Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
ta fito a daidai lkcn da Amir ya qaraso wajen su, a lkcn ne kuma motar ta hau titi ta qara gaba aguje ta basu waje. Amir ya dube su a lkc daya ya yi murmushi. . "'Yan mata adon gari." . Ya ci gaba da sanar da Sadiya. . "tun daga (North gate) nake biye daku a lkcn da kuka hau mota, ynxn nan dan aca6a ya sauke ni." . Rahma tayi tsammanin wani abokin karatun su ne, wanda ya san su ita bata san shi ba, sai ta ce da shi. . "Lah! Kaga mu bamu sani ba." . Sadiya ta kalli Amir, ta gane shi tun a kallon farko da yayi mata a lkcn da ya qaraso. Ta hade fuskarta cikin damuwa sannan tayi tsaki. Ta ce da Rahma. . "Don Allah ki xo mu tafi, ina da abin yi a gida." . Amir ya ce da Sadiya. . "Haba baiwar Allah, wai ke wacce iriyar mace ce? Ke fa ba makauniya ba ce, kina sane da irin ciwon son ki da ya kama xuciya ta. Na dade ina neman ki a makaranta, na ci wahala amma ban san inda zan ganki ba. Ynx cikin sa'a kuma Allah Ya sake hada mu na biyo ki har nan, amma har ynx dai kina nan akan bakan ki, ba zaki amshe ni amatsayin masoyi ba?" . Da Rahma ta ji abin da Amir ya fadi sai ta gano cewar shi ne saurayin da Sadiya take bata labari a kwanakin baya wanda ta ce sun hadu a labirari. Sadiya ta ce da Amir. . "Idan baka mance ba ai tun a wancan lkcn na fadi maka cewar bana yin soyayya. Kada ka 6atawa kan ka lkc a kaina kayi haquri ka je ka samu wata budurwar, amma ni a gsky ba zaka samu kar6uwa a waje na ba." . Ta dubi qawarta Rahma. . "Rahma zo mu tafi, na fadi maki sauri nake yi in koma gida." . Rahma ta dubi Sadiya cikin damuwa ta ce da ita. . "Gsky Sadiya bai kamata ki yi haka ba, bai cancanta a ce kin yi mashi haka ba. Duk wanda ya nuna maki irin wannan soyayya tsawon lkc, kuma ya ci gaba da bin ki har xuwa ynx gsky ban yi tsammanin zai yaudare ki ba ko ya cuci rayuwar ki. Wannan masoyinki ne, ya kamata ki amince." . Amir ya yi shiru yana bin ta da kallo tsawon lkc, yana jiran amsar da zata sake bashi. Sadiya ta sake 6ata fuska cike da gajiya da lamarin su. . "Wannan wane irin abu ne? Na ce bana so, to wai soyayyar dole ce? Ni soyayyar ce kawai bana ra'ayi a halin ynx. Na jingine soyayya kwata-kwata a rayuwata. To ku qyale ni mana." . Ta yi tsaki ta ce da Rahma a fusace. . "Idan ba za ki tafi ba ni kin ga tafiya ta." . Ta tafi a fusace ta bar Rahma tare da Amir wanda idanuwanshi suka fara kawo qwalla a cikin tsananin takaicin yadda Sadiya take wulaqanta shi a kowanne lkc haka. Rahma tayi ajiyar xuciya cikin tausayawa ta ce da Amir. . "Ka yi haquri zan taimake ka kuma in Allah Ya yarda, zata canza ra'ayinta, kada ka damu. Kada ka damu, bari in rubuta maka 'Department' din mu da kuma 'Block' din da za ka same mu a makaranta. Ka xo gobe mu tarar mata, zaka yi nasara." . Amir ya yi mata murmushin gdy cikin qarfin hali. . "Ni suna na Amir." . Ta ce da shi. . "ni kuma suna na Rahma, ita kuma dama ka san sunan ta Sadiya." . Amir ya ce. . "Sai ynx da na ji kin fada, ban san sunan ta ba lkcn da na fara ganin ta 'last week' a labirari." . Rahma ta rubuta masa inda zai same su a makaranta idan sun je yin lakca. Amir ya amsa ya yi mata gdy. Suka yi bankwana Rahma ta ruga da gudu cikin azama domin ta cim ma Sadiya wacce ta yi nisa tana tafiya cikin dushi. Daga nesa Amir yana iya jiyo muryar Rahma tana cewa da ita. . "gsky Sadiya ban ji dadin abin da kika yi ma shi ba, wannan wulaqancin gsky na ji kunya." . Amir bai ji abin da Sadiya ta fadiwa Rahma ba, ya dai ji tana magana cikin dushi daga nesa. A lkcn ne ya ji hawayen dake idanun shi sun fara fitowa waje. Yayi sauri ya share ya juya ya tare mai babur ya hau suka koma makaranta. . Da komawar shi ya samu Mustafa da Haidar tare sun dawo daga lakca suna tattaunawa akan wannan matsalar soyayya da ta same shi. Tun kafin su tambaye shi daga inda ya fito, ya miqa masu guntuwar takardar da Rahma ta bashi ya ce dasu cikin annashuwa. . "Na gano inda take, ynxn nan daga wajenta nake, sunanta Sadiya ga takardar da qawarta ta bani nan, ku je ku same ta Mustafa, ku taimake ni wata qila ku ku shawo kanta, ni dai nayi iya qoqarina amma ni Sadiya ta qi amincewa da soyayyata. Rayuwata tana cikin hadari..." . Amir ya dafe qirji ya shiga daki da qyar. Haidar ya ce dashi cikin qwarin guiwa. . "Kada ka damu Malamin soyayya, ka yi haquri tunda ka gano mana ita. . Ka kwanta ka huta, ka bar mu da ita dole ne ma ta so ka." . Amir ya dade a kwance yana xubar da hawayen radadin soyayyar Sadiya. . Sadiya ita ma da xuwanta gida sai ta fara xubar da hawayen takaicin abin da wani saurayi mai suna Amir ya ta6a yi mata, wancan Amir din na farko wanda bata ta6a ganin shi ba a duniya. . A lkc guda kuma a can garin su Sarkin noma yana can da qaton rawani a zaune yana tunanin ranar da za ace Sadiya ta zama matar shi a 'yan kwanaki kadan masu xuwa. . Ga lkc nan ya taho, ba a san me kuma zai faru ba. . . Lp=21 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 21 . . Ga lkc nan ya taho, ba a san me kuma zai faru ba. . . **~** . . Washe gari da xuwan Sadiya makaranta sun zauna a bakin ajin su ita da qawayenta su Rahma. Sai ga tawagar abokan Amir su biyar sun shigo sun shigo harabar inda 'yanmatan suke kowannen su cike da qwarin guiwa da kuma alwashin kasancewar su manyan samari da kowacce daliba ta san da zaman su. . Kafin xuwan su, a zaman da Sadiya tayi da qawayen ta, suna yi mata nasiha ne akan wulaqancin da ta yiwa Amir kamar yadda Rahma taxo ta basu labari. Wata daliba mai suna Siyama ta ce da Sadiya. . "Ki daina saurin wulaqanta saurayi Sadiya, akwai matsala babba idan reshe ya juye da mujiya, wata rana zai iya daukar fansar abin da kika yi mashi. Mu mata mu suke yiwa wulaqanci mu haqura mu shanye, amma su akwai su da zafi kin gane...? Kawai ki so shi (lo6e him) ku zauna lfy." . Daliban suka yi dariya, Sadiya ta yi murmushi bata ce komai ba. Wata daliba mai suna Ziyada ta ce da ita. . "na ta6a yin irin wannan Sadiya. Wani gaye ya so ni amma nayi ta kwafsa shi. Kullum sai ya xo gidanmu amma kwata-kwata bana sauraren shi, kawai sai ya koma yana son qawata, sai a lkcn ni kuma naji ina son shi domin yana masifar kulawa da ita. Da ya fahimci na dawo ina son shi ina masifar kishin ganin shi da ita.....waw na gane kuskure na. In fadi maki ya rama....fiye da abin da nayi mashi, sai da nayi kuka da idanu na. Don haka ki kula ba haka ake yin soyayya ba Sadiya. Ynx an daina yayin wulaqanta samari, kowa ya waye, ki so shi a tafi a haka." . Sadiya ta yi dariya ta ce da qawayen ta. . "ba wai son shi ne bana yi ba, ina son shi, to amma nayi alqawarin ba zan sake yin soyayya ba a rayuwata. Babu wani namiji da zan sake amincewa ya wulaqanta ni kamar yadda ya faru da ni a baya.". . Rahma ta ce da ita cikin fushi. . "Dole ne ki so wannan Amir din, in dai kina son ki zauna lfy damu a makarantar nan Sadiya. Kin ga wannan ai wani abin al'ajabi ne, wani Amir wanda bai ta6a ganin ki ba ya wulaqanta ki, ynx kuma kin samu wani Amir ya co zai share maki hawaye." . Siyama ta ce. . Haka ne Sadiya, wannan kamar sakayya ce Allah Ya yi maki da wani masoyin wanda zai riqe ki amana ba kamar wancan ba." . A daidai wannan lkcn ne abokan Amir suka qaraso dandalin da 'yanmatan suke zaune. Da xuwan su Mustafa ya fara yi masu sannu da hutawa, sannan ya tambaye su ko wace ce Sadiya. Sadiya ta dube shi cikin mamakin abin da ke tafe dasu har su biyar. Tace da shi ita ce. . "......Afuwan. Yau ina cikin wasu uxururruka. Kuyi haquri da wannan......" . . Lp=22 . A dai dai wannan lkcn ne abokan Amir suka qaraso dandalin da 'yanmatan suke zaune. Da xuwan su Mustafa ya yi masu sannu da hutawa sannan ya tambaye su ko wacece Sadiya a cikin su. Sadiya ta dube shi cikin mamakin abin dake taafe dasu har su biyar. Ta ce dashi ita ce. . "me yake faruwa?" . "Haba Sadiya!" . Mustafa ya ce da ita. . "Yaya ki ke so da rayuwar Amir abokinmu? Ciwon son ki ya kama shi, ynx haka yana can a kwance baya iya cin abinci, baya iya magana duk sbd tsananin begenki. Ya kamata ki ji tausayin shi ki amshi soyayyar shi don ya samu sukuni a xuciyar shi." . Rahma ta yi farat ta ce dasu. . "Na ji dadin xuwanku, dama ynx kun same mu ne mun tarar mata muna yi mata fada akan wulaqancin da take yiwa Amir." . Haidar ya ce da ita. . "bai kamata a ce kina kallon mutum a cikin azabar son ki amma kin juya masa baya ba. Idan ya mutu kamar ke kika kashe shi Sadiya. Ynx haka Amir bai san ko a wane hali yake ciki ba, rayuwar shi tana cikin hadari, komai zai iya faruwa." . Wani a cikin abokan Amir mai suna Fataye ya qara da cewa cikin lallashi. . "bamu yi mamakin yadda Amir ya rikirkice akan son ki ba, domin kuwa sanin kowa ne cewar irin ki ne matan dake tafiyar da hankalin ma'aboci bege, idan Amir ya rasa ki zai dade bai samu kwatankwacin ki ba." . Faruq saurayi na hudu kuma qwararre a wajen kalami ya dora da nashi bayanin. . "kamar yadda kika tsaya auna sigar irin son da Amir yake yi maki, wannan kin yi daidai, mun san cewa ba wulaqanta shi kika yi ba, sbd ba ki yi kama da masu wulaqanta mutane ba, kowa ya ganki ya san cewar kin san mutunci, kin fito daga gidan mutunvi. Kin tsaya gwada shi ne kawai domin ki fahimci ko da gaske yake son ki. To muna masu tabbatar maki da cewa Amir yana son ki har cikin xuciyar shi. Da kin ga halin da yake ciki da kin tausaya mashi." . Alphat wanda shine qarshe bai yi magana ba, ya ce da Sadiya. . "Ina tabbatar maki da cewa idan kika ba Amir goyon baya, zai yi maki gangariyar soyayya, kuma zai dora ki akan dausayin soyayya wanda babu wata mace da ta ta6a kusantar irin wannan dausayin dake a cikin xuciyar shi." . Sadiya tayi murmushi cikin kunya, qawayen ta suka rufar mata kamar zasu cinyeta da surutu. . Rahma tace. . "ki bamu amsa muna saurarenki Sadiya, kina son shi ko kuwa har ynx kina nan akan bakan ki?" . Ziyada . Page 23 . . "ki bamu amsa muna saurarenki Sadiya, kina son shi ko kuwa har ynx kina nan akan bakan ki?" . Ziyada ta ce. . "ba wani sauran shawara da zaki sake yi, ki fadi kawai tunda ga kowa yana sauraren ki." . Sadiya ta ce dasu cikin farin ciki. . "shi kenan, ya isa haka nan, na ji na amince ina son shi nima." . Abokan Amir suka yi kuwwa tare da sauran dalibai dake wajen, qawayenta suka tafa hannuwan su. Mustafa ya ce. . "Ynx tunda an yi haka, kamata yayi ki xo mu je ki fadi mashi da kanki, ya ganki da idanun shi don xuciyar shi ta samu sukuni." . Rahma ta ce da abokan Amir. . "Gsky kuwa, haka za a yi, zamu raka ta qafarta qafarmu, mu kaita wajen masoyin ta." . Suka tashi tare da Sadiya wacce ke murmushin kunya suka dunguma tare da abokan Amir suka nufi 6angaren da dakin su yake a sashin maza. . Abokai da qawaye suka yi qoqari wajen ganin sun hada masoyi da masoyiyar shi, sbd haka gangariyar soyayya ta fara kankama sosai a xuciyar wadannan masoya. Sadiya tana tafe tare da qawayenta cikin sauri zata je gano masoyin ta wanda bashi da lfy domin ta gaishe shi. . Da xuwansu daki suka iske Amir a kwance yayi shiru yana tunani. Sadiya dake gaba sun rako ta, ta durqusa a gaban sa cikin nadama ta ce dashi. . "gani na xo Amir ka yi haquri, na samun labarin halin da kake ciki a wajen abokanka da suka same ni ynx, na amince da soyayyarka Amir, ina son ka nima, ka yi haquri." . Amir bai yarda da abin da yake faruwa ba sai da ya dago kai yaga abokan shi da kuma qawayen Sadiya a baya suna murmushi suna kallon abin da yake faruwa. Ya yi tsammanin mafarki yake yi, kamar yadda ya saba yin mafarkin Sadiya, suna tare suna kallon juna. . Amir ya dube ta sosai ya kira sunan ta. . "Sadya, da gaske je ce kika xo waje na?" . Ta ce dashi. . "Ni ce Amir. Na san cewar nayi maka abin da bai cancanta ba, kada kaga laifina, akwai abubuwa ne da dama da suka faru da ni a rayuwa wadanda suka sa na dauki alqawarin na haqura da soyayya har abada. To amma ynx na fahimci kana sona tsakaninka da Allah, ba don ka cuce ni ba, kamar yadda wani ya ta6a yi mani." . Amir ya yi ajiyar xuciya ya ce da ita. . "Sadiya ban san da me zan kwatanta farin cikin wannan rana ba a xuciyata. Na godewa Allah da Yasa kika gane irin son da nake yi maki da kuma irin radadin da nake ji dare da rana yana azabtar da tunani na dalilin rashin goyon bayan da kika nuna min. Na dauki alqawarin daga ke ba zan sake son wata mace a duniya ba. Zan riqe ki amana kuma ba zan ta6a juya maki baya ba Sadiya." . Ta ce dashi cikin farin ciki. . "naji dadi da ka yi mani wannan alqawarin Amir, domin kuwa a rayuwata a halin ynx tana buqatar tsayayyen masoyi wanda zai kawar mani da kewa da kuma damuwar dake a raina. Nima na dauki alqawarin komai wuya komai dadi zan kasance tare da kai har abada, har qarshen rayuwa ta Amir." . Amir yayi murmushi cikin jin dadi. . "Na gode Sadiya, na gode da kika ceto rayuwa ta da kuma hankalina da ya kusa barin jikina. Na gode da kika dawo min da barcina wanda tuni ya qaurace min, ya bar idanuna. Na gode da kika dawo min da farin cikina wanda ya dade da guduwa ya bar xuciya ta. Ina fatan zaki fadiwa iyayenki da kuma 'yan uwanki labarina, nima zan yi gaggawar sanarwa nawa 'yan uwan domin kowa ya sani a riqe alqawari har xuwa lkcn da zamu ga ranar aurenmu." . Sadiya tayi dariya. . "ka daina jin tsoro Amir, babu wani da zai qwace ni daga gare ka. Kuma na san zaka samu kar6uwa a wajen iyayena da 'yan uwana. Amma ka daure gobe ka xo gidanmu domin ka gaisa da wata Inna ta wacce nake zaune a wajen ta a nan garin." . Amir ya ce. . "In Allah Ya yarda gobe zamu xo, kuma tun a goben zamu fara tattauna maganar auren mu. Na qosa in mallake ki Sadiya, xuciyata ba zata ta6a samun natsuwa ba sai ranar da kika zama mata ta." . Ta ce dashi . "nima haka Amir, nafi son muyi aure cikin qanqanin lkc, sai in ci gaba da karatuna a gidan ka." . Suka yi dariya a lkc daya. . "na gode Sadiya. . "nima na gode Amir, Allah Ya barmu tare. . Su Rahma qawayen Sadiya da kuma abokan Amir dake a tsaye a baya, suka yi tafi a cikin farin ciki, ganin yadda masoyan biyu suka fada cikin kogin soyayya a cikin qanqanin lkc. . Sbd haka sun zama shaidu akan wannan babban alqawari da masoyan suka qulla game da wannan gangariyar soyayya. . . Lp=24 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 24 . . Sbd haka sun zama shaidu kan wannan babban alqawari da masoyan suka qulla kan wannan gangariyar soyayya. . A qarsha Sadiya ta yiwa Amir sallama suka koma ita da qawayen ta, suka bar shi tare da abokan shi suna jinjina mashi da kuma taya shi murna Sadiya ta amshi soyayyar shi. . Har aka tashi daga makaranta da yamma, lkcn da Sadiya ta koma gida ita da qawarta Rahma xuciyarta cike take da farin ciki mara misaltuwa. . Sadiya ta ji komai yana bata sha'awa a rayuwar ta sbd sabuwar soyayya mai dadi da ta shiga xuciyarta. Dan qanqanin abu sai ya sanyata dariya da farin ciki, bata son su daina zancen Amir ita da qawayen ta. Tafi son suyi ta tambayarta labarin shi tana basu labarin irin son da take yi masa, da kuma fatan alherin da take yi wa soyayyar su har xuwa 'ya'ya da jikoki. . Sadiya tana matuqar son Amir, domin kuwa a kwanakin baya wani Amir ya wulaqanta ta ya ce baya son ta tun kafin ya gan ta su yi magana. Ynx ta samu wani sabon Amir din wanda bai hada komai da wancan Amir din ba. wannan dan makaranta ne bai ta6a wulaqanta kowa ba. yana da mutunci, yana da haquri, yana da tausayi, kai! Wannan Amir din shi yafi cancanta ya zama mijinta fiye da wancan Amir din na farko wanda ya zalunceta ya nuna mata qiyayya a idon duniya. . Labarin da Sadiya ta riqa baiwa qawarta Rahma kenan a lkcn da suka taso daga makaranta suka kama hanyar komawa gida, suna tafiya suna hirar Amir. Sadiya ta ji ta qosa ayi auren su. Ta cire babin aure a ranta kwanakin baya, karatu take so, sai ynx haduwarsu da Amir ta ji ya dawo mata da batun aure xuciyarta. Babu shakka wannan Amir din shi ne zai zama mijinta, su zauna tare cikin dauwamammiyar dangantakar soyayya ta har abada. . Da suka inda zasu rabu sai Sadiya ta shiga lungun gidan su, ta yi wa Rahma gdy, ta ce sai sun hadu washe gari da safe. Sadiya ta shiga gidansu fuskarta cike da farin ciki tana tunanin Amir, tana tunanin dadadan kalaman shi da kuma tattausar muryar shi mai kwantar da hankali. . Shigarta gidan ke da wuya ta ci karo da Haj. Uwani a zaure za ta fita, ta sa lullu6i. Da ganin Sadiya ta ce da ita. . "Dama ke zan ba, tun daxun ana ta jiran ki. Me kika tsaya yi haka? Babanki ne ya xo ya ci jira har ya gaji." . Sadiya ta ji gaban ta ya fadi. Ta shiga cikin gida ta iske Mal. Buba zaune akan tabarma, an ajiye mashi ruwa a kofi. . Tun kafin ta rage tsawo ta gaishe shi, Haj Uwani ta ce da ita. . "Sauri zaki yi ki shirya, tafiya gida zaku yi. Ya xo ne ya tafi da ke, karatu ya qare. Maganar auren ki ce ta sake tasowa. Ki yi sauri ki hada kayan ki kada kuyi dare ga hanya babu kyau ynx." . Sadiya ta ji kamar an dora mata duniya akan ta. Nan da nan farin cikin da ta shigo dashi ya rikide ya koma duhu mai tsanani. . A ranar da take murna ta yi sabon saurayi wanda take sa ran shi ne zata aura, a ranar ne kuma za a dauke ta a raba ta dashi, ita da Amir an raba su har abada! . An raba soyayya mai dadi!! . . **~** . . Washe gari tunda sassafe Amir ya fara murna yana yana xumudin sake ganin Sadiya sabuwar masoyiyar shi. Ynx Amir ya samu sauqi, farin cikin shi da annashuwar shi sun sake dawowa. . Ya dade yana xuba idanu domin ya ganta, amma abin mamaki daga ita har qawarta Rahma babu wacce taxo makaranta a rananr. Abin ya daurewa Amir kai kuma ya bashi tsoro domin kuwa a yadda suke cikin jin dadin kasancewa tare shi da Sadiya, ya san da wahala ta tsallake rana bata xo makarnta ba, ko don ta ganshi suyi hira ta xo, to amma har kusan yamma babu Sadiya babu qawarta. . Nan da nan Amir ya sanar da abokanshi biyu suka shiga mota suka garzaya unguwar su Sadiya domin ya gan ta ko ya samu sauqi a cikin xuciyar shi. . Su Amir basu sha wahala ba wajen gano gidan su Sadiya, gidan da innarta take aure a Zariya kusa da jami'a. . Da suka fito daga cikin motar su ukun, sai suka aiki wani yaro suka ce ya shiga ya ce ana son ganin Sadiya a waje. Ba a dade ba yaron ya fito ya ce dasu. . "wai an ce su wanene ke son ganin ta? . Amir ya ce. . "ka ce da ita Amir ne yake kiran ta." . YAUMA MUNA TARE KADA KUYI NISA . Yaron ya koma. Xuwa can ya fito tare da Haj. Uwani wacce tayi lulli6i da gyale. Ta dafa qofar gidan ta kalli samarin uku dake son ganin Sadiya, suna tsaye a bakin motar su, da suka ga matar ta biyo yaron, basu tsaya tambayar yaron ba sai suka qarisa wajen da take a bakin zauren suka yi mata sallama sannan suka gaishe ta. . "mama mu ne muke son ganin Sadiya." . "ai kuwa Sadiya bata nan." . "bata nan Mama, ina ta tafi. . Amir ya buqata cikin damuwa. Haj. Uwani ta ce. . "ta yi tafiya tun jiya, ta koma gida." . Amir ya dubi abokanshi cikin furgici. Ganin sun kasa fahimtar yadda abin yake sai Haj. Uwani ta ce dasu. . "dama karatu ne ya kawo ta nan Zariya, ni qanwar mahaifinta ce. Jiya babanta ya xo ya dauketa suka koma gida, tun jiya suka tafi..." . Amir ya katse ta. . "To Mam sai yaushe zata dawo? Ba zata wuce wannan satin ba ko? . Haj. Uwani ta rasa gane ko wadannan samarin su wane ne . "Ku su wane ne da kuke son ganin ta?" . Amir ya ce da ita... . Lp=25 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 25 . . Haj. Uwani ta rasa gane kowadannan samarin su wane ne. . "ku su wane ne da kuke son ganin ta?" . Amir ya ce da ita. . "Mu abokan karatun ta ne, mun ga ba ta xo makaranta bane yau shi yasa muka xo don muga ko lfy." . Haj. Uwani ta ce. . "Gsky ina fargabar sanar daku cewar da wahala Sadiya ta sake dawowa." . "Sbd me ba zata sake dawowa ba?" . Amir da abokanshi biyu Mustafa da Haidar suka tambayeta cikin rudani. Ta ce dasu kai tsaye. . "Sbd aure za a yi mata. Maganar ce ta taso shi ya sa aka xo aka tafi da ita cikin gaggawa." . "Aure!!" . Amir ya ji maganar ta soke shi kamar tsinin kibiya a cikin xuciyar shi. Ya dafe qirjinshi cikin xogi ya lumshe idanin shi. Wannan wane irin abin tsoro da xullumi ne ya fadowa soyayyar su a rana daya babu zato ba tsammani? Sadiyar shi wacce ke a cikin xuciyar shi tana murmushi yana ganin ta dare da rana tana debe mashi kewa, ita ce aka dauketa za a yi mata aure? Ynx shi kenan an raba shi da ita? . Ganin yadda Amir ya rikice sai Haj. Uwani ta tambaye su abin da yake faruwa a tsakanin Amir da Sadiya. Mustafa ya ce da ita. . "Bai kamata mu 6oye maki ba Mama. Wannan abokin namu shi ne masoyin ta, kuma gsky suna son juna shi da Sadiya, bamu ta6a tsammanin wannan al'amari zai taso ba a daidai wannan lkc." . Haj. Uwani ta ce dasu. . "Wato gsky in ban da wani abu da ya faru a can gida qauye tun farko da baku san Sadiya ba. Tun kafin ta fara karatu a nan Jami'a aka yi mata aure. To irin auren nan ne na can qauye da suke yi auren sadaka. Shi ne aka ba wani yaro auren ta wani baqo, mu bamu san ma ko daga ina yake ba, an dai ce daga 6angaren abokin mahaifinta yake. An daura auren amma sbd rashin mutunci yaron nan ya ce baya son ta ko ganin ta bai ta6a yi ba, ya aiko mana da zage-zage ya ce baya son ta shi ba zai auri 'yar qauye ba. Shi ne sai muka yanke shawarar da a bar ta a can gida mutane suna kallon ta bayan wannan wulaqancin da yaron nan ya yi mata, sai muka gwammace mu dawo da ita nan ta ci gaba da karatunta. Wannan ne dalilin shigarta jami'a har kuka san ta. Ynx da aka xo aka dauke ta wani mijin ne ya fito yake son ta, maganar karatu kuma ta qare, Sadiya zata tafi dakin mijinta." . Amir ya kalli abokan shi a tsorace, domin kuwa wannan magana da Haj. Uwani ke fadi ta so tayi kama da irin abin da ya faru dashi lkcn da yaje qauyensu ya kai zaiyara a watannin baya. Ya tambayi Haj. Uwani cikin firgici. . Ta ce dashi. . "Ba za ku san qauyen ba. Wani qauye ne da ake kira Turunkawa, can kusa da Gidan rijiya....." . Tun kafin ta kai qarshe Amir ya dafe kan shi a tsorace. Ya fara kuka cikin xullumi da furgici. . "...Gidan rijiya....qauyen Turunkawa!! . To ai can ne garin kakan shi, can ne ya je aka bashi aure. Dama ita ce Sadiya wacce bai ta6a ganinta ba? Dama ita ce wannan kyakkyawar budurwar wacce bai ta6a ganin ta ba? . Haj. Uwani da abokan Amir suka tambayi Amir me yake faruwa ne? Ya ce dasu. . "NI NE AMIR WANDA AKA TA'BA BA AUREN SADIYA NACE BANA SON TA! Nine wanda ki ke magana Mama. Mai unguwar Gidan rijiya shi ne kakana, shi ne ya je ya nemo min auren Sadiya lkcn ban ta6a ganin ta ba, shi yasa nace bana son ta. Ban san cewa ita ce Sadiya da muka hadu a makaranta ynx ba. Ni ne Amir! NI NE MIJIN SADIYA!! Ya kamata in yi sauri in koma in fadi masu su dawo mani da matata!!! SADIYA MATA TA CE! YNX INA SON TA!" . Amir ya dubirce yana sambatu. Haidar ya dubi Mustafa suka dafe kai a tsorace, domin kuwa ba zasu manta da lkc da Amir ya basu labari ba suka yi ta dariya ya auri 'yar qauye. Ashe ita ce Sadiya wacce suke lallashin ta a ynx a makaranta domin ta so Amir. Jikin su yayi sanyi domin kuwa sun ga ishara mai yawa, wacce basu ta6a ganin irin ta ba. Gashi ynx Amir ya ganta yana bin ta yana kuka da hawayen shi yana roqonta ta so shi bai sani ba. . Haj. Uwani ta dafe qirji a tsorace. . "Amir? Dama kai ne Amir din da muka ba Sadiya ka ce baka son ta 'yar qauye ce?" . Tayi salati tana tafa hannunta. Ta dubi samarin ta ce dasu. . "Bari in fadi maku, Wallahi mu ji tsoron duniyar nan, domin kuwan abin da ya faru ishara ce gare ku don ku yi hankali. Amir ka wulaqantamu, ka ci mana mutunci bamu yi maka laifin komai

Chapter 5 of 8