Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaki amma bamai nasara can dodannin suka fusata suka kara kaimi da himma suka addabi Zainur damiyagun hare hare nanfa lissafi yacanxa domin summa Zainur miyagun raunuka sukaishi kasa yabaje kamar yamutu aihakan nafaruwa Sai Zairura takwalla ihu Taruga aguje tanufi dan uwanta tana ihu tana xuwa Wani Dodo yasa hannu yamaketa bakita yafashe jini yai Feshi jini takwalla kara tabaje akasa alokacinne Zainur yabude ido yaga yar,uwansa akasa jini naxuba abaki wohoho aisai yamike yakwarara ihu yace kaitsinannu lallai kunkawa iyaka kuma kwanakinkuma,aduniya Sunkare tabbas yauce Ranar mutuwarku bakidaya Wani Dodo yakawomai sara Caraf Zainur yadamki hannun dodon yahadaguiwarsa jikake karass Zainur yakarya hannun dodon yakwarara ihu yakama kan yamurde dodon yafadi matacce shirm kamar ice Karr uba sauraran suka hassala gamida Fusata suka kwarma ihu da kururuwa sukai kan Zainur afusace shima yaikansu yadunkule hannayansa yarika tikar Dodanninnan yana kakkaryasu tamkar yana balla busasshe itace tamkar yana murde kan kaji haka Zainur yake murde Kan dodannin Zainur yahaukace yaxama kamar mahaukacin xaki ckin kankanin lokaciZainur yahallakasu bakidaya sannan yakwarara ihu Zairura da Lajmira suka rugo aguje Suka Rungume Zainur sufasheda kuka bakidaya jama,ar kayan maxa da matasaida suka hallara abakin koginnansuka kewaye Xainur Inda Sarkinsu yafara magana yanacewa muna godiya agareka yakai wannan bako hakika kataimakemu to muma xamu taimakeka abisa muradinka naxuwa Lambun Lajhur domin Samohuren So Mamaki yakama Xainur domin baifadama kowa wannan labariba kodako mai masaukinsa totayaya Sarki yasan wannan labari Domin jin tayadda yasani MUHADU ARUFAR SHAYIN RABI,U LELE MAISHAYIN GAYU KOBA KUDI AKAWO KOFIIIII #SARAUNIYA JUHA PART 4 J Lokacinda aljana Dufala taji bukatan tsohuwa cewwa tadauki Zainur da kanwansa takaisu lambun Lajhur sai idanunta sukai jajur hankalinta yatashi takwarara ihu tadubi tsohuwa tace baxai yuwuba lallai kisauya wannan bukata taki domin Lajhur samada shekaru dari bakwai babu wani mutun ko aljan da yataba xuwa yarayu lallai komai hatsabibancin halitta indai yatsinci kansa Lajhur to sai yamutu tsowahuwa tadubi aljana Dufal tace lallai inbanda wannan bukata nibanida wata buta aljanatafasheda kuka tace a,iya rayuwata mutane da aljannu sunnemi taimako awajena bantaba gaxawaba amma yau gashi abuguda yagagareni tabbas lokacin mutuwata tayi domin nayi rantsu adun lokacin dadana kasa cika wani alkawari danayima wani Mutum tokuwa xan kashe kaina take aljana Dufala taciro wata farar wuka xata burmama cikinta sai Zainur yace dakata yake aljana Dufala lallai xaki iya cika alkawarinki aljana takalleshi tayaya alkawarina xaicika Zainur yace idan harki karisa yankin Lajhur shine xaki hallaka tokidaukeni nida yar uwata kirage min hanya kawai baxan mancedake arayuwata kawai sai aljana tabusheda dariya tace maxaka shirya domin saina kaika dabda yankin lajhur Kawai saita sunkucesu tabace saida aljana lajhur tai tafiyar Kwanaki,arba,in asararin Samaniya sannan tadira awasu fararan duwatsu dingima dingima tsawo kamar xasu tabo samaniya Sai tada Zainur yakai babban jarumi kasani tsakaninka da Lajhu Tafiyace takwanaki uku ammafa zakajisune tamkar tafiyar shekaru uku domin akowace rana saika hadu da masifu marasa adadadi tabbas tsallake wayannan kwanaki Uku sune keda matukar wahala domin anakiran wadannan kwanaki Uku da kwanakin Mutuwa dayawamanyan jaruman Duniya aljannu damutane masu son xuwa Lajhur a kwanan dayan farko suke mutuwa kalilane suka taba wuce RananFarko amma kuma ba,ataba Samun wani mahaluki da yawuce Rana tabiyuba bai mutuba aljana tadafa kafadan Zainur tace amma kai inaji ajikina xaka karya wannan tarihi domin kai, Jaruntarka tasha banbanda takowa domin kai bajarumibane baka koyi yakiba sannan baka tsafi babu taimakon kowa kawai adalilin cikama kanwarka burinta kaxamo babban Jarumi maitar watsa maxa lallai inamaka fatan nasara kuma xakayi Kayya Aisai asaki waniRugugugi gamida tsawa hadi da walkiya sannan wata kakkausar murya tace karya kikeyi aljana Dufala Bashiba Kema ayau baxaki tsiraba domin yauce ranar mutuwarku tabbas kuma sai kun mutu aciki Fararan Duwatsu Kwatsam sai wasu fararan aljannu suka rika saukowa adingima dingiman Fararan Duwa tsunnan Aljana Dufala Tafashe da kuka AMIN AFUWA ABOKA RUBUTU BAYAWA UJULACE TATASO SARAUNIYA JUHA Littafi na biyar 5 Na Ibni Abdullahi Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com{#SARAUNIYA JUHA PART 5A} Lokacinda Aljana Dubala taga Fararan aljannu na saukowa daga Katon Farin Dutsennan Kamar saukan ruwan sama sai tafasheda Kuka tanacewa tabbas ranar mutuwammutatsaya domin baxamu tsallake kaidin Farar aljanaba da Jama,artaba Saida aljannu suka taru sama dubu arba,in sai akwarara ihu asakaki tsawa gari yabuga asaki wata Walkiya mai tsananin Karfi da Haske Kawai Saiga Farar aljana tana Saukowa daga Sama akan wani Farin Doki mai Fukafukai sannu ahankali tasauko kasa Dakarunta suka Sara mata Taimurmushi Sannan ta fuskanci Su,Zainur tace kai yaro lallai kasani Baxaka,iya xuwa Lambun Lajjuhurba Domin anan xaka Mutu Zainur yace ke aljana lallai tsakanimmu dake babu wata gaba danhaka Kada kija yaki yabarke atsakinimmu domin keda Jama,arkine Xaku mutu aljana tabusheda dariya tace kai yaro lallai Sharafar mutuwa nadibarka tadaga Murya tace kaitsinanne shin xaka Saromin kan kanwarkane da hannunka Koko sainasa ansaromin kanka Ran Zainur yabaci xuciyarsa takufula yakama Kafadar kanwansa yace toga Kanwata inka mai iya datsar koda gashin kanta Nikuma saina kasheshi ALJANA tafusata takwarara ihu ta umurci wani aljani dayadatso mata kan Zairura aljani yakwarma ihu yajijjiga Farar takobinsa yatunkari Zairura yana ihu aljana Dufala taceda Zainur lallai kayi kuskure domin Kaifi da tsini baya tasiri ajikinsu kwatakwata basa mutuwa Zainur yakalli Aljana Dufala yace to yau xasu mutu domin ita Muwa Dolece alokacinne aljani yakawoma Zairura sara cikin zafin nama Zainur yajanyeta yasa kafa yabanke aljanin tsananin karfin dukan saida aljani yaxube akasa wuyansa yakarye Wohoho ran aljannu yabaci suka kwarara ihu bakidaya sukayo kansa shima yakwarara ihu yaikansu batareda yarki makamiba akai haduwa irinta mutum da aljan nanfa aljannu sukasha mamaki domin Indai Zainur yagabxama aljani duka tofa sai yabaje akasa amma sai sumiki suci gabadakaimar sara Amma yarika Gocewa gamida xillewa anacikin wannan bakin artabune Wani aljani yakartama Zainur Sara agadan baya tsananin xafida xugi Yakwarara ihu jini yai Feshi wani aljanin yasokamar mashi akirji Yahuda Kirjin Zainur,Zairura takwarma ihu xatanufi Zainur Sai yadakamata tsawa yaceaa kanwata kitsaya a,inda kike, Zainur yadurkushe bisa Guiwowinsa jini natsiyaya akirjinsa da gadan bayansa Sarauniyar aljannu tabushedadariya tace wane yaro kuma wane uban yaro taima dakarunta tsawa tace kaiKubarshi adurkushe kusaromin kan,Kanwarsa domin yaga mutuwarta a idansa Wasu aljannunu sugoma Suka baxa aguje suna rigerigen Saro kan Zairura Kayya Zainur yakwarma Ihu yamike yakama mashin dake kafe akirjinsa yarintse ido yazaro mashin dakarfin tsiya yakwarara ihu saboda xafi yajijjiga mashin yacillama Dakarunnanda suka tunkari Kanwarsa daniyyarSare kanta yacilla musu Mashinnan Mashin yatafi a,aune damasifan gudu dakarfi alokaci guda Mashin yahuda Dakarunnan goma yatsiresu bakidaya suka xube agaban Zairura matattu Zainur yamake wani aljani yadauki farar takobinsa nanfa Lissafi yacanxa domin saradaya yakema aljanunnan suna wucewa kiyama yarikama Fararan aljanunnan kisan gilla yarika farke tunbinsu yana datse kawunansu kamar barnan Iska yaikaca kacadasu Sarauniyar aljannu takwarara ihu aikafin tarufe baki Tuni Zainur yadaka tsalle yadira agabanta yasanya tsinin wuka yasoke mako gwaronta ko ihubata samidamaryiba tasheka Barxahu inda Jiri yadibi Xainur yakife akasa ZAIRURA takwarma ihu tarugo aguje taje tatallabi dan uwantatarungumeshi tana kuka aljana Dufala takariso tabashi wani Ruwan magani yana kurba Ilahirin raunindake jikinsa yawarke Zainur yamike yakalli aljana Dufala yace ina godiya agareki dakikawomu wannan yanki xaki iya juyawa domin kincika alkawarinki aljana tace ina jinjina agareka namiji Uban maxaje lallai kasani Ayaudinnan kakafa babban tarihi aduniya domin babu wani Sadaukin Jarumi mutun ko aljandaya taba nasara akan Wadannan aljannu Anan sukai bankwana Tabace Sai Zainur yakalli Yar,uwansa yace yake kanwata kisani lallai hakammu nadabda cimma ruwa domintafiyar kwanaki Uku suka rage mana mu Isa Lambun Lajhur ammfa tsananin wuya da masifa dabala,indaxamu Fuskanta acikin wadannan kwanaki Uku daidai suke da tafiyar Shekaru uku Amma kadaki karaya Kuma kada kiji komai aranki domin nine garkuwanki Kawai ina rayuwane dominki Yadaga murya yace Lallai inamai rantsuwada Girmada Daraja Na yan,uwantakarmu baxan mutuba har saina cika miki burinki Zairura takasa koda motsawa tausayin Zainur yakamata tarika tuno irin masifu da bala,o,i da Zainuryashiga asanadinta kaiwa saita fasheda kuku tafada jikin Xainur tanacewa na yardadakai dan uwana Kaine rayuwata Suka rungume juna saida sudau lokaci mai tsawo sannan sukaci gabada tafiya acikin Fataran duwatsu suka fita sufada wanidaji maiduhu gamida bantsoro sukaita tafiya hargajiya tariskesu suka yada xango atushen wata katuwar itaciya Nansukaci abinci susha ruwa daga guzirinsu Kawai sai barci yakwashesu abinka da gajiyayyu tuniSushiga magagi kwatsam sai Zairura taji kamar antsikareta firgigit tafarka Nanfa hankalinta yatashi tsoro yakamata takama tsuma tana kakkarwa tatakarkare takwarara ihu mai raxanarwa KAI NATSORATA DUKDA BANGA ABINDA XAIRURA TA GANIBA atemakeni da kofin Shayi mai zafi {#SARAUNIYA juha;;;;;;;part 5 B} LOKAWCIN da Zairura takwarara Ihu Sai Zainur yafarka cikin Furguciarude baikalli ko inaba sai inda yaruwansa kekwance sukai ido biyu da ita yacemata Lafiya Zairura takasa magana Face taimasa nuni da hannu koda yakalli abinda tanuna masa Sai yaga wata kasace kwababbiya take xuvowa daga Sama guri guri har kimaniN Guri arba,in Zainunr yaciga dakallon Kasarnan tana xobowa tari tari saida adauki lokaci mai tsawo sannan kasar dadaina xubowa sannan tari tarin kasan suka rikide suxama wasu gabza gabzan aljannu na Laka masu tsananin Girma dakuma Muni aljannu arba,in na laka suka Hadu sukai Sahu Sukwarara ihu sannan babbansu yadakama Zainur tsawa yace kai biladama mai taurinkai lallai kacika Mahaukaci dakabiyema Rudin Mafarki kataho wannan mugun daji lallai kasani awannan Daji babu wani abu daxaka Samu Face mutuwa aljani yadaga murya yace tabbas Kaida Kanwarka Xaku hallaka Zainur yadakama al jani tsawa yace kai wawa Ita Mutuwa shawagi take Filin yaki kuma mai kwaran kwana take dauka lallai kasani tsakanin nidaku tabbas akwai masu mutuwa Amma kuma Sanin waye xai Mutukuma waye Xai Rayu tosai mun gwabxa yaki atsakaninmu Yadaga muryace kutahu Mugwabxa Yaki aljannu suka rafka Ihu sukai Kan xainur Shima yai kururuwa yaikansu Sukahadu sukacame da yaki inda Zainur yaraina kansa Kuma yashiga cikin tashin hankali Domin Idan yasa Takobi yasari aljannunnan Saikawai takobi taratsa jikin aljani tawuce akarke yakoma yade domin lakane inko yagabxama aljani Naushi to hannusa sai yanutse atabo amma idan aljannun nan suka dakeshi Sai yaji kamar Guduma sukamakamasa inko suka sareshi Tuni gurin kedarewa jini yabarke nanfa aljanun laka su arba,in sukarikata Zainur daduka Sara da suka Saida su yankeshi awurare arba,in ilahirin jikinsa Jini ke Xuba jiri yafara Dibarsa idanunsa Suka Fara Kafewa yafara ganin uku abiyu yatafi kasa xai Fadi sai yadogare abisa takobinsaDuniya tarika Juya Masa Sannan yarika ganin aljannun lakannan sukai Dubu arba,in Koda suga sunmai mummunan illa sai sukaja baya Sannan sukece dadariya Shugaban aljannu yace kai Jarumin maxa lallaibaxa mukashekaba anan xamubarka Kaci gaba da xuban jini Har jininka yakare kafadi ka mutu Sannanagaban idanunka xamu tafi Da yaruwaka Xairura kuma babu abida xaka iya Kawai sai Yai Umurni da wani aljanida yadauko Xairura aljaniYasungumeta Yasabata awuya Sukama Tafiya Kaiyya Nanfa Xainur yakama tunani halin dakanwasaXatashiga ahannun tsinannun aljanunnan yatuna lokacinda suke yara dakuma alkawarin da yaima mahaifiyarsu cewa shine xaixamo Garkuwanta baxai taba Barin wani abu yacutarda itaba ,amma yau gashi agaban idansa aljannu xasui gabada ita Dankari yatuna rantsuwa da alkawarin da yayima Kanwarsa cewabaxai mutuba har Sai yakaita Lambun Lajhur tatsinki Furan So da hannunta yabude idanunsa dakyar yaga Yar ,uwansa akafadar aljani tana kwalla ihun tana kuka tana neman taimako Kaico Zainur Yatsani yaga Kanwansa naxubda hawaye Sai yaji kamar rantane ke Futa aisaiyarintsa idanunsa Sannan yatakarkare yakwarara ihu wanda bakidayaSaida Dajin ya ammsa yamike aljannun lakannan suka juyo suna mamaki Zainur yadaka musu tsawa yace kai tsinannu kuna mamakin mikewatace lallai kusani Koda Mutuwa nayi inhar Kayi yunkurin cutarda kanwata tofa sainadawo dominhukuntaka aljannu sukece dadariya Sannan suka murtuke Fuska,shugabansu yadubi Zainur yace bamuyiniyyar kashekaba amma tsaurin idonka gamida taurin ranka tasa dole saimun kasheka kafin mutafida kanwarka shugaban yadubi wani aljani yace kai TURkuxa maxa kasaromin kan tsinannance aljani Yakwarara ihu yagirgixa takobinsa yaifutan burgu yaikan Xainur shima Xainur yakwarma ihu sannan yakarta Takobinsa ajikin wani katon Dutse Wata gagarumar wuta takama asaman dutsen gagga gagga Zainur yabar takobinsa acikin Wutar inda shikuma aljanin yacigaba da tunkaroshi yana ruri saida yaxo dabda Xainur ,sai Xainur yajawo Takobinsa dake cikin Wuta tayi jaja Wur kamar Garwashi aljani yakawoma Xainur Sara daniyar Sare masakai cikinxafinnama Yagoce sannan yasokama aljanin Laka takobin aciki aljani yafasa kururuwa masifar xafin wuta yaratsa ilahirin jikinsa take yabushe yatar watse aljannu suka kwarara ihu sufusata Sukayo kan Xairur bakidayansu inda shima Yakansu takobinsa na hucin wuta gamida tartsatsi Wuta ya,afkama aljannunan da sara da suka nanfa lissafi yacanxa domin duk aljanin Da yasara take yake kamawada wuta yaki yasarke aljannun sukarika Kaimar miyagun Sara da suka amma Xainur yarika gocewa yana tafkamusu sara aikoda adauki Lokaci ana wannan yaki Sai akanemi aljani daya akasa bakidaya Zainur yahallakasu Zairura tarugo aguje tarungume dan uwanta tana kuka Shiko sai yajanye jikinsa yakama hannunta suka fada cikin daji aguje yana dube duben Gan yayyaki dakuma Itatuwa har yasami abinda yakeso wani jan itaciyane medauke da wasu yankananan yaya take yakamacin yayan itaciyar aifara cin yayan itaciyar keda wuya sai Xainur yakwarara ihu yayanke jiki yafadi yakama aman jini bakinkirin hankalin Zairura yatashi tarika Rungume dan uwanta tana kwarma ihu saida xainur yadauki lokaci mai tsawo Sannan aman yadakata Sai yakalli kanwarsa yace kikwantar da hankalinki yaruwa wannan yayan itaciyan suntaimakenine wajan fudda dafin takubban aljannun can domin takubbasu nadauke da mugundafi Awurin Sukwana Washe gari sukai damarasuci gabada tafiya suna cikin tafiya sai sukaxo wani Fili da wata katuwar bishiya mai siffan Bil,adama Zainuri yakama hannun Kanwarsa yace karki Kara kallon itaciyarnan Kawai Sai suji itaciyar takama Babbaka dariya Tanacewa KUHALAKA,SHAYI,YAISOFA #SARAUNIYA,,,JUHA;;;;#PART;;#5C Koda Zainur yaji bishiyarnan tayi magana sai yarike hannun xairura yatsaya cik yafuskanci Katuwar bishiyannan mai suffan dan,adam kawai sai wani katon reshe yaxaxxago daga bishiyan yakawoma Zainur duka cikin xafinnanama Zainur yakauce yasa gatari yasare reshen jini yaitartsatsi Mamaki yakama Xairura dan uwanta yace kin dauka bishiyace to aljanace kuma kwanantane yakare domin Saina kasheta Kawai sai yaji bishiyar tabusheda dariya tanacewa karya kake yaro lallaikaine xaka mutu sai bishiyar tai girgixa amaimakon ganye sufado aisai aljannu suka rika Fadowa bibbiyu kamar kashin awaki ko wannensu narike da mugun makami Zainuryakaremusu kallo sai yai murmushi yaxaro Farar takobi wanda yakwata awurin Fararan aljannu yajijjigata yakwarara ihu yafalfala aguje suma aljannun sukayo kansa suka hadu sukai Kwaram kwatsam nan Sufara masayan takubba yaki yakaure jama,ar aljannu sunsha mamaki domin yanka aljannunnan yake Kamar goji yaimusu raga raga kawai sai yaji jijiyoyin bishiyarnan tadaddaureshi tamau tana neman fasashi dakarfin tsiya tsananin matsa saida Xainur yarika kwarara ihu yakasa aikata komai yasallama raidarayu yadauka mutuwarsa taxo wanikwallan bakin ciki datakaici suka gangaro a,idanunsa yafara ganin taurarin mutuwa hankalin Zairura yatashi ganin dan uwanta xai halaka tarika kwarara ihu tana kuka kaikoda taga kuka baxai mataba saita rarumi takobi taikan itaciyarnan daniyar soka mata kawai sai wani Reshe yamaketa taisama tafado agalabaice wohoho ai Sai Xainur yakwarara ihu yadauka Xairura ta mutune yaji wani karfi na ban mamaki yashigeshi yakara Kwarma ihu dakarfin tsiya yakarkatse jijiyoyin bishiyar Yai wani tsalle gamida alkafira Sau,uku yasokama bishiyar tsinin takobi atsakiyarta akwarma wani ihu yadire kasa yadaga takobi yas yaraba bishiyar gida biyu take bishiyar takamada wuta takone kurmus Xainur yafalfala aguje yanufi inda Zairura ke kwance yadauketa yajijjigata tafar fado sukai ido biyu sai suka rungume juna banyan sun huta sai sukaci gabada tafiya cikin tashin hankali domin sunsha matukar wahala sun karo da masifu marasa adadadi natsawon kwanaki ukunnan inda suka debe tsamani da rayuwa amma akarke Sai suka tsinci Kansu a Bahar Lajhur Babban kogine da Sai ka haureta xaka shiga Lambun lajhur koda suka iso bakin koginnan sai farin ciki ya lullubesu domin daga inda suke suna hangoLambun Lajhur tobayan sungama murnan sai murna takoma ciki domin sunyiduba iya dubawansu amma babu wata hanya daxata kaisu Lajhur dole sai sun ratsa ta Bahar Lajhur nanfa idanunsu yaraina Fata domin ganin idanunsu miyagun halittun ruwa kekai kawo acikin kogin Bahar Lajhur Xainur yaceda yar uwansa lallai indai munaso mu,isa Lambun Lajhur tofa dole mu sana,anta Jirgin ruwa nan sukama Saran manyan itatuwa sukama kera Jirgin Ruwa tsawon kwanaki Goma Sannan suka gama hada Jirgin ruwan bajira Xainur da XAIRURA Sukashiga sufara tuki sutunkari Lajhur saida sukai tafiya mai nisa lafiya babu wata matsala har suka kusa futa acikin kogin to asannanne ruwan yafara tangal tangal yana toroko yana tsiri sama ruwa yacika jirginnasu yafara kokarin kifewa Xainur yadage da tuki cikin wahala damasifa saikuma akwatsatsa tsawa mai bantsoro gari yakama rugugi sama tai bakinkirin Kawai sai akece daruwan Sama kamarda bakin kwarya gogin tacika tukin jirgin yafi karfinsum Jirgin Ruwan yajuye Zairura tabi Ruwa amma Sai Zainur yabita yakamota yarike gefen jirgin inda sukarika Watan gariya acikin Koginnan tsananin wuya saida Xairura tasuma Sau uku tana Farfdowa amma duk wuya duk rintsi Xainur bai saketaba har yainasaran juya jirgin ruwa yasanya Xai rura shima yashiga kuma Sai ruwan Saman yadauke dif Xainur yaci gabada tuki kwatsam saikuma akara kwarara ihu sai gawusu miyagun halittun ruwa sun bayyana asaman ruwa tamkar suna taka kasa haka suke tsula gudu abisa ruwa dakafafunsu da makamansu tsira ahannu sutunkaro Su Xainur tako,ina Tsananin Furgita da tsoro sai Xairura tafasheda Kuka takalli dan,uwanta tace lallai munratso masifu da bala,o,i masu yawa muntsira amma awannan karan baxamu tsiraba takara Fashewa da kuka tanacewa tabbas wannan abin bakin cikine Saida muxo gamu ga Lajhur sannan xamu mutu Zainur yakamu da tsananin tausayinta sai yaceda ita Yake kanwata lallai kisani Ruwada iska mutun da aljan baxasuhanamu karisawa Lajjhurba tabbas burimmu xaicika yace maxa kici gabada tuka jirgin kadaki tsoro kuma kada kikaraya nine nan xanxame miki garwa yadaga murya yace tabbas duk wanda yace xaishiga tsakanina da burina toko wanene Sai yamutu yakwarara ihu yaxare takobinsa nanfa ashiga danbarwa domin duk aljanin da yakusanci Jirginnan yaxamo matacce yaki yakame atsakaninsu ahaka harsukai gabar kogin Xainur ya Sunkuci Zairura yajefata tudu shima yadaka tsalle yadira kusa da yar,uwansa atare suka mike suka rungume juna Sannan suki junansu suka kalli kofar shiga Lambun Lajhur cikin Farincikida xakuwa cikin xumudi suke tafiya sutunkari Kofar Shiga Lammbun Lajhur saida suka xo dafda kofan Shiga Lakhur Sai akwarara wani Sakaran ihu gamida kururuwa wata kakkarfan iska tatashi Bakar Guguwa taturnuke ko,ina Zainur da Xairura suka ja baya saida adau lokaci iskan nakadawa Guguwan na toroko ana kwarara ihu da kururuwa Can akadaina jin ihun da kururuwan sannu ahankali iskar talafa Kuran ta yaye guguwar ta bace To awannan lokacinne Xainur yai toxali da tashin hankali domin duk tsananin dakewarsa da jaruntarsa saida xuciyarsa tabuga yajada baya cikin kaduwa Itakuwa Xairura tuni Tasume Nikuma NAFUTA AGUJE NAI RUMFAR SHAYI kai abokai nafa Tsorata#SARAUNIYA;;;;JUHA #PART;;;;#5DBakomai yatashi hankalin Zainur ba yakuma furgita Zairura harta sulalekasa sumammiyaba sai wata wata narkekiyar macijiya mai kai uku tsawota yakere bishir dogon yaro girmanta yafi katuwar bishiyan kuka kamta nafarko feshin wuta yakeyi kaina biyu aman dafi yakeyi Kaina Uku kuwa sara takeyi dashi koda Xainur yakalli wannan macijiya sai yatabbatar akwai rikici babba yana naxarin yadda xai afkamatane sai macjiyar tadakama Xainur tsawa tace kai mahaukaci lallai kacika wawa asoyayyar kanwanka dakabiyema yarintarta har kukawo kanku ga mutuwa tacigabada cewa yakai Zainur hakika jarumtarka da xumuncinka sun birgeni sam banaso inkasheku saboda haka ina mai baka Shawara daka dauki yar uwanka kukoma inda kufuto domin burinkubaxaitaba cikaba Zainur yace waceceke daxakice inhakura da bukatata lallai abudayane xaki fadamin in yarda shine kijanye jikinki kiban guri inshiga Lambun Lajhur nida kanwata domin cikar burinta nakarshe aduniya Macijiya tafusata taiwani huci takumbura ta sacce afusace tadakama Zainur tsawa tace kai wawa to kuwa xaka mutu abanxa domin baka dakarfi da jarimtarda xaka,iya shiga wannan Lambu na Lajhur kasani jaruman duniya aljannu da mutane sama miliya dubune sukai kokarin xuwa Lajhur wasu tun ahanya suka rasa rayuwansu wasu kuma suntabuka abin kirki wasu kuma awannan kofa suka mace kamar yadda kaida kauwarka xaku mutu ahannuna Wannan kalami namacijiya yabatama Zainur rai domin babu abinda yatsana, sai ka ambaci Mutuwar kanwansa, tofa komai xai iya Faruwa aisai yafusata yatunxuru yakwarara ihu yadakama maciyarnan tsawa yace ke bakar tsinanniya lallai ina ganin girmanki domin afarko kinyabeni kuma kinyabe Soyayyar danakema kanwata asaboda haka kikaucemin ahanya inwu cikin Lambun Lajhur nikuma Xan barki Kirayu Wohoho Kalaman Zainur sai suka xamo tamkar ruwa xafi yawatsama macijiyannan taiwani kuwwa mai Furgitarwa tairimi taiwani Sulu asama tasakanta daya tadaki kirjin Xainur tsananin xafi saida yai sama yaiwatsi dajini tabaki tahanci sannan yaje yadaki Wata katuwar bishiya take bishiyar takarye tadanneshi Xainur yayunkura dan yamike amma Sai yakasa daga bishiyarnan yayi iya yinsa amma yakasa aisai maciyarnan tabusheda dariya tace wane yaro Kuma wane uban yaro, tace saida nagargadeka amma taurinkai irinnaku na Bil,adama saika kangare kakama jayayya dani, takara bushewa dadariya tace lallai koda bishiyarnan bata dannekaba to baxaka rayuba domin nadaki jarumai maxada mata aljanu da mutane dawannan kannawa mai albarka babu wanda yataba Rayuwa tace na baka shawara kakoma kasarka kaida kanwarka domin xumunciku yadore kaki to yanxu agabanka xan hadiyeta sannan inyi tafita cikin Lajhur kaikuma kamutu da bakincikin mutuwar kanwanka sai tanufi inda Zairura ke yashe akasa sumammiya Hankalin Xainur yatashi yayunkura dan yature bishiyar data danneshi amma sai yaji komotsata yakasa yafasa kururuwa alokacinne macijiyar tasunkuci Xairura tafara yunkurin Hadiyeta Dankari ai Sai Xainur yakwarara wani Sakaran ihu wanda saida duk wata halitta dake wannan daji tatsorata hatta itakanta maciyarnan saida tagirgixa tadakata ta,ajuyo domin tai ido biyu da Xainur to alokacinne tasha mamaki domin ganinshi tayi agabata yana tsaye Yana wandamdam yana hamham kamar xai fashe domin Ihun da yakwarar yayine tareda wani yunkuri inda yai fatali da Itaciyar da tadanneshi Kafin macijiyar tagama mamakin jarumtarsa tuni Xainur yasokamata Wuka abakin da take rikeda Xairura tsananin masifar xafida Xugi tuni tasaketa Zainur yajayeta yakaita gefe guda inda yadawo yafuskanci macijayarnan bakinta naxubda jini, sakamakon sukan da yaimata afusace takawomai sara yakauce tawatsomai wuta yakara gocewa takwararomai ruwan dafi mai guba namma yakauce tai wani yunkuri da kugi takara makamai kanta, yai sama tabude bakinta maikama da kofangari zata hadiyeshi cikin Sauri irinna walkiya asaman Xainur yawulkita jikinsa yafado kasa dasauri yamike takawomai duka da bindi yatafkamata sara jini yai tsar tuwa Macijiyar tafusata taigunji tairimi takara tsawo sai tasa bindintata makama Xainur tsananin karfin duka saida yakusa suma tasanya bindin nata tanannadeshi tafara matseshi tana niyyar fasashi tsananin xafida xugi Xainur yaji kamar ana sassara kashinsa da gatarin wuta yarika kwarara ihu macijiyar tanufi Xairura gadan gadan domin ta hadiyeta nanfa hakalin Xainur yatashi yakwarara ihu inda yakwalama yar uwansa kira yanacemata tagudu xairura tafuta agujje macijiyar tana nannanade da Xainur dam sannan takifa da xairura da masifan gudu nanfa akasa tsere tsakanin Maciya da Xairura ga kuma Xainur natsakanin Mutuwa da Rayuwa Zairura tadage da gudu kamar ranta xai futa Itama macijiyar na binta da masifan gudu tana kakkarya manyan itatuwa inda duk masifan da zainur keciki na matsar macijiyarnan wanda har aman jini yake yi tabaki ta hanci amma bata rayuwansa yakeba ihu yakeyi yanacewa Kanwasa tadage taci gaba da gudu kada tasaya domin ceton Rayuwanta KAI WANNAN GUDU KAMAR GUDUN KARSHE NIBAXAN IYABA SAI NA NEMI sinadari SHAYI DAN MISIRA DOMIN SAMUN KUXARI NASHAFCE XUWA RUNFAR SHAYI ABOKAI ;;,#SARAUNIYA PART 5D,,,#5E,,,;;; Lokacinda Macijiyarnan tatasa Xairura agujee gashitana nannade da Zainur saitarika kakkarya manyan itatuwa tana kaima Xairura kamu da bakunanta tabbas tanasone ta hallaka Zairura koda XAinur yaga Macijiyar nadabda kama yar uwansasai yakwalama yar uwansa kira yace yake Xairura lallai kisani baxaki iya tseRema wannan tsinanniyar macijiyaba sannan nima baxan iya kwacewa daga rikon da taiminba yanxu kinufi lambun Lajhur kaitsaye dankari Xairura takarkata akalan gudunta tanufi Lambun Lajhur da masifan gudu kamar wata iska wohoho aikoda macijiyannan taga Xairura tanufi lajhur gadan gadan saimacijiyar takwara ihu tabi Xairura dagudu tana fesamata Wuta da ruwan dafi amma bata samunta indaitako Xairura ko waigowa batayi burinta tajita acikiN Lajhur Saida yarage saura kiris tashige Sai macijiyar tainasaran watsama Xairura ruwan dafi akafarta Xairura takwararaihu saboda masifar xugi taisama tafado adokin kofan Lambun Lajhurtana wani nunfashin Futanrai kaiyya Xainur yakama Wutsul wutsuldin kwacewa daga rikon da maciyar tamai amma yakasa hankalinsa yatashi yarasa abinyi can yaga ZAIRURA tafara futarda wani farin Kumfa abakita tana wani doguwarmika tabbas tana yunkurin Mutuwane kawai sai Xainur yakwarara ihu yahangame bakinsa yakafa ajikin macijiyar yacika bakinsa dam danamanta yamaka mata cixo iyakarfinsa yarintse idanunsa yaki sakin inda yacixa wani masifaffen xafine daxugi yaratsa ilahirin jikin macijiyarnan tuni tasaki Xainur ammashi saiyamanne acikinta yaci gabada fafara mata cixo macijiyar tairuri tai birgima taitsalle amma Xainur yaki sakinta har tagalabaita tabilafiyarkasa tamkar tamutu sannan yasaketa bakinsa cike dajini yanufi Xairura yasungumeta Macijiyar naji tana gani Zainur yashige cikin Lambun Lajhu ai yana shiga sai arafka guda anacewa tabbas Zainur dan Zairu yacika babban jarumi yashigo lajjhur aminci yatabbata agareka kaida knwarka kuna cikin yardada salama kushiga lajjur kuyi ko kwana nawane kudauki duk abinda kukeso domin kuncancanta Wani abin mamaki shine tunda suka shiga Lajhur shida kanwarsa suka sami cikakkiyar natsuwa da lafiya surikayawatawa acikin lambun harsu isu inda Furan SO yake koda Xairira taga Furan SO saita fasheda kuka tarungume dan,uwanta tanacewa kaikadaine gatana dan TALLATA HAJARKA A SHAFIN HAUSA EBOOKS AKAN FARASHI MAI RAHUSA . Shafin hausa ebooks shafine dake kawo ma yan uwa hausawa littatafan hausa cikin manhajojin PDF,TXT da doc, . A kowacce rana sama da mutane dubu biyar ne 5000 ke ziyartar shafinmu, hakanan sama da mutane 4000 dubu hudu ne ke download na littatafanmu, hakan yasa muka bude sashin tallata haja, . Inda duk wanda ya bukaci mu tallata masa hajarsa, zamu sanya a cikin shafinmu da kuma ebooks namu, wato littatafan mu, akan kankanin farashi . TSARUKAN TALLA DA KUDIN BIYA . 1, ADS in site, tsarin farko wanda ya danganci saka hoto, ko bayanin hajarka a sama da kasan shafinmu inda kowanne mutum ya shiga shafinmu zai gani, muna cajar dari biyar N500 akan wannan tsari, sannan yana karewa bayan kwanaki 31, 2,ADS in Ebook, tsari na biyu wanda shikuma yana fitowa ne a cikin littatafanmu, Makaranta da manzarta zasu runga cin karo da tallan hajarka yayin da suke karanta littatafanmu, Nuna cajar N100 akan wannan tsari ga kowanne ebook, . Kafin fara kasuwanci dole kana neman mutane su san abun da zaka siyar, Wannan tsarin zai yi matukar temako musamman ga Masu buga littatafai suna siyarwa, da masu senyawa a Okadabooks, da ma dukkan wani dan kasuwa . Domin tallata hajarka sai ka tuntube ni ta wannan namba 08181619967 Shuraih Usman 99% Chief executive officer @ www.hausaebooks.com.ng Gargadi, bana whattssap, just call me or send msg uwana ina alfahari dakai haka sukasance AcikinFarinciki tsawan kwanaki talatin suna rayuwa a Lajjhur sannan Zairura tatsinki Furen so Suka hau Doki maitashi yai sama dasu acikin kwanaki Bakwai dokin yakawosu kasarBannar dankari aikoda suka shiga cikin gari akai idobiyu dasu sannan jama,aa suga Furen So ahannun Xairura sai bakidaya jama,ar kasan sukai dafifi suka daga Zainur da Xairura Sama ana musu kirarin manyanmasoya yan,uwan juna makada suka saki ganguna mawaka sukarika rerama Xainur da Xairura wakokinyabo ba,axame ko,inadasuba sai gidan Sarki inda Sarki Hamma yasa musu albarka kuma aimusu Sarauta akasar Bannar tundaga wannan rana Sunan Zainur da Xairura yai gwauron suna aduniya inda manyan sarakuna sukarika xuwa ganinsu suna musu manyan kyaututtuka daganan kuma Manyan Sarakuna da yayan sarakuna da JarumanDuniya da attajirai da yayan attajirai sukama neman auran ZAIRURA domin bokaye suntabbatarda cewa duk kasan da Furan SO YAKE tokasar xata samu karuwar arxiki da xaman lafiya manema sukarika yimatatururuwa amma babu wanda Xairura ta amintadashi saboda tayi,imanin mafi yawancin masoyannnata basan gaskiya suke mataba suna suntane Saboda Furen SO KwatsamSaiwani kyakkyawan dan Sarkimai suna

Chapter 6 of 15