An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[3/26, 10:21 AM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
*Sadaukarwa ga Ahlina*
Hon- Tasiu Umar Munture (My mahaifi😘)
Haj Mariya Tasiu Umar (Kaunata uwa ta gari😍)
Aunty Khadija Tasiu Umar Dije (My yayas🥰)
Mahraz Tasiu Umar (Dan kanina)
Sailuba Tasiu Umar
Ibrahim Tasiu Umar
Halima Tasiu Umar
Hauwa'u Tasiu Umar
Safwan Tasiu Umar (Autan Ummuh)
Allah ya karama Mana zaman lfy da kaunar juna cikin wannan family kadan me albarka.
*Special gift to My kids*
My jinin jiki my ruwan jiki ƙalbi na.
Hairan & Affan Allah ya rayamin ku ya albarkaci rayuwarku data yaran musulmi baki ɗaya, My Affan naji kokenka insha Allahu ilahi zai amsa, yace Momynsa taƙi siyo masa ƙani sai auntyn Momy ce ta siyo masa ƙani.🤣🤣
*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.
*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.
*Gargadi*
Haramun ne wani ko wata ya canzamin littafi ta kowacce siga batare da izinina ba idan kina/kana ganin bazan iya nemoka na dauka mataki ba akwai Allah yasan duk inda ka boye a fadin duniya Kuma da sannu zai fitarmin da hakkina.
*PAGE 1*
★★★~~~★★★~~~★★★
“Bibo! Bibo!! Jummala wai ina Bibo ne nifa gsky na fara kosawa da abinda takeyi Mana Kullum zamuje gurin bauta saita makarar damu karshe ma tace bazata ba Jummah idan bazata rinka zuwa ba ta fadamin na daina wahalar da kaina"
Fitowa tayi daga dakin kasar da take ciki tace “Kincika korafi lantai Nifa bawai gurin bauta ne banson zuwa ba samarin garin nan ne suke takurani amma yau naji inason zuwa da alamun addu'a ta zata karbu gurin uwa me tsarki"
Jerawa sukayi kowacce dauke da yar salkarta ta ruwa suna tafe suna taɗinsu suna dariya, Lantai da Ladiyo da Innu sune suke ta shewarsu itakam Bibo hankalinta yabar garesu kamar yanda ta saba ji idan sun tunkaro wajen bautar yauma hakan ta rinƙa ji gabanta na faduwa zuciyarta na harbawa da ƙarfin da takasa sanin dalilinsa.
Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka dubi juna Lantai tace “Bibo yau ranar zagayowar haihuwar ki saboda haka ranar ta zama takice me daraja saboda haka kece zaki jibanci lamuranmu zuwa ga mika bukatunmu ga uwa me tsarki"
Lumshe dara²n idanunta tayi ta buɗesu tare da karyar dakai suka fara hawa saman Tsaunin gawo wanda wannan Tsaunin shine ya samar da asalin sunan wannan ɗan karamin kauye me dauke da albarkatu birjir a cikinsa kama daga ma'adanan ƙarƙashin ƙasa dake da jiɓi da manyan duwatsun da sukayiwa ƙauyen ƙawanya da kuma albarkar noma data samu tushe da tushiya tun kaka da kakanni da kuma albarkar ruwa wanda yake kewaye da manyan duwatsun da suka zagaye garin,
Wannan tasa al'ummar wannan ƙauye suke rayuwa cikin wadatar buwayi gagara misali. Al'ummar Kauyen Tsaunin gawo sun kasance Asalin Hausawa na fil azal marasa sallah wato waɗanda ake kira maguzawa, asalin kakanninsu suna rayuwa a saman wannan tsauni da ake kira Tsaunin gawo wanda ya kasance shine tushensu.
Mazansu da matansu yaransu da manyansu sun kasance suna bautawa wani dutse ne a saman wannan tsauni da suke kira Uwa me tsarki.
Shi wannan abin bauta tasu ya kasance wani mulmulallen dutsene da yake tsaye cikin hukuncin Ubangiji saman wani babban dutse kamar dai ka ajiye kwai kwaya ɗaya saman faifai.
Asali ba wannan ne yaja ra'ayinsu wa bautawa wannan dutse ba face ya kasance wannan dutse Ubangiji ya gina shi kamar ganga in ka sanya hannunka ka daki dutsen zakajishi da tauri ko kara bayayi amma idan kasami itaciya ko dutse ka buge shi dashi sai kaji yana baka wani sauti me zaƙi da daukar hankali kamar dai kana kada ganga haka zakaji sautin na tashi ya cika dukkannin dajin da wannan tsauni yake.
Ba iyanan bane abin ya tsaya a gefe da gefen wannan dutsen bauta akwai wasu dogayen massu guda biyu da suka kangeshi daga gangagewa idan iska ta busa, kuma su wadannan massu duk wata canza kala suke yi batare da kowa yasan lkc da sa'o'in da yake canzawa ba sannan ta saman su tsinin mashin kenan yana fesar da ruwa a kowanne lkc yana gangarawa kasa yana haɗewa da wani babban kogi da suke kira kogin wankin zunubi, shi wannan kogi aikinsa na zuwa ne a duk lokacin da wani ko wata ya aikata wani aiki da wannan al'umma take dauka na tur ne da Allah wadarai.
To a wannan lokacin ne za'a kama mutum a daure shi da sarkoki ajashi a ƙasa a kaishi a jefashi wannan kogi a tafi a barsa idan yayi kwanaki uku za'a dawo a dauki gawarsa to wannan shine yake nuna ya mutu salihin bawa domin sunada tabbacin uwa me tsarki ta yafe masa shiyasa ta karɓi rayuwarsa, idan kuma ba'a ga gawar mutum ba to wannan yake tabbatar da cewa wannan bai samu yafiya daga uwa me tsarki ba.
*****
Isa sukayi gaban abin bautar suka dunkule hannayensu tare da lumshe idanunsu suna karanto wasu addu'o'i da su kadai suka san meye suke cewa,
Tsayin lkc a haka sannan suka buɗe idanunsu Wacce suka kira da Bibo ta durƙushe saman gwiwowinta ta kika hannunta tafin yana kallon sama ta ɗora kanta samansa dogon gashinta ya bazo ya rufe mata fuskarta gabadaya bata damu da gyarawa ba domin tayi imanin a gaban majiɓinciyar lamuranta take,
Cikin siririyar muryarta me kama da busar sarewa tace “Mun kasance masu biyayya a gareki da gujewa saɓa Miki ya abar bauta meye yasa kullum nake kawo kukana gurinki baki sharemin hawayena Jimo Ciwake ya kasance me yawan ziyartarki da hidimtawa gareki, yau gashi can cikin halin jinya baya iya gane kowa da komi saidai ayi masa komai.
Yake wannan Uwa me tsarki idan har kin tabbata abar nufi da bukata to a matsayina na wacce bantaɓa aikata zunubi ba ina nemawa mahaifina lfy da amincewark....."
Da sauri dukkansu suka dago lkcn da ƙarar faduwar wani abu me karamin sauti ta ziyarci dodon kunnensu suka zubawa sashin da sukaji motsin idanu tare da miƙewa a tare saboda ganin baƙin halittun da suke takowa daga nesa dasu.
Turawa ne su uku sai wasu baƙin fata biyu samari, Ja suka fara yi da baya suma wadannan baki suka tsaya suna kallon kallo can Lantai tace “la ashe idan mutum yana mafarki gani shikayi uwa me tsarki jiya nayi mafarki naga fararen kwaɗi ashe turawa zan gani" yanda tayi mgnr ya Bama daya cikin bakaken fatar nishaɗi har Saida ya dara inda shi kuma dayan hankalinsa ke kan Bibo da ta sunkuyar da kanta ko dagowa batayi yana mata wani kallo na sama da ƙasa zuciyarsa na bugawa da ƙarfi hakanan yaji ruhinsa ya kwaɗaitu da son ganin fuskarta.
Ɗaya cikin turawan ne ya dubi abokan tafiyarsa yace “ ma iya tafiya ko?" Cikin harshen nasara yayi mgnr, inda wanda aka kalla ɗin yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yayi gaba, suka rufa masa baya har zuwa lkcn idanun Bibo na ƙasa Saida ta fahimci sunyi nisa sannan ta dago idanunta tabi inda suka bi da kallo karaf idanunta ya faɗa cikin na dayan cikin bakaken hakan ya haddasa masa tsayawar da bai shirya ba zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yace “Hasbinallahu wa ni'imal wakil........"
Tashin hankali wanda baasa masa rana jin kalamin wannan mutumin yasa Bibo saurin watsa sumarta baya ta zari kallabinta ta zuwa takalmanta ta nemi hanyar tsira da mugun gudu hakanan suma su Lantai suka rufa mata baya.
Sunaji wadannan baƙi na kiransu amma tsoro da tashin hankali ya hanasu juyowa saima ƙarawa gudun su ƙaimi da suke yi.
Baƙuwar kalmar tayi mugun firgita su karma Bibo Sarkin tsoro taji lbr musamman data tuna sanadin haɗa idanunsu ne yasa shi yin wannan furuci, to me yake nufi? Kodai tsorata yayi da ganin fuskarta kamar yanda da yawan mazan ƙauyensu suke faɗa? Ko kuma dai wannan kalmar ɗin waƙe ne a gareshi?
Batada amsa har suka isa cikin garin basu dakata da gudun ceton ran da suke yi ba inda suka bar waɗannan baƙi da mamaki gami da dariyar yanda suka razana da ganinsu amma banda wannan matashin mai furuci shi a bangarensa zuciyarsa ce tayi masa nauyi tsoro ya mamaye ruhinsa tunani barkatai suka cika masa kansa kardai ya tabbata duk abinda ya gani cikin mafarkinsa saiya zama gaske yayi mafarki zaije wani ƙauye na marasa addini kuma abubuwa da yawa sun faru ciki harda wannan fuskar daya gani yau a saman Tsaunin gawo wadda a lissafin falsafar mafarkinsa itace ƙaddararsa ta zuwa wannan ƙauye.......
“Meye ma'anar hakan?" Ya furta lkcn da suke isa ga dutsen da suka zo bincike akansa.... Duba na tsanaki Najeeb abokin tafiyarsa yayi masa “sauyin yanayi cikin ƙanƙanin lkc Abokina meye ne yake faruwa na lura daga kallon fuskar wannan ƴar maguzawan komanka ya canza anya ba gamo mukayi garin kurɗe kurɗenmu na masifa ba?"
Haɗiye wani ɗaci yayi a maƙwallatonsa ya furzar da iska ta bakinsa ya saita injin narkakakun idanunsa masu zubawa abin kallo kasala kan Najeeb yaja numfashi yace.
“Ba gamo mukayi ba Sarkin Gida ita ce ƙaddarata......" Da sauri ya kalleshi yace “Bamagujiyar Prince Habeeb meye haɗinka da BAMAGUJIYA da har zata zama ƙaddara?" Yarfa hannu yayi cikin halinsa na ko in kula yace “shine nima bansani ba Sarkin Gida gabana yana faduwa zan bar dajin nan na koma cikin gari kuyi duk abinda ya dace"
[3/27, 10:12 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.
*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.
*Gargadi*
Haramun ne wani ko wata ya canzamin littafi ta kowacce siga batare da izinina ba idan kina/kana ganin bazan iya nemoka na dauka mataki ba akwai Allah yasan duk inda ka boye a fadin duniya Kuma da sannu zai fitarmin da hakkina.
PAGE 2
★★★~~~★★★~~~★★★
Yanda suka shigo garin ya janyo musu kallo gurin jama'ar dake kai kawo kowa mamakin dalilin wannan gudun mara iyaka yakeyi,
Saida suka isa ƙofar gidansu Lantana sannan sukaci birki suna mayar da numfashi daƙyar suka kai ga wani kurutturen itace dake ƙofar gdan wanda da gani kasan an ajiyeshi ne don hutawa.
Sun jima suna sauke numfashi daƙyar Kande ta kawar da shirun da cewa yau naga masifa ke waɗannan bakin anya ba aljanu bane Nifa tunda nagansu gabana ya rinƙa faɗuwa" fasali Bibo ta sauke tace “wlh Nima bakiji yanda suka tsoratani ba ni saida nayi tunanin ma sace mu suka zo zasuyi...."
Kekam da daukowa mutane ɗaukakkiya Ni wannan kyakkyawan ne ya firgitani da surkullen da naji yana ambatawa
Dariya Bibo tayi tace “ke dallah ba surkulle bane addu'arsu ce ta addininsu kwanaki naji da Jimo Ciwake yayi baƙi yan burni sunayi a wannan abar da suke karawa a kunnensu...."
Mgnr ce ta tokareta a maƙoshinta lkcn da sukaga machine ya tsaya a nesa dasu kaɗan idanunta ya sauka kan wannan kyakkyawan inji Lantai da faɗa,
Sauka yayi daga babur ɗin ya zubanta idanu daga nesa yana ƙarasowa garesu sukuma suna ja baya suna ƙara matsar gdan nasu Lantai, takun maza dana mata ba ɗaya ba hakan ne yasa su cimma su juyawa Bibo tayi da sauri zata kwasa da gudu taji numfashinta ya tsaya cak ƙirjinta ya fara lugude ta ɗago da mugun sauri ta tureshi jikinta na rawar mazari ta shiga waige² kawai sai hawaye ya tsiyayo mata tayi ƙasa da sauri tace “Na shiga uku kayi hkr ka yafemin koma laifin meye nayi maka na rantse da uwa me tsarki idan Jimo Ciwake yaji hakuma tazo nemana ruwan wankin zunubi zai jefani shikenan rayuwata ta galgalce...."
Wani ihu ta saki jin ya sake sanya hannunsa ya riƙe ta sosai da sauri ya ɗauke hannunsa daya ya rufe mata baki tare da zaro mata manyan idanunsa.
Motsa bakinsa yayi kamar zaiyi mgn batasan meye ya tuna ba taga ya sake ta yayi gaba sakin baki tayi da rawar jikinta da taki barinta tasa hannu ta share hawayenta ta koma ta zauna Lantai dake laɓe ta fito dafe da ƙirji tace “Yau naga abinda yasa buzu ture naɗinsa nikam Bibo mutumin nan ba ɗan yankan kai bane kinga fah aradu irinsu ake bamu lbr suna shigowa jeji da motoci suna satar mutane suna zuwa sunayin kuɗi dasu"
Sharrrr hawaye ya sake zubowa Bibo tace “ni ba wannan bane matsala ta kinga fa har taɓamin jiki yayi nashiga ukuna ya zanyi yanzu Jimo Ciwake ina shiga zaiji warin maza a jikina....." Sai kuwa ta kuma rushewa da kuka zama Lantai tayi itama ta rushe da kuka tace “Nima na gani naji Miki wannan tsoron amma kinsan me? Tashi muje gidanmu in dafa Miki ruwa me zafi kiyi wanka bazaiji ba ai an ce ana watsa ruwa warin yake bajewa"
Wani numfashi ta sauke me nauyi ta mike suka nufi cikin gdan suka ɗebi yayi suka haɗa wuta suka dafa ruwan komai cikin gaggawa suke yinsa saboda kar Kakatu tazo ta tarar dasu,
Man gyaɗa ta shafa suka fita tanata sauke ajiyar zuciya suka isa gidansu Bibo sunata raɓe² Ɗantala ƙanin mahaifinta ya sawo kai ganinsu tsaye cirko² ya dakansu tsawa yace “durun uwarku kukeyi anan da kuka tsaya kuna tsinkawa mutane hanji” zabura sukayi Lantai ta kamo hannun ƙawar tata suka shiga gda sumsum, wuf suka faɗa ɗakin Jumme ta miƙe da sauri sukayi dako² kamar sunwa megari ƙarya da sauri Bibo tace “ba abinda kike tunani bane muna tafiya ta zame ta faɗa dagwalon kwatami shine muka biya gidanmu ta wanke jikinta" riƙe haɓa Jumme tayi tace “anya kuwa Habibah..." Nan suka kama rantse rantse da duk wani abu da zaisa a yarda dasu wannan ya kwantar mata da hankali tace.
“Ai shikenan ga abinci can na ajiye muku a madafi ki dauko muku kuci ki ɗauki kunun zaƙin kikai dandali" zama sukayi suka fara cin abincin kusan Lantai kecin abincin idan taga ta tafi tunani ta zungureta da haka suka gama sukayi kwalliyarsu anan suka dauki bahon kunun zaƙin suka fice suka nemi ɗan dako ya ɗauka.
Ko a dandalin batada wata walwala ɗan wasan da sukeyi da gaɗa duk bata da walwala kowa dake gurin ya fahimci hakan damma Lantai nata tausarta suna zaune ta rafsa uban tagumi wani almajiri ya iso ya tsaya yace “Bibo wai kizo inji Manuwa yana bakin tukuba"
Tsaki tayi ta kalleshi ta watsar Lantai tace “Kai kaje kace tana zuwa" miƙewa tayi ta zari bahon kunun zaƙinta tayi gaba tana cewa “ɗan baƙar jaraba kutumar ubansa zanyi masa ɗan Shegiyar"
Binta Lantai tayi ta riƙeta tace “bai kamata ba abinda kike yi ni banga uwar da Manuwa ya nema ya rasa ba da baki ƙaunarsa kinga fah babansa Sarkin Noma ne...."
Wani uban tsaki taja tayi gaba tana ƙara jan zaninta sama suna tafe Lantai nayi mata mitar wulaƙancin da takewa Manuwa.
Can nesa sukaga an haskesu basusan sanda suka rungume juna ba tsabar tsoro da firgici, ƙamshin daya gauraye hancinsu ne yasa su buɗe idanunsu a tare suka saukesu kan Najeeb dake tsaye a gabansu yanayi musu kallon wulaƙanta wulakantacce ya dubi Bibo yace “Meye sunanki?"
Ɗagowa tayi me arhar hawayen har idanunta ya kawo ruwa tsawa ya daka mata yace “banason ƙauyanci tambayarki nayi meye sunanki?" Cikin in...ina tace “Ha...bee...bah...." Lumshe idanu Najeeb yayi yace “Da gaske?" Kaɗa kai tayi yaja numfashi yace “ok dama Mun zo wani aiki ne nan shine ubangidana yakeson ƙulla ƙawance dake...." Zaro idanu sukayi sukace “ƙawance?" Ɗaga masu gira yayi yace “wannan shine gsky duk inda mukaje mukanyi ƙawaye Abokina kuma ubangidana baya ƙawa baitaɓa ƙawa ba amma yasoki kasance ƙawarsa kada kice a'a domin wannan abu ne da bazaki iya kaucewa faruwarsa ba".............
[3/30, 7:32 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.
*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.
*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Page 3*
★★★~~~★★★~~~★★★
Tunda ya fara mgnr suke kallonsa yana ida faɗin abinda yake faɗi ya juya yayi tafiyarsa wani kayan takaici wanda akace yana sonta da ƙawancen har yasha kwana yama riga tafintan nasa barin gurin taɓe baki tayi tayi gaba suna tafe babu me cewa wani Saida suka kusa rabuwa Lantai tace.
“Nifa lamarin ƴan birnin nan ya fara bani tsoro musamman akanki Bibo meye kuma ƙawance tsakanin namiji da mace?" Kawar dakai tayi tace “to basai yayi da gyatumarsa ba tunda shi bashi da ɗa'a aiko mahaukaci yasan wannan ba daidai bane"
Shigewa tayi gdansu Lantai ta wucce nasu gdan, tana shiga tayi watsi da komai ta shige dakinsu ta faɗa kan shimfiɗa ta kwanta tare da lumshe idanunta wannan wanne irin mutum ne? Meye yake nufi da ƙawance tsakaninsu? Tambayar data kwana da ita a ranta kenan har wayewar gari tada tashi wanke fuskarta tayi suka gaisa da uwarta ta nufi wajen gyatuminta ta ishe shi zaune yana shan kunu ta zauna suka gaisa tace “inason dama zanje gona ne" dubanta yayi duba irin na tsanaki yace “gona kuma?" Meye zakiyi a gona?" Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace “Sallau jiya yake cewa da Jumme ciyawa ta ɓata yabanyar gonarka idan ba'a cireba zatayi ɓarna wannan tasa naga ya kamata naje nagani koda abinda zan iyayi" jinjina kai yayi yace “shikenan kije Allah ya tsareki"
Ƴar ƙaramar dariya tayi ta miƙe ta fita saboda murna ko sallama batayiwa Jumme ba ta bar gidan ta nufi gonar tanata yan waƙoƙinta.
Tsakanin gonar da cikin gari akwai nisa sosai amma sabo yasa basa ganin nisan haka taci gaba da kurɗawa tayi nisa sosai daidai wata itaciya ta rinƙa jiyo ƙamshi me kwantar da zuciya tana dosarta ƙamshin na ƙaruwa harta isa jikinta, gabanta ya faɗi “Wayyoh!" Tana mgnr tana ja da baya ga mamakinta sai taga yayi murmushi ya taso daga gurin yace “kin tsorata ko?" Wata ajiyar zuciya ta saki me ƙarfi jin dirin saukar muryarsa har cikin lakarta.
Sake matsowa yayi yace “Ina zaki?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga buhun dake saɓe a kafadarta, batayi Masa gardama ba ta sakar masa ya fara dubawa yana kallonta Saida ya gama dubawa tsaf koda baisan amfanin kayan ba alama ta nuna masa gona zata hakan yasashi ɗagowa yace “gona?"
Da sauri a ƙoƙarinta na ganin ya barta ta tafi ta ɗagansa kai yaja fasali ya karyar dakai yace “zan iya rakaki inason na iya aikin gona...." Zaro idanu tayi tare da kunshe dariya ya zubanta idanu har Saida ta saita kanta yace “meye ya baki dariya?" Taɓe baki tayi tace “ba haɗi saniya da tallan kilishi" da sauri ya dawo da hankalinsa gareta yace “sabida me?" Gaba tayi taci gaba da tafiyarta tana cewa “ko cikin malalata akwai gwarzo kaikam ko riƙon lauje bazaka iyaba bare noma"
Murmushi yayi yabi bayanta yace “iya magana kamar ƴar mahauta kuma haka zaki koyamin ba"
Tsayawa tayi tare da haɗe fuska tace “Idan muka tafi gona tare zakasha wahala kuma mutanen garin mu zasuje su faɗawa Jimo Ciwake harma su ƙara da sherri ka taimakeni ka barni naje nayi abinda ya fito dani"
Fuzge buhun hannunta yayi yayi gaba batare da ya sake cewa da ita komai ba dole tasa ta rinƙa binsa da sauri tana cewa dashi “bakaji ba kagafa akwai nisa jikinka bai saba da wahala ba banaso kasha wahala....." Tsayawa yayi ta iso gareshi ya kai hannu zai riƙota tayi saurin ja baya tace “Aa haram giya a gdan Mallam kada ka kuma taɓani jiya daka taɓani Saida Jumme ta kusa ganewa da kuwa ta gane da tuni na zama tarihi don jefani za'ayi cikin ruwan wankin zunubi kuma zunubin nan bazai barni na tsira ba"
Zubanta idanu yayi yace “wanne zunubi kenan?" Taɓe baki tayi tace “ai babban zunubi ne namiji ya taɓa jikin mace a nan garin idan har hakan ta faru to duk inda tayi za'a rinka jin warin maza a jikinta kuma zaija mata ƙyama da tsangwama wannan dalilin zaisa taƙi auruwa domin babu wanda zai ɗauki karya yakai gidansa a matsayin uwar ƴaƴansa"
Murmushi Habeeb yayi yace “Al'adarku nada kyau da tsafta kamata yayi ace baku kuke da wannan tsarin ba mu musulmi mune zaifi cancanta da mu kasance a haka domin ubangijinmu ya hanemu da kusantar zina" daga wannan basu kuma mgn ba sukaci gaba da tafiya har