Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Daman Kaine David yafa'da Yana Danna mishi harara Cikin Tsokana yace Futo ka karyamin 'kanwa Kuma Allah inhar kafar nan Bai gyaruba 'karshen gauron taka yazo ehee yafa'da Cikin tsokana,dr Yayi fari DA ido Ahankali yace David helf mie my shoulder. Ohhh God David yafa'da Cikin sauri yabude motar yariko Dr Alokacin 'yan Sanda suka 'karaso jikin motar Ganin Dr Shima Yana bukatar taimako yasa Cikin sauri suka Taya David rikeshi musamman DA suka Gano wanene dr Obinna Hakan yasa Cikin rawan jiki suka Jefashi amotar su Dasauri David Yace kuje dashi asibitin Shi zamu karaso DA motar Shi,Saada DA Suwaiba yace sumaida Radiya Cikin motar Shi sutuka subiyo bayansu shibari yaja motar dr Obinna zuwa asibitin. *AUREN CHOCHI.* *Book one.* By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari. Freepage. *Page 15&16.* Ranga Ranga Aka shigo DA Radiya ND dr Obinna Cikin asibitin nashi,Ihu Radiya keyi lokacin DA nurse suka rikota Dan daurata Akan gado,Shikan dr Sosai yakejin azaba acikin 'kirjin Shi Wanda Duk dauriyar Shi yaukan yakasa matsewa Dole yake rintse ido Yana salati acikin xuciyar Shi, Cikin tashin hankalin ganin uban gidansu Cikin ciwo nurse tare da doctors Na asibitin suka Dauki dr zuwa emergency Itama Radiya emergency din aka wuce da ita. Taimakon gaggawa Likita suka Fara Bada Dr wasuko Suna Duba Radiya,Shikan dr Duk Da yanajin azaba Ihun Radiya dake Shirin fasa dodon kunnan Shi,Ko kadan bayi 'kaunar hayaniya Hakan yasa yakejin kansa Yana matukar Sara mishi tare da jin haushin Yarinyar ma shegen Zakin murya wajen ihu, yafi 'bata, Dr Cikin Dauriya yace "DA dr Mu'azu Dan Allah kusa yarinyar nan tayi shiru. AM SORRY dr kasan yarinyace gashi Muna zaton tasamu karaya, Dr Mu 'azu yafa'da Cikin Lallashi,Dr Sani yariko kafar Radiya Yana kallo, Dan San tabbatar DA abunda yake zargi Aiko tuni yagano matsalan Cikin harshen turanci azaton Shi Radiyar bataji yace Yarinyar nan tasamu mummunar tsagewan 'kashi Dan haka Muna bukatar Dr Iliya yanzu,Dr Mu'azu yace Yana hanya nayi masa waya tun dazu sbd dr Shima Yana bukatar taimakon dr Iliya, Rufe bakin dr keda wuya,Radiya ta kurma ihu Mai karfi tana fa'din wayyo Ammina Wayyo zan mutu Sun fasamin 'kashi, yaci remin 'kafa,Dr David yarikota Cikin tausayi yace"Yi hkr sister yanxu zaagyara Miki kafar taki, Dr iliyane yashigo Cikin emergency DA sauri,Batare da Bata lokaciba yayi Kan Dr Cikin damuwa Yana me Shi sannu kirjin yataba zai Fara dubashi Amman Sai dr Obi ya'daga mishi hannu,tare nuni side Na Radiya Cikin sanyin murya yace Fara Duba wancen Mai Ihun,Dr yace "Okey 'kafar Radiyan yakalla daya kunbura suntum Cikin turanci yace DA Nurse Da dr David kuri keta,Radiya ta zare ido tana Kuka Tareda fadin o.o....kafin ta Ankara caraf Nurse DA dr David suka rike Radiya,Riko suka Mata sosai Shiko dr Iliya Dasauri yarike kafar nata yafara gyara Mata, habawa ihu cizo harma DA yakushi yaukan sunsha Shi ahannun Radiya Hawaye kuwa Harda majina. Suwaiba ne DA Saada suka shigo emargency Dagudu Jin ihun Radiya Kamar zaa kaaheta, dr Mu'azu yace "plz kufuta Muna kan aiki,Cikin tausayin 'yar uwansu suka juya waje Badan sun soba saidan dokace baashiga matukar ana aiki,saidai Saada kadai tafuta Itakan Suwaiba ciki tashiga sosai tare da Tabbatar musu itama dr tace, daidai Kan Radiya ta tsaya tana Mata sannu yayinda hannun ta Ke Kan gashin Radiya tana shafawa tana rarrashi Sosai yakejin 'kaunar Auta gamida tausayin ta,tamkar tacire ciwon tadawo dashi jikinta. Radiya Kan Cikin tana Ihun Har Tayi shiru Sai ajiyan zuciya Na azaba,Kan agama gyaran tuni zazzabi yarufeta, Cikin tausayi Dr Iliya yace Kuyi Mata Alluran zazzabi jikin nata Yadauki akwai zazzabi Suwaiba ta rungumeta ajikinta Cikin hawaye tana Rarrashi Radiya Kan Baki yamutu gashi Babu karfi ajikinta tuni yakare Babu abunda takeyi Sai ajiyan zuciya gawani Bala in ciwo DA kafar yake mata. Dr Iliya Bayan yagama DA ita kirjin dr Obi yagyara,Shikan dr Obi ido ya rintse Har akagama Bai budeba, Sai zufan azaba yakeyi,dr Muazu yace "abun mamaki dukkansu entanal injury suka samu, Allah yakiyaye Na Gaba alhmdullh Mun auna arziki dr david yace sbd Babu Wanda yasamu Babban rauni,Dr Obinna Yana jinsu baice komaiba Duk haushinsu yakeji sbd Sunda meshi DA Surutu Daga 'karshe cewa yayi" David Bani key Na motane Dr David yakalleshi Okey Dr gashi yafa'da Yana Mika mishi key 'din,dr Obinna yayi yunkuri ahankali zai Mike saidai Dasauri dr David yace"Abokina Yaya DA haka Ina zakaje? Ko kallon Shi baiyiba yakuma yunkuri Akaro Na biyu Allah yabashi Iko yamike Gabaki Dayan su DA ido suka bishi. Wow Suwaiba tafa'da aranta,Sakamakon hango gashin dake lulllube DA kirjin dr Tacikin farar singlet sbd ancire riganshi lokacin DA zaaja kirjin, sosai kyau DA kwarjinin dr yatafi DA imanin ta,Ahankali dr Obinna yafara takawa Yana nishin azaba suko binshi DA kallo kawai sukeyi tunda sunyi mgn sunyi yaki ansawa, Ganin zaifuce adakin yasa Suwaiba Cikin Rigimah tace Mr man baka baiwa 'kanwata hakuriba Kana Shirin tfy. Basuyi zaton zai tankaba saidai GA mamakin su Gani sukayi dr yajuyo xuwa Gadon DA Radiya Ke Kwance, Kallon kallo sukayi shida Radiya,Shi aranshi Yana JINJINA yanda yakarya 'diyar mutane Babu zato Gata yarinya 'karama itako Radiya Kallon Takaici take mishi yasa andanneta anmata Jan 'karfi Domin DA Bai bugeta DA motaba Hakan baxai faruba. Am sorry Dr yafa'da Yana cizan labba, Radiya Takauda Kai Cikin hawaye tace"Issoryt Murmushi yayi tare da fadin thanks once again ND Allahummah yashfiki, DA sauri Radiya tajuyo Cikin Mamakin Jin mgnrshi dr Yana lura DA ita murmushin yakuma Yi Cikin nutsuwa yajuya yafuce adakin Dasauri dr Muazu DA wasu nurse sukabi bayanshi, itako Suwaiba mutuwan tsaye tayi Jin Yau dr shine Mai mgn fiye DA 'daya lallai Auta 'yar baiwace sbd bayau shine saninta DA dr Obinna ba tasan Shi tun tuni Kuma sosai tunfarkon saninta dashi yake bala'in burgeta saidai Kwarjinin dr yahanata tunkarar Shi Domin bataga fuskan wasaba. Saidai yaufa ganin Dr David Ashe yasanshi yasa ta kudura aniyar Kota wajen dr David Zata Shigar DA Kanta wajen dr,Niko nace lallai Suwayba kin taro March. Itakan Radiya mgnr dr shine yatsaya Mata Arai Sosai Muryan Shi Mai da'di gami DA nutsuwar mutumin yaburgeta ahalin yanxu jitake sakayau Duk wani haushin Shi yafuce aranta,musamman datagano Yana DA addini Abun yabata citta Original Surprise,anty Saada itace tashigo Idonta Duk ya kunbura alaman taci Kuka saidai ganin murmushi Kan fuskan Radiya yasa takarasa Gadon DA sauri tana Tambayar ta jiki Radiya tace"Alhmdullh aunty big, Cikin Dauriya Dan Ta kwantar Mata da hankali tace share hawayenki Zan warke insha Allah,Dr David Yariko hannun Saada Yana share hawayenta tare da fa'din SORRY darling Auta Zata warke very soon. Shikan dr Obinna futar Shi adakin emargency motar Shi dake fake yanufa, DA gudu 'yan sandan DA suka kawosu asibitin tare da security Na asibitin Sukabi tawo wajen Shi Cikin girmamawa Suna mishi sannu Dr Hannu kawai yake 'daga musu, Key Na Mota yamikawa 'daya Daga Cikin security din asibitin nashi Dasauri yakarba Bayan motar yabude mishi adaddafe yashiga Shiko security din yashige wajen direbin. Babban Cikin 'yan sandane yaleko DA kanshi wajen dr Cikin girmamawa yace "Dr shkn Babu Sauran matsala zamu ita tfy?dr ya gya'da Kai tare da Cewa kusamu Dr Muazu zaibaku Sako,godiya 'dan sandan yayi security yaja motar sukabar asibitin. Har Cikin gida Security yakai dr, shida Masu Gadi sune suka taimakawa dr zuwa Shiga Cikin gida sbd bazai iyaba kirjin tayi nauyi,Anitha dake Zaune Falo sunacin abinci Tamike DA gudu Ganin Dr rike ahannu Cikin Kuka tace uncle lfy?? Security dinne yace "DA Anitha baida lfy Anitha DA Hellin suka fashe DA Kuka,Dr Ya dannawa Anitha harara Tare da musu gargadi DA ido suyi shiru,Saidai yaukan Duk tsoron dr da takeji baisa tayi shiruba sbd ganin yanda aka kawoshi arike,Har Dakin masu Gadi sukayiwa Dr Rakiya Itakan Hellin Dakinta tawuce Cikin Tsoro tadauki wayarta ta Danna Kiran Momcy Cikin Kuka tasanar DA ita Abunda yake faruwa,Habawa Cikin ihu Momcy tace "Chineke God My Obinna Don't die Am cmin nw nw. Plx my Frnds share ND comments. Littafina Na ku'dine banyarda Wani Ko wata su karanta batare DA sun Biyani hakkina ba,gamai bukatar Shiga group Na *Auren CHOCHI* Just call me,08100044786. *AUREN CHOCHI.* *Book one* By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari. Freepage. *Page 17&18.* 3days DA faruwan hatsarin Kenan,Gidan dr Obinna cike yake DA 'yan uwanshi harma DA Momcy Dad kadai Bai dawo nanba saidai Shima tun faruwan abun kullum Yana hanyar Lagos,dr Obinna 'dan gatan kowa Kenan Sosai Iyayen Shi Da Duk wani family nashi Ke 'kaunAr Shi,Girki kuwa Daga asauke wannan saidai a'daura wannan masu Rai DA lfy Haka kayan dubiya DA ku'di Har Momcy tagaji DA amsa Domin dr Mai jamaane haka Iyayen nashi, Shikan dr gareshi San bayada nutsuwa sbd yasan akwai Tarin marasa lfy asibiti DA suke bukatar taimakon Shi Awani 'ban gare kuwa Yana son sake zuwa Duba maras lfyr DA shine sanadin kwanciyar ta wato Radiya. Zaune suke shida Momcy abedroom nashi Momcy tana Bashi Dambun Naman kaza abaki Shiko Cikin shagwaba yake karba, Anitha itace tashigo Dakin Rataye DA jaka alaman Daga schl tadawo Momcy tace"Anitha wlcm bck,Tnz Momcy Anitha tace sannan tace "Uncle OBi yajikin? dr Yadubeta Yana kallon Shigar jikinta Cikin tabe baki yace "Ban hanaki wannan bad dress din ba??Anitha ta turo baki Tare da 'buya abayan Momcy Dr yayi kwafa tare da fa'din futar min adaki Shasha kawai. DA gudu Anitha tafuta tana Jin haushi, Momcy tayi murmushi Cikin kaunar 'dan nata tare da jinjinawa Tsare gidanshi tace", Swthrt Menene aibin shigarta Wato Kana mantawa DA kaida ita addininku ba 'dayaba ryt?Dr Yaci Gaba DA cin Dambun Naman Shi Da hannun Shi Kamar baijitaba sanin bazaice komaiba yasa Momcy Tace shkn tunda Mommyn kashare barin bar Maka Dakin tafa'da tana Shirin mikewa Dr yayi saurin riko hannunta Cikin marairaice fuska yace"Momcy Allah baki hkr niban korekiba Amman Dai mommy Kinsan Ko Cikin addinin nata haram CE bad dress haba mommy dubeta saikace Sisi Lagos,Hahaha Momcy tayi dariya Tana fadin swthrt Barin Rarrashi bbyna tunda kasata Kuka,dr yace Yauwa mommy inason leka asibiti please yafa'da Kamar zaiyi Kuka. Wannan bashine Karon farko da dr Ke mgnr zuwa asibitiba shiyasa Momcy tace"Swthrt Agogo Sarkin aiki shkn Na amince zakaje Amman Nizam kaika inkuma dawo dakai,Dr yayi murmushi Cikin Jin dadi yace Na amince mommy tnz somuch. Barin jiraka Afalon Momcy tafa'da tare da fita abedroom din, Simple dress Dr yayi Cikin Hap Jamfa Black shadda Wanda farin fatar Shi tasaka kayan sosai yamishi kyau Keys Na motocin Shi yajawo acikin drowa ahankali yafara dubawa key Na Bakin Mota yadauka Cikin Jin da'din zaifuta yafuto falon 'kasa Anan yasamu Momcy DA Rahap Anitha Cikin shiri Dr yace "Momcy basai da wa innan Iyayen rawan Kan zamujeba? Momcy tace"Sorry swthrt Anitha zatayi driving Rahap Zata Tayani Zama abaya,Dr yace muje mommy Tare suka futa afalon Dr Cikin nutsuwa yake takawa sbd kirjin Bai warkeba karfin Hali kawai yakeyi Dan yafuta saidai alhmdullh Akwai sauki sosai. Bakaramin farin ciki doctors Na asibiti sukayiba ganin Dr yazoba,Shima dr Cikin faraa yake amsa gaisuwan su,Maimaikon dr yazauna Ina daki daki yadinga bi Yana Duba patients nashi Momcy DA 'kannan Shi suna biye dashi Cikin izza DA gadara Momcy uwar Mai asibiti sukuma Kannan Mai asibitin,dagani Babu tambaya itadin jinin dr ne Domin irin farinta shine farin dr Amman hanci Kan DA tsawo dr yadarata Babu Hadi,Duk da dukansu ba bakin fuska bane Cikin asibitin kasan cewan Suna zuwa bugu da Kari akwai Babban family picx nasu acikin office Na dr saidai kowa girmamasu yakeyi cike DA taka tsantsan Dan mazauna asibitin sun shaida sudin 'yan wulakancine masu gadAra DA naira. Emargency dr yashiga gazaton Shi Zai samu Radiya Kwance acan duk DA yaduba dakunan DA yake zaton tanacan Bai gantaba saidai nanma wayam Babu ita Babu alamunta,Sauran doctors DA nurse dasuke Cikin emergency Sai sannu DA jiki sukewa Dr tare da gaishe DA Momcy dake biye DA dr Duk inda yasa kafa Suna tare. Dr yace"Sani Ina patients Dina??Dr Sani yayi dariya Tare day fadin "kace Sarkin raki Mai kukan shagwaba,dr yaja tsaki Cikin kosawa DA mgnr yace Answer mie?Dr Sani yace"ai tun ranar Basu kwana asibitin nan ba Dr David yawuce DA ita General hospital,Dr Obinna Baice komaiba yace mommy muje tare suka futa adakin,Sallama yayi da maaikatan asibitin yashige Mota Momcy ma tashiga Anitha ta TADA Mota sukabar asibitin,Fara tfyrsu keda wuya dr yaciro wayarsa Cikin aljihu no David ya Danna Cikin second biyu David ya amsa Gaisuwa sukayi tare da Tambayar dr Yaya jiki,Dr yace "Wato shine dakazo gaisheni baka sanar Dani abunda kayiba Ko? To Gani ahanya zuwa asibitin naku, David yayi dariya Yana fadin "Afuwan Abokina Wlh autace tadage DA rikichi saidai mudawo gida, bt Kai hkr Aijikin nata dasauki ganima gidan nasu. Dr yace"Issoryt Turomin address Gani zuwa, wayar yakashe Cikin Shan Mur yace DA Anitha" Ke nemi gefen hanya kiyi parking, Anitha Cikin sauri tasaka trapic ahankali tanemi gefen hanya tayi parking,Momcy tace"Swthrt badai tukin zakayiba. Am sorry Mah dr yafa'da tare da fita amotar,Anitha ganin Hakan yasa tafuto Daga wajen driving dr Cikin nutsuwa yashige motar, test Na dr David ne yashigo wayar dr Obinna yabude ahankali yaharba hancin motar Kan titi address din yabi yanda dr David ya tiro mishi saigashi adaidai get din gidan Uncle Na Su Saada Dr yayi hon. DA sauri Mai gadin yabude mishi kyakkyawar gidan Wanda dagani Mai gidan yatara arziki, Momcy tace wow beautiful house Swthrt Gidan yamun kyau,dr yayi murmushi Yana fa'din Barin Kira David plx wayar Shi yadanna yakira Dr David Aiko saiga dr David DA Saada sunfuto Daga Cikin gidan Dan taryo dr Cikin faraa Momcy ta Amsa gaisuwar dr David tare day rungume Saada tana Jin da'din sbd ta hango kyau DA wayewa Jikin Saada azaton ta Wajenta dr yazo. Dr David Yariko hannun Dr Obinna Yana dariya, dr Obinna ya harareshi Tare day fadin "DA izinin wa kabaiwa patients Nawa sallama?Dr David yace "DA izinin Abokina dariya sukayi kafin Saada tayi musu jagora Har zuwa Babban falon gidan Wanda kafin akai gashi Saida suka wuce ha'da'd'dun Falo biyu kafin suka Kai Babban Wanda yasha kayan alatu DA kayan Duniya masu daukan hankali. Kamar amafarki Radiya taga Shigowan David DA Dr Obinna yayinda ha'da'd'diyar mace Mai ji da Aji Ke bin bayansu, Radiya tayi saurin Gyara kwanciyar ta Akan 3seta kafarta daure DA bendej Cikin Jin kunyar dress Na jikinta Wanda batai xaton Wani bakon fuska Zai shigoba, Saada tace mommy Ku zauna Kira ta kwalawa Mai aiki tare day fadin tawowa baki abinci DA ruwa,Bayan sun zauna Saada Takuma gaida mommy Itakan mommy Farin ciki takeji Na ganin Harkan arziki Domin ita macece maison abun Duniya. Tunda yashigo falon ya hangota Kwance Cikin kananun dress Mai kyau Na Shan iska kasan cewa ana zafi Kanta Babu Dan kwali anmata kananun kalba hanki tadaura akan Wanda Bai rufe gashin ba, Tayi kyau Kamar flower saidai DA alamun su Momcy Basu gantaba kasan cewar Kujeran DA take Yana lungu, Dr Obinna yayi gyaran murya tare da kallon side na Radiya Cikin sakin fuska yace "Sarkin Kuka Yaya jiki. *AUREN CHOCHI.* *Book one.* *By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.* *Littafina Na kudine banyarda Wani Ko wata sukaranta batare da tabiyani hakkinaba bance Allah ya'isa gaduk Wanda tayi Hakan ba saidai danso kuyimun adalci sbd hakkina nake nema ma'ana kasuwanci name,gamai bukatar mallakar nata just call me 08100044786 thanks all my Frnds.* *Page 19&20* Momcy Tasauke Idonta 'bangaren DA Dr yake mgn,Aiko charaf Idonta yahango Mata kyakkyawan Yarinyar Kwance Kan kujera kafarta nanna'de DA bendeji, afili Momcy tace"Ohh my God swthrt Meke damunta?? Dr yace "Momcy itace dat grl Dana buge DA Mota,Ayya sorry Momcy tafa'da Cikin sigan tausayi,Tare da mikewa tazo Kusa DA Radiya dake Kwance Radiya Cikin kunyar Momcy Wanda batasan daliliba ta Fara gaida Momcy Momcy ta Amsa tare da Tambayar ta Yaya jiki,Ahankali Radiya tace"dasauki,Rahap DA Anitha Suma Cikin tausayin suka gaishe DA Radiya, MOMMY CE tashigo falon Cikin shigarta Mai kyau Na kece raini wato matar uncle din su Saada Cikin faraa tace"Sannunku DA zuwa Momcy tawashe baki tanajin da'din girmamasu DA akeyi Cikin wannan gida, mommy tazauna Kan Kujeran kusa DA Saada itako Saada Kwanciya tayi ajikin mommy tana Mata shagwaba Aiko tuni mommy tabiye Mata Hakan yasa abun yabawa su Anitha Har ma DA Momcy shaawa Domin wannan ya tabbtr musu Basu kadai keda gataba haka shagwaban ma. Saada tace "mommy C dr Obinna Shine Wanda yabuge Auta wannan family nashine sunzo gaida auta DA jiki,Mommy tayi murmushi tare day fadin "Kai mungode sosai Ai tsautsayine Baya wuce ranar shi,Dr Obinna DA tunda suka Fara mgn baice komaiba Yana amsa call saiyanxu yayi mgn"mommy yagaisar tare da Bata hakuri Kan buge Auta dayayi DA Mota danshi harga Allah yadauka Mommy itace maaifiyar autan musamman daya Ganta Cikin dress dake nuna imafa ahalil kitab CE wato original kafura lolx. Mommy tace"Bakomai yawuce ai Gashi kunzo Daddyn nasu bayi Kasar saidai bakomai insha Allah zani isar DA sakonku, mommy tace Saada my Dota Kamar nasan fuskan nan tashi,Saada tace "Mommy ai dr Obinna ba biyeyye bane Hakan yasa Dole kiganeshi Aiko tuni mommy taganeshi Jin anfadi sunanshi Hakan yasa mommy tace haba no wonder Ashe shine shararren likitan nan da kusan kullum akesaka Programs nashi Cikin tashan African magic epic, Saada tace kwarai kuwa mommy. Mommy tayi dariyan Jin da'din Gano waye 'danta DA akayi lokaci guda,Hakan yasa tashafa Kan Radiya Cikin murmushi tace Allah yabaki lfy Hop Zaki yafewa swthrt I knw rashin sanine Kinga Shima yasamu rauni sosai,Itakan Radiya Kai Tasauke tana murmushi batare datace komaiba Har Cikin Ranta Taji da'din zuwan dr, sbd zuwan yanuna cewan shidin mutum arzikine Wanda yasan Hakkin Dan Adam, Horace ta kaure atsakanin su Anan Har mommy Ke gaiyatar Momcy auren Saada Nanda 3weks habawa Nan Rahap DA take kusan saan Saada tace Aiko zasuxo itama Momcy tace "Zasuxo Anitha hartana mgnr abasu anko,Shinkan dr Kallon Radiya yakeyi asace Yana nazarin Wani Abu game DA ita,Jin Muryan Dr David yayi Yana fa'din" Abokina muje Ko dr yakallesu Duka Ashe sunmike Dan tfy Harda momcy,Momcy tabude Jakarta ya'divo Kudi masu yawa tasaka acinyan Radiya tare day fadin Bby girl Kisha lemu Babu yawa,Radiya Tace"Don Allah kibarshi mamah wlh nagode Momcy tace"Ah ah Bazan barshiba saidai inkin rainane tafa'da tana Shirin Debo wasu takara. Radiya tayi saurin cewa"Ah ah mamah ban rainaba wannan ma sun Isa ngd Sosai,Dr Yayi murmushi ahankali yataka yazo gabanta Shima makudan Kudi yaajiye Wanda yafi Na Mommyn Cikin sanyin murya yace"Sarkin Kuka GA kudin kaza,Radiya tayi narai narai DA ido zatayi Kuka sbd DA ganin makudan kudi Wai Duka nata, Saada tace" mungode Lura datayi Radiya tana Shirin Kuka yasa tace Auta Jikinne? Radiya ta turo baki Cikin kunkuni tace " aunty big kifada mishi ba sunana Sarkin kukaba sunana Radiya, Dariya sukayi dukkansu sbd Jin mgnr Radiya shikan dr kafa'da ya'daga Cikin murmushi yace " olryt Nxt tym Redi Bye,tare dafuta Afalon Suma Momcy Bayan Shi sukabi Dan tfy gida. Saada DA mommy sune suka Kuma dawowa falon Bayan sun raka su dr DA Momcy, Cikin kulawa Saada tace" Auta Haryanzu kukan shagwaban akeyine ? Am sorry bbynmu Yi shiru Kinji,Radiya tace"Aunty Big Kijifa sunan daya kirani dashi Wani Redi saikace 'yar Baby Mommy tayi dariya itada Saada Jin mgnr Radiya Hakan yasa Radiya Sarkin shagwaba tafashe DA kuka, Subhanalla Suwaiba dake shigowa Falon tafa'da Cikin sauri Takaraso Jikin Radiya Auta lfy? Saada ta Dube Suwaiba DA yanxu dawowarta Daga aiki tace"Shagwabar Autane yamotsa Wai sbd dr Obinna yazo gaisheta yace....Radiya tace" wayyo aunty big Dan Allah karki fada plx tafa'da Cikin begging. Suwaiba tace"Wow nayi missn wlh,kardai motarsu naci Karo yanxu Ina Shirin shigowa anguwar nan Daga aiki,Saada tace indai Kinga ta Darlin to tare suka futa,Suwaiba tace tabbas shine Domin Naga Motar Brother David. I LYK HIM Suwaiba tafa'da Cikin shauki, Saada DA Radiya suka kalleta lokaci guda Suwaiba tayi murmushi Cikin tabbatar wa ta gyada Kai tare da fa'din "yes My sisters Allah nayi matukar kamuwa DA soyyr dr Obinna Wanda nakejin Zan iya komai Dan insameshi,Ras Ras gaban Radiya yafa'di Batasan lokacin DA tace"Aunty Daman saurayin kine? Kafin Suwaiba tayi mgn Mommy Takuma shigowa Falon Kujera tanema tazauna Tana fadin "Dotas kuxo Kuga kayan DA Daddynku yaturo Saiku Taya auntynku zaban kayan daki Dan muyake jira azaba yayi Oder. Mgnr zaban kayan daki shine ya shashantar DA mgnr Dr Obinna,saidai Itakan Radiya akasan Ranta haka kawai takejin Babu da'di Wanda batasan daliliba. Plz my fans share ND comments plx . Taku Har akullum matar Faisal. *AUREN CHOCHI.* *Book one.* By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari. *Littafina Na kudine banyarda Wani Ko wata sukaranta batare da kunbiyani hakkina ba Babu Allah ya'isa gaduk Wanda tayi Hakan saidai zanso nima kimin adalci, Mai bukatar complete just call me 08100044786.* *Page 21&22.* Barrister cikekken barrister ne Mai Zaman Kanshi sannan Mai arzikine Zan iyacewa Cikin masu arzikin Kano Yana 'daya Daga ciki Saka makon Gadon arzikin dayayi Daga maaifiyar Shi wacce ta kasance 'yar kasuwa Mai arziki, Ra'is Haifeffen 'dan KaNo uba,DA UBA. Bayan rasuwar maaifiyar Shi Anan yagaji arziki kasan cewan shikadaine 'danta Bayan rasuwarta Bada jimawaba maaifinshi yabita wato Shima Rai yayi halinshi Hakan yasa Gadon maaifiyar Shi Dana maaifinshi Duka yazamo nashi, Barrister Yayanke shawaran yin karatu Mai yawa tunda akwai kudinyin Cikin yardan Allah yasamu futa Kasar Chaina yayi karatu Bayan yashafe wasu shekaru masu yawa Yana karatu yayi nasaran gamawa DA nasara Mai yawa Hakan yasa Kasar Chaina tarikeshi sbd yamata aiki,ganin baida uwa DA UBA dazai dawo dominsu Hakan yasa ya amince. Barrister yazauna tsawon 7yr Yana aiki DA Kasar Chaina Anan yayi gamon Katar DA matar aure Wanda takasance itama Yar Nigeria Yar jahar Bayelsa saidai itadin Cristian ce,batare DA Bata lokaciba ganin ba haramun bane amusulunci yasa barrister Ra'is ya auri Uju,Dangin maaifinsa Dana maaifiyar Shi Ko kadan Basu soba saidai ganin shidin marayane yasa Basu tauye mishi hakkiba Hakan yasa sukayi ruwa sukayi tsaki Har auren Barrister DA Uju ya tabbata. Bayan anyi auren Anan Nigeria Cikin Jahar Bayelsa DA kano,Bada jimawaba barrister Yadauki matarshi suka koma Chaina. Aurensu uju DA barrister Ra'is,DA shekara 'daya chip Uju ta aifo danta namiji fari TAS Kamar yadda take Fara tas irin farin IGBO wato inyamurai, jariri tubar kallah Dakagan Shi kaga ruwa biyu Igbo DA Hausa fulani wato Yaren Uwa DA ubanshi. saidai hanci Kan DA tsawo Na maaifin shine, DAn Uju guntuwace saidai itama akwai kyau Babu laifi, Akan sunan yaro ansha artabu DA Uju inda tadage sunan kiristan zaasa Amman Ra'is yaki Daga bisani Ra'is yaradawa 'danshi Suna amasallaci Ahmed itakuma Uju ranar Suna tara'dawa 'danta Suna Obinna. Ahmed Ra'is Obinna shine sunan DA yake rubuce Jikin takardun aihuwan Shi,Uju DA 'yan uwanta sukan kirashi DA Obinna Daddyn Shi Da 'yan uwanshi sukan kirashi DA Ahmed,Bayan Aihuwar Ahmed Saida yayi 6yrs aduniya kafin Uju takuma aifo Ibrahim Wanda Shima take kiranshi DA Abraham,Bayan Abraham taaifo Rahap Sai Auta Anitha,Uju tayi kokari sosai wajen ganin yayanta sundauko addininta yayinda Ra'is Ke kokarin yayanshi su kasance musulmai. Akwan atashi Har yaransu suka Girma, Obinna Shikadai yakasance musulmi yayinda Duk 'yan uwanshi suka kasance kiristan,Lokacin DA Obinna yafara karatun jamiane Alokacin Daddynshi yayi ritaya yabar aiki DA Kasar Chaina inda ya tattara yanashi inashi yadawo Nigeria DA Zama saidai Maimaikon yakoma Kano Ina Ibadan yayada zango sbd Harkan kasuwanci daya fara. Barrister Ra'is Wanda yazamo dattijo ayanxu Kuma Daddyn Obinna, shida iyalinshi Dukkansu suka dawo ibadan, Obinna kadai akabari achaina sbd karatun likita dayafara. Ahmed RA'Iz Obinna,shine cikekken sunan DA yake amfani dashi Ko aschl,saidai tuni abokai DA lecturer sun dauki sunan 'karshen DA ita suke mishi inkiya wato Obinna Cikin yanaki harya Fara Amsa sunan tunda yasan bazasu dainaba. Cikin Ikon Allah dr ObinnaHar yagama karatun Shi tuni yasamu shaidar Zama cikekken ghanicologys Dr. Dr Obinna matashine kyakkyawa,son kowa kin Wanda yarasa, Mai tausayin na 'kasa dashi bugu Da Kari Allah ya 'daura masa kaunar addinin shi ta musulumci, Hakan yasa yake matukar kiyaye dokan Allah aduk inda yake, Haka family nashi Na uwa DA UBA ba karamin 'kaunar dr sukeba sbd always Yana Cikin musu alkairi, Momcy ND Dad DA Kannan Shi uku Wani madaran 'kauna sukewa Dr 'kauna bilhakki DA gaske,Shima dr Sosai yake fama DA 'kaunar family nashi infact Jiyake Zai iya sadaukar DA Duk arzikin daya mallaka

Chapter 3 of 12