke damunta ba kafin ta suma, umma tayi shiru batace komai, baba shehu yace toh Allah ya bata lafiya shine kawai fatan mu, yanxu dai doctor yace mutum daya zai zauna da ita, inya so gobe mazo mu ganinta, ya kalli kursum yace ke kizauna da ita harta tashi, hajiya mairo kuna iya tafiya tunda sai gobe za’a iya ganinta, “umma tace to shikenan bari mu wuce, gobe saimu dawo, my son let go, ta kalli kursum tace sumayya ki kula da mamanki sosai kinji, tace toh umma zan kula da ita sosai. baba shehu yace zan turo samira ta kawo muku abunda zaku bukata,tace toh”ya wuce abun shi. Har sun wuce ya yazid ya dawo da sauri yace Karki zauna kina game, akula da marar lafiya dai, ta murguda mai baki tace ina ruwanka toh:?:?…… yayi dariya yace zanyi maganin tsiwan nan naki, ya fice da sauri…… Ta tura kofan dakin ahankali, ta karaso gaban gadon da take kwance ga ruwan drip an daura mata, ta zauna

Chapter 3 of 6