Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
suka kai gonar Habeeb ya tsaya yana kallon gonar ba wata babba bace amma tayi kyawun yabanya da ta burge shi. Tsinkayo muryarta yayi tana cewa “kaje ka zauna ga bishiyar mangwaro can tunda ka nace Saida ka biyoni” miƙa mata kayan hannunsa yayi batare da yayi furuci ba bai kuma bi umarninta ba, ganin abin nasa na yine yasata wuccewa ta fara aikinta tanayi yana kallon yanda take tafiyar da komai yana gane irin ciyawar da take cirewa da haka shima yakai hannu ya fara tayata. Ba ƙaramin mamaki ta shiga ba da taga ko ita data saba aikin bata kaishi kwazo ba ta ɗago tasa gefen zaninta ta sharce gumi ta zubansa idanu tana mamakin inda ya iya aikin gona da kuma yabawa kyawun surarsa tabbas yakai kyakkyawa na gaske duk da ba fari bane amma yanada wani sihirtaccen kyawu da hasken fata na tsabar hutu da jin daɗi da yake bayyana kwanciyar hankalinsa. Ɗagowa yayi ya zubanta idanu tayi saurin kawar da kanta tare da basarwa ta sunkuya tana tattare kayan tana cewa “naga abubuwan mamaki a iya yau dana zauna dakai naga kana isa waccan ƙoramar kana wanke jikinka kana dungura goshinka ƙasa meye hakan yake nufi.... " Cikin mugun mamaki Prince Habeeb ya Kalli Bibo tare da kafeta da manyan idanunsa, yanzu ita a nufinta batasan sallah ba? Mamakinsa ya kawar da cewa “koda yake a ina zata sani?" Tayata tattare kayan yayi yace “Kada kiyi gaggawa da sannu kuma a hankali zakisan komai game dani tunda kin yarda da abotarmu" miƙewa tayi da sauri tana girgiza kai tace “Aa Nifa ban yarda da wata ƙawance ba...." Hannu yasa saman bakinta ta ɗago ta dubeshi idanunsa nakan fuskarta yace “kar kija da ƙudurina inason abota dake kuma ta ƙullu daganan har zuwa lkcn da zan bar garin nan naku kiji a ranki a koyaushe kuma a kowanne yanayi zamu kasance a tare Habeeba bana nufin cutarwa gareki saidai ke kin kasance ƙaddarata" “Ƙaddara" ta faɗa tare da ɗagowa da sauri, bai tsaya bata amsa ba saima gaba da yayi dole tasa ta bi bayansa suka nufi cikin gari duk inda suka wucce hankali akansu yake har suka je ƙofar gidansu taja ta tsaya shima ya tsaya sun jima a tsaye ganin bashida niyyar furuci sai kafeta da yayi da manyan lulu eyes nasa yasata juyawa tana cewa “Na gde ka huta gajiya" Shigewa tayi ciki yabi bayanta da ido abubuwa da yawa na ayyanuwa a ransa waɗanda ya kasa tantance yuwuwarsu ko rashin yuwuwarsu koda yake Hausawa sun ce da tsoro ake cire saa shikam zuciyarsa na rawa akan abubuwa da dama amma dai zai jarabba kalar tashi nasarar yagani idan yanada rabo. Da wannan tunanin ya isa masaukinsu Najeeb daya gaji da kiran wayarsa har ransa yayi ƙuna ya tareshi da cewa “Ina kaje?" Tambayar ce ta bashi haushi ya zabga masa harara ya nufi cikin gdan gdane me kyau nesa da cikin gari kaɗan ginin zamani dakunansu harda A C ga babban inji da aka sanya musu me bada wuta kowanne lkc sannan duk wata kalar kayan jin dadin rayuwa sun siya sun zuba a gdan a taƙaice dai idan ka shiga gdan bazaka gane a ƙauye kake asalin ƙauye irin Tsaunin gawo ba. “Habeeb tambayarka nakeyi ina kaje...." Juyowa yayi ya kafeshi da idanunsa wanda ba kowa ke jure sanya ƙwayar idonsa cikinsu ba ya tako gabansa yace “Ni kamar ni kake tambaya ta ina naje kamai dani wani ƙaramin yaro ne ko kamai dani mahaukaci da kake gadi na?" Yayi mgnr yana zare ƙafar wandonsa, harara Najeeb ya watsa masa yace “ka kuwa ɗaukowa kanka abinda zai dameka banga uwar da ta ɗauki hankalinka akan wannan yarinyar mara addini ba da har ka zaɓi zubar da mutumcinka akanta....." Tsawa ya daka masa yace “Wlh tallahi ka ƙara faɗar wata kalma mara kyau akan Habibah saina...." “Sai kayi me? an faɗa mara addini kayi duk abinda zakayi sakarai da idanunsa yake rufewa idan yaso abu kamar babu wani abu bay....." “Najeeb...." Ya faɗa tare da ɗaga hannu zai daukeshi da mari me kuma ya tuna saiya fasa jikinsa yana tsuma yace “Ficemin daga ɗaki kafin na illataka..." Hayaniyar tasu ce tayi yawan da har ta fito da James daga ɗakinsa koda bayajin Hausa yasan lallai koga yanayin fuskokinsu ran maza ya ɓaci ganin yanda Habeeb ke tsuma yana ruwan bala'i yana nunawa Najeeb hanya yasa James kama hannu Najeeb suka fice yana cewa “Kuma ka rubuta ka ajiye wlh indai ina raye zamu koma Dutse wlh saina rusa duk wani shirinka baka isa ka auro mana Arniya mara addini ka kawo mana cikin zuri'armu ba wawa kawai da baya lissafa rayuwa wannan abinda kake shirin aikatawa ai ya cika abin kunya ace duk matan da muke dasu a Family saika fito waje wajen ma ka rasa wacce zakaso sai BAMAGUJIYA to saika aura mu gani ai...." A hassale yace “Idan Allah yayi saika hana ai ɗan hana ruwa gudu kawai Ni na taɓa jin wannan jaraba kun dameni na kawo matar aure na kawo wacce nakeso nakasa samowa yanzu kuma lkc yayi kwatsam ta faɗo rayuwata amma kaine na farko da zakayimin hassada to barima kaji Ni kuma naci alwashin ko zan rabu da kowa da komai saina auri Habeeba....." [3/31, 7:39 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA* *(HOT LOVE AND DESTINY)* NA *FAUZIYYA TASIU UMAR* *OUM HAIRAN* *Tsokaci* Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa. *Jan kunne* Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi. *Sanarwa* Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma. Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700. *Page 4* ★★★~~~★★★~~~★★★ Tsaki Najeeb yayi yana huci kamar kububuwa ya fice daga gdan gabadaya shikuma ya nemi guri gefen katifarsa ya zauna shima yana fitar da iska me zafi sosai kalaman Najeeb sun taɓa zuciyarsa kwafa yayi ya miƙe ya shige bayi ya watso ruwa. Ba ƙaramar gajiya yayi ba ashe haka manoma sukeshan wuya lallai dole a gaida manoma sallar magrib yayi domin yasan ba kiran sallah zaiji ba Saida yayi Isha yayi shafa'i da wuturi sannan ya haɗa tea yasha dake shi ba ma'abocin abinci me nauyi bane indai da shayi to lfy lau ne. Tunda ya kwanta yake sakawa da warwarewa majigin hoton Habeeba yanayi masa gizo a idanunsa, tashi yayi ya zauna baisan meye ya tafi da ruhinsa gareta ba ba kowacce mace tafi komai ba ganinta kwana ɗaya yanajin kamar yayi shekara guda da ita baiji zai iya rabuwa da ita ba, saidai abubuwa biyu suna mugun kada masa hantar cikinsa baisan da yaya Sarki Khalil da Hajiya Kilishi mahaifiyarsa dama sauran danginsa na gdan sarautar dutse zasu karɓi wannan zabi nasa ba. Karfafawa kansa gwiwa yayi da sama kansa ƙumajin nasara tabbas zaiyi duk mai yiwuwa ya kafa kansa a wajen Habibah da iyayenta duk da suma a yanda suke da tsattsauran ra'ayi yasan za'aja daga kafin su bashi damar auren ƴarsu. Numfashi ya sauke ya koma ya kwanta daidai lokacin da wayarsa ta ɗauki ruri, gabansa ya faɗi ya mike ya ɗauki wayar numfashi yaja me ƙarfi ganin sunan mahaifiyarsa na yawo a saman sensor ɗin. Cikin mutuwar jiki ya kara wayar a kunnensa ta sauke ajiyar zuciya tace “Autan Mama kaji daɗin garin arna ka manta dani ko kiran ma da kakemin tun jiya da safe banjika ba ince dai lfy kake?" Wani wahalallen numfashi ya sauke ya shafa sumarsa yace “sorry My love wlh abubuwa ne sukayi min yawa shiyasa lissafin komai ya kwace min ya kike ya Mai martaba da sauran ƴan gida ina Hajiya da Inna duk ince dai suna lfy?" Lfy Alhmdllh ya jikin naka ina labarin surukata...." Wani damm ƙirjinsa ya bayar da sauri ya basar da cewa “Ohhh Mama wai nikam na dameki ne duk kunbi kun damu sai kun ɗora min nauyi nawa nake ne har yanzu ban rufa 30 years ba" katseshi tayi da cew. “Kai ar ɗan ƙaniyar uwa to so kake sai kakai ka wucce duk mazan gdan nan waye yayi girmanka babu aure? Faɗamin shi haba ubana shi aure ai ƙima ne kuma garkuwa ne ga ɗa namiji nikam gsky nima inason ganin ƴaƴan auta na kada ka manta fah ku biyu gareni maza daga babban yayanku sai kai yan uwanku duk mata ne ai Yakamata ku karɓi girman tunda wataran kune iyayensu duk girman mace ƙasan namiji take domin raunin mu faɗaɗɗe daga bakin ubangijinmu...." Wa'azin nata yaji zaiyi tsayi yace “Is ok Mama kin kusa samun suruka indai suruka ce very soon kinji" murmushi tayi tace “Ubana kenan Sarkin daɗin baki shikenan Allah ya kawo mana rabonmu na alkhairi" ajiye wayar yayi yana murmushi Hajiya Kilishi kenan kullum maganarta Habibunta yayi aure zaidai yi auren nan ko ta sake masa mara yayi fitsarinsa a nutse. ****** Ɗagowa tayi jikinta a mace tace “Na rantse da abar dogaro ba Rabe bane ya rakani gona baƙo ne ɗan birni muka haɗu dashi a hanya shine yace yanaso ya koyi noma Jumme saida nace karya bini yaki ji to ya zanyi masa tunda kince babu kyau jayayya da babba" Shiru ce ta ratsa gurin Jimo Ciwake ya ɗago yace “Shikenan amma dai banason wannan tarayyar taku saboda ƴan birni basu da gsky idan kin sake haduwa dashi ki faɗa masa nine nace banason alakarku ya nemi wata abokiyar bandake wannan sakarcin da shashancin shashatau ɗin baza ayisa dani ba" Jinjina kai tayi tace “Na gde zan kiyaye" miƙewa tayi ta koma ɗaki tayi tagumi a haka Kande da Lantai suka shigo suka ishe ta Lantai ce ta sanya hannu ta cire mata tagumin tace “yo yau naga watsiyar watsewa Jimo ne ya mutu ko Jumme da zaki rafsawa mutane tagumi haka?" Numfasawa tayi ta ɗago idanunta ya ciko da kwalla tace “yauma shine ya aiko ku?" Zama Kande tayi ta kama hannunta tace “Na rasa wannan wacce irin masifa ce kwana ukun nan kullum sai yazo dandali yasa an kiramu ya tambayemu meye yasa bakya fitowa? Munce masa baki da lfy to yau dai sakomu yayi a gaba wai sai mun rakosa munyi masa iso ya dubaki...." Dafe kirji tayi tace “Na shiga uku kada ku barshi ya shigo kuje kuce masa na tafi hayin badarawa gdan kakata kuma ba'a bin hanyar da dare saboda akwai wata mahaukaciyar damusa da take kashe mutane....." Zaro idanu sukayi. Lantai ta matso tace “Tabɗi bakisan yanda mutumin nan yake da naci ba ai na rantse da abar dogaro cewa zaiyi mu rakashi garama kiyima su Jumme wayo muje ku gaisa saiki dawo...." Motsin shigowar Jumme ne yasa su miƙewa cikin zaurancensu na ƴammata tayi musu nuni da suje su jashi bayan gidansu. Jumme ce ta dubeta tayi ƙasa dakai tace “don darajar Baba Tsauri uwarki kibarni yau naje dandali da Lawai me kura ake wasa inason wasansa" murmushi Jumme tayi tace “kin gamani da ƙarshen daraja jeki saikin dawo Allah ya tsareki" tsalle tayi ta saki ihun murna ta fice da gudu. Bayan gdan nasu tayi da sauri ta nufeshi duk wata gaɓa ta jikinta tana rawa ta baza gashin nan nata me taushi da aka ƙawatashi da kitso kananu iyakar gaban bayan aka barshi duguzunzun rigarta iya ƙirjinta ta rufe cikakku tsayayyu masu faɗin tushe da ɗaukar hankali ta killace su ɗamɗam cikin rigar saƙin. Cibiyar ta a waje take shafaffen cikin nan zanen tatu na kibiya anyi mata zanen flower me ɗaukar hankali ƙugun nan yaci uwar jigida kusan naɗi kusan hawa talatin ta cika mata faffaɗan ƙugun nan zaninta iyakar gwiwarta tukatukin ƙafar nan an ƙawata su da nadin duwatsu. Tunda ta taho ya zubanta manyan idanunsa da suke lumshewa fari tas yake jin zuciyarsa tana isowa ta tsugunna a gabansa ta kama ƙafarsa ta ɗaga ƙafarsa ta ɗora tafin ƙafarsa a tafin hannunta ta ɗago kyakkyawar fuskarta ta sakar masa murmushi da yaja dimple dinta ya lotsa Jan lips dinta suka baje a fuskarta tace “Aminci da nasara su tabbata gareka mutumin birni inata kewarka banganka ba banjika ba har rashin lfy nayi da Jimo Ciwake ya hanani fitowa saboda ka rakani gona...." Hannunsa yasa tsakanin ƙirjinta da hammatarta ya ɗagota suka fuskanci juna damdam haka ƙirjinta yake bugawa inda shima yake jin wata muguwar faduwar gaba ƙamshin wani turare daya kasa tantance wanne irine yana tashi a jikinta ya hadu da sanyin yanayin damunar ya saukar masa da wata sihirtacciyar kasala baisan sanda ya hadeta da jikinsa ba yasa hannunsa biyu saman ƙugunta ya kwantar da kansa a saman nata ya sauke wata mahaukaciyar ajiyar zuciya da baitaɓa jin fitar irinta a cikin rayuwarsa ba. [4/2, 2:43 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA* *(HOT LOVE AND DESTINY)* NA *FAUZIYYA TASIU UMAR* *OUM HAIRAN* https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg *Ramadan promo* Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma wannan tasa nayi muku discount nrml group 300 ya koma 200 PC 700 ya koma 500, wannan garaɓasar ta iya satin farko na Ramadan ne Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. *Sanarwa* Maganar tsarin post da kuke tambaya ta insha Allahu na tsara shi yanda bazai shafi ibadarmu ba zan rinƙa post kullum 9:30pm wato tara da rabi na kowanne dare. *Page 5* ★★★~~~★★★~~~★★★ Ɓambare jikinta tayi daga nasa ta ɗago manyan idanunta suka shiga cikin nasa hawayen da batasan sun taho ba suka gangaro kan kuncinta, gabadaya ilahirin jikinta rawa yakeyi saboda tsoro da tashin hankali. Juyawa tayi tana kokarin kwasa da gudu tare da toshe bakinta da kukan yake kokarin fin karfinta, riƙe hannunta yayi da himmarsa cikin tashin hankali yace “ya Allah Habeebah me nayi Miki meye yasaki kukan ko bakiyi murna da ganina ba?" Durƙushewa tayi ta turmutsa hannunta cikin ƙasa ta rushe da kuka me ban tausayi da ɗaga hankali, zama yayi da sauri yakai hannunsa don ɗago fuskarta ta tureshi da ƙarfi tace “ni nace ka daina taɓani ɗan birni na shiga uku so kakeyi sai an kasheni a garin mu yanzu idan wani yaga yanda ka kwaƙumani da jikinka zuwa za'ayi a faɗawa Jimo Ciwake kuma na tabbata kasheni zaiyi nima da wannan abin kunyar gara ya kasheni na huta kowa ya huta, duk jikina nasan yanzun warin maza yake...." Rufe mata bakin yayi da hannunsa yace “Ke bafa haka bane tsoratar daku sukeyi amma babu wani warin maza da ake ji a jikin mace don namiji ya taɓata amma tunda bakiso shikenan yi hƙr nayi alƙawarin bazan ƙara taɓaki ba amma fah inada sharaɗina nima in kin yarda" Da sauri ta ɗago tace “Wanne?" Lumshe idanunsa yayi ya ɗora habarsa kan tafin hannunsa ya buɗesu akanta ya motsa ƙaramin bakinsa a hankali yace “Wannan shigar zaki daina ki rinƙa killace jikinki kinga ita wannan shigar idan wani namijin yaganki da ita sako zai ɗarsu a zuciyarsa idan ya ɗarsu kuma zaiyi ƙoƙarin ya aiwatar aiwatarwar kuwa itace babban tashin hankali don zai rabaki da ƙimarki" sake kallonsa tayi tace “kamar ya?" Miƙewa yayi zaune yace “Zaiyi yunkurin keta alfarmarki ta hanyar sanin ki ɗiya mace ma'ana a gwari² zaiyi Miki fyade....." Miƙewa tayi a kiɗime ta dafe ƙirji tace “na shiga uku fyade irin wanda aka yiwa Tani ta mutu?" Jinjina mata kai yayi cikin jin daɗin yanda ya samu nasara cikin sauki yace “Wace Tani?" Hawaye ta goge ta kama hannunsa suka nufi wani kurutturen ice suka zauna ta sake goge hawayenta ta ɗago ta dubeshi shima ita yake kallo tayi ƙasa da kanta tace. “Tani yayace a gurina ƴa ce a wajen wan babana wato Baba Uda, ta girmeni amma soyayyar da take min tasa muka zama kamar ƙawaye komi namu tare mukeyi karshe ma Ni kusan a gdansu Tani na girma saboda gidansu akwai wadar yara abokan wasa nikuma gidanmu Ni kaɗai Jumme da Jimo suka haifa. Tare muke zuwa gona tare muke zuwa tallen kunun zaƙi baban Tani Uda yana dafa Burkutu tare muke ɗauka mukai gurin bauta mu siyar, wata rana da bana mantawa ana bikin kamun kifi baƙi daga gari² sunzo domin ganin wannan bikin gwaninta da akeyi duk shekara domin kaf yankin nan a garin nan ne kawai akeyi kuma shi dama wannan ruwan na bayan gari da muke kira ruwan tsarkakewa tun tale² baa kamun kifi a cikinsa sai shekara shekara wannan tasa duk kifin da aka kamo zaka sameshi narkeke to wanda yafi kowa gwanintar kamun kifi a wannan shekara shine zai auri sarauniyar ƴammata ta wannan shekara. Za'a ɗaukeshi a kaishi gdan Sarki aje a ɗauko sarauniyar matan shekara a kawo ta a daura musu aure kuma babu ruwan wannan bikin da cewa baƙone kai ko ɗan gari haka za'a bawa me Sa'a matarsa ya tafi da ita. Kasan meye ya jawa Tani faɗawar azal?" Numfashi yaja ya girgiza kai ta sunkuyar da kanta tace “Kyau ɗan birni mu kininmu muna da wani irin kyawu da bansan ta ina muka sameshi ba bawai zallar kyawun fuska ba a'a direwar halitta ga kuma wani farin jini da kakanninmu suka roka mana abar dogaro ta bamu, Tani kyakkyawa ce ta wucce misali don duk kyawun nan nawa da ake faɗa ni banfi rabinta ba saidai fatar mu iri ɗaya ce wankan tarwaɗa, hakan yaja mata cincirindon masoya daga cikin garinmu da makota harma da ƴan birninku da suke zuwa kallon ajabin da aka halitta a wannan ƙauye namu, amma taƙi tsaida gwaninta. Kwatsam sai Wannan shekara abar dogaro ta nunata matsayin sarauniyar ƴammatan shekara aikuwa maza suka rinƙa murna domin kowanne jarumi gani yake nasarar samun Tani tasace. Haka muka dukufa shirye-shiryen wannan biki mukayi alibidi yafi kala goma Baba Uda da mahaifina Jimo har awaki da toron agwagi suka yanka mana dake haka al'adar take a gidan su sarauniyar ƴammata za'ayi girkin bawa gwarzon shekara. Munata kaiwa da komowa munata hidima ranmu fes karma ni naji labari don ko hutawa banayi nakai na kawo ina tsokanar yaya Tani, abin dana fahimta saidai tayimin murmushi kawai idan na matsa mata sai ta kama hawaye inna tambayeta dalilin kukanta sai tacemin kawai tanajin tsoron a dauketa daga gari a kaita wani garin itadai tafiso mu kasance tare. Idan ta fadi haka nima sai jikina yayi sanyi naji zuciyata ta karye mu hadu muyita kuka har sai Lamunde uwar Tani ta fatattakemu, ranar Wannan babban biki na al'ada daya zame mana idinmu mukayi kwalliya ta bam mamaki muka zauna a gda sai yamma muka nufi bakin kogi don mu ganewa idanunmu gwarzon mu muna tafe muna rera ƴan wakokin yabo ga abar dogaro domin gareta muke neman sa'ar wannan aure na ƴar'uwata Tani. Tun a hanyarmu ta zuwa naji gabana yana faɗuwa nadai dake ban faɗawa kowa ba bayan mun isa mun zauna gurin da aka tanada domin mu ina riƙe da hannun yaya Tani ina mammatsa matashi naji taja ajiyar zuciya tace “Habibah" na ɗago da sauri don tunda nake da ita bata taɓa kiran sunana ba saidai tace dani Ƙanwa. Idanunta naga yana zubar hawaye nayi saurin kai hannuna ina share mata ina girgiza mata kai ta riƙe hannu na tace “gabana yanata faɗuwa Habibah inajin kamar wani abu zai faru a gurin nan saboda jiya Liti ya rako Jamilu wannan ɗan birnin shine Jamilu yake cemin bai iya su ba domin bai gada ba kuma har yanzu yananan akan bakansa na aurena babu ruwansa da kafirci na indai zan aureshi domin shima ba ibadar ya damu da itaba, yace naje na faɗawa su Baba Uda kada su bari a fara wasan nan tun a daren jiya su ɗaura mana aure idan kuwa sukaƙi to shakka babu zaiyi kiran abokansa ƴan daba na Birni su ƙaddamar min ya rantse da Allansu abin dogaronsu indai ba'a bashi niba saiya barwa Tsaunin gawo tabon da har abada bazai goge ba" Sosai kalaman sun girgiza duniyata amma saboda son kwantar mata da hankali sai nace “kayya yaya Tani kinada sanya abu a ranki kada kibar wannan soki burutsun haukan nasa ya dameki babu abinda ya isa yayi Saida sahalewar abar dogaro kuma inada yaƙinin bazata wulaƙantamu ba" Numfasawa tayi ta girgiza kanta tace “Hakane amma fa nikam na tsorata" da haka na rinƙa kwantar mata da hankali har zuwa wani lkc da aka buga tambarin nasara guri ya bushe da iface iface da kaɗe kaɗe da bushe bushe. Kwatsam saijin ihun mutane muka rinƙayi ƙura ta tashi muna ganin yanda mutane suke runtumawa da gudu su kuma makasan suna ihu suna ina Amaryar yau sai sun kasheta... Ai bangama jin hakan ba na mike na kama hannun yaya Tani itama ta rikeni muka runtuma da gudu muka nitsa cikin daji ashe dama Mun san abinda muka tunkara da munyi tsaiwarmu a can kilan abar dogaro ta bamu kariya. Muna gudu muna haki duk mun sassoke da kaya jikinmu ya kakkarce muka iso wata sarƙaƙiyar duhuwa muka tsaya muna mayar da numfashi, can mukaji motsi ta bayanmu yaya Tani ta rikoni don na sake ta na nufi wata magudanar ruwa zan ɗebo mata kasancewar nasan bata jurewa ƙishirwa, naji tace “Habibah da mutum anan mu gudu...." Bata ƙarasa ba suka bazar da ita a gurin ta saki ƙara nima na saki Jami ya diro daga kan wata itaceyar mangwaro muna ganinsa muka zaro idanu Tani harda ajiyar zuciya tayi tunanin me cetonmu ne nayi saurin kwacewa daga hannun wanda ya riƙeni na nufesa ina sauke numfashi nace “Yawwa Jami kayi mana rai kada su kashemu mun......" Wata mahangurɓa ya sakarmin a baki yace “Shegiya kin ɗauka cetonku nazo kafiran banza kafiran wofi uwarme zan ceta a icen jahannama kalidina fiha abada Nima rabona nazo ɗiba na rama cin amanar da kuka yimin kuma agabanki zanyi komai kije ki faɗawa manyan kafiran nine Jamilun Alh Kabirun Auta muga wanda karansa yakai tsaikon da zaija damu a fadin ƙauyen nan...." Yana faɗin haka ya dakawa wasu samari uku tsawa yace me kuke jirane kuyi aikinku" kafin na Ankara sun kamani sun ɗaure sun sanya wani tsumma sun rufemin baki sun watsar dani a karkashin bishiyar kusa da yaya Tani. Yaya Tani ta fara yunkurin tashi Jami yasa ƙafarsa ya taka ƙirjinta ta saki wata kara da nima bansan sanda na saki ba duk da bakina a daure yake don nasan ta azaba ce" Zamewa tayi ƙasa daga kan icen ta rushe da kuka shima ya sauko idanunsa sun kaɗa sunyi jawur jikinsa har rawa yakeyi yakai hannu zai taɓata sai kuma ya tuna ya janye yace “So....sorry please inajinki Habibah kinga dare ya fara" ɗagowa tayi ta sanya hannu ta riƙo hannunsa tace “A gabana akan idanuna ɗan birni suka ketawa yar'uwata haddi suka keta alfarmarta sukayi mata kaca² su biyar ƙarata akanta ita kaɗai tana kuka tana Nishi tana gunjin azaba amma roƙonsu takeyi kada su taɓani kada su cutar dani, nima kuka nakeyi inata kokarin kwance kaina amma na kasa Saida suka gama abinda zasuyi lkcn ta gama galabaita sannan suka kwanceni na angajesu da ƙarfin da bansan ina dashi ba na isa gareta ina kiran sunanta ina jijjigata suka tsallake mu sukayi tafiyarsu sunata ƙyaƙyala mana dariya. Na jima ina jijjigata sannan dabara ta fadomin na cire kallabina na nufi wannan gulbin dana nufa dazu na jikoshi nazo ina danna mata a jikinta sai kuwa taja ajiyar zuciya ta fara buɗe idanunta daidai lokacin da samarin garinmu suka shigo jejin suna nemanmu ashe wani manomi yaga duk abinda ya faru ya bazama gdan sarki ya faɗa, hannunta ta ɗaga ta kamo nawa ta ɗora a saman ƙirjinta

Chapter 2 of 6