Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
ba, sbd kawai mun nufe ka da alheri. Aure abin alheri ne, koda ace baka son Sadiya, bai kamata a ce kayi mata wannan wulaqancin ba, kamata ya yi ka same muyi maslaha, mu warware matsalar cikin sirri. Amma sai ka wulaqantamu Amir, ka aiko mana da zage-zage, ko Sadiyar ma baka gani ba. Ka kamo hanya ka dawo birni. To wannan Sadiyar ce tsohuwar matar ka, ita ce wannan Sadiya kuma da kake mutuwar so a halin ynx, kuma an yi mata miji ynx aure za a yi mata." . Amir ya ci gaba da kukan nadama. . "ynx daga nan ba zan koma makaranta ba, zan koma qauye in samu kakannina su je su roqi su Baba domin su dawo min da mata ta, in har ban auri Sadiya ba rayuwata tana cikin hadari." . "Ynx da wane ido zaka sake komawa wajen kakan ka? Da wane ido zaka je gidanmu wajen mahaifin ta? Da wane ido zaka kalli Sadiya ka ce mata kai ne din farko da ka guje ta? . . Lp=26>===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 26 . . Da wane ido zaka kalli Sadiya ka fadi mata cewar kai ne Amir din farko da ya gije ta, baka son ka ga irin ta? Kada ka koma qauye neman Sadiya domin kuwa zaka dorawa kanka aiki ne babba wanda ba zaka ta6a samun nasara ba. Na tabbatar idan ka je ynx, musamman a irin wannan lkc da ake maganar auren ta, sai sun ci mutuncin ka, kuma sai sun rama abin da ka yi masu." . Amir ya ce da ita. . "na dauki alqawarin zan koma in nemi afuwa a wajen su koda kuwa zan rasa raina ne a wajen neman ta. Haqiqa nayi kuskure a rayuwata, domin kuwa na kasance mutum mai karya alqawari kuma bana mutunta mutane. Daga ynx na dauki alqawarin ba zan sake yaudarar wani mutum ba ko mace ko namiji. Wannan abu daya faru da ni na san cewar alhakin mutane ne da yawa, musamman 'yanmatan dana zalunce su nayi masu alqawarin zan aure su daga baya na gudu na bar su, kuma na tabbatar basu yafe mani ba. Na yi nadama.....kaico da irin wannan rayuwa tawa...." . Amir ya sake fashewa da kuka. Haj. Uwani ta ji hawaye ya xubo mata, tayi sauri ta koma cikin gida tana al'ajabin wannan abu da ya faru tsakanin Amir da Sadiya. . Mustafa da Haidar wadanda ke tsaye jikin su babu qwari suka kama Amir suka shiga dashi cikin mota suna bashi haquri. Ya ce dasu. . "na tabbatar rayuwata ta fada cikin hadari abokaina, kuma zai yi wahala in fito daga cikin wannan bala'i dana fada. Alama ce dake nuna yadda zan fuskanci wahala da uquba wajen nemo soyayyar Sadiya. Ina son wannan abu da ya faru da ni ya zamo darasi a wajen ku. Domin kuwa tare da ku nake yin wadannan halaye marasa kyau, tare daku muke yaudarar 'yanmata, kun ga abin da ya faru da ni, sbd haka ku kiyaye, ku tuba tun kafin irin wannan ta same ku." . Haidar ya ce. . "Har abada na daina qarya, wallahi ba zan sake yaudarar wata yarinya ba." . Mustafa ya share hawaye ya ce. . "Ni kwata-kwata ma na daina soyayya a rayuwata, indai haka soyayya take zamowa a qarshe, to ba zan sake yarda so ya kama ni ba. Wannan ai bala'i ne. . . LKCN DA NA XO NAN WURIN A TYPING HAWAYE KE SARTU BISA KUMATUNA. BAN SANI BA ZAN DAINA DAGA YNX KO KUMA HAR QARSHEN LABARIN HAKA ZAN KASANCE? BAN SANI BA. "ALLAH SARKI AMIR." . Mayaudaran samarin uku sun yi nadamar munanan ayyukan da suka yi a baya na yaudarar 'yanmata, sbd sun ga ishara da idanun su. Yarinyar da Amir ya gudu ya barta tana kuka cikin 'yan uwanta, a gaban iyayen ta ynx kuma sun hadu yana bin ta yana kuka cikin azabar son ta. Mustafa ya yi gsky da ya ce wannan soyayya ta zama bala'i ga rayuwar Amir. . Da komawarsu Amir ya hada kayansa a gurguje ya yi bankwana da abokanshi suna kuka, suka yafewa juna. Ya hau mota ya nufi qauyen Gidan rijiya inda ya ce ba zai sake komawa ba. . KU CI GABA DA RIQE WANNAN SADAUKARWAR SOYAYYA TA AMIR A CIKIN XUQATANKU, NAN GABA AKWAI WASA QWAQWALWA. . . Ga Amir dai ya tafi nemo soyayya, ga kuma matsaloli can suna jiran shi da wahalhalun rayuwa maras iyaka. . . . **~** . . Da yamma liqis Amir ya isa Gidan rijiya, garin kakan shi Mai unguwa Mutawakkilu. Amir ya ji kunya da nadama sun cunkushe a xuciyar shi, a lkcn da yake tafiya a qasa xuwa cikin qauyen bayan ya sauka a mota a bakin titi, yana sagale da 'yar jakar shi yana wasi-wasin abin da zai biyo baya. Da kuma tunanin sake ganin rabin ran shi Sadiya. . Amir ya shiga cikin quyen ya iske mutane a zazzaune suna shaqatawa, dandalin matasa daban, na tsofaffi daban a gefe. Amir yayi masu sallama. Wasu suka amsa wadanda basu san shi ba, wadanda kuma suka gane shi, musamman xuriyar gidan kakan shi mai unguwa bin shi kawai suka yi da kallo suna mamakin abin da ya sake dawo dashi wannan qauyen, bayan cin mutuncin da ya yiwa mahaifin su Mai unguwa. . Amir ya wuce xuwa gida. Wasu matasa jikokin Mai unguwa suka bi bayan shi a fusace cike da alwasin in har sake dawowa yayi don ya yiwa tsohon rashin kunya, to sai dai a kwashe shi, amma sai sun karairaya shi. . Dama a wancan lkcn sa'a ya ci basu a gida suna gona, da suka dawo ne suka samu labarin rashin kunyar da ya yiwa kakan su. Sun ciji yatsa, domin kuwa da suna nan da sun nunawa Amir su tsagerun qauye ne idan shi tsageran birni ne. . Amir ya shiga gidan yayi sallama. Da shigar shi ya samu mata a waje suna aikace-aikace, wata matar mai unguwa tana tankade garin tuwo, wata kuma ta dauko buhun ciyawa zata zazzagewa awaki wadanda ke ta miqa wuya cikin qosawa. . Da suka dago kai suka ga Amir, sai kowacce ta tsaya da aikin da take yi suka qura mashi idanu cikin mamakin sake ganin shi, matan biyu suka yi mashi magana. Wacce ke tankade ta ce. . "Yau a gari in ji maqi baqo?" . Daya kuma ta ce. . "Yau 'yan birni ne suka tuna da mu?" . Amir ya gaishe su cikin ladabi har yana duqawa qasa suka amsa, a wannan karon babu wasannin jika da kakan da suka saba yi da Amir idan ya xo, ko idan suka je birni. Basu san me ya sake dawo dashi ba ynx, sun dauka har abada ba zai sake xuwa qauye ba, kamar yadda ya fadi masu a ranar da aka 6ata mashi rai a wancan karon. . Amir ya qarisa qofar dakin kakan shi mai unguwa. . . Lp=27 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 27 . . Amir ya qarisa qofar dakin kakan shi mai unguwa Mutawakkilu, ya same shi a zaune yana jiqa busasshiyar rama ramar d'aura danni a cikin qwarya. Amir yayi mashi sallama cikin ladabi. Mai unguwa ya amsa bayan ya dago kai yaga Amir. Ya tsaya da jiqa ramar cikin mamaki da kuma fushi a lkc daya, ya qurawa Amir idanu. Amir ya tsuguna a gefe guda ya gaishe shi, tsohon ya amsa. Akwai alamar ya matsu ya ji abin da ke tafe da wannan jika nashi a wannan karon. . "Har ynx baka huce bane, shi ya sa ka sake dawowa ynx kuma ka buge ni Amir?" . Amir ya ce da tsohon. . "Wannan magana ta wuce Mai unguwa, tsautsayi ne kuma ina roqon ku yafe mani, na san cewar nayi kuskure." . Mai unguwa ya ce. . "Ai kai zamu ba haquri, sbd a zahiri kai muka wa laifi tunda mun zalunceka mun hada ka aure da wata 'yar qauye wacce bata dace da irin rayuwar ka ta 'yan birni ba.". . Amir ya ce. . "Ba haka bane mai unguwa, shi wannan abu duka ya faru ne a bisa kuskure da kuma tsautsayi. Daga baya na fahimci ni ke da laifi, domin ku iyayena ne, kuna da ikon ku za6ar mani abin duk da ku ka san yana da kyau a gare ni, ko da kuwa bani so." . Kafin Mai unguwa ya sake cewa wani abu ne, samarin gidan suka yo qungiya suka xo wajen a fusace. Wani jikan Mai unguwa ya ce da Amir. . "kai mara mutunci, uban me ya sake dawo da kai gidan nan? Ko ka sake dawowa ka kuma yiwa iyayen namu rashin mutunci, kamar yadda ka saba?" . Wani faskeken qato qanin mahaifin Amir ya matso gaba a fusace daga shi sai yagaggiyar singileti shudiya wacce ta sha qurar gona, ya fara qoqarin kai mashi duka ya ce. . "Dan iska kawai mara mutunci, lkcn da ka zagi su baba ka ci sa'a bani nan na je yammaci, wallahi da sai an kwashe ka, shegu wadanda basu san darajar mutum ba, ka ce tak ynx idan ka cika mara kunya, ynx nan a je a bizne ka." . Mai unguwa ya dakawa samarin tsawa ya ce dasu. . "kai ku qyale shi, komai ya wuce, ku tafi abin ku ku rabu da shi." . Samarin suka tafi suna hararar Amir, wani a cikin su wanda ya dauko iccen garman shanu ya jefar dashi a tsakar gida. Amir yana tsugunne yana kallon su a gaban Mai unguwa Mutawakkilu. Tsohon ya ce dashi. . "Yaya damuna a can birni, ana samun ruwa kuwa?" . Amir ya yi saurin cewa da shi. . "Eh, ana samu jefi-jefi, don ko jiya ma an yi ruwa da safe." . Mai unguwa ya ce dashi. . "Ai wannan al'amari na bana sai addu'a. Abin da farko ya so ya bamu tsoro, sai da aka yi kusan wata daya babu ruwa a nan. Ni dai a iya wayau na abin da zan iya tunawa ba a ta6a daukar lkc ana roqon ruwa irin na wannan shekarar ba. Wasu gonakin sai dai a haqura dasu, duk fari ya sa amfanin ya qone ya bushe wasu kuma sai dai a dan kalaci abin da yayi saura. Kai bana mun ga jarabta a duniyar nan." . Amir ya ce da shi cikin girmamawa. . "Abin haka yake a ko'ina, an samu qarancin ruwa bana." . Mai unguwa ya ce. . "To masifu ne gasu nan ta ko'ina sun cika duniya. Ya kamata mutane su gane cewar wannan fa ishara ce a gare mu a bisa 6arnar da muke yi kullum babu qaqqautawa. Mutane idon su ya ya rufe wajen neman abin duniya, zalunci da rashin da rashin mutunci ya zama ruwan dare a wannan zamani. Yara sun 6aci da rashin tarbiyya da futsara, manya kuma basu son maqwabtan su sai zaman gaba da mugunta da yiwa juna hassada, babu wanda yake son wani ya ci gaba, kowa kan shi ya sani shi kadai sbd rashin adalci. . Ga xubar da jinin mutane da ake yi kullum, wasu 'yanmatan sun koma karuwai a gaban iyayen su ana kallon su. Fasiqanci da badala ya karade ko'ina. Ba amana a tsakanin mutane da abokan huldar su. 'ya'ya sun raina iyayen su, sun zama abokan fadan su....ga abubuwa nan marasa mara sa kyau barkatai Amir. To ka fadi min yadda za ayi mu zauna lfy a haka ba tare da mun gyara dabi'u da halayen mu ba." . Amir ya yi shiru yana sauraren tsohon. Yace . "Gsky ne mai unguwa, akwai matsaloli masu yawa da ke tattare da mutane...." . Bai san me ya kamata ya ce da shi ba, domin kuwa xuciyar shi akwai tunanin da take yi. 'Tunanin Sadiya' . Tsohon ya ci gaba da cewa. . "bayam matsalar ruwa da muka fada a ciki, ga kuma matsalolin rashin albarkar dukiya. Ga abin nan dai kullum ana nema kuma ana samu, amma babu albarka, 'yar matsala kadan sai kaga ta xo tayi awon gaba da abin da mutum ya yi shekara yana tarawa. Da ka samu kudi zaka rasa inda suka nufa kamar kudin iska, duk wadannan fa masifun ne, Amir, mutane basu ganewa. Sannan kuma babbar matsalar da tafi damun mu ta wadannan shugabannin namu marasa adalci. Da un haye kujerun mulkinsu, kan su kawai suka sani da 'ya'yansu, idan matsalarsu ta taso a rana daya zasu ware miliyoyin kudi su magance ta, amma idan matsalar talakawa ce sai su shekara suna zama taro da shawarwari ba zasu ta6a mayar da hankali akan ta ba. . Shugaba daya sai ya tara abin da mutum milyan dari zasu amfana dashi ya 6oye. Kullum muka wayi gari sai mun ce gara jiya, a haka ake tafiya, baya tana fin gaba sauqi, gaba tana fin baya tsanani da uquba. Me ya jawo mana wadannan bala'o'i? Sbd mun kasance mutane masu 6arna da laifi. . . Lp=28 >===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 28 . . Sbd mun kasance mutane masu 6arna da laifi, mu ne zamu gyara kanmu mu dawo mutane na gari. Idan muka gyara halayenmu, da yardar Allah zamu samu sauqin wadannan fitinu da masifu dake qara addabarmu a kullum." . Amir ya ce. . "Gsky ne mai unguwa. . Ya ci gaba da lalla6a tsohon suna hira, har xuwa wani lkc sannan ya ce da shi. . "Mai unguwa na xo ne dama in sanar da kai cewa ina son Sadiya ynx, in son a ba iyayen ta haquri akan abin da nayi bisa kuskure, na amince ina son ta." . Mai unguwa ya kalle shi cikin mamaki da al'ajabi. . "kana son ta kuma ynx? Ban gane wannan magana da kake fadi min ba." . Amir ya ce dashi bayan ya duqar da kai. . "Sadiya 'yar wajen abokinka da aka bani auren ta a watannin baya na ce bana so, ita nake nufi." . Mai unguwa ya ce. . "Kai da ba ka ta6a ganin ta ba, ta yaya kum ka ji kana son ta ynx?" . Amir ya yi ajiyar xuciya ya ce da tsohon. . "Gsky ba zan 6oye maka ba Mai unguwa, naga Sadiya, mun hadu a makarantar mu inda nake karatu a halin ynx." . Ya kwashe labarin abubuwan da suka faru tsakanin sa da Sadiya ya fadiwa Mai unguwa, har xuwan su gidan qanwar mahaifinta dake a Zariya, da labarin da ta basu na dauke Sadiya da aka yi za a yi mata aure a halin ynx. Amir ya kai qarshe yana hawayen nadama. Tsohon yayi shiru yana wasi-wasin abin al'ajabin da ya faru. Ya yi ajiyar xuciya shima ya ce. . "Ta6! Lallai wannan al'amari shi ne hukuncin Allah. To Amir wane tudu wane gangare kuma lamarin ya kasance haka? Sadiyar nan fa da ka gani a birni ita ce wacce ka ci mutuncin mu akan ta sbd kawai mun baka auren ta kyauta, ita ce ka gani ka ke so a halin ynx?" . . KAI WANNAN TSOHO DA MASIFAR MITA YAKE, ACE ABIN DUNIYA BA ZAI WUCE BA A WURIN SHI? . Amir ya yi shiru bai ce komai ba cikin nadama, yana mai alhinin yadda al'amarin ya kasance haka daga baya. Tsohon ya ce. . "Rayuwar nan da ka ke gani haka Amir, kamar idaniyar ruwa ce, babu wanda ya san ta inda take 6ulla. Kaga da farko mune muka nemo maka auren Sadiya cikin sauqi kana zaune, amma ka wulaqantamu ka ce baka son ta 'yar qauye ce, ka tozarta mu a idon duniya. Ynx kuma gashi ka dawo mana kana kuka da gawaye mu taimake ka mu sake xuwa mu nemo maka auren ta a karo na biyu." . Tsohon ya yi shiru yana tunani, xuwa can ya ci gaba da cewa. . "bakin alqalami ya riga ya bushe Amir. Ynx haka iyayen Sadiya sun yi mata miji, za su yi mata aure. Ka san cewa ba zai yiwu mu sake xuwa wajen su mu tunkare su da maganar auren ka da Sadiya ba, bayan wulaqancin da aka yi masu a baya. Wannan ba zai yiwu ba Amir. Iyayen Sadiya sun fusata sosai akan wannan cin mutuncin da akayi mana, danginta sun yi kuka da idanunsu, akwai mutane da dama wadanda ke son yarinyar nan, amma ka hana su ita aka bamu, duk da cewar abota ce kawai da zaman tare ya hada mu da su ba 'yan uwantaka ba. Amma ka watsa masu qasa a cikin ido Amir. Kayi mana kunya son ran ka. Da wacce fuska ka ke tsammanin wani a nan zai sake komawa Turunkawa ya ce ya xo akan maganar ka a sake baka auren Sadiya sbd ynx ka dawo kana son ta? Wannan al'amari har abada ba zai ta6a yiwuwa ba. Tun farko kai ka dauki wuqa ka da6awa kan ka da kan ka. Ynx gashi wani zamani ya xo ka dawo kana son matar da har abada ba zata ta6a zama matar ka ba koda kuwa zaka ras ranka ne akan neman ta. >=== "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 29 . . Ynx gashi wani zamani ya xo ka dawo kana son yarinyar da har abada ba zata ta6a zama matarka ba. Ko zaka rasa ranka akan wannan yarinyar Amir ba zaka aureta ba. Kuma kai ka jawo ma kanka wannan matsalar tun farko." . Amir ya dafe kanshi a cikin tsananin azabar da yake ji a halin ynx. Tabbas ya yi kuskure a baya. Ya fara kukan nadama yana tausayawa rayuwar shi. Mai unguwa ya ci gaba cewa. . "Mu din nan da kuke gani mutanen qauye akwai irin namu hikimomin rayuwar wadanda suka sha banban da irin naku. Mun san cewar irin wadannan aurace-arcen da muke yiwa yaran mu a nsn tun suna qanqana, kuna ganin kamar bamu waye bane. Muna yin haka ne domin mu tsare su daga irin badalar da muke gani tana faruwa a wasu wuraren. A nan zaka samu wani talaka ne bashi da kudin aure, to don gudun kada irin su suyi yawa har su fara yada 6arna a cikin al'ummar mu, shi ne muke basu sadakar aure. Wannan shi ne gatancin da muka yi maka Amir, amma sai ka kasa fahimtarmu kai a ganinka bamu waye ba, ku 'yan zamani 'yan birni kune wayayyu. To ynx ga sakamako nan ka fara gani tun ba a je ko'ina ba. Sbd haka ka daina wulaqanta mutane, ka riqa girmama al'adunsu domin baka san hikimomin dake ciki ba." . Amir ya share hawaye. . "Na gode da wannan nasiha da kayi min, na gode da afuwar da kayi min. Amma duk da haka zan je garin su Sadiya da kaina, in nemi afuwarta da kuma iyayen ta." . Mai unguwa ya ce. . "Ina sake gargadinka, kada ka kuskura ka je Turunkawa, domin idan har iyayen Sadiya suka qyalla ido suka gan ka komai ya faru da kai, kai ka jawo wa kanka. Ka cire wannan yarinyar daga xuciyarka, ba matarka ba ce, iyayenta b zasu ta6a baka auren ta ba." . Amir ya ce. . "na gode mai unguwa sai dai ku taya ni da addu'a, idan kuma wannan yarinyar ita ce ajalina ku yi min addu'a Allah Ya gafarta min, ina son ta, ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba, kuma na dauki alqawarin zan tafi har garin su in nemi auren ta." . Mai unguwa ya ce dashi. . "to wannan kai ka daukarwa kanka, ni babu abin da zan iya cewa a halin ynx, na dai fadi maka gsky." . Amir ya tashi ya yi mashi sallama dauke da jakar shi, ya fita a cikin sauri. Iyalan mai unguwa Mutawakkilu suka xo wajen mai unguwa baki dayan su suka tambaye shi abin da ya sake dawo da Amir a wannan lkc. Tsohon ya fadi masu abin da ya faru tun daga farko har qarshe, sannan ya ja hankalin yara kan su bi duniya a hankali, ban da rashi kunya, ya basu misali da irin sakamakon da Amir ya samu. . Sbd haka Amir ya zama mai nacin soyayya, gashi nan ynx ya kamas hanyar Turunkawa, zai tafi nemo soyayya duk kuwa da hadarin da aka gargade shi zai iya cim mawa a can. . . **~** . . Tun a satin farko da Sarkin noma ya miqa qoqon barar shi wajen neman auren Sadiya, nan da nan sai Mal. Kalla da Mal. Buba suka tara 'yan uwa suka sanar dasu wannan abin alherin da ya same su, babu wanda ya yi jayayya akan maganar, kowa ya amince a ba Alh. Mamuda sarkin noma auren Sadiya. . A satin ya kawo kudin sadaki da kuma dukiyar auren da suka sara mashi bai rage ko anini ba, duk da a ganin su sun cika mashi kudin. A tarihin qauyen ba a ta6a aurar da wata yarinya da tsadar sadaki ba kwatankwacin Sadiya. . A ranar da aka kawo kudin auren ne da safe, nan da nan Mal. Buba ya shirya ya bazama birni dauko Sadiya, suka dawo gida domin kuwa sun ga abin na yi ne, ba maganar wasa ba ce. . Da Sadiya ta dawo gida ne ta samu maganar da ake yi har komai ya yi nisa, har an kawo kudin auren ta iyayen ta sun fara kacalcala su suna saye-saye. Sadiya ta ji tsoro ya kama ta, ta ji duniya ta yi mata qunci, domin kuwa a wannan karon iyayen ta sun sun shiga rayuwarta da yawa. Ta samu labarin mutumin da za a bata wani tsohon najadu ne, kuma matan shi uku ita ce ta hudu. Iyayen ta basu damu ba sai faman haja-hajarsu suke yi suna shawarwari, suna ta kasafin kudaden da Sarkin noma ya aiko dasu. . Qanin mahaifin ta Mal. Buba shi yafi daukar maganar da zafi-zafi. Tun a hanya da zasu dawo gida shi da Sadiya yake yi mmata fada yana cewa. . "wannan mutumin daya fito ya nemi auren ki mutumin kirki ne, duk fadin lardin nan babu wanda bai san shi ba wajen yiwa mutane alheri, sbd haka kada ki kuskura mu ji kin yi masa sakarci. . A wannan karon ita ma mahaifiyar Sadiya ba a bar ta a baya ba, domin kuwa da Sarkin noma ya kawo kudin da suka sara mashi naira dubu sittin, don a samu hadin kanta ta jawo hankalin Sadiya, sai Mal. Kalla ya ce a ware mata naira dubu ashirin, wannan nata ne tayi 'yan saye- sayensu na mata. . Aka kira ta dakin da ake zaman shawara an xube kudin akan tabarma, suna kallonsu suna xufa. Mal. Buba ya qirgo dubu ashirin ya miqa mata, ta amsa hannunta yana kyarma. A kaf shekarun da tayi zaune a wannan qauyen bata ta6a ganin tulin kudi masu yawa irin wadannan ba. . Sau daya ta ta6a yin adashi aka bata kwasar jaka goma- sha-hudu, shima sai da aka shekara ana yin shi, 'yar ribar da take samu ce ta qosai da take yi da safe da kuma surfen da take yi tana sayar da dusar in ta tare. . . Lp=30>===< "SO BAYAN RAI" >===< . . Page 30 . . 'Yar ribar da take samu ce ta qosai da take yi da safe da kuma surfen da take yi tana sayar da dusar in ta tara. . A wannan karon sai gata ita kadai an dunqulo mata har dubu ashirin, jaka dari fa kenan! Nan da nan tayi sauri ta kai su daki ta qudundune su a cikin leda ta daga katifarta 'yar sale ta cusa su a qarqashi daga nesa, ta dora katifar akan ledar, ta gyara ko'ina don kar a gane inda suke. Ta jawo kayayyaki da tsummokara ta kila su akan katifar, ta tsaya tana kallon wajen. Duk da haka bata yarda ta bar dakin ba ko daidai da qyaftawar ido, tana nan kusa da inda ta cusa kudin. Lkc-lkc tana daga katifar tana leqawa don ta tabbatar ledar tana nan a inda ta ajiye ta? . Sadiya sun dawo gida ita da qanin mahaifinta babu dadewa, sai mahaifiyarta ta fara yi mata fada tana cewa. . "Ynx ke dai ba yarinya bace qarama da za a saki a gaba a yi tayi maki fada, kin riga kin mallaki hankalinki, sbd haka kamar yadda babanki ya ce in tsare ki in ja kunnenki. To kin dai ji abin dake faruwa. Wannan mutum gsky babban mutum ne, sbd haka idan kin nema mana mutunci a wajen shi to kin kyauta mana, idan kuma baki bi shi kin nemo mana martaba dai mu kika jowo mawa, abin da ya rage ynx kawai sai sa ranar daurin aure, kuma ina jin gobe da safe zasu xo a yi magana." . Sadiya tayi shiru tana mamakin wannan abin al'ajabin irin wannan rayuwa da ta tsinci kan ta a ciki. Ta san cewar wasu 'yan qananun kudi suka rudi iyayen ta har suka rikice haka suke rawar jiki akan wannan tsoho da yake so ya aure ta, wato Sarkin noma. Talauci ya quntata tunanin su, basa tunanin idan suka bata wanda bashi da kudi wata rana zai iya samun wanda yafi na Sarkin noma. Ba ruwan su da soyayyar Amir dake a xuciyar 'yar su Sadiya. . Sadiya tayi tagumi tayi shiru tana tunanin Amir sabom masoyinta wanda ta baro a makaranta. Ta san cewar ynx haka yana can yana neman ta ruwa a jallo, Amir ba zai ta6a samun sukuni ba a rayuwar shi sai ya gan ta. . Sadiya bata son sa6awa umarnin iyayen ta, a lkc guda kuma bata son ta rabu da Amir. Shi yafi dacewa da irin rayuwarta, shi ne kawai zata zauna dashi ta more quruciyarta, kuma ya debe mata kewar duk wani abu da ta rasa. . Da misalin qarfe takwas da rabi na daren, qannen ta suka rugo aguje suka same ta a dakin mahaifiyar ta zaune tayi tagumi. Suka ce da ita. . "Sadiya ki xo Sarkin noma yana kira." . Ta ce dasu tana xuwa. Suka koma aguje suna murna, da gani ta san cewar ya bi su da naira goma-goma ne wataqila. Ta lura dai kowa yana son shi a gidan sbd kawai yana da kudi. Kafin Sadiya ta tashi ta canza kayan jikinta ne ta ji Mal. Buba qanin mahaifin ta ya fito tsakar gida yana daka mata tsawa. . "wai ke wacce uwa kike yi ne a dakin Sadiya? Ashe ba aiko ki je waje kin yi baqi ba?" . Nan da nan tayi sauri ta daura zani ta sa takalmi, ta warware gyalen ta yafa a waje ta fita qofar gida. A lkcn da ta fita ne ta same su a tsaye jikin wata (Bus) da suka xo da ita, su biyu suna sanye da manyan kaya. Daya a cikin su yayi siririn rawani wanda take tsammanin shi ne Sarkin noman. . Sadiya ta qarasa wajen su tayi masu sallama a sanyaye, suka amsa suna fara'a, sannan ta gaishe su cikin ladabi. Gama gaisuwar keda wuya sai ta qyale su. Duk da babu haske sosai a wajen ta ga fuskokin su. Sarkin noma shi yafi razana ta, ta ga fuskar shi baqi wuluk kamar kwalta, babu alamun sawaba ko rangwame tattare dashi, a qalla zai kai shekaru hamsin, abokin shima tsohon ne zai iya kaiwa hamsin. Dukanin su dattawa ne wadanda in a duniyar mutanen kirki ne zasu iya zama kakannin ta amma kuma ynx samarin ta ne. . Abokin Sarkin noma ya fara magana. . "mun san cewar kin samu labarin komi a gida Sadiya, sai dai dan qarin bayani da ya kamata muyi domin ku fahimci juna ke da sahibinki da yake sauraren abin da zaki ce ynx." . Sadiya bata ce komai ba, tayi shiru tana tunanin yadda rayuwarta zata kasance a haka tare da wannan tsoho, da kuma makomar Amir masoyinta da ke

Chapter 6 of 8