Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
tunkari hanyar ma unnaru wani wawan tsawa aka daka masa boka karibu yayi duba ga mai yi masa tsawan sai yaga wani basamuden aljanine aljanin yace kai bil adama ka tsaya a matsayin ka lallai bamu da niyyar kashe ka amma in ka kara taku daya kai gaba ba baya ba lallai yau zaka mutu boka karibu ya dubi aljanin ya kece da dariya yace kai maigadi lallai kasani yaro ake wa umurni yabi amma uban gida sai dai ya baza iko. Ya nuna aljanin da dan yatsa yace to kasani koda kakan ku ifritu minal jinni zaizo nan to bai isa yasa in juya da baya ba lallai tunda nazo nan babu wani mahalukin da ya isa mutum ko aljan ya hanani diban ruwan nan lallai in kukace zaku dakatar dani to mutuwa ce zata yanke hukunci tsakanin nidaku aljani ya kwarara ihu yayi umurni da a afkawa Boka karibu . Lokacin da wani yanki na aljanu sukayi kan Boka Karibu sai yayi girgiza take ya rikide ya zama wani basamuden dodo ya mika hannu sama sai wani mahaukaciyar guduma ta bayyana a hannunsa yayi kansu a fusace har wani aman wuta yakeyi take ya zamar wa aljanun nan alakakai ya shiga shirga musu guduma duk wanda ya daka ya tashi daga aiki kenan domin tarwatsewa yakeyi aljanun nan hankalinsu ya tashi suka kara zage dantse suka zagaye shi suna kokarin su masa kofar rago koda boka karibu ya fahimci haka sai yayi wani gurnani sannan ya bude bakinsa take wata wuta zazzafar wuta ta futo a bakin sa tayi wa aljanun nan kurmus. Turkashi gaba da gaban ta aljani ya taka wuta nanfa aljanu suka sha jinin jikinsu katon aljanin nan da ya masa tsawa a farko ya dubi boka karibu ya kece da dariya yace lallai ka cika shu'umi amma zaka san kazo gidan iyayen ka kafin Boka karibu yace wani abu tuni komai da komai na wurin ya bace ya dawo tantagarya sahara boka karibu ya dawo siffarsa na asali ya fara dube dube yana waige waige kawai sai yaji an kwashe da dariya ba kakkautawa tsit akayi shiru kawai yaji An tabka masa sara jini yayi tsartuwa ya waiga a fusace sai yaga wani aljani ya nutse acikin yashi boka karibu yaje gurin amma baiga ko wani alama ba kamar fitar kibiya wasu bakaken aljanu kimanin su arba in suka fito daga cikin karkashin kasa. Suka kewaye shi suka afka masa da sara da suka yaki mai tsanani ya kullu atsakaninsu tabbas aljanu ne masu taurin rai domin sun dauki tsawon sa a uku suna kafsa yaki amma ya kasayi wa ko daya kwarzane haka suma sun kasayi masa komai saboda tsananin naci sai da suka gajiyar da shi lilis sannan suka daka tsalle suna dira sai sunutse acikin kasa Boka karibu ya kama waige waige yana haki kamar kibiya haka wasu aljanun suka kara futowa daga karkashin kasa suka farwa Boka karibu da azababben yaki wannan karon sai da aljanun nan sukayi wa boka karibu yanka har uku ganin haka ransa ya baci ya takarkare ya kwarara ihu ya far musu da sara da suka. Kafin kace haka ya kashe aljanu uku koda aljanun nan suka ga haka sai suka nutse acikin a yashi ran yan maza ya baci yayi wani muni ya kumbura ya kara tsawo ya koma kamar wani dodo sai ya kama kirari saini boka karibu bn kalab in sha jini in barwa yaro fata tsafi gado nane mugunta ajini nane saini azzalumi dan azzalumai wane yaro kuma wane uban yaro sai ya kurma ihu ya daka tsalle yayi alkafira sai ya nutse acikin kasa waiyo bala i ya auku ai sai karafkiya da karar mazaje kakeji haka kawuna da kafafuwan aljanu suka yo waje gunduwa gunduwa daga karkashin kasa tabbas yau aljani ya taka wuta sai tsalle acikin kankanin lokaci boka karibu yayi kaca kaca da aljanun dake karkashin kasa sai gashi ya bayyana a saman sahara kai in ka kalle shi sau daya bazaka sake son kallon sabaSIHIRTACCIYA . Littafi Na Biyu 2 part B . Lokacin da Boka karibu bn kalab ya bayyana a sararin sahara sai ya takarkare ya kwarara ihu yayi girgiza wani kura ya tashi yayi wani surkulle wani gora cike da da ruwa ya bayyana ahannunsa yak kwarara ruwan akansa ya girgiza kansa yana samun natsuwa sai yayi arba da wani makeke gida ginin dutse da dutse sai yaji wata kakkausar murya tana cewa dakyau abokina lallai kayi kokari amma kasani wannan gida shine wahalarka ta karshe domin wannnan ruwan ma unnar yana cikin wannan gidan saboda haka ka shige shi kasani tsagwaron karfi da tsafi bazai fitar da kai awannan tsinannen gidan ba dole sai kayi amfani da ilimi da basira da kuma lura kai tsaye Boka karibu ya tunkari gidan dutse babu fargaba ba tsoro tafiyane na a mutu ko ayi rai. Al amarin Sarbila kuwa lokacin data farfado sai ta mike tasa mabudin kofar karshe ta bude kofa tana budewa sai tayi arba da bakar damisa a tsaye a bakin kofar tabbas babu wata hanya da zata iya wucewa face ta gwabza fada da bakar damisar kawai sai ta jada baya taku uku sannan ta sheko aguje ta afkawa damisar nan suka kacame da fada damisar tayi wa Sarbila mugayen rauni har guda Uku ita kuma tayi nasarar karye wa damisar wuya tilas tazube akasa tanaji tana gani Sarbila ta wuce Sabila na shiga sai ta tsinci kanta awani wawakeke kogo ga fadi ga zurfi sai taji muryar bokanya alimma tana cewa tabbas aikin ki yazo karshe domin awannan kogon ne zaki samu takobin tarihi wanda da itane zaki iya kashe babban makiyinki Boka karibu bn kalab amma kisani zaki sha azabar da baki shaba abaya lallai kishirya shirin tunkarar mutuwa ko rayuwa . Lokacin da Sarbila ta tsinci kanta awannan wawakeken kogo sai taci gaba da tafya tana tafiyane anatse tare da shiri ko ta kwana sai ta riski wasu hanyoyi guda uku kowacce hanya anyi rubutu akan allo ankafe ahanya ta farko an rubuta ya mai tafiya wannan hanyar in ka bita lallai zaka sadu da arziki mai tarin yawa hanya ta biyu an rubuta ya kai mai tafiya idan kabi wannan hanyar to zaka riski ajalinka hanya ta uku an rubuta ya kai mai tafiya shin kana bukatar samun sarauniyar kyau ko sarkin kyawawa na samari kabi wannan hanya. Sarbila tayi nazarin wadannan rubutun tace nidai banzo nan da niyyar samun dukiya ba sai tace haka kuma kwata kwata ban shirya yin aure ba sannan bana bukatar mutuwa ayanzu har sai na cika burina ta rasa hanyar da ya kamata tabi can sai tayi dogon tunani tace ance hanya ta biyu zan riski ajalina to idan na gagari mutuwar akarshe dole akwai wani abu da zan samo kai tsaye ta danna kai hanya ta biyu sai taji wata murya tana cewa tashirya mutuwa masheka kushirya shirin aikata kiyama. Kawai sai taji wani shuuu abayanta tana waigawa sai taga wasu kibiyoyi sama da guda dubu sun nufota bata da zabi dole tasa gudu suka kasa tsere da kibyoyin nan abin mamaki ko tayi kwana sai kibiyoyin suma sunyi kwana sai da ta shafe sa a uku tana tika gudu amma kibiyoyin nan na biye da ita atsiyace ta tabbatar in zata shekara tana gudu baza su daina binta ba gashi kuma haki na neman yaci karfinta take taja ta tsaya ta fuskanci kibiyoyin nan ta zaro wani dogon mashi tana jiran zuwan kibiyoyin nan suna karasowa sai ta shiga karkade su suna faduwa kasa abin mamaki indai bata daki kibiyar ba toko kibiyar bazata fadi kasaba tana nan tana kokarin neman Sarbila. Sai da ta dauki lokaci mai tsawo sannan tayi nasarar karkade kibyoyin nan duk da haka sai da wasu suka soketa sun kuma yi mata munanan raunika sarbila ta durkusa ta zare kibiyoyi uku ajikinta jini ya tsartuwa dakyar tayiwa kanta magani sai ta baje akasa ai tana kwance sai taji ana shawagi akanta ta kyalla ido sama sai taga wasu maka makan angulaye ne ke shawagi asamanta tayi zumbur ta mike ai kamar suna jiran mikewarta sai suka afka mata wai zasu cinyeta da ranta dakyar ta samu damar ciro makami suka shiga bata kashi sai da angulayen nan sukayi mata fata fata amma tayi nasarar kashesu gaba daya ta durkushe tasa guiwarta akasa. Ana wata ga wata sai ta hangi wata ruduna na mzaje sun tunkarota da muggan makamai ta rintse idanunta ta bude ta girgiza kanta tace ance in aski in yazo gaban goshi zafi gareshi tabbas gaskiyane sai ta ware baki tayi kururuwa gami da karajin fusata tazaro wasu takubba ta mike ta shiga aguje ta afkawa mazanjen nan dayakin mutuwa. Ko sau daya bata ba wo wani damar ya sare ta ba duk lokacin da ta kai sara to bata kuskurewa rayuka kawai take dauka cikin dakika kadan takarar da mazajen nan ta kwarara ihu ta zama kamar mahakaciya tayi cikin kogon agoje ba mutum ba ko aljan ya sha mata gaba sai ta rabashi gida biyu ahaka tazo gaban wani katon tebur sai taga wata jar takobi wanda har wani mele mele takeyi tabbas itace takobin tarihi ta tunkareta sai nau'in aljanu da miyagun dabbobi da shu uman mutane da tsuntsaye kai har da iska da ruwa suka shiga fuskantar ta amma sarbila take kashesu tamkar dutse take jinta ita kanta sarbila ta mance kanta sam bata tsoron mutuwa yaki take ba tare da tasan me take yaka ba ita abinda take hange kuma take iya gani itace takobin tarihi saboda haka duk abinda yasha gabanta to kwanansane ya kare. Lokacin da Sarbila tayi nasarar sa hannunta ta dauki Wukar tarihi bata san wukar tana tsakiyar narkakkakiya ruwan dalma bane sai da ta jefa hannunta sannan taji wani bala in masifaffen zafi kamar na fitar rai amma saboda tsananin kafewa da jarumta sai da ta dauko takobin tana daukowa gaba daya halittun suka bace ita ko sai tayi maza ta daure wukar a damarrarta sannan tafal falo aguje ta nufi kofar fita kamar ana jiranta kawai sai kogon ya shiga rushewa duk inda sarbila tasa kafa ta cire take gurin zai burma gudu takeyi kamar ranta zai fita sai taji an tattarata an watsota waje tayi koli koli ta fado cikin dajin ikbal tana kallon kogon yana narkewa ta shafa wukar taji ta tana nan take sarbila ta suma saboda tsananin wahala . Al amarin boka karibu kuwa gadan gadan ya tunkari gidan nan ya tadda kofar arufe ya takura ya tara jini ya kumbura yasa kafa ya banke kofar take kofar ta babbake ta sama ta fadi wani yanki na gidan ya kama rugujewa kai tsaye ya fada cikin gidan yana shiga sai ya tarar gidane lungu lungu sako sako ya fuskanci wani lungu yayi tafiya mai nisa sai yaga wani matattakala yayi sama ya tunkari matattakalar nan yana zuwa ya fara hawa ya taka matattakalan farko yawuce ya taka na biyu ya wuce a na biyun sai matattakalar ya kauce aiko sai Boka karibu yayi cikin wani wawakeken rami sai tafiya yake ba alamar zai kai karshen ramin tun yana ganin haske har ya daina ganin haske tun yana numfashi har ya fara jin iskar tana masa kadan. Daga kasa kuma wani masifaffen zafine keyowa sama Boka karibu yayi duba zuwa kasan ramin sai ya hango wuta gagga gagga tayo sama tabbas yana gab da halaka tuni ya kama kalaman tsafi gami da surkulle yayi tsatsuba gami da kalaman surkulle take wata kakkarfar igiya ta zuraro ramin daga sama caraf ya kama igiyar ya fara yowa sama da masiffen sauri haka itama wutar tayo kansa sukasa tsere tirkashi lallai wuya badadi da masifaffen gudu ya karaso bakin ramin yayi tsalle ya fito yana fita wata dunkulalliyar wuta tayi waje. Boka karibu ya kece da dariya yace lallai na shigo shu umin gida sannan ya koma yayi nazarin matattakalar nan sai yayi murmushi kawai sai ya kama hawa in ya taka na farko to bazai taka na biyu ba in ya taka na uku to sai ya tsallake na hudu da na biyar ahaka yawuce ya isa wani fili wanda aka kawatashi da kayan alatu ga kujeru luntsuma luntsuma an ajiye abinci kala kala Boka karibu yayi murmushi kawai sai ya wuce kayan dadin nan kaaaaaiii yaji an daka masa tsawa yayi duba ga mai yi masa tsawar nan sai yaga wani narkeken kato rike da takobi yace wa Boka karibu idan kanaso kawuce lafiya to dole sai kaci wani abu daga abubuwan dake cikin wannan falo Boka karibu yace to bana bukata katon nan yace to lallai kuwa zaka mutu boka karibu ya zare takobi yace wa katon nan taho mu gwabza suka runtumo aguje akayi haduwar gwanaye Yaki ya sarke atsakaninsu mai tsanani tamkar zasu kashe kansu tabbas karfi yazo daya saida suka shafe sama da sa a bakwai babu wanda yayi nasarar yankar wani kai koda Boka karibu yaga wankin hula zai kai shi dare sai ya canza salon yaki ya shiga yin tsalle gamida alkafura yana kai yanka ta sama ta kasa ai nan take lissafi ya canza tuni yayi wa katon nan fata fata kankace haka ya sare masa hannaye guda biyu ya baje akasa kawai sai boka karibu yayi gaba ya barshi akwance yana tafe sai ya tarar hanya ta kare sai ya juya zai koma da baya kikam nan ma sai yaga kofa tarufe nanfa hankalinsa ya tashi yafara surkulle gamida tsatsube tsatsube yayi gumi yayi sharkaf amma bai samu kofa ba sai ya koma ya kalli gaba yayi nazarin gunkin dake gabansa ya tabbatar dole akwai kofa ajikin katon gunkin daya toshe masa hanya kuma lallai zayui ya zama daya daga cikin sassan gunkin nan ne zai zama mabudin kofar take ya kama hannun gunkin. Caraf gunkin ya rike hannunsa ya matse shi gam tsananin zafi da zugi boka karibu ya fasa ihu sai dakyar aka sakeshi ya kara kurawa gunkin ido nanfa yashi ga rudani ya rasa inda zai taba ajikin gunkin nan yayi kumaji ya cafki nonon gunkin nan haba ai sai yaji an rufeshi da duka ko ta ina bakakkautawa sai da akayi masa lilis aka hada masa jini da majina sannan aka rabu dashi. Wata kakkausar murya tana cewa kayi kuskure na karshe muddin ka sake lallai zaka halaka Boka karibu bn kalab ya natsu yayi nazarin gunki sosai kawai sai yayi kundun bala ya damki cibiyar gunkin take yaji wani kara sai kofa tabude ya kunna kai ciki nan yayi arba da rijiyar ma unnar take ya nufeta gadan gadan nanfa kwankwamai suka taso masa da mugun nufi inda shi kuma ya haukace sai girbesu yake yi anyi bakin artabu kuma anyi mummunan arangama domin sai da aljanu suka karya boka karibu amma saboda naci da juriya bai tsaya ba sai da ya dangana da bakin rijiyar ya dauki gugan karfe ya zura arijiyar aljanu suka yanyame shi amma sai da ya jawo ruwan suna dukansa suna yankansa sai da ya dura ruwan a wani gora ai yana durawa sai gaba daya aljanun nan suka kama da wuta gidan ya kama girgiza zai rushe duk da karayar kafansa in kaga gudun da yakeyi sai ka dauka aljanine yana fita gidan ya rufta kasa ya nutse take boka karibu ya suma. Acan kasar Manohar kuwa tun saura wata guda jama'a suke bulbulowa daga sassan duniya guri ya cika ya batse take kasuwan duni ta wanzu agurin mutane harda aljanu sunata halarta kasar Manohar dandazon taron mutane afilin gasar sun cika ko ina ba masaka tsinke kowa yana ta harkansa sai akaji wani tsawa gamida rugugi jama'a suka samu natsuwa aka mai da hankali inda tsawar ke fitowa kura tayi sama ba a iya ganin komai sannu ahankali kurar ta yaye sai ya bayyana Boka karibu bn kalab yana bisa wani toron giwa yana sanye da rigar fatar damisa yana rataye da wata zabgegiyar takobi sannan ya makale wani kuttu akugunsa Take fili ya fashe da ihu da shewa da tafi Boka karibu yana cika yana batsewa sai kumbura yake yana fashewa tirkashi har tsakiyar filin gasar giwan nan ya kawoshi yayi tsalle gami da katantanwa sannan ya dire atsakiyar fili yan kallo suka dau ihu da tafi suko mutanen kasar manohar sai suka shiga cikin damuwa ganin Boka karibu ya dawo babu duriyar Sarbila hankalin dan uwanta Sarbilu yafi na kowa tashi inda ya kama zirga zirga yana kaiwa yana komowa shi ko Sarkin kasar manohar wato yayun Sarbilu da Sarbila tuni ya fara kukan zuci yana tunanin in har Sarbila bata dawo ba to lallai zasu fuskanci wulakanci na karshe awurin Boka Karibu bn kalab Kawai sai boka karibu ya takarkare ya kwarara ihu mai firgitarwa wanda sai da mutane suka fara guje guje yakara tsaga ihu take jama'a suka shiga taitayinsu yakama kirari sai ni boka karibu Dan mai dole in sha jini inbarwa yaro fata wane mutun wane aljan ni bakar fura dakar iblisai yaro ya shani ya kwana kiyama ni tuwon tulu mai wuyar kwasa ya kara tsandara ihu sannan ya nuna inda jama'ar kasar Manuhar ke zaune yace ku gayyar matsiyata lallai kusani baku da tabbacin cewa yar uwanku zata dawo to koma ta dawo lallai zan kasheta in kifar da kasar ku lallai sai an rubuta tarihin rushewar kasar ku tabbas duk wani mai rai akasar Manuhar ba mutum ba aljan koda kwaro ko dabba to sai ya dandani azabata lallai sai na muku azaba kala dari sannan kowannenku sai na kasheshi sau dari da sannu zaku san yar uwanku ta jawo muku bala'i da masifa mara adadi. Kaiiiiiii Sarbilu ya dakawa boka Karibu tsawa yace kai mahaukaci ka saurara dakyau shin bakaji karan takun tahowar mutuwar kaba to idan baka jiba ka saurara lallai ajalinka na tunkarar ka amma kai wawane baka gane ba kawai sai akaji kasa na girgiza jama'a suka kalli inda takun ke fitowa sai kawai aka hango Jaruma sarbila bisa wani kasurgumin namijin zaki tab di ai sai kallo yakoma sama ihu ya barke shewa shi kansa sarki Maridu sai da ya mike yarika tafawa yar uwansa inda jama'ar kasar manuhar sukasa wata waka mai tsananin dadi inda gaba daya filin baki daya na garin suka dauki wakar nan wohoho nanfa fili ya rikice Sarbilu sa yaruga aguje yaje ya rungumeta suka fashe da kukan murna jama'a suka ci gaba da raira waka ran boka karibu ya fara tafarfasa yana kuna ya cika ya batse wani dunkulin abu yazo ya tokare masa kirji kishi ya mamaye ruhinsa ya takarkare ya kwarara ihu mai razanarwa take guri yayi tsi masu waka suka daina masu kida suka jefar da ganguna masu rawa suka shiga taitayinsu na zaune ya mike na tsaye ya zauna sam babu natsuwa a zukatan al umma hatta manya manyan sarakuna dake wannan fili sai da suka firgita guri yayi tsit. Sarbila ta saki dan uwanta ta haye kan zakinta cikin takama da nuna isa da izza Zakin nan ya nufi filin gasa kai abin ya bada sha awa ta yadda jama'a sai suka sawa Zakin nan tafi tana isa tayi tsalle tayi katantanwa sau uku sannan ya dira agaban Boka karibu bn kala ta kalleshi sai ta fashe da dariya tace yaya har kishi ya kama kane ganin jama'a na rera min wakokin yabo to ai tsakanin nida kai akwai bambaci kai azzalumi ne ni kuma adalace kaga dole in kasance ni na jama'a ne Boka karibu ya daka mata tsawa yace ke yarinya ki fadi iya abin da zaki iya fada amma kisani a karshe mutuwa zakiyi ta daga murya tace kai bakin azzalumi kasani ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya lallai yau ce ranar ka ta karshe a duniya kamar sun hada baki suka jada baya taku bakwai sannan suka kwarara wani kururuwa mai figitarwa da suka zare makamai suka falfalo aguje za ai haduwar karshe wanda zai mutu ya mutu mai rabon ganin badi ya gani Zan Cigaba Insha Allah >SIHIRTACCIYA Littafi Na Biyu 2 part 3 . Lokacin da suka jada baya taku bakwai kamar an dakatar dasu sai suka tsaya cak sannan suka zare makamai kamar an busa musu usur sai suka falfalo da ma tsanancin gudu sai da suka kusa haduwa sannan suka daka tsalle suka hadu asama suka sarke da bala en en fada tabbas fadan ba kyan gani kuma yayi muni ga yan kallo sai da sukayi dakika dari biyu asama suna kafsa fada sannan suka diro kasa dole jama'a suka sa tafi domin kowannensu ya nuna bajintarsa Boka karibu bn kalab ya shiga jerawa Sarbila miyagun hare hare ita kuma tana karewa cikin zafin nama ahaka ya yanketa akafada da kuibin cikinta ta jada da baya tayi kamar zata fadi tayi ta maza ta jawo wani kyalle ta daure kuibin cikinta sannan ta kalli boka karibu tayi masa nuni da yazo ta shirya ya sheko aguje ya kawo mata wani wawan sara ta damki hannunsa ta shiga auna masa wasu mudikam naushi sai da yayi sama sannan ya fado kasa yayi kokarin yunkurawa amma ya makara tuni tayi kwallo da shi yaje ya bugi wani katon dirka yayi kara sannan a fusace ya mike ya kwarara ihu gamida kururuwa yayi kanta ahaukace Wani masfaffen sabon yaki ya fara tashin hankalin gaba daya yan kallo sun rude sun kidime tsoro ya kamasu tuni wasu sun kama kuka wasu sunyi hijira kai bala i lallai wannan yaki ya amsa sunansa fadan karshe domin gaba daya Sarbila da boka karibu sun yiwa junansu kaca kaca a dai dai wannan lokacin ne Boka karibu ya shammaci Sarbila ya watsa mata MA UNNAR ruwan wuta take sarbila taji jikinta yana wani sassandarewa tabbas akwai abinda ke shirin faruwa agareta shi ko boka karibu sai ya fara sheka dariya duk da jikin Sarbila ya fara canza kala zuwa kamannin gunki sai da tayi kukan kura tasa takobi ta sare hannun boka karibu wanda ke rike da kuttun MA UNNAR ruwan take hannun ya tsinke ya saki kuttun Sarbila ta cafe ta watsa masa ruwan boka karibu yayi kururuwa take shi da sarbila suka zama gumaka kowanne a kamannisa amma a matsayin gunki Gaba daya filin ya rude da ihu wasu suna kuka wasu na murna an rabasu da alakakai domin dama boka karibu ya gallabi duniya awannan taron aka nemi gunkin Boka karibu aka rasa bayan kowa ya watse sai aka daukin gunkin sarbila aka shigar dashi Garin manohar daga ranar aka canza abin bauta suka kama bautawa Gunkin sarbila shi kuma Sarbilu har ya mutu yana yiwa gunkin hidima har mutuwa ta rikeshi Samar ya karasa labarinsa da cewa wannan shine labarin SIHIRTACCIYA WATO MAKARBIYA KUMA JARUMA SARBILA. Majalisa tayi tsit can wani dattijo yace ya kai yarima samar yanzu yaya za ayi a tashi sihirtacciya samar yayi gyaran murya yace lallai hanya daya ce dole sai anje Darul sabah domin dibo wani ruwa a wata rijiya mai suna Baroki tabbas wannan ruwa babu sihirin da baya karyawa amma kusani masifa da bala in da suke hanyar zuwa Darul Sabah dai dai yake da ka tunkarar karanta littafin kudin tsatsuba kuma kusani idan mutum yayi nasarar zuwa darul Sabah to mutanen kasar zasu sa masa sharadi guda daya matukar mutum bai amince ba to komai jarumtar mutum da hatsabibanbcinsa sai dai ya hakura. Kuma kusani da zarar munyi nasarar tada Sihrtacciya to duk inda gunkin Boka karibu bn kalab yake to shima zai tashi gaba daya yan majalisa suka mike suka kurawa Yarima Samar kallon mahaukaci ganin zai taso masifar da bayan shekara dari bakwai da ya shude Yarima Samar yace yaku shuwagabannina ya zama dole agaremu mu tashi Sihirtacciya domin kwanaki casa in Sarki shaddadu ya bamu zai zo ya dauki sarauniyar mu Yazrina tabbas yafi karfinmu kuma kuna sane da matukar ya dauketa har ya kusance ta to masifa da bala'i zasu rufto mana saboda haka gobe zan dauki hanyar Darul Sabah lallai sai na tashi Sihirtacciya in cece mu . Gari na waye wa sai garin manohar yayi tajin jita jita ko ina ka shiga akasar sai kaji ana cece kuce wasu na cewa basu ga laifin Yarima Samar ba in yace zai shiga Jandaki wasu kuwa cewa sukeyi akan me zai bude dakin da yakai shekara dari bakwai arufe dakaru sun hau layi waziri ya dube su yace yaku dakarun kasar Manohar lallai ku tsaya tsayin daka ku hana Yarima Samar shiga wannan daki lallai masifa zata iya rufto mana sai wani barde mai suna Zaidu ya ware sannan yace ina tabbatar muku ni bazan yaki Yarima Samar ba kuma idan kakuce zaku yakeshi to ni zan goya masa baya take rundunar mayaka suka rabu biyu wasu suna bayan waziri wasu suna bayan Samar nanfa aka fara jan ido ana neman afar wa juna kai kai aka daka musu tsawa sukayi duba ga inda tsawar ta fito sai sukayi arba da Yarima Samar yana rike da wata sharbebiyar takobi sun jero da yar uwansa gimbiya Yaxrina suna tafe cikin takama da izza da nuna isa suka isa gurin dakarun nan yace akan me kuke neman ku yaki junanku bai dace ba. Magoya bayana na gode muku masu kokarin takamin birki mu zuba ya dubi sarauniya Yazrina yace muje ki bude min kofar inga mai burin mutuwa yasha gaban ki take ta wuce ta nufi jandaki wani da kare yasha gabanta samar yayi fatali da shi ya mai da wukansa cikin kufe ya murza hannunsa yace tabbas bazan kashe dan kasata ba amma in takama zan kakkarye shi nanfa suka shiga kokarin tsai da ita shi kuma yasa kafa ya banke wancan ya make wannan ya sunkuci mutum yayi watsi dashi da dakaru fulu fulu Akasa Yarima Samar ya kakkarye su dole kanwar naki suna ji suna gani Yazrina ta sanya mabudi tabude jandaki Yarima Samar yadubi jarumai yace duk wanda ya isa ya kuma cika namijin duniya to ya biyo mu ciki Ya kama hannun yar uwansa suka shige Jandaki suna shiga kofar tarufe tsananin duhu dake cikin jandaki sai da Yarima Samar da Yazrina suka firgita suka rungume juna sai sukaji kamar ana tahowa da sauri suka saki juna Samar yace yake yar uwata mene sirrin duhun nan tace tabbas haske zai bayyana amma bayan ka zayyano nasa barka ga dangin uba guda goma ba kuskure lallai idan ka fadi daya ba daidai ba to zamu halaka dakika biyu kawai ya rage mana ahalin yanzu muhalaka. Take samar ya kama fadar nasabarsa Nine SAMAR DAN SAFAR DAN BAHAR DAN BADAR DAN MARIDU DAN SAFFA'U DAN ZAFFAR DAN SAKIB DAN SAMRU DAN ZAMRA'U SAFARA'U. take haske ya gauraye dakin tirkashi ai sai sukayi arba da kayayyakin yaki kala kala iri daban daban Samar yabude baki yana kallo cikin mamaki da ajibi kuma wani abin mamaki kowane kayan yaki dake cikin dakin to akwai wani katon gunki a tsaye akan kayan yakin Sarauniya Yazrina tace ya kai dan uwana kasani duk kayan yakin daka gani a jandaki to kayane na tsofaffin dakarun mayakan kasar nan tsawon shekara dubu biyu duk wani jarumi da yayiwa kasar Manohar wani abin tarihi to bayan mutuwarsa a jandaki ake ajiye kayan yakinsa bayan mutuwarsa yace to yaya idan ina so in dauki kayan yakin. Sarauniya Yazrina ta zazzaro ido tace ya kai dan uwana kasani daukan kayan yakin wani jarumi acikin jandaki to dai dai yake da yaki da mai kayan lallai zaka

Chapter 3 of 5