Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SO BAYAN RAI (c) Shafi'u Dauda Giwa Mai gidan littafi . Daga http://fb.com/hausaebooks >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . . . Page 1 . . Kowacce shekara akan yi bikin shigowar sababbin dalibai a jami'ar Ahmadu Bello dake a birnin Zazzau, duk sa'ar da wannan lkcn yazo dalibai da dama daga jihohi daban- daban na cikin gida da kuma na wasu qasashen qetare. Su kan zo suyi dafifi a ko ina a cikin jami'ar wacce ta tserewa sa'o'inta ta fannin girma, tsarin gine-gine da kuma uwa uba bila'adadin guraben karatu, musamman fannin kimiyya da fasaha. . . Ba dalibai kadai ke murna da zuwan irin wannan lkc ba. Su kansu sauran mutane wadanda basa karatu a makarantar sukan zo suyi kallon yadda dalibai ke gudanar da sha'anin murna. Samari da 'yan mata daga garuruwa daban-daban, musamman irin wadanda ke da abokai ko qawaye a makarantar sukan zo taya su murna, su dauki hotuna tare da kuma yawo a cikin faffadar makarantar wacce ke kama da babban birnin wasu qananan jihohin. . . Sau da yawa samari "'yan ido mai na ci ban baka ba" a wajen irin wannan kallon suke yin sababbin 'yanmata. . ko a cikin daliban makarantar sau da yawa wasu a irin wannan ranar suke haduwa da baqin 'yanmata har kuma soyayya ta qullu. Wannan ba wani abin mamaki ba ne domin kuwa idan mutum ya yi la'akari da zuqa-zuqan 'yanmatan dake jami'ar wadanda suke daukar idanu kamar an 6aro su a leda da kuma wasu baqin 'yanmatan dake qure adaka, su halarci bikin yaye dalibai, an san cewar dole ne samari su garzayo kowa yazo ya za6i dai dai qarfin shi, domin kowacce qwarya da abokiyar zubinta. . . Kyakkyawan saurayi Amir na daya daga cikin daliban dake karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma shima yana daga cikin samarin da ke fafutikar samun sabuwar budurwa a duk wani taro ko shagali da za'ayi na musamman a makarantar. . . Amir farin Saurayi ne mai matsakaicin tsawo. Wanda a kowanne lokaci baya rabuwa da tabarau Kalar hadari wanda ke bayyana qwayoyin idanun shi dake tsaye tarwai suna kallon mutane ta cikin gilashi. . Amir yana kulawa da sumar shi fiye da komai na jikin shi, domin kuwa a cewar wasu abokanshi dake a makarantar wai duk kudin tallafin da gwamnati take baiwa dalibai (scholarship). Amir yana 6atar dasu ne kawai wajen gyara sumarshi. Ko daga nesa idan mutum ya hangi Amir, zai fahimci yadda sumar shi take qyalqyali a rana, kuma ta dan qadandane kadan. . . Amir yana kyau da qananun kaya fiye da dogaye. Fahimtar hakan ne ya sanya baya rabuwa da qananun riguna da wanduna (jeans) masu tsada dake kama jikinshi sosai tare da dunqulallen takalmi mai rufi dake kama da dutsen guga na zamani. . . Shekarun Amir ashirin da takwas da haihuwa. Kuma shekarun shi uku kenan yana karatu a jami'ar ta Ahmadu Bello dake a Zariya. Yana karatu ne a fannin adabin turanci. Amir yana da farin jini a wurin dalibai domin kuwa kusan kowa ya san shi. . Idan aka dawo 6angaren 'yan mata kuwa, anan sai dai ayi shiru, domin kuwa a tarihin makarantar ba a ta6a samun wani dalibi da 'yan mata suke son shi kamar su hadiye shi ba kwatankwacin Amir. 'yanmata bila'adadin sun same shi kai tsaye sun sanar dashi cewar suna son shi. Wasu kuwa ta hanyar abokanshi suke bi suyi kamun qafa, domin a shawo masu kan Amir ya amince ya ce yana son su. . Abin yana bawa abokan Amir mamaki qwarai da gaske, domin kuwa sun tsorata da wannan saurayi. Sun san cewar kyakkyawa ne wanda ya iya saka suttura, kuma tabbas ya iya magana. To amma duk wannan bai kai yadda za'ace 'yanmata fiye da dari suna rububi akan shi ba kamar wani tauraro, kowacce da zarar tazo maganar ta bata wuce. . "Ina son wannan abokin naku Amir, don Allah ku fada mashi" . To amma kuma inda Amir yake girgiza samari shine, duk matsayin mace kuma duk kyanta, duk tsadar motar da take shiga, in har tace tana son shi, to ba zai ta6a sauraron ta ba, ya fi son ya ga mace da kan shi ya furta mata cewar yana son ta. Kuma ya fi son mace ta riqa ja mashi aji tana nuna mashi kamar ba ta damu dashi ba. To amma kuma babu wata budurwa dake iya ja mashi aji. Duk wacce ya ce yana so da wahala ta tsaya wani ja mashi aji. Don kada tayi sakaci wani abu ya 6atawa Amir rai har yayi fushi ya rabu da ita ya je yaso wata budurwar. Idan har Amir ya nemi soyayya to yana sa rai da samun nasara, kuma ko da ace ma bai nema ba yana da tabbacin dole ne suzo wajenshi su ce suna son shi. . Amir baya tausayawa 'yan mata a rayuwar shi, domin kuwa da zarar ya fara soyayya da wata budurwa, ko wata daya ba zasu yi ba zai watsar da ita, ya canza wata sabuwar budurwa. Idan irin haka ta faru, 'yanmata da yawa sukan garzayo wajen abokan shi, wasu har kuka suke yi domin kuwa basu san laifin da suka yi wa Amir ba amma kuma ya guje su. . "Ni ban san laifin da nayi mashi ba haka kawai na ga ya qurace min. Kuma na roqe shi ya fada min ya qi ya sanar da ni komai. Ku tambaye shi idan laifi na yi mashi ya fada min in roqe shi ya yi haquri." . Irin wadannan qorafi a kowanne lkc basu rabuwa da abokan Amir, musamman wasu guda biyu da suka fi shaquwa dashi wato Mustafha da kuma Haidar. Wadannan samari 2n sun san halin Amir fiye da kowa, domin kuwa daki daya suke kwana . Page 2 . . . Wadannan samari biyu sun san halin Amir fiye da kowa, domin kuwa daki daya suke kwana a makarantar. . Da yake daga su har shi Amir din duk 'ya'yan talakawa ne, da irin wannan suke samun kudi a wurin 'yan mata. Idan Amir ya yaudari budurwa, bayan ta kamu da matsanancin son shi, idan tazo wajen abokanshi a rude doin su taimake ta, sai su yi mata qaryar Amir bashi a kusa. . "Dole ne sai mun sa kudi a waya mun neme shi, ko kuma suce "yana cikin gari ya fita cikin gari tun daxun, sai dai mu shiga taxi mu neme shi mu ji abin daya hada ku, zamu roqe shi yayi haquri ku sasanta, amma aiki ne mai wahala gaskiya." . . Idan su Mustafha da Haidar suka fadi haka, sai 'yanmatan su basu kudi masu yawa suce su sayi katin waya su nemo Asmir a duk inda yake. Wani lokacin Amir yana daki a kwance yana jin irin diramar da ake tsakanin abokanshi da 'yanmatan. Haidar shi yafi amsar irin wadannan 'yanmatan. . "Amir ya tafi Kaduna, kuma gaskya indai kin matsu to sai dai ki bishi can, domin wannan maganar ba maganar da zan tunkare shi a waya ba ce, sai munyi "(face to face)''. . 'Yan mata da yawa sukan bude jaka su dunqulo maqudan kudi su bawa Haidar da Mustafha. . "Ku je Kaduna ku dawo dashi, zan jira ku 'please' . Su kuma da zarar sun amsa sai su dawo cikin daki suna ihu, suna haurin iska riqe da kudin. Amir ya kan ce dasu yana daga kwance. . "Baku da kyau mutane na, ku basu wahala sosai, babu sassautawa". . Da irin wannan kudin suke rabawa su uku kowa ya sayi kati ya zubawa wayar shi. Idan kuma an sam budurwa mai dan sukuni, idan ta 6arar da kudi masu yawa don a sasanta ta da Amir, sukan je kasuwa su uku su shiga shagunan sayar da kayan sawa na manyan 'yan gayu su sayi takalma masu tsada da riguna, kuma a ciki suke shiga su ci abinci a manyan 'Restaurant'. . . Wasu 'yanmatan kuma Amir bai fara soyayya dasu ba, sune kawai ke haurin gidauniyar su, suke zuwa wajen su Haidar da Mustaha domin kamun qafa. Irin wadannan daruruwan 'yan matan sukan bawa samarin isassun kudi, domin su ji dadin karkato masu da hankalin Amir ya so su. . "Kada ki damu bebi, dole ne Amir ya so ki, ki bar wannan a hannun mu". . Koda sun fadiwa budurwa haka, ba zasu ta6a cewa Amir ya so ta ba, su ukun duk bakin su daya, kuma dukan su mayaudara ne, kuma duk lkcn da suka zanua, ko kuma idan dare ya yi suna daski, sukan dauki lkc mai tsawo suna dariyar wahalallun 'yan matan da suke yaudara. . . Duk a cikin 'yan matan dake son Amir babu wacce Haidar ya fi jin dadin hulda da ita, irin Shema'u domin kuwa yarinyar akwai dasla ga motaci na kece raini. Ta ta6a bawa Haidar chek din dubu dari. . Mtsew kuyi haquri, Na Katse Maku Karatu Ba tare Da Na Tsammaci Hakanba, Sai Don Wani Uzuri Da Xan Shiga. . .>===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 3 . . Duk a cikin 'yanmatan dake masifar son Amir babu wacce Haidar yafi jin dadin hulda da ita irin wata mai suna Shema'u, domin kuwa yarinyar akwai kudi ga motoci na kece raini. Ta ta6a ba Haidar cek din kudi dubu dari kyauta tace yasa kati a waya, don kawai ya shawo mata kan Amir yaso ta. Kuma a kowanne lkc hannunta baya gajiya da ciro rafofin dubu dai-dai a cikin jakarta. Inda Amir ya gagari samari shi ne, yana soyayya da 'yanmatan qasashen qetare dake karatu a jami'ar, musamman Indiyawa da larabawa, kuma abin dake qara masa nasara da kwarjini shine yana jin turanci da larabci sosai. Ya iya larabcine tun a karatun Islamiyya da yayyi mai xurfi a unguwarsu dake a cikin birnin Zariya, turanci kuwa ba a magana, domin yana a shekararsa ta uku ne a jami'ar kuma adabin turanci yake karanta. . Bayan haka Amir saurayi ne dake son waqe-waqe, kuma ya iya dadadan waqoqi na turanci da kuma larabci. Sannan yana rera waqa da Hausa cikin taushin murya. Wannan baiwarce ta sa idan yana tare da budurwa bata so su rabu. 'yanmatan dake son shi idan suka samu sa'a yazo wajensu sun sha su roqe shi. . "Amir ina son ka rera mani waqa mai dadi yau." . Idan Amir yana waqe masoyiyarshi sai tayi shiru tana kallonshi ko qiftawa bata yi. Wata kuma sbd kalaman soyayyar da yake fadi sai tayi ta hawayen soyayya. Ko kuma tayi tagumi tana sauraren daddadar muryarshi. Shi yasa da zarar ya daina kula 'yanmata duk sai su rude su fara biyo shi. A lkcn ne kuma zasu fara 6arar da kudi a wajen abokanshi, domin a dawo masu da Amir dan soyayya. . A ranar da irin wannan bikin yaye daliban yaxo ne, Amir yasa qananun kayanshi da yake ji dasu, sannan ya qara gyara sumar shi ta fito sosai, tare da dan tabaron shi da yake sakawa kadan akan dogon hancin shi. Ya shiga cikin dubban daliban dake kaiwa da komowa domin kuwa ya dade bai yi sabuwar budurwa ba, rabonshi daya 6are wata budurwa a leda tun kwana sha uku da suka wuce da yaga wata budurwa balarabiya 'yar qasar Pakistan ya ce yana son ta. . Kwanansu shida kacal ya daina saurarenta, kuma ko ta kira shi a waya baya amsawa. Sau uku tana xuwa wajen abokanshi nemanshi, xuwa na farko suka tsara ta suks ce bashi a kusa sai dai a nemo mata shi idan tana so. Sai a xuwa na biyu ne ta samo kudi ta bawa su Mustafa, a xuwa na uku suka ce ta sake dawowa ba a same shi ba. Kuma ita ma tana nan bata haqura ba tana nan da son dan saurayi mai farin jini Amir. . Amir ya riqa yawo a cikin dalibai yana waige-waige, 'yanmata suna ta kallonshi suna yabawa. Amma kuma babu wacce ya gani da ta kwanta mashi a rai. . Sai bayan wani dan lkc da yaxo wucewa daidai inda wasu 'yanmatan turawa suke daukar hotuna tare da wasu qawayensu hausawa da suka shaqu a makarantar, Amir ya hango wata a cikinsu wacce shi a wahenshi tama fi turawan kyau, domin kuwa fatarta irin kalar da ba a san takamaiman yadda za a kira ta bace, duk jikinta daga sama har qasa kalar hoda-hoda ce, kuma da ganinta haka take a halicce, idanunta kuwa masu tsawirya ne irin wadanda masana sirrin kyawawan mata suka ce, wai sai a tara mata dubu ba a samu mata hudu dake da irin kalar idon ba. Daga nesa idanun budurwar kamar ruwan toka- toka suke, amma idan mutum ya matso kusa sai yaga idanun kamar sun cika maqil da hawaye, suna yawo a cikin laima. . Amir ya tsaya a wajensu yana murmushi, ya gaishesu kai tsaye kamar yadda wayayyun samari ke tunkarar budurwa kai tsaye ko wacece babu shakka ko tsoro ya ce da budurwar cikin harshen turanci. . Ku biyo Iliyas dauke da page 4 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 4 . . Sannan ya nuna wacce ya gani yana so da yatsa ya ce da ita cikin turanci. . "Wurinki naxo 'yanmata." . Budurwar tayi dariya. Tana sanye da dofuwar riga baqa marar hannu wacce ta bude da kuma baza a qasa kamar dawisu. Ta taso ta biyo Amir, sauran 'yanmatan turawan suna yi mata wasa. Amir ya jata suka tsaya a jikin wasu shuke-shuke a bakin hanya. . "suna na Amir." . Ya ce da ita yana kallon xubinta da dirinta. . "Ni kuma suna na Ni'ima." . Sai a lkcn da yaji sunanta sannan ya fahimci bahaushiya ce daga irin lafazin harshenta, idan tayi turanci akwai jirwayen hausa a ciki. Don haka tana jin hausa. Amir yayi mata hausa kai tsaye ya ce da ita. . "gaskiya Allah Ya hore maki kyau baiwar Allah, mutane naea suke fadi maki haka a kowacce ranar duniya?" . Ni'ima tayi murmushin farin ciki, sannan ta ce dashi. . "ko a yau samari fiye da goma sun fadi min haka har ma na gaji da saurare." . Suka yi dariya a lkc guda. . "haka ne Ni'ima." . Amir ya ce da ita. . "amma kuma masoya suna yawan fadiwa duniya cewa kyau bashi da muhimmanci in har ba aci moriyarshi ta fuskar soyayya ba. Ma'ana in har mace kyakkyawa ce to yana da kyau ta amshi soyayyar wanda ya fada a tarkon sonta, ta haka ne zata fahimci ko ita wace ce a duniyar 'yanmata." . Ni'ima ta ce dashi. . "nima ina girmama soyayya a rayuwata, kuma ina da sauqin kai wajen amsar soyayyar wanda ke neman soyayyata. To amma kuma na cika tsoro da kuma fargaba, ina matuqar tsoron soyayya, in har aka ambaci wannan kalmar na kan ji gabana ya fadi." . "sbd me Ni'ima?" . Ta dan yi tunani kadan kafin ta ce. . "sbd na dade ina ganin qawayena suna fadawa cikin tarkon soyayya, kuma suna matuqar shan wahala kafin su fita. Ina tsoron fadawa cikin irin wannan tarkon Amir. Shi yasa mafi yawa nafi son in zauna cikin mata 'yan uwana, ina jin tsoron in zauna da wani saurayi." . Amir ya yi mata murmushi kafin ya ce. . "lallai kin bar dadin duniya Ni'ima, ni kuma kin ga a duniya babu wani abu da ya kai zama da masoyi dadi, soyayya ni'ima ce daga Ubangiji Ya yiwa 'yan Adam kyauta, ko baki da komai zaki iya zama da wanda yake sonki, kema ki yi farin ciki irin na kowa, zaku kasance a cikin annushuwa da begen juna. Soyayya zata iya wanke duk wani baqin ciki dake a cikin xuciyarki komin dadewarshi a tare dake. Kuma soyayya zata iya canza maki halaye ki qara wayo da hikima da qwaqwalwa. Idan kika riqe soyayya da kyau a xuciyarki, to zaki mance da wasu wahalhalun rayuwa dake damun sauran mutane a wannan duniyar. Me yasa zaki bar irin wannan babbar gara6asar mai dadi Ni'imah?" . Budurwar taji Amir ya burgeta sosai, akwai alamun gaskiya a maganganunshi, daga baya sai tayi ajiyar xuciya sannan ta ce. . "gsky naji dadin ganinka Amir, domin kuwa babu wani mutum daya ta6a fada min wannan sirrin dake tattare da soyayya. Me yasa to sauran mutane basu san haka ba? Me yasa kowa ba zai xo ya riqe soyayya ba?" . Amir ya ce. . "Sbd ba kowa ya san sirrin soyayyar ba Ni'ima. Akwai wani abu guda daya da har ynx masoya basu gane ba. Sau da yawa soyayyar da jini yas hada tafi soyayyar da idanu suka hada nesa ba kusa ba, idan jinin masoyi ya hadu dana abin son shi ko basu ta6a ganin juna ba, to da zarar sun yi arba kuma zasu fahimci sun dace da juna, kuma kai tsaye zasu fara soyayya ba zasu so abin da zai nisantasu da junansu ba. Amma soyayyar da fuskoki suka hada ita ce wacce kawai saurayi zai ga budurwa ko kuma budurwa taga saurayi su ji wani abu dake tattare dasu ya burge junansu, daga baya kuma sai su yanke shawarar fara soyayya, to anan ne daya daga cikin su zai fara qoqarin sanar da dayan domin neman amincewar shi. . Soyayyar jini ta zarce soyayyar da idanu suka hada qarfi da inganci, domin kuwa bata warwarewa har abada, idan jini ya hadu a tsakanin masoya to basu da buqatar tsayawa kokwanto ko wasi-wasi, ko a wanne yanayi suka samu kawunansu a yanayin zasu dora soyayyarsu, kuma ba zasu ta6a bain juna ba komai wuya komai dadi." . Ni'ima taji a cikin dan qanqanin lkc wannan saurayi ya canza mata tunani, basu fi minti goma da haduwa ba, amma kuma gashi har ya qareta da wani ilimi, domin kuwa da ace bai sanar da ita irin wannan sirrin na soyayya ba da ynx ta bashi haquri sun rabu domin ya tafi ita kuma ta koma cikin qawayenta. Amma kuma ynx bata son komawa cikinsu, tafi son ta ci gaba da tsayawa da Amir yana bata labarin soyayya. . Amir yana yiwa mata wannan salon ne a duk lkcn da ya fahimci budurwa bata da ra'ayin soyayya a ranta, kuma bata da ra'ayin zama da masoyi. Don haka tun a tsayuwar farko zai fara canzawa budurwa tunani, don ta fara ta kanshi. . Ni'ima ta.... . .Ni'ima ta tambaye shi. . "to amma kuma Amir tunda haka ne me yasa zaka ga wasu masoyan suna samun sa6ani a tsakaninsu? Ni a ganina in har abin da ka fadi a game da soyayya gsky ne, ma'ana in har jini ke hada soyayyar mutane biyu su zama daya, to me zai sa kuma wani abu yazo daga baya ya shiga tsakaninsu? . Amir ya ce da ita. . "mafi yawa daga cikin masoyanmu na wannan zamanin soyayyarsu bata gamon jini bace. Wasu suna yin soyayya ne don su samu kudi ko kuma don kyau. Sau da yawa zaki samu budurwa mai aji wacce maza ke jinjina mata, amma da zarar wani saurayi ya fito da kudi da motoci ko wane ne shi, kuma ko daga ina yake sai ki ga ya amshe soyayyarta daga hannun sauran samarinta, sbd yana yi mata hidima babba, kuma a haka zasu tafi har ya aureta. Sai bayan sun yi aure idan wani zamani yaxo, idan kudin sun qare sannan zata fara fahimtar ashe dama tun farko ba sonshi take yi ba, kin ga daga nan sai maganar rabuwa, tunda babu soyayya a tsakaninsu." . Haka abin yake wajen saurayin da yake son mace kawai don wani abu da yake sa ran zai samu. A qarshe zaki ga ko idan ya samu abin su zauna lfy da matar, ko kuma in ya rasa su rabu." . Sannan kuma wannan ya kan shafi wadansu da suke yin soyayya don kyau. Domin kuwa shi kyau wani abu ne da Ubangiji Ya yiwa 'yan adam, kuma yana tafiya ne tare da rayuwar halittar da aka yiwa. Kuma halittar mutum bata qarewa har sai ranar da ya koma ga Mahaliccinsa, don haka yau da kullum mutum ya kan canza a dalilin wasu matsaloli na rayuwa ko canjin yanayi. Wanda sau da yawa kyau ya kan gushe ko kuma ya ragu. A nan ma idan har masoya don kyau suke son junansu to dole ne soyayyar ta samu miskila wanda kuma rabuwa ce zata biyo baya." . Ni'ima ta ji ta kamu sosai da son Amir, domin kuwa bata ta6a ganin saurayi irin wannan ba a rayuwarta, shi ne saurayin da yake da wani irin salon soyayya wanda duk lkcn da ya kasance da wata budurwa sai ya sanar da ita wani abu mai muhimmanci wanda bata sani ba game da soyayya a rayuwarta kuma ya kamata ace tuntuni ta san shi, wannan shi yasa 'yanmata suke rububinshi, domin suna son ya nuna masu hanyoyin soyayya da kuma sabuwar hanyar rayuwar matasa. . Amir ya yiwa Ni'ima bankwana ya bar ta a cikin murna tana tambayarshi. . "sai yaushe kuma zamu sake haduwa Amir?" . Tana so ace kodayaushe su ci gaba da zama tare a haka matsayin masoyinta. Gashi Amir ya tafi. Mai yiyuwa ya dore ya ci gaba da xuwa yana nuna mata irin wannan soyayyar. Tana addu'ar Allah Yasa Amir ne zai ci gaba da zama a matsayin masoyinta. . Bata sani ba a lkcn da take wannan addu'ar akwai 'yan mata fiye da dari dake irin wannan addu'ar a wurare daban-daban, har ma da wasu qasashen. A cikin irin wadannan 'yanmatan akwai Rahma, Shema'u, Walida, Aysha, Salma, Ikhram, Rukayya. Ko wacce ya sha yi mata alqwarin zai aure ta, kuma ita kadai zata zauna tare dashi har abada babu kishiya. . Cikin irin wadannan 'yanmatan wasu tuni har sun fadiwa iyayensu da 'yan uwansu tare da qawaye. Cewar sun samu mijin da zasu aura. Kuma suna yawan fitowa da hotunanshi suna nunawa danginsu domin kowa ya san shi, kuma a san a ina yake. . "Sunan shi Amir." "......yana mutuwar so na kamar ya hadiye ni." ".....Allah Ya barku tare da shi." "......Allah Ya nuna mana ranar aurenku mu gani." "......Allah Ya amshi addu'arku, na gode. . 'Yanmata bila adadin kenan, kuma a garuruwa daban- daban ke wannan addu'ar. . . SHEMA'U ta fi kowacce budurwa takaicin yadda Amir ya guje ta haka kawai ba ta san abin da tayi mashi ba, gashi kuma abokan Amir Mustafa da kuma Haidar sun qi su shawo mata kan wannan saurayin wanda soyayyarshi ke ta faman azabtar da ita. . Babu abin da ya fi komai tayarwa da Shema'u hankali irin ganin Amir da take yi yana yawo tare da wata sabuwar masoyiyar shi, kuma daliban makarantar da suka san irin son da take yi mashi, suma suna yawan xuwa su bata labari. . "Amir ya yi sabuwar budurwa." . Shema'u bata son ta riqa nuna abin ya dame ta idan tana cikin mutane, to amma kuma idan ta koma daki ta kwanta sau da yawa ta kan yi kuka ita kadai babu wanda ya sani, kuma tana yawan tambayar kanta. . "me yasa Amir ya guje ni?" . Shema'u ta kan tuno lkcn da tauraruwar soyayyarsu take tsananin haske ita da Amir, a lkcn da suke yawan xuwa dandalin daukar joto a harabar korayen ciyayi dake a jikin katangar jami'ar, a lkcn da suke tsayawa a cikin farin ciki a daukesu hoto tare, dalibai suna kallonsu daga nesa. Bayan sun gama daukar hotunan kuma sai su taho suna takawa sannu a hankali suna hirar soyayya har su komo cikin makaranta. . Sau da yawa Shema'u ta kan zauna a daki tayi tagumi ta dauko hotunan da suka yi ita da Amir masoyinta, tana kallon hotunan a lkc guda kuma tana hawaye tana tunanin ranar da za ace wannan surayi ya zama mijinta. . Sbd tsananin amincewa da soyayyar da Amir yake yi mata yasa bata 6oye masa duk wani sirri da ya shafi rayuwar ta, kome ya faru da ita har qosawa take yi... . >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 6 . . Saboda tsananin amincewa da soyayyar da Amir yake yi mata yasa Shema'u bata iya 6oyewa mashi duk wani sirri daya shafi rayuwarta. Kome ya faru da ita har qosawa take yi ta sanar da Amir domin ta ji ra'ayinshi. . A ranar da mahaifin ta ya xo makarantar ya kawo mata ziyara da kuma tsaraba cike da bayan motar shi, sai Shema'u ta cire kunya ta bashi labarin Amir, amatsayin saurayin dake taimaka mata a makarantar. Mahaifinta ya nuna mata jin dadin shi sosai da kuma goyon bayan kasancewarta tare da Amir in har ta amince da halayen shi. . Shema'u ta ji farin ciki ya lullu6eta, amma kuma abin takaicin shi ne, tun

Chapter 1 of 8