Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
ya fara biyowa ta hancin shi yana xubowa a jikin shi. . . ALLAH SARKI AMIR, MALLAMIN SOYAYYA. JARUMIN JARUMAI A DA'IRAR SOYAYYA." . . Yana nan a saman bishiyar sai ya ga mutane suna xuwa cikin qauyen ana ta hayaniyar sha'ani da ake yi. Amir ya dago kan shi daqyar ya bude idanun shi ya hango mutane a cikin qauyen sun yi dandaxo ana daurin aure a qofar gidan su Sadiya. . Ya san cewar Sadiya ce ake daurawa aure da mutumin da aka bashi labari. Amir ya koma ya kwanta ya dafe qirjin shi da hannun shi a ynx xuciyar shi tafi komai damun shi da radadi. . . Lp=36 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 36 . . A ynx xuciyar shi tafi komai damun shi da radadi a jikin shi. Ya dade a haka kafin ya sake bude idanun nashi. A lkcn har mutane sun fara fitowa daga qauyen suna ta dararraku, wadansu a qasa wadansu kuma akan kekun da babura. Har an daura auren Sadiya da Alh. Mamuda Sarkin noma. . Bayan mutane sun watse sun bar qauyen, can da yamma tayi sai ya hango motoci uku sun shigo qauyen zasu dauki amarya tare da 'yan biki. Yana iya jiyo hayaniyar su daga nesa suna shewa da farin ciki, babu wanda ya san cewar yana saman bishiyar a bayan gatin. . Amir ya ji tsoro ya kamashi lkcn da ya ji ciwon shi ya sake yunqurowa fiye da na kowanne lkc a lkcn da yaga wasu mata sun fito da Sadiya, tana tsakiyarsu tana tafiya tana kuka tare da share hawaye, zasu shiga da ita cikin mota su kai ta dakin mijinta wanda bata so. . Amir yana kallo suka shiga da ita cikin motar dake gaba, mata sai guda suke yi da hanyaniya. Amir ya daga mata hannu duk da ita ba zata iya ganin shi ba, bata san yana nan a kusa da ita ba. . Shi kenan Sadiya sai wata rana, na gode da soyayyar da kika nuna min duk da bamu dade tare ba. . Shi kenan Sadiya, saduwar alheri, Allah Ya zaunar dake lfy ke da mijinki, da fatan za ki yafe min, nima na yafe maki. . Amir yana kallo aka tuqa motar aka tafi da Sadiya, sauran motocin 'yan rakiya suka debi sauran mata suka bi bayan motar da ta dauki Sadiya, ya ci gaba da dagawa motar hannu da qyar jini yana xuba ta hancin shi da bakin shi, kayan jikin shi duk sun yayyage yana a saman bishiyar a 6oye yana kuka. . Bayan sun tafi kowa ya 6ace sai Amir ya ji kamar an dauki xuciyar shi ne an tafi da ita, ya ji baya son ma zama a saman bishiyar. Domin kuwa ya tabbatar a ynx Sadiya tayi mashi nisa. Ya yi alqawarin koda ace mutuwa zai yi to dole ne sai ya kusanci inda take. Amir ya kamo reshen bishiyar ya sauko da qyar ya fadi qasa. Ya fara rarrafawa yana kama itatuwa da ganyaye a haka har ya yi nisa. Ya yi alqawarin sai ya je har qauyen da Sadiya tayi aure, shima zai raka ta kamar yadda sauran mutane suka raka ta. Ya san cewar idan har ya mutu a can Sadiya ta samu labari zata qara tabbatarwa da irin son da yake yi mata. Wannan ce kadai soyayya ta qarshe da zai nuna mata a halin ynx. . Ba zai mutu ba sai ya je garin da take, wannan shi ne hanya daya da zai bi ya wanke kan shi bisa laifin da yayi mata a baya. . . **~** . . Washe gari bayan an tashi biki da yake kwana daya aka yi, sai 'yan uwan Sadiya suka koma gida, aka bar ta a zaune tayi tagumi ta dora kanta bisa guiwarta tana ta kuka. . Sadiya ta ji tana matuqar jin tsoron gidan da aka kawo ta da kuma dakin da aka ajiye ta. Duk da qyale-qyalen kayan amarcin dake cike da dakin ba wani abu da yake bata sha'awa. Bata so danginta suka tafi suka barta ba. . "ki daina kuka, ki yi haquri, ki bi mijinki Sadiya, mu zamu tafi sai wata rana idan mun xo ganin ki." . Sadiya ta ji kamar 'yan uwanta sun kawo ta wani waje da za a kashe ta. Bata ta6a zaton rayuwarta zata fada tagayyara irin wannan ba. Har ynx masoyinta Amir wanda aka hana ta shi ne kadai wanda xuciyarta take hange. Sadiya tana matuqar tsoron wannan baqin azzalumin mutumin da aka bata a halin ynx, iyayenta da danginta suna can suna ta dariya, domin kuwa Sarkin noma ya basu kudi, sun barta a dakin tana ta rusa kuka, sun mance da ita. . Sarkin noma yana can tare da mutanen dake qauyen yana kaiwa da komowa da babbar riga yana dariya. Wannan rana ce mai kyakkyawan tarihi a cikin rayuwar shi. Ya san cewar Sadiya bata son shi, to amma shi ina ruwan shi da wata soyayya? Wannan sai yara 'yan zamani. Shi dai ya san ya saye iyayenta, don haka bai damu da irin zaman da zai yi da amaryar shi Sadiya ba. . Suna nan a cikin qauyen bayan rana ta dan fara dagawa, ba zato ba tsammani sai ga wasu yara dake kiwon shanu a bayan gari sun garzayo cikin qauyen aguje. Da aka tambaye su abin da ya tsorata su suka dawo sai daya daga cikin su ya ce. . "wani mutum ne rigar shi duk jini ya fadi a bakin hanya, yana can a kwance. . Nan da nan mutane suka fara garzayawa aguje domin su ga kowane ne. Sarkin noma shi ne a gaba, mutane suna bin shi a baya. Da xuwan su bakin hanyar shigowa qauyen, sai suka tsinkayi saurayin wanda yake ta aman jini a kwance yana kallon rana, kayan shi sun yayyage duk jikin shi rauni. Mutane suka yi baya a cikin tsoro da tausayawa. . Sarkin noma ya kalli saurayin ya dan yi tunani sannan ya ce da mutane. . "Wannan yaron shi ne yaron da ya je wajen mata ta kwanakin baya a can gidan su, yaron nan dake birni, shi ne ynx ya sake biyo ta nan." . Ya kalli samarin dake a wajen ya ce dasu. . "ku tattaka shi ya qarasa mutuwa, ba komai, ba abin da zai faru. . Sadiya tana cikin dakinta tana kuka, tana alhinin rabuwa da masoyinta daya wanda ba zata sake son wani namiji kamar shi ba, sai ta ji yara sun shigo gidan suna bada labari. . "Wani mutum ya fadi a bakin hanya, yana can a kwance rigar shi duk jini." . Sadiya ta ji gabanta ya fadi, tayi sauri ta dago kanta a tsorace. . . Lp=37>===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 37 . . Sadiya ta ji gaban ta ya fadi tayi sauri ta dago kanta a tsorace. Bata san ko wane ne ba, amma kuma babu shakka ta ji kamar ana fuxgar xuciyarta xuwa waje domin ta je taga abin da yake faruwa. . Tana nan a cikin dakinta na amarci sai ta ji wani saurayi ya shigo gidan yana bawa matan dake a gidan labari irin na yaran da shigo daxu. . "mutane sun taru da yawa a wajen, amma babu wanda ya san ko daga ina yake, ina tsammanin matafiyi ne rashin lfy ta kama shi ya fadi a hanya." . Sadiya ta fito waje a tsorace. Maganar da saurayin yake fadi tamkar yankan wuqa ne a jikin ta. Bata san kowane ne ba to amma kuma haka kawai sai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya, tana son ta je ta ga kowane ne wanda ake ta labarin ya fadi a hanya mutane sun zagaye shi. . Wata tsohuwa ta shigo gidan Sarkin noma a tsorace, ta ce da matan dake tsaye suna sauraren labarin da ake ta shigowa ana fadi masu. . "Jama'a gari babu lfy, kun ji abin da yake faruwa kuwa? Wai an ce wani saurayi yana ta aman jini akan hanya. Wasu sun gane shi, wai wani saurayi ne da ya je Turunkawa suka yi fada da matasan garin suka bubbuge shi kwanakin baya...." . Tun kafin tsohuwar ta kai qarshe Sadiya ta fashe da kuka, tayi waje da gudu, domin kuwa ynx ta gane ko wane ne. Amir din ta ne, Amir masoyinta!! Shi ne ciwon soyayya ya jawo shi ya biyo ta har garin da ta yi aure. . Matan Sarkin noma da sauran mutanen gida suka fara kuwwa suna cewa. . "mun shiga uku, jama'a amarya ta gudu, ku kira Alhaji ya xo gida babu lfy." . Nan da nan da nan aka sa matasa da yaran gidan suka bita suna kuwwa amma kuma Sadiya ta yi nisa, ta qosa ta sake ganin Amir ruhinta. . . Sarkin noma ya ci gaba da dakawa talakawan mutanen wajen tsawa. . "na ce ku kashe shi, babu abin da zai faru..... . . Page 38 . . Sarkin noma ya ci gaba da dakawa mutanen dake wajen tsawa. . "na ce ku kashe shi, babu abin da zai faru, domin kuwa rashin albarkar yaron nan tayi yawa, matar tawa zai biyo har nan garin sbd su yaran zamani basu gaji kunya ba?" . Mutanen dake wajen suka kasa ta6a Amir, domin kuwa jikin su ya yi sanyi, Amir yana kwance cikin jini ta baki ta hanci, duk jikin shi rauni ne, da qyar yake numfashi, saura kadan ya ce ga garin ku nan, ba zasu iya ta6a Amir ba, domin kuwa ta6a shi da xummar cutarwa rashin imani ne bayyanannne. . Suna nan a tsaye cirko-cirko tare da Sarkin noma wanda ya fusata yana ta huci, sai ga Sadiya ta fado wajen da suke, ta kutsa cikin mutane tana kuka ta ga Amir a kwance cikin jini. Tan ganin shi ta fadi a gaban shi tana kuka. . "Amir? Amir kai ne ka koma haka....?" . Ta tambaye shi a rude tana kuka da qarfi. Amir ya yi qarfin hali ya fara qoqarin bude bakin shi yana qoqarin ya kira sunan ta, yana kallon ta, a lkcn ne ya sake yin aman jini. Sadiya ta dora hannuwan ta akai tana kuka a tsorace. A halin ynx shi kan shi Sarkin noma ya yi saranda. . . NIMA A HALIN YNX DA NAKE TYPING HAWAYE KE SARTU BISA KUMATUNA. . . Amir ya fara shessheqar kuka, yana magana bakin shi yana kyarma, ya ce da Sadiya. . "ki yi haquri ki yafe min..." . Ya saurara ya huta, sannan ya sake yunqurawa ya ce . "na zalunceki a wani lkc da ya wuce, na guje ki a cikin rashi sani....ina neman afuwarki ki yafe min...." . Ya fara hawaye, ya dora hannuwan shi akan qirjinshi, domin ya samu sauqin azabar dake damun shi a ciki. Sadiya ta ce tana kuka. . "na yafe maka Amir duniya da lahira, nima ka yafe min..." . Amir ya yi ajiyar xuciya, wannan shi ne hadarin soyayya, domin kuwa a wani zamani da ya wuce shi ne wanda daruruwan 'yan mata ke son shi, shi kuma yana yi masu wulaqanci, yana sa su kuka, yana karya masu alqawari. Ga wani zamani kuma ya xo, Amir ya biyo yarinya daya 'yar qauye, ya rasa ransa akan ta bai same ta ba. . Amir ya daga hannayen shi biyu ya fara yiwa Sadiya bankwana. Yun yana iya motsa idanun shi a qarshe sai ya koma ya tsaya da motsi, Sadiya ta rusa kuka. Mutanen dake wajen suka fara xubar da hawaye, shi kan shi Sarkin noma mijin Sadiya sai da yayi tagumi. . "dama ashe haka ake yin wannan soyayya da yake jin labarin ta shekara da shekaru? Shi bai san yadda abin yake ba sai ynx.da a ce ya san haka zai ga wannan abin tausayi me zai sa ya matsa sai ya auri Sadiya? Da tuni ya barwa wannan saurayin ita. Sun yi auren su na soyayya." . To amma bakin alqalami ya riga ya bushe, Amir dai ya riga ya rasu a gaban masoyiyar shi kuma a gaban mijinta, a gaban mutane wadanda zasu zama shaida a matsayin shi na masoyin gsky. Mutanen dake a wajen suka yi sauri suka janye Sadiya suka kawar da ita, aka sa wasu mata da suka tsaya a baya suna kallo, aka ce su mayar da ita gida ta huta. . Suka qiqe Sadiya tana kuka tana waigawa baya tana yiwa GAWAR MASOYINTA KALLON QARSHE, suka mayar da ita dakin mijinta suna 6ata bakinsu wajen bata haquri. Sadiya ta ci gaba da tunanin Amir. . "Allah Sarki Amir masoyin zamani. Ta tuno ranar da ya fara ganin ta. . "Laifi ne don mutum ya tsaya yana kallon kyakkyawar mace irin ki?" . Ya yi mata dariya yana so ya nuna mata sabuwar soyayyar shi a gare ta. . Shi ne wanda ke ce mata. . "zan ci gaba da son ki Sadiya, kamar yadda nake son ki a halin ynx, har sai naga ranar da zaki tausayawa xuciyata ki amshe ni a matsayin masoyin ki." . Amir kenan gwanin iya kalaman soyayya, ya ce da ita. . "haba baiwar Allah, wai ke wacce iriyar mace ce? Ke fa ba makauniya ba ce, kina sane da irin ciwon sonki da ya kama xuciyata." . Sadiya ta tuno lkcn da abokan Amir suka xo suna bata haquri kan ta taimaki abokinsu ta amshi soyayyar shi, da kuma qawayen ta a makaranta irin su Rahma Sani da Siyama Ibrahim sai kuma Ziyada Yazid sune suka fi hawo hankalinta aka ta amshi soyayyar Amir. Kowa a birni yana son ta da Amir, gashi yau Amir ya rasu a gabanta yana mai neman afuwar ta yana kuka! . . Sarkin noma da kan shi ya shiga gaba aka nemo mutanen garuruwan Turunkawa da Gidan rijiya dangin Amir, aka fadi masu labarin abin da ya faru har Amir ya rasa ran shi. . Mai unguwa Mutawakkilu ya xo yana kuka, domin kuwa duk a dalilin shi labarin wannan so ya samo asali. Shi ya fara hada wannan soyayya, har abin ya zama matsala daga baya. . A garin Maqera inda Sarkin noma yake aka rufe Amir tare da mutanen da suka yi ta dukan shi a kwanaki uku da suka wuce, domin kuwa a halin ynx jikin kowa ya yi sanyi, kuma sun gane cewa laifin da Amir ya yi masu a baya bisa tsautsayi ne. Kuma nadama ce ta dawo dashi qauyen ba nufaqa ba. . Daga baya hr Zariya suka dunguma suka fadi yadda abin ya faru daga farko har qarshe. Da labarin ya samu abokan Amir a makaranta, sai da Mustafha da Haidar suka kwana biyu suna kuka, suna tuno abokinsu wanda ya rasu sanadin soyayya. . Da 'yanmatan dake a makarantar suka samu labarin rasuwr Amir, Amir dan soyayya, wasu sun yi kuka, musamman 'yanmatan shi...suna matuqar son shi. . . Lp=39 Iliyas Ishak Gundutse > "TASKAR GIDAN LITTAFI" >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 39 . . >=<><>=< KAMMALAWA >=<><>=< . .SANARWA! Bayan wannan littafin akwai littafin dake dauke da ci gaban labarin mai suna SADIYA wanda zamu ci gaba dashi gobe in Allah Ya kaimu. . . A halin ynx samari da 'yanmatan da suka samu labarin mutuwar Amir, sun girgiza kuma sun ga ishara. Sun gano cewar soyayya ba qarya ba ce, gaskiya ce akwai ta a raye a xuciyar kowanne mutum. Don haka in dai akan soyayya ne kowanne irin hadari zai iya faruwa ga masoyi. Tabbas ba zasu ta6a mancewa da labarin Amir ba, shi ne jarumi kuma malamin soyayya. . . **~** . . Da dare ya yi kowa ya yi barci, duk mutane sun kwanta suna hutawa, duk sun mance da al'amarin da ya faru a qauyen mai ban al'ajabi da kuma takaici. Dare ya yi babu kowa a waje sai hasken farin wata da ya ke ci kamar rana a tsakiyar sama da kuma motsin ganyaye da reshina a jikin bishiyu tare da kukan tsuntsaye. . Sadiya ta bude dakinta ta fito xuciyarta a bushe. Sadiya ta fito dauke da qunshin kayanta wadanda ta qulle su a cikin zanin ta. Lkc ne ya yi da ta dade tana jira. Lkc ne ya yi da zata gudu ta bar garin, ta gudu ta shiga duniya ta koma wani garin. Domin ta yiwa mutanen da suka raba ta da Amir nisa, domin ta yiwa baqin ciki dake damun ta nisa.....domin ta yiwa garin da aka kashe masoyinta nisa.....baqin gari wanda ba zata ta6a mantawa dashi ba. . A lkcn da wannan al'amarin ya farune ta shiga daki ta zauna a ciki tana ta kuka ita kadai. Tun lkcn da wannan al'amari ya faru ta fara 6oyewa mutane, bata son kowa ya xo kusa da ita, domin kuwa duk irin su daya. Sune suka kashe mata masoyin ta Amir. Tun a lkcn ta ji bata son komai face rabuwa dasu. Ta riqa jira dare ya yi domin ta fita ta bar gidan. . Sadiya ta fito ta bar gidan, babu wanda ya gan ta, ta riqa tafiya ita kadai a cikin hasken farin wata, ta bar gidan bata san inda zata nufa ba. Xuciyarta ta karye a dalilin alhinin soyayya, kuma tunanin ta ya dabirce. Tana sa ran idan ta tafi zata tsinci kanta a wani gari dake can gaba, ta na sa ran zata tsinci kanta a wurin da babu wanda ya san ta, ballantana ya dawo da ita, tana sa ran zata zauna a can har abada....har mutuwar ta. . Don haka ita ma ta tafi, ta rabu dasu kamar yadda suka raba ta da masoyinta. Don haka ita ma ta tafi ta bar su, kuma ba zasu sake ganinta ba, don haka ita ma ta tafi ta bar su!! . Sadiya ta tafi har ta yi nisa bata sake waigowa ba, Sadiya ta tafi tayi nisa a cikin daji, bata damu da ciyayi da bishiyun da take wucewa a hanya ba. Bata damu da duhun da ya kan lullu6e ko'ina a sararin samaniya ba. Bata damu da duwatsun dake bisa hanya ba, wadanda suke ta yi mata rauni idan tayi tuntu6e dasu ba. Sadiya ta tahi har ta yi nisa bata sake waigowa ba!! . Bata buqatar dan rakiya a lkcn da zata yi bankwana ta canza gari a sakamakon tashin hankalin soyayya. Bata buqatar wanda zai rakata sai inuwarta da ke biye da ita suna tafiya tare.... Sadiya ta yi nisa!! Bata buqatar wanda zai xo ya rakata sai hawayen dake biye da ita, idan wasu sun xubo sai wasu su sake biyo bayan su. Sai kuma takaici da damuwa dake a xuciyarta . A da can ba haka rayuwarta take ba. A da can tana rayuwarta ne cikin farin ciki....tare da 'yan uwanta....tare da iyayenta wadanda a ynx su suka kashe mata Amir, a da can ba haka rayuwarta take ba, domin kuwa babu abin da ya faru da ita cikin masifun soyayya. Sai da larurar soyayyar Amir ta kama ta sannan duk wadannan abubuwan suka shigo rayuwarta. Gashi ynx ta gudu ta bar kow, ta nufi wata duniya mai nisa a cikin dare ita kadai tana kuka....a da can ba haka rayuwarta take ba. . Ta tafi sai wata rana idan da rabon ganawa, idan wani ya ganta a wani gari cikin mutanen garin su, ko kuma a cikin 'yan uwanta....idan tana raye. Ta tafi sai kuma wata rana, idan da rabon ganawa, wataqila su gano inda take su rarrashe ta su bata haquri. Ta tafi sai wata rana idan da rabon ganawa. . Sadiya ta ci gaba da tafiya har tayi nisa, tun ana hangenta har ta fara 6acewa a cikin dajin....a cikin daren. Sadiya ta ci gaba da tafiya haka har ta hau saman wani tsauni dake a can nesa. Farin wata ya haske ta kamar tsuntsuwa, Sadiya ta ci gaba da tafiya har ta yi nisa tun ana iya hangenta har ta..... 6ace. . . Alhamdulillah. Dukanin godiya ta tabbata ga Allah (SAW) da Ya bani ikon Kammalawa wannan littafi mai suna SO BAYAN RAI (Labarin Hadarin Soyayya) . Jinjina ga maigidan littafi SHAFI'U DAUDA GIWA . Ina yaba maku Sadeeq Shehu Shariff Yusif Iliyasu Abdulkadir Yarima A Gangariya Shuraih Usman Muhamammed Anas Bn'malik Hassan Atk Tanko . Madallah da ku Alh. Aminu Duniya Gafai Hasheem Salees Adam Kayarda Abubakar Isah Dibboncy Usman SafUs Rano. . Ni Iliyas Ishak Gundutse (Madugun Taska) ke sadaukar da wannan labari ga ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI" gaba daya. Sai kuma mun hadu gobe idan Allah Ya kaimu a ci gaban labarin mai suna Sadiya An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8