Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shirin kiran Ma'u sai kuma ya kama Waya da Nana data kirashi. Anan ya shantake har bacci ya d'aukeshi bai nemi Ma'u ba. Yana tashi da safe ma da shirn fita yafito, kasancewar Abokinshi Jabir yashir yamasa'Yar walima suda Abokansu da suka yi Karatu, san da ya riga 'Dakin Ma'u don yin magana da ita aka ce tana Wanka, shi kuma ba zai iya tsayawa jiranta ba, saboda an dameshi da kiran a Waya, don haka ya juya ya fice. Wannan abin ya k'arawa Ma'u tsoro a ranta har take ganin tata ta k'are guqin Ahmad, ba shi da sauran lokacinta, kuma yanzu bata k'ara ganinshi a Gidan ko jin Wayarshi ba har dare sai 'yan kawo Amarya suka fara jerin gwano da Motoci, tun tana iya ganin adadin motocin da suke ta zuwa har ta kai ga gaza yin hakan, harabar Gidan k'ato ne zai iya cin motoci k'anana hamsin, kuma 6angare Nana da Ma'u daban, akwai 'yar tazara mai nisa ma. Asalin Gidan Alhaji Nura Kwangila ne da ya 6ata shekaru yana ginawa ya bai wa Ahmad da zummar shi zai k'ara gina wani Gidan nasa. Gud'ar kawo Amarya da ake yi kamar cikin ran Ma'u ake yinta, gashi lokacin babu kowa a Gidan, duk jiya aka zo mata, daga ita sai musu Aiki sai ta fashe da kuka ta had'a kai da bango tana kuka. Gabaki d'aya Gidan yayi mata zafi da kunci, Babu abinda take so illah ta fita ta barshi ko yata huta. Tana nan har 'yan kawo Amarya suka watse. Can wajen k'arfe goma da 'yan mintuna Ahmad ya iso Gidan. Kai tsaye 'Dakin Ma'u ya nufa, ya sha mamakin ganin bai ga komai akan fuskarta ba na 6acin rai, don ita kad'ai ta san abin da ta k'udurce a cikin ranta. Ya d'an zolayeta tana murmushi ya buk'aci suje sashin Amarya tace ba dai yau ba sai gobe. Ya ajiye mata kasonta da ya shigo da shi yayi mata sai da safe ya nufi sashin Nana cikin d'okin da yakasa 6oyuwa akan fuskarshi don yau kusan tare ya yini da nana, Kwalliya ta dinga yi ta tsumashi k'warai da gaske, wannan abin ya yiwa Ma'u ciwo k'wari da gake, yana fita ta k'ara fashewa da kuka. Wai yau Ahmad d'inta ne ke nuna zumud'in akan wata mace ba ia? ta dinga kuka, kusan haka ta kwan da damuwa. Shi kam Ahmad yana shiga 'Dakin Amaryarsa ya d'an zolayeta tak'i sakin jiki sai ya sureta cak suka yi ban'aki yin alwala idnta a rufe da kunya. A gsky a matse yake da Nana don tun randa ya ganta kusan tsirara sha'awarta ta gama nuna a cikin ranshi, don haka suna idar da Sallar ya fara nuna mata buk'atarshi da yake itama ta jima da jiran wannan lokaci bata yi wani nok'e- nok'e ba ta bayar da kanta. Abin da ya bashi mamaki bai wuce ganin bai sha wata wahala kamar yadda ya sha akan Ma'u ba, nan da nan yaji ya gamsu. Bayan ba haka yake so ba, yayi kykkyawan shirin da zai yi yanda yaso, sai dai bai samu ba yanayin shekarun Mace 'yar shekar 16 17 da mai shekara 23 da 24 akwai bambanci, don ita 'yar 17 komai nata k'ank'ani yake bai saki ba, sa6anin na wacce ta d'an yi shekaru 20. Sannan kuma a daren ya fuskanci Nana tana da tsawon buk'ata, sai yayi mamakin dalilin da sanya ba tayi aure da wuri ba. Ko da yake da alamunta bata ta6a yin mu'amala da wani na. 3 November 2015 at 10:02 · Public Save · More Like React Comment Share Like38 Write a comment... · Samira Umar DAMAHAKA SUKE Like · React · Reply · More · 4 Aug 2019 Abdul Zuhra Mun gode allah ya kara kaifin basira Like · React · Reply · More · 4 Aug 2019 Usman Aliyu Taller Godiya mai yawa Like · React · Reply · More · 3 Nov 2015 Rukayyah Abk tnx Like · React · Reply · More · 28 Feb 2017 Ibrahim Ubali GD Like · React · Reply · More · 3 Nov 2015 Binta Binta Muna godiya Like · React · Reply · More · 27 Feb 2017 Muazz Alawo tnks Like · React · Reply · More · 3 Nov 2015 Abubakar Ibrahim Good Like · React · Reply · More · 3 Nov 2015 Isah Aisha Hmm ai maza dama haka suke mtswwww Like · React · Reply · More · 27 Feb 2017 Hafsat K Dawud Godiya muke Like · React · Reply · More · 3 Nov 2015 View more comments… Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Jamila Umar Tanko Books DAME AKE ADO 4**21 Ko da yake da alamunta bata ta6a yin mu'amala da wani namiji ba don ta d'an wahala, amman sai yaji daren farkonshi da Ma'u yafi wannan nesa ba kusa ba, amman ya bar abin a cikin ranshi. Ita kuma Nana wannan shi ne dare mafi alkhairi a rayuwarta. Sai a yau ta gano ashe tana k'warar kanta da rayuwarta, jikinta yana bukatar wani abu da take tauye masa lallai Ahmad ya kai ta gurin da baa ta6a zuwa ba, bata ma ta6a Mafarkin zuwa ba. Da safe duk da Ma'u tana ranshi gajiya da kasala bai barsu sun fito da wuri ba rai wajen karfe goma sha daya na safe. Lokacin sun shirya ya ce da Nana tazo su shiga gurin Ma'u su gaisa suka jera suka nufi shashin nata. Masu aiki suna ta hidimarsu, suka shiga suka dinga gaishesu, sai wata Yaya abu ta fito daga Kicin da sauri ta mik'awa Ahmad wata takarda tace inji Hajiya tace a baka. Da mamaki yace "Wacce Hajiya ke nan? Ciki ldabi tace, 'Hajiya Ma'u mana...." Tana ina yanzu, tana cikin 'Dakin ne?" Tace, "Eh ta fita tun wajen Asuba....." Ya katseta da fargaci "Ma'un! ina ta tafi? "Wallahi ban sani ba nima Alhaji. Damuwa da tashin hankali suka bayyana akan fuskarsa, sai ya ce Babu damuwa jeki kawai. Ya kalli Nana dake kallonsa da fargaba sannan ya maida hankalinsa ga wasikar ya bud'e. Ga abinda ta k'unsa, Mijina Ahmad. Nayi iyakacin kokari na danne zuciyata na zauna da kai, amman na kasa don na gano a yanzu kayi mini nisa, ka girmi rayuwata, wancan Ahmad din Mijina da muke dai-dai shi ne Talakan nan mai kula dani, da cina da sha na, mai kula da yanda na kwana da yanda na tashi, ba kai ba babban mutum! A yanzu rayuwarka tafi dacewa da d'iyar masu Kud'i da arzik'i irinka ba wadda kake taimako ba, mai ilimin degree da Master's da wayewa. Rayuwarka ta girmi ta Ma'u yanzu, don haka naga yafi dacewa na matsa na baku guri, na san ba zaka iya sakina ba saboda kunya da tunanin kad duniya ta zageka, don haka na hutar da kai na tafi inda ba zaka k'ara ganina ba, ba zakaji kunyar iyayena ka sakeni ba, amma ina son wata rana ka furta sakina ko cikin ranka ne, don kada nayi ta yawo da aurenka. Ga kuma amanar 'ya'ya nan, wata k'ila zan gansu watarana. A lokacin daza ka ci karo da wannan wasik'ar tawa tuni nayi nisa daga inda kake! ina yima ka fatan alkairi kai da Matarka! -ASAM'U MATARKA A BAYA Wani irin abu yabi ta jininshi ya wuce zur! Kamar wutar nepa taja shi, ya waro ido da fad'in, "Wht? Me kika aikata haka Ma'u, yaya kike tsammanin zan rayu babu ke?" Nana ta kalleshi ganin kamar yana shirin zarewa ne tace, Yaya Ahmad lfy, me ya faru?" Cikin kid'ima tace, "Ma'u ta gudu! Tabbas cikin satin nan na wofintar da rayuwarta, ban damu da damuwarta ba, hakan ya sanya ta yi zaton na daina sonta ne! Yaya zan yi, na shga ukuna, wallahi idan babu Ma'u ba zan rayu ba, bari naje na gayawa Abba da Umma....." Sai ya juya ya nufi hanyar fita daga Falon, nana tayi hanzarin ruk'oshi da sauri tace, "Haba yaya Ahmad, wannan matsala ce tsakaninka da Matarka, ka san ko ina Ma'u zataje ba zata yi nisa da kai ba, 6acin rai ne ya sanyata tafiya, idan ka gayawa iyayenta kamar ka tona muku asiri ne, zaka iya janyowa su yi fishi da ita" Maganganun Nana suka shgeshi yace, Haka ne, Yanzu me ya kamata nayi? Don Allah gaya mini Nana, kaina ya kulle, ina tsananin son Matata!" Ta ciza baki tace, Kaje kowanne Gida da kasan zataje Bada sunan cigiya ba da sunan kaje gaishesu ne, ta haka zaka gano inda ta shiga..." Yace, "Yauwa haka za ayi Bari na dawo. Yafice da sauri a rud'e, ta bishi da kallo idonta ya cika da k'wallah. Lallai Ma'u tayi nisa a zuciyar Mijinta, idan kuma tace sai tayi gasa da ita zata iya zamantowa a cikin takaici, abu d'aya ne zai janyo sonta ya zama d'aya dana Ma'u ko ma ya fishi shi ne Asiri, wanda bata ta6a sha'awar yin sa ba, don wad'anda taji labrin sun yi ma bai amfana musu da komai ba. Ta goge hawayen dake zubo mata ta nufi sashinta. GA AHMAD kuwa, dukkan inda ya san zai samu Ma'u sai da yaje har yamma tayi masa ya gaji lik'is ba tare da ya gano inda take ba, ya fara sarewa da tunanin ko ya sanar da iyayensa, don duk Wayoyinta Ma'u a kulle suke. TUN DA MA'U ta isa garin zaria gidan k'awarta Maryam wacce tayi aure kusan shekaru uku da suka wuce ta auri wani Soja take kuka da k'yar Maryam ta rarrasheta ta sanar da ita abinda da ya faru ta had'a da rok'onta akan ta rufa mata asiri ta barta kada ta gayawa kowa tana gurinta har zuwa sanda zata san inda zata tafi don ba zata ta6a komawa gidansu ba ko gurin damginta ba har abada! Maryam tayi matuk'ar mamakin jin labarin da Ma'u ta bata, amman sam bata ga laifin Ahmad a cikin wannan labari ba, ko don ita ma tana da Kishiyar ne? ita ce Amarya. Da Ma'u ta san irin halin da Kishiyarta ta shiga san da zai aureta da ta ce Ahmad d'an Aljannah ne, don haka ta fara baiwa Ma'u hak'uri da bata labari kala-kala na Mazajen da zasu yi aure, 4 November 2015 at 11:34 · Public Save · More Like React Comment Share Like47 Write a comment... · Muhd Dawud Rano Mungode Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Ibrahim Dm Naimat good nd 5n Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Bakoji Lamara Misau Gud Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Abubakar Sulaiman Kaura Yar shegiya kawai Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Rabi'u Khulsum Inuwa replied · 3 replies Hassana Gwarmai Nice Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Umar Dahiru Tnx Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Abubakar Ibrahim Hmmm Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Hasana Auwal Abbakar karkaga laifinta Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Ummu Khadijah Ummu Adnan Hmmmm Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 Azinatu Umar TNX Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015 View more comments… Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Jamila Umar Tanko Books DAME AKE ADO 4**22 duk da jikin Ma'u yayi sanyi amman tace ma ta ita dai ta kyaleta. Daga k'arrhe ta d'ora da ce mata. "Yanzu haka mijin nata yana gidan Uwargidan zai mata kwana biyu ba zata k'ara ganinsa ba sai bayan kwana biyu koda cuta zata kasheta ita da d'anta kuwa, ga rashin wadatasu da yake yi, aikinta shi ne gatanta (Da yake tayi Karatu mai zarfi har digiri) amman tana lalla6a aurenta domin ta jima bata sami yin saba. Duk da maganganun Maryam sun shigi Ma'u amman kishi ya rufe mata ido tace ta kyaleta, Sai ta rok'eta ko Massage ne ta yiwa 'yan Gidansu ta sanar da su inda take don hankalinsu ya kwanta, sai Ma'u tace ashe tana fatan Ahmad ya dawo mata ma ke nan? Haka suka dinga tata6uza har dare yayi. Sai dai wani abu da yake bai wa Maryam shi ne, tsawon yinin wannan Rana Ma'u tana kallon huton Ahmad Mijinta a cikin wayarta da ta sanya sabon layi, abin sai ya bai wa Maryam dariya. Wajen k'afe gama na dare aka fara buga K'ofar gidan da yake Gida ne irin na k'ananan masu rufin Asiri, babu Maigadi. Da sauri Maryam ta d'auki Wayarta tace, "a k'araso? yauwa gani nan zuwa. Ta nufi Kofa, sam Ma'u bata kawo komai a ranta ba. Tana kwance akan Kujera ta rintse idonta har suka turo K'ofa suka shigo. K'amshin Turaren da taji ne ya sanyata bud'e ido da sauri, Turaren Ahmad daya ne, tun yana talakansa har zuwa yanzu da yayi kudi, don haka ko cikin Bacci ba zai 6ace mata ba. Yana tsaye jikin Kofa idonshi yayi jajir! kamar Gauta, duk yayi bak'i yarame, yini daya tal! Bak'in ciki ya cika Ma'u, ta kalli Maryam da tsananin takaici da harara. Maryam tace, Kiyi hak'uri Ma'u, idan har na bar Mijinki da iyayenki cikin damuwa bayan na san halin da kike ciki ban yi musu adalci ba, ban kuma cika masoyiyarki ta gsky ba. Ma'u ta mik'e a fusace ta nufi K'ofar fita, amman Ahmad ya cafkota ya matseta tsam a jikinsa, ta dinga fisge-fisge da k'ok'arin k'wacewa amma ta kasa, sai ta fash da kuka tana fad'in, Me ya sanya ka biyoni, nace bana son aurenka, kaje ka zauna da 'yar uwarka. jininka, ka barni na tafi dom Allah Yaya! Ka tafi Yaya!!" Tana magana tana kukka, amman tana rik'e gam a jikinsa ya ki sakinta. Sai da tayi mai isarta tayi shiru tana shesshek'ar kuka, Maryam tana tsaye tana kallon ikon Allah, soyayyar Ma'u da Ahmad na burgeta. Cikin sanyin murya Ahmad ya fara magana, Wallahi Ma'u da Maryam bta sanar dani kina gidanta ba da babu abnda zai hana zuciyata bugawa, tun daga lokacin dana gano baki tare dani ban huta ba, ban sha ruwa ko mukurwa goda ba, ban ci abici ko loma daya ba, Na gode kwarai da gaske, Allah Ya bar zumunci. Ya dauko Bandir d'in Kudi da bai san adadinsu ba ya bata ta amsa da zumud'i tana godiya, don daman wata yayi nisa bata da kud'i, kuma komai nata ya kare. Har gaban Mota Maryam ta rakasu, sai da taga tafiyarsu sannan ta juya ta nufi gida. Bayan ta kulle gidan a ranta tana cike da sha'awar soyayyar Ma'u da Mijinta Ahmad su dai kam basu yi sa'ar aure ba sam! A can hotel d'in Ahmad ya dinga lalla6a Ma'u da k'yar ta yarda zata yi wanka tace amman ba zatayi tare da shi ba, dole ya kyaleta. Tana daga Ban'Dakin taji kira ya shigo Wayarshi, don bai jima da kunna Wayar ba, sai ta jiyoshi yana "Eh na ganta...!!" Ban san sanda zamu dawo ba gaskiya....Sai da safe...!!" Daga yanda yayi maganar ta san da Nana yake, sai taji tausayin Nanan ya kamata tana bin Namiji yana mata yanga. Shi kuma haushin Nana yake ji yanzu don yana ganin kamar itace ta janyo masa duk wannan matsalar ma. A6angaren nana har sai da tayi hawayen takaici. Duk da Ahmad yaso samun wani abun a wajen Ma'unsa amma sai yaga ta had'e rai ta kwanta a Falo ma, dole ya k'yaleta. Washe gari da safe suka wuce Kano. Nana taji dad'in ganinsu taji dad'i, tay murna, ya had'u guri d'aya yayi musu nasiha da rok'on arzik'insu su zauna lafya. A gurin ne Ma'u tace ta bai wa Nana kwananta na Wata guda, Ahmad bai ji dad'in haka ba, amman babu yanda ya iya tunda lalla6ata yake yi. Ita kuwa Nana dad'i ne ya kamata har farin ciki ya bayyana akan fuskarta. Cikin wannan Watan Ahmad ya shiga tsananin damuwa da tashin hankali, ya yin da Nana ta more Amarcinta yanda taso. Mijinta ya d'ebe mata dukkan damuwa da kewa. ita kuwa Ma'un da wannan damar tayi amfani gurin neman NAFISA LILI 'YAR NIJAR ta harhad'a mata Magunguna na gyaran jiki, wato MAI DA TSOHUWA YARINY! Ta dinga Sha da Tsarki dana Turare. Cikin wannan lokacin ita kanta ta san ta sauya, don haka Ahmad idan ya ganta kamar ya cinyeta, Don akwai sanda ya gaza hak'uri ya matseta a d'aki suka dinga rikici tace wallah ta d'auki alk'awarin bazata ci amanar nana ba sai dai suje gabanta ya gaya mata shi ne yace sai ta karya, abinda ta san ba zai iya ba. Haka dole ya hak'ura ya kyaleta don ba yai iya yin Raping d'in Matarsa ba, don yana matse k'warai da gaske, dole ga nana ya kai bukatarsa. 5 November 2015 at 10:51 · Public Save · More Like React Comment Share Like37 Write a comment... · Shuraihat Ummu Ammar da kyau ma'u but nana kina bani tausayi nd i love u oll!! Like · React · Reply · More · 16 Oct 2019 Rahmat Mums Tnks Like · React · Reply · More · 15 Aug 2018 Safiyya Hussain INA YINKI MA,U Like · React · Reply · More · 22 May 2019 Habibu Abubakar TNX.PLS LETS GO AHEAD Like · React · Reply · More · 18 Oct 2018 Firdaus Feedy Paradise Tnx Like · React · Reply · More · 5 Nov 2015 Hafseeyat Hafseeyat Abubakar Namadi Dan allah acigaba allah qara hazaqa Like · React · Reply · More · 5 Nov 2015 Umar Sg Asma'u Aci gaba pls Like · React · Reply · More · 9 Nov 2015 Umar Dahiru tnx Like · React · Reply · More · 5 Nov 2015 Bakoji Lamara Misau Gud Like · React · Reply · More · 5 Nov 2015 Hafsat Ibrahim Garba Tanx Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 View more comments… Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Jamila Umar Tanko Books DAME AKE ADO 4**23 Dole ga nana ya kai buk'atarsa. Wannan ya yiwa Nana dad'i, wannan abu da ma'un tayi mata ya sanya take girmamata k'warai da gaske, sannan ta rik'eta kamar 'yar uwa, za a gaisa ayi wasa da dariya dai-dai gwargwado. Ammam ranar da Ahmad zai koma 'Dakin Ma'u Nana ta raina kanta ganin yanda yake ta zumud'i da rawar k'afa har taji Kishi ya rufeta a ranta tace sai kace ba gurin tsohuwa zai je ba. Tun daga iri rigar baccin da Ma'u ta sanya ta tsokanoshi ya dinga binta da kallo tana wani kwarkwasa da yanga har dai ya gaji ya janyota yana fad'in, "Yarinya wallah baki isa haukatani ba. Ta fashe da dariya don ta gano ya shiga tarkonta.Ranar kam saida ta raina kanta don a daren nan saida ya fanshe watanshi guda, musamman da yaji ta kamar ba Ma'unshi ba ta koma masa wata 'yar Budurwa kamar daren Amarcinsu. Wannan daren kam sun k'arar da shi gurin nunuwa juna yanda suka yi rashin juna. AHMAD ya gama gano yanayin Matansa, don haka yaci Maganin zama da kowacce dai-dai halinta. Ita dai Nana tana da tsananin buk'ata, don haka kafin girkinta ya fita sai ta isheshi, ita kuma Ma'u shi ne yake da tsananin buk'atarta saboda gyara da kuma yanayin halintarta, don haka har Nana ta ganoshi dole ran Girkin Ma'u d'okin yake yi da zumud'i, ita kanta Ma'u ta gano hakan, sai dai yana iyakacin k'ok'arinsa gurin ganin ya kamanta gsky da adalci a tsakaninsu, sai dai bai isa ya 6oye soyayyar ma'u ba, duk da itama Nana yana bata wani matsayi na ita ce jininsa, 'yar uwarsa da yake sun fahimci juna sai suka zauna lfya. Cikin shekarar ne duk Allah Ya albarkacesu da smun juna biyu, tsakaninsu wata guda ne kacal, Nana ce tafara haihuwar k'aton Namiji yaci sunan ABDULLAHI (Mujahid), Yaron da yaga soyaya da gata gurin dangin 'Yam Leman. Sai kuma Mau da ta kara haifo Mace. Itama ta sami gata, Ahmad dai shi ne mutumin da ya karya alk'adarin canfin danginsu na haihuwar d'a d'ya ko biyu, sai gashi da biyar cur! wannan ya sanya iyayensa jin dad'i. Adalci da Ahmad yayi a Gidansa da ya kwantarwa da Ma'u hankali shi ne hana Nana yin aiki ya ce shi ya dace ya nemo, duk da Nana ta damu da farko, rigima har gurin Babanta, amman da bata sami goyon baya gurin Iyayenta ba dole ta hak'ura, don Babanta yace ita kanta Mahaifiyarta digiri biyu gareta, kuma saboda k'warewarta a makaranta suka had'u suka yi aure, amman bata aiki saboda su Family d'insu suna da tsananin kishi, wanda tayi a baya ma Allah Ya amfana. Hakan ne ya sanyayar mata da guiwa, Ahmad ne yayi k'ok'arin k'ulla auren Mahaifinsa da Hajiya Amina don Mijinta shekaru biyu ke nan da rasuwarshi. Hakan ya yiwa kowa dadi Musamman kakarshi data damu yayi aure. Ita dai nana tun daga haihuwa 1 shiru babu k'ari da yake itama jinin iyalin ne suke ta6ata. GAME DA UMMI kam a yanzu ta yarda Ahmad yafi karfinta da ta gano matsayinshi dole ta samarwa kanta lafya, amman Iyayenta sun yi da sun sani da takaici, musaman da Mahaifin nata ya gano mahaifin Ahmad tsohon Ubangidansa ne, shi ke bashi kaya kafin kaninsa ya cigaba da bashi. wata rana kafin tayi aure ta hadu da Ahmad a Super Market ta gaya masa shi kadai take so amman ta hakura da shi zata auri wani ta bashi tausauyi kwarai da gaske, sai dai ya san bai isa ya karawa Ma'u kishiya ba, sai ya amshi lambar Accunt dinta ya tura mata kudi masu yawa wanda dasu ne tayi komai na auremta. WATA RANA sunje Gidansu da yamma ana ta hira sai suka jiyo kuka a harabar gidan, suka fito da sauri dasu Umma dasu Ma'un da Yaya Auwal da sauransu da yake duk ranar Lahadi da yamma annan ake hake had'uwa ayi ta hira. Lami suka gani dawata k'armasashiyar Mata kamar Fatalwa, Matar ta fadi Lami na kokarin tashinta tana kuka, ta lalla6a ta tasheta ta rungume a jikinta tana takawa da kyar! har ta isa kusa dasu ana tsaye cirko-cirko. Mal. Sulaiman ne yace, Lami wace ce kuma wannan? Cikin kuka Lami tace, "Yaya Raliya ce! Kusan Wata hud'u ke nan da aka kawota da cuta mai karya garkuwar jiki (H.I.V) dukkan abinda nake da shi ya k'are gurin Magani, kullun Mahaifinta idan zai zo gurinka sai nace ya gaya maka sai yace a'a shi ba zai fad'a maka ba, shi ne ni kuma da naga kamar zata mutu ne na kwasota tafiya bata iya yi don ku taimaka mata. Yaya Auwal yace, Raliya ce wannan Lami Subuhanallah!" Kowa ya tsorata da ganin yanda Raliya ta koma Yaya Auwal yace a kaita Asibitinshi zai yi mata komai kyauta, shi kuma Ahmad ya basu Kud'i mai yawa yace kuma duk k'arshen Wata ta dinga zuwa gurin Ma'u tana amsar Kud'i. Raliya da Lami suka fashe da kuka. Umma tace "Ato, duniya ke nan, tafi duk yanda ka d'auketa, sakayya ce take zuwar muku. Suka lalli juna da mamaki. TAMMAT BIHAMDILLAH!. Surayya 6 November 2015 at 12:10 · Public Save · More Like React Comment Share Like35 Write a comment... · Saihanatu Umar Umar Mun gode sosai Like · React · Reply · More · 6 Mar 2019 Adama Abdulkarim Kiyawa To alhmdllh mungode kwarai da gaske Allah ya kara daukaka da basira ubangiji yayi jagora Allah ya saka da alheri masha Allah Like · React · Reply · More · 2 Sep 2018 Sa'adeeyer Zarah Muna godia. Kuma muna jin dadin shi ... Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 Muhd Suhunun Muhd Tank Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 Maryam Abdul tnx Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 Rahama Adamu Allah ya taimaka Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 Bakura Sheriff Kayima allah yabadasa,a Like · React · Reply · More · 11 Nov 2015 Aisha Saleh Aliyu TNX Like · React · Reply · More · 6 Nov 2015 Zaynarb Abdullahi tnx Like · React · Reply · More · 11 Nov 2015 Amirah Muh'd Tnx sury allah yabar zumunci Like · React · Reply · More · 7 Nov 2015 View more comments… An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin

Chapter 14 of 15