Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
Mama, Mama kuwa bama tasan abin da ake ba , domin ta shagala da jan carbin dake hannunta "Uncle lafiya kuwa."? Laila ta sake masa shishshigi🤣 Agogon hannunshi ya kallah kana ya yi ajiyar zuciya. Kamar kuma bazai kalli Laila ba , sannan ya juyo gareta yana cewa. "Kina son yaron nan Mahmud." Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 13 & 14 Ajiyar zuciya Laila ta yi , kana ta kalli Uncle din nata tana cewa. "Yaya ni ban za bawa kai na kowa ba , duk wanda ya dace dani daga gareka nake jiranshi." Murmurshi Yaya Nasir ya yi, sakamakon yadda yaji abin da bai yi zatonsa ba Kawai ya mayarmata da cewa. "Jeki kawon abincin." Anan kuwa Abdallah da Fatima ne cikin mota , suke tafe a hanyar zuwa gidansu Fa'iza "Gaskiya fa kina son Fa'iza da yawah." Abdallah ya yi maganar ga Fatima yana murmurshi Ita ma Fatima murmurshi tai tana cewa. "Eh wallahi, haka nima take sona Dear, wallahi rayuwar Fa'iza abin tausayi ne , zan yi komai dan farin cikinta." Murmurshi Abdallah yay yana sake cewa. "Hmm ai na gani , gashi zamu shopping kin ce a biya a daukota. Nima ai ina san abin da kike so ." Murmurshi Fatima tai tana kallon masoyin nata Yayin data duba fuskar wayarta tana duba wani sako da ya shigo mata . "Karki manta yau muna da ganin likita." Hawaye ne suka ciko mata idanu , ta kalli Abdallah tana cewa. "Ina matukar kaunar ka Abdallah." Abdallah ya juyo yana murmurshi yayin da take ganin wannan hawaye. Bai iya cewa da ita komai ba , domin ji yay baki da ya ta karya masa zuciya. Fatima tai murmurshi ta fice sa'ilin da ya yi parking daidai kofar gidansu Fa'iza Kallo ya yi ta binta dashi har ta shige ciki Kana yayi murmurshi da ajiyar zuciya yana cewa "Allah sarki baiwar Allah Fatima ta, kyakykyawa mai hankali, ya Allah ka bani ita a kaddarata." "Fa'iza tashi , tashi." Fatima tai maganar tana janye malullubin da Fa'iza ta lulluba . Ta tashi zaune tana cewa. "Kai Fatima na tashi to mene." Dariya Fatima tai tana cewa. "Ki fito , ina ta kiran wayarki, Abdallah ne a waje zai kaimu shopping." Wani faduwar gaba Fa'iza taji ya ziyarce ta dajin sunan Abdallah "Abdallah kuma." Fa'iza ta nanata "Ehh tashi-tashi-tashi." Ta fada tana jawota , kana tasa kai waje tana cewa. "Ki sauri ki fito muna waje." Yadda Fa'iza take a wannan tsayen kawai ajiyar zuciya tai , ba tare data motsa ba "Aminiyata ce Fatima, bani da kowa bayan ke , tabbas bazan rusa mana alaka ba Fatima ko zuciyata zata fashe." Ta karasa maganar tana jawo wata doguwar rigarta mai launin marun gami da yellow Cikin sauri ta fara shiryawa Domin zuwa ta same su a waje . Tana fita kofar gida ta fara hangensu daga cikin gilas din motar , sai farin ciki suke abinsu Murmurshi tai sannan cikin nutsuwa ta fara takawa wajensu Murfin motar baya dake a bude nan ta shiga tana cewa. "Soyyaya ruwan zuma." Abdallah ne ya juyo yana mata murmurshi kafin ya ce komai Fa'iza ta sake fad'i. "To ina zamu ne ." "Zamu je Abdallah ya siyo mana abayoyi ne Fa'iza." Fatima ta bata amsa murmurshi Abdallah ya yi kana daga karshe kawai ya dore da dariya. Anan kuma Laila ce ita da wani had'ad'd'en saurayi a cikin falonsu . Bayan sun gama gaisawa da Mama, kana Mama ta shiga ciki ta barsu "Wato Laila tunda naje America, duk rayuwata babu dadi na yi matukar kewarki sosai fatan dai alkawarin mu na nan ." Saurayin mai suna Usman ya yi maganar A daidai lokacin Yaya Nasir ya nufo cikin falon Hakan yasa ya dakata sakamakon muryar Laila da yaji tana cewa. "Nima na yi kewarka sosai , amman har gashi kayi shekaru da yawa a America, gaskiya ban yadda ka damu dani ba , ko nema na baka taba yi ba ." Laila tai maganar cikin shagwaba Zuciyar Yaya Nasir ce ta sake karyewa a take a wannan wajen Cikin rashin ya ke cewa . "Usman ne ya dawo ."? Ya yiwa kanshi tambayar "To Laila auren mu shi ne zai tabbatar da irin kaunar da nake miki, amman ko rana daya babyna bata wucewa ba tare dana tuna ki ba ." Usman ya sake fada cikin soyayya Murmurshi mai jan hankali Laila ta yi sannan ta bude baki da niyyar cewa wani abu. "Assalamualaikum." Yaya Nasir ya shigo da sallama ya tari numfashinta. Sallamar ta amsa masa cikin far'a Kana Usman ya zamo daga kujera yana gaida Yaya Nasir Babu wani salo ko shauki Yaya Nasir ya amsa gaisuwar Sannan ya shige ciki. "Laila ko dai har yanzu Yaya Nasir yana fishi dani ne , ai yanzu na shiryu na gyara halayena Laila." Laila tai ajiyar zuciya domin ganin Uncle din nata a haka duk bata ji dadi ba Shi kam Uncle dakinshi ya shige ya zauna , Domin tabbas sam bai ji dadin ganin Usman ma . A lokacin baya Usman ya shigo rayuwar su da matukar son Laila , duk da cewa uncle baya son kowa ya kusanci Laila komin mutuncinsa kuwa. Sai Uncle yayi amfani da yadda Usman yake takadiri kuma mara ganin girman mutane ya raba shi da Laila. Soyyayar Laila ita ce ta gyara Usman har ya shiryu ya zama mutum , domin a halin yanzu shi yake rike kasuwancin mahaifin sa Alhaji Shehu shanshani , mutum ne mai matukar dukiya. A halin yanzu sam Uncle ba ya jin dadin dawowar Usman. To za mu ji yadda zata kaya tsakanin wannan mutane. Shin ko Mahmud ne zai auri Laila ko Usman ko wani daban . Muje mu tambayi Uncle kawai, Laila 'yar gwal ce .😝 Domin kuwa duk wani saurayin Laila Uncle baya son shi🤔 Yanzu mene ai bun Usman da Mahmud Uncle? Tom ba dai musan me Uncle yake nufi ba , mu dai mu sha bikin shalele 😆 Ga kuma bangaren Fa'iza da Fatima Ga kuma Batula To dai alkalamin Autar Marubuta ne. Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 15 & 16 "Haba dan Allah khairat, wai sai Uncle ya min fada ne , wallahi mun yi yawo sosai , duk na gaji." Laila ta fada cikin mita "Ke wallahi Laila munguwar matsala ce dake , Uncle Nasir da ba ya bari kina fita , shi ne yau kin fito amman sai mitar jaraba, ai gara ai miki auren ma , ki zaman gidan da hujja ." Dariya Laila ta kwashe da ita yayin da suke hada kafad'a da kafada suna tafiya Laila ta ce . "Aure manya , ai saina aurar da Uncle tukun." Da sauri khairat ta kalli Laila tana cewa. "Allah sarki harkin tuna mini Batula, wallahi Laila tana son Uncle sosai ." "Wai wace wannan Batulan kina yawan fada mini ita , kuma Uncle yana santa ."? Cewar Laila Khairat ta ja wo hannun Laila su kai wani lungu tana cewa. "Zo muje gidansu ki ganta , wallahi tana san Uncle." Wata gajiya ce ta sake rufe Laila da ganin yadda khairat tajata wannan waje . Hakan ya sa ta fincike hannunta tana cewa. "Wai duk ina kika san wannan wajejen, ni fa ba kowacce zan bari Uncle ya aura ba , sai wacce ta isa ." Khairat kawai taja mata tsaki Gidan Alaji Muktar Yana zaune ya yi tagumi , kawai yana tunanin irin yadda yayan da ya haifa suke ta mutuwa, a lokacin da yake bukatar su . Duk wacce danta ya mutu sai ya saketa , yana cikin wannan yanayin ne wata matarshi Hadiza ta shigo falon Zama tai kusa dashi tana cewa. "Alhaji lafiya kuwa." Ba tare da ya ce da ita komai ba ,kawai ya zaro wata takarda a aljihunsa ya mika mata . Faduwar gaba taji dasss Hannunta na rawa ta amsa tana budewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un Alaji ni zaka saki , innalillahi 😭." Kawai ta fara kuka , ya mike ya bar mata falon . Ana cikin haka sai ga uwar gidan nasa Hajjiya Ma'anatu ta shigo Tana kallon Hajjiya Hadiza da takarda a hannu tana kuka ta ce . "Innalillahi wa inna'laihir raji un Hajjiya Hadiza sakin ne ko, shi ke nan sauran ni , tunda daman Allah ya yiwa mahaifiyar shi Hajjiya rasuwa shi ke nan tamu ta kare ." Hajjiya Hadiza ta sake fashewa da kuka . Anan kuwa Batula ce zaune kan kujera tana wanke-wanke Ta yi nisa sosai kadan ya rage mata ta gama , sai ga sallamar su Laila Sai da Batula ta fara zuba musu wannan murmurshi nata kana ta amsa sallamar cikin farin ciki Suma cikin far'a suka karaso kusa da ita. Kafin wani ya bude baki ya ce komai , sai ji sukai wani "Shamm" Wasu uban kayan wanki wata mata mai zubin hajjiyoyi ta zube a kan Batula dake wanke-wanke. "Uban me kike har yanzu baki gama ba , to ga wanki nan , maza ki gama ki dora girki sannan ki fara ." Cikin biyayya Batula da amsa da "To Mommy." Kana wacce ta kira da mommy ta juya ta koma ciki Murmurshi Batula ta sake yi musu tana cewa. "Khairat ki dauko wa Laila abin zama mana." Ta karasa maganar tana kallon Laila da duk jikinta ya yi sanyi "A'a! Ke da kike aiki tafiya zami ." Laila ta fada cikin nufar hanyar fita . Bayan sun yi sallama khairat tabi bayanta Tunda suka fito Laila bata ce komai ba haka ma khairat, kowa yana sake-sake cikin ransa "Wai ita Batulan aiki take yi a nan gidan , kinji harta sanni ." Laila taiwa khairat maganar cikin sanyi Murmurshi khairat tai tana cewa. "Allah sarki Batula, yadda take son Uncle ba dole tasan ki , kin gan ta wallahi tana shan wahala , nan fa gidan yayan babanta ne , iyayenta sun rasu."... Nan khairat duk ta bawa Laila labarin Batula na abin tausayi da yadda take son Uncle A karshe duk tausayin Batula ya rufe zuciyar Laila Fa'iza ce tsaye gaban mudubi sanye da rigar da Abdallah ya siyo musu ita da Fatima "A gaskiya rigar nan ta yi kyau Abdallah." Fa'iza ta fada a cikin zuciyar ta, yayin da take sake juya jikinta tana ganin rigar Wayarta dake ringin yasa tai saurin juyawa ga wayar Kana ta zauna bakin gado tare da daukar wayar tana karawa a kunne da cewa. "Hello Rabin Raina Fatima." Daga can bangaren taji muryar Fatima tana cewa "Wallahi bana son fada miki wannan zance a waya kizo dan Allah." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kana ta maida mata da cewa. "Gaskiya 'a'a Fatima." Ba tare da Fatima taji haushin hakan ba , cikin sabon farin ciki ta sake cewa. "An yi mana baiko da Abdallah, ashe dadi sun tsai da magana." Yadda kasan an yi ruwa an dauke, duk Fa'iza sassan jikinta suka dena aiki Sai bugun zuciyarta da yake yi kamar zai fito "Uhm wai da gaske." Fa'iza ta fada yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata Cikin farin cikin dai Fatima ta tabbatar mata da wannan lamarin mai dadin ji . Bayan sun gama wayar , kawai Fa'iza tai murmurshi tana fad'in. "Fatima Allah ya tabbatar da alheri, Allah ya baku zaman lafiya da Abdallah." Ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi Farin ciki ya cika zuciyar Fatima, tana zaune cikin falonsu da wannan farin cikin ne mahaifin ta ya shigo , Sakin fuskar shi ya yi sosai ga yartashi guda kamar rai Zama ya yi yana fad'in. "Me ake yi ne me sunan Mama, kin sha magani ko." Shalelen baban nata baki ta zumburo tana cewa. "Daddy wai shi likitan nan ya yi ta bani magunguna, ni ban sha ba na gaji." Zaro idanu ya yi yana fad'in. "A'a yi hakuri mana 'yata, ai lafiyarki ita ce kwanciyar hankalina dana mahaifiyar ki , daure mana ai kin kusa samin lafiya in sha Allah." Murmurshi Fatima tai tana cewa. "To Daddy na , amman kafin bikin mu da Abdallah daddy ina so ka kai ni Umara , daddy idan da hali hadda Fa'izata." A lokacin mahaifiyar Fatima ta shigo tana cewa. "To masu Daddy." Ta karaso ta zauna Murmurshi Alaji ya yi yana fad'in. "Shi ke nan Fatima, zaku je in sha Allah karki damu." Cikin farin ciki ta mike tsaye tare da cewa. "To Daddy bari naje nasha maganin." Ta wuce cikin farin ciki Murmurshin Hajjiya tasa tana cewa. "Fatima ke nan , Allah ka bawa wannan yarinyar lafiya." Ajiyar zuciya Alaji Usman ya yi kana ya fara da cewa. "Wallahi Hajjiya ciwon yarinyar nan yana damun rayuwata, zan so ace Allah ni ya sanyowa wannan ciwo na zuciya a maimakon Fatima, wallahi zuciyata kullum bata samun nutsuwa idan na tuna da halin da take ciki." Cikin rarrashi mahaifiyar Fatima ta fara cewa da mijin nata Alaji Usman. "Haba Alaji! Ai shi bawa kowa da irin tashi kaddarar, muma irin tamu ke nan , ya jarafce mu da yarinyar da muka fi so , to mu yi tawakkali kawai mu gode masa , tunda gashi dai tana samun lafiya. Kuma ka ga Abdallah da danginsa zasu kula da yarinyar nan , dan sun san halin da take ciki kuma suna santa ." Alhaji Usman ya dukar da kai kasa ya d'ago yana fad'in. "Haka ne , badaban Fatima na son yaron nan ba , kuma auren sa zai faranta mata, da gaskiya ni bana son tai nisa damu , amman farin cikin ta shi ne namu." Hajjiya ta ce . "Haka ne." Anan ma Alaji Sani Shanshani ne zaune cikin wani furgitaccen had'ad'd'en falo. A gaskiya ciki da wajen wannan gida ya matukar haduwa ba a magana. Gefe guda kuma ga wata Hajjiya can da gani babu tambaya matarshi ce Sannan wasu 'yan mata su biyu masu kama da juna , suma zaune a kujera kowacce tana danna wayarta Sallamar dansu ce ta sa suka kalli kofar shigowa falon Yayin da hajjiyan ta amsa sallamar "Usman ina aka je ne."? Mahaifiyar shi Hajjiya ta masa tambayar Yana sosa keya ya karaso ya zauna yana fuskantar mahaifin sa Murmurshi mahaifin nasa ya yi yana fad'in. " Lafiya kuwa, meke tafe da kai ."? Satar kallon Hajjiya Usman ya yi sannan ya dukar da kai kasa lokaci guda kuma yana sosa keya "Daddy a kan maganar Laila ne." Murmurshi gami da dariya Alaji Sani Shanshani ya yi Sannan ya kalli matarshi yana fad'in. "Ai ni nasan akwai magana." Sannan ya koma ya kalli Usman yana fad'in. "Ai Usman a matsayin ku na 'ya'yana , bazan gaza muku a kan komai ba, tun daga lokacin da kowannen ku ya fara numfashinsa na farko a wannan duniyar, idan akwai wanda ya nemi abu daga gare ni ya rasa ya sanar dani." Ya kalli sauran yayan nasa Sannan ya cigaba da cewa . "In sha Allah zaka aure ta , bari daman ita ce sanadin shiryuwar ka , ai alhamdulillah." Su kai dariya Yayin da hajjiya ke cewa. "Sai a kawo mana ita mu ganta , domin kullum kiran sunan ta ake tun kana America." Usman ya yi dariya da cewa. "Za ta zo kuwa mommy." Anan gurin aikin Nasir kuwa. Tashinsa ke nan ya shiga mota da nufin tafiya gida Muryar kanin mahaifin sa Alhaji Bashir yaji tana kiran sunan shi Da sauri ya fito daga cikin motar zuwa waje , yayin da ya durkusa yana gaida Alaji Bashir. "Wai meke damunka ne Nasir, duk ka rame haka , ko akwai wata damuwar a gida ne ban sani ba."? Alhaji Bashir ya yi maganar cikin saurin baki kamar yadda ya saba . *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 17 & 18 Murmurshi Yaya Nasir ya yi , kana cikin girmamawa ya fara cewa. "Wallahi babu komai , komai lafiya lau." Alaji Bashir ya ce . "To ai shi ke nan Allah ya rufa asiri , ka gaida Maman." Yana gama maganar ya juya cikin bugaggiyar shaddarshi da malum-malum ya koma ciki Yayin da Yaya Nasir yake cewa. "Zata ji in sha Allah." Sannan Yaya Nasir ya sami damar shigewa mota . Anan kuwa Mama ce zaune ita da Laila, gama cin abincin su ke nan , domin ko kwanukan basu kwashe ba , wani ma da sauran abinci a ciki Laila wayarta ta aje gefe , ta kalli Mama tana cewa. "Mama Uncle ya taba baki labarin Batula."? Mama ta maida mata da cewa. "Wace kuma Batula." Laila tai murmurshi sannan ta ce . "Mama budurwar Uncle ce , tana son Uncle sosai , wallahi Mama rayuwar ta abin tausayi sosai , iyayenta duk sun rasu tana shan wahala." Mama ta maida mata da fad'i. "Allah sarki." A lokacin Nasir ya bankado labulai ya shigo tare da sallama Kusa da Mama yaje ya zauna a kujera yana ajiyar zuciya Ido suka hada da Laila, hakan yasa ta ce dashi . "Sannu da zuwa Uncle." Ya ce . "Sannunki ke ma ." Ido suka sake hadawa a karo na biyu, Laila tai murmurshi tana sunkuyar da kai "Uncle kana lafiya kuwa."? Laila ta tambaya "Duk ka rame sosai ." Murmurshin ciwo Uncle ya yi , sannan ya ce . "Alaji Sani Shanshani jiya da kanshi ya zo a kan maganar auren ku da Usman." Laila ta zaro idanu cikin mamaki Kafin ta ce komai Uncle ya cigaba da cewa. "Amman bazan bari ki auri Usman ba bai dace dake ba Laila." Laila ta sunkuyar da kai Mama ce ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa. "Nasir wannan abin ya ishe ni , lokaci ya yi da zaka bawa Laila miji ko ka barta ta zaba, tunda ka nuna mana kafi kowa iko da ita . Domin bazan zuba ido yadda kaki aure ba , ka zaunar da Laila ita ma a cikin gida, abin ya isa haka ." Wani furgitaccen zafi Yaya Nasir yaji a zuciyarshi , domin ya lura da batun Mama babu wasa a ciki "Ko Usman ko Mahmud, duk wanda Laila take so , ka aura mata, wannan abin ya isa haka tom." Ta shige daki Cikin yanayin damuwa Laila ta kalli Nasir, babban tashin hankalin data gani yasa duk tunanin ta ya rude Hawaye ta gani bisa idanun Uncle sun zaru suna shirin zubo . Kawai ya mike ya fita kafin a kai ga wannan lokacin Ajiyar zuciya ita ma Laila ta sauke me zafi tana kallon kofar da Uncle din nata ya fice , duk ta rasa me yasa ta damu yanzu haka , kuma tausayin Uncle duk ya kamata. Yaya Nasir ya na fita gidan Umar ya nufa kai tsaye . Shima Umar ya yi mamakin ganin Uncle a wannan lokacin da bai saba zuwa ba Babu korafi Umar ya masa iso har falo suka zauna. Shi kan shi Umar ya fuskanci Yaya Nasir yana cikin damuwa "Abokina lafiya, tunda ka zauna kai shiru , ko wani abun yana faruwa ne ."? Yaya Nasir ya kauda kai tare da ajiyar zuciya "Hmmm." Abin da Umar ya iya fada ke nan Hakan yasa Yaya Nasir ya kalli Umar ya fara cewa. "Mama ce ." "So take na aurar da Laila." Murmurshi Umar ya yi yana fad'in. "Laaa kaji wani zance me dadin ji , alhamdulillah Masha Allah, ai Mama wannan abin da tai shi ne daidai , domin baka da niyyar aurar da ita ." Cikin sauri da mamaki Yaya Nasir ya kalli Umar dake kusa dashi Cikin farin ciki Umar ya sake jaddada masa da cewa. "Wallahi wannan ya yi , a cikin Mahmud da Usman, nasan Laila zata so daya ." Da sauri Yaya Nasir ya mike tsaye tare da wata ajiyar zuciya Idanunsa suka canza kala "Wallahi Umar bana son aurar da Laila ga kowa, idan naji ko naga wani na binta da sunan soyayya sai naji duk na tsane shi , bana son rabuwa da Laila Umar, ban shiryawa hakan ba." Ya karasa maganar yana rike rigar Umar kamar mai shirin zarewa. Tsoro ne ya rufe Umar da ganin yadda Nasir yake . Kawai Nasir ya yi murmurshi ya sake shi sannan ya kama hanyar fita ba tare da yace komai ba "Ikon Allah." Umar ya fada yana bin sa da kallo Bayansu Fatima sun fito daga lecture, kawayenta sai matukar farin ciki suke da jin yadda aka sanya bikinsu da Abdallah Fa'iza tana cikin class a zaune, domin tunda aka fita bata fita ba , ko zuwa duba Fatima ba tai ba ko sun fito Durkusar da kai tayi bisa benci Babu kowa cikin ajin , daga ita sai wani dalubi da yake karatu a can bayan benci Wata me suna Maryam ce ta shigo ajin yayin da take kallon wannan dalubi da cewa. "Munaf. Sannu da kokari." Ya amsa mata da "sannu Maryam." Kai tsaye gun Fa'iza ta nufa , yayin da take kiran sunanta tana kuma kokarin d'ago mata kanta sama Cikin jajayen idanu Fa'iza ta d'ago "Maryam ya akai ." Maryam cikin rike haba ta fara fad'i. "Haba Fa'iza, wai meke damunki, duk sai ramewa kike yi , haba dan Allah mene ne ."? "Babu abin dake damuna Maryam." Fa'iza ta maida mata da amsa Ba tare da jira ba Maryam ta sake maida mata da cewa. "Gashi idanunki sun yi jah , alamun kin yi kuka , ai shi ke nan , idan tayi wari maji ." Dariyar da bata kai zuciya ba Fa'iza ta yi Sannan ta ce . "Ina Fatima."? "Fatima tana can tana ta nemanki fa , bata san baki fito ba ."..... Fatima ce zaune kan gado tana kallon hotonta dana Fa'iza Murmurshi tai tana shafa furkar Fa'iza, sannan ta fara cewa. "Ban san meke damunki ba , wani abu ya dade yana damunki amman kin ki sanar dani ." Zama ta gyara tana sake zumin din hoton ta cigaba da cewa. "Aminiyata har a aljanna, ina kaunarki Fa'iza, in sha Allah zan yi kokarin sanin meke damunki, tun da baza ki sanar dani ba ." Ta karasa maganar tana kallon saman dakinta kamar me yin wani Nazari . "Wannan wanne irin rashin mutunci ne da cin fuska , yanzu yarinyar nan Laila kina ji wai yaron gidan Alaji Sani Shanshani zasu bawa." Inna tai maganar bisa wayar dake hannunta ta kara a kunne "Mene ne Alhaji Sani yafi mijin Rabi ? Tsabar cin mutunci, to wallahi wannan lamarin ba a a yi shi ba ." Daga can bangaren Bahijja cikin muryar girmamawa ta fara cewa da mahaifiyar tata "Dan Allah Inna ki yi hakuri abi wannan lamarin a sannu , yanzu haka ma ba haka zancen yake ba ." Cikin wannan fada dai Inna ta sake fadin "Kamar ya ba haka zancen yake ba , wallahi naje gidan naci mutuncin Nasir din , tunda ba shi data ido ." Bahijja ta sake fad'in "Ni dai dan Allah Inna ki hakuri, karki je gun Nasir da wannan maganar." Inna ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar tata Anan kuwa Batula ce ke girki ta kunna wayarta Tana sauraran wakar hamisu breaker mai taken "So Ne." "Banza jaka kin damu mutane da waka." Juyowa Batula tai tana kallon Rahma dake fada mata wannan maganar Batula kashe sautin ta yi kana ta cigaba da abin dake gabanta "Ai wallahi bari daddy ya dawo , zan fada masa Musa me gyaran takalmi yana son ki gara kawai a aura masa ke mu huta ." Da sauri da tashin hankali Batula ta kalli Rahma tana cewa. "A'a dan Allah Rahma, karki fadawa Daddy wannan maganar, Musa ba san shi nake ba , kuma daddy zai kama zancen ki ." Cikin maraici Batula ta karasa maganar "Hhhhhhhhhh to ai taimakon ki zai , banda shi waye yake son ki , can zaki talauci ya kashe ki banza ." Tasa kai Batula tai saurin riko rigar Rahma, hakan yasa Rahma ta dakata tana kallon ta cikin zafin rai "Uban me zan miki kika riken riga kazama kawai." Ba tare da Batula ta damu dajin wannan maganar ta Rahma ba ta fara cewa... *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta _______________________________________ Babu editing Page 19 & 20 "Kar ki fadawa Daddy, Musa kowa yasan ba ilmi ne dashi ba ." Rahma tasa hannu ta doke hannun Batula, taja tsaki sannan ta wuce Kawai hawaye Batula taji ya zubo mata Anan kuwa Alaji Sani ne yake yin waya ,yadda ranshi yake a turbune bai canza ba ya fara cewa. "Haba Akilu, to ita wannan yarinyar yar gidan waye, da zaka ce an nemeta a garin nan an rasa, bayan na fada maka ina tafiya a titin babbar unguwa ta taalakawa na ga yarinyar, sai da nai ta jira ko zanga inda ta shiga amman ban gani ba , gaskiya ka sake kokari Akilu ka zo min da labari mai dadi ." Yana gamawa ya aje ajiyar zuciya tare da cewa. "Gaskiya wannan yarinyar tamin , lokaci guda san ta ya kamani, tomm Hajjiya kishiya na tafe a gidan nan." Ya yi maganar shi kadai yana tunano yadda yadda ya ga wannan yarinyar, sai abin yake faranta masa rai . Sakamakon yau asabar babu inda Uncle yaje , tun wajejen hantsi yake a falo , har zuwa wannan lokacin da rana ta kusan faduwa. Idan har kasan Yaya Nasir, to yanzu idan ka

Chapter 3 of 5