An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ο»Ώ*MAHAUKACIN SO* π
Na
Autar Marubuta
______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βπ»πΌπ»
πΉ__________πΉ_________πΉ__________πΉ_________πΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_π€²πΌ
<><><πΉ><><><>πΉ<><><>πΉ<><><><>πΉ<><><><><>πΉ<><
Babu editing
Page 1 & 2
Wani mutum ne magidanci kakkaura zaune cikin wani tafkeken falo ,jarida ce bisa hannunsa yana karantawa.
Wannan mutum ba kowa bane face Alaji Muktar mazaunin kaduna
Mutum ne mai kudi bana wasa ba .
Wata dattijuwa ce ta shigo falon, kallo guda zaka ga babu wahala jikin wannan tsohuwa.
Tsayawa tai ta zuba masa ido tana kallon shi .
Bayan ya lura da ita ne , ya yi sum-sum ya cire gilashin dake fuskar shi yana aje jaridar .
"Hajjiya lafiya kuwa."?
Ya yi wa dattijuwar tambayar
Kawai tsaki tai tare da juyawa ciki tana cewa.
"Duniya ce ."
Alaji Muktar ya yi murmurshi yana cewa.
"Hajjiya ke nan ."
Kallon hoton dake falon dakin take kamar zai motsi a yadda take gani , sake kura masa ido take tana kallon dayar matar da suke tare a cikin hoton da suke matukar kama da juna .
Wata mata ce ta katse mata tunanin data fara da cewa.
"To Mama zan tafi Allah ya jikansu Allah ya bada hakurin rashi."
Sannan Mama ta dawo hankalinta tana kallon wannan matar tana cewa.
"To mun gode Zuwaira , Allah ya bada lada."
Kana matar ta fice
Mama ta kalli Nasir dake tsaye da jaririya a hannunsa yana jijjigata ta ce .
"Sannu Nasir da raino , ai idan suka zo suka dauketa sai ka huta ."
Rai ya hade mata yana cewa.
"Haba Mama , ni fa baza a basu wannan yarinyar ba , kawai kar ma su zo."
Mama ta kalli autarta Ummi dake gefenta suna hada idanu.
Sannan ta koma ta kalli Nasir tana cewa.
"Kamar ya baza a basu ita ba , yarinya jaririya kai ne zaka shayar da ita ."?
Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da shigewa cikin daki ba tare da ya ce komai ba .
Gidan Mama ke nan mutuniyar kirki wacce tun shekarun baya mijinta ya rasu, kana kanwarta wacce suke tare ita ma Allah ya yi mata rasuwa, sai Mama ta zamo ita ka dai , sai 'ya'yan ta da Alaji ya bar mata
Ibrahim, Nasir, sannan Ummi
Wanda a kwana uku da suka wuce ne babban dan nata Ibrahim da matarshi Allah ya yi musu rasuwa, sanadin hatsarin mota.
Wanda suka tafi suka bar jaririya yar karama mai suna Laila .
Sai dai tunda a kai rasuwar yau har kwana uku Nasir yaki bawa dangin matar jaririyar , ya ce ita kawai yake gani yaji dadi tunda babu yayanshi Ibrahim..
Wannan ke nan
Yana zaune a falo jaririyar sai kuka take , ya tashi ya dauko fidarta dake cike da madara ya fara dura mata , har ta fara sha , amman tasake bingirewa da kuka .
Ya mike tsaye ya dauko ruwa ya bata , sannan tai shiru ya fara yi mata waka yana jijjigata da cewa .
"Lailo, Lailo rigima, Lailo Lailo rigima, kukan ya isa haka ."
Tai shiru ta tsura masa idanu , yanayin wata rawa da yayi mata ya sa ta sake fashewa da kuka .
Sai ya cigaba da jijjigata yana mata wannan wakar .
A lokacin Mama ta shigo , ta kalli Nasir cikin takaici tana cewa.
"Wai Nasir mene kake yiwa yarinyar nan , saboda taurin kai ka basu yarinyar nan amman ka ki , kullum kuka a cikin gidan nan , yarinya jaririya duk ta rame ta yi baki , to wallahi bazan yadda ba sai ka basu yarinyar nan."
Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa.
"Haba Mama dan Allah, ni zan kula da yarinyar nan idan ku baza ku iya ba , babu inda zan kai ta ."
Mama cikin fada ta ce .
"To ai ka basu su shayar da ita ko , idan kuma kana da nonon da zaka bata naji ."
"Haba Mama, Laila fa watanta biyar a duniya, ai ta kai lokacin yaye , ni wallahi na yayeta babu wanda zai shayar da ita ."
Mama tai shiru tana kallon Nasir domin takaici ya sa ta rasa abin cewa.
A lokacin wata kawar Ummi ta shigo , ta durkusa da gaida Mama .
Sannan Nasir ya sa jaririyar shi a baya ya goyata .
Washe gari
Wajejen hantsi wata dattijuwa zubin masu fada tana zaune a tsakar gida ,
Tsinke ne a hannunta tana sakace, ta jefar da tsinke tare da tsaki da fadin .
"Bahijja, Bahijja."
Tai kiran tana tura kanta cikin dakin da Bahijjan take .
Bayan Bahijjan ta amsa ne , ta fito tare da zama gaban mahaifiyar tata tana cewa.
"Gani Inna na yi zatan ma bacci kike yi."
Inna ta ce .
"Shiryawa zaki mu je mu dauko wannan yarinyar idan baso suke su kashe taba .
Ita Maman Nasirun fin karfinta ya yi da baza ta ce ya bada ita ba , ya bayar ."
Bahijja tai ajiyar zuciya me zafi tana cewa.
"Dan Allah Inna kibar musu ita."
Inna ta ce .
"Lallai ne Bahijja, ai daga ke har Nasirun babu wanda yasan zafin haihuwa, shi ya sa baku damu ba ,
Kuma wannan yarinyar Laila ai nima jikata ce , ina da iko da ita , dole zan je na karbota mu anan akwai wanda zai shayar da ita ."
Ta karasa maganar tare da mikewa tsaye ta shige daki , da nufin shiryawa domin zuwa gidan Mama.
Anan kuwa Nasir yana zaune a falo sai kwalawa Ummi kira yake yana fad'in
"Wai har yanzu ba a gama wankan ba ne ."?
Ummi ya yi mata kiran yafi a 'yarga , harta gaji ta dena masa magana
Ita ma Mama dake zaune a falon ko kula shi ba tai ba , Kamar ma bacci take son yi
A lokacin Ummi ta shigo rike da Laila a hannunta an san ya mata kaya masu kyau .
Sai suka ji ana kwankwaso kofar falon .
Nasir ya mike ya karbi Laila a hannun Ummi yana cewa.
"Je ki duba ."
Mama kawai taji dariya ce ma ta kamata .
Ya zauna tare da Laila a hanunshi , Ummi ta nufi kofar tare da budewa .
Inna da Bahijja ne , hakan ya sa cikin sakin fuska Ummi ta musu iso zuwa cikin falon .
Amman yadda Ummi ta kula furkar Inna babu annuri ko kadan , musamman yadda taji ta ratsa tsaki da ta ga Nasir.
"Sannunku da zuwa Inna , ku ne a gidan ."?
Mama ta fada yayin da take gyara musu gurin zama .
Zama suka yi , Bahijja ta gaisa da Mama cikin far a
Sannan Nasir ya kalli Inna yana cewa.
"Inna ina kwana ."
Ya mutse fuska ta yi sannan ta ce .
"Lafiya lau , kawota ."
Ta mika hannu, Nasir ya kalli Mama kamar bazai bada Laila ba sannan ya mika mata .
Murmurshi Mama ta yi tana kallon furkar Inna da babu annuri tana cewa.
"Ya mutanen gidan suke , ya karin hakuri."
Inna ta kalli Mama tana cewa.
"Hakuri kam muna ta yi , tunda ga shi mun zo mun ga yarinya jaririya duk ta canza , saboda wahala .
Shi ya sa na taso domin yau zaku bamu ita."
Inna ta aje maganar tana kallon Nasir
"Tafiya da ita kuma ."?
Nasir ya tambaya
Inna ta maida masa da amsa da cewa .
"Ehh ko zaka hana ne ubanta ."
Nasir ya mike tsaye tare da cewa .
"Amma ai na ga mu ne dangin mijin yarinyar nan , dan haka mun fi kowa iko da ita."
"Wallahi idan ka ce zaka min rashin kunya zan kwashe ka da mari anan wajen ."
Inna ta maida masa
Mama ce tai ajiyar zuciya tare da kallon Inna tana cewa.
"Ki yi hakuri Inna, ai abin bai kai haka ba , za a baku ita ."
"Mama kamar ya za a basu ita , a kan me ."?
Mama ta kalli Nasir cikin fushi tana cewa.
"Idan ka sake samin baki a magana sai na bata maka rai ."
Inna ta kalli Ummi tana cewa.
"Shi ga ki debo mini kayanta ."
Mama tai saurin dakatar da ita da cewa .
"Ba sai an yi haka ba Inna in Sha Allah gobe da kai na zan zo na kawo muku Laila, in Allah ya yarda ."
Nasir yaji wani abu ya tokare masa zuciya
"To shi ke nan Allah ya kai mu goben , muna jiran ku."
Inna ta karasa maganar tare da mikawa Ummi jaririyar tana kuma tashi tsaye
"Haba ! Ko ruwa baku sha ba zaku tafi ."
Mama tai magana tana kallon Inna , yayin da ita ma Bahijja ta mike tsaye
"Eh zamu tafi muna da komai a gida, sai naji ku goben ."
Tana gama fade ta fice Bahijja tabi bayanta...
Autar Marubuta βοΈ
07040805269
WhatsApp only
*MAHAUKACIN SO*ππ
Na
Autar Marubuta
*AUTAR MARUBUTA CE*βπ»πΌπ»
πΉ__________πΉ_________πΉ__________πΉ_________πΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_π€²πΌ
<><><πΉ><><><>πΉ<><><>πΉ<><><><>πΉ<><><><><>πΉ<><
________________________________________
Babu editing
Page 3 & 4
"Haba Mama dan Allah, hakurin ki ne ya sa matar nan take mana haka , basa da wani iko da Laila, domin a yanzu bata da wani uba da ya wuce ni ."
Nasir yayi maganar cikin bacin rai
Mama ta ce .
"Nasir bana san tashin hankali, dole gobe zan mayar musu da yarinyar nan, idan ya so tai shekara biyu sai su dawo da ita , ba shi ke nan ba ."
Nasir ya ce .
"Nima zan iya rainon shekara biyun ai , gaskiya babu inda za a kai ta ."
Mama ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa.
"Kai mahaukacin ina ne wai Nasir, to wallahi gobe dole za a basu yarinyar nan ko kana so ko baka so , baki daya shekarun naka nawa suke , tunda aka haifi yarinyar nan ka haukace mana a gida . To Allah ya kai mu goben zan kawo karshen komai ."
Tai tsaki ta shige daki.
Nasir ya karbi Laila a hannun Ummi, yayin da wasu hawaye suka zubo masa .
Har dare yayi Nasir yana cikin takaicin gobe ta yi .
Domin duk wata mafita ya duba domin ganin an bar masu Laila a gidan amman ya rasa yadda zai yi .
Haka da dare ya yi Ummi da Mama suka shige daki da Laila suka kwanta , shi kuwa Nasir yana falo zaune ko abinci ya kasa ci .
Washe gari da safe
Wajejen hantsi Inna na zaune tana hutawa tana tunanin yau za a kawo mata jikarta
Anan kuwa Ummi tunda Allah ya sa ta kula cewa Laila bata nan hankalinta ya tashi , ta duba duk gidan amman bata ga Laila da Nasir ba
Hakan ya sa ta tashi Mama a bacci take fada mata
Nan ita ma hankalinta ya tashi matuka
"To kira shi a waya mana , ko ya tafi kai musu ita ."
Mama ta fada
Ummi ta ce .
"Wallahi Mama wayarshi a kashe tun d'azu."
Mama tai ajiyar zuciya tare da fadin
"Oh ni Nasir ina ka shiga ."
Ta fita ta nufi dakinsa, koda Mama ta kula da yanayin dakin sai ta ga kamar Nasir ya debe kayansa
Da sauri ta koma dakin su ta duba kayan Laila, ta ga riga guda biyu ce kawai a cikin akwatitinta
"Innalillahi Ummi ba dai Nasir guduwa ya yi da yarinyar nan ba ."
Ummi taji gabanta ya fadi , ta kalli Mama da cewa
."kamar ya Mama me kika gani wai ."
Cikin tashin hankalin nan Mama ta kara mata da cewa .
"Na duba dakinsa kayanshi basa nan , kuma dubi kayan Laila."
Cikin faduwar gaba Ummi ta sa hannu cikin akwatin ta ga rigunan Laila guda biyu sai wata takarda da akai rubutu da fensir a ciki .
Da sauri ta dauki takardar tana zaro ido tana kallon Mama
"Shi ne ya aje takardar ko , karanta muji ."
Ummi cikin jin tsoron abin dake cikin takardar ta zura mata ido da nufin fara karanta wa .
"Mama ku yafe ni , ni na tafi da Laila, sai wata rana karku neme ni , kar kuma ku d'aga hankalinku , idan da rabo zamu gana watarana babata . Sako daga Nasir."
Abin da Ummi ta karantowa Mama ke nan
Mama hannayenta guda biyu ta dora a kai cikin tashin hankali tana cewa.
"Innalillahi wa inna'laihir raji un. Yanzu abin da Nasir zai mana ke nan , wannan wanne irin mahaukacin yaro ne .
Innalillahi wa inna'laihir raji un."
Mama ta sauke hannayen kasa tare da zama a bakin gado cikin wani yanayi
Dogon numfashi Ummi taja , sannan ta aje shi cikin matukar takaici da tunanin irin abin da Nasir ya aikata musu
"Yanzu ni me zance zanin aro ya bata ."
Mama ta fada tare da fara kuka
Ummi ta durkusar da gwiwowinta kasa a gaban Mama , sannan ta dafa kafar mahaifiyar tasu cikin rarrashi ta fara magana.
"Dan Allah Mama ki dena wannan kukan , in sha Allah duk inda Yaya Nasir ya je da Laila zasu dawo."
Cikin sabon kukan takaici Mama ta ce .
"Yi shiru Ummi kar zuciya ta buga , yanzu ina zansa rai na idan wannan zancen ya fita."
Ummi ta durkusar da kai kasa , yayin da wasu hawaye suka gangaro mata , domin tasan tabbas abin da Nasir ya yi ba abin da kuda zai bi bane , dole Mama ta shiga tashin hankali.
Har wajejen 12 na rana , su Mama suna cikin wannan tashin hankali, duk sun kira wasu daga cikin 'yan uwa , da suke tunanin Nasir zai je amman babu labari.
Anan ita ma Inna sai mita take yi, har Bahijja ta gaji da ji
"To yanzu dan Allah Inna yaushe garin ya waye , ai tunda suka ce zasu kawota , zasu zo ai ."
Inna ta maida mata da cewa .
"Shiru kike ji makad'i ya fad'a rijiya ai , gaskiya abin ya ishe ni haka ."
Bahijja tai ajiyar zuciya tare da gyara zaman yaron dake kafarta mai kimanin shekaru biyar da haihuwa
A lokacin wata 'yar Innan ita ma ta shigo gidan me suna Rabi .
Yaron mai suna Mahmud ya tashi daga kafar Ummi da gudu ya nufi Rabi , ita kuma tasa hannu ta dauke dan nata sama .
Murmurshi Bahijja tai tana cewa.
"Lallai Mahmud ka kyauta ."
Mahaifiyar Mahmud ta ce .
"To kinga lefinshi , dan gatan babanshi .".
Ta karasa maganar tana kallon Inna da cewa .
"Inna har yanzu basu zo ba ne ."?
Inna ta dauke kanta , dariya ce taso kama Bahijja, domin wani abin idan Inna tai yana matukar bata dariya .
Kallon Inna tai tana cewa.
"Inna ke fa kina da jikoki , da zaki bar musu Laila, kinga Mama bata dasu ."
Kawai Inna ta fashe da kuka tare da face majina da gefen zaninta tana cewa.
"Allah ya jikanki Batula , Allah ya miki rahma , saboda ita nake son rike wannan jaririyar.
Allah ya jikanki Batula."
Duk sai jikinsu ya yi sanyi , yadda suka tuna 'yar uwar su .
Bayan sallar magari ba Mama ta dukufa da addu'a ,
Domin har yanzu babu labarin Nasir
Bayan Mama ta idar da adduarta, ta kalli Ummi da ke gefe ta yi tagumi ta ce .
"Kira kanin mahaifin ku Alaji Bashir, kiji wanne hali ake ciki ."
Cikin mutuwar jiki Ummi ta nufi daki domin dauko waya .
Washe gari
"Zancen banza , zancen wofi , kamar ya Nasir ya bata tare da Laila."?
Inna tai maganar cikin masifa , Bahijja dai tai shiru , hakan ya sake ingiza Inna tana cewa.
"Ai zancen duniya ba ya buya , tun jiya abin ya faru amman baza su iya sanar damu ba , Allah wadaran sirikai irin wannan wallahi
Aikin banza aikin wofi ."
Ta sake kallon Bahijja da ita ma abin ke dukanta tana cewa.
"To yanzu wanne hali ake ciki , shi kanin baban nasu Bashir me ya yi akai ."?
Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata.
*MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal
Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services
Sai shaidar biya a 07040805269
Bana son katiπ
*MAHAUKACIN SO*
Na
Autar Marubuta
*AUTAR MARUBUTA CE*βπ»πΌπ»
πΉ__________πΉ_________πΉ__________πΉ_________πΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_π€²πΌ
<><><πΉ><><><>πΉ<><><>πΉ<><><><>πΉ<><><><><>πΉ<><
________________________________________
Babu editing
Page 5 & 6
A daren yau ma kuka Mama take ta yi , carbinta na hannunta
Ummi ce take rarrashin ta da cewa .
"Mama ki yi hakuri dan Allah, kinji abin da malamai suka ce , suna cikin koshin lafiya , kuma kin san Baba Bashir zai cigaba da kokarin ganin Nasir ya dawo , ki dena kuka ."
Mama cikin wannan kukan ta ce .
"Ki bari kawai Ummi , Nasir ya yi abin kunya , kiji irin maganganun da mutane suke yi , ba kuma sa duba cewa Nasir kanin mahaifin Laila ne , amman wasu har cewa suke yankan kai zai shiga da ita , wannan wacce irin masifa ce ."
Ta sake fashewa da kuka .
Bayan wata daya
Anan cikin wani babban gida kuwa , Alhaji Usman ne zaune a falonsa yana wasa da wata yarinya me kimanin shekaru biyu, yarinyar kuwa sai dariya take ta yi abinta
A lokacin matarshi ta shigo tana murmurshi da cewa.
"Alaji ke nan fatiman ce dai sai wasa ake da ita , kamar baza ka fita office ba ."
Dariya ya yi yana daukar yarinyar bisa kafarsa yana cewa.
"Wato Hajjiya wannan yarinyar tamu Fatima , tafi min komai , idan ina tare da ita duk wata damuwa mancewa nake da ita ."
Hajjiya ta ce .
"Hmm Alaji ke nan ."
Alaji Usman ya sake fadin .
"Allah dai ya raya mana ita , ta taso cikin daula da rikon amana da sanin ya kamata."
Ta ce .
"Ameen ya Allah, kamar dai halin babanta."
Alaji ya yi dariya.
Inna ce nan zaune a cikin daki ,
Bahijja ce ta shigo sanye da kayan makaranta .
Zama ta yi kusa da Inna tana cewa .
"Wash Allah na gaji Inna."
Inna ta kalleta da cewa .
"Ai ana rana , amman yau kun taso da wuri ."
Bahijja ta ce .
"Wai Inna mancewa ki kai muna jarabawar fita ne ."
Inna tai dariya ta ce .
"Au haka ne fa , to Allah ya taimako."
Bahijja ta ce .
"Ameen Innarmu , daman yau ina son naje gidan Aunty Rabi ."
"To ai shikenan Allah ya kaimu."
Cewar Inna
Sannan ta kara da fad'in
"Ohhh ni duniya, har yanzu babu labarin Nasir ko."?
Bahijja ta ce .
"Ummmm Inna ke nan ."
Inna ta rufe da cewa .
"To Allah ya kyauta, abin ya wuce yadda muke tunani.".
Bayan shekaru biyu biyu
Mama ce a zaune a tsakar gida tare da carbi a hannunta, ta kalli Ummi dake gefenta ke danna waya tana cewa.
"Wallahi babu abin da zancewa kanin mahaifin ku Alaji Bashir, sai fatan alheri.
Ki dubi irin wannan kayan dakin da ya yi miki , wallahi sai dai godiya , ai da wani ne bazai yi ba ."
Ummi ta kalli Mama ta ce .
"Uhmmm! Haka ne Mama. Ya rike mu da gaske , sai dai mi fatan Allah ya bamu ikon biyanshi ."
Mama ta ce .
"Haka ne , Allah ya bada lada , sauran kwana goma fa , kamar yau aka sa bikin nan ."
Ummi ta sunkuyar da kai tana murmurshi, yayin da Mama take sake cewa .
"Ga Bahijja yanzu ta kusan shekara a dakin mijinta ."
Ummi ta ce .
"Haka ne ."
Anan gidan Alaji Usman kuwa
Shi ne tsaye a cikin falo , yana bude murya yana cewa da matarshi .
"Wai haryanzu baki shirya fatiman ba ne , na ga alamun kina son na makara ."
A lokacin matarshi ta fito rike da hannun Fatima wacce aka shirya tsaf da kayan makaranta tana cewa.
"A yi hakuri mana Alhaji, ai gamu mun fito ."
Ya rike hannun yarinyar tasu ya yi waje , yayin da yarinyar ke kallon mahaifiyar tata tana cewa.
"Bye-bye mommy."..
......
Bayan wasu shekaru
Kasaitacciyar budurwa ce kwance kan gadonta tana hutawa, domin ko alamun bacci babu a tare da ita .
Wayarta ta jawo a gefe kai tsaye ta nufi wata number da kai saving da My fa
Ta dannawa number kira , bugu daya , wata mace me dadin murya ta d'aga tana cewa.
"Hello Fatima ya kike ya mommy."?
Fatiman ajiyar zuciya tai tana cewa.
"Wallahi Fa'iza lafiya lau , daman ina son mu hadu ne ."
Daga can bangaren wacce aka kira da Fa'iza ta fara cewa .
"Ba damuwa Fatima , zan zo in sha Allah."
Ta karasar maganar da yaren masu jan kunne (turanci)
Bayan sun kammala wayar , Fatima na saukewa wani kiran ya shigo mata , wanda ya matukar faranta mata rai , ba kowa bane face muradin aurenta Abdallah.
Anan gidan Mama kuwa, bayan shekaru masu yawa babu abin da ya canza a wannan gidan , idan ka cire wasu shekaru a can baya da Mama ta kasa gane kanta sanadiyar shigowar Nasir cikin gidan babu zato babu tsammani
A yanzu haka duk suna zaune a falo , a kan carpet suna karyawa .
Nasir ne ya kalli Laila da duk hankalinta ke kan wayarta yana cewa da ita .
"Laila bana hanaki danna waya ba , lokacin cin abinci."?
Baki ta turo gaba kamar mai shirin kuka , sannan ta kalli Mama ta ajiye wayar a gefe ,kana ta maida hankalinta ga abincin dake gabanta
"Uncle N , ina so naje gidan Aunty Ummi."
Laila ta yi maganar tana kallon Nasir
Shima kallonta yayi sannan ya maida mata da cewa .
"Ki bari sai gobe zan kai ki ."
Laila ta ce .
"Tom Uncle."
Mama dai bata ce dasu komai ba
Wannan ke nan , shekarun baya da suka wuce Mama tana zaune da rana cikin gidanta , sai taji sallamar Nasir ya shigo , hakan ya matukar tada hankalinta sosai , domin tare da Laila ya shigo a hannunsa, lokacin tana da shekaru uku ,
Babu abin da Mama ta iya cewa a kan wannan lamarin , domin tunda Nasir yasa kafa ya fice da Laila tana jaririya, bai dawo da ita ba saida ta shekara uku .
Mama kawai kuka ta fashe dashi mai matukar taba zuciya, mutanen