Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
iya dauka amma bayan ka sare gabobi masu mahimmanci guda bakwai ajikin gunkin dake gadin kayan jarumin sannan kasani koda kai nasarar sare gabobi bakwan dake jikin gunkin to kafin ka fita da kayan yakin to sai ka fuskanci turjiya lallai wannan aikine da zaka iya rasa rayuwarka takama hannunsa tace yakai dan uwana ina baka shawara da ka hakura kazo mu fita awannan dakin domin zamu iya halaka akoda yaushe awannan dakin ya fizge hannunsa ya jada baya yace haba yayata kisani bokana ya tabbatar min da cewa matukar na samu nasarar dauko kayan yakin jaruma sarbila guda biyar da damarar ta da takobinta da Garkuwar ta da mashinta da kuma takalman yakinta lallai ba makawa sai naje Darul sabah na samo ruwan waraka kuma ya tabbatar min da cewa lallai indai nayi nasarar wannan tafiya zakiyi aure kuma zaki hayayyafa kuma babu abinda zai taba mutuncin kasar mu lallai ina bukata kamar yadda muka rasa zurriyar mu dalilin kare kasar mu to mu sake yaduwa ta dalilin kare kasar mu. Yazrina ta fashe da kuka ta rungume dan uwanta sai da suka dauki lokaci mai tsawo ta sakeshi tace ya dan uwana lallai na tabbatar duk duniya babu mai gatana kai kadaine dan uwana aduniya amma kanaso ka saida rayuwarka saboda ni hakika ina son aure amma an haramtamin dole na hakura saboda kasata kaje dan uwana darajar soyayyar yan uwantaka babu abinda zai same ka tabbas zakayi nasara Samar yai murmushi ya sumbaci yazrina sannan ya fuskanci bangaren inda aka ajiye kayan yakin Gimbiya Sarbila tun kafin ya karasa Gunkin dake gadin kayan yakin Jaruma Sarbila ya fara motsi jajayen idanunsa suka fara jujjuyawa wata kafceciyar takobi ta fado hannun gunkin wani zabgegen mashi ya fado hannun gunki wani hayaniya ya fara tashi adakin. . YARIMA Samar yana tunkarar kayan yakin Jaruma Sarbila sai gunkin shima ya tunkari Samar takobinsa ahannu suna haduwa sai suka kacame da masifaffen yaki suka shiga dauki badadi suka dinga kaiwa juna miyagun hare hare yarima Samar yayi iya kokarinsa ganin ya kare duk wani hari da gunkin nan ke kawo masa abin takaici shi kuma in yayi nasarar saran gunkin sai yaji kamar ya sari dutse yayi iya dabaransa ya samu makama ajikin gunkin nan amma abin ya gagara samar ya shiga tashin hankali Gimbiya Yazrina tace dan uwana yi kokari ka sari kafadarsa. Cikin sa a ya zabgawa gunkin sara akafada sai da gunkin yayi kara kafadar ya tsinke duk da haka sai gunki yakara azama wajan yakar samar har ya yankeshi acinya Samar ya fusata ya afkawa gunkin da fada yasa tsinin takobi ya tsire idon gunki yayi kara cikin zafin nama Samar yayi kwance kwance ya sare kafar gunki ya koma mai kafa daya hannu daya ido daya amma har yanzu bai saurara wajen yakar Samar ba saima azama da himma sukaci gaba da yaki mai tsanani da tashin hankali Samar ya shammaci gunkin yakara soke idon yasa takobi yakara sare daya kafar take gunkin yakoma yahade sannan ya kame kamar ba shiba SAMAR ya mika hannu zai dauki kayan yaki sai yaji an daka masa tsawa ko saurarawa bai yiba sai ya dauki kayan kawai sai kota ina aka saki guda har da tafi take ya sanya kayan yakin ya dubi Yazrina yace muje yar uwata muje ta kama hannunsa suka tunkari kofar ita kanta kofar tasan shirin yanzu yafi na dazu da kanta kofar tabude sai gasu sun fito dole kanwar naki. Gaba daya dakaru da masoya da makiya sai da suka sarawa Yarima Samar da Gimbiya yazrina inda mutanen gari musamman yan mata suka shiga rera wakokin yabo ga yarima Samar suna tafe jama'a na bin su har tsakiyar fada sannan yakama yar uwansa ya daurata akan karagar mulki sannan ya dubi jama'ar dake fada ya daga murya yace yaku jama'ar kasata kusani Yau saura kwanaki hamsin Sarki Shaddadu yazo kasar nan da niyyar daukan yar uwata Gimbiya Yazrina kuma kun sani matukar ya dauketa amatsayin mata to kuna sane da bala ine zai rufto mana mara adadi har sai mun tarwatse mun watse baki daya tarihin mu zai rushe sai an nemi mutum daya daga ahalin wannan gari an rasa kuma bamu da karfin da zamu iya hana Sarki Shaddadu hana daukar Gimbiya yazrina domin ya fimu karfi ya fimu tsafi rundunansa taninka namu sau dubu goma lallai hanya daya ne mafita shine mu tashi Sihirtacciya daga daskarewar da tayi na shekaru dari bakwai ya dubi al umma yace toni bance kowa ya taimake niba kuma babu mai hanani zuwa gaba daya jama'a aka dauka muna mafatan alheri mun yarda mun amince daga nan Samar yace babu lokaci gobe zan dau hanyar zuwa Darul Sabah domin samo Ruwan waraka arijiyar Baroki. Tsai tsaye suke kamar gumaka sun kai kimanin su dubu dari yau kwanansu bakwai atsaye kuma da rayukansu basu mutuba sun tsayane suna jiran Boka Balbuna ya fito daga haular tsafinsa daya shiga yau kwana bakwai can sai gashi ya fito fuskarsa baki kirin babu annuri babu wani alamun tausayi yayi sharkaf da zufa har diga yakeyi ya dubi jama'ar da ke tsaye yace yaku dakaruna kusani shigan halwar tsafina na samo bayanai kusani na gano wani saurayi mai burin tada sihirtacciya lallai jarumine na gaske da alamu zai iya zuwa darul sabah sai dai zuwan sa ba alheri bane ga matsafa da kafuran duniya domin da yuwwar ya dawo da sabon addini kuma tabbas addinin mai rinjaye ne akan kafurci Wani sadauki yace yakai Boka Balbuna yanzu meye mafita Balbuna yace mafita shine muma mutashi sihirtacce Gaba daya dakarun suka tsorata suka zazzaro idanu suka dan jada baya suka fara yiwa boka Balbuna kallon mahaukaci wai zai tashi Boka Karibu bn kalab Daga daskarewar shekaru dari bakwai. . Afirgice wani dakare yace yakai babban Boka kasani tada Sihirtacce kamar tsokano masifa ne tana kwance Boka Balbuna ya kece da dariya yace kasani ko mu tashi sihirtacce ko kar mu tashe shi tunda yarima Samar yayi kudirin tashin Sihirtacciya to masifa zata fado mana matukar yayi nasara lallai sai kafurai da mushirikai da matsafa sun koka sai mu nemi gurin buya barden nan yace ya shugaban bokayen duniya yanzu menene abinyi Boka Balbuna yace Zamuyi tafiya ta kwanaki talatin zuwa dawowa zamu tafi tsibirin kumana don mu samo bakin ruwa wanda zamu tada boka karibu bn Kalab Acan Birnin Manohar kuwa Yarima samar yayi bankwana da jama'arsa ya durfafi daji yayi gabashin duniya da niyyar zuwa Darul Sabah domin debo ruwan waraka a rijiyar baroki sai da ya shafe kwanaki bakwai yana keta dazuzzuka da kwazazzabai wata rana daga ranakun tafiyarsa sai ya hango wani ayarin fatake sun taru kimani su dubu yana karasowa sai ya tarar yan fashine suka taresu suna karbe musu dukiya Samar na isa sai wani ya daka masa tsawa yace yakai kyakkyawan saurayi maza ka sauka akan dokin ka ka ajiye damararka da takobin ka da guzurin ka kakoma gefe kamar yadda sauran jama'a sukeyi Samar yayi murmushi yace to aini ba rago bane bakuma sakarai bane sannan ni ba mace bane da har wani zai min muzurai ya karbi kayana wani barkeken bakin kato mummuna dake zaune a tushen wata katuwar bishiya ya mike yana gurnani ya cika yana batsewa ya takarkare ya daddage yakwarara ihu ya nuna Samar da yatsa yace kai yaro wanene kai me ka taka shin duniya tayi maka kunci ne kake son ka mutu Samar yayi dariya yace sam babu daya aciki kawai kayana ne bazai karbuba idan ko ana son a karba to sai dai mu gwaza yaki tsakanin ni dakai duk wanda yayi galaba akan dan uwansa to sai yaci ribar fadan. Katon mutumin nan ya kece da dariya ya dubi yaransa yace kunji wani mahaukaci wai da Kodago zaiyi yaki suka fashe da dariya sukace maigida ai sai ku jarraba lallai yau zamu sha kallo Kodago yace wo yaransa lallai zamu gwabza fada tsakani na da wannan wawan kuma ina gargadinku da kada kowa ya tayani wannan fadar koda kuwa yaga za a hallakani ransa abace ya dubi Samar yace fiye da shekara talatin ina fashi awannan dajin amma ban taba ganin mahaukaci kamarka ba domin babu wanda ya taba gangancin tarata da fada koya yi min kallon banza balle ya tareni da yaki Samar yace kana haduwa da yan matane yau kuma ka hadu da namijin gaske lallai yaune karshen fashinka awannan dajin Kodago ya kwarara ihu ya shata layi da takobi ya daga murya yace yaku mutanen ayarin da mukayi wa fashi kusani daya daga cikin ku ya takale ni da yaki kuma zamu gwabza lallai kusani in yayi nasara to kun tsira daga kaifin takobina amma matukar nayi nasara akansa lallai sai na yanka ku daya bayan daya cikin matafiyar ya duri ruwa Kodago ya nuna Samar da takobi yace yaro lokacin mutuwarka yayi taho. Samar yayi wa dokinsa kaimi ya nufi kodago afusace sukayi wani irin haduwa mai tattare da mugun nufi yaki ya kullu atsakaninsu suka shiga neman ran juna hankalin yan kallo ya tashi domin kowa zai iya nasara awannan yaki kaiwa juna sara sukeyi ba kakkautawa ran Kodago ya baci kamar shine wani karamin yaro ke jayayya dashi ya canza salon fada ya shiga kaiwa Samar farmaki ta sama da ta kasa take ya rikita Samar kuma har ya yankeshi a kafada jini yayi tsartuwa Kodago ya kece da dariya yace yaro lokacin mutuwarka yayi taho in karasa ka afusace Yarima Samar ya afka wa kodago da wani azabebben yaki ya shiga auna masa wasu mahaukatan hare hare dakyar kodago ke iya karewa can Samar ya kawo wani nagartaccen sara dakyar kodago ya kauce amma duk da haka sai da saran ya sauka awuyan dokin take ya guntule kan dokin Kodago ya baje akasa kafin ya tashi Samar ya diro ya damke shi yayi sama da shi ya maka da kasa. kodago yayi kara Kafin ya rufe baki tuni Samar ya tsinke masa kai da takobinsa ai tuni sauran yan fashin suka cikawa wandon su iska suka shiga daji don neman tsira matafiya sukayi murna kowa aka bashi dukiyansa sannan kowa yakama hanyansa Samar yakara gaba sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya isa wani katon birni ya kunna kai cikin garin babu wanda ya damu dashi yana tafe sai ya taradda wata dattijuwa ta hada kai da guiwa tanata kuka ga kuma wasu yan mata biyu suna gefenta suma kukan sukeyi yarima Samar ya sauka yaje gurinsu yace musu yanaso su taimake shi da ruwan sha duk da suna halin bakin ciki sai matan nan ta umurci daya daga cikin yan matan nan data kawo masa ruwa bayan yasha sai ya tsaya yana kallonsu cikin tausayi matar nan tace masa kai ka nemi taimako mun maka to me kake jira Samar yace kuyi hakuri amma ina son inji dalilin kukan ku matan nan ta mike tace koda mun fada maka lallai ba abinda zaka iyayi don haka karu fama kanka asiri ka kara gaba samar yace ki fada min ba mamaki in muku maganin matsalarku ta kyalkyale da dariya sannan ta daure fuska tace wane kai yaro abun ya wuce sanin mutum sai dai Aljan Samar yace karki damu kiban labari da yuwan in zame muku garkuwa ta daure fuska ta haderai kamar wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta nuna shi da yatsa tace kasani ka nemi taimakon mu mun taimaka idan har kaji damuwar mu kaji labarin mu to ya zama dole ka fuskanci bala i da masifa dake cikin labarin mu Samar yace na amince tace to ka biyo mu cikin gida . tabdijan aradu bazan bisu gida ba ko akwai Wanda ze rakani>SIHIRTACCIYA Littafi Na Biyu 2 part D . Lokacin da suka shiga cikin gidan sai matar nan ta Samar tace yakai wannan bako namu kasani sunan wannan garin JAMHU mun kasance muna bautawa wata tsohuwar rijiya ne kuma akwai wata aljana acikin rijiyar mai suna TSAMURA ita wannan aljana duk shekara sai an kai mata mutum biyu saurayi da budurwa tasha jinin su to shine zamu samu albarkar shekara in ko muka ki bata to masifu da bala o i ne zasu dinga kunno mana na rashi ruwa ciwuwwuka mace mace tabbas munyi imani da aljana Tsamura dari bisa dari domin duk wata bukata to a wurin ta muke nema boka LAMAMU shine shugaban bautan wannan rijiyar kuma shine mai karbo sako daga gurin aljana Tsamura yazo ya gaya mana kuma duk shekara shine zai ce aljana tsamura tace akai mata wane da wance bawai ina karyata aljana tsamura bane Aa ni ina shakkane akan cewa boka lamamu duk shekara yana zaben son ransa ne kawai ya mikawa aljana ta shanye jininsa. Yarima samar yace me yasa kike zargin Boka lamamu da son zuciya matar nan tace boka lamamu ya dade yana so yayi lalata dani amma naki bashi hadin kai wannan ne yasa wata shekara ya bada sunan kannena mace da namiji amatsayin wanda za atsotse wa jininsu sai da akayi shekara uku yana bada yan uwana yau kuma gashi ya bada suna yayana guda biyu ta fashe da kuka tace tabbas wannan ba tsarin abin bauta bane kawai Boka lamamu ne kemin ramukon gayya duk shekara Samar yayi murmushi yace to yanzu wani taimako zanyi muku tace nidai so nake rayuwar yarana su tsira samar yace to idan ko hakane ya zama dole in kashe aljana Tsamura matar nan ta kwarara ihu tace karyane kai bazaka iya ba kuma ma duk duniya babu wanda zai iya yaki da ita. Domin wata shekara an taba ambaton yar sarkin garin nan amatsayin wanda za aba aljana tasha jini sarki yayi tsalle ya dire ya hana runduna ta jarumai da mayaka ya aika dan aje a yaki aljanar nan amma an kasa domin fitowa tayi arijiyar gaba daya tayi kaca kaca da kowa ta kuma koma rijiyarta kuma a shekarar nan mun dandana azaba da masifu kala kala lallai ko yaki aka zo mana ya kasance anfi karfin mu to komai yawan tarin runduna to ita kadai take watsar dasu tabbas ta gundire mune kawai dalilin kashe mana yara da takeyi ta hanyar shanye jinin su Samar yace yau shene za a kaisu ga wannan aljana azzaluma tace gobe Samar yace ina tabbatar miki yayanki sam baza su mutuba ta buda baki zatayi magana yace kar kice min komai lallai ki saurari gobe lissafi zaicanza daga gobe kawai kibani wurin kwana ta nuna masa gurin kwanciya Washe gari gaba daya gari ya tashi da kide kide da wake wake akayi wa yara wanka aka caba musu ado sannan aka nufi bakin rijiya dasu aka tsaida su agabanta sannan aka cigaba da kide kide yara sai rusa kuka sukeyi ita mahaifiyarsu tana can gefe tana sharba kuka kwatsam sai wani hannu ya fito daga rijiyar ya kama wuyan macen zai murde Samar yayi fitar burgu ya zare takobi ya zabgawa hannun sara take hannu ya guntule akayi wani mummunan kara daga cikin rijiyar jama'a suka rude suka kama guje guje aljana tayi yo sama ta fito afusace daga cikin rijiyar wata doguwar aljanace mai matukar tsawo ga wani karamin kai kamar gwan gwani tana da hannaye shida kuma akwai kaho atsakiyar kanta ta kalli hannunta da Samar ya sare take hannu ya koma dungulmi sannan ta kama kumbura tayi wani fadi tana cika tana batsewa sai ta takarkare ta kwarara wani uban ihu ta dubi Yarima Samar tace lallai yaro ka debo ruwan dafa kanka tabbas sai nayi gunduwa gunduwa dakai. Samar ya kece da dariya yace tabbas kin dade kina karo da maza suna shan kashi ahannunki amma yanzu lissafi ya canza domin yau kece zaki kwashi kashinki ahannu tayi kururuwa ta bude bakinta harshenta ya fito yayi dogo kamar maciji yaje ya shakewa Samar wuya idanun Samar suka zazzaro numfashinsa na kokarin tsayawa yasa takobi ya sare harshen kafira sai yaji kamar ya sari dutse yayar da takobinsa ya dauko wata karamar wuka adamararsa baki kirin ya yanke harshen kafura zafi da radadi ya shige ta tayi kara afusace ta zare takobi tayi kan Samar shima yayi kururuwa ya dau takobinsa ya karci kasa yayi kanta za ai ragab mugun gamo haduwa mafi hadari da firgitarwa. . Lokacin da akayi taho mugama tsakanin Samar da aljana sukayi wani mummunan gamo sukayi karan batta wani miyataccen kara ya tashi suka sarke da masifaffen yaki mai tsanani suka shiga musayar takubba guri yayi guri kura tayi sama tabbas karo da aljani badadi amma tabbas Samar yakara kwazo domin sai da ya rikitata ta rude Samar ya shiga sauke mata luguden sara da suka take ya yanke mata hannu daya tayi kururuwa tasa kafa ta makeshi tayi wuf ta cafki wuyan Samar tayi wuji wuji dashi ta maka da kasa yayi yunkurin tashi tasa kafa tayi kwallo dashi yaje yabigi wata katuwar bishiya take bishiyar ta karye kansa ya fashe bayansa ya makale ya kasa mikewa ya daki kasa ya ciji lebe hawaye ya zubo a idanunsa aljana tayi girgiza hannun da Samar ya sare ta kece da dariya ta nuna Yarima Samar tace wane mutum wane aljan aljanu ma sun buga dani sun barni yau shekarata Dari uku ina matsayin abin bauta na wannan kasa amma rana daya kace zaka yakeni wanene kai baka isa ba. Ta sheko aguje da niyyar tayi masa kwaf daya Samar yakama sumbatu yana surkulle yana karanta kalaman siddabaru take wani masifaffen karfi yazo masa yaji kamar zai iya yakar duniya tana zuwa daf dashi yayi wuf ya shaki wuyanta ya matseta gam tayi ruri saboda tsananin zafi ya tattara karfinsa ya murda kan kafura ya tsige kan yasa kafa ya banke gangar jikin ya fada rijiya yasa kafa ya take kan take kan ya tarwatse yayi wani surkulle take rijiyar takama da wuta takone kurmus da gudu matar nan ta rugo da gudu ita da yayanta suka rungume Samar suna masa godiya daukacin jama'ar garin sun taru suna yiwa Samar godiya dama wannan kazamar bauta ya damesu suka nemi da ya zauna dasu Samar yace akwai abinda ya raboshi da gida yayi musu bankwana ya kara gaba. Al amarin Boka Balbuna da rundunarsa kuwa suna keta dazuzzuka da kwazazzabo sai suka ji an daka musu tsawa take suka tsaya sai wani Mutum ya bayyana kamarsa daya da Boka Balbuna koda sukayi ido biyu sai suka ruga da gudu suka rungume juna sai da suka dau lokaci mai tsawo sannan suka rabu da juna Boka Balbuna ya dubi bakon yace yakai dan uwana Balduna ina kashiga tsawon shekara biyu ba labarinka Balduna yace tabbas nayi nisan kiwo domin na tafi Birnin Alkarmar binnin mafiya yawan jama'ar duniya kuma acan ne sarauniyar kyau na duniya take tabbas na kamu da sonta amma tasa gasa cewa duk mutumin da ya raba Yarima Samar da takobinsa yakai mata to shine zai zamo mijin Sarauniya Lubiya mai sarautar kyawawan duniya Boka Balbuna yace gaskiya dan uwana ka dauko aiki kuma kana bukatar taimakona wajen ganin mu hada karfi da karfe don raba Yarima Samar da takobinsa gashi ni kuma nay niyyar nemo bakin ruwa dan tayar da Sihirtacce wato Boka karibu bni kalab. Koda Balbuna yaji burin dan uwansa sai ya kece da dariya yace to ai wahalar banza kakeyi domin da zarar Yarima Samar ya samo Ruwan waraka daga rijiyar baroki dake Darul sabah ya yayya fawa Sihirtacciya to da zarar ta tashi ba makawa shima Boka karibu bn Kalab zai tashi kaga kai baka da bukatar samo bakin ruwa koda boka balbuna yaji wannan zance sai ya kece da dariya sannan yakara rungume dan uwansa sannan yayi rantsuwa cewa ko zai rasa rayuwarsa to sai ya taimaki dan uwansa wajen ganin ya sami gimbiya Lubiya Boka Balduna yace na gode dan uwa amma kasani akwai manya manyan jaruman duniya da manyan matsafa da suke burin auren gimbiya Lubiya saboda haka sun watsu aduniya suna neman Yarima samar don su rabashi da takobinsa Boka Balbuna yace tabbas raba Yarima Samar da takobinsa tamkar raba Zakanya ne da danta Al amarin yarima Samar kuwa nagajiSIHIRTACCIYA Littafi Na Biyu 2 part e Al amarin yarima Samar kuwa yana tafe cikin sassarfa akan dokinsa kwatsam sai yaji an nannadeshi acikin ragar karfe kuma aka rataye asaman wata katuwar bishiya kawai sai wasu murda murdan katti suka bayyana akalla sunkai su dari suka kewaye bishiyar suna kyakyata dariya tsit sukayi sakamakon bayyanar shugabansu ya dubesu yace dakyau yarana kunga mun samu takobin Jaruma Sarbila a saukake yasa hannu ya dauki takobin da dama ya fadi akasa yayin da tarko ya kamashi kawai sai yace da yaransa tunda mun samu abin harin mu kawai muyi gaba koda Samar yaga sun juya zasu tafi sai ya takarkare ya kwarara ihu ya kumbura yayi gunji take ragar karfen ya kekkece yarima Samar yadiro kamar wani zaki yana wani gurnani tamkar damisa mai yaya idanunsa suka kada sukayi jajur yana kumbura yana sacewa tamkar aljani ya takarkare ya daka musu tsawa tabbas duk da suma jarumaine sai da suka razana amma sai suka dake sannan suka gyara tsayuwarsu yarima samar ya irgasu yace tabbas ku dari da dayane amma ko daya daga cikin ku babu wanda zai rayu shugaban dakarun nan ya kece da dariya yace tomu gwabza mugani waye zai mutu kuma waye zai rayu sukayi kansa afusace suna wani ihu mai ban tsoro ko motsi YARIMA SAMAR BAIYIBA yana tsaye kikam kamar ice sai da ya gyara tsayuwarsa ya dunkule hannayensa ya fara wani huci kamar wani kumurci. . Lokacin da Samar ya tunzura ya gama fusata yakai makura afushi sai yazaro wata yar karamar wuka ya tunkari kattin nan suma afusace suka nufo shi suna haduwa akayi karan batar uwar bare ya suke mutum biyu yasa kafa ya make shida lokaci guda baki daya ba wanda ya motsa ya shiga cikinsu afusace yayi zarya atsakaninsu da wasu miyagun soke soke tuni sai ga fiye da rabinsu akasa kwance ba wani mai amfani saura ba sufi arba inba suka tsorata suka jada baya Samar ya kallesu yayi dariya yace kai ya kuke jada bayane kodai ku matayene ransu ya baci jin an kirasu da mata sukayi kansa da wata irin zuciya kakkarfa nanfa aka yamutse ai banban goro sai magofin karfe tuni yarima samar ya sadasu da makomarsu saura babbansu Samar ya dubeshi yace To yaro gashi yanzu ka rasa jama'arka zaka bani Takobina ne ko sai mun gwabza yaki katon nan ya kafe takobin akasa yace yallabai ga takobin ka. Sai da yarima samar ya saki jiki zai dauka sai yaji wani shararren naushi afuskar shi sai da ya tashi sama sannan ya baje akasa bakinsa ya fashe katon nan ya fashe da dariya ya nuna yarima Samar da yatsa yace kai wawa me kadaukeni in samu takobin Gimbiya Sarbila sihirtacciya shine zamu kama ta cikin sauki lallai kayi kuskure ai dole ne sai mun goga sai munyi yar kashi dakai yarima Samar ya tashi yayi wani Girgiza Afusace ya sheko da gudu shima katon ya fallo afusace suka daka tsalle suka hadu asama ai tun asama labari yasha banban domin tuni Samar ya sossoki katon nan sau sama da arba in aduk sassan jikin katon nan suna dirowa Yarima samar ya dire shiko katon ya baje akasa yana kakarin mutuwa ko kallonsa yarima Samar baiyiba ya dauki takobinsa zai wuce sai katon mutumin nan yakira Sunansa Samar ya juya ya kalleshi mutumin yayi murmushin karfin hali alokacin yana gargaran mutuwa dakyar yabude baki yace da Yarima Samar sam bazaka zauna lafiya ba matukar kana rike da wannan takobi to ka zama abin farautar Sarakunan duniya da Jarumai da bokaye sai ya mutu Yarima Samar yana mamaki ya cigaba da tafiya yana keta daji sai ya isa wasu manya manyan duwatsu guda biyu makotan juna ya ratsa ta tsakiyar dutsan nan yawuce sai da ya kusa fita atsakanin duwatsun nan sai yaji saukan wani guduma akansa take kansa yayi girim duniya ta fara juya masa tun yana gani dishi dishi har ganinsa ya dauke numfashinsa ya tsaya cak ya kame kamar gunki ya fadi kasa tamkar gawa. Boka balbuna da dan uwansa Balduna sun iso gunda Yarima Samar ya fafata yaki da kattin nan sukaga kattin nan akwarkwance matattu sai Balbuna yace yakai dan uwana kasani lallai Yarima samar yana kusa tabbas bayyi nisaba Shine ya kashe duk mutanen nan kuma bai dade da kashe suba Balduna ya durkusa ya debi kasa ya watsa ya kura mata ido iska ta debi wani yanki na kasar tayi kudu da ita Balduna yace tabbas kudu yayi taho mubi bayansa lallai burin mu nadaf da cika suka sa gabansu kudu suna tafiya cikin sauri domin su riski yarima Samar suna tafe sai suka iso manyan duwatsun nan guda biyu sai Boka balbuna yace mu dakata anan domin nayi binkice gameda wadannan duwatsu lallai ban yarda da suba ta yuwu akwai wani hadari aciki take ya sabi wasu zantuttuka yana wasu sambatu ya sassarka sarkakkun kalmomin tsafi can sai wani bakin hayaki ya tashi yayi sama Boka balbuna yazazzaro idanu yayi dogon numfashi ya girgiza kai Balduna yace yakai dan uwana me kagani acikin wannan tagwayen duwatsu Boka Balbuna yace da matsala tabbas da matsala lallai Yarima Samar yana cikin wadannan duwatsun kuma shima yana cikin hadari domin akwai wani mugun abu atsakanin duwatsun nan kuma yana da matukar hadari domin na kasa gane iya girman lamarinsa Balduna yace to menene abinyi Boka balbuna yace ya zama dole mu fuskanci duwatsun amma fa zamu kasance ne atsakanin SIHRTACCIYA Littafi Na Biyu 2 part F . Lokacin da Boka balduna da dan uwansa suka tunkari tagwayen duwatsun sai suka kasance cikin shiri kuma suka kasance da dari dari sai da sukazo tsakiyar duwatsun sai sukayi kicibis mugun gamo wasu sharba sharban maridai ne masu cin naman mutane suke fitowa daga lungunan duwatsun nan da daya da daya sai da maridan nan sukayi fiye da dubu daya sukasa Boka balbuna da dan uwansa atsakiya sai muzurai sukeyi tabbas mutanen nan ba su da kyan gani ga tsawo ga girma ga fadi Boka balbuna ya daka musu tsawa yace kai lalatattu masu cin naman yan uwansu kusani bagurinku muzoba saboda haka karfa ku jamu da fada lallai zakuyi dana sani Shugaban mariddan nan ya kyal kyale da dariya sai da ta isheshi sannan ya daure fuska alokaci guda ya turbune fuska ya nuna balbuna da yatsa yace kai karamin halitta kasani kashigo tarkon mu kai da dan uwanka kuma sam bazaku tsiraba ran boka Balduna yabaci ya kwara ihu ya sabi wasu kalaman surkulle ya kama jujjuya hannunsa take wata wuta takama guri guda ya daki wutar tayi kan maridan nan take shima shugaban mariddan yayi kolo kolo yayi sambatu irin na matsafa ya nuna wutar take wutar ta mutu nanfa suka shiga musayar tsafi sukayi wa juna kaca kaca suka koma bakake sidik saboda tsananin bala i kai tsafi gaskiyar mai shi sai wannan ya turo kura wancan sai ya turo zaki ya gama da ita kai koda suka ga karfin tsafinsu yazo daya sai suka jada baya sukayi kururuwa suka falfalo aguje kowanne takobinsa azare suka kacame da yaki tofa ai sai sauran maridan nan suma suka zare makamai suka afkawa rundunar boka Balbuna tashin hankali wanda ba asa masa rana yaki yarin cabe masifa tayi masifa. . Babban tashin hakali awannan yaki shine kaifi da tsini sam baya tasiri ajikin Maridan nan amma kuma su sai kashe mazaje sukeyi take sukayi wa jaruman Boka Balbuna kan kace ahaka sun karar da

Chapter 4 of 5