Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ASHE KAINE MIJINA? MARUBUCIYA HAUWA M.JABO ASHE KAINE MIJINA?1...? Na HAUWA M. JABO... Ke nazia kiyi sauri ki tattaro kayanki kizo mu tafi yayanki yana jiranmu, ko walle mu tafi mu barki! ganinan zuwa inna! nazia ta baiwa inna amsa tan a qoqarin fitowa daga tadinka da dan gunshin kayanta a hannu, da yar jakar ta inna ta kalleta a hantare, kekam kinji haushi Kullum idan za'afita sai an barki, duk zumudin da kike ya zama na banza tunda har na rigaki shiryaw a, nazia ta kwashe da dariya, wallahi inna kesan kayana sunada yawa shi ya sa ban samu na fito da wuriba, ke dan Allah wuce ki bani guri ko in hantar eki, mara kunya, dama haka kike kullum da baqar shiririta, ta qara kwashew a da daria, hadda gyagyataWa, duk wanda yaga nazia a gida idan ya ganta a waje zai dauka ba ita bace, yanda take daure fuska kamar bata taba murmush i ba, zaka dauka kamar ma bata taba dariyaba a rayuwarta,tafito da dan gud u gudu tana kallon ko ina idan basuyi Mantua ba ta kalle ko ina amma komai babu tafito tana murmushi, yayanta ya kalleta, ke wallahi kinci albarkac in inna da sai mu tafi mu barki kinfi kowa cewa a koma birni amma kuma kin fi kowa shiririta, mtsww yayi tsaki, na qyalqyale da dariya abina na fada jikinsa yi haquri y ayana, yanzu ai gashinan na fito mu tafi ko, amma fa abu daya ya rage min , inna da yaya duk suka juyo suna kallon juna da mamaki, inna tace dama ba ki kammala ba Nazia??? aah inna na qare komai amma ai kince inje gidan.... ... ASHE KAINE MIJINA..?? Na HAUWA M. JABO.... Amma ai kince inje gidan su abban fatin birni in musu ban kwana, Inna ta saka salati tana tafa hannu, dama nazia da nace kije ki musu salla ma bakije kin musu sallama ba, yar duniyar ta qara kyalkyalewa da dariya, amma anyi shaqiyiyar yarinya inji inna, ta kawo min duka amma ina na kauce , na qara kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza, sai ta ishimutane da dari ya sai kace mai tabin jinnu, yaya ya gama qufula, baice komai ba.!!! Na za bga a guje ina ta dariya, ina shiga dayar kwanar na daure fuska, kamar ban ice mai kyalkyala dariyannan ba, na gyara hijabina nashiga gidansu hafizun birni mamanshi tana ganina ta hau washe baki,tana min kirarin da ta saba amma ko ajikana nasha magani abina tace auta matar auta, badai tafiyar cet a tashiba, kamar banason magana na kebe baki nace, E, tace yar nan Allah y a kaiku ya lafiya gashi sameer baya nan da sai in ce ya baki number yayan naki nura idan kunje sai ku nemishi ku riqa qaisawa, bance mata komai ba, ta qare surutanta, nace zamu wuce su yaya hafizu suna jirana, tace to yar nan Allah ya miki albarka, ta bani kudi wai insha ruwa a hanya amma naqi in karba, nace ina fati take? Allah sarki bata dawo makaranta ba idan ta dawo xan fada mata kun tafi, xatayi kewa Wallahi xan wuce yarnan baxaki ka rbi kudin ba nagode hajiya, dama itama ta sanni da taurin kai aranta take cewa tauri da tauri sai qaqa.. ...... ASHE KAINE MIJINA..3? Na HAUWA M. JABO Sai qaqa, koda na qaraso na tarar da an kulle gidan mu kuma ba motar yaya ba labarinta!!! Tuni hanjin cikina suka shiga kadawa idona suka cika fal l da hawaye sai kuka, yanzu su yaya da inna sun tafi barni, kuka Sosai nakeyi na zauna dirshan a qofar gidan mu na rufe ido ina kuka,maimakon in dan xagaya amma anan na dabe ina kuka, sai ji nayi ankwasheni da mari ta g efen fuskata ! Kutumar uba waye yake dukana duk da ina cikin qunci amma da bala'e na dago kai inga wane dan iska ne yake dukana!!! Daga kan da zany i sai kawai naga yaya, fuskar nan a turnuqe kamar an aiko mishi mutuwa, wa llahi idan baki tashi mun wuce ba zan babbalaki anan, mamaki da tsoro ya c ikani, araina nace su tafi su barni sannan kuma yaxo yana dukana da zagi, araina na fara balaee na daure fuska, ashe nice banida kai mota gatachan gaban gidan mu kadan kwana sukayi suna jirana, da yake ni idan ina tafiya bana qage sai ban hango motar ba, na kuwa sha kunu na fuske abina, ya shig a gaba ina bin bayanshi saida muka isa jikin mota naja na tsaya, kamin kac e kwabo inna ta wankeni da wani marin,ta buda baki xatayi magana na rigata nashiga uku, nace minayi muku kukeson ku kasheni,sai inna ta shige mota t a barni, naci gaba dan kunga ina zumudin zuwa birnin ne ake min wulaqanci. ..!! to Wallahi na fasa zuwa birnin banaso, bazanjeba asaukemin kayana...! ! ba inda zanje, na qara fashewa da wani kuka.... yaya ko kallona baiyiba shima ya zagaya ya shiga mota ya kunna yana jiran in shiga amma ina taurin kai ya motsa, ko ajikina, yayi horn alamar in shiga a mma ina sai ya fito ......, ASHE KAINE MIJINA..4 ? Na HAUWA M. JABO sai ya fito, kinsan Allah nazia idan baki wuce muka tafi ba zan babbalaki yanzu nan, ko kallonsa banyiba, na kauda kaina gefe, yaga da gaske nake y akaimin duka, ko in kauce na tsaya qiqam mugun halin ya mosta hakan ya qar a bashi haushi, dama shima gwanine a gun xuciya amma dai bai kaini ba, ya fara dukana har na fadi yasa qafa yayi ball dani, hankakin Inna ya tashi t asan idan zai kasheni a gurinnan ba tashi zanyiba, kuma tunda nace bazan j eba ba tafiyar zanyiba, tazo ta janye yaya hafeez daga gareni, ba halin ta mishi fada yanda taga ya chanza har fuskarshi tayi jaa dan tsananin fushi ,da yake shi yaya hafeez fari ne Sosai ko kunya yaji sai kaga yayi ja, ha ka lokacin sanyi ma jaa yakeyi, uwa uba idan yayi fushi sai yayi jaa kamar bature haka yake, tayi gefe dashi ta daura hannunta akan kafadar shi ta d ama, haba yaya!! Ya zaka biyewa nazia? Yarinyar da ba hankali ya ishetaba , kuma sam batasan ciwon kantaba, wuce ka shiga mota bari in daukota, yayi mini wani mugun kallo, rai a bace ya shiga mota yana huci "nima dai m. ja bo da nake biye dasu ya bani tsoro dan nayi niyyar in gudu sai mun hadu bi rni amma dai nayi ta maxa na tsaya" inna tazo ta durqusa kusa dani, tace b a tafiya mukayiba kinsan haryar qaramace shine sai yayanki yace bari muyi kwana kamin kizo shi yasa baki hango muba kuma ke gashi bakya kallon hanya kina zuwa baki ganmu ba maimakon ki duba gefenki sai kawai kika nemi guri kika zauna kika fara kuka, abin ya bani haushi ne dan kada yayanki yace n a goyi bayan ki shi yasa nima na dakeke amma nima raina baiso ba....!! hab a autan inna kuka ba naki bane kinga kin bata wa yayanki lokaci kusan awa biyu fa muna jiran ki kuma ya gayamana yanada aiki kuma duk ke kika janyo araina ......, ASHE KAINE MIJINA..5 ? Na HAUWA M. JABO Araina naji dadi ko banza na bata masa Lokaci, amma kuma naji jiki, Lallai nice banida gaskiya sabida ina zuwa kawai banga motaba sai na zauna na fara kuka, kuma ni kaina nasan ba yanda za'ayi su tafi su barni, wauta ce take damuna ko qauyanci? na bude baki cike da yawu da jini na zubar da yawun ge fen inna, inna da taga jini hankalinta ya qara tashi, maimakon in sassauto in lallaba in tashi mutafi sai na fuske, "kamar jabo tayi rashin kunya ta fuske" ina sheshe kar kuna bace inna ba inda zani na fasa tafiya,birnin ban za, dan yaga inason inje birni ne shi isa yake min wulaqanci, yanxu kuma na fasa zuwa asaukemin kayana, ashe yaya yana jina, da qarfi ya fito motar y a bude bayan motar motar ya ciromin kayana ya jefini dasu kikaji jakar timm n akaina, tabbas wannan yafi dukan da yamin qonan rai, inna ta kalleshi, ta daure fuska, ashe bakada hankali? Mi kayi kenan? To sai ka fito min da naw a kayan nima ba zaniba, tunda abin naku rainin hankaline, hankalin yaya ya tashi, nima dai naji tsoro kuma naji kunya, ya durqusa inna.... kamin shiru ka fito min da kayana nace ba zaniba ko dolene,!! Narasa yanda zanyi akain a ake mishi fada kuma nice banida gaskiya ga uban taurin kai, ya juyo gurin a nazia dan Allah kiyi haquri?? na sunkuyar dakai, banji dadin abinda na ma sa ba... Itama inna taga rashin dacewar hakan abu ya hade masa biyu ta miqe tsaye ke nazia tashi ki shiga mota kaima wuce mu tafi sumui sumui kamar munafuk a na miqe zan dauki jakar kayana yaya ya karba inna tace sake mata kayant a ta dauka da kanta, Lallai ban kyautaba kuma duk ni na janyo amma...... ASHE KAINE MIJINA..6 ? Na HAUWA M. JABO Amma ya zanyi fuskewa kawai zan cigaba dayi yaya yashiga mota nima nashi ga, nasani sarai idan akwai abinda ya tsana baifi ashiga bayan mota a ba rshi shi kadai a gaba ba, na kuwa fuske nabi Inna baya, ya kalleni irin k allon tausayi muka hada ido amma na fuske abina, na bude baya zan zauna, Inna tace nan kika saba zama?? Sumui sumui naje gaba na zauna, yaja mota sai sakwato birnin shehu, sokoto garin dan fodiyyo garin karamci qarin m utumci, garin dattako, garin kashe kunya, na jinjina muku sakwatawa, Alla h ya barmu da qaunar ma'aiki.!! Tunda muka shigo nake raba ido sabida qarin yamin, Gaskiya qarin yanada k yau da tsabta, sai kalle kalle nake sabida tunda nake ban taba zuwa sokot o ba sai yau, rabona da sokoto tun ina shan nonon innata, haka kawai naji hawaye suna saukomin, Lallai ban kyautawa yayaba! Na mishi butulci Sosai , shine wanda Kullum burinsa ganin farin cikina! Shine Kullum burinsa far antawa mahaifiyata,! Muna qauye amma ba wanda zai kirani da ba qauya! Ba wanda zai rainani, a qauyen mu nice gwana, nice yar gayu, nice kowa yakes o, kuma duk albarkacin yayanane, yanzu haka da na shigo cikin birni duk y an matan da na riqa hangowa a mota, ba ko wacce na gani da irin tufafinab a, sai daidaiku, cox yaya yayi ta fadamin tufafin da yake min ai na manya n matane dinkin ma haka, tufafina masu tsada na yayan masu kudi amma shin e zan yiwa butulci irin wannan gaskiya dole in........, ASHE KAINE MIJIN A7? Na HAUWA M. JABO Dole in bashi haquri, na dan faki ido na kalleshi, sai ya qara bani tausa yi,matuqa narasa irin halina, tun bayan rasuwar mahaifin mu munsha wahala r duniya, wanda daga baya yaya yana karatu yana bin motar daukar kayan gw ari irinsu ayaba da lemo da mangoro, duk dai wani fruits da ake yayi, ha ka zasu loda cikin mota idan sun isa gari sai su sauke, ana biyansu, kuma ahakan yake karatu yana wannan sana'ar har ya qare secondary anan mai ga ri ya dauki nauyinsa da yake mai qarin mu abokin marigayi babane, ya dauk i nauyinsa yaje dan fodiyyo sok anan yayi dgr na farko yana kammalawa ya fara karantar wa a sokoto cement primary anan dai ya sami kudin shiga Sos ai har ya ci gaba da karatunsa, duk albashinsa akan mu yake qarewa sabida yaya mutum ne mai zuciyan yi kuma yanada son fitarda kanshi dama wani na shi kunya shi isa tun yana qarami da yake dako kayan kwalliya ina dasu ko mai yana siyamin har na tasa nadan girma, kuma sam bashida qyashi duk abi nda ya samu inna da naxia, Mu biyu muke a gurin mahaifin mu ni da yaya, mahaifin mu ma'aikacin priso n ne yana gadi a sokoto prison a wani rikici da akayi a gidan yari aka ha rbeshi anan Allah ya karbi ranshi, tun daganan muka dawo qauyen mahaifiya ta da zama tun ina shan nono ataqaice dai bansan mahaifinaba..... ASHE KAINE MIJINA 8? Na HAUWA M. JABO Bansan mahaifinaba sai yaya da inna stakanina da yaya shekara takwas ne, s abida inna tace har ta daina tunanin haihuwa sai ta sami cikina ta haifeni , yaya na matuqar sona kamar shine babana, bansan wahalar rayuwaba sam, Ki fito mun iso naji ya fada cikin sassanyar murya, tausayinsa ya qara k amani, ban san lokacin da na masa murmushiba, amma sam fuskar sa bata ka ina, gidan da na gani ya tsoratani, wani fakacecen gidane, da gate yaya ya bude, muka shiga, naga ikon Allah araina nace a cikin wannan gidan za mu zauna, sabida ko a mafarki ban taba ganina a iran wannan gidan ba, gi dane bangare biyu ban gare daya an kammala ginin dayan banqaren kuma ba' a kammalaba amma wanchan bangaren da ba'a kammalaba yafi banqaren mu gir ma, muka shiga, muna shiga na tabbatar da yaya yamin gatan da yake fadar zai mini, naga so da qaunar da yace zai nuna mini, tabbas nayi sa'ar da n uwa, wasu hawaye suka sake zubomin, yaya ya shigo da kayan mu, ya nuna min dakina komai a tsare hattana kayan make up an saka min toilet dina sai wanda ya gani dakin inna ma haka komai tsab an gyara, sai dayan daki n da ya nuna mana na baqi, ya nuna ma inna kitchen da kayan abinci da ko mai a ciki duk da tana daure masa fuska yana mata bayanin komai nima yam in bayanin komai amma yaqi bari mu hada ido yayi waya ya........., ASHE KAINE MIJINA 9? Na HAUWA M. JABO. Yayi waya yace aturo yaron sun iso, almajiri ya nema mana wanda zai riqa mana cefane da sauransu, ya baiwa inna kudi kamar yanda ya saba sai kawai yace sai anjima ya fita, nida inna mukayi jugum jugum sabon gida sabuwar rayuwa, Lallai yaya ya cika min alqawarina, sabida ya kawo ni birni kama r yanda kullum nake cewa inason akawoni birni gurin mijina, yau gani a bi rni a birnin ma sokoto birnin shehu, gari mai kyau kuma gida mai kyau, i n kalli inna ina tsoron in mata magana naga ta daure fuska, sai na tashi nashige dakina, nayita kalle kalle, komai a tsare kuma tsab dai dai da bu qatar duk wani dan birni, hotona dana yaya da inna munyi kyau Sosai anyi babban frame dinsa an kafa a dakina, nayi kyau a hoton yarinta na a fuska qarara amma bai hana kyauna fitowa ba, yar qaramar fuskata das da manyan idanuwana das dasu, hmmm gaskiya nayi kyau a hoton, na zauna jigum, sai na fara tunanin qawayena na qauye fatima yarin yayar nura ce duk qauyen m u ita kadai tamu tazo da ita sabida itama yar gayuce iyayenta suna birni amma ita tana qauye abinta, nura shine wanda tun da mahaifiyata ta sami c ikina yace idan mace aka haifa matarshice, hak kuwa akayi tunda aka haife ni ya ke sona ana cemin matar nura, mamanshi takance dani auta matar auta , tun inada shekara uku, ya koma birni gurin yayanshi baban fatima qawata ban qara ganinsa ba har yanzu da nakeda shekera 14 a duniya...., ASHE KAINE MIJINA.10?? Na HAUWA M. JABO Shekara14 A duniya, tun ina cewa a kaini birni gurin mijina har na daina da na fara wayo na fahimci ba sona yake ba, lamarin qauye ne kawai, gashi kuwa mahaifina yace bai yarda in auri wani idan bashiba, kuma kowa ya sa n ni matar nura ce, amma nura sam bai damu da harkataba, bai damu daniba, ko.qauye yaje gurin mamarshi baya kwana ranar da yaje ranar yake dawowa ban taba qaninsaba sai dai yakan yomin tsaraba tuli tuli, nida fatima, da alama ma iyayen fatimar ne suke min siyayyar, sabida komai iri dayane ni da ita, shi isa shima yayana komai iri daya yake mana da ita, Allah sarki fatima ko Yaushe xamu qara haduwa gashi tace xata bani address din qanwa r ta idan naxo birni muyi qawance amma naxo tna skull ina cikin wannan t unanin sai naji kiran inna natashi naje, kizo ki hada mana abinci idan k in iya nidai kam ban iya aiki da gas cooker ba, nace nima ban iyaba, nada uki a shana naje gurin da ake wancan ginin na tattaro itace na hura wuta na mana girki, muka danne abinmu,har lokacin fuskar inna a daure take nar asa yanda xanyi in bata haquri sai bayan maqreeb yaya ya dawo yashigo da ledodi,dayar ledar tablet ce da kuma wayoyo guda biyu, ya bani tab din y a hadamin da wayar, da sim itama inna ya bata wayar ya nuna min yanda ake kunnawa da kashewa da Sauran abubuwan duk dai fuskar shi ba yabo ba fall asa amma yaqi bari mu hada ido yace zancen skull dinki gobe zan kaiki mak arantar da zakiyi karatu sai kiganta dama anyi komai kaiki kawai xa'ayi....... ASHE KAINE MIJINA 11?? Na HAUWA M. JABO Xa'ayi, naji dadi Sosai a raina da jin zancen makaranta sabida har nakai jss3 nayi jlc kawai aka shigo da zancen birni, yaya ya juyo gun inna ya s assauta murya, ya fara baiwa inna haquri abinda ya faru dazu da safe, inn a tace ba komai nima nan na Sami dama na bashi haqurin rashin ta idon da na masa, dan uwa rabin jiki aka yafi juna muka dawo kamar yanda muke ada, farin cikina ya qaru ganin cewa yaya na da innata sun daina fushi dani, duk mun saki jiki kamar ba'abinda ya faru da safe har na bama da yaya lab arin yanda mukayi girki, yasha dariya, qarshe yace za'asamo wa inna wacc e zata tayata zama da aikace aikace tunda ni makaran zan riqa zuwa, dagya r dai inna ta amince da mai tayata zama, mun shiga kitchen yaya ya nuna m in yanda ake amfani da komai, mukaje bayi yanuna min yanda ake komai da k omai, munyi hira Sosai dashi daga bisani ya wuce dakinsa nima nabi inna d akinta dan nasan bazan iya kwana ni kadaiba, naje muka fara hira nida inn a ta, acikin hirarta dai ta hada da wa'azi, ta qara jan hankalina akan za fin rai irin nawa, taja kunnena akan yanzu nashigo wata sabuwar rayuwa mu tane daban komai daban so dole sai na san yanda zan riqa hulda da mutane, kuma ta ja min kunne daga yin mugayen qawaye, da kama kai kada in riqa s hishigi ga wayanda suka fi qarfina, in kama mutuncina insan cewa ni ba ko wa bace, ta qare muka dauko waya na nuna mata iya abinda na gane nasan ku ma zata qane, ni kuma nahau daddana tawa ina qara fahimtar abubuwa, haka dai har bacci mai nauyi ya daukeni nabar inna tana......... ASHE KAINE MIJINA ?? Na HAUWA M. JABO Nabar inna tana ta kallon wayarta,dama tunda asuba yaya yace in shirya za i wuce aiki yanason ya kaini skull,din mu ai ko dan kada amaimata dan gid an jiya tun asuba ban koma bacci ba, bayan mun qare break fast muka dauk i hanyan makarantar da za'akaini, tun daga nesa na hango hadaddun motoci suna sauke yaransu, nasan cewa wannan skull din ta well to do ce, araina nace yaya ya kawoni gurin yayan masu kudi, tun bamu isa admn block ba na ba na fahimci wasu yara yan mata suna ta kallona suna dariya, araina nace ko dai sun gane cewa daga qauye nake, haka na fuske abina,sabida nasan b anida munin da za'amin dariya, haka ni bana tafiya bazar bazar " kamar za inb khalifa princesszee" bare ince na kwafsa, to dai haka har muka iso ad mn block ina tunane tunane, matsalar farko dana fuskanta rashin iya speak da English , ina gane duk abinda ake fada amma bana iya bada amsa, shima dai da ni daqiqiyace da dan karatun qauye ba abinda xan iya yaya ya bada C. A dina daya karbo a qauyenmu, akamin interview dagyar dai suka amint a na zauna jss3 maimakon ss1 da zanje, shima jss3 din saida yaya ya dage dan jss1 sukaso su kaini tunda bana iya magana da English, admn off ya ki ra wana yarinya yace ta nunamin clss dinmu, ta kuwa nunamin nashiga nayi sallama da yaya, na wuce clss Lallai sabuwar rayuwa da mutane kala kala, abinda yafi bani haushi kallona da suke suna dariya na qare musu kallo ka f ba wacce takaini ko kyau bare ........ ASHE KAINE MIJINA.13?? Na HAUWA M. JABO. Takaini kyau bare suce ni mummunace, Lokaci daya naji na tsanesu dukan su na tsani rayuwar birni ma, ina tsoron in musu magana akan dariyar da su ke min in gudun su faramin turancin iskanci dan na kula ba wanda yake Hau sa cikin su, haka na kama mutuncina, na zauna a clss din a quntace ba dad in rai har aka tashi break fast, sai yanzu na tuna yaya bai bani ko gwan dalaba, Kuma gashi banzo da wayataba, haka dai na zauna idona sukayi rau rau, kamar zanyi kuka, ina zaune ni kadai wata yarinya tashigo ga dukkan alamu na girmeta, sister bissimillah ko, nidan bansan miye takeshaba dan yaya baitaba kawo mana irin abin ba, nayi murmushin dole, no na gode, ta yi dariya ai wallahi saikinci, ta bani dariya yanayin rigimarta kamar fat imata ta qauye,kuma ga kama da sukayi da fatimar nace aah ina azumine da yake yau Monday da mizai hana in siyo nima inci, ta kwashe da dariya, nad auka ta gane qaryar dana sharamatane, ta kalleni kice dai qawar tawa mala mace, araina nace yaushe na zama qawarki haduwar minti biyu, ta kalkeni s unan khadija, Muhammad, ana kirana da sista kd, amma fili na maimata suna nta sista kd, tace of course, ko sunan ba dadine, nayi murmushi araina na ce kada ta faramin turancin banxa,Aah da dadi mana inason in zabi wanda z an kiraki dashine, tayi murmushi da yake ta cika baki da cake, ke ya suna nki, sunana nazia Muhammad, itama ta mimaita sunan, yadai, no kamar na ta bajin sunan ne a wani guri amma na manta, nikuma araina nace nikam a guri n fatima ce naji sunan ki sista kd , nice to meat you, nace thanks, na ka sa daurewa nace nihal dan Allah miyasa tunda naxo sukemin dariyane? Itama tayi dariya tace sabida kin....... ASHE KAINE MIJINA 14?? Na HAUWA M. JABO. Sabida kin saka sababbin kaya baki musu iron ba, kinsan fa yanzu an waye a n ci gaba, ba yanda za'ayi ka saka sababbin kaya baka musu iron ba, ana ga ninka za'agane kuma sai a maka dariya, shi isa kikaga suna dariya, amma k ada ki damu gobe idan zakizo sai koyi qoqari kiyi iron din uniform dinki k amin kizo, araina nace da yake su yan birni yan iskane ba dole suma mara i ron dariya, a fili nayi murmushi, na kalli kayana na tabbatar da cewa

Chapter 1 of 7