Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
ganshi zaka iya cewa ba shi bane. Duk da cewa shi ba mitum bane mai kiba , amman yana da matukar kyan gani Lokaci guda kuma yanzu duk yabi ya lalace , tunda Mama ta fara maganar auren Laila. Wayarshi tana gefe kusa dashi , yayin da shi kuwa yake kwance a kujera. Laila ce ta fito daga dakinta sanye da hijab ta karaso gabanshi "Uncle dan Allah me yake damunka , ko abinci har yanzu baka ci ba ." Uncle ya kauda kai gefe kamar bai ji maganar tata ba . "Uncle magana nake ." Kallonta ya yi cikin wani yanayi na isa yana cewa. "Tashi ki bani guri ." Ta kalleshi tana sunkuyar da kai da ajiyar zuciya Mikewa tai ta juya zata koma inda ta fito Taji muryar Uncle Nasir yana cewa. "Babu abin da yake damuna Laila." Hakan yasa ta juyo ta koma ta sake zama , Shima Yaya Nasir ganin ta zaune ne ya tashi zaune. "Uncle bani da kamarka a duniya, haifata ne kawai baka yi ba , idan nagan ka cikin wani yanayi bana jin dadi ko kadan , dan Allah Uncle idan a kan aure na ne ka dena damuwa, bazan auri kowa ba , sai wanda ka zaba mini koda bana san shi ." Nasir ya yi murmurshi mai ciwo , sannan ya ce . "Karki damu Laila, ina miki kaunar da bana son kowa ya rabe ki , amman akwai alamun lokaci zai raba mu ." Mama ce ita ma ta fito rike da carbi a hannunta ta samu guri ta zauna. Laila ta kalli Uncle cikin zumudi tana cewa "Yawwa Uncle, shi ne baka taba fadan komai a kan Batula ba ko." Wani dasss Yaya Nasir yaji ya dakar masa zuciya Ya kalli Mama da sauri Ba tare da Laila ta dubi yanayin da yake ciki ba , ta cigaba da cewa . "Gaskiya Uncle tana san ka , naji kuma an ce ko saurararta baka yi ." "Marainiya ce fa Uncle, wallahi tana shan wahala." Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke tare da cewa. "Nima ai maraya ne , sannan ke ma haka , babu wani soyyaya a tsakani da wannan yarinyar Batula, kin ga Laila ki dena maganar ta ." Kafin Laila ta bude baki tai magana Khairat ta turo kofa ta shigo tana sallama Abin da ya basu mamaki ganin Batula biye a bayanta "Wow Uncle, ka ga Aunty Batula 'yar halak." Laila ta fada ta tashi da gudu tana rungume Batula Yaya Nasir ajiyar zuciya yayi yana kauda kai gefe Mama cikin far a ta kallesu tana cewa "Auu wannan ne Batulan."? Mama ta aje maganar daidai da inda Batula ta zube gaban Mama tana gashsheta Nan Mama ta gaisa da Batula cikin sakin fuska, wanda hakan ya yiwa Batula dadi "Yaya Nasir ina wuni ."? Khairat ta fada bayan sun gaisa da Mama Ita kuwa Laila Sam bakinta ya kasa rufuwa , ta tsaya a kansu ta kasa zama "Ina wuni Yaya Nasir." Batula ta fada cikin sunkuyar da kai "Lafiya." Ya fada a takaice "Gaskiya Uncle kun dace sosai da juna .". Laila ke nan ta fada yayin da Yaya Nasir ya hade ransa Mama dariya ta yi kana ta mike tsaye tare da shiga ciki Kujerar da Mama ta tashi Laila ta zauna a hannunta tana magana cikin shauki "Ke khairat taso mu bar musu falon." Kafin khairat ta tashi Uncle ya mike zai fita "Uncle baku gaisa ba fa." Laila ta fada Dariya ya yi kamar me jin kunya kafin yace komai Khairat da Laila suka fita Kamar abin arziki Uncle ya koma ya zauna Hakan yasa Batula ta d'ago kai tana cewa. "Kayi hakuri Yaya Nasir , na zo ban sanar da kai ba , wallai ina cikin damuwa kala-kala , ganin ka ne zaisa naji sauki , shi yasa nazo tunda baka iya zuwa inda nake ." Wani takaici Yaya Nasir yaji ya turke masa zuciya Ya kalleta cikin zafi yana cewa "Ki dena yaudarar kan ki Batula, babu wani soyyaya tsakanin mu , babu yarinyar da nake so , hasalima bansan ya ake jin soyyaya ba , ya kamata ki sani bana san ki , kar kuma ki kuma zuwa inda nake babu abin da zaisa na soki har na aure ki ." Ya tashi ya fita Ajiyar zuciya mai zafi Batula ta sauke Gaff da kuka , zuciyar ta na mata zafi Lokacin Khairat da Laila suka shigo Wani murmurshi na yake sosai Batula ta jefa musu "Har an gama soyyayar Aunty."? Cewar Laila cikin tsokana Baki khairat ta tabe tana cewa. "Ki dubi wannan fuskar tata kice wani an sha soyayya. Laila Yaya Nasir fa baya san Batula maganar gaskiya ke nan ." Murmurshi Batula tai duk da bata ji dadin maganar ba "Inji waye 😏, shi kuwa yake sona , ina kaunar Yaya Nasir Laila, kaunar da bansan daga ina take zubowa ba." Ta aje maganar tana rike hannun Laila fuska da hawaye Zafi Laila taji a zuciyar ta , ta kankame hannun Batula tana cewa. "Uncle mijinki ne Aunty Batula kar ki damu dan Allah." Murmurshi Batula tai tana cewa. "Allah ya sa ." Matukar tausayin Batula ya sake rufe Laila "Kira Mama mi sallama mu tafi." Khairat ta fada tana mikewa tsaye. Fatima ce ta fito daga wanka , gama sa kayanta ke nan , Fa'iza ta shigo tana cewa. "Wai dan Allah tun yanzu zaki tafi , ki bari sai anjuma mana ." Harara Fatima ta jefa mata yayin da take sanya man lebe ta ce da Fa'iza. "Ai dole ki fadi haka , tunda kwanan da nayi ma bai miki ba ,ke fa Fa'iza sau daya kika taba kwana a gidanmu." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kafin ta ce . "To ai naga nan da can din duk daya ne , amman ina nan zan zo na kwana karki damu ." Fatima tai shiru yayin da take kallon babban madubin dakin tana kallon irin yadda tai kyau Yadda Fa'iza ta lura da ita ne yasa tai murmurshi tana cewa. "Wayyo kyau , ka ga amaryar Abdallah, gaskiya baby kin yi kyau ." Dariya Fatima ta sake yi tana cewa. "Wato dan ki wayantar da zancen da muke ko , ai shikenan." Fa'iza mikewa tsaye tai tana rike hannun Fatima cikin kauna ta fara cewa. "A"a Rabin Raina Fatima, babu abin da yake damuna, to idan ina tare dake mene zai dame ni , bari ma gashi kullum kina samun lafiya, ai wannan kadai ya isa ." Murmurshi Fatima tai tana fad'in "Alhamdulillah, to tunda haka ne gaskiya kawai ki shirya Abdallah ya aure mu tare domin ban shirya rashin ki ba ." Cikin sauri da firgita Fa'iza ta saki hannun Fatima lokaci guda kuma ta fara dariyar da Fatima bata gane ba . "Haba dai , ai ni Abdallah ya min kauyenci , sai dai ke shalelen babanta." Cikin tsokana ta aje maganar Dariya kawai Fatima tai , ba tare da tace komai ba ta dauki Jakarta ta rataya.. Dariya Fatima ta juyo tana yi , "Jiya na tashi sallah da dare ina ta tashin ki baki tashi ba ." Fatima tai maganar tana sanya agogo a hannunta "Hmmm , wallahi Fatima kawai bacci ne yaja ni , kuma kaina sai ciwo ." Fa'iza ta mayar mata Da sauri fateema ta fara cewa. "Daman haka zancen yake ai, kullum ciwon kai , saboda kina da damuwa baza ki fadan ba ." Fa'iza ta ce . "Hmmm". Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 21 & 22 Baiwar Allah kamar kullum, yanzu ma wanke wanke take yi , Allah Allah take ta gama ta yi shirin zuwa islamiyya Jin muryar Rahma tai a bayanta tana cewa. "Ke kizo daddy yana kira." Ta juya ta koma ciki Da sauri Batula ta mike tana share hannunta ta nufi inda suke zaune suna kallo Sallama ta fara yi kafin ta shiga ciki Duk da babu wanda ya amsa ta nufi kusa da mahaifin Rahma ta zauna tana sunkuyar da kai . Kamar saukar aradu ta ji yana cewa. "Wannan yaron Musa, ya zo neman auren ki , kuma daman yanzu Rahma take fadan kina san shi ." Da sauri da tashin hankali Batula ta d'ago kai tana kallon shi "Daddy ba haka bane , kasan Musa ko asalinsa ba a sani ba kuma .." "Ke rufe min baki ." Baban Rahma ya fada "Ke da zaki farin ciki kin samu miji , kina ganin ko ita Rahma bata sami irin shi ba ." Kuka Batula ta fashe dashi tana fad'in "Wallahi Daddy bana san shi ." "Tashi ki tafi ki bani guri , ni nasan abin da ya dace ." Baban Rahma ya fada , yayin da matarshi taja tsaki tana cewa "Karyar banza, idan bamu aura miki shi ba , waye me son naki ." Batula ta fita tana tare da tarin damuwa a fuskantar ta. Abincin safe suke ci , wajejen karfe 10, sakamakon yau Yaya Nasir bai fita aiki ba, kana garin an tashi da sanyi, yasa suke ta bacci abinsu. Sallamar Alaji Bashir ne yasa Mama sanya mayafi bisa kanta, lokaci guda kuma tana amsa sallamar Laila ta kalli Uncle din ta tana murmurshi "Shigo Alhaji Bashir." Mama tai maganar tare da canza wajen zama . "Assalamualaikum." "Sai yanxu kuke karyawa ke nan , an gayu." Laila tai dariya Gurin da Mama tai masa nuni da ya zauna , nan ya zauna tare da aje babbar wayarshi da mukullin motarsa "Baba ina kwana."? Laila ta fada ta na kallonshi Cikin saurin baki kamar yadda ya saba ya maida mata. "Laila lafiya kalau ." Sannan shima Nasir ya mika masa gaisuwa Yana gama amsar gaisuwar Nasir ya fara gaida Mama cikin far'a Tare da tambayar yanayin sanyi da aka fara shiga Nan Mama ta tabbatar masa komai da kowa lafiya. Sannan ya ce ."To Masha Allah haka ake so ." Shiru suka yi na wasu sakanni Sannan Alaji Bashir ya kalli Mama yana cewa. "Wato abin dake tafe dani, ba komai bane face Inna mahaifiyar babar Laila ta zo ta same ni ." Yaya Nasir da sauri ya kalli Mama, suka hada ido sannan Mama ta koma tana kallon Alaji Bashir "Ta sanar dani cewa, kai Nasir zaka bawa Laila yaro mara tarbiya , alhalin ga Mahmud can yana san ta . Kuma sannan ma kai waye a wajen Laila, bayan ni ina raye , da har zaka ba wani Laila, ba tare dana sani ba ." Yaya Nasir yaji zuciyar shi tai wani irin bugu suka hada ido da Laila Laila tai ajiyar zuciya ta mike tsaye tare da nufar dakinta "Ke Laila zo nan , ina zaki ." Alaji Bashir ya fada , sannan Laila ta dawo ta zauna Ajiyar zuciya Alaji Bashir yayi , sannan ya cigaba da cewa. "Ni bazan aurar da Laila ga wani ba , amman kasan cewa har yau bakai aure ba , sannan naga alamun Laila ma zaman gidan kake so tayi , domin ina samin labarin komai ." "Tom na baka lokaci daga yau, ka tsayarwa da Laila mijin da zamu aura mata , kuma na baka wannan damar ne domin yadda ka kula da Laila da yadda kuka shaku." Mama ta ce . "Wannan gaskiya ne , nima abin da nake so ke nan ." Alaji Bashir ya ce . "Yawwa wannan shi ne abin da ya kawo ni, domin Hasana yata kanwar Laila yanzu tana dakinta, Kuma kaima ya kamata kayi aure zuwa yanzu ." Matukar tashin hankali ya bayyana a furkar Yaya Nasir Ajiyar zuciya yayi ya kalli Alaji Bashir yana cewa. "Alaji abin da yake faruwa, har yanzu ban sami wanda zan aurawa Laila ba , Kuma wallahi da zarar an yi maganar auren Laila sai duk hankalina ya tashi ." Alaji Bashir ya mike tsaye tare da cewa. "Na dai baka lokaci, da zarar ya kare ni zan aurar da ita ga Mahmud." Ya nufi hanyar fita tare da sallama da Mama. Zumbur shima Nasir ya mike tsaye, duk su Mama ya basu tsoro Hanyar fita ya bi kai tsaye gidan Umar ya nufa babu ko takalmi a kafarshi. Dake babu nisa tsakaninsu sosai , cikin babban tashin hankali Yaya Nasir ya nufi gidan Umar. Umar na kokarin shiga gida, ya hangoshi yana tahowa, sai da ya zo gaff da Umar, Umar ya fara murmurshi tare da cewa. "Ka ga angon Batula." Lokaci guda yana kallon kafarshi da ya lura babu takalmi Kafin Umar ya sake maganar Yaya Nasir har ya juya ya sake nufar hanyar gidansu. "Kai lafiya kuwa, ko dai wani abin ne yake faruwa a gidan ."? Umar ya tambayi kanshi yayin da yake hangen Yaya Nasir dake komawa gida cikin dafewar kai Da sauri Umar ya shiga gida, da nufin ya dauko wayarshi ya bi bayansa. Laila ta mike ta koma kusa da Mama cikin matukar tausayin Uncle dinta ta fara magana. "Mama me yake faruwa da Uncle ne, yanzu fa ko takalmi babu ya fita , kullum sai ramewa yake ." Mama ajiyar zuciya ta sauke , sannan ta ce da Laila. "To nima ta ya zan sani Laila." Rufe bakin Mama ke nan Uncle ya shigo , kai tsaye kuma ya nufi dakinsa. Shima sai ga Umar ya shigo tare da sallama "Auu Mama nayi zatan wani abin ne yake faruwa, na ga Nasir cikin wani yanayi , shi yasa na biyo bayanshi ." Mama ta ce "Ummm ! Kai ma dai ka fada Umar, gashi nan daga maganar auren Laila ya koma haka ." "Bari na shiga dakin nashi ." Umar ya fada tare da nufar kofar dakin Koda Umar ya shiga , Yaya Nasir yana zaune bakin gadonshi ya dafa kanshi . Haka ya amsa sallamar Umar ba tare da ya d'ago ba . "Me yake faruwa ne Nasir."? Umar ya yi masa tambayar yana zama a gefenshi Hakan bai canza komai ba daga Yaya Nasir Sai bayan wasu sakanni sannan ya d'ago kai yana cewa "Ni ne fa na raini Laila Umar, ni ne fa ." Sai wasu hawaye sharrrr suka zubo masa "Tabbas ya kamata Laila tai aure , amman akwai ciwo a zuciya ta , bana son rabuwa da Laila , Umar in takaice maka zance ina MAHAUKACIN Son Laila , so na aure , da zamu rayu tare da juna har abada.".. Umar cikin tashin hankali ya damke masa baki , domin kar su Mama suji wannan kazamin zance . Lokaci guda gumi ya ketowa Umar *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 23 & 24 Yaya Nasir ya wurgar da hannun Umar gefe, Cikin buguwa kamar dan maye ya koma ya kwanta. Wani das das das zuciyar Umar take bayarwa , ya kalli Nasir dake kwance cikin rashi yana cewa. "Wai daidai naji kuwa? Ko dai Nasir ya haukace ne , an ya kuwa abin da ya fada haka naji."? Ya aje ajiyar zuciya me zafi, kana da ya lura yayi bacci Ya nufi hanyar fita. "Ahh Umar tafiya zaka yi ne." Umar ya ce . "Eh Mama." Sannan shima ya fice kamar furgitacce Laila ta kalli Mama tana cewa. "Wai Mama baki ga Yaya Umar gumi yake ba , bayan sanyin da ake yi Ko dai fada sukai da Uncle."? Mama kawai ta ce mata "Ummm." Fitowar su ke nan daga harabar makaranta, suna jiran Abdallah. "Fatima da kin zo mun hau nafef kawai mun tafi Abdallah ya bata lokaci." Fatima cikin wasu idanu ta kalli Fa'iza sannan ta ce . "Fa'iza akwai abin da ya rikeshi , kuma yanzu zaki ganshi , gashi kaina yana matukar ciwo sosai , zazzabi nake ji Fa'iza." Murmurshi Fa'iza tai tana rike hannun Fatima, yayin da motar Abdallah tasha gabansu . Tun dazu Batula take zaune a falo tana jiran fitowar yayan babanta da take kira da daddy Domin wajen minti 30, ke nan tana zaman jiranshi Sai da aka sake kwasar minti biyar sannan Alhajin ya fito tare da matarshi. "Au ke Batula kina nan ashe." Ya fada yayin da yake lunkuma wani naman kaza a bakinsa . Sannan sai ga ita ma Rahma ta shigo rike da wannan naman a cikin plet, Sai da ya cinye wannan naman na bakinshi tasss , sannan ya kalli Hajjiya yana cewa. "Ita kun bata naman ko."? Rahma da sauri ta maida masa da cewa "Daddy ai idan taci nama wai zuciyar ta ke tashi." Tai maganar tana mata gwalo Kawai Batula tai murmurshi "Kaji yar baiwa shi ke nan Musa ya huta da siyen nama." Alaji ya fada Wani bakin ciki Batula taji ya turnike mata zuciya, Yadda Rahma tai mata sharrin bata cin nama bai bata mata rai ba , kamar yadda Alaji yanzu ya ambato sunan Musa mai gyaran takalmi. Shanyewa tai kawai tai shiru , sannan Alaji ya fara da cewa . "Batula abin da yasa na kira ki , ke kamar yar cikina ce , domin ke yar kanina ne Abubakar , mutum ne mai biyayya, kuma daman an ce mutuncin ya mace gidan mijinta." Tunda Batula taji wannan batu tasan inda ya nufa Hakan yasa suffar ban tausayi ta sake kamata "Jiya magabatan Musa sun zo mini , kan neman aurenki ." "Amma na ce su jira ni zasu ji daga gare ni , fatan dai kin shirya auren yaron nan , domin mutumin kirki ne , zai rike ki da mutunci, sauran gadon mahaifin ki dake hannuna sai ai miki kayan daki dasu ." Murmurshin mai matukar ciwo Batula ta ajiye sosai , domin yadda wani bakin ciki ya tsaya mata a zuciya yasa ta dole tayi wannan murmurshi. Duk da haka ba tai kasa a gwiwa ba , ta kalli yayan babanta tana cewa. "Daddy akwai wanda nake so , amman wallahi ba Musa ba ne , ka bani dama domin ..." "Ke dallah yi shiru, yana magana kina magana ko ."? Mahaifiyar Rahma ta fada Rahma ita ma ta dora Da cewa . "Karya take yi ma daddy babu wani wanda yake santa ." Alaji ya cigaba da cewa "Ai baza ai haka ba Hajjiya ,." Ya koma ya kalli Batula yana cewa. "Na baki kwana uku , ki kawon shi yaron da kike so , idan har ya cancanta to zan aura miki shikenan." Zumbur Batula ta mike cikin farin ciki tana cewa. "Na gode daddy Allah ya saka da alheri." Ta mike ta fita . Rahma tana jan wani tsaki . Tsabar farin ciki Batula ta rasa yadda yadda tai , amman lokaci guda ta kame tare da tunanin yadda zata kawo Nasir gaban Alaji , to tabbas wannan babban lamari ne, Amman ta yanke shawarar shiryawa ta nufi gidansu khairat. Fitowar Nasir ke nan zai tafi wajen aiki , ya kalli Mama sannan ya ce . "Ina Laila ta shiga kuma Mama."? Mama ta maida masa da amsa tana cewa. "Taje gidan kawarta ne ." Sannan Mama ta sake kallonshi tana cewa. "Ka ga yadda ka rame kuwa Nasir,duk ka lalace jijiyoyi ta koina haba Nasir meke damunka ne ." Yaya Nasir ya yi murmurshi sannan ya ce ."Mama ta ke nan , babu abin dake damuna, bari naje na dauki Umar mu tafi office." Yasa kai yana murmurshi Bayan Yaya Nasir ya isa gidan Umar, Umar ya fito suka tafi , sakamakon motarshi na wajen gyara . Suna tafiya cikin mota , Umar bai iya cewa da Nasir komai ba , domin kawai tunanin irin maganar da yaji yayi yake yi , "Shin wai gaske ne ko dai bai ji daidai ba , ta ya Nasir zaka ce kana son Laila." Umar yake maganar cikin ransa yayin da take kallon Nasir ta gefe . "Umar kana lafiya kuwa. Tunda muka fito kayi shiru ."? Yaya Nasir ya fada yana kallon shi . Murmurshi kawai Umar yayi , kafin ya ce . "Ai kai za a tambaya Nasir, duk ka rame ka lalace, kamar wanda cuta ke cinsa ." Duk yanayin fuskar Uncle ta canza , ya kalli Umar, sannan ya maida hankali ga tuki yana cewa. "Lokaci ya yi da zaku san Laila rayuwa ta ce , duk da cewa kaji na fada shekaran jiya, kar kai tunanin ba na cikin hayyacina." Umar ya ji gabanshi ya sake faduwa da sake jin maimaicin wannan babbar zugar maganar daga Nasir. "Wai dan Allah Nasir kan ka daya kuwa , magana ake ta Laila kai ne ubanta , babu aure a tsakaninku, dan girman Allah kai shiru da wannan maganar, idan kuma wasa kake ka dena kar zuciya ta , ta buga . Wannan zancen kasan girmansa kuwa."? Da babban tashin hankali Umar ya masa maganar. Yaya Nasir ya aje ajiyar zuciya sannan ya ce . "Babu aure ka ce tsakani da Laila, tabbas ina son Laila Umar, Kuma wannan zancen dole ya fita waje, domin Laila tare zamu kasance." Hadiyar yawu Umar ya yi yana cewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un. " Tafiyar dactor ke nan ya gama duba lafiyar Fatima, sakamakon yadda bata jin dadi , Alaji Usman duk yabi ya tashi hankalinsa Fatima na zaune tare da mahaifin ta , sai ga Fa'iza ta fito daga dakin Fatima sanye da Jakarta a hannu . "Ba dai tafiya zaki ba , bayan mun yi dake anan zaki kwana , Kuma kin sanar a gida ." Fatima tai maganar tana kallon ta . Kawai Fa'iza tai dariya tare da juyawa tana cewa. "Daman so nake naji bakinki." Dariya Alaji yayi sannan Fatima ta tai saurin dakatar da Fa'iza da cewa . "Fa'iza ko zaki shiryawa Abdallah wani abin , ya ce mini zai zo yau ." Fa'iza ta juyo tare da cewa. "To ranki ya dade." Fatima tai murmurshi. Fa'iza na komawa dakin ta aje jakar tare da murmurshi tana cewa. "Fatima ke nan . Abdallah manya Allah ya kawo ka ." Matukar tashin hankali Umar yake ciki ,domin samm ya kasa fahimtar wannan zancen na Nasir baki daya , Idan yayi tunanin abin da yasa Nasir yake ramewa ke nan , Kuma yaki bawa Laila kowa ta aura, sai ya ga kamar gaske son Laila ya ke kuwa Amman Umar sai yayi tunani sosai , sannan ya koma ya tuba , domin lamarin tabbas ya yi muni sosai . *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 25 & 26 Khairat da Batula ne a zaune, bayan Batula ta gama zayyanawa khairat tarin damuwa da yadda sukai da Alaji mahaifin Rahma. "Amman gaskiya Batula wannan lamarin babba ne , yanzu ta ya har Uncle zai yadda da aureki , cikin kwana uku har yazo gidan ku , Tabb." Khairat ta fada cikin gano matukar wahalar abin . Batula ta amsa da cewa. "Haka ne khairat, wallahi sai yanzu nima hankali na ya tashi, amman ya zanyi idan Musa shi ne kaddara ta ." Ta aje maganar tana kuka , duk sai zuciyar khairat ita ma tai sanyi , amman haka ta fara rarrashin ta , duk da ita ma khairat bata da wani kwarin gwiwa. "Assalamualaikum." Laila ta shigo dakin kharait tare da sallama Ita ta amsa sallamar ciki murya mara wadatuwar kuzari "Ahh me zan gani haka , Aunty Batula mene ya faru kike kuka kuma." Laila tai maganar tana durkusawa a gabansu. "Mutuwa aka yi ne khairat."? Laila ta sake fada. Sai da khairat tai murmurshi sannan ta ce . "Babu wata mutuwa, maganar auren ta ne, yayan babanta yace ta fito da miji kwana uku ko ya aura mata Musa, kuma kinsan Yaya Nasir take so . Sai kuma sauran matsaloli da baza a rasa ba ." Cikin rarrashi Laila ta fara cewa. "Haba Aunty Batula, dan Allah ki dena kuka , kuma in sha Allah da ikon Allah zaki auri Uncle dina , wallahi Aunty Batula zan yi duk yadda zan domin ki aure shi ." Murmurshin farin ciki Batula tai tana cewa. "Wallahi da burina ya cika Laila, da kuwa dukkan bakin cikina ya yaye." Laila ta ce . "Karki damu anuty." Murmurshin jin dadi ita ma khairat tai sannan ta fara cewa. "Ka ga yar gidan Uncle, daga ina haka ." Laila ta ce . "Hmmm daga gidan su Sadiya , kinsan yau ne Usman zai zo muje gidansu." Dariya khairat tai tana cewa. "Eh wannan gaskiya ne kuwa , ka ga amaryar Usman, sirikar Alaji Sani Shanshani." Duk suka kwashe da dariya. Sannan khairat ta sake kallon Batula tare da cewa. "To ya maganar jarin ya baki baban Rahman." Baki Batula ta tabe tana cewa. "Tab! Ni na ce ma ko a kudin gadona ne ya bani , amman yaki, bazai banba , bai bani da cikakken hankali, kuma wallahi ina son bude shagon atamfofi da takalma ko salun ne ma." Khairat tai murmurshi, yayin da Laila ta kara da "Ummm Auntyna Batula." Fa'iza ta gama shirin tarbar Abdallah tsaf,domin babu dadewa Sai ga Abdallah ya zo , sai da ya kwashi gaisuwa wajen Alaji da hajjiya sannan tare da yi musu ya mai jiki, sannan ya samu damar isa inda Fatima da Fa'iza suke . Tafiya suke cikin mota , babu wanda ya ce da kowa komai , sai dai kowa sake-saken shi yake a zuciyar shi. Fargabar Umar kar Nasir yaje gida ya bayyana Mama wannan zancen, domin tabbas yadda ta tsufa sai ya kasheta kasheta lokaci guda, tunanukan da Umar ya ringayi ke nan , Ganin Nasir ya kusan kawoshi gida yasa shi fadin . "Mu wuce gidan naku domin madam bata nan ." Ba tare da Yaya Nasir ya bashi amsa ba ya cigaba da

Chapter 4 of 5