Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [12/02, 21:41] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA ƊAYA Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake ɗamfare a birnin zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raɗaɗin da ke kwance kane-kane a cikin ranta. Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta. "Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne, za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana." Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin magana A'ilo ta sake katse ta. "Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake faɗo mini ɗaki sai mun sheme shi." Ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya sa ta yi musu shimfiɗa a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa 'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce ta mayar da yaranta ɗaki. A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir. Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. Gyangyaɗi take yi daga zauna, don haka ta kishingiɗa da gefen gadon. Don kada ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya yi awon gaba da ita. "Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni." Kururwar Fatima ta katse mata daddaɗan baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta. "Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?" Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance. Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiɗe, duk ta gama gigita ta. Hijabinta ta ɗauko, ta ɗauki Fatima mai kimanin shekara uku ta goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuɗi, amma ita kanta ba ta da tabbacin za ta samu kuɗi masu yawa. Naira ɗari biyu taci karo da ita, da sauri ta ɗauka ta fita tsakar gida, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama. "Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa." Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta harbe ta." "Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu ɗaya ba." Lawisa ta furta tana daga ɗaki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta ɗaga labule ta miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta." Fauziya ta karɓa tana faɗin. "Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya." Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya." Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis ɗin da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari. 'Bayan kemis ɗin Bala ina zan kai Fatima?'' Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta sake ɗaga waya ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da bayanta suke yi. Ta ɗan jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya da ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo. "Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?" Mai ɗan sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma. "Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis." Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta ɗan waiga ta ce. "Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki." Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni, wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka." Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su. Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu ɗari biyun don ya ɗauki kuɗinsa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa. "Assalamu alaikum." Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar. "Don Allah Kabir fa?" Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi. "Hajiya lafiya?" Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce." Sai a lokacin mutumin ya ɗan faɗaɗa fara'arsa. "Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i, ni kaɗai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi." Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki fuska ta ce, "To shi kenan na gode." Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko Allah zai sa ta shiga. Bugun farko ta ji an ɗauka, don haka ta yi saurin faɗin. "Hello." Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne ya maimaita abin da ta faɗa. "Abban Na'ima kana jina?" Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin wurgar da ita. Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga duk lamba ɗaya ce da wacce ta kira da farko. Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar shagon tana faɗin. "Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe ta." Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya ɗebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce. "To nawa ne kuɗin?" Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaɗaya kuɗinki dubu huɗu da ɗari biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huɗu ba za a saye ta ba ta ce. "Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi ɗari biyu ce kawai a hannuna." Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta. "Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini ba ki da kuɗi, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huɗu da wani abu ki tafi da su ba." Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..." "A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da safen sai ki kawo kuɗin. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuɗin allurar da na yi mata." Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a aljihunsa yake ciko. A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta. "An ya Kabir ɗina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta tana sake tuna muryar wacce ta ɗauki wayar. "Kabir ɗina babu macen da take gabansa." Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima shimfiɗa a tsakar ɗaki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan. Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki. Suna shiga ɗaki ta ɗebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba. "Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba." Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin 'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi a cikin zuciyarta. "Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka. "Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir ɗinki kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waɗannan kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?" Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za ta taɓa yarda ba. "Kana nufin wacce ta yi mini tsaki ɗazu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba." Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba? Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan canjin da na samo." Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa. "Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi ɗinki irin na yau ba." Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai. "Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi mini ƙarya?" Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi. "Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki ban sani ba." "To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya ce. "Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuɗin da Alhaji ya biya ni ne. Wannan shinkafar kwano ɗaya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce. "Wanna kuma fulawa ce kwano ɗaya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha da shayi tun da har madara na sayo." Har a ranta ta ji daɗi, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai kuɗin ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da abin da ya faɗa mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye. "Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka ɗauki wayar da kika kira, amma kin san babu wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki sa a ranki don Allah?" Jin sunan da ya faɗa mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi. Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce. "Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa." Har zai fita ta katse shi. "Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa." Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce. "Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci." Sai ya ɗan yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?" "Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi." Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta. "To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja." Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce. "Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima." Da yake hanyar banɗakin, da hanyar fita duka kusan hanya ɗaya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta ɗauka tana faɗin. "Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga." Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka."

Chapter 1 of 11