samu taci tsoka uku ganin taƙi sakewa taci a gabansa ya sashi karkacewa ya zaro kuɗi yan ɗari biyu rafa guda ya bata yace “ki riƙe a hannun ki saboda sa kati ban yarda a kira kowa ba bayan Ni" zaro wayar yayi da kwalayen turare ya aje mata ya miƙe ya kama hannunta ya sumbata ya fice da sauri saboda ganin idanunta ya kawo ruwa yasan tsaf zata karya masa gwiwa gara karma ya tsaya domin tafiyar tasa tafi zamansa muhimmanci........
*Share please*
[4/9, 6:25 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Free Page 8*
★★★~~~★★★~~~★★★
Koda ya fito tsakar gdan Saida ya bawa Marka kasonta sannan ya ƙara mata wasu masu tsoka da zata kula masa da habibansa kafin ya dawo duk da ya ƙudurce a ransa bazai daɗe ba hakan bai hanashi jin kewar abar ƙaunar tasa ba,
Cikin ƙaramin lkc yayi sabo da ita sabon da yake jin zagawarta a cikin jininsa yanajin zuciyarta na bugawa daidai da bugun tasa zuciyar, yana shiga masauki jakar kayansa kawai ya ɗauka drivern campanyn simintin na mahaifinsa ya ɗauke su suka ɗauki hanyar Dutse tsakanin Tsaunin gawo da Birnin Dutse tafiya ce ta gaske kasancewar Tsaunin gawo cikin ƙasar Kano take a rankin wata babbar ƙaramar hukuma.
Sun gajiya lkcn da suka shiga Dutse dare yayi nisa wannan tasa ba kowa ne yasan da dawowarsu ba, kai tsaye sashinsa ya nufa ya watsa ruwa yayi sallar magrib da Isha ya kwanta yana hucce gajiya amma zuciyarsa taki barinsa a Jigawa ta ɗauke shi ta mayar dashi Tsaunin gawo, hakanan ya wanzu yanata murmushi yana tunano irin wani yanayi da ya tsinci kansa ɗazu da yana kissing kyakkyawan bakin Beebansa tabbas akwai nutsuwa a cikin kasancewa da abinda zuci take muradi dole yayi bakin kokarinsa yaga ya mallaki Beebah bada jimawa ba ko ya samu zuciyarsa ta samu salama.
Da waɗannan tunane² bacci ya ɗauke shi me sihirtaccen daɗi cike da mafarkin abar ƙaunarsa cikin kyakkyawan yanayi wanda ya sanyashi jin shauƙin kasancewarsu tare aikam yana tashi da asuba ya watsa ruwa ya sanya doguwar riga ya nufi masallacin cikin gdan sarautar sai lkcn ƴan'uwa barori da kuyangi suka fahimci ashe autan Kilishi ya dawo Auta me dakawa maza gumbar wuya a hannu.
Kaffatan duk wani ma'aikaci dake cikin wannan gda yana masifar shayinsa bawai don tsabar zalumcinsa ba a'a saidai don masifar kwarjininsa ko kusa baya ɗaukar raini da wargi tun ma yana ƙarami bare yanzu da yake jinsa sama da kowa a duniya.
Bayan idar da sallah kamar yanda al'adar gdan take Saida suka gama gaisawa da juna ƴan'uwansa sunata yi masa sannu da zuwa yanata jin daɗi duk da kacokan hankalinsa yanaga Mai martaba domin shine dalilin zamansa so yakeyi ya samu damar magana dashi a yau ɗin nan.
Shi a burinsa ma baya fatan maganar aurensa da Beebah ta wucce wata guda saboda ji yakeyi kamar zai iya zautuwa idan bai sameta ba.
Mai martaba yana karɓar gaisuwa fiye da rabi na hankalinsa yanakan Habeeb tabbas da yanayi ya fahimci ɗan nasa yana cikin damuwa domin ya rame sosai ga wani duhu da yayi kamar wanda ya tashi daga jinya, Saida Sarki Khalil ya sallami kowa sannan yayi gyaran murya yace “Habibullahi an dawo lfy ya aikin muna fatan komai ya tafi yanda muka tsara?"
Ƙasa yayi da kansa yace “Muna fatan hakan Allah yaja kwananka..." Shiru ce ta ɗan ratsa har yanzu mai martaba kallonsa yakeyi can ya numfasa yace “Kayi rashin lfy ne?" Da sauri ya ɗago yana duban kansa ashe dai da gaske Najeeb yakeyi ya rame ɗin shi rabonsa da duba madubi har ya manta bare yaga yanayinsa.
“Muna sauraronka Habibullah" abinda mai martaba ya faɗa kenan hakan ya bawa Habeeb damar karkacewa cike da faɗuwar gaba ya lankwashe kafa kamar me neman gafara yace “Allah ya taimakeka dama mgnr da kuka daɗe kunayi min ce ta taso game da aure...." Sai kuma yayi shiru kamar me jin tsoron furtawa, murmushi Mai martaba Khalil yayi yace “Masha Allah ai dama hakan muke fata Habibu naji daɗin wannan labari a ina take, ya sunanta kuma ƴar waye a ƙasar nan sannan meye matakin karatun ta ɓangaren Islama da boko?......"
Dam gabansa ya buga kwata² ya manta da dokar gidan nasu na cewa macen aure sai saukakkiya wacce ta karanta ƙur'ani kuma ta haddace koda uzufi talatin ne a kanta matakin karatun boko degree sannan ba ƴar kowanne mutum ake kawowa gdannan ba sai wanda aka san sunansa a ƙasar, itako Beebah batada komai gata ba ƴar kowa ba gata ba musulma ba bare ayi maganar karatun Kur'ani boko kuwa ba itaba duk garinsu ma baiga wanda yayi ko gaba da primary ba.
Wani gwauron numfashi ya sauke lkcn da mai martaba ya katseshi da cewa “ka samu a gaba kayi mana shiru ko abin faɗarka ya ƙare ne?" “Ba musulma bace....." Ya faɗa cikin son arowa kansa dakiya, wannan kalma ta sanya mai martaba saurin ɗagowa yace “Wht? Ya Salam subhanallah Habeeb wannan ai zancen banza da wofi ne da bazai yiwu ba kafira kuma kakeso zaka auro mana cikin zuri'armu don taɓewa da lalacewa...."
Da sauri ya ɗago kalmar kafirar nan na mugun taɓa zuciyarsa miƙewa Mai martaba yayi ya saɓa babbar rigarsa ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga masallacin Habeeb yayi saurin miƙewa yasha gabansa ya zube yace “Kayimin rai ka fahimceni wlh Mai martaba inason Habeebah itama tanasona nasan zata iyayin komai donni bana ko tantama zata musulunta duk abinda ake nema zata samu nidai burina ku yarda na aurota Allah ya taimakeka ka taimaka min wajen wannan jihadin wlh saboda Ni Beebah har gdan iyayenta ta bari yanzu haka tana gdan Sarkin garinsu....."
Ɗaukeshi da mari Mai martaba yayi ya nunashi da yatsa zaiyi mgn takaici da bakin ciki ya hanashi iya cewa komai ya fice da sauri daga masallacin ya sake binsa yana masa magiya bai saurareshi ba ya shige sashinsa ya datso ƙofarsa take Habeeb ya zube a gurin zuciyarsa na tafasa tabbas wannan shine ake cewa yaƙi saida uwa shikam baiga laifinsa ba cikin son farantawa zuciyarsa na auren Beebah ba kuma baiga dalilin da zaisashi janyewa daga ra'ayinsa a faɗin duniyar nan ba.
Da wannan ya juya ya koma ɗakinsa ya rinƙa zagayashi yana dukan iska zuciyarsa tana masa wani mugun tuƙuƙi daya kasa samawa sassauci.
Wanka yayi ya sanya kayansa ya nufi cikin gdan fuskar nan kamar hadari saboda damuwar dake danƙare a ƙasanta Saida ya shiga ko ina suka gaisa yanayinsa yasa babu wanda ya tankasa sunsan yanzun rai zai ɓaci, ɓangaren Kilishi ya nufa ya ƙwankwasa ƙofar tana zaune saman sallaya da ƙur'ani me tsarki a hannunta tana muraja ya shigo ya samu guri ya zauna ta dubeshi ta mayar da hankalinta ga karatun ta.
Saida ta ida inda takeson tsayawa sannan ta ɗago ta dubeshi tace “Autan maza Ina ka shiga ne tun jiya naji lbrn dawowarka sabanin ko yaushe baka zomin ba" ajiyar zuciya yayi ya ɗago idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya sauke ajiyar zuciya da tasa gaban Hajiya Kilishi faɗuwa tace “naga ta kaina Ni Ummusalma Habibu na meye ya sameka ne naganka a ɗefare a lalace kamar kayi jinya?"
Sunkuyar da kansa yayi yana wasa da yatsansa ta kafesa da idanunta tana mamakin ramar ɗan nata tace “Habibu! Ɗagowa yayi ga mamakinta sai taga hawaye sharrrr a idanunsa gabanta ya faɗi tace “Ina dalilin hawayen?" Numfasawa yayi taja fasali tace “to tashi kaje bazakazo ka tayarmin da hankali ba bayan bankai sanin damuwarka ba...." Saurin ɗagowa yayi yace “Ba haka bane Hajiya kawai dai ina tsoron kema kada kiƙi fahimtata kamar yanda mai martaba yaƙi tsayawa ya fahimceni ne!"
Murmushinta na Dattaku tayi tace “Habibu kenan ai indai kaga ban fahimceka ba to yanayin da kazo dashi ne baiyi daidai da a fahimceka ba maza ina sauraronka" numfashi ya sauke nan ya zayyane mata komai taja wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske tayi kasaƙe tana tunana wannan gingimemen aikin da Habib ya kinkimo duk da bataji taƙi abin a ranta ba duba da dalilin daya zayyana mata amma ta hango hargitsi na gaske a tafiyar tabbas kafin aci Zomo sai anci gudu tunda mai martaba yaki fahimtar Habeeb to batasan kuma waye zai samu nasarar fahimtar dashi ba, tunda yaki wannan lamari bataga wanda zaisa yasoshi ba saidai in Allah yayi to ikonsa sai yasa ya rusuna yabi ko bayaso.
Sosai jikin Habeeb ya ƙara sanyi lakwas yace “Hajiya kinyi shiru don Allah kice kuma kisa albarka da bakinki me albarka inada tabbacin indai kika yarda kuma kika bani goyon baya Allah zai amince kuma zamu samu lada in har Habeebah ta yarda ta karbi addinin Musulunci Hajiya ki duba ladan da zaki samu ki aminta ki cire kokwanto"
Taguminta ta janye ta ɗago ta zubansa idanunta tayi masa murmushi na karfafa gwiwa tace “Na baka goyon baya Habib kaje ka nemi auren Habibah ka aurota ku rayu cikin aminci amma fah ina horon ka da kabi komai a hankali Kuma kayiwa mahaifinka biyayya shine kawai zaisa nasarar ka ta ɗore"
Numfashi yaja cikin jin daɗin wannan nasara daya samu gurin mahaifiyarsa yayi mata gdy yanajin wani haske ji yake yama samu Habeebah ya gama, da wannan ya miƙe ya fice daga gdan ya nufi gdan babban yayansu da yake da yakinin idan ya samu Mai martaba da mgnr zai ɗauketa seriously ya ishe shi yana shirin fita gurin aiki suka gaisa tare da nufar office din tare suna tattaunawa akan abinda ya shafi fam ɗin nasu.
Bayan sun huta komai ya lafa ne Alh Ahmad ya dubi Habeeb yace “Kace kanada mgn dani Habeeb ina sauraronka" sosa kansa yayi sannan yayi masa bayanin komai Alh Ahmad ya ɗago yanayi masa kallon bashida hankali yace “Wannan shine tabbatar da har yanzu lissafinka ba daidai yake ba tunaninka ya goce nikam bazan iya shiga maganar nan mara yiwuwa ba mai martaba yaci mutuncina gara kai dama kaine ka siyawa kanka da kanka, Habeeb idan shawara kake nema nikam ina baka shawarar ka hƙr da wannan aure da kakeson yi kazo ka zaɓa a matan Fam ga ƴammata nan duk sun gama karatu wasu ma daga wasu ƙasashen suka dawo amma kai kasan ba'a fara ba kuma bazaa fara akanka ba Bamagujiya Habeeb haba wannan faɗuwar daraja tayi yawa da yawa to ka a musulmi Mai martaba baya aminta da ƴar talaka bare kuma ƴar maguzawa......"
Miƙewa yayi ya dauki wayoyinsa ya zuba a aljihunsa ya fice daga office ɗin da takaicin meye yasa ma zuciyarsa ta raya masa yazo gurinsa bayan ba mafita zai bashi ba? Tsaki yaja ya nufi inda yayi parking motarsa ya shiga yaja ya fice daga harabar ma'aikatar.
*Share please*
[4/11, 7:44 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Last Free Page 9-10*
★★★~~~★★★~~~★★★
Bai koma gda ba sai yamma koda ya fito daga ma'aikatar yayan nasa tasu ma'aikatar ya nufa amma abin arziki ya kasa hassalawa sai juyi da yake a kan kujera wayar Beebah yaketa kira taki tafiya duk damuwa tabi ta cunkushe masa zuciya sai bayan magrib ya nufi gdan babu wani karfi a jikinsa saina imani wanka yayi yana shirin fita Masallaci sallar Isha wayarsa tayi ruri ya ganin number Mai martaba yasashi haɗa nutsuwarsa ya daga Mai martaba yace “in ka dawo kazo inason ganinka" amsawa yayi tare da fita yaje yayi Sallah sannan ya nufi kiran na Mai martaba ya shiga da sallamarsa yana zaune saman shimfiɗun Kilishi da farin tabarau a idanunsa ya amsa sallamar Habeeb ya nemi guri ya zauna yace.
“Allah yaja kwana gamu mun amsa kira" ɗagowa yayi yayi masa murmushi ya miƙe ya saita zamansa yace “Am dama wani babban uzurine ya taso munason zamu haɗa gwiwa da wani campany dake Japan domin haɓakar masana'antunmu" jinjina kai Habeeb yayi yace “hakan yayi Allah ya taimakeka hakan zai kawo ci gaba ƙwarai" murmushi Mai martaba yayi yace “shiyasa nakeson ka Habibullah to dama ba komai bane yasa na kiraka campanyn sun buƙaci a tura mutum ɗaya daganan domin yaje yayi course na yanda ayyukan suke kasancewa kamar yanda suma zasu turo nasu wakilan don faɗaɗawa juna fasaha.
Na duba naga babu wanda ya dace da wannan tafiya saikai duba da kwazonka da basirar ka saboda haka kaje ka fara shiri nan da sati biyu zaka tafi in Allah ya yarda...."
Tunda Habeeb yaji ƙudurin Mai martaba gumi yake karyo masa yasan tabbas da manufa cikin wannan shiri, a sanyaye ya ɗago ya buɗe baki zaiyi mgn Mai martaba ya ɗaga masa hannu yace “banason kace komai kaje Allah yayi maka albarka shekara ɗaya ne babu yawa idan Allah ya amince kafin lkcn zan sama maka matar data dace dakai na aura maka na turota tunda na fahimci yanzu hankalinka ya hadu kana buƙatar auren" a kasalce yace “Habeeban fah ranka ya daɗe...." Shiru mai martaba yayi masa shi kuma ya kasa tashi jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali bai iya jurewa ba yace “Na rantse da Allah bazan iya zama da duk wacce zaka aura min ba Allah ya taimake ka indai bazaka amince nayi jahadin janyo Habeebah daga duhun kafirci zuwa hasken musulunci ba idan bazaka amince min na rayu da abinda raina da zuciyata suke muradi ba to ina roƙonka da kayi hkr ka barni na ƙarasa rayuwata ni kadai kamar yanda na shirya yinta a baya...."
Tsawa Mai martaba ya daka masa yana huci yace “Ni Habeeb Nine nake faɗa kake faɗa harma na zartar da hukunci kace baka amince ba lallai ya tabbata ka girma kakai shiyasa har kake jayayya dani akan kafira, to na rantse da Allah kaji dai kuma ka sani bana saurin rantsuwa akan lamarin rayuwa to nayi akan wannan yarinyar indai kaga ka aureta to kodai ka canza uba ko kuma bana numfasawa, tashi ka ficemin a daki kafin na nakasaka"
Tsuma jikin Habeeb yakeyi saboda ɗimuwa da gigita rantsuwar mahaifinsa tayi mugun girgiza shi Shikenan ta faru ta ƙare Mai martaba ya gama yanke hukunci yanzu babu bakin da zai iya fahimtar dashi ya gane...."
Sashin Hajiya Kilishi ya nufa da ƙannensa biyu mata da suke ciki ɗaya da sauran matan gdan duk suna babban falon suna kallo yazo ya shigesu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa ya faɗa kan gadonta saboda mugun sanyin da yaji yana keta ƙashinsa yaja bargo ya rufa.
Kallon kallo sukayi Hajiya Zulai ta dubi Hajiya Kilishi da Hajiya Hauwa tace “Salma?" Dubansu Kilishi tayi tace “Naam Zulai" Hajiya Hauwa ce tace “Soja ƙalau kuwa?" Numfasawa tayi tace “da alamun ba ƙalau ba wato ɗebowa yayi da zafi aure yakeson zaiyi kuma ba musulma bace yarinyar da yakeson aure, nikam na fahimceshi kuma na bashi goyon baya to amma fah tunda mai martaba bai fahimta ba babu wanda ya isa ya fahimtar dashi"
Miƙewa Hajiya Zulai tayi ta nufi ɗakin tace “Babana komansa daban banda rigima irinta tarar aradu daka inashi ina kafira matsayin mata...." Tana faɗin haka ta bude dakin ta shiga yanda taji gadon na rawa yasata nufarsa da sauri ta yaye bargo tace “Innanillahi Ni Zulaihatu Babana meye hakan kuka kamar wani ƙaramin yaro...."
Tashi yayi zaune ya kama hannunta yace “Don Allah ku ceci rayuwata ku faɗawa mai martaba zanje Japan ɗin amma ya barni na auri Beebah Hajiyan soro bazan iya taɓuka masa komai ba indai ya rabani da Beebah nasan itama bazata iya rayuwa babu Ni ba"
Numfashi taja tace “Akan mace kakeson kashe kanka dubi fa yanda kake rawar sanyi Habeeb yanzu waye kake tunanin zai iya tunkarar mahaifinku yace zai fahimtar dashi?"
Hajiya Kilishi ce ta cafe da cewa “kaje inda ya umarce ka kayi masa biyayya insha Allahu zaka dace idan kace zakaja yaja kaine zaka faɗi ƙasa" zama sukayi sunata rarrashinsa shikam banda zafin jiki ma babu abinda suke ƙara masa kafin wane wannan zazzaɓi me zafin gaske ya lulluɓeshi Hajiya Kilishi ta shiga damuwa tabbas bada wasa Autan mazan nata ya ɗauki lamarin ba da gaske yakeyi don duk abinda yasa a ransa har yakai masa jinya to ya isa kallo.
Ranar sai ɗakin tabar masa bayan likita ya duba shi baccin wahala ya ɗauke shi zuciyarsa taƙi samun sukuni
Washegari da asuba ya duba wayarsa ya zabura ya tashi zaune yana latsa wayar bugu biyu ta daga cikin muryarta me cike da gajiya da kasala tace “Tunda ka tafi nake kiran ka naji ko kun sauka lfy bana samu ɗan birni ina fatan lfy kake..." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yace “kamar bakida lfy meye yake damunki?" Kukan da ta kwana ta nayi shine ya dawo mata sabo tace “banasonsa wlh tsohone idan suka auramin shi kashe kaina zaiyi ɗan birni kai nakeso...."
“Wa?" Ya faɗa da ƙarfi yana miƙewa daga gadon cikin kuka tace “Sarkin Mahauta...."
Miƙewa yayi daga gadon yace “Wa...waye yace zai bashi ke waye...." Kashe wayar tayi yayi bin duniya ta kasa ɗagawa aikuwa ba'a wayi gari dashi a gdan ba ya nufi tasha ya hau mota saboda bazai iya tuƙi ba shata ya ɗauka har garin Tsaunin gawo bai zame ko inaba sai gdan Dagaci a ƙofar gida ya tarar dashi sunashan hantsi ya mike da sauri ya tareshi suka gaggaisa yace “Ina Beebah?" Sunkuyar dakai Dagaci yayi cikin kunya yace “Tana ciki wani abu ta faɗa maka?" Iska ya furzar yace “waye wanda suka bawa ita?" Gabansa ne ya faɗi yace “Mai Tukuba ne nasan kasanshi a zaman da kayi a garin nan don ko zaman yini ɗaya kayi a garin nan indai ka shiga cikin mutanen garin nan zagaji sunan me tukuba ɗaiɗai yarinyar data zama bazawara a garin nan da bashine ya mayar da itaba a yanzu haka matansa na aure sha tara a gidansa Bibo itace ta Ashirin yau da yamma yace zai kawo komai na aure a ɗaura zai ɗauketa su tafi rani nayi iya yina na kasa yanada manya a karamar hukumar nan yanada bokaye sannan yanada kuɗi kaga dole na sakar masa iko...."
Numfasawa yayi ya dubi agogon hannunsa 12:12pm ya dago jajayen idanunsa yace “akwai masallaci a garin nan?" Girgiza kai Dagaci yayi yace “Saidai Hayin Fulani" ajiyar zuciya yayi yace muje ka rakani"
Babu musu suka nufi hanyar da zata kaisu Hayin Fulani suna zuwa suka tarar anyi shimfiɗu a ɗan ƙaramin masallacin juma'ar Liman ɗin dakansa ya fito ya taresu yana kallon Habeeb da mamakin abinda ya kawo shi musamman da yaji ance shine baƙon.
Karkacewa yayi masa bayanin komai da uzurinsa liman ya kalli na'ibi suka jinjina sukace “kaiko ɗannan miye naka da auren ɗiyarga ta Jimo kaje ka nemi wata mana ko a rugar nan ne baka mukayi"
Girgiza kai yayi yace “ita nakeso liman taimakon ta zanyi bayan soyayya akwai tausayi kanaganin wanda sukeso subawa aurenta yarinya ƙarama nawa Habeebah take wlh Kona aureta saina raineta kafin ta gama haɗa hankalinta sone yayi mana gaggawa, liman ka yankan sadaki na biya a ɗaura bisa tsarin addinin musulunci"
Ɗagowa Liman yayi yace “Duk da inajin tsoro bazanƙi ɗaurawa ba amma hanzari kace ita yarinyar ba musulma bace kaga kenan akwai jumurɗa abinda zaifi indai ta amince zata aureka to ta yarda ta musulunta auren zaifi sauki..."
Gumi ya share yace “zata musulunta daga baya nidai a ɗaura ɗin shine me wuyar" baƙin nacinsa yasa dole Dagaci ya karbi waliccin Bibo na'ibi ya karɓi na Habeeb aka ɗaura wannan rikitaccen aure akan sadaki saniya biyu kamar yanda al'adar Waliyyin angon take.
Wayyoh zo kuga murna gurin Habeeb har sujjada yayima ubangiji na cika masa burinsa da yayi, ya manta da duk wata kwantacciyar ƙura da ɗaura wannan aure zai tayar ya manta da rantsuwar mahaifinsa ya manta da alwashin da yaci akansa muddin ya auri Habeeba, ya manta da ƙudurin Mahaifanta da sukaci alwashin saisun kasheshi sun kashe Bibo muddin ya matsa akan aurenta......
Sai a lkcn abubuwa suke ta dawo masa yayi zugum zuciyarsa ta kasu biyu wani sashi farin ciki wani sashi ɗinbin damuwa, Dagaci ne ya katse shirun da cewa “Mal Balaji tunda dai wannan aure ya ɗauru Habeebah matar Habibu ce to zaifi ya ɗauke matarsa subar garin nan don tabbas maganar zata fasu kuma indai har ta fasu batare da yabar ƙauyen nan namu ba to kuwa ko zai fita zai fita cikin rashin hayyac...."
“Kwarai kuwa munafiki zai fita cikin rashin hayyaci domin kuwa bazamu bawa abar dogaro kunya ba kamar yanda muka alƙawarta zamu kasheshi mu kasheta sayi auren a lahira na rantse indai nine Buba Sarkin Noma to yau saina raba wannan yaron da rayuwarsa bai isa ya auri jikanya ta ba macuci masu shanye jinin bil'adama......"
Wani sara ya kaiwa Habeeb daidai lokacin da Habiba ta kwace daga riƙon da yayi mata ta hankaɗe Habeeb suka zube can baya tare sai gashi a ƙasa ita kuma tana kwance a samanshi.
Idanunta ta buɗe cikin idonsa ya sakar mata wani murmushi yasa hannunsa ya riƙe weast ɗinta ta kwantar da kanta luf a ƙirjinsa dagashi har ita wata nutsuwa ce take kwarara a ƙasan zukatansu....
Babu wanda yasan meye yake faruwa saida sukaji Liman yana cewa “Buba Aure ne mun riga mun ɗaurashi Habiba ta tabbata matarsa kada kuja da ikon Allah shine ya hukunta wannan aure kuma babu wanda yasan rabon dake tsakani wannan....
Dakata nace ka dakata Mal Liman kun hana mu taɓashi amma fah ka sani idan har kukaga yabar ƙauyen nan to warware auren nan kukayi...." Janyewa Habiba tayi a jikinsa zatayi magana Uda ya kai mata bugu Mal Liman ya janye ta ya turata gdansa ya dubi Habeeb yace shiga ciki akwai zauren baƙi ka jirani"
Zaku iya samun littafin nan ta website na arewabooks ku karanta cikin sauƙi ga waɗanda karatu keyi musu wuya a WhatsApp, ko kuma ku sauke app na arewabooks a wayoyin hannunku ga link ɗin domin shiga ta website ku biya ku karanta cikin aminci👇🏼
https://arewabooks.com
*Share please*
[4/13, 8:45 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Kunata cewa promo ɗin dana baku yayi kaɗan to gashi nan na ƙara daganan zuwa jibi zaku sameshi a 200 PC 500
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241 ƴan Niger kuma zaku tuntuɓi wannan number don biyan kuɗinku +227 95 04 58 22.
*Free Page 11-12*
★★★~~~★★★~~~★★★
Ankai ruwa rana kafin su fita daga Hayin Fulanin Saida aka shigar da jami'an tsaro sannan suka samu suka fita da Habeeb daga garin da sharraɗin Habeebah zata zauna a gdan Liman zuwa wasu kwanaki kafin mijinta ya dawo ya ɗauketa.
Inda su Jimo sukaci alwashin muddin suna raye wannan aure bazashi ko inaba shidai Habeeb bai bawa mgnrsu muhimmanci ba yaja ƙafafunsa suka bar ƙauyen cike da kewa shauƙi da ƙaunar matarsa.
Itako Habeebah lkcn da taji hukuncin da aka yanke da kuma furucin da mahaifinta yayi akan aurenta sai duka jikinta yayi sanyi bataso aurenta ya kasance a haka ba bataso ace ta samu matsala da iyayenta ta dalilin aurenta ba Shikenan sun sallamata babu su babu ita saboda Habeeb?"
Hawaye ne ya sulalo mata ta zauna a shimfiɗar da Hajjo matar Liman tayi mata ta zuba uban tagumi hawaye wani nabin wani zuciyarta tayi ƙunci duniyarta tayi duhu.
Tunda ta taso takejin iyaye mata suna cewa duk matar data ɗauki namiji uba saita mutu marainiya! Yanzu ita meye ribar da zata samu data amince tayi baram baram da iyayenta akansa? Waye shi??Meye yake ma nufi da aurenta??? Meye yasa ya tsallake matan dake birni yace sai ita?.
Tambayoyi barkatai marasa amsa tunanin Jumme ya faɗo mata ta kuwa rushe da kuka me gigita tunani da taɓa zuciya yanzu Shikenan bazata sake ganin Jumme ba? Ta rabu da mahaifiyarta me ƙaunarta da ƙaunar farin cikinta har abada?
Kuka takeyi sosai me taɓa zuciya, a haka Hajjo ta ishe ta ta tafa hannu tana salati tace “Haba yarinya Meye kuma abin kukan ai gdy ya kamata kiyiwa Allah