Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  SIHIRTACCIYA . Littafi Na Daya 1 part A . author:abdul,aziz sani m/gini . TYPING:goni a abubakar . POAT: REAL PRINCE RAYYANU . Kasar manohar ta kasance mai girma wanda tana dauke da mutane sama da milyan dari biyar ta kasance mai tarin arziki wanda awannan zamanin samun kasa kamarta sai antona wata hamshakiyar sarauniyace ke mulki akasar anace mata sarauniya YAXRINA a kalla zatakai shekara sittin amma bata taba yin aure ba shahararrun matsafa na duniya sun tabbtar da cewa duk ranar da sarauniya Yaxrina ta kwanta da wani da namiji to tarihin kasan zai karya zakuma su shiga cikin masifu da bala o i daban daban wanda a karshe sai sun fi kowa talauci a duniya wannan daliline yasa sarauniya Yazrina tacire aure a ranta gaba daya tana gudanar da mulkinta cikin adalci da tausayi shi yasa talakawan kasan na mutukar son ta har suna jin za su iya bada ransu sabo da ita mutanan kasar Manohar sun kasance suna bautama wata kyakykyawar gunkiyace wanda suke kiranta da suna makarbiya wannan gunkiya tana da mutukar girma da daraja agaresu hakika sunyi imani itace take basu komai sabo da koyaro karami bai kaunan wanda baison gunkiya manuniya . Sarauniya Yaxrina tana da wani kani mai suna SAMAR wanda kuma shine sarkin yakinta cikakkaken jaumine nagaban kwatance domin duk girman kasar manohar babu mai iya kaishi kas sunyi mutakar shakuwa da juna wanda takai in ba barci ba ba abin dake rabasu kai ko barcin ma wataran a dakin sarauniya yake kwana domin sau da yawa inya shiga dakin sarauniya suna hira idan barci ya kwashe shi maimakon ta tashe shi sai kawai ta dora shi a gado sai da safe. . Watarana fada ta cika tayi makil ana fadanci sai gawani jarumi yashigo fada ya nufi gurin sarauniya dakaru su tare shi yace nidan sakone ya mika musu takarda suka karba suka mikama saraniya Yazrina tamikama maga takarda shi kuma yafara karanta takarda kamar haka. Daga sarki JUNDARU na birnin Bangus hakika na sami labarin sarauniyarku bata da aure to tasami miji lallai in kunaso kutsira daga mutuwa to lallai kugama shiryamin amaryata nan da wata uku zanzo indauketa idan kukaki to lallai zan rushe birninku inkashe maxajenku kuma in kame matayen ku amatsayin bayi kuhuta lafiya daga sarki Jundaru mai duniya na birnin bangus. Koda mutane sukaji abinda ke cikin wasika sai fada tarude take wasu suka fashe da kuka kai hatta sarauniya Yazrina sai da takama zubar da hawaye bawani abu bane yasa mutanen kasar Manuhar rudewa face sanin wanene sarki jundaru mai duniya na brinin bangus wani hatsabibin mutumne wanda gaba daya ya gallabi duniya gagararrene tun yana dan shekara goma yazama rikakken dan fashi wanda in yaje fashi saidai yashigo gari da rundunan sa yafarma mutane da sara tun yana yaro ba ataba galaba akansa ba lokacin daya girma yakai kimanin shekara ashirin sai ya tunkari kasar Bangus da yaki wanda alokacin duk duniya itace na daya ayawan jarumai da kuma iya yaki a tarihi babu wata kasa data taba nasara akansu saboda haka kusan sune suke juya manyan sarakuna duniya amma Jundaru yatunkari kasar da mayaka dubu goma akayi wata guda ana zuba yaki gaba daya sai da dakarunsa suka kare amma shi sai da akwana uku ana dauki badadi dashi wanda arana na hudune Jundaru yai nasaran sare kan sarkin kasar Bangus kuma ya kashe sarkin yakin garin ya zamar musu kamar aljan kashe mutane yake kamar kiyashi bisa tilas suka mika wuya ya zama sarkin Bangus tun daga haka sarakunan duniya suka masa mubaya indai yaga mace yanaso tokuwa zai aikone kushiryata zai zo yadauketa rana kaza inko kukaki to kasar garimma bazatai kyan gani ba. Ranar da majalisar kasar Manuhar taxauna akan yadda za afitoma lamari majalisa tarikice wasu nacewa amika saraniya ga sarki Jundaru wasu nacewa bazai yuwuba domin ko an mikata ba atsiraba tunda mutukar sarki jundaru yakwanta da ita to sai nasifata rufto makasar manuhar nan gardama tasarke ana neman aba hammata iska Samar wato sarkin yaki kuma kanin sarauniya Yaxirina ya takarkare yakwarara wani wawan ihu gaba daya majalisa tai tsit sannan ya fara magana yace tabbas mun shi ga tsaka mai wuya in mun bada sarauniya bala i yabiyo baya in muka hana masifa tazo ta samemu yace to akwai mafita guda daya tak sukace wace mafitace Samar yace sai dai mutashi SIHIRTACCIYA WATOGUNKI MANUNIYA gaba daya majalisan babu wanda bai mikeba gami da kokarin ficewa daga majalisan Wannan .SIHIRTACCIYA Part 2 Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Abdul aziz sani m/gini Lokacin da Samar ya ga yan majalisa na kokarin watsewa sai ya takarkare ya kwarara ihu wanda tasa dole yan majalisa suka tsaya cak kamar an hura musu usur sai suka juyo sukai ido biyu da samar ya dube su ya daga murya yace wato mutuncin kasar namu kuke so mu mikata a banza to ku sani idan duk duniya zata taru babu wanda ya isa ya dauki yar uwata ya mika wani wawan sarki ya mai da ita baiwa to sai dai inna mutu. . Gaba daya yan majalisa suka dawo suka zauna daya bayan daya Samar ya kare musu kallo sannan yayi murmushi yace shuwagaban nina ina mai tabbatar muku indai har zaku mika gimbiya Yazrina to ku shirya shirin yaki da ni ya juya zai fita shugaban yan majalisa ya kira shi cak ya tsaya sannan ya juyo ba tare da yayi magana ba cikin takama da nuna izza ya tako yazo ya tsaya a gaban yan majalisa shugaban majalisa ya dube shi yace a matsayinka na dan gidan sarautar kasar nan zaka iya gaya mana wacece sihirtacciya . Samar yayi gyaran murya yace shekaru dari uku da hamsin da biyu a wannan kasa na Manuhar anyi wani gawurtaccen sarki mai suna Maridu shi wannan sarki ya sha hare hare a duniya domin a zamaninsa babu wata kasa da takai kasar Manuhar tarin arziki da yawan jama a da kwanciyar hankali sarki maridu yana da wasu kannai tagwaye Sarbilu da Sarbila waɗan nan kannan sarki maridu sun kasance yan gata kuma yan lele a kasar Manuhar Sarbilu kwata kwata bai da jarumta kuma sam baya sha'awar koyan fada duk da yana da zubin jarumai sabanin yar uwan sa Sarbila wanda ta kasance zakakuran jarumai indai har za a lissafa jarumai to dole za asa da ita. A can kuma kasar Dulima wani hamshakin bokane wanda yasha alwashin sai ya mayar da duniya an koma bauta masa yayi rantsuwa da kakansa bazai bar wata kasa tazauna lafiya ba matukar ba su karbi bautan gunkinsa ba boka Kalibu bn kalab ya shafe sama da kasa arba'in gaba daya ya ruguza abubuwan bautansu ya gina katon gunkinsa a kasashe da yawa idan boka kalibu yazo zai yaki gari to mika wuya kawai sukeyi domin sun yi imani ko sun futo agabza yaki to dai dole zasuyi biyayya bayan an kashe musu mutane wannan ne yasa ake kiransa da boka karibu da gagara badau. . Kwatsam boka Karibu da tawagarsa na aljanu da mutane ta sauka a bayan garin Manohar boka karibu ya rubuta takarda zuwa ga sarki maridu ni boka karibu gagara badau na sauka a bayan garinka ina mai umartanka da ka dauko abin bautanku kai da jama arka ku futo bayan gari ku rusashi a gabana sannan ku konashi in baku gunkina kuci gaba da bautamin in kukayi haka kun kubuta daga a zabata lallai kuyi nazari kuna da yaya kuna da mata kuna da tarin dukiya to kusani bjiremin yana nufin kun sallama yayanku da matanku da dukiyarku da rayukanku gaba daya koda sarki maridu ya samu sakon Boka karibu sai ya rude ya tara mashawartansa gaba daya sun rude kai tsaye suka amince da a dauki gunkinsu abin bautansu mai tarihi a kai gaban boka karibu a kona amika wuya koda jin wannan batu sai jaruma sarbila ta takarkare ta takwarara ihu wanda daukacin kasar Manohar sai da suka ji tai zarya ta zare takobi tace narantse da kasata babu wanda ya isa ya dauki abin bautana ya rusashi in har ina nunfashi tabbas zaku iya mikashi amma sai bayan mun gabza yakin cikin gida in kun kasheni to sai ku mika in kun kasa to ya zama dole kubini ta daga murya tace tabbas nasan karo da boka karibu masifane amma zan tunkareshi koda zai hallakani to sai na bar masa abin fada. Sarki maridu zaiyi magana ta daga mai hannu tace in har mutum ba zai goyamin baya ba to kada ya kuskura ya samin baki gaba daya a kawatse ana mata kallon ta haukace ita kadai ta rage a wajen sai dan uwanta sarbilu ya ruga da gudu yaje gaban ta yace yake yar uwata hakika ni ban kasance jarumi ba amma ina da karfin zuciyar da zan biki wannan yaki koda zan halaka Sarbila ta dubi dan uwanta tayi murmushi sannan tajawoshi ta rungume tana cewa tabbas za muyi nasara gobe ni dakai sai mun barma duniya babban labari lallai zamu kafa tarihin da sai jaruman duniya sun sara mana Zan cigaba insha Allah Admin Goni S Abubakar SIHIRTACCIYA Part 3 Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Abdul aziz sani m/gini Gari na wayewa Sarbila ta kama shiri ta sanya wata farar riga da wando wanda aka sana annta ta da gashin farar damisa ta daura fatan zaki a kanta ta dibo wasu kananan wukake zasu kai hamsin ta shiga ɗanasu a damararta kaf sai da kowacce wuka ta samu wurin zama ta dibo wasu kana nan adduna guda biyu ta soke a kugunta hagu da dama ta rataya takobi a kafadanta sannan ta makale wasu kana nan gatura guda biyu a gadan bayan ta takalli sarbilu yayi mata jinjina kawai sai tayi waje sarbilu ya take mata baya duk inda ta ratsa acikin gari sai mazaje su sunkuyar da kai kasa. Ta isa kofar futa dakaru suka bude mata tayi waje ita da sarbilu aka kulle kofa. Abin mamaki boka karibu ya dube ta ya daka mata tsawa yace ke yarinya ina sauran jama ar gari da sarkinku da kuma abin bautanku Sarbila ta daka mai tsawa tace kai bakin azzalumi lallai kasani ni ba yarinya bace kuma zan tabbatar maka da hakan sarkina da abin bautana sun fi karfin su zo su amsa gaiyatarka kayi kadan nine dai dai da kai yaro wayyo boka karibu yaji kaman sarbila ta watsamai wuta ya takarkare ya kwarara ihu sannan yace bana son takara dake daya a duniya. Tuni wani yanki daga cikin dakarun boka karibu sunyo kanta sarbila taja da baya tayi taku uku kawai sai ta zaro kananan wukaken nan guda hudu ta watsa su wukaken suka farma dakarun nan sai da suka caki sama da mutum talatin sannan wukaken suka koma hannun Sarbila ta cukesu adamararta tayi kururuwa tazare adduna guda biyu ta falfala da gudu ta daka tsalle ta fada tsakiyan mazaje. Nan fa yaki ya kullu masifa ta tashi karan takubba ya gauraye wajen ta shiga farke cikin maza tana datse kawunan su nan fa jini ya fara malala dakaru sai tuttudowa sukeyi ita kuma tana ajalinsu ta zamar musu alakakai ta addabesu ba mutun ba aljani. . Shi kan shi boka Karibu sai da zuciyarsa ta buga ganin yanda Sarbila ke sama da mutane da Sai da suka dauki sa'a shida ana fafata yaki tsakanin jaruma Sarbila da dakarun boka Karibu gawarwakine kwance kamar an hake gyada mai yaya, kura tayi sama ta mamaye sararin samaniya ba a ganin kowa sai kura sai sautin haduwan karafa can komai yayi shiru bakajin koda motsi sannu ahankali kura ta lafa duhu ya yaye. Kawai sai ga sarbila a tsaye tana layi jiri na dibanta saboda gajiya amma kuma ilahirin jaruman nan ta aikasu kiyama ko ina ajikinta jini ne ke zuba kamar hawaye ganin haka boka karibu ya kwarara ihu ya zaro takobi yayi kan sarbila a guje da mugun nufi. Ganin haka sarbilu ya daka masa tsawa cak boka karibu ya tsaya sannan ya dubi sarbilu yace to kai da ba jarumi ba meye namin tsawa kabari in kashe jaruman daga nan sai in dawo kanka sarbilu ya fashe da dariya ya dubi Boka karibu yace aikai ma ragon ne domin ka kasa nuna jarumtanka ga yar uwata sai da tayi yaki sama da mutum du arba in ta gaji shine dan lalaci zaka afka mata da yaki. Take boka karibu ya watsar da makamansa ya nuna sarbila da yatsa yace lallai dan uwanki ya ceci rayuwarki da kalamansa kije kiyi jinya na wata biyu a sannan ne zan fuskan ceki gaba da gaba dan in nuna ma dan uwanki nacika sadauki uban mazaje kawai sai boka karibu bn kalab ya bace sarbilu ya ruga da gudu ya rungume sarbila suka fashe da kuka. Labarin jarumtar sarbila ya cika duniya ana ta fadin wata jaruma ta kada boka karibu wannan labari ya ba tama boka karibu rai inda yayi na dama rashin kashe ta sarbila gashi yanzu shi da yake so sunansa ya gauraye duniya sai ya sami tozarci da nakasa ita kuma Sarbila sunanta ya bazu a duniya yan mata da kananan yara har waka suke mata. Wannan abu sai da Boka karibu yaji kamar ya kashe kansa dan haushi amma sai yasha alwashi indai suka sake haduwa to sai ya mata kisan wulakanci irin kisan da a duniya baza ta taba manta shiba Zan Cigaba Insha Allah Admin Goni $ AbubakarSIHIRTACCIYA Part 4 Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Abdul aziz sani m/gini. Al amarin jaruma sarbila da dan uwanta Sarbilu sai yarugume ta suka koma gida koda suKa shiga gari sai jama a suka fara taransu da murna take sarbilu ya daka musu tsawa ya ɗaga murya yace narantse da yar uwata sarbila duk wanda yayi gangancin matsowa kusa da mu to lallai sai na kashe shi kun kasa futa yaki saboda tsoran mutuwa yanzu kun ga mun dawo shine zaku dau murna ko to ku sani lallai babu wani maha lukin da zai zo kusa da yar uwata ni kadai zanyi jinyarta sai da yayi sati yana mata magani sannan ta watsake kuma har ta warke bai taba magana da Dan uwansa ba wato sarki maridu haka ita sarbilatu data warke sai taci gaba da ba kanta horan yaki takara kwarewa da zama hatsabibiya. Akwana a tashi har wata biyu da boka karibu bn kalab ya diba ma Sarbila suka cika tun da dare take shiryawa tayi shiga irin ta manyan sadaukai tayi juguf acikin kayan yaki tun asubahi aka din ga jin wasu mahaukatan saututtuka da zantuttuka irin na surkulle sannan ana kyakyata dariya wata kakkausan murya tana cewa hakika yau mutanen kasar manohar bala i da musifa ta afka musu kuma ba kowa ya jawo muku ba sai yar ku jaruma sarbila ina umurtanku gaba dayanku mazanku da matanku yara da kankananku da ku fita bayan gari an shirya filin gasa inda ni Boka karibu bn kalab zan fafata yaki da jarumarku jaruma sarbila lallai rayuwarku na hannunta in tayi nasara to kun tsira idan ko nayi nasara wayyo lallai kusani zan dandana muku azaba kala kala ta yadda kowane dayan ku sai ya mutu sau goma maza kufuto dan kallan yadda zanfara wulakanta jarumarku. . Kai tsaye ja ama ar kasar manohar suka fara futa bayan gari sun sha mamaki ta yadda suka ga an shata fili ankawata shi dakujeru wanda yan kallo zasu zauna abin mamki shine duk wani sarki da ka sani ya tun batsa a duniya to yana gurin shi da jama arsa suka zauna a inda aka tanada dominsu ga kuma mutane bila adadin ba iya ka sai ihu sukeyi wasu kuwa tuni sunbude filin kasuwanci jama a inda kasan antara mutanen duniya mutanan kasar Manohar antaja musu gurin zama na musamman suka samu wuri suka zauna hankalinsu a tashe domin sun san an shirya musu wulakanci maigirma a wannan rana saboda haka kowa ka gani afilin yana murna amma banda mutanen kasar manohar. . Shi ko sarki maridu yayan sarbilu da sarbila tunda ya zauna ba abinda yakeyi sai kuka domin ya tabbata yaune ranar karshe na rayuwan yan uwansa agefe guda kuma yana tunanin irin wulakanci da kaskanci da zai fuskanta a wajen boka karibu ibn kalab. Kwatsam sai akaji wani ihu da kururuwa daga sama nan take kallo ya koma sama aiko sai aka hango boka karibu bn kalab yana sauko wa daga sararin samaniya ran shi abace take guri yagauraye da ihu da kuma sowa harda tafi inda wasu suka tashi ganguna aka kama rawa sannu ahankali boka karibu ya sauko ya dira afilin da aka tanada dan fafatawa jama a suka kaure da ihu harda tafi suna tsalle inda mutanen kasar manohar suka fashe da kuka domin sun tabbatar mutuwarsu tazo. Boka Karibu ya kwarara ihu gaba daya gurin yayi tsit kamar ba kowa a gurin Boka karibu ya fashe da dariya ya daga murya yace dole kanwannaki lallai yau mutanen duniya zan tabbatar muku da cewa ni kadaine za a bautama lallai sai nama sarbila da dan uwanta sarbilu kisan gilla kuma sai na kona gunkin bautansu a gabansu in yi fitsari a tokar abin bautansu lallai yau.... . Bai karasa maganar shi ba sai akaji wata kakkausar murya tana cewa karya kake bakin azzalumi lallai yau duniya sai tama dariya jama a sukayi duba zuwa inda maganar ke fitowa sai sukayi tozali da jaruma Sarbila tayi wani gagarumin damarar yaki kamar zata yaki duniya jama a suka kaure da ihu gami da tafi tana tafe dan uwanta na take mata baya jaruma sarbila ta falfalo a guje tayi alkafi gaida tsalle tayi juyi sau uku a sama sai ta diro atsakiyar filin gasar guri ya kara kaurewa da ihu. Ran boka Karibu ya fara tafarfasa ya dubi Sarbila yace ke yarinya lallai ke kadaice a duniya kika taba sani hawaye da tsananin bakin ciki tabbas yau sai na sabule kayanki a bainar jama a kuma sai nayi lalata da ke kowa yana kallo kana daga bisani in sabile fatar jikin ki in yi gunduwa gunduwa damanki lallai yau sai na dandana miki azaba kala dubu goma kafin ki mutu Sarbila ta fashe da dariya ta nuna shi da yatsa tace kai bakin mayaudari sam wa yannan kalaman naka bazasu taba tsorata niba kawai ka gwadamin jarumtarka ba barazana ba. . Boka karibu yayi kururuwa ya sheko a guje ita ma tayi kansa a fusace sai da suka kusa haduwa suka daka tsalle sukayi sama akayi wata haduwa irin ta shirwa tun a sama suka kacame da azababben yaki karan takubba ya gauraye gurin sun himmatu da kaima juna sara da suka sai suyi tsalle nan suyi tsalle can. Tun abin nabawa mutane sha awa har yazo ya fara basu tsoro domin yakin ya kazanta domin sarbila ta yanki boka karibu sau hudu shi kuma ya yanketa sau shida tirkashi duk da suna mutukar zub da jini amma babu wanda ya nuna karayar sa a lokaci guda suka watsar da takubbansu domin sun dakushe kawai sai su shiga bugun juna bakakkautawa . lallai boka karibu ya san ya gamu da gamonsa domin sai da sarbila ta din ga mai ruwan naushi tamkar mai dakan sakwara dakyar yake karewa take ya sauya fada zuwa fannin tsafi ya rikide ya zama wani katon bakin zaki yayi kan ta take sarbila ta rikida zuwa karamin halitta take suka kaure da fada guri ya dau tafi da ihu su kansu mutanen kasar manohar sai da tsoro ya fita aransu suka kama ihu da tafi...... Zan Cigaba Insha Allah Admin Goni $ AbubakarSIHIRTACCIYA . Littafi Na Daya 1 . part 5 . . WANNAN NAKUNE . MUH'D JAMAL . GAZALI HASHIM BAKURA . STARBOY UMAR . nagode addu'o'in dakuke min ana mugun tare . Zaki da dage suka kacame da fada duk inda zakin nan zaiyi yayi yaga ya dakama dagen nan wawa amma sai dagen ya kurda ta karkashinsa kuma kafin ya futo sai ya tabbatar ya kaftama zakin nan cizo haka idan yahaye bayan zakin sai ya kaftamai cizo cikin kankanin lokaci zakin nan yajiggata sai ya rikide ya koma maciji take dagen ya koma shirwa suka shiga kafsa fada guri yadau ihu da tafi domin fadan ba karamin sha awa yake ba dawaba. . Cikin sa a macijin nan ya kaftama shirwan nan sara tuni shirwan ya baje akasa yana wani shure shure hankalin jama a ya tashi musamman ma mutanen kasar manohar domin sun fara hango mutuwarsu shi ko sarki maridu tuni ya tube rawaninsa ya fashe da kuka shi ko Sarbilu suma yayi a tsaye maciji yayi rimi gamida guda ya nufi shirwan nan a guje sai da ya tara iya muguntansa zai tafkama shirwan sara wuf shirwan ta shaki wuyan macijin tayi sama da shi ta girgiza ta sako shi kasa gaba daya fili ya haukace da ihu tafi guda kide kide rawa har da tsalle kai da yawa sun saki fitsari a wandonsu don murna da shewa tun a sama ya fara rikidewa yana komawa siffarsa ta asali sai ga boka karibu ya diro a filin gasa gaba daya jikinsa babu inda bata buba yayi kaca kaca dakyar yake iya tsayuwa haka itama Sarbila ta diro filin gasa a siffarta ta asali itama tayi biji biji tabbas mai tausayi dole ya tausaya musu amma a haka suna tafe suna layi sai da suka shaki wuyan juna su kaima juna karo wasu taurari suka baiyana musu su kayi baya duk da haka sai da sukayi amfani da kafafuwansu su tokari juna sukayi tsalle baki dayan su a sume suka fado take aka nemi Boka Karibu aka rasa a guje Sarbilu yaje ya rungumi yar uwansa ya fashe da kuka guri yayi tsit wani babban sarki daga cikin sarakunan yankin ya mike yace jama a lallai har yanzu yaki bai kare ba saboda haka kowa ya koma kasar sa kuma muna fatan zamu sake haduwa anan kwanaki casa in masu zuwa lallai kowa ya dawo gaba daya jama a suka watse kowa yana fadar albarkacin bakinsa idan ka kasa jama ar da suka halarci wannan wuri in an kasa su dari to tamanin da biyar suna goyon bayan Sarbila lallai suna fatan a karo na gaba sarbila ta samu nasara domin shi Boka karibu azzalumi ne. . Boka karibu bai bayyana ako ina ba sai a wani kungurmin daji mai cike da abubuwan ban tsoro tunda ya sanya guiwansa akasa bai motsaba sai da yayi kwana bakwai yana kuka arana ta takwas ya mike ya takarkare ya kurma wani uban ihu sai da kananan halittu suka dinga karo da juna koramu suka dinga ambaliya duwatsu suka dau tiriri bishiyoyi suka kama kadawa yayi futan burgu sai da yayi gudun sa a uku sannan ya riski wani katon kogi kai tsaye ya dulmiya cikin ruwan ya nutse aciki. . Al amarin Sarbila kuwa tunda sarbilu ya sunkuceta bai zame ko ina ba sai dakin ta ya shimfada ta a daidai lokacin ne sarki maridu da wasu likitoci suka shigo dakin sarbilu ya daka musu tsawa yace kada ku karaso kuma ina umurtanku da kuyi maza ku fita tun kafi in dauki mummunan mataki akanku Sarki maridu da likitoci sukayi baya baya lokacin da suka futo waje sai suka taradda gaba daya daukacin jama ar kasar sun taru akofar fadar sarki maridu yace yaku jama ata lallai har yanzu kannai na suna fushi damu a bisa kin taimaka musu da mukayi a farkon wannan yaki amma kar ku damu mu kasance masuyi mata addu a tasamu lafiya Shugaban gidan bauta ya mike yace ranka ya dade lallai zamu kasance masu mata addu a kuma sam baza mu koma gidajan mu ba kuma baza mumotsa a nan ba baza mu ciba kuma baza musha ba har sai sarbila tasami lafiya koda kuwa zata shekara lallai muna nan. . Take kowa ya samu guri ya zauna yaro da babba mata da maza hatta tsofaffi suna nan suna zaman dirshan suna ta addu a shi ko sarbilu yana ta faman yi mata magani sai da yadauki tsawon sa o i casa in da biyu sannan ta farfado take ya rungume ta yafa kuka sai da suka dau lokaci mai tsawo sannan suka rabu da juna sai Sarbila ta mike ta shiga wanka bayan ta gama taci abinci ta kwanta sai da tayi kwana uku tana barci sannan ta farka. Akwana ukun nan sarbilu bai leka

Chapter 1 of 5