ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara ni."
Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan Sallar magriba, duk yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba."
Sury ta ɗan yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa."
Kabir ya yi saurin faɗin, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo mana kansa ba za mu daɗe ba, muna gama gani za mu wuce."
Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yin sallama da ita ya koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓa ta ranta.
Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta ce.
"Gaskiya sai dai idan kunnenka ne."
Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba, amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce, "Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina wayarki take?"
Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa.
"Tana falo!"
Ta ba shi amsa a taƙaice.
Falo ya koma ya ɗauki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya ce.
"Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane ɗauko mini suna drowerta."
Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buɗe drowersa ta ɗebo masa hulunan ta ba shi, sannan ya sake fita. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan ta furta.
"Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana da key da yake buɗe ƙofa. Ya zama dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala."
Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar.
"Hello!"
Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya a can ƙasa, sai kuma ta ji muryar Abdul yana kuka.
"Wai kana nufin ba ka fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?"
Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a kan Maimuna ya ce.
"Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita nutsuwata take yi ba."
Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta kwaɗaitu ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata.
"Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je ni kaɗai, shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba."
Nazir ya kwaɓe murya kamar wani mace ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya yi mini irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da mutuwar sonki kuwa..."
Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba.
"Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake son mu rabu lafiya."
Wani irin mugun kallo take jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka iya yi mata rashin mutumci ba ni zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko wacece."
Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar a kashe take, amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni faɗa da iyalina ina zaman lafiya da ita."
Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka ta a blacklist, sannan ta ce.
"Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ma ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula 'yanmata."
Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai.
"Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka."
Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!"
Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa." Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gama ta leƙa gidan Maimuna.
Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronta. Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin idan Jafar ya yi mata laifi, matuƙar shi ne ba shi da gaskiya har kusan tsugunna mata yake yi.
Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiye wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da ya shiga cikin shagonsu yana duba wayarsa ya ga misscall ɗinta. Hannunsa har rawa yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki.
"Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kake bala'in jin tsoronta."
Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haɗu ai za ki gane ni jarumin gaske ne "
Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta.
"Yanzu dai ba wannan ba, na lura haɗuwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fi so na dinga ganinki ina jin daɗi ko na samu nutsuwa."
Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?"
"Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi, kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba."
'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?'
Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daɗi.
"A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci."
Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faɗin, "Lafiya My Moon, ko kina da wata damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka." Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?"
Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki."
Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo maka account number ina zuwa." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake.
Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury. Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa tana faɗin.
"Mu haɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni a bakin layin ƙarshe."
Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya bi. Yana zuwa a daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce.
"Lah bai gane matarsa ba."
Da sauri ya waiga, cikin mamaki yake bin ta da kallo.
"Wai baby ke ce?"
Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idan hagu ta ƙi sai a koma dama. Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka. Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe."
Kabir ya kanne mata ido ɗaya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa yau na yi kewarki."
Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yake fargabar wani ya gan shi, kuma a yanzu kowaye ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce.
Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata.
"Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayan wani lokaci zan taɓo ki a waya sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafunci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta ƙofarsa ta langa-langa ce."
Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta ƙaraso.
Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga haske cikin gidan.
Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta, fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi tsam, tana faɗin.
"Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata nawa ba a gama ba?"
Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga yawo da hannunsa a jikinta. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmu ba zai haure shekara ba."
Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga a ciki, sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa.
Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za ta zo ganin gidansa, ya ci alwashin saninta a wannan ranar. Yana tsaka da yawo da hannunsa a jikinsa, ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba.
"Mene ne wannan?"
Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace.
"Gabannin magriba period ɗina ya zo!"
Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?"
Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba?" Ya sani sarai, domin Fauziya duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba, ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi, tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri, ya sa ya ɗauka don ya ji abin da za ta faɗa masa.
"Hello!"
Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!"
Ya ɗan yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu Banat, ya jikin?"
Ta amsa masa tana wurga masa tambaya.
"Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?"
Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa ya faɗi.
Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina za a sallame ni."
Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana shirin yin magana ya ce.
"Ayi mini afuwa."
Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba da sarrafa shi. Sai da suka ɗauki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da guga ya yi wanka da ita sannan suka fito daga gida.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[12/02, 22:24] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA HUƊU
Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta. Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje.
Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida, shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran abokinsa Abbati ya shigo masa.
"Ya Abbati kana iya?"
Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh yane kake yi wa mutane."
"Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne. Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna."
Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati, Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi."
"Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza mana, don Allah ka taho muna jiranka."
Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani lokaci tuni ya yi wa kansa caji.
Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce.
"In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..."
Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali.
"Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo."
Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa.
"Don Allah... kar ki min faɗa... ni babu abin da na shaaaa..."
Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru.
"Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi bacci... ki zo ki buɗeeee."
Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi.
"Fauzinaaaa."
Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi. Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe da tafi A'ilo ta ce.
"Ke dai Maman Sabir a kullum maraɗinki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faɗa ɗakin da ba na ki ba."
Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini ban ji da daɗi ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba yana jirana."
Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya.
Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi zaraf ta leƙo ya ce.
"Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili."
Tana faɗar haka ta koma ɗaki.
"Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki."
Maman Sabir ta furta cike da tsoro.
Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka.
Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce.
"Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu ƙari."