dr Shikadai Har guda 3 Sai family pictures nasu Wani Kala ba irin Wanda tagani afalon gidanshiba.
RADIYA Tamike Jikin photon taje ahankali tasanya Hannu tashafo fuskan dr Obinna,sosai takejin shauki aranta da tsananin 'kaunar Shi,harta saita Wayarta Camara Zata dauki photon fuskan dr Obinna meta tuno oho tafasa wayae ta kawar Jikin photon.
Tare da komawa wajen zamanta, saiyanxu cikinta Yafara Kuka alaman yunwa Yafara damunta,Haushine yakamata data tuno tana DA break fast amota Cikin jakar Hannunta saidai fidis tamanta Bata daukoba sbd rudewa Kan dr.
Dole ta maida yunwarta Tacigaba DA Zaman jiran dr, jikinta ta jingina ajikin Kujeran Zaman banxa datake Zaune a office din, ahankali tafarajin bacci Yafara daukanta Abunka DA Wanda Daman bacci Bai ishetaba Tuni ta bingire Tacigaba DA kwasan baccinta.
Dr Obinna Saida yayi awa uku cur kafin suka Gama aiki,Cikin Sauri yashige Dakin change dress baijimaba yafuto,Hannu suka Fara sha DA abokan aikinshi tare da murnawa juna Kan Saar aikn DA sukayi wato sunyi aiki Cikin nasara Domin Allah yayarda ansamu hanyar warakan matar.
Office nashi yawuce Bayan yabar komai Na matar ahannun abokan aikinshi, Saida yayi nokin Kamar ba office nashiba.
kafin yashiga Dan gudun Karya Ganta Cikin Wani Hali Dan yasan Mata bakowa keda hankalin kintsiba, Aiko Yana Shiga yahangota Kwance Kan kujera tana baccinta hankali Kwance,ta dukunkune DA hijab DA alaman sanyin AC Yana damunta, akanta yatsaya Yana Kare mata Kallo.
Ko kadan Babu hayaniya acikin baccinta Kamar ba maceba, Ahankali numfashinta Ke Shiga dafuta,fuskanta fayau Babu ado Sai Jan janbaki DA tasanya akaramin labbanta,gashin Idonta yabazu sbd tarufe Idonta Hakan yakara Mata kyau,dr yatabe baki aranshi Yana fa'din Balaifi tana DA.....shiru yayi sakamakon Bude Ido DA Radiyar tayi sbd Jin alaman kamar ana tsaye akanta.
Dr yahade Giran Sama Dana 'kasa Cikin Hararanta yace" Karki batamun lokaci kisameni amota,harya juya zaifuta yatsaya Daga nesa yace"While ki tabbatar kina DA kudin biyana ladan Mun bacci a office without my permission.
Baijira amsarta ba yafuta a office din,Itakan Radiya mgnr dariya yabata Hakan yasa Yana futa ta fashe DA dariya,Dasauri tabude Wani kofa Wanda take zaton bandakine Aiko Cikin saa tasamu hakane,fuskanta ta dauraye sbd baccin datayi agaban Mirrow Na toilet din ta tsaya tasake Gyara fuskan ta Duk dababu kayan makeup fuskar tayi kyau .
Jin hon Na motar dr Obinna Daga waje yasa DA gudu tafuto Daga bandaki,Cikin Sauri tayi wajen motar nashi Domin Har yayi Ribas Murfin Gaba tabude tashige, yayinda patients dake bin layi dr Hassan Yana Dubasu Wanda ya wakilci dr Obinna ayau suka bita DA kallo aransu Suna mamakin wacece ita Dan sunga Ko kadan basuyi kama DA dr ba bare suce Ko 'yar uwanshine.
Cikin Haki sbd gudun DA tayi tace"Am sorry dr,Dr ya kauda kai Yana tukinshi maigadi shine yabude masa get tare damishi adawo lfy,Saida suka Hau Kan titi kafin dr Yajuyo gAreta Azatonta mgn zaiyi Mata Amman saitaga sabanin Hakan Takardan daya ajiye dazu shine yadauka yabude hannun Shi daya Yana tuki Dayan Yana rike DA Takardan time to time Yana Kalla Yana gyada Kai DA alaman Wani abun yake dubawa.
Itakan Radiya Hannu tasa abayan motar ta dauko Jakarta I rish nata DA lemun Coca cola ta'dauko Cikin Jin yunwa tabude Atsakiyan su tasaka itada dr Tace "Dr Bismillah.
Dr ya girgiza Kai alaman ah ah,saidai itama Bataci DA yawaba sbd kunyar dr din datakeji Duk DA yinwar DA take tsananin Ji karshe lemun kawai ta iyashan Rabi ta mayar Cikin Jakarta taajiye.
Tfy sosai suka farayi Wanda bakajin komai Sai iskan mota,Daga ita harshi Babu Wanda tace DA kowa komai.
RAdiyAr nema Cikin karfin Hali tare da sonjin Muryan Dr din DA Bata gajiya dajinshi, tace"Nawa zanbiya kudin baccin? Gara kasanar Dani intanadi kudin biya sbd nasan dole lallausan Kujeran nan yayi da'din tsadan biya.
Sarkin surutu dr yafa'da aranshi Bayan yagama Jin mgnrta,saidai abun mamaki kanzil baice mataba sabanin hakanma wayar Shi dake Saman mota yadauka yafara dannawa Kida ya yasa Wayarshi tare dayin connection Cikin Bluetooth dake kunnan Shi Yafara saurara motar ya karawa gudu tare da sake tamke Belt Na Mota dake jikinshi,Ido ya maysr Kan Radiya Cikin kallon uku taro Sisi yace"Daura belt.
Ikon Allah Radiya tafa'da aranta Wai Yau itace tazamo Sarkin surutu Wanda Har ana kosawa DA ita,atarihin rayuwarta tasan itaba Mai shishshigi Ko yawan mgn bane Abu daya tasani itadin Sarkin fadane uwar Rigimah Amman Yau Sanadin makauniyar soyy Tazamo Aku kuturu.
Ido ta rufe ta budesu Akan dr dake sharara gudu Cikin Jin haushi tayi kwafa tace zanramane.
Plz my Frnds share ND comments.
08100044786.
*AUREN CHOCHI.*
*Book one.*
*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*
*Page 43&44*
Wow Aljannar Duniya Radiya tafa'da aranta,sakamakon Shigar DA Mota DA dr Obinna yayi Cikin Wani ha'de'd'an gida Mai tsananin kyau infact tunda tazo Garin lagos Har Yau izuwanta Cikin Ibadan Bata taba ganin gidan DA yamata kyau tundaga bakin get irin wannanba, Ranta tace Allah kadai yasan iyakar Tsaruwan Cikin gidan.
Motocine jere reras acikin gidan kamada motocin Daddy motocin Momcy danasu Rahap harma DA Na dr Obinna DA suke fake acikin tangamemen get din Cikin runfar maadana motocin,Wanda akallai motocin sunkai 14 Afake wasu arufe DA tanfol wasu abude.
Dr Obinna kusa DA wata katuwar Jep yatsaida motar nashi Cikin nutsuwa yayi parking, Murfin gaban Motar yabude baice komai DA Radiyaba ganin yafuto yasa itama Dasauri tabude mazaunin ta tafuto,Bayan motar tabude taciro madaidaicin jakar kayanta tarataya akafadarta tare da daukan jakar Hannunta.
Baba Mai gadine DA masu baiwa fulawa ruwa DA Sauran Maaikatan gidan dasuke Zaune Kan fararan kujera Suna Hira suka taso DA Sauri Dan kwasan gaisuwa awajen dr, Cikin ladabi suka ringa gaisheshi,yayinda dr Ke amsa musu Cikin faraa tare da Tambayar su aiki.
Da'alama.
Itama radiyA gaisuwa suka Fara Mika Mata tare da kokarin karban Jakarta RAdiya ta Amsa Cikin sakin fuska,saidai fur tahanasu Jakarta ganinta jakarBabu nauyinda harsai antaimaketa dashi.
Dr Obinna Kai tsaye Yafara takawa izuwa Cikin gidan nasu, DA fari Radiya Ido tabishi dashi Bata bishi ba Dan son ganin iyakar gudun ruwanshi saidai ganin Ko ajikinshi Bai sake in ta kantaba yasa DA Dan Sauri Itama Radiya tabi bayanshi, tana turo baki sbd Ganinta aiko Babu komai zaice Mata muje tunda ita bakuwace agidan, Amman dake shidin Dan rAinin wayone jishi yayiwani tfyrshi,Ido taware tana karewa kyakkyawan gidan kallo inda yaji kyau saikace gidan shugaban kasa,aranta tace shiyasa Suda 'yan uwanshi sukeda girman Kai Ashe sudin attajirai ne.
DA Dan gudu gudu Radiya harta cimmashi, Cikin haki sbd tayi gudu,gefen dr din tabi suka jera zuwa Cikin gidan,DA wutsiyar Ido take kallonshi kozai Mata mgn Amman Ina wayar shima yaciro Yafara amsa call,Jin yace alhmdullh Mun iso lfyne yasa tagane DA dr David yake mgn,Aiko kashe wayar dr din keda wuya saiga Kiran dr David yashigo wayar Radiya, daidai lokacin DA suke Shiga Cikin haraban DA zaikawo su Shiga Babban falon gidan.
Wayar ta Kara akunnanta Cikin ladabi tafara gayda dr David,Shima Cikin Faraa yace"Tnz God kun Isa lfy ai yanzu mutumina yace kun iso Anyway kishiga inkin huta zamu Kira anjima GA auntynki tana Miki sannu DA hanya,Radiya tayi dariya Tana fa'din"Ngd broda Dr Bari Inna hutan zankira ace Ina gayda Aunty big.....Ihun DA Rahap tayine Na murnan ganinsu yasa Radiya takashe wayar Bata shiryaba,Rahap ta chakumo Radiya Cikin farinciki tana Mata oyoyo sanye take DA Dan karamin mini skt Sai Yar best DA ya'dameta Duk Rabin nonuwanta awaje Kanta yasha gashin attachment.
Itakan Radiya sarin gashin Kan rAhap Tuni yadameta shiyasa Cikin dabara tazame ajikin Rahap din tana faraa tare da rungume Momcy dake Miko Mata hannu,shikan dr Obinna Wajen Daddynshi yayi Cikin faraa suka Yi musabaha Daga bisani suka rungume juna.
Tare suka wuce Cikin falon Na Momcy,Masha Allah gida yatsaru fiye DA zaton Mai karatu Duk DA gidan daddy akwai kayan Duniya DA arziki Ko kadan bazaka hadashi DA gidansu Dr Obinna ba Dan Babu Karya yakere Na Daddyn akomai.
Cikin farin ciki Momcy tariko Radiya zuwa Dinning table,abinci tafara Kokarin zuba Mata Radiya tace"Barshi Momcy kar inbaki wahala barin zuba DA kaina tafa'da Cikin ladabi,Aiko Hakan ya Burge Momcy Hakan yasa tace"God bless you my Dota okey.
Hakikanin gaskia,Radiya taga gata,wajen
.'yan gidan su dr Obinna, DA alaman sun Sanda zuwan Radiya sbd tarba sosai suka Mata Kama Daga Na abinci abunsha harma DA shinfidan fuska Wanda hausawa suke cewa tafi shinfidan Tabarma.
Shikanshi Daddy bazakace yaune farkon ganinshi DA Radiyarba Duba DA Yanda take amsa gaisuwar ta Cikin faraa,tare da Tambayar ta mutanan gida DA gAjiyan hanya,RAdiyatace"Lfy Lau since agaishe ku.
Haka Momcy Rahab Abraham Harma DA Shi kanshi Daddy din Sai nan DA nan sukeyi DA Radiyar Kamar wata Yar uwansu.
Sosai Radiyatasamu nutsuwa,sabanin inda take DA adarare ganin zatazo inda Bata sababa.
haka Farin Cikin DA tagani awajen Family Na dr saboda zuwan shi dr din sosai yabAta mamaki Duk DA tasan Dr din Dan gatane Duba DA Yanda 'dan dajinshi da family nashi tagani saidai Yau tsantsar kulawa DA inaka Saka inaka dauka DA akeyi DA dr din yakara tabbtr Mata dr Obinna Na musamman ne awajen iyayenshi harma DA 'yan uwanshi.
Abun mamaki dr Kamar bashine Mai cin 'daciba,sosai yasake acikin family nashi Suna Jin da'din ganin juna,Saima shagwaba DA Sakalci dayake tayiwa Momcy Kan cewan shibazaici Sakwaraba DA miyan ogun Wanda yasha Naman kaxa DA busheshshen kifi yace shifa saidai ahada mishi Chekas custard.
Aiko DA Sauri Momcy Tamike DA Kanta tashiga Kicin Dan aiwatar DA Abunda ran Dr Obinna keso.
Itakan Radiya Yar kallo tazama agidan,Duk saitaji dr din yakara burgeta Yayinda Tsananin begenshi gami DA 'kaunar life style nashi yakara burgeta.
Tfyr momcy bAta jimaba tadawo falon Hannunta rike DA Dan tea cup dake Kan karamin tire Na tangaram Sai karamin Glas DA aka Saka sugA aciki Wanda zaiyi amfani DA Shi son ranshi.
Cikin kulawa tace" my swtheart tashi Kasha kasan Bana son zamanka DA yunwa, Dr yamike Zaune Daga Kwance ajikin Daddynshi Cikin Shagwaba yace tnz my swthrt much love you.
ITAKAN Radiya Yar kallo tazamo afalon Duk DA tagama cin nata abincin tun dazu saidai framam dr Obinna DA iyayenshi yahanata tashi tashiga Daga ciki Kamar yadda tun dazu Rahap kebinta suje tarage kayan jikinta Tai wanka kodata huta Gajiyan hanya.
Wayar Radiyar CE tayi Kara,alaman ana Kira, ahankAli tadaga wayar dake Kan cinyarta saidai ganin sunan Halil Akan wayar yasa tadanja karamin tsaki Cikin dabara tacire ringtone Na wayar izuwa silent, Ko kadan Bata 'kaunar abunda Zai Tabata DA kallon fuskan dr Cikin wannan Hali Na shagwaba Wanda yake tsananin tfy DA imanin Duk wata mace Mai Rai DA lfy.
Radiya Kanta Takuma mayarwa Kan dr dake Shan kunun custard Cikin nutsuwa inda yake Dibanshi DA tea spun Kamar yaro karami,Momcy Sai lallashinshi takeyi Cikin kauna shikoyana Kan Zuba Tabata.
Daddy Kan dariya yakemusu sbd yasaba DA ganin wannan kauna,Cikin tsokana Daddy yace"Kai swthrt Wato yanzu Ahmed yakwace soyyta Ko? Yaushe Rabon kibani abinci abaki?
Momcy tarike baki tana murmushi,tace"Kai Daddyn Yara Rufamin asiri Har yau Har gaban abada bazan bar bakA kulawaba,bt amun Afuwan sbd Obinna bakone I know tsananinta 2 days Zai wuce.
Momcy tajuyo Kai,tace DA "Rahap Kai Radiya daki ta huta,ki kaita Dakin kusa danaki hop angyara Babu datti?Rahap tace"Yes Mommy aitun DA safe dabroda yakira waya yasanar Tuni Blessing ta Gyara,Momcy tace"Yawwa to kuje.
DA alaman agajiye take, taje ta Dan watsa ruwa Inta huta saita sauko tayi Hira anjima,dafatan Radiya kin koshi DA abinci?Radiya datake mikewa tace "Yes Mommy ngd sosai Allah yakara zumanci Momcy tace Amin kuje.
Radiya ta Kalli Daddy Cikin ladabi tace" Daddy barinje Sai anjima,Daddy yace "Tnz Radiya jeki ki huta Nima barin tashi naji anfara Kiran sallar laasar son Sauri kagama muje,Radiya batasan lokacin DA murmushi ya kufce Akan fuskantaba Jin Daddy yace zaije Sallah Hakan ya tabbatar Mata shidin musulmi ne.
Wani sanyine Dadine Yafara sauka ajikinta,yayinda Taji Kamar ansata Cikin ni'imar aljanna Itakan harga Allah Ranta Yana 'kaunar dukkan Wani musulmi sannan Ranta Yana tausayin taga mutum Har mutum Amman Babu addinin Allah.
Rahap ne takarbi jakar kayanta itako radiyA tariko jakar Hannunta,harta juya tafara bin Rahap din tatsaya sakamakon tuno DA Laidan sakon aunty Saada datayi,Hakan yasa Tace"Ayya dr nayi mantuwa amotarka PLC Ko xakabani key indauko tafa'da Cikin langwabe Mai.
Dr yatabe baki Yana Shan kamun shi,Kamar baxaiyi mgn ba Har tacire Rai Zata bi Rahap,Muryan Shi ta tsinta Yana cewa zanshigo Miki dashi anjima Hakan yasa Momcy dake kusadShi. Tasauke ajiyan zuciya sbd kunya DA Yafara kamata Na Shirin DA dr din yayi.
Radiya tace"Tnz somuch,Bayan Rahap tabi Cikin takunta Mai tattare DA nutsuwa.
Bayan sallar isha'i dukansu suka hadu afalo Kan dining table dancin abincin dare,blssn Mai aiki tare day Jon sune sugama Hada dinning table din,Tuwone ruwan shinkafa miyan Kalkashi Wanda yaji Naman Rago DA Ganda, Sai soyyan agada DA Farar taliyan laida DA yaji miyan jajjage.
Dr Obinna Kujeran Shi kusa Dana Daddynshi Hira sukeyi Cikin aminci DA 'kaunar juna,Sai Mommy dake gefensu Sai Abraham Dana Rahap sAi radiyA akusa DA Rahap din sukansu kowa takiyar DA miyan jajjage yasa,dr kadai DA Daddynshi Momcy Tazuba musu tuwo kowa DA fulet nashi.
Cikin nutsuwa dr yasanya fararan hannunshi sol Cikin roban wanke Hannu Bayan yawanke fulet din tuwan yajawo yayi Bismillah afili kafin Yafara yankan tuwan Yana kaiwa bakinshi Ko Rabi baiciba yamatsa DA fulet din gefe,hannunshi ya wanke Daddy yace"Ahmed badai ka koshiva? Dr yace"Alhmdullh daddy Mommy tace"Ahmed mekaci DA kakoshi sbd dakaifa akayi tuwan nan Dan nasan kanaso.
Dr Obinna yaturo karamin bakinshi,Yana cewa"Mommy kinmanta dazu nasha custard yafa'da Yana shafa cikinshi alaman yakoshi,Mommy tace"Shkn swthrt I know Koda Na takura baci zakayiba plx Dan Allah kadinga cin abinci sbd Kai likitane kafini sanin muhinmanci abinci ajikin Dan Adam,Daddy yace"Gaskiane fa'da mishi Dan Naga wannan Yaron nakiBayi kiyaye dokokin nasu DA suke fadakar DA mutane koyaushe,Dr yayi murmushi Bai Kuma cewa komaiba yamike DA Goran ruwa ahannu Cikin sassarfa Yafara hayewa Kan benen DA Zai sadashi DA dakinsa gabaki dayansu suka bishi DA ido Cikin soyy,Itakan Radiya Jitayi taliyan yafuta aranta sbd rashin dr awajen Cikin yatsina fuska Kamar maicin mgni Tacigaba dacin abincin batawani chi dayawaba Tamike Akan Kujeran dinning table din Takoma Kujeran Falo inda Rahap take tafara kallon Tv.
Plz my friends share ND comments.
Taku Har akullum matar Faisal Zakhari.
08100044786.
*AUREN CHOCHI.*
*Book one.*
*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*
*Littafina Na kudine sbd masoyana masu kaunar book dina Na mayar DA complete 1 kyauta bt 2 kadai Zaku biya kudinshi Cikin farashi Mai sauki only 300NaiRa, gamai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me,08100044786.*
*PAge 45&46*
Hira suka cigaba dayi afalon Suna dariya,Rahap tace Momcy Gaskia banji dadiba DA broda baizo mana DA Anitha ba DA hiran tafi armashi, Abraham yace"Ainima banji dadiba DA munsha dariyar tsokanar sis,Momcy tace"Aikunsan swt Son, Dan ganin damane Yau Baiyi niyar zuwada itabane.
kawai Duk muyi hakuri konima ainaso ganin Yar 'diyata agefena bt no problem tunda GA Auta aita Maye gurbin Anitha Daman Auta DA Autane Momcy tafa'da tana kallon Radiya.
Hakan yasa Radiyar tayi murmushi tare day Jin da'din mgnr Momcy, baki tabude zatayi mgn saidai Jin alaman Taku Daga Sama yasa tayi shiru tare da kallon inda Taji takun.
Matattakalar benen yake takowa anutse kunnan Shi Manne DA karamin waya Yana Mgn, ahalin yanzu yacanza Kaya Kanshi cike DA ruwa DA alaman Bai Jima DA futowa awanka ba,sanye yake DA 3kwata navy Blue iyakar shi guiwanshi Sai YAr karamin Riga body hok itama Navi blue wacce ta Dan kama jikinshi,sosai sturactuce nashi yafuto yayinda kake hango gashi Kwance lub ajikin tsintsiyar hannuwa DA kafafunshi, Shigar tafutar DA Duk Shep Na jikinshi,takalmin sosone qkafarshi irin Na turawa Wanda kafarshi takarawa takalmin kyau abun Sai Wanda yagani lolz.
Itakan Radiya kallo daya taimishi Takauda Kai sbd bazata jure kallon Shi Cikin sex dress.
Dr Kan DA alaman yayi Shirin baccine yafuto Dan yin Wani Abu sbd Shigar gaskia yayi madaran masa kyau.
Momcy takalleshi Cikin 'kaunar Shi Mai zafi tace"Son Baka kwantaba ainayi zaton kayi bacci Kai naji dadi daka sauko muyi Hira Dan bangaji DA kallonka ba yhu knw I miss u elot.!
Dr Obinna yacire waya akunne, Bayan yagama ansa call Cikin murmushi yace"Sorry swthrt wlh mantuwa nayi, yafa'da Yana kallon Rahap Cikin Bata Rai yace"Ke jeki Kan table afalona kidau komun makullin motar danazo dashi,DA Sauri Rahap Tamike,Dan xuwa Aiken dr Obinna, shikan Abraham dariya yayi sbd ganin Yanda Rahap tatsure Azatonta masifa zaiyi, sbd suturan banzar da yataras DA ita dashi dazu Dan tun dazu take Gilman wasu Abraham din Kan cewa Dr Yau yaganta DA Shigar DA baiso Baiyi korafiba.
Dr Obinna yadaka mishi harara Cikin Jan tsaki yace " Dariyar me kakeyi? Abraham yatoshe baki Yana danne dariyar sa dr yaja Babban tsaki Yana nuna Abraham DA Wayarshi wato Bakuji Ko? Wlh kushiga hankalin ku Naga rawan kanku Yana yawa to zanyi mgnin Ku,Karki a Bani Garin kuce Zaki lalace wlh Nakusa in babballaku agidan nan,tun wuri kushiga hayyacinku.
Daddy dayanzu yake shigowa Falon yace"Son Yau Babu hirane?Dr Obinna yashafa kanshi Yana dariya,Daddy yace"Babu Kenan tunda kaki mgn anyway Shikenan ai tunda Babu Kai ahiran Nima barin Koma dakina inyi Bacci Daman muryanka danaji yasa Na futo.
Dr Obinna yayi murmushi Yana fa'din"Am sorry dad wlh wasu Dan ayyuka zanyi sbd 5days yarage inyi exams wa dalibaina So dat shine nake Dan Hada abubuwan aiki....Daddy yace "No problem dear son Allah yataimaka yakuma Baka ladan Hidima DA kakeyi damu DA mutane Allah yakawo macen kwarai,Dr yarufe Ido Yana murmushi ahankali yace Aminn,itama mommy dariya tayi tace" aminfa Naga abun naku Yar wariyace.
DAddy Yace gud night my son Tare day fadin madam Ina jiranki,Momcy tace"Okey dear.
Shikan dr Kara rike Kujeran Dinning table yayi DA hannunshi Wanda Daman tun Tuni atsaye yake, Duk DA Tarin kujeru masu tsananin kyau DAke falon waj falon shikan Bai zaunaba tsaye yayi Jikin Kujeran Dinning table.
Ta kasan Ido yake Kallon Radiya DA tun shigowar Shi falon tashiga hayyacinta, sbd Shi,Dariya yayi acikin ranshi Na ganin Yanda take sussunkuyar dakai Kamar Tsohuwar munafuka, baki yatabe Yana Kare mata kallo.
Momcy, tace"haba son,kadan zauna mana kafin tAfuto aizaka gaji,"Dr yayi fari DA ido Cikin shagwaba yace"Momcy kinmanta Ni din jarumine Aina Saba DA tsayuwa, Abraham yace" tafff wayaga Jarumi Bayan asibiti kake ba filin yakiba ai wannan saimu sojojin asali,Dr Obinna Yace"Kai waye ragon? Zan ballakafa yafa'da Cikin Hada Rai sbd Abraham Yana Shirin Bonsashi agaban Radiya, Abraham yace"Am sorry broda Ina nufin fa nine soja mune muka gaji tsayuwa,Momcy datake jinsu tace ayi hkr Kar ballashi inka ballashi dawani kafar zaije gidan soja o.o Rufamin asiri Abraham sojane soon.
ayimusu afuwa zasu farajin mgn very soon,Son aikaima jarumine sbd karatun likita ba aikin ragobane musamman irin Na swthrt ba Duk mazaba Momcy tafa'da Cikin kulawa Aiko dr yadan saki Rai Yana Jin da'din mgnr Momcy.
Shikan Abraham baki yaturo aranshi Yana fAdin tome mukayi Daga dariya Sai masifa,RahAp CE tadawo Daga Aiken dr, key car,tamiko mishi,dr yace"Ubanme kika tsayi adakina Sai yanzu Zaki dawo? Rahap tace "Ayya broda wlh key dinne ban ganiba shinata dubawa sbd kace Yana Kan table saidai banan Na ganshiba Akan Fridge nagani,dr yagya'da kai Yana Mai gAskatata Dan tabbas yayi mantuwane Anan Kan fridge ya ajiye, Hannu yamiki yakarba key din Tare da fa'din tnz.
Ina zuwa yace DA Momcy kafin ya yafuta acikin falon,futar Shi baijimaba yadawo falon hannunshi rike DA katuwar laida Wanda aunty Saada tabaiwa Radiya tsAraban Momcy, DA sallama yashigo falon Radiyace kawai ta Amsa ahankali su Kan Sauran DA ido suka bishi,dr yashigo falon gabaki daya,Laidan hannunshi ajiye Akan Table dake tsakiyar falon Baice komaiba ba yafAra haurawa Sama,Saida yakai matakala 3 kafin ya Dan tsaya,Kamar bakinshi Yana ciwo Yafara mgn batare DA yajuyoba yace" kije ki kwanta Ko kinmanta gobe kinada exams, Mitsw Banda shirme Aida karatu kikayi yamiki kallon Tv.
Dukkansu sunji mgnrshi, baran ma Radiya DA ta tabbatar DA ita yakeyi,sukan Sauran dariya suka fara Daga Momcy Har Rahap dariya sukayi Jin mgnr dr, shikan Ko ajikinshi Yana fa'da yacigaba DA haurawa Sama, harsaida yabace.
Tsit Radiya tayi Kamar wacce ruwa yacinyeta sbd Jin mgnr dr,Aiko Yana shigewa Dakinshi itama Tamike Cikin murmushin furicin dr DA yamata dadi sosai sbd tabbas gaskia yafa'da yadace hakadin,musamman DA ta tazo Ibadan, DA Yar karamar laptop Na aunty Saada acikin kayanta sbd karatu,Hakan yasa tayi Naam DA mgnr dr, Daman zamanta afalon sbd shine Dan tana kaunar kallon fuskan Shi tare da jin mgnrshi Mai da'di shida Momcy,saidai tunda bazai zoba itama zamanta awajen bayida amfani,Radiya DA hannu Akan table tadauko Babban laidan DA dr yaajiye,Agaban Mommy tazo taajiye Cikin ladabi tace Mommy gashi inji auntyna saada.
Momcy tayi dariya, tana fadin Kai mungode sosai Allah yasaka,Radiya tace Amin,sallama tayi DA Momcy Momcy tace"Aynima yanzu xanwuce sbd nafarajin bacci,Hakan yasa itama Rahap Tamike tana fa'din muje sis Momcy gud night,Momcy tace night my Dotas Mukwana lfy, Abraham kadai akabari afalon Yana canza Tasha izuwa tashan kwallo.
Bacci Rabi DA Rabi Radiya tayi sbd Tunanin exams,Duk DA tana DA fahinta sosai Kan karatu Amman exams Na jamp Tsoro yake Bata sbd yanda bakowa Ke samuba,Hakan yasa Taraba dare tana salli tare da rokon Allah DA yabata saan exams.
Sallar asuba akunnanta aka Kira Hakan yasa Tamike DA salati abakinta bandAki tashiga tadauro alwala tana idar DA Sallah tafa'da bandaki wanka,Duk DA Sanyi Sam Bata DA matsala sbd bandakin akwai Ruwan zafi Cikin water heater Hakan yasa tasamu enough Ruwan zafi tayi wankanta.
Batayi Wani makeup ba tunda tasan inda zataje Kamar schl yake tunda jarabawa zatayi,Dogon rigan atanfa ta'dauko Mai ratsin fari DA ja tasaka 'das tafuto gwanin shaawa tayi kyau,Dan kwalin tadaura sannan ta'dauko Yar karamar jacket tasaka Mai baki DA fari sbd yarage Mata sanyi Yar siririyan gyale fari ta'dauko tayafa akanta,Plat Na Takalmi ta'dauko fari tasaka, Bata dauki Ko wayaba Dan tasan ba lallai abarta ta tafi dashiba Sai Yar Karamar laptop nata dake Cikin karamin jakarshi taciro ta rataya awuyanta Cikin Sauri ta Daura agogon hannu baki Aiko Ras tayi kyau Kamar ka saceta kagudu sbd kyau,I d cat nata tadauka tasa ajakan laptop din sbd shaidan tabiya jamp.
Labulen window tadaga taleka Aiko nan taga gari tafara haske DA alaman tadauki lokaci wajen kwalliyan.
Kofar tasa hannu Zata Bude Aiko kwankwan Taji ana bugawa Hakan yasa tabude DA Sauri,Rahap tagani ciki kayan bacci,RAdiyA tace"Gud mrng Aunty Rahap,Rahap tace"Morng Auta hop kinshirya Radiya tace"eeh Rahap tace"Ainaga zahiri tomuje Daman Momcy tace intasoki kiyi breakfast kafin ki wuce Radiya tace" Tnz,Rahap tace" gaskia kinyi kyau sosai,Radiya tayi murmushi Rahap tace"muje.
Momcy DA Rahap kadai suka tashi Sauran Kan Suna bacci,itama Rahap Koda tarako Radiya fatan alkairi tai Mata Na exams Takoma Dakinta Dan time Na tashinsu baiyiba,Radiya ta durkusa Har kasa tagaida Momcy,Momcy ta Amsa Cikin sakin fuska tana Jan Radiyar jikinta.
Momcy DA Kanta ta hadawa Radiya break fast,ta turo Mata gabanta tace Maza chi kafin Direba yafuto DA Mota sbd nasanar dashi inda zaikaiki Tunjiya,Radiya tace",ngd sosai Momcy Momcy tace habawa aiwannan yiwa Kaine Maza CI abincin Ina zuwa.
Radiya tajanye fulet Na Soyayyan Kwai DA chips agabanta, Ahankali tasa chikali Mai yatsu tafara chi,yayinda take kurban Ruwan shayi Wanda yaji Madara DA Milo aciki.
Takun DA Taji shiyasa ta'dan dAga Kai Azatonta momcyne tafuto,saidai sabanin Hakan dr tagani Yana saukowa Daga Saman sanye yake DA hap Jamfa Na yadin kaftan Yello Sai yellow jacket dake Kan kayar yana tafe Yana taje gashin Kanshi Wanda yake Lup Lup Kamar Na larabawa.
Radiya batasan lokacin DA murmushi ya kufce Akan fuskantaba,Cikin Faraa tace"Yaya Ahmed Ina kwana,Yar tsikan jikinsu Duka yatashi GA Dr Yanda takira sunan nashine yashiga jikinshi,Itakan Radiya Shigar tashine yamata kyau haryafara Jin Kamar Ana mutstsinin jikinta,Muryan Dr ta tsinta ahankali Yana fa'din lfy.
Tare da fa'din " hop kingama?RAdiya tace"Eh Momcy ne tashigo falon,ganin dr Cikin Shirin futa tace"Son katashi?dr yace"Yes Mommy gud mrng "Momcy tace mrng dear dafatan komai lfy?yes Mommy dr yafa'da Yana ajiye kum daya taje Kai Akan table dake tsakiyan falon.
Mujeko yace DA Radiya DA Kanta Ke sunkuye tana Wasa DA Yan yatsunta,Momcy tayi murmushi tace"Son aihar nayi mgn DA Direban Rahap banyi zaton dakai zamujeba,Dr Obinna Yace"No problem yahuta Ke muje karkiyi Latti,Momcy tace haba son bari mana tagama cin abinta, Dr yaja tsaki Yana fa'din remain 27 minutes Suga exams,Momcy tace " Swt kingama cin abincin Radiya tace "nagama mommy Okey muje inrakaki Mota Momcy tafa'da tana riko hannunta.
Har Mota tarakasu tana musu fatan alkairi,Direban Rahap kuwa Tuni Momcy tace yaje yahuta Obinna zaikaita.
Saida
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12