ta ta karye, tunanin when last tashiga mota take yi tun ranar da aka kawo ta gidan masoyin ta Abdulkarim Kuru. Lokacin da ta cire tsammanin wahala a rayuwar ta sai gashi yanzu ɗan uwan masoyin ta na gasa mata aya a hannu.
Suna isowa Lauwali ya ciro kayan ya shigar da su gida, abun mamaki lokacin dabar su Kawu babu kowa sai Aminu Aljan. Basu mishi magana ba suka kutsa cikin gidan. Bayan sun ajiye komai Mamah ta shimfiɗa wa yaya Ishaq sallaya ya zauna sannan ita ma taje tayi sallah.
Mutuniyar kuwa kwantawa taje tayi.
Har Mamah ta idar da Sallah bata ga giftawar Zahrah ba yasa ta ƙwala mata kira
“zahrah, Zahrah fito ki je ki siyo wa Ishaq ruwa gidan su Badi'ah.”
Zahrah da bacci ya ɗan fara kwashe ta ta turo baki gaba sannan ta fito. Mamah sake baki tayi tana kallon ta ganin ko Sallah bata yi ba. Harara ta ɗan yi mata sannan tace
“wuce kije kiyi sallah”
Juyawa Zahrah tayi tana ɓata fuska kamar wainar fulawa sannan taje tayi alwala don yin Sallah. Lauwali kuwa ya gama wanke kayayyakin kamar yadda ya saba yayi ma Mamah sai da safe. Yaya Ishaq ne ya ƙira shi bayan yazo ya zaro 5k a aljihun shi ya bashi.
Godia sosai Lauwali yayi sannan ya wuce.
Zahrah na idar da Sallah ta fito, gefen yaya Ishaq ta zauna sai wani tura baki gaba take yi kamar wani pipe😄.
Harara Mamah ta maka mata kafin ta ce
“tashi kije gidan su Badi'a ki siyo masa ruwa da lemo.. ba musu ta miƙe duk da cewa bata don zuwa gidan.
Badi'a Sa'ar ta ce ammah basa shiri ko kaɗan saboda yadda suke treating nata. Gaba ɗaya unguwar babu wanda ke kyautata musu inda ka cire gidan Cancellor sai kuma Ammin Badi'a, ita dai bata tsangwamar su ammah bata shiga sabgar su.
Bayan ta siyo ta kawo gaban shi ta ajiye, Mamah ta zubo mishi Masar a plate sannan ya fara ci ba tare da jin ƙyamar su ba. Ita ma Mamah tace tare da Zahrah.
Bayan sun gama ci yaya Ishaq ya sanar da Mamah ƙudurin shi na maida Zahrah private school da ke kusa da su. Mamah tayi farin ciki sosai har da kukan ta zai aikin godiya take rabza wa Ishaq, shi kuwa duk kunya ta cika shi.
Da haka yayi musu sallama ya wuce zuwa gida zuciyar shi wasai.
★★★★★
Sai wajen ƙarfe sha biyu na dare (12:00pm) Kawu ya dawo, su kuwa lokacin sun riga da sun rufe gidan. Bugawa yake ta yi babu ƙaƙƙautawa sai kututtuma ashar yake yi.
Sama sama mamah ta jiyo ƙarar buga ƙofa,, a zabure ta miƙe zuwa hanyar waje.
“dan abu ta kazar ubanki ki kizo ki buɗe min ƙofar nan inda ba haka ba in na shigo sai na lahira ya fiki jin daɗi.
Jinjina kan ta tayi kafin taa nufi ƙofar. Tana buɗe ƙofar ko ya banko ta har sai da ta buge kan Mamah. Layi ya shigo yana yi alamun yayi mankas abun shi.
Mamah kuwa cikin zuciyar ta tana Allah wadaran wannan miji nata.
Ƙunshi ledar hannun shi ya ya ƙara ƙanƙamewa kamar za'a ƙwace mishi daga hannun shi. A haka ya nufi ɗakin shi cikin tangaɗi har ya isa bakin ƙofa.. juyowa yayi ya kalli Mamah before ya shige ya na banko ƙofar.
Hawayen da ke zuba kan fuskar ta ta gode haɗi da wucewa nata ɗakin. Ba ita ta ta kwanta ba sai da ta yi alwala ta fara jera nafila tana roƙon Ubangiji ya kawo mata ɗauki.
_______________**********_______________
Ina kuke bayin Allah masu buƙata! Ina waɗanda ke cikin damuwa, ina waɗanda suke buƙatar neman wani zaɓi wurin Ubangiji.
Toh ga damah nan wacce take guarantee.
Manzon ALLAH صلي الله عليه وسلم yana cewa:- “idan dare ya wuce tsakiya ALLAH ( Subhanahu wata'ala ) yana sauƙowa zuwa saman duniya sai ya ringa cewa:- ( shin akwai mai neman gafara a gafarta masa ? ) yana ta fadar hakan har zuwa ketowar alfijir.
( saheeh musleem )
Saboda haka duk wata damuwa da kike da ita, don't hesitate to ask Allah, baya gajiya da amsa buƙatun bayin sa. Ki tashi kiyi sallah, koda raka'āt biyu ne sun wadatar ki roƙi Ubangiji kina mai yaƙini da shi, sai kiga ya amsa miki.
Kina cikin damuwa? Matsalar gidan aure ko kuma jarrabawar rayuwa, toh kada ki kuskura ki cire yaƙini a addu'a.
YA hayyu~ya~Qayyum!! Kayi gafara agaremu da iyayanmu da 'yan uwanmu da masoyan mu da sauran al'ummar musulmai.
KO YA ZATA KAYA?
WANE NE KAWU?ME ALAKAR SHI DA ZAHRA?, MEH YASA YAKE CUTAR DA ITA?
YA KUKE TUNANIN ZATA KAYA IDAN KAWU YA FAHIMCI CEWA WANI NA ƘOƘARIN TAIMAKAWA MAMAH?
AMSOSHIN KU NA NAN TAFe, BA A FARA LABARIN BA HAR SAI MUN JE BABBAN GIDA.
KU CI GABA DA KASANCE WA DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY DOMIN NISHAƊANTUWA DA KUMA ILIMANTUWA.
COMMENTS ƊIN KU KAWAI NAKE SO DON SHINE ƙWARIN GUIWA TA
ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎🤟
Oum Zainab ce!
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙱 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣3️⃣
Shafin ku ne ƙawaye na
ZAINAB SHEHU UMAR ( ZEELY)
SA'ADATU LAMARA ZULKHAIRAT (Matar mijinta)
RABI'ATU ABDULLAHI HASSAN (matar Ɗan jagade)
FATIMA AHMAD ABDULLAHI (Fatima anatomy)
Ina ƙaunar ku saboda Allah
Barkan ku da Sallah
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Sassafiya Mamah ta tashi da aikace-aikacen gida. Sai around 8:00am Zahrah ta fito tana miƙa
“oooooooooooh”
Mamah ce ta kalle ta sannan ta kawar da kai. Wurin Mamah ta taho
“ina kwana Mamah"
“lafiya ƙalau Zahrah kije kiyi wanka sai ki siyo manah ƙosai da koko gidan Mati."
Da “toh Zahrah ta amsa tana wucewa banɗaki. Bucket ta cika da ruwa sannan ta shiga toilet ɗin. Wanka tayi ta fito. Rigar ta ƴan kanti wacce ta ɗan ji jiki ta saka kafin ta shafa mai. Tana gamawa ta janyo hijabin ta da saman shi ya ɗan koɗe saboda dukan rana.
Fitowa tayi ta cewa Mamah
“kawo kuɗin”
miƙa mata 500Naira tayi sannan tace
“ki siyo bread 🍞 Babba guda ɗaya da canjin.
“toh"
Daga haka ta fita zuwa gidan Mati da ke kan kwanar layin su.
Tana fita ƙofar gidan su nan a cike kamar wadda za'a yi taro sun cika rumfar wasu kuma har da kan dandamalin da ke jikin gidan sai ihu suke suna buga uban shewa da gani kaga tataccun ƴan iska. Kallo ɗaya tayi musu ta kau da kanta gefe haɗi da tsaki.
Aljan ne ya hango ta sai wani fara washe baki
“ƴar oga! Ina zaki haka da sassafe"
Bata yi tunani da ita yake ba shi yasa ko kallo bai samu daga gare ta ba. Su kuwa sauran ƴan dabar suka saka ihu nan suka fara tsokalar Aljan.
Da ɗan gudu ta isa gidan sannan ta bada kuɗin ta haɗi da miƙa jug ɗin roba da ta zo da shi.
Ana sallamar ta ta amsa bread wajen Bala Mai shayi daga nan ta wuce gida.
Kamar dai ɗazu wurin a cike yake ammah haka ta wuce abun ta saboda gargaɗin Mamah kan kada ta kuskura ta ce zata kula wani a dabar.
A ɗakin mamah suka karya, Bayan sun karya Mamah ta ɗauƙo wasu kuɗaɗe daga aljihun doguwar rigar da ke jikin ta. Kuɗin zasu kai 15k. Da mamaki Zahrah ke kallon kuɗin, duk da bata da wayo sosai ammah ta san wannan kuɗin da yawa suke
“mamah kuɗin menene wannan?”
“yayan ki Ishaq na da kirki sosai, ya bamu ne mu ƙara a jarin masa”
Ko rufe baki Mamah bata yi ba taga ana shigowa da kayan abinci, shinkafa, taliya, macaroni, indomie da mai har da manja.
Mamaki ne a fuskar su har lokacin da aka ce
“a ina za'a ajiye su?”
Nuna musu ƙofar ɗakin ta tayi don kuwa nan ne wajen da zasu rabauta daga hannun Kawu.
Suna gama shiga da su suka fita. Mamah bata bar mamaki ba ammah tayi shiru abun ta.
Sai wajen 11:00am Kawu ya banko ƙofar ɗakin shi fuskar nan duk yawun bacci alamun ko sallar asuba bai yi ba. Wata shegiyar miƙa da yayi abun takaici Mamah dai jinjina kai tayi tana roƙon Allah ya shirya Yunusa..
Wani kallon banza ya watsowa Mamah sannan yace
“ke ɗan ubanki shine jiya kina ji ina buga gida kika ƙi buɗe min? Gidan na ubanki ne? Nace na ubanki ne gidan?”
Mamah dai bata kula shi ba ta ci gaba da yi wa Zahrah bayanin yadda zasu sauya kasuwancin nasu.
Sheƙa Kawu yayi hakan yasa ya kawo wa Mamah wani uban duka.
Caraf Zahrah ta tare ai kuwa sai a tsakiyar kanta wanda yayi sanadiyar faɗuwar ta ƙasa sumammiya. A firgice mamah ta yo kanta tana jijjiga ta ammah shiru.
Hakan bai ishi Kawu ba sai da ya ƙara kawowa Mamah wani dukan. Bata damu ba saboda hankalin ta da ya matuƙar tashi kada taje ta rasa ɗiyar ta.
Ba tare da ya damu ba ya fice zuwa dabar tasu. Wani ihu suka sa suka fara yi mishi kirari
“Takawar ka lafiya Yunusa BabanMutuwa, kayi yadda kaso da uban kowa, ita kanta mutuwar tsoron ka take, kaga sarki mai cikakken iko”
Dariya yayi jin yadda ake fasa mishi kayi nan da nan majalisa ta fara, ana shan sigari ana gulma tare da kututgumo ashar. Authubillah!
★★★★★★★★
Ta ɗauki kimanin mintuna 20 kafin Zahrah ta ja dogon numfashi wanda lokaci ɗaya ta saki wani irin ihu. Mutanen da ke waje kan su sun tsorata bare kuma Mamah dake kusa da Zahrah, wasu faratu ne zaƙo zaƙo suka fara fitowa daga hannun ta sannan ƙwayar idon ta ta juya baka ganin komai sai farin idon da ya sauya zuwa blue colour ga wani girma da jikin ta ya ƙara tamkar wata aljana da ta fito filin daga.
Mamah ko rasa yadda zata yi da ita tayi, banda ɓari babu abun da jikin ta ke yi.
Miƙewa tsaye Zahrah tayi tana nufar hanyar waje, Mamah bata yi ƙoƙarin riƙe ta ba saboda ita kanta a tsorace take.
Hakan yayi daidai da shigowar Kawu cikin gidan.
Zaro idanuwa yayi cikin kiɗima ya fara ja da baya da niyyar guduwa..
Kirif!! Ƙofa ta rufe kanta yayin da halittar dake gaban shi ta sheƙe da wata dariya maras daɗin ji.
“Hahhhhhhhhh_hhhhhhhhh_hhhhhhhhhhh” dariyar da bata tsaya ba sai bayan minti 10. Kawu kuwa duk rashin tsoro irin nashi yau yaji, ai ance faɗa da aljani ba daɗi.... gabaɗaya zufa ce ke ketowa a jikin shi, bata yi mishi komai ba kawai hannun ta ta ɗaga sama lokaci ɗaya Kawu ma ya ɗago bisa iska.
Gefe ta wulla kawu kafin ta ƙara daga shi can sama a wannan karon, wani irin jujjuya shi take wanda hannun ta ne ke famar yin wannan aiki ɗin, bugawar da tayi mishi sai da ƙasa ta jijjiga, tuni ƴan majalisa suka watse duk da basu san daga ina bane hakan.
Ko motsi Kawu baya yi hakan yasa ta busa mishi iskar bakin ta daga wurin da take.
A wahalce yaja wani dogon numfashi. Bai zata ba bai nufa ba sai ka cinnaku sun kewaye shi, cizo ta ko ina yi masa suke. Babu abinda yake banda susa da kururuwa.
Duk abinda ke faruwa Mamah ta kasa cewa komai. Sai can ta samu bakin magana
“zahrah don Allah kiyi haƙuri ki bar shi haka ai yaji jiki”
“hhhhhh_hhhhh" bayan wani lokaci tayi shiru sannan ta juyo tana fuskantar Mamah
Cikin haɗe fuska take magana
“Madina! Wannan ba Zahrah bace nice!” ta faɗa cikin Muryar ta maras daɗin saurara..
Jikin Mamah ne ya fara tsuma hakan yasa Zahrah hura wa Kawu iska, nan da nan cinnakun suka ɓace ɓat! Jikin shi kuwa duk ya kumbura, ga uban ciwon da yake masa. Banzan kallo halittar ta watsa mishi sannan tace
“Idrisu BabanMutuwa!"
A tsorace Kawu ya ɗaga sannan ya maida kan sa ƙasa
“ka saurare Ni da kyau! Ka gama naka mulkin yanzu lokaci na ne!
Ka daɗe kana cutar da mahaifiya ta da bata taɓa zaluntar ka ba!”
A lokacin mamah ta zube a ƙasa sumammiya. Duk wannan na daga cikin shirin halittar.
“Idrisu Ni na san ka! Ka cutar da rayuwar mu, baka san cewa na san kai ne ka kashe mahaifi naba koh?, Kai ne ka hana Mamah komawa ga dangin ta ta hanyar sihiri koh? Toh wallahi ka kuskura ka ƙara wani kuskure kan hakan zan tona asiri har ƙwayoyin da kake siyarwa”
Kawu dai an rasa bakin magana,kai kawai yake jijjigawa.
“magana zaka yi ba jijjiga kai kamar gwaje ba”
“eh na daina wallahi na daina”
Daga haka ta ɗaga hannun ta lokaci ɗaya shima ya tashi bata direshi ko ina ba sai cikin ɗakin sa.
Tana fitowa ta ɗaga Mamah ma ta kai ta kan katifar ta.
Daga nan ta hura mata iska ita kuma ta faɗi ƙasa kamar matacciya..
Numfashi Mamah ta sauƙe lokaci ɗaya kuma ta tuna meh yake faruwa. Tana juyo wa taga Zahrah kwance kamar gawa..
A hankali ta nufo ganin kamar bata motsi yasa Mamah saurin ɗebo ruwa a cup, addu'ah ta tofa ciki sannan ta shafa mata a fuska.
Numfashin da Zahrah ta ja yasa Mamah jin sanyi cikin ranta. A hankali ta fara buɗe idanuwan ta tana mai tuna abun da ya faru.
“Sannu Zahrah, ina ne yake miki ciwo?” ta faɗa a kiɗimce
“mamah kai na”
“sannu yi haƙuri bari na je na siyo miki magani, ki jira Ni kada ki fita kinji..”
Hijabin ta ta janyo ta fito, karo suka ci da ya Ishaq ƙofar gida ba tare da yan shi bane ta gota zata wuce. Cike da mamaki yace
“mamah meh ke faruwa?” sai a lokacin Mamah ta ɗago
“zan siyo paracetamol me a nan chemist zahrah ce ba lafiya.”
“subhanallah, toh ki koma ciki bari na shigo Mu kai ta asibiti.”
Da kan shi ya ɗauko Zahrah ya saka ta a mota. Babu ƙaƙƙautawa suka isa asibiti. A&E (Accident and Emergency) aka nufa da Zahrah.
Taimakon da ta samu daga wurin likitoci yasa ta ɗan ware.
Sai wajen 5:00pm aka sallame su ammah kafin nan Doctor ya nemi magana da namijin saboda matar kam duk a ruɗe take.
Bayan sun shiga office ɗin doctor, a hankali doctor ɗin ya kalli yaya Ishaq
“bawan Allah garin ya kuka bar ƙanwar taka damuwa ta mata yawa, yarinya ƙarama a ce BP nata na elevating haka tun yazo, gaskiya da matsala ko ma meh take so ya kamata Ku bata”
A sanyaye yaya Ishaq yace “in sha Allah doctor za'a kiyaye”
Daga haka ya fito.
Da kanshi ya ƙara ɗaukan Zahrah suka nufi mota har suka isa babu wanda yayi magana. Bayan sun isa Mamah da kanta ta wanki Zahrah da ruwa mai zafi sannan ta haɗa mata tea Mai kauri da sauran kayayyakin da Ishaq ya siyo musu.
Bayan sallar maghrib yaya Ishaq ya fita sallah sannan Mamah ma tayi. Kallon Zahrah tayi tace “zaki iya sallar?" Kai ta gyada a hankali Mamah ta taimaka mata tayi alwala a zaune sannan tayi sallar ma a zaune.
Bayan yaya Ishaq ya dawo Mamah ta shiga kitchen don girka abinci, ya rage iya yaya Ishaq ne da Zahrah. Kallon ta yayi yace
“cutie, meh ke damun ki haka kike sa damuwa a ranki”
“babu komai yaya Ishaq, meh ka gani?”
Wani kallo ya watsa mata
“baki yadda Ni ɗan uwan ki baneh da ba zaki iya sharing damuwar ki da Ni ba ko?”
Jijjiga kai tayi tace
“aah yaya babu komai fah, Ni mah ban San meh ya same Ni ba kawai dai Kawu ya zo dukan Mamah shine na tare, daga nan ban san ina nake ba”.
Shiru yayi yana nazarin wannan kawun da take faɗa, yana don ganin shi gaskiya.
“shikenan cutie, ki huta kafin Mamah ta gama girki”
Bayan sun ci dinner tukun na Yaya Ishaq ya tafi.
TOH FAH, YA RAI ZA'A KAYA, YAU KAWU ANJI JIKI WURIN ALJANU
KO kAWU ZAI SAUYA HALI?
Duk cikin babban gida.
BA'A FARA WASAN BA, JUST FOLLOW MY INK
THE DIAMOND BHATOOL💎🤟
LIKE AND SHARE
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡BABBAN GIDA🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕽0️⃣ 4️⃣
Ina matuƙar godiya masoya na! Wannan PAGE ɗin naku ne. Allah ya bar ƙauna. Much love 😘😘😘
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Har zuwa lokacin nan Kawu bai fito ba, ganin haka yasa Mamah zuwa ƙofar ɗakin ta leƙa.
Suna haɗa ido ya galla mata harara hakan yasa ta fito waje babu shiri.
Sai bayan sun shiga ɗaki Kawu ya fito. Jikin sa yayi ruɗu ruɗu kamar wadda aka yi ma bulala.
A hankali ya lallaɓa ya fice.
Kai tsaye gidan Aminiyar shi jummai Rubber ya nufa.
Masu gadi sanin shi da suka yi da irin yadda yake alaƙa da uwarɗakin su yasa suka buɗe mishi. Ba tare da ya kula su ba ya wuce zuwa cikin gidan.
Zaune take daga ita sai wani matsiyacin shiru wanda da shi Gara babu, sai kuma bra.
Fara ce sol, jibgegiya. Can ƙarshen parlourn wasu ƴan mata ne da ba zasu wuce 23years ba tsirara haihuwar uwar su sai masha'ar su suke yi (authubillah). Ko kunya babu haka suke ta abun su basu daina ba har sai da Jummai Rubber ta Basu umarnin fita zasu yi magana da baƙo..
A haka suka fice yayin da Rubber ta zubawa Kawu ido tana nazartar shi.
“Takawar ka lafiya gwarzo jarumi, ka daki kowa ko zagi kowa, ko mutuwa tsoron ka take ji”
Murmushi yayi da jin kirarin Rubber sannan ya maida hankalin sa gare ta.
“Rubber magana mai muyi”
Dariyar shaƙiyyanci ta saka sannan tayi shiru
“ai in na ganka idrisu na san magana ta kawo ka, ina jin ka”
“yau wani mummunan abu ya faru da ni”
Nan ya kwashe drama ɗin su da Zahrah ta bata. Ita kanta abun ya girgiza ta in dai har kuwa da gaske ne akwai matsala.
“ni babbar samuwa ta ma bata wuce sanin Ni na kashe baban ta ba, ga kuma sanin ƙwayoyin da nake miki safara”
Cikin kwantar da hankali Rubber tace “Kaga kada ka wani damu, shawara ɗaya ce zan baka idan ka bita to zaka wuce wannan step ɗin”
Cike da ƙaguwa ya kalli Rubber sannan ya rungume ta (nace oh ita ɗin ma matar shi ne kam?)
Cikin kunnen shi ta faɗa mishi wata magana wanda duk gulma ta ban jiyo meh suke faɗa ba sai ji nayi yace
“gaskiya Rubber me ta daban ce”
Murmushi tayi sannan ta manna mishi peck a kumatu daga nan wasan ya sauya salo
(Authubillah)
Sai da suka gama suka yi wanka tare. A nan ya suka ci abinci kafin ya nemi wani ɗaki ya shiga. Wata ƴar Siriyar budurwa ce ta shiga ɗakin Bayan shi, jikin ta babu wasu kayan arziƙi haka ta shiga tana wani karairaya kamar macijiya. Tare da Kawu suka kwana suna sheƙe ayar su Ni kuwa nace (Allah ya shirye su).
★★★★★★★★
Alhamdulillah! Cikin ikon Allah jikin Zahrah yayi sauƙi, da safe Mamah da kanta tayi musu girki, bayan sun karya Mamah ta kai mata ruwan zafi toilet tayi wanka! Ba'a daɗe ba yaya Ishaq yazo.
Tayi murnar ganin yayan ta sosai shima yaji daɗin ganin jikin da sauƙi..
Gaisawa suka yi da Mamah cike da girmamawa. Ya Ishaq yace
“cutien yaya jiki yayi sauƙi koh"
Cike da jin daɗi tace
“eh yaya na warke”
Cike da zolaya ya ce
“ai na yi zaton da safe zan zo cin jallof ne”
Ya faɗa yana kanne mata ido.
Cike da shagwaɓa tace
“kai yayah! Ai sai ka riga Ni mutuwa ma”
“ni rufa min asiri! Damah so kike na mutu ko”
“aah yaya" ta faɗa tana zare ido
“alright in kin ji sauƙi zuwa gobe sai na kai ki makarantar koh?” cike da farin ciki tayi hugging nashi tightly
“na Gode Yaya Ishaq Allah ya ƙara maka buɗi ya faranta maka”
“ameen cutie, to same Ni kafin ki karya ni ko”
Ɗan tura baki tayi ta matsa gefe.
Haka suka yini suna shan hirar su har azahar, sallah yaya Ishaq yayi kafin ya dawo Mamah ta haɗa mishi nashi abincin.
Ita kuma Zahrah ana rikici ita wallahi ba zata ci abinci ba ta ƙoshi
Da ƙyar da siɗin goshi ya lallaɓa ta suka ci tare, bayan sun gama yake sanar da Mamah batun makarantar da zai saka Zahrah yayin da ta ke ta sharɓar bacci abun ta.
“wacce makaranta da ɗin take zuwa Mamah"
“nan makarantar gwamnati ne bayan inji mai wando”
“ammah ta gama primary ai”
“eh yanzu haka sun shiga jss 1 ne”
“ohk shikenan goben zamu je sai a gama mata shirye shiryen saboda nimah sati mai zuwa zan bar ƙasar”
Da mamaki Mamah ke kallon Ishaq
“ina kuma zaka je”
“mamah zan je nayi masters ɗinah be, zan kammala biyan kuɗin jss ɗin ta, nasan zan shigo bayan shekara uku ko biyu”
Duk da cewa basu wani saba ba ammah Mamah tana jin Ishaq a jikin ta tamkar yaron da ta haifa.
“toh Allah dai ya bada abun da za'a ke nema ɗin”
“Ameen Mamah bari zan wuce nikam, sai goben”
“toh Ishaq sai ka dawo, ka gaida gida, Allah ya saka maka da alkhairi”
“Amin” yace yana ficewa daga gidan.
Majalisar Kawu kuwa yau babu wanda ya zauna tun bayan jijjigar da suka ji anyi duk suka tsorata. Shima Kawu yana can yana sheƙe ayar sa gidan Rubber.
Da yammah jikin Zahrah ya warke, tace wa Mamah bari ta ɗan zagaya unguwar don Allah
Bata hana ta ba ko ba komai jikin ta zai ƙara ƙarfi ai ina ta zagaya.
Wanka tayi ta fita tana ƴar waƙar ta har ta zo ƙarshen layin su, wata ƴar ajin su Lawisa Musa ta gani. Kamar wasu manya suka ɗan fara taɗi abun su
“ah Zahrah Abdulkarim dama a unguwar nan kike?”
Da mamaki Zahrah ta kalli Lawisa
“kar ki raina min wayo mana Lawisa, ina banda uban ƙarya zaki ce baki san nan layin nake ba”
Sanin halin ta da Lawisa tayi yasa ta yi shiru kafin tace
“sorry ƙawa ta, na shafa'a ne, toh ya gida”
Farr da ido tayi tace
“lafiya ƙalau"
“jiya an zo duba masu fashi, Man Labour ya ɗauki sunan ku ammah ke Amira ta ce wai baki da lafiya da gaske ne”
“eh wallahi Lawisa, jiya har asibiti aka kwantar da Ni"
Cike da tausayawa Lawisa tace
“Allah ya sauwaƙe Zahrah Abdulkarim, bari na wuce gida nikam, aika na Umma ta tayi”
Daga haka suka yi sallama. Zahrah ta juyo saboda duk ta gaji ƴar tafiyar da tayi.
A ƙofar gida suka ji karo da Kawu, ko kallon arziƙi bai samu ba daga wajen ta. Duk da cewa yana tsananin shakkar ta ammah hakan ba hana shi dakewa ba don da wuya ka gano tsoron Kawu.
“ke don ubanki baki iya gaisuwa ba neh?”
Cikin halin ko ina kula tace
“mutanen kirki masu daraja mutane su ake gaishe wa” ta faɗa tana gurmuɗa baki.
Shaye da mamaki ta tafi ta bar shi, ya rasa meh yake masa daɗin haka nan lokaci ɗaya yayi wata shu'umar dariya
“shawarar Rubber zata yi aiki kwanan nan inda ba haka ba zasu ruguza min buri na, kai!!! Basu isa ba, dole na dakatar da su. Dole.
Sallahr maghrib suka yi, sannan isha', ana kiran ishà Kawu ya fice ta uwar shayibu.
Bayan sun yi dinner suka ɗan yi hirar su.
“mamah" Zahrah ta ambaci sunan ta
“na'am Zahrah, menene?”
“mamah yanzu haka zamu ci gaba da zama a gidan nan?, Wallahi Mamah Ni na gaji da rayuwar gidan nan, dubu fa duk mutane gudun mu suke yi saboda wannan banzan mijin naki”
“ke Zahrah! Ki kiyaye kalaman ki, kar ki manta ɗan uwan mahaifin ki ne shiɗin kuma miji na! Bana kuma son jin wannan zancen kinji ko”
Takaici duk ya cika ta tace
“shikenan Mamah, toh Ni ki kai Ni wajen wata ƴar uwar ki manah! Ni tunda muke baki taɓa kai Ni wajen su ba”
Ba tayi mamakin