Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
mayakan baki daya saura boka Balbuna da Dan uwansa sune suka zamarwa Maridan nan alakakai can sai akaji wani kara gamida hargagi yaki ya tsaya cak sai wani sintimemen katon Maridi ya bayyana girmansa yayi icen rimi kaurinsa tamkar rumbu idanunsa manya manya kamar tulu wagegen bakinsa kamar kofar gari gaba daya maridan nan suka durkusa suka gaidashi ko kallonsu bayyi ba sai ya dubi balbuna da dan uwansa yace kun kasance kuna neman Yarima Samar domin kusace takobinsa dan wata bukata taku to kusani Yarima Samar yana hannun mu kuma kun shigo hannun mu . . Boka Balduna da dan uwansa sukayi kukan kura sukayi kan kafcecen mutumin nan yayi murmushi yasa hannu ya makesu tamkar ya make beraye haka suka baje akasa sumammu ya kece da dariya yace saini Gurdo babba dan babba inci mutum insha kwanyarsa kawai sai yayi gaba take yaransa suka kwashi balbuna da balduna sukayi awon gaba dasu sai da sukayi tafiya mai nisa acikin duwatsun nan sai suka isa birninsu wani dan karamin garine mai cike da tarin maridai akalla maza da mata zasu kai dubu goma koda aka hangosu sai gaba daya maridan suka kaure da ihu da tsalle an samu karin nama take aka bude wani katon keji aka wurgasu aciki sai suka fado agaban Yarima Samar kuma tsananin zafi da radadin buguwa da sukayi da murda murdan itacen kejin nan tasa suka farka daga suman da sukayi sai sukayi ido biyu daYarima Samar ya kamayi musu murmushin mugunta sai suka ji hayaniya abayansu atare suka waiga nan ma sai sukayi arba da tarin cincirindon maridai maza da mata sunata kallonsu suna lashe baki tamkar zasu ci danye. . A tsorace suka dawo da kallonsu ga Yarima Samar Sai ya kyalkyale musu da dariya yace kai ya dai tagwaye kun kasance kuna bin bayana dan ku rabani da takobina to kuma Gashi ni daku muna hannu mayu masu cin naman mutum danye lallai kusani sun kama mu ne domin gobe zasuyi bikin haihuwar matar sarkinsu kuma mune abin yanka awannan biki lallai gobe za ayi ta ko dai mu mutu ko mu rayu cikin biyu tabbas sai anyi daya ko mu ko su suka zazzaro ido Yarima Samar yace kuma kusani idan har mun rayu to zumu gwabza yaki tsakanin NI DAKU IN KUN kasheni ku dauki takobina ni kuma tabbas inna samu dama to ba makawa sai na kasheku. . Gari ya waye haske ya gauraye ko ina sai maridan nan suka fara fitowa daga gidajensu nanfa suka fara shirye shiryen biki tirkashi mata da maza sai kaiwa da komowa sukeyi kafin wani lokaci sun taru sun cika guri sai kade kade da wake wake sukeyi wani abin tashin hankali shine kafin sarki ya fito an yanka mutane sunkai bakwai an jefasu cikin tukunya wanda aka a'sana an tata da kasa duk wannan shagali da akeyi agaban yarima Samar akeyi da su Boka Balbuna boka balbuna ya dubi dan uwansa yace dan uwana lallai yau sai buzun mu dubi mahaukatan mutan nan yadda suke dafa naman mutum kalli yanda suke gasa hanjin dan adam lallai tamu tazo karshe Balduna yace tabbas dan uwa neman duniya ya kawo mu ga halaka. . Koda yarima Samar yaji wannan hira sai ya fashe da dariya yace kai lallai da sauranku a gwagwarmayan duniyar yanzu kuna nufin har kun sare ne kun yarda ayau zaku mutu balduna yayi wa Samar kallon mahaukaci yace yanzu kana nufin kana saran kubuta daga hannun mayun nanne Yarima Samar yayi murmushi yace kwarai kuwa tabbas sai dai insha wuya amma ina da yakinin cewa bazan mutu ahannun maridan nan ba Boka Balbuna ya tintsire da dariya yace haba dan samari ka daina yaudarar kanka amma ina tabbatar maka yaune ranar karshe na rayuwarka Yarima Samar yayi murmushi irin na mazajen fama ya dafa kafadar Boka balbuna yace kaidai ina baka shawara duk lokacin da ka samu dama to kayi kokarin guduwa. . A dai dai wannan lokacin ne sarki ya fito gabaki daya maridan nan suka fadi kasa mata da maza suna gaida Sarki bayan ya wuce ya zauna awata katuwar kujera wanda aka sana'antata da dutse sai kowa ya mike sarki ya fara jawabi jama'a muna muku barka da zuwa wajen wannan kayataccen biki domin taya 'yata murnar bikin karin shekara saboda haka afito da mutanen da aka tanada don a yanka mata take aka zaro Yarima Samar Su balduna aka tsaidasu agaban sarki malamin yanka ya fito babban kuskuren da maridan nan sukayi shine da suka zabi makamin yarima Samar ya zama abin yankansu wasu katti biyu suka gabato da takobin an ajiye ta a wani katon baka sannan aka ajiye bakan agaban su. . Yarima Samar gadan gadan malamin yanka ya taho domin ya dauki wukar ai sai da ya durkusa zai dauka sai yarima Samar ya jijjiga kafarsa ya tabkatawa malamin yanka sai da yayi sama kamar kibiyar da aka harba sannan yayi wani kara na azaba tsananin mamaki Maridan nan suka tsaya kallon inda duk girman malamin yanka ke cilla gudu asama kawai saboda yarima samar ya masa kafa lokacin da hankalinsu ya dawo jikinsu sai sukayi arba da Samar rike da takobinsa sai muzurai yakeyi nanfa aka fara kallon kallo Sarki ya daka wa Yarima Samar tsawa yace kai yaro kada kuruciya ya dibeka lallai bazaka iya yaki damu ba tabbas kwananka ya kare dama kadan gana ka mutu a saukake da yafi maka . Samar yace karyane maza dangin gujjiyane lallai sai anfasa ake sanin mai kwaya lallai zan gwabza yaki daku ko ni ko ku za agane wanene jarumi afusace sarki yayi umurni da ai kaca kaca da Yarima Samar take maridai sukayi kanshi shima yayo kansu yana karaji yayi kururuwa ya afka musu da sara ai sai mayun nan suka sha mamaki domin zarya biyu yayi acikinsu sai ga mattatu sama da dari ransu ya baci suka rufe shi da sara da suka amma sai ya zamar musu alakakai yaja tunga ya bude daga yayi runfa ya shiga turasu kiyama guri ya yamutse ya hargitse bakajin ihun komai sai ihun mazaje Yarima Samar ya zama kamar wani aljani har wani tsalle yakeyi sama yana dawowa kasa idan maridan nan ya rufe Burinsu kawai suga sun illata SAMAR . Sun mance da Balduna da balbuna su kuma tun da suka ga ba a ta ta su sai sukayi wa kansu kiyamallaili suka bace bat afilin sannan suka yanki daji tuni sukayi nisan ban mamaki afilin daga kuwa maridawa sunji badadi Yarima samar sai shiga da fuce yakeyi atsakan kaninsu kuma duk inda ya gilma sai dai kaga maridan nan na faduwa kamar bishiya dole sukaja da baya koda ganin haka sai sarkinsu ya kwarara ihu ya mike yana wani huci yana wani kumburi ya takarkare ya kwarara wani uban ihu sannan ya nuna Samar yace kai karamin halitta lallai ka cika shaidani yau kimanin shekaru dari ba a taba samun mutum ko aljan ko wata muguwar halitta da tazo ta iya kashe mana mutum biyu ba amma kai yau ka kashe mana mutane sama da fin kirge lallai dole sai ka mutu kuma tabbas sai munci naman ka danye Yarima Samar yayi dariya yace to karka soma gwada yaki dani domin bazaka iyaba tabbas in ka gwada mutuwa zakayi. . Sarki ya kwarara ihu yayi kan Samar sukayi wani irin mummunan haduwa yasa kafa ya banke Samar take ya baje akasa sarki ya daga takobi da niyyar raba shi gida biyu af ai ya makara tuni Yarima samar ya rarumi takobinsa yayi wani yunkuri jikake cas ya farwa sarkin maridan tsananin zafi ya kwarara ihu ya kama tsalle yana birede Yarima Samar ya daka tsalle kamar tsuntsu ya tashi sama ya sare kan sarki ai sai ga kai daban gangar jiki daban wayyo ai sai maridan nan kowa yayi ta kansa Yarima Samar ya baje akasa tamkar ya mutu saboda tsananin gajiya yana nan kwance yana numfashi sama sama sai ya farajin wani iska asamansa dakyar ya iya bude idonsa Dan kari ai sai yayi arba da wasu maka makan angulaye girmansu yayi girman saniya suna shawagi asamansa lallai tsigu ne bata kareba domin suna shirin afko masa ne wai suma sunga nama Lokacin da Yarima Samar ya daga kansa yaga wasu ma yunwatan angulaye suna neman daka masa wawa sai yaji gaba daya gajiyan dake jikinsa yakau yayi zumbur ya mike yafara jada baya da niyar zai gudu amma sai yaga sun kewaye shi sama da kasa wasu asamansa wasu kuma sun dira a kasa sai ya dage ya zare takobinsa yaja tunga kamar suna jiransa ya shirya kawai sai suka falfalo aguje suna wani irin kara mara dadin ji. . kwaram kwatsam aka fara tafka yaki angulayen nan suka haukace suna kawo masa wafta suna kokarin hallakashi shi kuma ya himmatu wajen kaucewa da zillewa sai da aka dauki tsawon sa'a biyu suna tabka gumurzu koda YARIMA samar yaga wankin hula zai kaishi dare sai ya fusata ya kumbura yayi dam ya cika ya batse tamkar zai fashe sai ya wage baki ya saki wani wawan ihu kai ihun maza in suka fusata dole kananan jarumai suja baya ba shiri Angulayen nan suka tashi sama suka yiwa Samar runfa su basu gudu ba kuma basu afka masa ba ya fita aguje angulayen nan suka rufa masa baya da masifan gudu ta sama da ta kasa.SIHIRTACCIYA . PART END . Kaico da angulayen nan sunsa bala i da masifar da Yarima Samar zai kunno musu to da baza subi bayansa ba suna cikin gudu sai ya tsaya cak sannan ya juyo yana wani sambatu yana damdam yana hamm ham yayi tsawa gamida nuna Angulayen nan na sama da yatsa take wata curarriya wuta tayi sama sannan ta watse asama take ta kone angulayen nan ya dunkule hannu ya daki kasa take kasa ta rufta da angulayen dake binsa ta kasa ya kwarma ihu wuf wata katuwar Angulu ta sunkuci takobin yarima Samar ta fita da gudu tana gare gare akasa . Samar ya bita aguje suka kifa tsere ya kure mata gudu saura kiris ya cimmata sai tayi wuf ta tashi sama Yarima Samar yayi girgiza take ya zama wani jibgegen tsuntsu sukasa tsere asararin samaniya da matsananci gudu irin na fanfalaki ya kure mata gudu ya cimmata suka fara dauki badadi asararin samaniya gumurzu yayi gumurzu ba shiri sukayo kasa tun kafin su karaso kasa gaba daya suka rikide suka koma suffarsu Samar ya koma Samar ita kuma angulun ta rikide ta zama wata santaleliyar budurwa tana rike da takobinsa ahannunta cikin tsananin mamaki ya kalleta yace ke wacece ke idan har mazaje na bukatar takobina dan su auri Sarauniyar kyau na duniya Gimbiya lubiya to ke me zakiyi da takobina tace kayi hakuri domin ni bukatata yasha banban da bukatar sauran mazajen domin ni ina neman sane don tseratar da masarautata da jama'ata Yarima Samar yace a ina Masarautanki yake kuma menene ke muku barazana tace zanfada maka amma ka kasani lallai idan har kaji labarina cikin biyu dole ne ai abu daya Samar yace na amince Al amarin Boka balbuna da dan uwansa Balduna kuwa tun sa'ar da suka samu damar tserewa agurin maridan nan sai suka samu kansu awani daji mai yalwa itayuwa da ganyayyaki bayan sun samu natsuwa sai Balduna ya fashe da kuka ya dubi boka Balduna yace kaico dan uwana hakika ina matukar son Gimbiya Lubiya to amma ya zama dole in hakura tunda na tabbatar takobin Gimbiya Sarbila bazai kwatu ahannun Yarima Samar ba Zumbur Boka Balduna ya mike ya kwarara ihu yace karyane ace dan uwan haihuwata ya nemi abu awannan duniya ya rasa alhali ni ina raye tabbas sai ka samu gimbiya Lubiya koda ko zan rasa raina Balduna ya mike yace kaico dan uwana karmu yaudari kan mu na hakura. Boka Balbuna ya kwashe dan uwansa da mari sannan ya fashe da kuka ya rungume shi sai da suka dau lokaci mai tsawo sannan suka rabu da juna Boka Balbuna ya dafa kafadar dan uwansa yace tabbas zamuyi nasara kawai ka saurareni Boka balbuna ya share kasa ya rubuta wasu murdaddun rubutu ya share sai ya kece da dariya ya mike ya kama hannun dan uwansa yace tashi muje Balduna yace ina zamu yadan uwana Ya tintsire da dariya yace gurin hatsabibi dan hatsabai kaji mutum da rabinsa mutum rabinsa shaidan dan shaidanu kaji haihuwar mutum da aljan iblisu uban shaidanu garnakaki garkami wandon karfe koya saka ya kwana atsaye tinjim yasha kundum mijin masifa da bala ii. . Koda Balduna yaji irin wannan kirari da zuzutawa da dan uwansa kewa wani mahaluki sai yace yakai dan uwana shin wani Hamshakin Bokane wannan da kake kururutawa haka Boka Balbuna ya kece da dariya yace babban malami nane abokanci lallai ya shahara kuma ya tumbatsa aharkar tsubbu da bokanci ahalin yanzu yana can gidansa dake karkashin kasa adajin Sauban lallai in har muka riskeshi tabbas zai mana maganin matsalarmu amma akwai matsala guda daya Balduna yace menene matsalar yakai dan uwana boka Balbuna yace tabbas kafin mu isa gidan Boka Ruman sai mun dandani azaba da masifu kala dari lallai daji ne da akewa lakabi da kurman adajin akwai miyagun mutane da shaidanu aljanu adajin Sauban amma idan muka jajirce kuma mukasa aranmu sai munyi nasara to kuwa lallai sai munyi nasara Balduna yace ai matukar zuciya zata samu abinda takeso to gangar jiki zai daure wuya tunda ba haushe yace wuya bata kisa sai suka rungume juna . Al amarin yarima Samar da budurwar nan kuwa sai ta miko masa takobinta sannan tace ni sunana Kaulatu bintu Kaluta sunan kasar mu kahunam ya kasance babban birni dake cike da mutane maza da mata muna zaune cikin soyayyar juna da kaunar juna domin mahaifina shine Sarkin kahunam kuma ya kasance adali mai tausayi ga talakawansa ya tsani zalunci kuma baya son azzalumi gashi sam baya bambance tsakanin talaka da mai kudi matukar wani zai zalinci wani tofa bazai kyaleba wannan dalilin ne ya haifar mana da kwanciyar hankali da soyayyar juna tabbas mutanen kasar Kahunam sun kasance jarumai kuma zakakurai afilin daga sam bamu san tsoro ba kuma muna da tsananin hadin kai domin idan masifa ta samu dayan mu to duk tsananin wuya baza kaga yan uwansa sun gujeshi ba tabbas sai sun taimake shi koda ko za ayi asarar rayuka. Da mutanen Kahunam su ga mutuwar dan uwansu agabansu to ina tabbatar maka gara su rasa rayuwarsu gaba daya koda kuwa sun kai su dubu da wannan hadin kanne muka gagari makiyan mu domin bamu da munafiki kuma bamu da rago kwatsam muna zaune lafiya sai wata annoba ta fado birnin mu wata muguwar cutane ta bayyana akasar haka kurum sai mutum ya kama kuraje ajikinsa ta ko ina da zarar an kwana biyu sai fatar mutum ta fara rubewa haka kuma da an kara kwana biyu sai fatar ta fara zagwanyewa haka za kaga mutum ya koma ba komai ajikinsa sai kashi kuma abin mamaki sam mutum bazai mutuba tun ana ganin abu kamar wasa sai abu ya cika gari ko ina cuta tayi yawa ta buwayi jama'a munyi duk yanda zamuyi mu samu maganin cutar nan amma abin ya gagara. . kwatsam rannan ana fadanci sai wata aljana yar gajeruya ta bayyana atsakiyar fada dakaru suka zare takobi sukayi kanta sai ta sabi kalaman surkulle gami da kalaman tsatsuba ta nuna dakarun da su nufota take wuta ta konesu wasu suka taso mata tayi hura da bakinta wata kakkarfar iska ta sunkucesu tayi waje dasu har yanzun nan da nake maka bayani ba a sake ganin su ba kuma ba a san inda suke ba koda sarki kaulata yaga haka sai ya hana Dakaru fuskantar Aljanar nan take kowa ya tsaya da fada tayi shiru bakajin motsin komai sai wurwurga idanu jama'a sukeyi suna kallon aljanar nan atsorace can Sarki ya mike yace yake wannan bakuwar aljana menene dalilin ki na zuwa wannan guri aljana ta kece da dariya tace da tun farko kun tambaye ni ai da mutanen ku basu mutu a banza ba . taci gaba da cewa ni sunana gurdil kuma nice sarauniyar gajerun aljanu tabbas mun kasance muna bukatar Takobin Jaruma Sarbila wanda ahalin yanzu takobin tana hannun wani jarumi wanda ya kasance jinin tane na asali mai suna Yarima Samar to wannan takobin muke so kuje ku raba Yarima Samar da ita Sarki Kaluta yace mu mutane ne ku kuma aljanu ne me zaisa bazaku karbo da kanku ba alhali kun fimu karfi kuma kun fimu karfin sihiri aljana ta daure fuska tace kasani yakai wannan sarki Ahalin yanzu Samar yana hannun Maridan nan masu tsananin tsawo da karfi lallai inda wadannan maridan suna raye to da bamu da damar kusantar dajin nan domin sun fi mu hatsabibanci amma ku zaku tsince shine abagas bayan ya gabza yaki da muridan nan yasha wuya ya galabaita to sai ku shammace shi ku wafce takobinsa Sarki kaluta yace to idan har muka dauko takobin nan menene ladar mu agareku Aljana Gurdil ta kece da dariya tace zamu muku maganin cutar dake damun ku Sarki yace tayaya zamu amince da cewa zaku iya yi mana maganin cutar dake damum mu aljana tace akawo kwarya aka kawo ta karba takama surkulle tana sambatu take kwaryar tacika da ruwa tamika kwayar tace abawo masu fama da cutar nanfa aka fara bawo wasu na farko yana sha tuni sai yakoma kalau tamkar bai taba wani cutaba nanfa aka shiga rububi ana shan ruwan nan duk bakin wanda yasha ruwan nan sai da ya warke koda ganin haka shine muka tari aradu daka muka shirya muka fito farautarka Koda Balduna yaji irin wannan kirari da zuzutawa da dan uwansa kewa wani mahaluki sai yace yakai dan uwana shin wani Hamshakin Bokane wannan da kake kururutawa haka Boka Balbuna ya kece da dariya yace babban malami nane abokanci lallai ya shahara kuma ya tumbatsa aharkar tsubbu da bokanci ahalin yanzu yana can gidansa dake karkashin kasa adajin Sauban lallai in har muka riskeshi tabbas zai mana maganin matsalarmu amma akwai matsala guda daya Balduna yace menene matsalar yakai dan uwana boka Balbuna yace tabbas kafin mu isa gidan Boka Ruman sai mun dandani azaba da masifu kala dari lallai daji ne da akewa lakabi da kurman adajin akwai miyagun mutane da shaidanu aljanu adajin Sauban amma idan muka jajirce kuma mukasa aranmu sai munyi nasara to kuwa lallai sai munyi nasara Balduna yace ai matukar zuciya zata samu abinda takeso to gangar jiki zai daure wuya tunda ba haushe yace wuya bata kisa sai suka rungume juna . Al amarin yarima Samar da budurwar nan kuwa sai ta miko masa takobinta sannan tace ni sunana Kaulatu bintu Kaluta sunan kasar mu kahunam ya kasance babban birni dake cike da mutane maza da mata muna zaune cikin soyayyar juna da kaunar juna domin mahaifina shine Sarkin kahunam kuma ya kasance adali mai tausayi ga talakawansa ya tsani zalunci kuma baya son azzalumi gashi sam baya bambance tsakanin talaka da mai kudi matukar wani zai zalinci wani tofa bazai kyaleba wannan dalilin ne ya haifar mana da kwanciyar hankali da soyayyar juna tabbas mutanen kasar Kahunam sun kasance jarumai kuma zakakurai afilin daga sam bamu san tsoro ba kuma muna da tsananin hadin kai domin idan masifa ta samu dayan mu to duk tsananin wuya baza kaga yan uwansa sun gujeshi ba tabbas sai sun taimake shi koda ko za ayi asarar rayuka. Da mutanen Kahunam su ga mutuwar dan uwansu agabansu to ina tabbatar maka gara su rasa rayuwarsu gaba daya koda kuwa sun kai su dubu da wannan hadin kanne muka gagari makiyan mu domin bamu da munafiki kuma bamu da rago kwatsam muna zaune lafiya sai wata annoba ta fado birnin mu wata muguwar cutane ta bayyana akasar haka kurum sai mutum ya kama kuraje ajikinsa ta ko ina da zarar an kwana biyu sai fatar mutum ta fara rubewa haka kuma da an kara kwana biyu sai fatar ta fara zagwanyewa haka za kaga mutum ya koma ba komai ajikinsa sai kashi kuma abin mamaki sam mutum bazai mutuba tun ana ganin abu kamar wasa sai abu ya cika gari ko ina cuta tayi yawa ta buwayi jama'a munyi duk yanda zamuyi mu samu maganin cutar nan amma abin ya gagara. . kwatsam rannan ana fadanci sai wata aljana yar gajeruya ta bayyana atsakiyar fada dakaru suka zare takobi sukayi kanta sai ta sabi kalaman surkulle gami da kalaman tsatsuba ta nuna dakarun da su nufota take wuta ta konesu wasu suka taso mata tayi hura da bakinta wata kakkarfar iska ta sunkucesu tayi waje dasu har yanzun nan da nake maka bayani ba a sake ganin su ba kuma ba a san inda suke ba koda sarki kaulata yaga haka sai ya hana Dakaru fuskantar Aljanar nan take kowa ya tsaya da fada tayi shiru bakajin motsin komai sai wurwurga idanu jama'a sukeyi suna kallon aljanar nan atsorace can Sarki ya mike yace yake wannan bakuwar aljana menene dalilin ki na zuwa wannan guri aljana ta kece da dariya tace da tun farko kun tambaye ni ai da mutanen ku basu mutu a banza ba . taci gaba da cewa ni sunana gurdil kuma nice sarauniyar gajerun aljanu tabbas mun kasance muna bukatar Takobin Jaruma Sarbila wanda ahalin yanzu takobin tana hannun wani jarumi wanda ya kasance jinin tane na asali mai suna Yarima Samar to wannan takobin muke so kuje ku raba Yarima Samar da ita Sarki Kaluta yace mu mutane ne ku kuma aljanu ne me zaisa bazaku karbo da kanku ba alhali kun fimu karfi kuma kun fimu karfin sihiri aljana ta daure fuska tace kasani yakai wannan sarki Ahalin yanzu Samar yana hannun Maridan nan masu tsananin tsawo da karfi lallai inda wadannan maridan suna raye to da bamu da damar kusantar dajin nan domin sun fi mu hatsabibanci amma ku zaku tsince shine abagas bayan ya gabza yaki da muridan nan yasha wuya ya galabaita to sai ku shammace shi ku wafce takobinsa Sarki kaluta yace to idan har muka dauko takobin nan menene ladar mu agareku Aljana Gurdil ta kece da dariya tace zamu muku maganin cutar dake damun ku Sarki yace tayaya zamu amince da cewa zaku iya yi mana maganin cutar dake damum mu aljana tace akawo kwarya aka kawo ta karba takama surkulle tana sambatu take kwaryar tacika da ruwa tamika kwayar tace abawo masu fama da cutar nanfa aka fara bawo wasu na farko yana sha tuni sai yakoma kalau tamkar bai taba wani cutaba nanfa aka shiga rububi ana shan ruwan nan duk bakin wanda yasha ruwan nan sai da ya warke koda ganin haka shine muka tari aradu daka muka shirya muka fito farautarka Kawai sai yarima Samar ya mikawa Kaulatu takobin ta kalleshi yace jeki maza ki ceci Jama'arki ta karba takama hanya ta nufi birninta saura kiris ta isa kofar garin Kawai sai taji kasa na girgiza tana tangal tangal kamar zata kife kwatsam sai ga jerin gwanon tawagar wasu Shirga shirgan mutane suna bisa wasu maka makan giwaye sun tun karota ta juya da baya sai tayi arba da wata tawaga ta murza murzan mayaka su kuma sukan nagartattun dawakai bakake sidik Gabas da yamma kudu da arewa mazaje ne sun kewaye KAULATU Tab bari na pece kafin abu yazo ya dugunzume hehehhhe MUHADU A LITTAFI NA UKU DON JIN YANDA ZATA KASANCE nàku real rayyañu An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5