gari kuwa kafin kace komai sai gari ya dauka ga Nasir can ya dawo shida Laila
Haka Alaji Bashir Shima ya sami labari , bayan ya zo ya ganewa idanunsa ya matukar fitar da bacin ransa da takaicin sa ga Nasir, domin har wani zance yaso ya fitar da zaisa Nasir ciikin mugun yanayi, amman Mama ta hana shi .
Tashin hankali aka yi sosai kafin komai ya dawo daidai , ita ma Inna da guntun bala'inta tazo , ta juyewa Nasir
In takaice muku zance Mama harda hawan jini sai da ta watanni babu lafiya , kuma tai matukar fushi da Nasir
Lokacin da Nasir ya so kare kanshi yake basu hakuri, tare da tabbatar musu ba ya son a dauke Laila a gidansu ya sa yayi wannan abin , domin sam baya son a raba shi da jaririyar yayan nashi .
Sai dai babu wanda ya amshi uzurinsa , domin ba abin da za a kama bane
Nan Inna ta sake tada jijiyoyin kai , a kan dole sai an bata Laila,
Yadda Nasir ya ga Mama na matukar fushi dashi yasa bai ja dasu ba
Sai dai bayan sun dauki Laila, abin bai musu dadi ba , domin kullum kuka babu wanda take kira sai sunar babanta Nasir, haka ta rame ta lalace babu wanda ta saba dashi sai Nasir.
Hakan yasa dole suka dawowa da Nasir yar shi
Bayan wannan ya faru sai komai ya fara lafawa , domin Nasir yayi matukar nadama , hakan yasa Mama ta yafe masa .
Har yake bata labaranin yadda ya kula da Laila
Nan ne aka sanyata makaranta, ta fara wayo
Shi kuma Alaji Bashir bayan Shima ya huce , ya bawa Nasir aiki.
Sai Mama taji duk farin cikinta ya dawo , domin a halin yanzu Laila ta gama makaranta.
Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.
*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati๐
MAHAUKACIN SO ๐
Na
Autar Marubuta
________________________________________
Babu editing
Page. 7 & 8
Nasir ne zaune a cikin office dinshi , yayin da abokin shi Umar ya kawo masa ziyara
Wayar Umar ta fara ringin, ya kalli wayar dake bisa teburin aikin Nasir da yakan iya ganin me kiran
Sannan ya kalli Nasir yana cewa .
"Mutuniyar ka fa ke kira. Dan Allah ka bawa yarinyar fuska , wallahi tana san ka ."
Nasir
kawai yaja tsaki tare da jan bakinsa yayi shiru
Hakan baisa Umar jin haushi ba , ya sake cewa dashi .
"Yanzu dan Allah to sai yaushe ne za kai aure, dukkan abokanmu sun yi aure , amman kai ko a jikinka , bayan ga yarinyar nan Batula na son ka kamar zata mutu."
A lokacin Nasir ya maida masa da cewa .
"Ni fa duk wani aure baya gabana , kuma babu yarinyar da nasa gaba , kawai sai na aurar da Laila tukun ."
Umar kawai ya yi ajiyar zuciya.
Anan kuwa Fa'iza ce kwance kan gadon Fatima, yayin da Fatiman take gefe bisa gadon a zaune
"Har yanzu dai kin ga Abdallah shiru ."
Fatima tai maganar tana kallon Fa'iza, murmurshi na yake Fa'iza ta yi tare da kauda kanta gefe .
A karo na biyu , Fatima ta sake bude baki cewa.
"Ai na ce masa bani da wata kawar data wuce ki , domin kawancen mu ya koma 'yan uwan taka ."
Murmurshi Fa'iza ta kuma yi , kafin ta ce .
"To ni wallahi da baki kira ni ba , yaushe muka gaisa da Abdallan ? Ko sati biyu ba ai ba , da naje shopping na ganshi ."
Fatima ta maida mata da cewa .
"Amman shi ya ce kun dade baku hadu ba , yana son ku gaisa."
Fa'iza ta ce .
"Ai shi ke nan ."
Lokacin ne wayar dake bisa hannun Fatima , ta fara ringin
Hakan yasa ta yin murmurshi tana cewa.
"Kin ga kiranshi , ya zo ke nan .".
Tana karasa maganar ta dauki kiran .
Bayan ta gama ne ta fita , yayin daba wani dadewa tai ba ta bugo wayar Fa'iza tare da sanar mata .....
Wani tsoro Fa'iza taji duk ya kamata , jikinta kuma duk ya mutu, haka ta tashi ta nufi babban harabar gidan su Fatima inda suke tare da Abdallah
Dogo ne sosai kalar hutu, da gani yaron manya ne , duk da ba fari bane .
Haka Fa'iza ta karasa gabansu tare da cewa.
"Assalamualaikum masoyan juna ."
Murmurshi Fatima ta yi , yayin da Abdallah ya amsa mata da cewa.
"Wa'alaikis Salam aminiyar sarauniya ta."
Ba tare da Fa'iza ta kalli fuskar Abdallah ba ta sake fad'in.
"To ya kazo , ya kawar tawa."
Wani murmurshi me kyau da jan hankalin Abdallah ya yi sannan ya maida mata da cewa.
"Lafiya kalau Fa'iza, amman wato yadda alakarku take da fateema abin yana matukar burge ni , rayuwar ku abin birgewa."
Dariya Fatima da Fa'iza sukai a tare da juna , kana Fatima ta maida masa da fadin.
"Ai ni Fa'iza ta wuce komai a guri na , domin rikon amana da matukar mutunci, ta yadda ranta ya baci idan na wani zai yi fari , haka kuma ..."
Fa'iza ce ta dakatar da ita da cewa.
"A'a wannan ai kowa yasan halinki ne , ke mutuniyar kirki ce , ko rabin ki ban yi ba."
Abdallah ya yi dariya cikin wani yanayi mai kyau , sannan ya kallesu yana fad'in.
"Abin naku abin birgewa."
Sannan Fa'iza ta kalli Fatima tana cewa.
"Bari na shiga ciki, sai kin shigo , Abdallah sai anjuma."
Su kai sallama sannan Fa'iza ta nufi cikin gidan.
Allah-Allah Fa'iza take ta shiga ciki , domin ci take kamar kafafunta baza su dauketa ba , bayan ta karasa dakin Fatima, ta fada gado cikin wani yanayi ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi.
Anan gidan Mama kam
Tana zaune cikin falo suna kallo da Laila, Nasir ne rike da jakar office ya turo kofar falon.
Bayan ya yi sallama ya sami daya daga cikin kujerun falon ya zauna.
"Mama sannu da gida ."
Nasir ya fada
Mama ta maida masa da fad'in.
"Sannu Nasir da hanya ."
Kana Laila ta kalleshi tana cewa.
"Uncle sannu da zuwa ."
Ya maida mata da cewa.
"Yawwa."
Sannan ya maida hankali ga kallon da suke , lokaci guda kuma yana cewa.
"Mama Allah ya sa dai ba tuwon kikai mana ba ."
Mama ta ce .
"Hmm."
Ba tare data kara cewa dashi komai ba , bai damu da hakan ba ya kalli Laila yana cewa.
"Yawwa ke Laila, wai mene hadinku da Mahmud ne , na ga kwana biyu abin bana gane masa ."
Cikin mamaki Mama ta kalli Nasir tana cewa.
"Kaji mini yaro , Kamar ya mene hadin su , ba d'an uwanta bane ."
Kawai Laila ta kwashe da dariya mai cike da bayyana matukar kyanta
Yadda Nasir ya ga tana dariyar ne yasa yaji farin cikin sa ya karu .
Mama ce ta bude baki tare da cewa.
"Ai kai ta zamanka , har Laila ta yi aure , kana nan a gida tunda abin ba ya damunka."
"Hhhhhhhhhh. Mama ke nan ai bazan aure ba , sai na aurar da Laila, domin bazan bar rayuwar Laila ta shiga garari ba."
Mama ta ce .
"Ai shi ke nan , sai ka zauna har lokacin barina duniya ya yi , ban ga yayanka ba ."
Dariya Nasir ya kuma yi yana fad'in.
"A'a wallahi Mama babu inda zaki in sha Allah."
Mama tai murmurshi tana cewa.
"To zaka ci abincin ne ko zancen za kai ta yi."
Nasir ya ce .
"A'a Mama mu dai cigaba da zancen , domin tabbas sai me sa'a ce zata aure ni , kuma me sa'a ne zai auri Laila,
Kuma idan na shigo gida na ganku tare da Laila sai naji duk damuwa ta ta tafi, shi ya sa Laila tunda ta ga ma secondary kawai ta zauna , domin bana so ta cigaba da karatu maza suna biyo mini kyakykyawa ta."..
"Dan Allah ka yi min shiru Nasir.".
Mama ta fada
Yayin da Laila ta kuma dariya .
"Sai surutu kake yi tunda ka shigo, ka je kaci abinci ma ya gagara."
Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da murmurshi yana cewa.
"Mama ke nan."
Laila ce ta kalleshi da cewa.
"Uncle N na kawo maka abinci ne."
Shima ya kalleta ya maida mata da cewa.
"Karki kuma ce min Uncle ko Uncle N, Yaya Nasir kawai."
Yadda Laila ta ga alamun da gaske yake ya sa ta cewa.
"Tom."
Sannan Mama tai dariya tana cewa.
"Ai ni lamarin ku dariya yake ban , ai kuma Baba ya kamata ki rika ce masa ."
Dariya Nasir ya yi yana cewa.
"A'a Baba kuma Mama, kina ganin had'ad'd'en saurayi."
"To ai irin yadda kai wahala da Laila tana karama, idan tace baba ai batai laifi ba."
Nasir ya ce .
"Haba Mama mene na tone-tone kuma."
Dariya Mama da Laila su kai , Mama tana cewa.
"To mene Laila bata sani ba ,ai an bata labarin komai ."
Duk ka suka kwashe da dariya Nasir na cewa.
"Allah sarki duniya."
Anan cikin gidan Inna kuwa , bayan shekaru masu yawa, tana nan yadda take , idan ka cire wata yarinya jikarta Farida da aka kawo mata suke zaune tare
Inna na zaune taji sallama, tun ba a shigo ba hakan ya faranta mata rai ta fara nuna farin cikin ta , domin ta dau murya.
Wani had'ad'd'en saurayi ne sanye da kananun kaya , rike da mukullin mota ya shigo .
"Sannu da zuwa Mahmud, angon Laila in sha Allah."
Inna ta yi maganar cikin farin ciki, yayin dashi kuma dukkan hakoransa suka bayyana yayin da yake dariya.
Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.
*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati๐
*MAHAUKACIN SO*๐
Na
Autar Marubuta
________________________________________
Babu editing
Page 9 & 10
Guri Inna ta sama masa ya zauna yayin da suka gaisa cikin raha da girmamawa take tambayar mahaifin nashi da mahaifiyarshi Rabi
Nan ya tabbatar mata duk suna lafiya
"To Inna ina Faridan ta shiga ne ."?
Mahmud ya tambaya
Inna cikin sakin fuska ta ba shi amsa da cewa.
"Tana islamiyya , ba a ta so ba ."
Mahmud ya ce .
"To Masha Allah."
Su kai shiru na wasu sakanni, hakan yasa Inna cewa.
"To ko daga wajen Lailan kake ."
Sarkin dariya, ya yi dariya yana cewa.
"A"a daga gida nake , gurin ki na zo kawai ."
Inna ta ce .
"To ai ka kyauta, amman ya kamata ka biya gidansu Lailan."
"To ai Inna Baban nata ne kamar ba ya son zuwa na fa ."
Inna ta ce .
"Kamar ya , wai Nasir, duk tsiya Laila jininka ce ai bai isa ya hanaka zuwa ba , gara a samu a tura kawai , idan ma wani yake son bawa ya fasa."
Mahmud ya yi murmurshi yana cewa.
"Haka ne Inna, amman kina ganin ban yi wuri ba ."
"Babu wani wuri da ya yi , tunda dai ta gama makaranta tun -tuni , to me ake jira kuma."
Mahmud ya ce .
"Haka ne ."
Haka su kai ta hirarsu , lokacin da ya tashi tafiya ya debo kudi ya bata , sannan ya hau motarshi ya koma .
Suna cikin tafiya a mota , Laila ta kalli Nasir yayin da suka hada ido sukai wa juna murmurshi
Ajiyar zuciya Laila ta sauke , kana ta kalli Nasir tana cewa.
"Uncle ina da.."
Ba tare da ya bar ta ta fadi abin da take so ba ,ya katseta da cewa.
"Laila bana ce ki dena cemin Uncle ba ."
Murmurshi tai tare da hadawa da dariya tana cewa.
"Ni Uncle gaskiya na saba , ka barni a hakan ."
Shima yayi dariya yayin da yake murza kan mota ya ce .
"To shi ke nan."
Murmurshi ta kuma masa tana cewa.
"To Uncle yaushe za kai auren hankalin Mama ya kwanta."
Zuciyar shi yaji wani bugu yana fita da ya kasa gane dalilin sa
Ba tare da ya kalli fuskar Laila ba ya fara cewa da ita.
"Laila ba ko yaushe ake samun so na gaskiya ba.so abu ne mai wahalar da zuciya da kuma rayuwa, zan yi aure Laila karki damu ."
Kallonshi tai cikin sakin fuska tana cewa.
"To Uncle wace zaka aura , zan so ganin wannan ranar ."
Murmurshi ya mata , a sa'ilin da yake shan kwanar gidan Ummi yana cewa.
"Ki samo mini wacce ta dace Laila."
Cikin far a ta sake cewa dashi .
"A kwai kyawawan mata da zasu dace da kai Uncle."
Kallonta ya yi tare da katseta da cewa.
"A'a bana son kyakykyawa Laila, wacce take da kyan zuciya kamar ke, take da hankali da tausayi kamar ke Laila."
Sunkuyar da kai ta yi tana murmurshi, kana daga bisani ta dago tana cewa.
"Uncle dina ke nan , duk kasa naji kunya ma , ni bansan so ba Uncle, amman ina gani ina kuma ji a littattafan hausa, so guba ne me karya zuciya
Mai hana sukuni idan ba kai dace ba , sannan kaddara ne da ba a sanin lokacin da yake bibiyar mutane."
Dariya Nasir ya yi tare da cewa.
"Wato haka kika san so ke nan , karki mamaki idan kika ga komai ya faru a sanadin so ."
A lokacin ya bude kofar motar ya fita , kana Laila ta bishi da murmurshi tana fad'in
"Allah sarki Uncle dina , Allah ka ba shi mace ta gari , ka faranta rayuwar shi , shi ne komai na , kunnuwa na maganar shi kawai suke ji ."
Ta wajen gilashin motar ya matso kusa yana cewa da ita .
"To zaki fito ne ko kuwa."
Dariya ta yi kawai ta bude murfin motar ta fita , kana ya tasa ta gaba suka shiga gidan Ummi kanwarshi.
Sallama Laila ta fara yi a cikin falon , yayin da taci karo da wani karamin yaro yana zaune yana wasa.
"Sultan ina maman naka ."
Laila tai maganar yayin da ta dauki yaron a hannunta.
"Sannunku da zuwa."
Ummi ta turo labulan falon tana fad'i
"A she Aunty Ummi kina nan na yi zatan Sultan kika barwa gidan."
Dariya ta yi sannan ta kalli Nasir tana cewa
"Yaya Nasir ka zauna mana."
Nasir zama ya yi kamar yadda kanwarshi ta bukata
"Aunty Ummi khairat bata zo nan ba ke nan ."
Laila ta tambaya
Ummi ta kalleta tana cewa.
"Ta zo tana ta zaman jiranki har ta tafi."
Laila ta zumburo baki tana kallon Nasir da fad'in.
"Wallahi duk uncle ne yaja , tun dazu nake cewa ya taso mu taho."
Nasir ya yi dariya yayin da ya kara da cewa.
"To ba sai na kai ki gidan nasu ba , ko ba wannan kawar taki kanwar soja ba ."
Kafin Laila ta ba shi amsa Aunty Ummi ta fara magana.
"Wai ba ku ce min Mama kalau take ba , bamu gaisa ba , sai wani zance ake kuma ."
Dariya Laila ta yi kana ta kalli Aunty Ummi, lokaci guda kuma tana gyara zaman Sultan dake hannunta yana wasa , tana cewa.
"Mama tana lafiya kalau , ta ce a gashsheki sosai da sosai da jikokin nata ."
"To Masha Allah." Abin da aunty Ummi ta fada ke nan
Sannan Yaya Nasir ya maida mata da cewa.
"To ina yartawa ne kuma Mama na."
Aunty Ummi ta ce .
"Au wai Mommy, tana makaranta."
Laila ta ce .
"Mai sunan Mama ai akwai son makaranta."
Aunty Ummi ta kalli Laila tana cewa.
"Na yi zatanfa da Mahmud ma zaku zo wallahi."
Kawai Yaya Nasir duk ya canza ya koma wani yanayin daban
Murmurshi Laila ta yi kana ta ce .
"A'a Uncle ne ya kawo ni ."
Kawai Yaya Nasir ya tashi tsaye , sannan ya karbi sultan a hannun Laila tare da mikawa Ummi shi ,
Fuska babu annuri ya ce .
"Tashi mu tafi."
Duk mamaki ne ya rufe su da ganin Nasir ya canza musu a wannan yanayi
"Tashi mu tafi na ce ."
Ya sake jefawa Laila maganar mai tafe da umarni
"Hakan ya sa Laila ta mike jiki a sanyaye
"Haba dai Yaya Nasir, daga zuwa kuma , ko gaisawa ba a gama ba , ko ruwa baku sha ba zaka ce zaku tafi."
Aunty Ummi tai maganar tana nuna rashin jin dadinta a zahiri
Ba tare da Nasir ya ce da ita komai ba , kawai ya nufi kofar fita kana yana fad'in.
"Sai wani lokacin."
Ya fice
Da sauri Laila ita ma ta zura takalmi tana cewa da Aunty Ummi.
"Zan dawo wani lokacin Aunty."
Tabi bayanshi da gudu gudu
Ajiyar zuciya Aunty Ummi tai tana cewa.
"Ikon Allah, Yaya Nasir fa sai a hankali ."
Anan kuwa bayan Fa'iza ta fito daga lecture ta sami guri ta zauna.
Babu dadewa sai ga Fatima ita ma fito daga tata lecture din
Kai tsaye in da tasan tabbas zata sami Fa'iza nan ta nufa
Aiko tana karasa ita ma ta sami guri kusa da Aminiyar tata ta zauna tana cewa.
"Washh Fa'iza, gaskiya yunwa nake ji ."
Fa'iza ta kalli Fatima cikin murmurshi tana .
"To sai muje muci abinci ai ."
Kafin Fatima ta maida mata ne kiran waya ya shigo mata
Wani murmurshi Fatima ta saki tana kallon Fa'iza.
Hakan ya tabbatar wa da Fa'iza cewa Abdallah ne ke kira .
"Hello Abdallah."
Abin da Fatima ta fada ke nan ba yan ta kara wayar bisa kunnenta
Fa'iza tai ajiyar zuciya tare da kauda kai gefe , amman hankalinta na kan wayar da Fatima ke yi
Yanayin yadda taji Fatima na maganar soyyaya ya sa idanun Fa'iza suka kada sukai jajir lokaci guda kuma kanta ya fara ciwo.
Mikewa tai tsaye tai nisa da inda Fatima take tana share hawaye
Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.
*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son kati๐
*MAHAUKACIN SO*
Na
Autar Marubuta
*AUTAR MARUBUTA CE*โ๐ป๐ผ๐ป
๐น__________๐น_________๐น__________๐น_________๐น
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐คฒ๐ผ
<><><๐น><><><>๐น<><><>๐น<><><><>๐น<><><><><>๐น<><
________________________________________
Babu editing
Page 11 & 12
Bayan Fatima ta gama wayar ta hangi Fa'iza can nesa da ita , hakan yasa ta mike tsaye ta nufi wajen Fa'iza
Fatima na karasa wajen ta , tai ajiyar zuciya tana cewa.
"Wai nan kika taho."?
Fa'iza juyowa tai da murmurshi mai ciwo tana cewa.
"Eh ."
Lokaci guda kuma tana kokarin boye idanunta na kuka .
"Kuka ki kai Fa'iza, mene ya faru ."?
Fatima tai maganar tana fuskantar Fa'iza
"A'a ba kuma nai ba Fatima."
Fa'iza ta maida mata da amsa
Murmurshi tare da ajiyar zuciya Fatima ta yi tana kuma cewa.
"Wai ba kuka ki kai ba , dubi idanunki fa ."
Fa'iza ta sunkuyar da kai kamar wata yarinya tana murmurshi.
"Dan Allah me yake damunki Fa'iza, akwai abin da kike boye mini."
Fatima ta fada tana rike hannun Fa'iza.
Hakan ya karyawa Fa'iza zuciya, kawai ta fada kafadar Fatima tana kuka mai gwanin ban tausayi.
"Ya Allah."
Abin da Fatima ta fada ke nan cikin mutuwar jiki
Cikin wannan kuka Fa'iza ta fara cewa.
"Babu abin da yake damuna Fatima, kawai dai kwana biyu na kan yi kewar mommy, ta tafi ta barmu cikin damuwa, duk duniya bata min dadi Fatima, rashin mahaifiya babban abu ne."
Fa'iza ta aje maganar tana shekar kuka.
Murmurshi Fatima ta yi tare da d'ago Fa'iza daga kafarta tana cewa.
"Haba kawata , rasuwar mommy ta girgiza mu , amman a halin yanzu adduar mu kawai take bukata.
Dan Allah ki yi hakuri ki dena wannan kukan , Allah ya gafartawa mommy."
Ta karasa maganar tana sharewa Fa'iza hawaye da hankicin dake hannunta
Murmurshi Fa'iza tai tana cewa.
"Haka ne Fatima na gode ."
Fatima ta mika mata makullin motar dake hannunta tana cewa.
"Yau ke zaki tuka mu , karbi ."
Fa'iza ta amsa tana dariya.
Nasir ne a tsaye bakin mota tare da Batula
Batula tai murmurshi tana kallon masoyin nata tana cewa.
"A gaskiya na yi matukar farin cikin ganinka a kofar gidan mu ."
Yaya Nasir ya yi murmurshi yana cewa.
"Batula ke nan , to idan banzo gunki ba , gurin wa zan zo , ke ce fa wacce nake burin aure , uwar yayana farin ciki na , kaf mata banga ta biyunki ba , wallahi Batula ina san ki ,so na gaskiya babu yaudara."
Wani farin ciki ne ya lullube zuciyar Batula, wai yau Yaya Nasir ne ke mata wannan zance
Cikin zabura Batula ta farka a baccin da take , sakamakon ruwan sanyi da taji an watsa mata .
Tana ajiyar zuciya Batula ta farka , lokaci guda kuma tana kallon wacce ta watsa mata ruwan
Ba wata babba bace domin Batulan ma ta girmeta .
"Asararriya , har yanzu baki tashi kin yi wanke-wanke ba , to uban waye zai miki , wallahi kika bari na fadawa Daddy sai ranki ya baci ."
Tana gama maganar ta fice
Ajiyar zuciya Batula tai tana murmurshi da cewa.
"Daman mafarki nake Nasir bai zo ba ." Tai ajiyar zuciya
A lokacin Khairat ta shigo dakin tare da sallama
Batula na ganin kawartata tai murmurshi ta ce .
"Khairat ke ce."?
Khairat tai murmurshi tana cewa.
"Eh wallahi , zan biya gidansu Laila shi ne nace bari nazo mu gaisa."
Ta karasa maganar tana kallon yadda duk jikinta ya jike da ruwa
"Rahma ce ta watsa miki ruwa ko , ai naga fitarta da kofi."
Batula tai murmurshi mai ciwo tana cewa.
"Wata rana sai labari ai khairat, yanzu ina iyayena suke , haka kowa zai bar duniyar ai ."
Tsaki khairat ta ja tana cewa.
"Kullum haka ki ke cewa Batula, yanzu a ce kanin mahaifin ki wai bazai iya rike ki da mutunci ba , matarshi ta wulakanta ki yarshi ma haka , sannan shima bai barki ba ."
Murmurshin nan me ciwo Batula ta sake yi kana ta kalli Khairat tana cewa.
"Ai da babu abin da zan dana biki naje naga Nasir ko zan ji dadi ."
Khairat tai dariya tana cewa.
"Ke fa sai a hankali, yanzu ko islamiyya bakya zuwa , Yaya Nasir kuma Allah ya waiwayo da hankalinshi gare ki ."
Batula ke nan yarinya me kalli da nutsuwa, duk da ba sa'arsu khairat ba ce , amman suna tare da juna cikin aminci, sakamakon haduwarsu a islamiyya
Batula ta dade tana wahala a rayuwa, domin tunda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa ta fara fuskantar rayuwa a gidan kanin mahaifin ta .
Wanda komai wulakancin da suka debo kan ta suke zubeshi.
Sai dai Allah ya jarafci Batula da san Yaya Nasir, domin babu abin dake faranta mata rai face ganin hotonsa ko wani jinin shi .
Duk da cewa har yau yaki bata fuskar da zata nuna masa soyyayar da take masa .
Ni ko nace Yaya Nasir a duba maraicin Batula mana๐ค
Anan kuwa Yaya Nasir yanzu ya dawo daga aiki
Tun kafin ya shiga gidan ya tabbatar wa da kansa tabbas sun yi baki , cikin far'a da sakin fuska ya nufi ciki,
Duk da bai san wanne suka zo ba
"Assalamualaikum."
Nasir ya yi sallama cikin falon ya yin da yake raba idanu
Rabi ya gani mahaifiyar Mahmud zaune a doguwar kujera, kana Laila tana kusa da ita , sai kuma Mahmud din a kusa da Laila wato dai duk kujera guda.
Sannan Mama a gefe fuska cike da far'a
"Wa'alaiku mussalam Nasir."
Rabi ta amsa ita ma cikin far 'a
Murmurshin yake Yaya Nasir ya yi , sannan ya samu kusa da Mama ya zauna yana cewa da Rabi .
"Yau ku ne a gidan namu , sannunku da zuwa."
Ya karasa maganar yana murmurshin da bai kai zuci ba
"Ina wuni Yaya Nasir."
Mahmud ya fada
Sai da Yaya Nasir ya d'aga kai ya kalleshi sannan ya amsa masa
Sannan ita ma Laila ta kalleshi tana cewa.
"Sannu da dawowa Yaya."
Ya d'aga mata kai , alamun ya amsa
"Ina wuni Aunty Rabi."
Nasir ke nan
Rabi ta maida masa da fad'i.
"Lafiya lau Nasir, ya gida ya aiki .
Ya wajensu Ummi."
"Lafiya lau suke ."
Aunty Rabi ta maida masa da cewa .
"To Masha Allah, ai Mahmud ne ya dameni , in zo in ga Laila, sai kace ban taba ganin ta ba ."
Ta karasa maganar tana kallon Mahmud da cewa.
"To mun zo hankali ya kwanta ."
Dariya Mahmud ya yi tare da kallon Laila dake kusa dashi cikin matukar yanayin shaukin soyyaya.
Duk a kan idon Yaya Nasir da ke murmurshin yake mai ciwo .
"Ai in sha Allah Mahmud, Laila matarka ce."
Yaya Nasir yaji maganar har cikin kansa yayin da Aunty Rabi ke fada
"To Allah ya tabbatar da alheri, tuwo na mai na ke nan ."
Mama ta fada cikin murna .
Kawai da saurin gaske Yaya Nasir ya mike ya shige dakinsa
Nan su kuwa suka cigaba da hirasu , yayin da Yaya Nasir ya kan iya jiyo su daga daki .
Bayan Mahmud ya dau mahaifiyar tashi sun tafi..
Sannan Yaya Nasir ya fito falon ya zauna cikin matukar mutuwar jiki.
"Uncle baka ci abinci ba har yanzu ."
Laila ta fada tana kallon shi
Kawai kau da kanshi yayi gefe ba tare da ya ce komai ba
Laila ta kalli