Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
Mamah addu'a. Yau da safe Zahrah na zaune gefen Mamah yayin da take bacci kawai taji Muryar Mamah na magana. “Tabbas na riga na cuci rayuwa ta da na gudu na bar dangi na wanda bana jin har abada zan ƙara ganin su, Alhaji Baba da kuma Hajjaty ina roƙon ku yafe min bana jin zan iso gare ku mutuwa zata riske ni.... Nan da nan jikin Mamah ya ji ƙera da zufa sai wani karkarwa take yi. Addu'a ta tofa mata nan da nan taci gaba da bacci ta. “Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari game da rayuwar Mamah na, ya Ubangiji kafi kowa sanin ɓoyayyen al'amari da kuma bayyananne, ya Rabb! Ka bawa mahaifiya ta lafiya ka kuma bani ikon haɗa ta da dangin ta” ta ƙarasa hawaye na zubowa daga idanuwan ta. Kwanci tashi asarar mai rai Mamah ta shafe wata guda tana jinyar da aka gagara gano wace iri ce, a lokacin kuma baba amarya ta fara shiga tana gaishe ta kullum. Ita dai Zahrah bata kawo komai a ranta ba don yanzu babu laifi suna gaisuwar mutunci da BABA AMARYA ɗin. Ana cikin haka result ɗin su ya fito, a ranar kuwa suka dukufa zuwa school bisa tursasawar Ammi. “Zahrah ki tashi kije ki shirya a can tare da Badi'a kuje school za'a buɗe muku result” cikin fuskar dake bayyana tsantsar damuwa tace “Ammi don Allah ki barni na zauna a nan tare da Mamah, Badi'a sai ta duba min" “Aah Zahrah tashi zaki yi ku tafi, ina nan zan kuka da mamah” Babu yadda ya iya ta wuce gidan Ammi a can suka shirya suka shiga adaidaita saboda Abba ya tafi Kaduna. Suna isa ganin classmates ɗin su Zahrah ta ɗan ware, ihun murna suka yi da suka hango Zahrah da Badi'a. Da gudu suka rungume su tamkar zasu faɗi ƙasa. Murya uncle Hashim me ta dakatar da su “Hey! Are You alright?” waskewa suka yi suka ce “yes sir” Yace “Alright You guys should FOLLOW me to the computer library so that your results will be checked” Yana tafe suna bin bayan shi har suka iso. Ɗaya bayan ɗaya ake dubawa kuma Alhamdulillah duk duk sun samu abun da ake so na tafiya senior class. Badi'a ce second to the last, Tana fitowa tayi hugging Zahrah “best frightful and colourful result” Tsalle Zahrah tayi “Alhamdulillah, bari na dubo nawa ki jira ni” Kamar yadda Badi'a ta fito da gudu haka Zahrah ta fito da gudu “Awful and marvelous result" Farin ciki tamkar su yi yaya. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣1️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Bayan an duba wa kowa PC ya haɗa musu assembly. “Good day to you all our graduating junior students, you indeed deserved to be honored because you all perform well an fantastic.” Tap tap tap sukafara tafi “The most amazing part of your success is that three students from this school were honored with money 💰.” Tap tap tap “I'll like to see Mayam Muhammad on the stage” M² ta fito a natse, “the state's board of junior secondary School examination awarded 100k to you for your wonderful performance and this school specifically honored you scholarship in to the senior class.” Nan da nan ihu ya kacame sai tafi Tap tap tap A hankali ta koma tana murmushi. “Badi'ah Kabir Umar, shi also perform wonderfully in this exams the board awarded 300k to you, congratulations Badi'a, and to you also the school management awarded a scholarship to you in to the senior class” Ihu ta ka ina da ƙyar suka yi shiru. “The champion, Zahrah Abdulkarim Kuru being the overall best student to write this JSSE in this state at large was awarded the sum total of 500k and sane, management of the school awarded a scholarship to you" Murna ta ko ina sai da PC ya tsawatar musu suka yi shiru. “Congratulations to you all, I hope you'll improve and do better next, Maryam, Badi'a, Zahrah see me in my office" Daga haka kowa ya watse yana farin ciki bayan an raba musu admission letter nasu da deadline na registration ɗin. Zahrah tafi kowa yin farin ciki ko babu komai Ubangiji ya kawo mata mafita. A office ɗin PC aka ɗauki pictures nasu aka ce su turo iyayen su gobe before a sallame su. Daga haka suka wuce. Abba, Mamah ammi duk sunyi farin ciki. Alhamdulillah jikin Mamah yayi sauƙi kwanan nan saboda amfani da magungunan ISLAMIC da take yi. Yayin da suka fara sabawa da baba amarya. Da yake babu registration bana, on their resumption day sassafe suka fice don yanzu Abba ya samar masu driver da zai ke kula da zuwan su da komawar su. Direct old ss1 suka nufa. Around 7:30 kuwa sauran students suka fara zuwa, da yawa sun dawo ammah wasu sun sauya school ne wasu kuma barin gari zasu yi. Bayan anyi assembly Uncle John who's the only Christian cikin staff ɗin su ya fara shigowa. “good morning sir” “morning, sit down” Bayan sun zauna ya fara yi musu bayani cikin harshen turanci. “Ina yi muku Barka da shiga ajin senior. Fatan zaku ƙara maida hankula ku ga karatun ku. Shi wannan aji da kuke gani na senior mataki ne daga cikin matakan rayuwa, idan kika tafka kuskure cikin sa yana iya wargaza ƙaddarar rayuwar ki. Saboda haka ku nutsu ku san MEH kuke yi” Nan ya ci gaba da bayani wanda a fakaice career guidance ya Basu. Cike da zumuɗi da farin ciki bayan ficewar Uncle John suka fara magana. Zainab Sani tace “Ni fah da kuke gani tun ba yau ba na riga na ware abun da zan karanta nan gaba. A rayuwa ta ina matuƙar ƙaunar yadda Nurses ke kula da maras lafiya. The way they show their concern, care and love to their patients drove me to like the profession” Idanuwan su suka zuba mata yayin da ta ci gaba da bayani. “kun san MEH, yadda suke salwantar da lokacin su don kula da patients, Baku gani doctors zuwa kawai suke na wani lokaci su tafi, ammah Nurses suna yin 8hrs suna kula da patients da zarar wata ta tafi wata zata zo saboda kada abar patient a haka. Da wannan profession ɗin zaki samu lada da yawa, sai ki samu aljanna sanadiyyar su” Kowa ya gamsu da bayanin Zainab. Ɗan gyara zama Zahrah tayi tace “Babban buri na a duniya bai wuce na zama cikakkiyar alƙaki wato judge mai cikakken iko ba. Ina so naga ko yaya mai laifi yake an hukunta shi. Akwai wani babban rabo a rayuwa ta da yasa nake don ganin duk mai laifi ya karɓi hukunci daidai da laifin shi.” Shiru kowa yayi yana nazarin Zahrah. Sun daɗe suna ta maganganu game da career nasu. Har lokacin tashi yayi Duk malamin da ya shigo maganar da yake yi musu kenan tare da basu shawarari kan yadda zasu yi karatun su successfully. Bayan Zahrah ta koma gida ta tarar da jikin Mamah babu daɗi. Ina banda kuka babu abun da take yi tana roƙon Ubangiji da ya bawa Mamah lafiya. “mamah tah! Ke kaɗai ke gare ni bayan Allah. Don Allah Mamah na ki tashi ko kaɗan bana son rasa ki.” Cikin bacci taji kukan Zahrah ita ma lokaci ɗaya hankalin ta ya tashi. Cikin Muryar ciwo ta kamo hannun Zahrah “Ɗiya ta! Ki sani kowanne rai sai ya ɗanɗani mutuwa, dole ko ban mutu yanzu ba zan mutu nan gaba. Addu'ar ki kawai nake buƙata Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani kuma ina da burin zuwa ga ahali na sai dai na kasa. Amma ke bazan so ki ci gaba da rayuwa tare da wannan maras imanin ba ko da kuwa bayan raina ne. Yanzu ki tashi ki shirya ki tafi islamiyya" Maganganun Mamah sunyi matuƙar tasiri a zuciyar Zahrah, gyara mata shimfiɗa tayi ta zuba abinci a plate sannan tayi feeding Mamah. Sai da ta bata ruwa ta tabbatar ya tsirga kafin ta kwantar da ita. A gaggauce ta samu ta shirya gashi lokaci ya kusa ƙurewa. Sallama tayi wa Mamah ta wuce gidan Ammi. Ammi kaɗai ta tarar a parlourn zaune tana kallo. Da sallama ta shiga sannan ta zauna jikin ƙafar Ammin. Cikin Muryar ta mai sanyi tace “Ammi ina yini” Murmushi Ammi tayi tana yabawa da nutsuwa irin ta Zahrah wacce lokaci ɗaya ta zo ba tare da tsammani ba tamkar wahayi. “lafiya lau zahran Mamah, ya jikin mamah” “da sauƙi” “toh Allah ya ƙara sauƙi, Badi'a Badi'a ki fito manah tun ɗazu Zahrah ke famar jiranki” Daga room ɗin ta ta ce “sorry zahrahty gani nan zuwa” Bayan Badi'a ta zo suka wuce islamiyya. Yau gabaɗaya Ustaz ya kasa fahimtar Zahrah, fuskar ta ɗauke take da zunzurutun damuwa. Zuwan ma kawai tayi ne ba wai ɗin taso ba. Gani take kamar ina ta bar Mamah mutuwa zata zo ta ɗauke ta. “Zahrah! Zahrah!! Zahrah” bakin shi uku ammah bata amsa ba. Babu alamun ma ta san MEH ake ko a Ina take. Badi'a na taɓa ta ta zabura sai wani zare ido take yi. “zahrah baki da lafiya ne yau gabaɗaya hankalin ki baya kan aji. Baki na yafi uku ammah baki san ina yi ba" Cike da basarwa ta ce “lafiya ƙalau Ustaz kawai tunani ne yayi min yawa.” “Zahrah tunani meh kike yi haka ƴar ƙarama da ke da zai sa ki shiga irin wannan yanayin?” Bata yi tsammanin jin irin wannan tambayar ba daga Ustaz shiyasa kawai tace tunani take yi. Murmushin da iyakar shi fuska ne tayi sannan tace “laaaaa Ustaz ba fah wani tunani nake yi ba kawai duniyar ne ban jin daɗin ta” “toh Allah ya sauqaqa Zahrah ammah ki rage tunani” daga haka ya wuce. Badi'a dake nazartar ƙawar ta tunda suka fito daga gida gashi yanzu fararen idanuwan ta sun yi jazur da su. “Zahrah, gaba ɗaya yau tunda muka fito nake nazartar ki, anything wrong?” “just nothing” ƙura mata ido Badi'a tayi kafin tace “ƙarya kike Zahrah akwai, kawai dai ban kai matakin ki faɗa min baneh na gode” Ta faɗa cike da fushi. Kamo ta Zahrah tayi kafin tayi murmushi “yi haƙuri ƙawa tah, kin kai har kin wuce ki ji damuwa ta. Ba komai ke damu na ba in banda rashin lafiyar Mamah, yau da na dawo abun yayi worst, kin ga yadda Mamah ke shan wahala, Badi'a bazan iya jurewa ba bazan iya jurar ganin Mamah a haka ba” Ta faɗa ƙwalla na zubowa daga cikin idanun ta. Cikin sigar rarrashi Badi'a tace “Zahrah ke musulma ce kuma kinyi imani da Allah da sauran rukunai na imani?” Gyaɗa kai Zahrah tayi don kuwa maganar ma kawai tana yin ta ne ba don tana so ba. “kin sani kowanne bawa da kalar tashi ƙaddarar, khairan ta zo ko akasin haka dole ka rungume ta a matsayin ka na mai imani. Jinyar Mamah na daga cikin jarrabawar ku ke da ita, Zahrah addu'a kawai ita ce mafita, ki ƙara akan yadda kike yi nimah nan ina yi miki haka Ammi na da Abba na” Maganar Badi'a sun rage mata damuwar da take ji sosai. Murmushi Zahrah tayi ta riƙo hannun Badi'a “ƙawaye iri iri ne ammah tawa ƙawar ta musamman ce, ban san wani aiki mai kyau nayi Wa Ubangiji ba da ya azurta Ni da ke da kuma ahalin ki, duk wuya duk rintsi ina ƙaunar ki. Allah ya saka muku da alkhairi ke da Ammi da kuma Abba”. Ci gaba da tafiya suka yi hannun su riƙe da na juna kamar wanda aka yi attempting raba su. Sai da suka iso suka yi sallama kowa ta wuce gida. Tana komawa ta wanke uniform ɗin ta ta dawo gefen Mamah ta zauna. Mamah da ke bacci bata ma san Zahrah ta dawo ba. Ganin bacci take yasa zahah ɗauko Quran ɗin ta tana rerawa. Kamar daga sama taji tarin Mamah. Ajiye Quran ɗin tayi ta matso wajen ta tana shafa bayan ta. “Sannu Mamah na sannu, na kawo miki ruwa" Kai ta gyaɗa. Zahrah ta bata ruwa sannan ta ci gaba da karatun ta. Lokaci ɗaya kuma tayi shiru yayinda ta faɗa duniyar tunani. “Kawu ko sau ɗaya bai taɓa leƙowa don duba jikin mamah ba talkless of yace zai kai ta asibiti. Anya kuwa Kawu mijin Mamah ne?, Toh idan mijin ta ne ma ba na tunanin auren soyayya suka yi. Dubi rayuwa ta fah! Shin ko don Ni ƴar yarinya Mamah ta cancanci kyautatawa daga Kawu idan ma ace tayi masa wani laifi ne a da. Allah Sarki Mamah nah, in Sha Allah Ni zan zama gatan ki, zan kula dake har lokacin da zaki samu lafiya zan kuma ƙwata mana ƴancin mu da zarar na samu damar hakan. Bani da burin da ya wuce na zama cikakkiyar alƙali, Kawu sai na karɓawa mahaifiya ta haƙƙin ta daga wurin mutumin da tunda na tashi ban taɓa ganin ya yi mata alkhairi ba kullum cikin musguna mata yake. Ina son haɗuwa da ahalin Mamah sannan ina son haɗuwar ta da ahalin ta, nasan su ma zasu yi farin ciki” “nayi alƙawari Mamah nah kinda kuwa haɗa ki da ahalin ki shine abu na ƙarshe da zan yi tabbas zan so cimma shi” Ganin tunanin babu yadda zai kai ta gashi maghrib ta gabato. Tashi tayi ta matso kusan Mamah, Ɗan taɓa ta tayi a hankali, “mamah lokacin sallah yayi, bari na kawo miki baho kiyi alwalar, ina zaki iya?” Ɗaukowa baho tayi da ruwa tayi wa Mamah alwala daga nan ta sanya mata hijab a jikin ta ta juyar da ita ta fuskanci alƙibla sannan tace. “kiyi sallar mamah” duk da raɗaɗin jinya hakan bai sa ta yin farin ciki ba, wai yau Zahrah da kanta take cewa tayi sallah, Zahrah da bata don sallah a da. Alhamdulillah. Ita ma alwalar tayi tayi sallar ta ta roƙi Allah ya bawa Mamah lafiya. Sauran masa da miyar rana ta ɗauko taci bayan yaci ta ɗauko Quran ɗin ta taci gaba da koyon hadda. Haddar ta ta koya tana gamawa ta rufe Quran ɗin ta ɗanyi addu'oin ta waɗanda yawanci roƙawa mamah lafiya take wurin Ubangiji. Lokacin ishà ma da kanta ta taimaka wa Mamah tayi sannan ita ma tayi. Tana idarwa taji sallamar Ammi da kuma Badi'a,amsa musu tayi cikin sassanyar muryar ta. “Wa alykumussalam, Ammi sannu da zuwa” “yauwah sannu Zahrah” “ku zauna manah,” Zama Ammi tayi bakin bed ɗin kusa da Mamah. Cike da kulawa tace “ys jikin madinar?” “da sauƙi ammi” “Zahrahty ya jikin Mamah? Badi'a ta faɗa fuskar ta ɗauke da damuwa. “da sauƙi Alhamdulillah” “Allah ya ƙara sauƙi” “zahraj tashi ki ɗan zuba mata abincin nan ta ɗan ci ko kaɗan ne ko ta samu ƙarfin jiki” Ammi ta faɗa tana nuna mata basket ɗin da Badi'a ta ajiye gefen ta. “Ammi ai bata iya cin abincin, ɗazu ma ƙin ci tayi sai Ni na cinye shi da na dawo” ta faɗa tamkar zata yi kuka. Shikenan zubo ki miƙo Ni zan bata la'alla taci. Zahrah ta zuba abinci ta kawo kusan Ammi ta ajiye, a hankali Ammi ta ɗan taɓa mamar.. “madinah ya ƙarfin jikin?” Da ƙyar ta amsa “da sauki” “toh Allah ya ƙara sauƙi, ga abinci ki ɗan tashi ki ci ko zaki ji ƙarfin jikin ki” Ta faɗa tare da ɗago mamahn. A hankali take feeding ɗin ta, wani abun har da yunwa ta ɗan ci da ɗan yawa kafin ta janye kanta gefe alamun ta ƙoshi. Bata kwantar da ita ba sai da ta tabbatar abincin ya tsarga. A nan suka zauna har 10:00pm suka wuce. Damuwa ta taru tayi wa Zahrah yawa, da ƙyar bacci ya ɗauke ta bayan ta rufo musu ɗakin da addu'a. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣2️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Kamar daga sama ta jiyo Muryar Mamah na ƙiran sunan ta. “Zahrah, Zahrah zahrah” ta faɗa tana lalumowa ko zata ji ta. A firgice ta tashi jin kamar mafarki take. “mamah” ta matso daga da Mamah dake zaune, “kunna haske” cike da mamaki take kallon Mamah. “mamah ke kike magana haka, Alhamdulillah Alhamdulillah” Rufe mata baki tayi sannan ta fara magana ƙasa ƙasa yadda babu wadda zai ji su “ki kunna haske, zan nuna miki abu ne” Lalumowa hasken tayi ta kunna sannan ta zuba wa Mamah ido. Da ƙyar ta miƙe ta nufi wata ƴar adakar ƙarfe dake ɗakin, ɗan murɗa wasu abu dake jiki kamar zobe tayi sannan adakar ta buɗe. Wata haka da ta sha ƙura ta gani ta ɗauko sannan ta rufe adakar. A hankali take takowa dan kuwa ba wani ƙarfin jikin ta take ji ba. Zahrah da mamaki yayi kusan kashe ta ga wani tsoro da ya shige ta lokaci ɗaya. Ta ma rasa wane irin tunani zata yi. Ta tuna taji ana cewa idan mutum yan jinyar ajali toh yakan samu sauƙi daf da mutuwar shi. Saurin kawar da wannan tunani tayi jin an dafa kafaɗarta. “Zahrah!", Ta ambaci sunan cikin raunananniyar murya yayin da Zahrah ta kasa amsawa sai ma wani firgici da ya mamaye ta. “Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani, kuma bana so ki ci gaba da wannan rayuwar idan aka ce babu Ni. Ina ji a jiki na bazan yi tsawon rai ba, sai dai yanzu naji wani ƙarin guiwa na tunkarar ki da batun ahali na. Tun ba yau ba kina tunkara ta da maganar ina basarwa saboda yadda nake jin wani mololo ya tare min zuciya da zarar an yi min tambayar. Yau bana jin abun shiyasa nake don sanar da ke Ni wacece, ban ce ki ci gaba da zama cikin gidan nan ba saboda babu rayuwa mai daɗi cikin shi. Ina da rai ma baki samun kulawa daga wajen kowa sai Ni yin idan babu Ni ban san ya zaki ji ba. Ammah a matsayi na na mahaifiyar ki kuma mai ƙaunar ki,ko da bayan raina ne bazan zo ki bar cikin gidan nan ba saboda shi ɗin tamkar gidan mahaifin ki yake. Ammah idan kika ji ba zaki iya ba ko kin takura da hakan, ko kuma anci gaba da tauye hakkin ki toh ki nemi ahali na. Wannan jakar da kike gani mallaki na ne kuma ita ce motar da zata sada ki da dangi na, zan damƙa ta a hannun ki da zarar na sanar da ke labari na, kuma zan so ki adana ta kamar yadda nima na adana ta.” Ɗan dakata wa Mamah tayi da bayanin tare da ƙanƙame hannun Zahrah cikin nata yayin da hawaye ke zubowa daga cikin idanun ta, ga kuma alamun gajiyawa a tare da ita. Ganin hakan yasa Zahrah share nata hawayen. Cikin ranta kuwa tunani take “kamata yayi ace nayi farin ciki da wannan daren, kamata yayi ace naji murnar da ban taɓa ji ba a wannan daren saboda tsantsar tarihin da zai buga cikin rayuwa ta. Daren da zan samu abun da na daɗe ina fatan samu tun ina ƴar ƙarama ta, abun da tambayar da ke sa mahaifiya ta tayi fushi da ni gashi kuma zata bani shi a yau. Ammah meh yasa Ni bana jin naji wannan labari da na daɗe ina son ji?, Labarin da zai kasance makullin baƙin ciki na?” “Tabbas ina don sanin tarihin ki Mamah, ina son sani idan nace bana so toh nayi ƙarya. Ammah Mamah ba a irin wannan lokacin ba. Ina don ki sanar da Ni labarin ki ne a lokacin da in naji zanyi farin ciki, a yanzu baki da lafiya kuma bamu da kowa sai Allah, sai kuma bayin sa Ammi da Abba da ya aiko cikin rayuwar mu. Zan so ki Dakata da faɗin labarin nan zuwa wani lokaci” Itama Mamah ɓangaren ta tunani kawai take yi game da rayuwar ta, yarintar ta, tasawar ta i zuwa auren ta da masoyin ta Abdulkarim Kuru. Haihuwar ɗiyar ta Zahrah, da mutuwar ba zata da mijin ta yayi, auren ta da Kawu da kuma irin baƙar izayar da ya gasa mata ita da yarinyar ta. Shiru shiru babu wanda yayi magana cikin su, Mamah na jiran amsa daga ZAHRAH kan ta fara bata labari yayin da Zahrah ta kurma cikin duniyar tunani. Mamah da ta gaji da zama ne ta ɗan kishingiɗa, hannun ta dake cikin na Zahrah ne ya zame wannan shine dalilin farkawar su duka biyun daga duniyar da suka faɗa ta tunani. Bubbuga ƙofar da suka daɗe basu ji anyi ba ya sa suka miƙe tsaye a tare. Har Mamah ta miƙe zata buɗe ƙofar Zahrah tayi saurin dakatar da ita. “aah Mamah, na san bai wuce Kawu baneh kuma ba zaki buɗe masa ba" bata yi mamakin jin maganar Zahrah ba hakan yasa ta zauna bakin bed Babu musu. Jikin ƙafar ta Zahrah ta zauna tare da kwantar da kan ta kan cinyar Mamah. A hankali ta ɗago ta kalli idon Mamah sannan ta kawar da nata gefe. “mamah ba haka kawai yasa na tsani Kawu ba sai don rashin nuna ƙaunar shi gare ki a matsayin ki ta iyalin shi. Ba ma wannan ba tunda kika kwanta bai taɓa tako ƙafar sa don ya duba jikin ki ba balle yace yau a kai ki asibiti ko ya karɓi takardar magani yace zai siyo ba bayan kuma Ni da kaina na sanar da shi baki da lafiya.” Tabbas abun da Zahrah ta faɗa bata ga laifin ta ba ko kaɗan at least ya kamata ko sau ɗaya ace ya zo ya duba ta ɗin. Gyangyaɗin da Zahrah ta fara ne yasa Mamah cewa ta dawo su kwanta gobe da kammala maganar su. Ba musu Zahrah ta kwanta jikin Mamah nan da nan bacci mai daɗi yayi awun gaba da su. Safiya ta gari. Ba su suka tashi ba sai da gari ya fara wayewa Mamah ce ta fara tashi ɗauke da addu'ah a bakin ta. A hankali ta sauƙo ta fita, ɗan watsa ruwa tayi a jikin ta ta haɗo da alwala sannan ta yi sallah. Bayan ta isar da Sallah ta yi azkar ɗin ta. Miƙewa tayi don tashin Zahrah tayi arba da jakar nan, a kasalance ta ɗauke ta ta jefa ta cikin wardrobe ɗin kayan ta dake sama can. Bayan ta tashi Zahrah ta ɗan fara kaɗe ɗakin. Tana yin Sallah ta gaida Mamah “ina kwana mamah” “lafiya zahrah” “ya kwanan jikin?" “Alhamdulillah, yi maza ki tashi kiyi wanka kada ki makara" “toh" tace tana miƙewa, ninke sallayar tayi sannan taje tayo wanka. Uniform ɗin ta ta manta ba'a goge yake ba, a hanzarce ta shiga gidan Ammi ta goge lokacin Badi'ah ta tashi. Sanya uniform ɗin ta tayi tana gamawa Mamah ta zubo mata jallof ɗin taliyar da ta musu, ita dai Zahrah mamaki take don rabin ta da cin girkin Mamah tun kwanaki basu fi biyu ba bayan kwantar da ita da aka yi a asibiti yau kuma ta tsiro girki. Bayan ta ci abincin tana santi ta wanko hannun ta tayi brush daga nan ta zari school bag ɗin ta da kuma hijab ta zura ta fito. A bakin ƙofa suka ci karo da Badi'a ita ma ta shirya tsab” “har kin shirya kenan, bari na miƙa wa Mamah sai mu wuce" ba tare da ta amsa mata ba tayi waje. Tana miƙa wa tayi wa Mamah ya jikin ta fito, driver ne ya kai su school sai dai yau Zahrah tamkar ba ita ba, tunani ya addabe ta. Babu abun da ya tsaya mata a rai irin hirar su ta jiya tare da Mamah. Hirar da ta tsaya mata cikin zuciyar ta. “meh Mamah take nufi kenan,idan na fahimta

Chapter 6 of 11