Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yayi firgigit yamike har alokacin yana tsammanin zolayace amman yasan Abbansu bayamasa irin wannan wasar Umma tamike tashiga cikin daki tadauko hijab tamikawa Asma'u tana fadin Allah yayimaki Albarka yabaku zuria dayyiba yasa Anyi kenan sauran suka amsa da Amin ma'u ta amshi gyalenta tasanya takasa yin komai don tsabar fargaba kamata kuwuce mana malam yakara basu umurni Ahmad saiyake ganin da kunya yakama hannun ma'u musaman da malam ya ambaci matarsa ce wai ayau don haka yawuce dasauri yanufi soro agobe yake kokarin yatattara kayansa yadawo rayuwa da ummansa ashe bashida rabon sake zama tare da ita wato yabarta kenan har abada Umma takama hannun ma'u domin takula duk tarude tarikice gabadaya abinda kedamun umma dayane yanda bata taba koyarda ma'u komai na rayuwar gidan mijiba atsammaninta saitakara girma takara wayo da hankali ashe bazatakai wannan lokacin ba ayimata aure ba bata tsammanin kofar shinkafa ma'u ta iya dafawa wannan kadai shine abinda zaidameta har abada har saida takaita bakin zaure sannan tatsaya tana fadin maza wuce kutafi Allah yayi muku Albarka Malam dasauran yaran suka taso suka rakosu hargaban babur din sannan yakarkatamata takama ta hau yatuka suka tafi suna daga musu hannu malam yadubi sauran yace to masu iyali suwuce gidansu kukuma marasa iyali kushiga kutaya mahaifiyarku kullin kayan daurin aure nizan wuce gidan malam habu nasanar dashi dahaka yawuce suma yaran kowa yakama gabanshi sai samari dakanana ne suka shiga cikin gida suka fara din Salisu yace Umma waidaman kunshirya hakanne da Abba bakusanar damuba Umma tagallamasa harara tace bansaniba tambai sarkin tambaya sainaji matsa zanbaka Amsa yanda ta amsa maganar afusace yadan bashi tsoro yace Allah yahuci yahuci zuciyarki Umma kiyi hkr hakan datayiwa salisu yasa kowa yakunshe tashi acikinsa saiwani lokaci Ahanya suna tafe bisa babur kowa da abinda yake sakawa cikin ransa itakam ma'u har lokacin bata yadda ba mafarki takeba domin ko alittafin hikaya bata tabajin irin wannan lbr maiban mamaki ba shi kam Ahmad jinjina kyautayin da karamcin bayin Allah nan ne aransa dama zai iya sakamusu da karamcin dasuke yimasa waye zai iya aikata irin wannan abin dasuka aikata awannan zamani daya lalace darayuwa irinta jari hujja tabbas sai antona harsuka isa kofar gidan kowa yana sakawa da kwancewa yatsaida babur din yasauka yarike yana fadin sakko 1⃣9⃣ DAME AKE ADO 2 Yakalleta da kulawa saiyaji duk kunya dafargaba sun kamashi wai ma'unsa kanwarsa yau itace tazama matarshi Allah sarkin iko dabuwaya yadaure yacemata muje mana Tashige yanabinta abaya har suka isa kofar yasanya makulli yabude suka shiga tatsaya atsakar gidan tana karemasa kallo bata kawo komai arantaba sai daman anshirya komai itace kawai ba asanarwa ba tunda gashi har gidan antanada ansanya komai yakalleta amman baibari sunhada idoba yace kije dakin can kiyi sallah ki kwanta dasauri tace to tanufi dakin kamar wacce ke kan kaya daman yabita dakallo har tashige sannan yanufi dan dakinsa shago yasamu wuri yazauna yadafe kumatu Raliya ta tafi Asma'u tashigo shin ita wanne irin zama zasuyi kenan ko amafarki baitaba hango wannan ranana balle idan yafarka yayimata wani nazari hakan yasanya yakasa tabuka tunanin komai sai gyada kai kamar dan kadangariya tana shiga daki tazauna gefen gado tana karewa dakin kallo daga gani natane sabuwar amarya amman yaya akayi ba asanarda ita komaiba duk wani shirin da akeyi meyasanya sanda yaje baisanarda ita cewar za ahada auren su ba sai yabata lbr Aurensa da Raliya amman da alama shima baida masaniya akan komai tuno raliya datayi yasanya zuciyarta yin kunci waton daman ita kishiyar raliya ce a iyakacin tunaninta bata taba tunano zasa hada miji da Raliya ba meyasanya su Abbanta sukayimata haka tadafe kirjinta yana bugu kamar zaibullo yayo waje idanuwanta suka ciko da kakwalla jikinta yadauki rawa saitakejin kamar ana likamata kiyayyar raliya aranta kishi maigirma yarufeta saita fashe dakuka meya sanya rayuwarta tazomata da wannan akasin itama matar yayanta Ahmad ce tadade tana kukanta kamin tayunkura tafito tsakar gida tadauro alwala takoma daki domin yin sallah ta idar da sallah tana kallon dakin tana lazimi tana sakawa da kwancewa harzuwa sanda tagaji tamike da hijab din jikinta dakomai tahaye gado takwanta saidai me haushin karnuka datake jiyowa akan titi dakukan gyare sun sunhadu sunbirkitama ta tunani sun assasamata tsananin tsoro bata taba kwana ita kadai adakiba idan tana gida tana makale bayan ummanta har bacci yadauketa sai cikin dare umma ke zamewa tagudu dakin maigidanta da anyi kiran sallar farko tadawo takwanta amakaranta kuwa dakinsu su goma shatara ne don haka bata taba kwana itadaya ba ta mike dasauri tana waigen dakin tome yakamata tayine shin yayanta yakamata takira kokuma rufe kofa zatayi harta kama kofa zata tura saitaji kamar anmata kuwwa cikin kunnen ta danhaka tafito daga cikin dakin dasauri danma dahasken wutar nefa tajima tsaye atsakar gidan tana sakawa da kwancewa tarasa madafa saitaga kamar gidan yana yimata gizo dan haka tayi soro dasauri yayi sa a kofar dakin nasa abude take dan haka tasamu guri ta tsuguna tanannade jikinta cikin hijab tamkar maijin sanyi ahaka har bacci yafara daukara 2⃣0⃣ DAME AKE ADO 2 Ahmad yanaciki baisan abinda kefaruwa asoronba tunda yazauna yakasa motsawa yarasa abinda yadace yayai tsawon lokaci yana awannan halin hardare yafara ja saiyaga dacewar yatashi yadaura Alwala yayi sallar isha'i sannan yanemi yardar Allah da amincinsa bisa wannan auren dayazomasa bagatatan yamike yanufi kofar dakinsa yayi baya tsorace yana ambatan sunan Allah domin karo dayaci da ma'u wacce keta shirgan baccinta haikan babu wata fargaba saida yanutsu sannan yasan itace mamaki yakoma kamashi yamatsa kusa da ita yanakallonta meyakawota nan meyasanyata bacci ahaka cikin daga murya yafara ambaton sunanta domin yaga alamar batasan dashi agurinba tafarka afirgice cike da tsananin tsoro dafirgita tana waige waige yadurkusa agabanta nine nana kwantar da hankalinki meyakawo ki nan kina bacciya yafada cikin rarrashi domin yakula duk akidime take tayi narai narai da idonta domin tana tsoron kar yadaketa Allah yaya tsoron dakin nakeji sai naji kamar anamotsi abayan kyauren yayi murmushi yace nana haryazu ke sokuwace ko? Tomeyasanya baki sanar da niba tasunkuyarda kai tanasosa keyarta cike da tsananin kunya yakula tunda suka iso gidan ma 'u kejin kunyar hada ido dashi shima nauyinta yakeji kwarai dagaske jinbata niyar cewa komai yasanya yamike yakama hannunta yanafadin taso muje ki kwanta kada kikara kwanciya anan bamusu tabishi amman hankalinta amman hankalinta yatashi saboda rikemata hannu dayayi saiya sanya tsikar jikinta tashi ahaka harsuka isa dakin yazaunarda ita gefen gado yanafadin to kwanta bari nakwanta akasan yadauko filo daya daga kan gado yajefar kan tayal yakwanta yajuyamata baya Umma tana kwance datsananin damuwa idonta nazubda hawaye batasan sheshshekar kukanta yabaiyanaba malam yamike zaune yakunna fitilar dakin yakalleta duk da tajuya masa baya yasan ba bacci takeyiba cikin raunanniyar murya yakira sunanta khadija kitashi nasan ba bacci kikeba tashi kisanarda ni dalilin kukanki tsoro dafargaba suka kamata ashe kukanta yabayyana har malam yajiyota tashiga ukku meyadace tayi yanzu nace kitashi muyi magana khadijah tsawarshi tasanyata mikewa dasauri jikinta yana rawa domin takula ran malam yabaci yatsareta da idonshi wanda yakada tayi jajir kisanardani abinda keranki khadija kigayamini komai da bakinki cikin rawar murya tace wlh malam bakomai araina karya kikeyi akwai abinda keranki deeje mutum bayayin kuka kawai saida damuwa nalura dake tunda nasanar dake auren ma'u da Ahmad yanayinki yasauya furkarki tanuna bakiji dadin hakaba shinkina kyamar Ahmad dan bayada ubane kece kike nuna jin haushin abinda wasu kemasa kamin wannan lokaci deeje baibarta tabada amsaba taci gaba dafadansa idan harkikayi haka kinbani kunya kinkuma ci Amanar ahmad Ahmad zaitabbatar da lallai bashida uwa bashida galihu kowa yana kyamarsa yakarasa maganar da kunci dazafin zuciya tadaga kai tanafadin kodaya malam wlh abinda kake zato nahaka bane bantaba kin Ahmad ba 2⃣1⃣ DAME AKE ADO 2 Bantaba danasanin kasancewarsa tare daniba bantaba danasanin zamanshi danaba haka banajin komai game da aurensa da ma'u kukan dakaga inayi banakin aurensu bane illah tausayinsu gabadaya Asma'u yarinyace karama bata iya komaiba saiwauta da tsiwa bankoyamata komaiba na rayuwar aureba nayi sakaci bantaba bata lbr meye aureba shikuma Ahmad yarone dabaisan komai gameda rayuwar aureba shin yaya zai kalli ma'u da halayenta inatsananin jin tausayin ma u dakewarta wlh wannan shine kadai abinda ke damuna amma har abada bazantaba dana sanin hada auren nan da akayiba nayi mamakinma da wannan zargin yazo ranka malam takarasa maganar datsananin damuwa yayi ajiyar zuciyar cike dagarinciki acikin ransa yana godiya ga Allah dayasanya ba abinda yake zargibane aran deejen ba yakalleta yayi murmushi Amman shirmenki yayi yawa waton har abada mace bata girma danwannan abinne kawai yasanyaki damuwa kodayake nasani harda soyayyar ma u dakukan rabuwa da itako yakarasa maganar da zolaya tasunkuyar dakai tana murmushi kasa kasa malam yaci gaba dajawabi kikwantar da hankalinki daga Ahmad har ma'u duk rainonkine watakima ahmad yafiki sanin halayen ma 'u dan haka babu wani abu dazaibiyo baya insha Allah sai Alkhairi nayi imani zaikoyarda ita komai tunda kinkoyamasa kokin manta da dannaki ya iya girki kala kala ne? Yakarasa yana dariya abinda yasanyata darawa itama ya dinga zolayarta haryasamu ta sakko Suka fahimci juna sannan suka kwanta baccinsu sunawa yayansu addua tunda asuba yatasheta tayi sallah shikuma yawuce massalaci bayan yadawo yazarto dakin yazauna yacigaba da lazimi itakam baccinta takara komawa aranta tanaganin babu abinda yafi gadonta dadi kamar wacce akatasa karfe bakwai tafarka ta tadda yayan nata har lokacin yana lazimi tamike tsam tanufi kofa ya bita da kallo kamar zaiyi magana saikuma yafasa don yayi zaton bandaki zatashiga itakam kicin tawuce tayi zaune tanasakawa da warwarewa akan abinda yakamata tayi domin sanda yatafi masallaci umma takira wayarshi tadauka umma tace waye tace nice tace yauwa daman kedin nakeson kidauka domin nasan yanzu Ahmad yana masallaci kinaji idan gari yawaye kishiga kicin ki girkamuku abinda zaku karya sannan kishare gidan kigoge ko ina nasan kin iya shara daguga dan kinayi amakaranta ko dasauri tace eh inayi tace to kitabbatar kinyi kinjiko? 2⃣2⃣ DAME AKE ADO 2 Takoma amsawa da to shine yanzu tana tsaka da bacci maganar Umma tatasheta tadauko doya tafara ferewa bayan takammala tayankata gutsi gutsi kamar zatayi faten doya sannan tadauki kwai ukku tafasa akan doya ta kunna risho tadora mai kozafi baiyiba takama kwan da doyar ta zuba tana jiran su soyu daga can acikin daki yafara jiyo kauri dasauri yamike domin zuciyarsa tabashi ma'u ce yanufi kicin din dasuri saiyaga doya da kwai da mai sunata zabalbala yarike baki damamaki yana fadin Nana mezakiyi? Mekike dafawa? Tayi firgigit ganin kallon dayake mata tace doya da kwai zanyi sai akacemiki kuma haka akeyi waye yasanyaki girki kuma baki iyaba cikin zafin rai yake maganar tayi kwal kwal da ido tana jada baya domin tana gudun kada yadoketa tace Umma ce tace nayi abincin Kari kuma............kuma..........yadoka mata tsawa get out mekika iya bayan shirme yadauko kaskon suyar daga kan wuta yayi waje dashi sukaci karo abakin kofa tana tsaye tana gunguni yayi baya dasauri dan sauran kiris yakifamata yakoma kuluwa yace Amman bakyajin magana nana bance kibar gurinnanba dasauri tawuce tabar wurin takoma gefe tatsaya yanufi gindin rariya da abinci yasamu kwano yazuba yasanya ruwa yawanke kaskon sannan yanufi kicin din tana tsaye tana kallonsa yadauki wata tukunya yazuba ruwa yadaura shayi duk tana tsaye tana hangensa yanata kaiwa da komowa acikin gida harya kammala dafa shayin yajuye aflask yanufi kofar gida tana ganin yafice tanufi kicin Don ganin abinda yayi bata hango komaiba tafara bubbude kwanika cikin tsautsayi bataga flask din yazuba shayinba tabangaje yafado jikake tush flask din yafashe shayin yazube atsakar kicin din tarike baki cike da tsoro dafargaba saita kasa gaba takasayin baya kamar ancilloshi yashigo gidan tundaga nesa ya hangota akicin yakarasa da sauri yana fadin nana meyakawoko kicin dinnan bance kada kisake kishigaba tayi tsuru tsuru daidai lokacin daya karasa yadauki dogon salati sanda yaga flask din shayi duk kwance akasa yana ambaliya ya kalleta yama rasa abinda zaice cikin rawar murya tace Allah yaya bangani bansan da flask agurinba yayi ajiyar zuciya yayi kokarin hadiye fushin shi domin ma'u yargaban goshin shice duk da banzan rawar kanta yanunamat kofa zokiwuce daki maza tataho tana rakube rakube tana goge ido tana gudun kada yadoketa har ta isa bakin kofa data samu tafice ta falla da gudu saida tadire acikin daki sannan tazaya tana haki da dariya wai Allah nagodema da yaya Ahmad ya mini irin ko rankwashinsa ne aida naga takaina tarike haba tana haki shi kam kada kai yayi da takaici sannan ya shiga yashare kicin din yakara dora wani shayin yazuzzuba akofi yakaimata nata hardaki ta amsa tana fadin nagode yaya 2⃣3⃣ DAME AKE ADO 2 yadaga kai kawai sannan ya zauna yafara shan nasa ma'u tadubeshi yana shan shayin tace yaya don Allah zankoma makaranta kaga ranar monday za afara jarrabawa kuma Abba yace saikayadda zankoma yadaga kayi yakalleta saiyaga ikacin gaskiyarta take maganar babu wani bayani dazaiyi uagamsada ita saiyace aibazakiyi wannan jarabawarba kihakura kawai tawaro ido cike da fargaba yaya kanufin nadaina karatu kenan kainefa kace zanzama likita yajijjiga kaida damuwa ma'u tayi kankanta da Aure tayi kadan dafuskantar irin wannan matsalolin donhaka gara yasanar da ita gaskiyar komai yadubeta da nutsuwa yace nana kinsan yanzu ke matar aure ce ko? Tadaga kai alamar eh yagyara zama yauwa kinga ai makarantarku ta yanmatace babu matan aure ko? Towannan dalilin yasanya bazaki kara komawaba kinkammala makarantar kenan yanzu zakizauna zaman aurenki kinemi Aljannarki tamike atsorace cike dafaduwar gaba yaya zakace haka yaya Ahmad shikenan niyanzu bazankoma zuwa ko inaba sainan gidan kuma bazan zama likitaba......yaya bakayin karya amman yanzu kayi meyasanya tambayar tacazamasa kwakwalwa harya rasa amsar dazaibata saiyasake hade ransa yace kincikani dasurutu nana tashi maza kiyi wanka kishare gidan kiwanke kwanika tayi narai narai da ido domin tana matukar son karatunta tace amman yaya...............yadaka mata tsawa isaid get out ma'u jikinta yadauki yadauki rawa hawaye yamakale ido yafara tafice dasauri ta nagoge idonta tana aiki tana kuka yanajiyo sautin kukan nata bashida zabi babu yanda zaiyi abba yagama yanke hukunci daga karshe ma saiyayi wanka yafice yabar gidan wannan shune yakara dagamata hankali saitaji gidan yakara mata girma tazauna tsuru babu abinyi sai tsoro yafara shigarta tamike tanufi soro takama leken waje tana hango mutane dake kaiwa da komowa saitaji sanyi aranta donhaka saita zauna akofar gidan tana kalle kalle dakaramin hijab akanta idan taga abin dariya tayi idan taga abin mamaki tayi mutane suna wucewa suna kallonta babu wanda yayi zaton matar gidance domin komakota basusan ankawo amaryaba sunyi zaton Raliya ce itakuwa daga yanayin kawayenta da gantalin datake fita kullum yasanya suka gano bamatar arzikiceba donhaka babu wani wanda yarabeta tsawon lokaci tananan zaune tana cike da nishadi shikam Ahmad gidansu yanufa kaitsaye yatadda yan uwansa sunzo dayake ranar assabar din karshe sati ce anata cafta saiyazauna anatayi dashi Umma saishige dafice takeyi wurin ganin takammala kirkin rana kunya da nauyi sunhana ta tambayi ma'u takula shima Ahmad kunyar yimata maganar ma'u yake amman daga yanayinsa talura babu wata matsala anan sukaci abinci lokacin da inna tazuba abincinne ma yatuna da ma'u da abinda zataci saidai Allah yataimakeshi umma tacika flask din da dambu datayi tadire tace gana yar gidanka Ahmadu yaji dadin hakan danyana kammala cin abincin yadauki flask yahaye babur dinsa yanufi gidanshi abinda ybashi mamaki da tsoro baiwuce hangon ma'un shi zaune akofar gida daramba tana hirarta da wasu yara da alama yayan makota tasamu tabiye musu yanacigaba da karatowa mamakinsa nakara linkuwa harzuwa sanda ya iso indatake da babur dinsa tadaga kai takalleshi saitadan firgita masamman yanda yanayinsa yacanza lokaci guda takalli yaran dake gabanta tayi duru duru sai tamike ta shige cikin gida dagudu batayi birki ko inaba saibayan gado tana huci talabe cankurya tana maida numfashi yashigo gidan ransa yana suya ya iso harbayan gadon yajawo kunnenta tafasa ihu jikinta naci gaba da bari dan Allah yaya Ahmad kayi hakuri Uban wa yace kifita waje kizauna komunkoya miji wannan tarbiyar agidane? Cikin sheshshekar kuka tace A ah gidan ne shiru ga tsoro shine naleka waje don Allah kayi hakuri tafashe dakuka yadunkule hannu ya rankwasheta yana fadin koda zanhakura saikinji ajikinki kifita kofar gida kizauna kamar wata sokuwa inakikakai aurenki yakoma rankwashemata kai kwas akanta takuma sanya ihu saida yajeramata guda hudu sannan yasakarmata kunne takuma fashewa dai kuka lokacin yafice daga cikin dakin yanufi shago domin yasanya uniform dinshi yatafi wurin aiki saidai yanashirin kukan ma'u yana dukan zuciyarshi tuncan baya bayason bacin ranta yakanyi komai dankar abatamata rai balle dayaji sunan mahaifiyarsa ne akasanya mata hakan yakara soyayyarta acikin zuciyarsa yanzu kuma gashi tazama matarsa wato yanzu soyayyarta agareshi hawa ukku ce don haka dole intana kuka yarikaji harcikin bargonsa da kyar yakammala shirinsa yanufi soro da zummar yafice saikuma yaga rashin dacewar hakan dan haka yajuya cikin gidan yanufi dakinta tana rakube a inda yabarta abayan gado tana kuka ya isa inda take tahada kai da gwiwa tana sharbe yakira sunana tadago takalleshi dafaduwar gaba don batasan yadawo dakinba tayi zaton kara dukanta zaiyi donhaka tafara ja dabaya tana sharbe majinarta tana kuka 24 April 2015 at 08:03 · Public Save · More Like React Comment Share Like51 Write a comment... · Aminu M Sirajo Tnx Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Omar Uba Abbaskk tnx Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Bakoji Lamara Misau Gud Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Bilkisu Mukhtar Tnx.. Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Zainab Yahaya Bappah mungode muna jira Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Hassan S Saddiq tnx Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Usman Mustapha Yayi Kyau Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Faisal Sa'ad Isma'il Mungode Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Afra Ahmad Please ayi posting kallon kitse Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 Fatima Yaquub tnx Like · React · Reply · More · 24 Apr 2015 View more comments… Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Sirrin zuciya DAME AKE ADO part 11. 2⃣4⃣ DAME AKE ADO 2 Dan Allah kayi hakuri wlh bazan kara fitaba nadaina..........yakada kai yana karemata kallo wlh da Abba yayi shawara dashi dazaice abar ma'u takammala karatunta tazama cikakkiyar mace kafin ayimata wannan auren yarinya ce tsaba yanzu tafara kirgen dangi irin namata baikallonta da komai haryanzu sai kanwarsa ihunta yadawoda shi hayyacinsa yace kinga badukanki zanyiba cewa zanyi kidaina fita waje idan nafita zanturo miki yaran sudinga tayaki hira kinjiko? Tadaga kai dagamsuwa tanacew to tuni kukun nata yakoma ciki tafara dariya gawannan idan kinason cin wani Abu kisaya gakuma abinci can aflask Umma tace akawomiki ta amsa hannu biyu tana godiya yakada kai yafice tabishi dasaikadawo yaya kamar yadda tasaba yimasa agida ya amsa da Allah yasa yafice takalli dari nan tadaka tsalle cike da murna waiyau itace keda dari duk tatace lallai Allah yasanya yara sushigo su siyomata agwalima yayi sa akuwa yan yaran dayatadda azaune dasu har lokacin sunanan zaune suna wasansu don haka yace maza suje sutayata hira dahanzari suka shige gidan suna murna sallamarsu tatsinkayo acikin gidan tayi waje dagudu cike da murna sai alokacin tahango flask din abinci tashiga kicin tadauko faranti tadebi nata suma tazuba masu nasu suka zauna sunaci suna hira itakuma tana kwasar dariya tundaga wannan rana gidan nata yazama gidan yara domin ance laifi yaro kiwa laifin babba rowa Asma'u kam hannunta asake yake akwaita da kyauta Ahmad hankalinsa yakwanta shike hadamusu abinci dazasuci dasafe darana da dare saidai idan yasan yanada aikin safe tun asuba zaidora kirkin rana yazuba aflask ya ajiyemata da daddare kuwa yazomata da ( take away ) domin yace batayi wayon dazatayi girkiba harta kunna risho ba aikinta kawai wanke wanke da shara ko wanki shine kemusu sanda yakeda lokaci saidai yanashan fama da kurciyar ma'u da shirmenta yautunda safe yakammala girkin yazubamata aflask yarufe harya kammala shirinsa tana gindin Tv tana kallon NTA muhawarace akeyi da daliban makarantarsu dana wata makaranta cikin harshen turanci tanajin kamar tatsallake tafada cikin tv idan anyi tambayar dayan makarantar suka kasa amsawa tasani saitayi karaf tace dan Allah kazane kuce kaza ahaka ya isketa tsahon zamani yana kallonta batasan yazoba tausayinta yakamashi ma'u tanason karatu kwarai shima yanason tayi karatun saidai yanada tsananin kishi bazaitaba yadda ace matarsa tanazuwa makaranta kullumba dama dai ace takammala karatunta akayi aurensu dayaga batada niyyar dawowa hankalinta yakira sunanta tawaiga dasauri tace la yaya harka gama shiri zo dan Allah kaga wadannan sokayen sunkasa amsa tambayoyo nafi sauki kumafa sinio dinmune a school yayi murmushi yace nana nidake sauri zantafi aiki inanakeda lokacin kallo amshi Nan yamikamata kudin tasanya hannu ta amsa yaci gaba da magana zanwuce sainadawo akwai abinci aflask banason barna dawarkai kada kilalata komai kinjiko idankuma andauke wuta kikashe kayan kallo duka dan kada akawo wuta sulalace ta amsa dato tana cigaba da kallonta haryakai bakin kofa baiji tace saikadawo ba yawaiga yakalleta yace yauba babu adawo lfy kanwata dasauri tace lah yaya namanta adawo lfy tana fadin haka tamaida kanta wurin kallonta yayi dariya yafice baijima dafitaba kuma nepa suka dauke wuta bakinciki kamar yakasheta domin taso taga karshen wasan takoma kan kujera takwanta tafara tunane tunanen duniya kwatsam yayarta kuma kishiyarta tafadomata saitaji gaba daya ranta yabaci saidai abinda kedauremata kai baiwuce rashin zuwa gurinta da yaya Ahmad keyiba ko maganarta ma bayayi sam tanason tatambayeshi amman kishi da haushi raliya yahanata don haka tabar abin cikin ranta tana kwance tana sakawa da kwancewa har kawayenta suka fara shigowa tamike tafita suka fara lido A'ilo daya daga cikin yaran ta kalleta tace waike ma'u bakyayin sabon girkine kullum saidai naga kindebo acikin flask ma'u tatabe baki da damuwa ban iya girkinba yayana ne yakeyi yazuba acikin flask A'ilo tace cabdijan to idan bakya gwalgwalawa yaza ayi ki iya kinganni bankai girmankiba har wake dashinkafa nake dafawa babanmu arisho bama da murhuba mamaki yakama ma'u tace ke A'ilo koni danagirmeki ummana bata bani girkina saitace kazantane saidai kawai na izamata wuta amman kice harwani girki akebaki A'ilo ta tafa hannu tadoki cinya shekarata shabiyu amman wlh ina girki tambayi kanena ma sale idan yashigo saiga sale yashigo da gudu tamkar yasan nemansa ake A'ilo tace yauwa sale zo dan Allah banayiwa ummanmu girki sale yatsaya yana haki kinayi mana ranar har danwake kikayimana ma'u tafe kirji danwake lallai kin iya girki daman inason na iya don allah ya akeyi A'ilo tayi murmushi dadai akwai fulawa ne dasai nanuna miki yanda akeyi ma'u tace bari naduba inada yake ajiye kayan abincin nasa Allah yasanya da fulawar daman nagaji dacin shinkafa da miya ko dafaduka shikenan fa abinda ya iya tanufi dakin taduba ga rashin sa arta bata tadda fulawaba amman saitace ga kudi asiyo gwangwani ukku nafulawa su kwaba dadi ya cika yaran suna murna yauzasuci girkin amarya ihu suke yi tamkar ranar sallah nandai sale yafalle dagudu yasiyo fulawa aka kwada aka kunna risho aka fara kokarin saka danwake gabadaya akaduru akicin din sugoma A'ilo ce agan risho tun ruwan bai tafasaba akafara saka danwake duk sanya daya sai anyi ihu tafi ahaka akammala sakawa aka koma gefe anajiran yatafasa gabadaya danwake ruwa yahadu ya cakude ahaka akafara kokarin saukewa anduba babu tsumman da za asauke ma'u tace bari tasauke bakin zanenta takama tana kokarin saukewa ashe zanin yalaso wuta zafin wutar dayatabota yasanya tafasa ihu tasaki tukunya da zaninta dayakama da wuta nanfa akayi waje ana ihu domin ruwan danwake yafadi akasa yafallasawa kowa zanen ma'u yacigaba daci dawuta sukuma suna ihu gobara! Gobara!gobara haryafara laso kayan kicin kamar Anjefo shi Ahmad yashigo agigice jin ihunsu yahango abinda kefaruwa yakalli ma'u dake ihu daga ita sai siket duk saiya dimauce yama rasa mezaiyi candabara tafadomasa yadauki wani omo da ruwa yanufi kicin dagudu yafara watsawa dakyar yasamu tamutu yadawo dabaya yatsaya yana haki saikuma suka kama ihu wai wutar tamutu takaici ya isheshi yanufesu afusace yafara dukan yaran suka sukayi waje aguje afirgice domin abin yabasu mamaki domin sunsan duk ihun dasuke baya ce musu kala amman yau saigashi harda duka yakoma kan ma'u yazabgamata mari yakoma zabgamata tafasa ihu tarike kunce maimakon tabashi tausayi saima kuluwa yayi yahauta da bala I sai da yayi iyakacin son ransa sannan yanufi kicin din yafara gyarawa ranar dai har dare yana bala'i da masifar dabatasanshi da itaba tayi kum adaki saikuka washe gari baije ko inaba yakuma hana kowashigowa gidan duk yaron dayazo saiya fatattakeshi yafita dagudu dan haka adaki tawuni tawuni tanakuka saidai tagama saka abinda zatayi lokacin daya fita sallar isha'i tadauko kayanta data kulle adankwali tanufi hanyar soro tanatafe afirgice cike da tsoro domin batason kowa yasan inda zata gudu tagaji dazaman gidan tunda aiba birsina baceba tafito tajanyo kofar gidan ahankali tabi gefen duhuwar dake kofar gidan tafara sauri tana waige don batason wani yaganta HMMM MUHADU AKASHI NA UKK U DAME AKE ADO BOOK 3 1⃣ DAME AKE ADO 3 Ma'u tanatafe cikin duhuwa tanata sauri burinta tayi nisa dagidan cikin ranta tana saka bazataje gidan yayyentaba kogidan umma bazata ba domin zasu iyadawo da ita gidan yaya Ahmad shikuma yacigaba da dukanta yana kulleta cikin gidan kamar mayya bata Ankaraba tayi karo Dawani mutum kayanta suka zube yayi taga taga kamar zata fadi Allah daiyasanya bata fadinba mutumin yazabga salati yana kokarin bata hakuri saigabanta yahau bugabawa domin muryan yayan natane hakan yasanya tagintse bakinta batace komaiba tasuri kullin kayanta tawuceshi dasauri cikin ikon Allah aka kawo wuta daidai lokacin da Ahmad kebata hakuri yadan bita da kallo da mamakin jin wacce yabuge din batace komaiba

Chapter 5 of 15