Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
waje ba haka ma jama ar gari suna nan tsawon kwanaki shida baci ba sha sai addu a sukeyi Sarbila ta dubi dan uwanta tace ya zama dole in ziyarci bokanya Alimma dake tsaunin karkif domin samun wasu bayanai suka shirya suka futo sai sukayi arba da mutanen kasar baki daya sun taru a kofar fada kai tsaye zasu wuce sai sarki maridu ya mike yace yaku kannai na tabbbas mun yi laifi amma mun karbi laifin mu. . Kuma mun saduda tabbas kin nuna cewa kece birnin nan mu kuma mun tabbata hoto to kisani matukar kikace ba zaki kara kula mu ba to kamar yadda mukayi kwana shida a nan haka zamu cigaba da zama baci ba sha har mutuwa ta riskemu koda Sarbila taji zancen dan uwanta sai tayi murmushi tace lallai kun sami afuwa agareni na yafe muku tace yanzu zanje in ziyarci bokanya alimma domin karbo wasu bayanai kamar yadda Boka karibu bn Kalab ya nutsa a kogin nilu domin ganin aljani makus bn kwas domin ya karbi bayanai tabbas tsakanin ni da shi sai wani ya mutu a hadu ta gaba WAYE ZAI RAYU Zan Cigaba Insha Allah SIHIRTACCIYA Part 6 Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Abdul aziz sani m/gini. Typing... by Goni. Lokacin da boka karibu bn kalab ya nutse acikin kogin nilu sai da yayi tafiyar kwana biyu da wuni daya sannan ya isa wani katon gida duk da gidan acikin ruwa yake kwata kwata babu alamar ruwa a jikinsa boka karibu ya tsaya a bakin kofar gidan ya rufe idanunsa ya fara karanto wasu kalaman tsafi take kofar ta bude ya kunna kai cikin gidan tamkar gidan shi sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya isa wani katon fili sai akace masa maza ka zauna sai ya fara kokarin zama a bisa ciyawa abin mamaki lokacin da ya kai kasa sai ya ji shi akan wata lumtsumemiyar kujera koda yayi duba izuwa filin nan sai kawai yaga filin ya bace ya tsinci kansa a wani tankamemen daki wanda aka kawata shi da kayan alatu sai wasu tsala tsalan mata suka shigo suka kawo ma boka karibu kayan ciye ciye da lashe lashe sai da yaci ya koshi kawai sai ya ga aljani Shamsuna a gaban shi yana babbaka dariya boka karibu ya daure fuska yace haba babban abokina yazan tozarta a idon duniya kuma ka ringa min dariya kuma kasan na zo neman taimako ne a wajen ka aljani Shamsuna ya daure fuska yace abokina kayi kuskure ne kar ka manta na fada maka duk garin da ka tunkara in ka ga mutum daya ne ya iya tunkarar ka shi kadai to kafin kayi yaki da shi lallai ka tuntube ni amma sai kaki tuntubata boka karibu yace nayi kuskure ka taimake ni ajani yace mafita daya ne ya zama dole kaje dajin hadiqatul maut ka samo ma ulnar wanda ake ce mar daskararren ruwa domin da shine kawai zaka iya galaba a kan jaruma sarbila kuma kasani shiga dajin hadiqatul maut daidai yake da tunkarar ajalinka kwata kwata abubuwa uku zaka fuskanta amma sai kayi da gaske zaka tsira da rayuwarka boka karibu ya budi baki zaiyi magana sai aljani shamsuna ya daga masa hannu yace babu lokacin tambaya kuma babu lokacin amsata maza ka dauki hanya kawai. . al amarin Sarbila kuwa ta dauki hanya zuwa bakin tsauni domin ta gana da bokanya Alimma lokacin da ta isa bakin tsauni sai ta ja da baya tayi taku shida sannan ta falfalo a guje ta daka tsalle ta kama tsaunin nan tamkar kadanga haka take hawa tsaunin nan sai da sa a bakwai tana hawa tsaunin nan sannan takai kan tsaunin kawai sai ta taradda bokanya Alimma atsaye sarbila ta durkusa tayi gaisuwa alimma ta dago sarbila tace na gaisheki tauraruwar zamani lallai akwai aiki a gabanki babu lokaci yawaita surutu lallai ya zamar miki dole idan har kina son kiyi nasara akan karibu to sai kije dajin ikbal domin kishiga kogon zum ki dauko wukar tarihi da itane kadai zaki iya kashe makiyinki Sarbila za tayi magana alimma ta daga mata hannu tace babu lokacin tambaya ki kama hanya take ta dauki hayar dajin ikbal tayi tafiya na tsawon sati uku sai ta riski dajin ikbal tun da ta shiga dajin taji komai ya canza wani masifaffen zafi gami da wari tana tafiya zafi na karuwa warin na karuwa tabbas akwai wani abu a gaban ta Kwatsam sai tayi kicibis da wani katon gwaggwan biri yayi girman katuwar bishiya yana rike da wata katuwar guduma sai gurnani yakeyi taja tunga birin nan ya daki kirji ya sheko da gudu ta gyara tsayuwarta sai da ya kawo mata duka tayi sulu ta shige ta osinsa ta ta mike tayi wuf ta cakumi kugun birin duk girmansa sai da tayi sama da shi ta sandara da kasa birin yayi ihu ya mike ya cafi wuyan ta ya shake ta taji azaban shaka idanunta suka furfuto ta farajin kanshin mutuwa ta fara ganin manzannin mutuwa tayi na maza ta bude hannayenta ta tara iya karfinta ta daki kunnuwansa tsananin radadi da azaba da zafi birin yayi wurgi da ita tayi wani irin juyi a sama ta kara gabza masa naushi a makoshi birin yayi sama sannan ya fado kasa kamar rushewar gini amma saboda naci sai ya mike ya ja da baya ya daki kirjinsa ya falfalo da gudu ita ma Sarbila ta sheko da masifaffen gudu za ayi haduwar karshe Zan Cigaba Insha Allah Admin Goni S AbubakarSIHIRTACCIYA Part 7 Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Abdul aziz sani m/gini. Typing... by Goni. Lokacin suka zo daf da juna sai birin nan ya kaima Sarbila wani wawan duka ɗan kadan ta zame kuma tayi amfani da wata yar karamar wuka ta karta masa a makogwaronsa take jini yayi tsartuwa birin ya durkushe kasa bisa guiwowinsa sannan ya fadi matacce ko kallon shi batayi ba sai ta cigaba da tafiya burin ta kawai ta isa kogon zum inda zata dauko wukar tarihi sai da ta kwana ta yini tana tafiya sai ta isa wani katon dutse dutsen baki kirin kamar zunubi amma babu tsiro daya a kansa ta zagaye dutsen hagu da dama ta tabbatar babu hanya matukar tana so ta wuce ya zamar mata dole tabi takan dutsen nan ta kalli saman dutsen ta tunkare shi ta fara kokarin hawa kamar aradu taji wani tsawa gami da rugugi sai taji ance mata ke karamar jaruma kada ki kuskura kice zaki hau dutsen nan lallai zaki mutu taja da baya ta kalli saman dutsen sai tayi arba da wasu murda murdan katti. Tunda Sarbila take a rayuwarta bata taba ganin mutane masu girma da kauri da tsawo irin su ba tabbas sai da tasha jinin jikinta domin tasan karo da maza ba dadi wani kato ya daga murya yace yadai karamar jaruma kin karaya ne a haka zaki dauko wukar kisa wukar tarihi lallai ina mai baki shawara da ki koma gida ki jira ranar rushewar birnin ku. . Wadannan kalamai sun harzuka sarbila taji kamar katon nan ya watsa mata wuta ta takarkare ta kwarara ihu taja da baya tayi taku shida ta zaro wani kakkaifar gatari ta daga murya tace kuuu la anannu tsinannu lallai kunyi kuskure da kukayi batanci ga kasa ta abin alfahari na tabbas sai na wuce ta gabanku in kun cika mazaje ku tareni tayi kururuwa ta falfala a guje ta kama hawa dutsen nan kai kace tana gudu ne a shimfidaddiyar kasa kattin nan suka zare makamai suka tunkareta sukayi wani irin mugun haduwa mai sa rago futa aguje kamar tana girbin amfani haka take gididdiba kattin nan daga tasa kafa ta make wannan sai tasa hannu ta make wancan ko tayi amfani da gatari ta faskara kato kafin kace haka sai ga kattin nan suna gungurewa kasa tayi faca faca da jini kisa takeyi baji ba gani yaki yayi yaki yan maza sun ji ba dadi dole suka ja tunga suka tsaya cikin takama da izza Sarbila take hawowa dutsen tana gama hawa gaba daya kattin sukayi gaisuwa tayi murmushi tace dole kanwarnaki ta kunna kai tayi gaba ko waigensu bata karayi ba. . Al amarin boka karibu kuwa nausawa yake cikin daji tafiya yake baji ba gani sai ya isa wata korama dama yana fama da matsanancin kishi sai kawai ya nufi koramar ya durkusa don ya dibi ruwa yana sa hannu caraf aka cafke hannun aka fizgoshi cikin ruwan aka kuma nutso da shi sai yayi arba da wasu dodanni masu kama da mutane amma basu da kunnuwa sai wasu kaho guda biyu da wata zabgegiyar bindi gawasu gatsogatson hakora kai da gani kasan za suci naman mutum danye boka karibu yasa wuka ya yanke hannun dodon da ya rike shi dodan yayi kara yan uwansa suka tasoma boka karibu yayi kururuwa ya afka musu nan aka kulla cinikin rayuka boka karibu ya shiga aikasu lahira yana musu kisan wulakanci wani abin takaici shine dodannin sai karuwa sukeyi kamar tururuwa hankalin boka karibu ya tashi domin yasan matukar za a cigaba da wannan yaki.tofa zai kasa domin jiki da jini sai kawai yayi wani yunkuri yayi sama kamar kibiya sai gashi yahudo saman ruwa kamar yana taka tudun kasa haka yake falla gudu suma kuma haka suke binsa kamar jela koda karibu ya waigo ya ga tarin yawan dodannin nan wanda sun fi karfin lissafi sai yakara dagewa da tsala gudu a saman ruwa tsananin gudu har numfashin shi na neman daukewa saura kiris su cimmasa ya daka tsalle sai gashi a tudu ya futa a cikin ruwan cikin dodanin suka tsaya suna kallonsa suna lashe baki ya dube su ya tintsire da dariya yace kwalelen kare da hantar kura dole suka juya shi kuma ya nausa cikin daji domin ya isa dajin hadikatu maut inda zai samo ma unnar ruwan mutuwa. . Al amarin sarbila kuwa tayi nisa cikin tafiyar ta inda tazo wata hanya da ta kasu biyu ta rasa wanne za tabi bayan dogon tunani da wani dan nazari sai kawai tabi hagu sai taji an fashe da dariya wata murya na cewa wayyo yarinya cak ta tsaya har zata juya zata koma baya sai ta sauya tunani bisa nazari da tunanin yaudara irin na aljanu sai kawai.ta cigaba da tafiya kawai sai taji an kama kuka ana cewa hatsabibiyar tayi nasara ta iso wani dan yanki mai dauke da itatuwa gaba daya sai taji gurin bata yadda da shi ba sai tasa nutsuwa gami da taka tsantsan tabbas tana da gaskiya domin malafar wani gawurtaccen zaki ne da ya hana duk wata hallita a yankin kwanciyar hankakli kamar daga sama sai ya diro a gaban jaruma Sarbila ta kalli zakin nan taji tsigar jikinta ya tashi sabo da tsananin muninsa sukayi ido biyu da zakin nan . kamar an bashi umurni sai ya tunkaro ta a guje ya daka tsalle da nufin danne ta tayi wuf ta kauce ya kara kai mata bara nan ma ta kara zillewa ya kara yanko ta shi akaro na uku ranta ya baci itama ta daka tsalle suka hadu a sama tun a saman suka shiga kafsa fada.' sukayi dungure a kasa zakin nan kamar mutum haka ya rika jera ma sarbila naushi ta shaki wuyan zakin ta matse gam zakin yaji azabar shaka yayi wani gunji gami da girgiza take yayi watsi da Sarbila gefe a fusace yayi kanta baki bude take ta kama surkulle tana karanta dalasumai na tsafi ta nuna zakin da yatsa cak ya tsaya sannan ya karaso gurinta a hankali ta shafi kansa sai kawai ta dare gadan bayan zakin kamar doki sai ya nausa da ita cikin daji . Al amarin boka karibu bn kalab kuwa yana cikin tafiya sai yaji an zabga mar duka a take ya fadi sumamme bai tashi farfadowa ba sai ya tsinci kansa a daure tamau ga arnan daji nan suna ta kaiwa da komowa da alama biki sukeyi ba shi kadai ne aka kamoba sun kai su bakwai kuma a gabansa daya bayan daya ake daddatsa mutum a jefa namansa a wata katuwar tukunya da aketa faman dirka mata wuta gadan gadan malamin yanka da mukarrabansa suka tunkaro Boka karibu domin su yanka shi a jefa a tukunya asha shagali lallai da bakar fitina a nan hhhhhhh . Zan Cigaba Insha Allah Admin Goni S AbubakarSIHIRTACCIYA . Littafi Na Daya 1 . part 9 . Lokacin da Sarbila taji kalaman da ake fada sai ta harzuka take ta murza mabudin kofar tayi wani irin kara sarbila taja da baya ta shirya shirin kota kwana kawai sai kofar ta bude take sarbila ta kunna kai cikin kogon ba tare da tsoro ba ko fargaba ba ta iske kogon wani wawakene ya tafi har bata ganin iya karsa ga wasu gumaka masu suffar mayaka maza da mata kowane kamar yayi magana tana tafe tana dube dube cikin natsuwa sai taga wani kyakkyawan gunki kamar kirar jarumai sai ya bata sha'awa sai tasa hannu ta shafi kan gunkin kaico da sarbila tasan masifar da zata tsokano ma kanta tabbas da bata taba gunkin nan ba. Taba gunki keda wuya sai ya motsa take ya dawo mutum haka suma daukacin gumakan dake wurin sai da suka tashi gaba daya sukayo kan Sarbila makaman su azare tofa duniya makwanta rikici dole sarbila ta zare takobi tayi fito na fito suka kacame da yaki suka shiga kai mata sara da suka tana karewa kuma tana mai da musu da martani abin takaici shine idan ta sare ma daya kai take zai durkusa ya dauki kansa ya mayar da ita inda take ya cigaba da yaki lallai wannan ba karamar masifa bace domin duk abin da ta sara ta sari banza domin zasu dauka su mayar suci gaba da yaki. Sarbila ta fara gajiya inda tayi iya kokarinta taga tayi nasara akan daya daga cikinsu amma ta kasa nan fa gajiya ya riske ta inda mayakan nan suka shiga tamola da ita sukayi mata kaca kaca lallai sarbila ta san ta shigo kogon Zuum kogon bala i can tayi karaji gamida kururuwa ta daka tsalle ta tashi sama kamar tsuntsuwa sai gashi tana taka kawunan mayakan nan cikin sa a sai ta taka kan gunkin da ta fara shafa mar kai. Cak ya tsaya sannan ya koma gunkinsa take sauran ma suka kame kam suka koma siffofinsu na gumaka a wurin ta zube saboda tsananin gajiya tana maida numfashi daya bayan daya sarbila ta kama wani mimimi da baki tana wani karanto karatun surkulle take wani dan karamin gora ya bayyana a gabanta take ta damki goran ta kwankwadi ruwan cikin goran tana sha sai ta wartsake ko kwarzane babu ajikinta sai ta mike ta tunkari kofa na gaba ta isa jikin kofar sai ta tarar da wata siririyar kofa wanda koda an bude ta to dakyar mutum daya zai iya wucewa ta karema kofar kallo gami da nazarinta sai tayi niyyar sa dan mabudin don ta bude sai taji an kwarara uban ihu ana ce mata kar ki kuskura ki bude lallai zaki budo ajalin ki zaki hallaka Sarbila tayi nazarin maganar sannan ta fahimci wani abu take ta gyara tsayuwarta sannan ta cusa dan mabudin ta murza tana murzawa sai ta daka tsalle gefe guda ai kuwa kofar na budewa sai wata mahaukaciyar wuta ta kawo bara duk da hanzarin Sarbila sai da wutar ta laso damararta duk da kofar ta bude to tana rufe kanta kuma tana bude kanta da karfin ban mamaki kuma hakan na faruwane acikin dakika biyu kacal sarbila ta tsaya agaban kofar sannan tayi nazarin kofar ta tabbatar indai tana son ta shige ta wannan kofar to dole ne ta wuce acikin dakika biyu rak in ko ya wuce haka to ba makawa kofar ne ajalinta ko kuma ta koma baya abinda bazai taba yuwa ba kenan wai ta koma da baya. Al amarin boka karibu kuwa Kamar daga sama aka dakama Boka karibu tsawa ana cewa kai abokina ahaka zaka dibo ma unnar ruwan guba to maza ka mike kamar tsinke yayi zumbur ya mike aka ce masa maza kabi wannan hasken lallai shine jagoranka kuma kasani acikin hasken zakayi karo da abubuwa masu hatsari lallai zasuyi kokarin hallaka ka kuma kai ma dole ne kayi kokarin kaisu kiyama kuma kada ka kuskura ka tsaya dole ne ya kasance kana yaki kana tafiya acikin hasken nan domin idan harka sake hasken ya gudu ya barka to kai da cika burinka har abada kuma tabbas sai ka hallaka. Take wani haske ya bayyana kafin Boka karibu yayi wani abu tuni hasken ya fara tafiya ya fara yin nisa cikin hanzari da masifaffen gudu boka karibu yabi hasken nan amma hasken sai kara guduwa yakeyi kamar ransa zaifita haka yake gudu amma ko kusa da hasken baiyi ba take boka karibu ya sabi wasu kalamai masu kama da gwalan gwalan din yara yayi wasu sarkakkun kalmomi daga cikin kalaman tsafi ya kira wani hargi tsatstsan suna sau uku take wani zabgegen aljani ya bayyana suka sa tseran tare suna ahalin gudu aljani yace lafiya mai gida ka kirani a wannan lokaci kuma a wannan tsinan nan dajin mai hatsarin tsiyar. Afusace Boka karibu yace masa kai sha sha sha ba surutu nake so ba maza ka sada ni da hasken can da yake kokarin kulewa kamar ka dauki dutse ka ajiye atsakiyar ruwa haka aljanin nan ya dauki Boka Karibu bn kalab ya ajiye atsakiyar hasken nan tashin hankali wanda ba a sa masa rana lallai wannan daji bala ine kuma masifane domin shi kan shi boka karibu bn kalab da yayi arba da miyagun halittun dake cikin hasken nan sai da ya tabbatar da cewa ya tunkari ajalinsa . SHIN BOKA KARIBU DA SARBILA ZASU SAMU ABIN DA SUKA FITO NEMA KUWA? SHIN YAUSHE ZA A FAFATA GASAR KARSHE TSAKANIN BOKA KARIBU DA SARBILA? SHIN WAYE ZAI CI NASARA A WANNAN GASAR? SHIN SAMAR ZAI YADDA YA AURAR DA SARAUNIYA YAZRINA GA SARKI JUNDARU NA BIRNIN BANGUS KUWA? Gaba daya wannan amsar mu hadu a SIHIRTACCIYA littafi na biyu don jin yanda zata kaya daga mai nishadantar da ku wato real rayyanu ke cewa mu hadu a littafi na 2 SIHIRTACCIYA Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz Sani m Gini Ebook created by Shuraih 99% Published at www.hausaebooks.com.ng SIHIRTACCIYA . Littafi Na Biyu 2 part A . Lokacin da Boka karibu bn kala yayi arba da masifun dake cikin hasken nan sai ya zazzaro ido wasu mahaukatan damusai ne mace da namiji suka tunkaro shi gadan gadan sai boka karibu yayi wani surkulle take wani dogon mashi ya bayyana a hannunsa suka fara dauki badadi da damusan nan yayi iya kokarinsa dakyar ya kashe daya amma sai dayan ta zamar.mishi alakakai tana neman ta tsayar da shi alhali an masa kashedin kada ya kuskura ya tsaya ran boka karibu ya baci sai yayi wurgi da mashin hannunsa aiko sai damisar nan ta dako tsalle caraf ya shaki wuyanta ya matse gam kuma yaci gaba da gudu ba tare da ya tsaya ba a haka tayi ta shure shure ahannunsa har ta mutu boka karibu yayi jifa da gawar damisar kuma ya cigaba da tsala gudu acikin hasken nan kamar kibiya haka wasu garza garza mayaka sanye da bakaken damarar yaki suka bayyana acikin hasken nan. Take suka tunkari Boka karibu aguje kamar masu gudun tsira boka karibu ya kara yin surkulle take bakin mashi ya bayyana ahannunsa ya jijjiga mashin ya daga sama ya auna wasu mayaka dake kan gaba wajan tunkararsa ya cillo mashin nan mashin yayi wani futar borgu kai kace an harbo shine daga cikin baka mashin ya tafi a aune ya caki wani barde ya hudashi ya fita ya caki na bayansa kai sai da ya hallaka mayaka goma ya cigaba da tsala gudu acikin haske haka shima hasken ke tsala gudu kokarinsa ya guduma boka karibu shi kuma boka karibu yaki amincewa gudu yake ba kaukautawa mayakan nan suka farmar da sara shi kuma ya shiga tsiresu da mashi ba kakkautawa kai maza gumbar dutse boka karibu yana gudu amma yana daukar rayukan mazaje yana shallake wasu yana kwalloda wasu yana bangaje wasu wani aiki dai sai mai shi. kwatsam wani jarumi ya daka tsalle ya cakumi Boka karibu kafin kace haka jarumai sama da dari sun rungume shi da karfin tsiya yayi iyayinsa domin ya kwace amma ina ya kasa domin yawa suke karawa suka taru akansa hasken nan sai tafiya yakeyi har ya gudu ya bar boka karibu koda Boka karibu ya ga hasken nan yana neman yayi masa nisa gashi kuma mayakan nan sun yanyame shi burin su hasken ya bace koda boka karibu ya fahimci nufin su ya kuma tuna gargadin da aka masa na cewa indai ya saki hasken nan ya bace masa lallai dukkan burinsa ya ruguje sai ya takura yayi wani wawan kara gami da gunji hadi da wani nagartacen yunkuri take yayi watsi dasu sai ga mayakan nan suna shawagi asama kamar tsuntsaye suna kuma fadowa kasa kamar buhuna tim tim boka karibu ya fita da wani matsanancin gudu saboda tsananin gudun har bacewa yakeyi kamar mai kokarin hayewa doki. Haka yake kokarin kamo hasken wuf ya fada cikin hasken fadawarsa keda wuya sai yatsinci kansa agaban wasu furda furdan aljanu sama da dubu dari uku wasu sun kewaye wani bakin ruwa wasu sunyi sahu sahu wasu sai zirga zirga sukeyi makamai azare fuskar su ba imani bare tausayi kai da ganinsu kasan babuma suwa ciyeta Boka karibu ya tsaya cak hasken nan ya bace sukayi ido biyu da aljanun nan shi baice da su haka ba suma basuce da shi komai ba sai zazzare idanu kawai sukeyi suna wani hucin wuta Al amarin Sarbila kuwa sai tayi nazarin kofar nan mai bude kanta kuma ta rufe kanta acikin dakika biyu kacal ta fahimci cewa lallai wucewa ta kofar nan kamar tsallake mayen damisace mai yaya gashi kuma babu wata hanya sai ita Sarbila tayi duk wani surkulle wai don ta tsaida kofar nan amma Abin ya gagareta A karshe sai taji muryar bokanya alimma na cewa lallai in kika ci gaba da tsayuwa a wanna guri kuma a gaban wannan kofa to dakiku kadan ya rage ki hallaka take ta jada baya tayi taku shida ta falfalo ague tana zuwa daidai kofar nan sai tayi sufa kamar walkiya ta wuce tana wucewa kofar ta rufe da matsanancin karfi tafada ciki ai kuwa sarbila tana mikewa sai tayi tozali da tarin dandazon tashin hankali lallai bala in da Sarbila ta gani ya ninka wucewa ta kofar sau biyu tashin hankali. Wasu irin hallitu ne masu kama da zakuna amma sun ninka girman zaki sau bakwai yawansu zai kai dari bakwai suna da wani katon kaho mai tsawo da kauri da tsini kamar tsinin mashi gawasu mahaukatan hakora kamar takubba sai wani turza sukeyi sai dalalarda yawu sukeyi kai da ganinsu kaga mayu kamar an hura musu usur sukayi turza suka fakai a kasa da kahonsu kawai sai suka tunkaro Sarbila da mugun nufi sarbila ta gyara tsayuwarta ta girgixa mashin ta tayi murmushin da ba mai iya fassara shi ta kwarara ihu tayi turza kura ya tashi ta tunkari halittun nan da bakar zuciya don agwabza yakin mutuwa. . Lokacin da akayi arangama tsakanin halittun nan da Jaruma sarbila sai abin yayi muni domin wani bakin gumurzune aka fara kaftawa tirkashi lallai mai karfi sai Allah ya isa sarbila ta shiga sukan halittun nan tana gabza musu naushi duk in ta naushi halittan nan sai ta baje a kasa amma abin takaici sai ta tashi da matsanancin fushi ta tunkari sarbila haka kuma koda sarbila ta soki halittun nan da mashi to mashin baya iya huda fatar su gashi dai Sarbila ta zamar ma halittun alakakai. Amma ta kasa kashe koda guda dayane hankalin sarbila ya tashi tayi iya dabaranta da nuna hikima da kwarewa na yaki amma abin yaki gashi ta fara gajiya har dabbobin nan sun fara cin galabarta domin sun karceta da kahonsu har guri hudu matsanancin jinine ke zuba can wani dabba yayi kukan kura ya surfafu da gudu sarbila takai masa sara dabban ya kauce wuf ya sunkuceta da kansa yayi wurgi da ita tayi sama ta dawo kafin takai kasa wani ya kara sa kai ya gabza mata duka ta fado atsakiya dabbobin nan. Nan fa suka far mata sukayi ta kwallo da ita suna tattaka ta sukayi budu budu da ita saura kiris su hallaka ta domin numfashinta ya fara nisa su kansu halittun sun dauka ta mutune saboda haka suka jada baya suka tsaya suna mata kallon gawa suna wani turza da kafa can wani iska ya hura sanyi ya ratsa kunnuwan sarbila da hancinta nan ta fara motsawa take ta fara yunkurawa ta mike ta zauna dabbobin suka zura mata ido cikin mamaki domin sunyi zaton ta mutu ta yunkura ta tashi ta mike tsaye ta kwarara ihu gamida girgiza wani kura ya tashi ta daga kafar ta na dama ta daki kasa ta kara kwarara ihu Sarbila ta karewa dabbobin nan wani irin kallo ta tuna irin fafatawan da sukayi a farko ta tuna duk wani wuri data sara ajikin dabbobin nan da inda ta soka amma batayi wa ko daya rauni ba ta karewa halittun kallo sai tayi murmushi sannan tayi wani surkulle gami da wani sambatu ta karanta wasu sarkakkun kalmomi da kalaman surkulle ta daga hannunta sama take sai wani kakkaifar gatari ya bayyana a hannunta baki.kirin ta girgiza shi take gatarin ya kara girma da tsawo harda kaifi tayi kururuwa ta nufi halittun nan afusace halittun nan sukai wani irin gurnani suma suka tunkarota wai wai rikicin duniya. Nanfa sarbila ta fitowa halittun nan ta bayan gida sai tasa hannu daya ta damki kahon dabba sai tasa gatari ta sare kahon take sai dabba ta sheka barzahu nanfa Sarbila ta fara musu kisan gilla kai masifa tayi masifa Sarbila ta fitowa dabbobin nan a shaidaniya kashe su kawai takeyi kamar kisan kiyashi halittun nan suka jada baya domin sun tsorata sarbila tayi murmushi kawai sai takara afka musu nan fa suka tarwatse ta shiga binsu tana daukan rayukansu haka suka sa tsere suna gudu tana binsu duk wanda ta samu sai ta kama ta daga sama sannan ta sare kahon a haka kaf sai da ta gama da halittun nan saura daya tak nan fa suka fara tsere saura kiris ta kama dabbar nan sai suka isa kofa na uku take dabbar nan tayi tsalle ta wuce Sarbila ta daka tsalle sai kum ta hadu da murfin kofa domin tun kafin ta rufe. Take Sarbila ta fado kasa asume Al amarin Boka karibu kuwa sai yayi duba izuwa ga aljanun nan masu gadin bakin ruwan nan ya tabbatar wannan bakin ruwan shine ma unnar domin ruwan har wani turiri yakeyi wani zubin har wuta ke kamawa a saman ruwan sannan yayi duba ga aljanun wadanda sukayi sahu sahu suna tsaye kikam sai muzurai sukeyi kamar zasu ci babu sannan yayi duba ga masu zirga zirga da miyagun makamai sai ya tabbatar ma kansa cewa lallai in har yana so ya debi wannan ruwa to dole ne sai ya gwabza da duk wadannan dakarun aljanu aransa yace karo da maza badadi amma ni zan kara da su. Kai tsaye sai ya

Chapter 2 of 5