Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka. "My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?" Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana." Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu." Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..." Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [12/02, 21:42] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYU Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faɗuwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar. "Abban Na'ima wankan kenan?" Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo ɗaya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a ɗan diririce ya ce. "Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe ɗaurin aure ban gama mata ɗinki ba." A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa. "Abban Na'ima!" Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi. "Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?" Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce. "Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya." Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata. "Hello!" Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa. "Uwar gida sarautar mata!" Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi. "Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaɗai." Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya ɗauki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana. "Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni." A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri." Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya ɗauka ya wuce banɗaki, ita kuma Fauziya ta wuce ɗaki duk sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba. "Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane. Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan. Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar. Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar da su a ɗaki. Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren, ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe. Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa, ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki. Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce. "Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan shaye-shaye ba ne." Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi. Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta. "Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin A'ilo ya faɗa." Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin. "Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara ne kuna zaune za su ba ku kunya..." A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka, za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata kai sannan ta ce. "Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba." Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda mata magana da habaici haɗe da yin dariya. "Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana shaye-shaye?" Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce. "Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake jin kun faɗi haka." Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta." Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a ɗaki kuna yi kun ji." Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta. Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin. "Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?" Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta nake yi." Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?" Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake yi." Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta cigaba. "Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi." Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta yi ai ɓata masa rai kika yi." Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba." "Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai tsaya ɓa ta lokaci a kanta..." Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya. "Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu kawai." Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu babu macen da yake kulawa." Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci na fita, na ƙara wani laifin." Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce. "Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi sallama A'ilo ba ta amsa mini ba." Fauziya ta furta, "Hmmm ke dai bari, wallahi shi ya sa zaman gidan duk ya gundure ni." Fauziya da Sadiya sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa. Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can ɓangara aka ɗauka. "Barka da safiya sarauniyata!" Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai." "Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar muryarki." Jafar ya furta cike da sha'awa. "Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na sallami yara." Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu ruwana, kai da Maman Nana." Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!" Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa. "Na'am Abban Nana!" Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce. "Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faɗa. Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai." Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce. "Baby ya yi?" Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a cikin zuciyata." Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa ya ce. "Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar." Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba. "Moon! Ba ki ce komai ba." Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce. "Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa ɗaya muka." "Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haɗu a unguwa ba. Wallahi ko hotel zan iya kama mana..." Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!" Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta. Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa. "Maimuna da wa kike magana?" Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce. "Ni... ni... kuma?" Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi. Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?" Sury ta ɗan haɗe fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya ɗaya matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni gidan da kake gini?" Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce." Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir. Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani. Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka. Yana ɗauka ya ji ta fashe masa da kuka, shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa. "Kukan na mene ne?" Kabir ya furta cikin tattausan lafazi. "Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata. Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake azabtar da ni Kabir?" Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?" Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau." Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki." Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka zo." Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaɗaitar da shi irin salon tata soyayyar. Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai gaskiya ɗinki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan haka ma, Oga yana raba mana ɗinki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai zuwa gobe za ki gan ni." Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina ɗaukar wayata ji nake kamar mun shekara ɗari uku." Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago. Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir? Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji daga gare ku.😄 Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [12/02, 22:13] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA UKU Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan Azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, a zuwan ya ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa ɓacin ranta. "Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi. Na kai kwana nawa ina son

Chapter 2 of 11