Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
har dinner daga gidan Ammi. Sun ɗauke su tamkar jinin su hakan yasa damuwar Mamah ta ragu uwa uba yanzu babu wata alaƙa tsakanin ta da Kawu, sai ya share watanni biyu basu haɗu ba hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba lokaci ɗaya daga ita har Zahrah suka murmure jiki ya ƙara kyau. Bana amarya ma dai bata shiga sabgar su saboda bata samu damar hakan ba ammah ƙudurin ta yana nan dangane da su. Tufafi ma dai basu rasa ba saboda Abban Badi'a yana siya musu, school fees kuwa already Yaya Ishaq ya biya mata har kammala junior studies nata. Wasu lokutan in ta zauna ita kaɗai babu abun da ke faɗo mata sai yaya Ishaq wanda a halin yanzu bata san ya yake ba, ko yana lafiya ko akasin haka. Takan yi mishi fatan alkhairi domin kasancewar shi haske cikin rayuwar ta, sanadiyar shi yanzu ta samu wayewa fiye da da, addu'a kuwa kullum cikin sallolin ta bata mantawa da yaya Ishaq tare da fatan Allah ya dawo da shi lafiya. Bahaushe yace sannu sannu asarar mai rai yanzu haka Zahrah sun kammala jss 1 ɗin su, sakamako mai kyau mai haskaka wa kowa mamaki yake yadda Zahrah Kuru ta zama popular cikin school ɗin duk da cewa lokacin da tazo makarantar she's nothing but a stupid girl. An now she shines everywhere gata dai yarinya ce ammah akwai ƙwaƙwalwar manya. Hakan yasa ta samu farin jini da ɗaukaka kama daga ƴaƴan uwanta students, seniors ɗin ta, teachers na baa barsu baya ba hakan duk da taimakon uncle Hashim da kuma Aminiyar ta Badi'a. WANNAN KENAN TEAM ZAHRAH KUYI FARIN CIKI MUTUNIYAR KU TA DAGE FAH KO INA YAYA ISHAQ HAR YAU BAI NEMI CUTIEN SHI BA? HAJIYA BABS AMARYA FA TANA NAN TANA SHIRI, KO ZATA CI NASARA. KU BIYO NI TARE DA ALƘALAMI NA DON JIN YADDA ZATA KAYA. BA'A FARA WASAN BA HAR YANZU. DIAMOND LADY 💎🤟 CE (Oum Zainab) ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣9️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Yau rana ce ta musamman da aka ware a cikin makarantar ALMUNAUWARA ACADEMY kamar yadda ya kasance cikin tarihin makarantar duk shekara akan gudanar da bikin yaye ɗalibai -speech and prize giving day-. Ko ina na makarantar ya ƙawatu kasancewar makarantar ta ƴaƴan masu hannu da shuni ne. A nan aka fara gabatar da programs da ke a agenda na taron. Cikin programs ɗin akwai drama show da wasu students zasu gabatar. Drama ɗin an shirya ta ne only to motivate the students. Cikin lokaci MC ya sanar da agenda na gaba, wanda shine drama show. Wani curtain da ya kasance tamkar decoration naga an yaye. Babu abun da ya bayyana sai herarrun seats da aƙalla zasu kai 30 daga can baya. Ta gaba ɓangaren hagu akwai evidence box sai kuma ta can tsakiya kujeru biyu da kuma tables biyu. Ɗaya ɓangaren by the right hand side wasu kujeru ne dake facing waɗannan seats sai kuma can jikin bango babban table da wata lallausar kujera. Haka wajen ya tsaru, babu ɓata lokaci jama'a suka fara shigowa suna zama a waɗannan seats ɗin. Badi'a ce da kuma khalid suka shigo cikin kayan lawyers ɗauke da files a hannun su. Suna zama sai ga Umar ya shigo ya tsaya near the evidence box. Maryam kuma ta zauna a seat ɗin dake facing mutanen by the right hand side. Onportunately sai ga Zahrah well dressed in judge's dress, ga kuma wasu sanye da kayan police na biye da ita. A hankali ta ke takowa har ta iso seat ɗin da aka tanada domin ta. Kowa a lokacin ya miƙe har sai da ta zauna sannan ɗaya daga cikin police ɗin ya miƙa mata files da sauran abubuwa gaban ta. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ciro glasses 👓 ɗin ta ta sanya, nace MASHA ARRAHMAN, Files ɗin ta fara buɗe wa sannan ta umarci Muhammad da ya karanto cases da suke da shi. Cikin harshen turanci ya fara magana a nutse.. "Case na farko: Ana zargin Mallam Uba Idi da safarar ƴan mata da kuma miyagun ƙwayoyi tare da lalata wata ƴarinya da tazo Companyn shi neman aiki wacce a halin yanzu ta mutu. Case na biyu: Ɓarayi guda uku, Dauda, Muhammadu, Idris da shiga gidan wani attajiri don satar daga ƙarshe har ta kai ga kashe mutumin da ahalin sa" Daga haka ya ɗan rusuna sannan ya zauna. Zahrah da ta make ta ce “su waye lauyoyi” Badi'a ce ta fara tashi haɗe da rusunawa “Suna na Barr.. Badi'a Kabir, nice lauyan Wanda yayi ƙara” sannan ta rusuna ta zauna. Khalid ma ya miƙe “I'm Barr. Khalid Umar, I'm for defense counsel" daga haka ya rusuna. Cike da ƙwarewa suka yi zaman nan tamkar dai a court ɗin gaske suke gudanar da shari'ar sannan aka yanke wa masu laifi hukunci daidai da laifin su. Daga nan aka sauƙe curtain. Manyan baƙin mu appreciated the drama sannan sun bada kyaututtuka da dama wa waɗanda suka yi wasan, yayin da wasu suka ware kyauta ta Musamman ga Justice Zahrah Kuru wacce ta matuƙar burge mutane da damah. Haka aka ci gaba da gabatar da programs har aka kammala. Daga nan aka fara raba prizes. Zahrah ta karɓi prizes sosai ita da Badi'a. Irin prizes ɗin da ta karɓa yasa a wajen wakili Governor ya Bata kyautar garin kuɗi har 100k haka sauran jama'ah suka yi ta mata kyaututtuka na ban mamaki. Anyi taro lafiya an gama lafiya. Lokacin tashi Abba yazo ya ɗauke su sai gida. Mamah da Ammi sun yi matukar alfahari da ƴaƴan nasu ammah duk wannan sha'ani da ake yi Kawu da amarya babu wanda ya sani. Shaye shayen Kawu kuwa sai abunda ya ƙaru...dabar su ma ta dawo tamkar dai da yanzu kuwa har shiga cikin gidan suke yi saboda samun dama daga Bana amarya. Ranar Monday suka je makaranta. Principal ne ya aiko a ƙira mishi Zahrah Kuru. A tsorace ta fito daga class ɗin su ta nufi office ɗin principal da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga bayan ya bata umarnin hakan “good morning sir" “morning Zahrah, how's studies?” “Alhamdulillah sir. I was informed that u want to see me” Ba tare da ya bata amsa ba ya ɗaya phone ɗin shi ya kara a kunne, bayan few seconds aka yi picking. “Assalamu Alykum" baa jin meh ake cewa daga ɗaya ɓangaren daga bisani ya miƙa mata wayar. Ba tare da ta san wanene ba cikin Muryar ta mai daɗin sauraro tayi sallama. A lokacin kuma principal ya fita daga office ɗin. Jin Muryar cutien shi ya sake wani murmushi mai ɗan sauti “wa alykumussalam cutien yaya” Bata san lokacin da ta cilla wani ihu ba saboda farin ciki sai kuma hawaye sharrrr “aah cutien yaya kuka kike yi? Toh shikenan lemme hang off the call and I won't call again” Da sauri ta share hawayen ta kamar tana gaban shi “i'm sorry yaya Ishaq, kukan farin ciki ne, ina kwana ya karatun" “Alhamdulillah cutie, ya Mamah?” “lafiyae ta ƙalau, kusan kullum sai tayi jajen ka” “Ayyah ki gaishe ta zan aiko muku saƙo in Sha Allah” “toh Yaya mun gode, i thought har ka manta da mu" “ni ina na isa na manta da ƙanwa ta!, Rufa min asiri kullum cikin kewar ku nake" Murmushi mai ɗan sauti tayi daga ɗaya ɓangaren yace “ba wannan ba dai cutie, jiya naji abun alkhairi da kika yi, kuma na gani. Ina alfahari da ke ƙanwa ta, ki ƙara dagewa Please” “in sha Allah yaya” “shikenan sai anjima, damah I called only to complement on your performance and I'm proud of you zahrah" “thank you yayah, bye” Daga haka ƙiran ya katse. Principal ne ya shigo tare da uncle Hashim da uncle Suraj. A nan kowa ya yabe ta tare da faɗin irin alkhairin da makarantar ta samu sanadiyyar drama show ɗin su, Governor daga baya da kanshi ya aiko wa makarantar saƙo kuɗaɗe masu yawa haka manyan mutane suka bada kuɗaɗe su mah. She's totally speechless on how victorious she's, and she promised to do better than this. Daga ƙarshe yace ta turo baban ta domin karɓa mata kyaututtukan da ta samu, in ta fita ta kira mishi Badi'a. “ohk sir" daga haka ta fice zuwa class. Badi'a ma same message aka yi passing mata. Finally they decided to send Abba, don ita ko karen huka ne ya cije ta ba zata taɓa turo Kawu matsayin wani nata ba. Toh me mah ya kai ta? Mutumin da bai san ci ko shan ta ita da mahaifiyar ta ba a matsayin shi na wadda hakƙin su ke a wuyan shi, bai don ko da lafiyar su da rashin ta ba. Inaaaah ba zata taɓa ba ko da kuwa alkhairi zai wuce ta ne. Haka har lokacin tashi suka koma gida daga nan suka tafi islamiyya. Bayan sun dawo kowa ya wuce gidan su. ★★★★★★★ Tafiya suke ita da Asabe Bala'i cikin wani ƙungurmin daji wanda ke da matuƙar duhun tsiya suna tafiya suna sare ice saboda irin bishiyoyi masu canopy ɗin an ne a ciki. Sunyi tafiyar da ta kai kimanin 2hours kafin su iso wajen wani old building Wanda ke zagaye da wasu bishiyoyi masu baƙaƙen leaves. Daidai ƙofar wajen suka nufa. Tsawa aka buga musu “kai!!! ba'a shigowa nan da ƙafar damah! Ku fice” A tsorace dukan su suka juyo don irin yadda Muryar ta kasance maras daɗin sauraro da kuma mugun tsoratarwa... “zaku iya shigowa yanzu ammah kada ku kuskura ku shigo min da ƙafafun dama” A ruɗe suka shiga kamar dole. Wani irin gini ne maras kyawun fasali, jikin ginin baƙi ƙirin ga wasu ƙwari baƙaƙe dake yawo jikin ginin, duhu ne ya mamaye wajen lokacin ɗaya suka rasa inda da zasu sanya kansu yayin da suka ji wata guguwa ta tashi, rumtse idanuwan su suka yi sannan suka ji iskar ta janye su zuwa wani sashe. Lokaci ɗaya haske ya bayyana a wajen, suna buɗe idanuwan su suka gansu zube gaban wani mutum mummuna.. Idan nace muni to fah munin ya wuce misali, fuskar shi ne baƙa ƙirin ta yamutse ga uban gashin kai kamar na wata baindiya sai dai nashi babu alamun gyara, gemun shi ya kai saitin guiwar shi Tsayin sa kuwa ba'a magana haka girman jikin sa ya wuce misali. Sam ba shi da daɗin gani. Dariyar shi ce ta ƙara tsoratar da su suka fara zazzare idanuwan su kamar waɗanda suka yi wa sarki ƙarya. “Hhhhhhh.....Saudatu Kwalba tare da ƙawar ta Asabe Bala'i. Hhhhh...hhhhhhh.....barkan ku da zuwa fadar Bulebule Bokan kowa hhhhhhh....hhhhhhh....” “mun go....de...ran....ka..shi...daɗe....” Lokaci ɗaya ya haɗe fuskar shi ya fara duban su. “Kwalba kin zo akan kishiyar ki ko?" Cike da mamaki ta ɗan kalli boka Bulebule. “kin zo ne akan ta mutu ammah ba yanzu ba sai nan da shekara biyu sannan ki mallake mijin ki da kuma ƴar ɗan uwan sa zahrah” “eh haka ne ranka shi daɗe ka taimaka min” “shikenan kada ki damu" Wata ƙwarya ce ta bayyana a gaban shi, cikin ta ya fara surkulle yana furta wasu maganganu. Can ya buga kwaryar nan da nan ta ɓace “Akwai matsala! Matar nan ba zata mutu ba sai dai zanyi miki wani aiki da zata haukace, idan ta haukace ita da kanta zata fara jinya sai ta gudu ta bar gidan. Ita kuma ɗiyar ta zaki mallake ta ammah akwai babbar matsala don kuwa akwai manya manyan sheɗanu a tattare da ita wanda Ni kaina tsoron taɓo su nake. Mijin ki ki sa a ranki kin mallake shi. Hhhhh....hhhhhhh...hhhhhhh..” “yauwah ranka shi daɗe na gode sai kuma kuɗin aikin" Dariya yayi sannan yace “bulebule baya karɓar kuɗi kasafai sai dai ladan aiki da zaki bashi wanda ya kasance mai sauƙi. Zaki zauna a tare da ni na kwana biyu, zan yi amfani da ke sau biyar” Ba tare da ta damu ba tace “shikenan ranka shi daɗe na gode” “ke Asabe zaki iya tafiya ita sai nan da kwana biyu ammah in kina so zaki iya zama zan baki ɗaki kema anan” “shikenan ranka shi daɗe zan kwana a nan ɗin” (Authubillah!!! Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace :duk wanda yake wurin ɗan duba, ko kuma boka, kuma ya aminta da abun da ɗan duban ya faɗa masa toh haƙiƙa ya kauracewa abun da aka sauƙin min” Mata muji tsoron Allah mu sani mutuwa tana nan tana jiran mu, MEH yasa in muna da bukata bazamu riƙa wurin Allah ba? Shi fah in ka roƙe shi zai amsa maka kuma baya gori dan ya baki. Saboda haka ki kiyaye in son mallake mijin ki toh ki kyautata masa da haka zaki sace zuciyar sa kai har ma da ta dangin sa matsawar kina kyautata musu. Allah ya tsare). ★★★★★★★ Abba da kan shi ya amso musu kyaututtukan su. Cike da farin ciki ya dawo yana nunawa Ammi. Sunyi farin ciki da nasarar yaran musamman Zahrah da ta kasance babu mai tsaya mata damah. Sai da yammah dab da dawowar su daga islamiyya suka wuce zuwa gidan Mamah. Tabarma ta shimfiɗa musu “sannun ku da zuwa maraba lale” “sannun mu Maman zahrah” Bayan sun zauna ta ɗebo musu ruwa. Ba tare da nuna ƙyama ba Ammi ta kurɓi ruwan. “ina wunin ku ina gajiya” “lafiya ƙalau Maman Zahrah" “ya hidima kumah, Allah dai ya saka muku da alkhairi Abban Badi'a" “amin babu komai Maman Zahrah ai yiwa kai ne," Murmushi mamah tayi. Abba ya gyara murya sannan ya fara magana “toh kamar dai yadda kika ganmu a nan mun zo ne don taya ki murna bisa nasarar da Zahrah ke samu a makarantar su ta boko. Shekaranjiya anyi tarin yaye ɗalibai a makarantar tasu, toh a nan ta samu kyaututtuka da dama, akwai kuɗaɗen ta kimanin Naira Dubu ɗari biyu (200k) Wanda ta samu daga wurin manyan mutane a faɗin jahar da kuma wajen ta. Saboda haka ne ma na amso musu saƙon ita da ƴar waje na Badi'a.” Cike da farin ciki Mamah tace “madallah Allah ya saka da alkhairi Allah yasa mai amfani ne” Ammi ta amsa da “Ameen” “toh saboda haka ne nake ganin MEH zai hana kije ki buɗe account sai a zuba miki kuɗin a ciki” girgiza kai mama tayi “Aah Abban Badi'a ba za'a yi haka ba, kawai ka riƙe kuɗin a wajen ka ina ga zaifi. Idan a waje na ne zai iya salwanta a banza ammah idan a wajen ka ɗin ne kamar zai fi. In yaso in an tashi amfani da shi sai ayi nan gaba" Abba bai Musa da shawarar Mamah ba haka Ammi. Girman ta kuwa a idon su ya ƙara ƙaruwa. Daga nan suka yi sallama suka wuce gida. TOH GA FA BABA AMARYA DA KUMA TUGGUN TA GA MAMAH DA ƊIYAR TA GA KUMA YA ISHAQ SHIMA ASHE YANA NAN. KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY DON JIN YADDA ZATA KAYA COMMENTS DIN KU KAWAI NAKE SO SABODA SHINE ƙWARIN GUIWA TA. DIAMOND LADY CE 💎🤟 Oum Zainab. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣0️⃣ Bazan manta da ku ba ƴan uwa na kuma rabin jiki na Aminatouh Adamu Hassan (Dr. Meenal) Sa'adatu Adamu Hassan (Shaheedah) A'ishah Saleh Uthman da kuma Safiyya Saleh Uthman (Autar Umma) SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau daɗi gobe akasin haka. Tun ranar da BABA AMARYA ta dawo daga wurin boka Bulebule komai ya sauya a gidan nan. Cikin sati guda ta fara shimfiɗawa Kawu sarautar mulkin ta a gidan, tana cewa abu har rawar ƙafa yake don yayi mata. Wannan shine mafarin zancen. Zaune take akan taburmar da ta shimfiɗa yayin da Kawu ke mata tausa a tsakar gidan. “mai gida tashi ka ɗaura mana sanwar nan manah don Ni na riga da na gaji” Da sauri ya miƙe kamar mai cika umarnin mahaifiyar sa ya fara haɗa ice cikin murhu. Ba don komai ta sashi ba sai don kawai haka tayi ra'ayi. Da ƙyar wutar nan ta kama ammah haka tace ya daure yayi musu girkin nan. Tun bai wuce 11:20am aka fara girkin ba har 1:00pm da ɗori ba a saka shinkafa ba. Lokacin da Zahrah ta dawo daga school tayi arba da Kawu na girki. Shewa ta buga sannan tayi hanyar ɗakin Mamah tana dariya. Batayi tsammani ba sai jin Muryar shi tayi yana ƙwalla mata ƙira.. “Zahra'u zahrah'u”.....babu alamun zata tsaya ballantana na ta amsa ta wuce ciki abun ta. Kamar yayi kuka haka ya tasa tukunya da murhu a gaba, gashi babu yadda ya iya tunda gimbiya ce ta bashi girkin. Ana cikin haka Badi'a tayi sallama da basket ɗin abinci a hannun ta, a hanzarce ya miƙa ya zo gaban ta yana miƙa mata hannu. “ɗan matsa zan wuce” “kawo na shiga da shi” da ƙyar Badi'a ta danne dariyar da ta kama ta sannan tace “gyara na wuce ko sai na yi wa bodyguards ɗina magana” kasancewar bai san ta ba kuma yaga ƴar gayu yasa yayi tunanin da gaske ne. Direct ɗakin Mamah ta miƙa abincin sannan ta fita. Kawu da ya gama galabaita ga rana, ga zafi ga hayaƙi in Banda zufa babu abun da ke ketowa daga jikin shi. Bana amarya kuwa ta tsare ina bai dafa ba ko ta dafa ba zai ci ba don ba bashi zata yi ba. “kiyi haƙuri kizo ki amshi girkin nan, Ni babu abunda zan iya wallahi yanzu haka na wahala” Hararar shi tayi ta gatsina hanci tukun tace “ita waccar ta ɗakin uban meh take yi a gidan da bazara dafa ba, maza je ka taso ta” Zungui zungui babu kunya ya ja ƙaton kanshi zuwa ɗakin Mamah. Lokacin kuwa sun zuba fried rice da kuma papper meat da aka kawo daga gidan Ammi suna ci. Yawun Kawu duk ya tsinke ammah ya dake. “madina ki fito in ji amarya kiyi girki” Idan gini na magana toh, Mamah ko kallon shi bata yi ba gashi yanzu duk jin zuciyar sa yake yi a mace ba zai ma iya dukan ta ba. Ya fi 10minutes yana jira ko zata fito ammah shiru, hakan yasa ya ja dogon kafar shi ya koma wajen bana amarya. Marairaice mata fuska yayi “don Allah gimbiya kiyi haƙuri ki zo ki ƙarasa, gaba ɗaya sun ƙi kula Ni su ma. (Nace ah su Kawu anyi luƙus kenan” Harara ta ƙara banka mishi “toh ita ɗin uwar ka ce da ba zaka ce ta fito ba, koma kace ta fito” haka ya ƙara komawa kamar ɗan ta. “tace wai ki fito" banza Mamah ta ƙara yi mishi. Babu yadda ya iya ya ƙara dawowa. Wasa wasa abinci har 3:00pm ba'a zuba shinkafa ba. Da ya gaji kawai ya fice shagon gyaran babur da yake ya zauna Allah ya taimake shi wani ya kawo gyara sannan ya samu ya ci abinci. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, duk shekara sai lashe kyaututtuka masu yawa daga makaranta da kuma wajen makaranta. Yanzu har su Zahrah suka shiga aji uku (jss 3) kwacakwam hankalin su ya koma kan karatun su, gashi Badi'a na shirin yin sauƙa saboda damah can tayi wa Zahrah nisa. An samu sauyi cikin gidan Kawu sosai don kuwa yanzu Kawu ya zama dolo, babu abun da ya isa yayi sai da umarnin baba amarya. Ya bi ya rame har abun tausayi ammah hakan bai taɓa zuciyar Zahrah ba. Yaya Ishaq har yau shiru babu shi, sai dai wasu lokutan ya kan kira wani staff ya haɗa shi da Zahrah. Su Zahrah an girma,duk ƙiriniya irin ta Zahrah yanzu babu, ko dan ance zama da maɗaukin kanwa wai shi ke kawo farin Kai. Toh Zahrah ma dai ta sauya. Ga wani irin kyau da take yi yanzu wanda ake kira da ƙyalƙyalin ƴan matanci....ta ko ina Zahrah batada makusa. Idan kyan fuska ne toh Zahrah ƙarshe ce, kana ganin ta kaga fuskar Mamah kamar anyi copy sai dai Mamah da yake wahala ta dafar da ita yasa Zahrah ta fita haske sosai. Uwa uba wani rashin don magana da Zahrah ta ɗauko abun mamaki idan har kaga tana magana toh an taɓo ta ne. Hakan ba ƙaramin ƙara mata kwarjini a idon ƙawayen ta yayi ba don kuwa kowa shakkar ta yake. Zahrah ce zaune a class yayin da mates ɗin ta suka kewaye ta tana kwatanta musu yadda ake solving wani equation a maths, da ƙyar suka samu suka fitar da amsar. Bayan sun gama ne ta ci gaba da koya musu sauran abubuwan da suka kamata. Aikin su kenan kullum a school yanzu idan sun je saboda an ma daina shiga clsss ɗin su. A lokacin exams kuwa Zahra ta nutsu ta rubuta abun ta. Bayan an kammala aka sallame su har sai result ya fito za'a neme su don yin registration na senior class, ranar sunyi kuka iya kuka saboda wasu ba a nan zasu ci gaba da karatu ba. Zahrah na ɗaya daga cikin waɗanda suka cire tsammanin dawowa ALMUNAUWARA don ci gaba da karatu duba da sponsor nata baya nan kuma babu alamun zai dawo, kuɗin kuma yafi ƙarfin mahaifiyar ta. “Dole zan koma government school ne na sani ammah Alhamdulillah for these three good years I've learned a lot” Da haka ta lallaɓa zuciyar ta tare da fauwalsws Ubangiji komai. Yanzu iya islamiyya suke zuwa. Zahrah ta maida hankalinta sosai kan karatun addinin ta, wanda ya kawo sauyi mai kyau cikin rayuwar ta. Rayuwar ta haskaka sosai, a da Zahrah bata iya riƙe bakin ta duk maganar da ta zo mata ko a waye kwaɓa mata take yi ammah yanzu Alhamdulillah an samu great improvement don kuwa a rana maganganun Zahrah ƙirgaggu ne, sanadiyyar islamiyya yanzu Kawu yana cin arziƙin gaisuwa daga gare ta, haka baba amarya ma idan ta ganta takan gaishe ta. Sana'ar Mamah ta ja baya sakamakon jinya da take yawan yi yanzu sauƙin ta ma suna samun abinci ko da yaushe ga kuma kyakkyawar kulawa daga sabon ahalin su. Jinya abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, an je asibiti abu yaƙi yiwuwa. Duk san ɗin da za'a yi sai ya nuna normal hankalin Zahrah duk ya tashi. Damuwa ce fal a ranta ga wata dama da ta fara yi. Fahimtar haka da Ammi tayi yasa ta yanke wata shawara ita da mai gidan ta. “Ni wallahi Abban Badi'a abun ya ɗaure mun kai, mutum mai lafiya lokaci ɗaya sai jinya, duk da cewa ba abun mamaki baneh kaɗan daga hikimar Ubangiji ammah jinyar Maman Zahrah akwai sa hannu astaghfirullah, a ce duk wani investigation da aka yi sai ya nuna normal bayan kuma gata nan tana jin jiki” “ni kaina nayi tunanin hakan, ita wannan mata gaskiya tana ganin jarrabawar rayuwa, kiga fa mijin ko sau ɗaya ban taɓa ganin an zo da shi ba” “wallahi kuwa Ni haushi yake bani daga shi har amaryar tasa mai zubin karuwai. Wallahi haƙƙin Madina da ɗiyarta kaɗai ya ishe shi, da sannu zai fahimci hakan tun anan duniya. “Allah zai saka musu kam” “Ammah Ni ina da wata shawara fah, ko za'a gwada ISLAMIC medicine me?" “shawara Mai kyau sai mu gwada ai.” Tun da aka fara ISLAMIC medicine ta ɗan fara samun sauƙi, sai dai yanzu ta fara wasu irin surutai musamman ina tana bacci. Wani lokacin Zahrah sai dai ta zauna tayi ta sharar kukan ta daga ƙarshe ta ɗaura da yiwa

Chapter 5 of 11