dakin tsayawa yayi chak akanshi yace "muje ka shirya mutafi ai ba'a office kakeba yanzu kana gida" dan dagokai yayi ya kalli Arham din wata yar gajeren tsaki yaja yace "Omg wai why did u initiate this dinner stuff at the first place ma eh? Goddd! Mutum cannot rest again yayi abinda yakamata, am so so sick of this wedding, gosh!" girgixa kai Arham yayi ganin yanda yake masifa bil hakki ya karbe laptop din tareda shutting nashi down yarufe yarike ahannu sanan ya mikamai hannu yace "muje mushirya" ahankali yatashi Arham yabishi da kallo yana sanye da faran t-shirt sai wani 3quater short daya tsayamai wajajen gwuiwa shima fari, kafafunshi sanye cikin farin bathroom slippers, gashin kafarnan kwance lub lub irin na mugun dan hutun nan. Ahankali kaman wanda kwai yafashe wa aciki yake tafiya Arham yabude kofar hadadden bedroom dinshi suka shiga ciki, wajen wardrobe dinshi yayi yafito dawasu kaya da bama abude ba yazube su kan gadon sanan yabude ya shiga shiryawa cikin wata white suit na ermenegildo zenga, suit din yamugun fitting nashi daga kasan waje akamai order suit din aka tahomai dashi, sanan yadauki cover shoe dinshi na dinner sabo fil Black, designers shima na Testoni, tsayawa chak Arham yayi yana kallonshi yamugun yin kyau sai kallon kayan yake, juyowa Waleed yayi ya mikamai bow tie din dake hannunshi yace "tayani sawa blood" karban bowtie din Arham yayi yashiga samai kaman ba zaice komiba saikuma yace "amman wanan takalmin da suit din bashi mukaje muka sayo tareba a dunes ko?" girgiza mai kai yayi yace "Uncle yazomin dashi daga Ukraine jiya daya iso" gyadamai kai Arham yayi baisake cewa komiba yana gama samai yawuce yaje wardrobe yaciro wayanda suka sayo tare, yazaro tashi suit din black, dan abokan ango black suit zasu saka shikuma ango white, ya shirya tsaf sanan yataho key motar Waleed ya dauka yace "let's go" fitowa sukayi daga dakin, har zasu fita daga falon Ammi ta shigo dakin sun kusan cin karo, binsu tai da kallo yanda suka mata kyau sosai kafin ta sauke idanunta kan Waleed dayay mata wani irin kyau batasan lokacin data saki wani kayataccen murmushi ba, wucesu tayi tazauna kan sofa sanan takalli Waleed tace "zonan Son" tahowa yayi ahankali kaman wanda baison tafiya yazauna kusada ita inda take nunamai, hannunta takai tai cupping face dinshi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi kafin ta shafa fuskar tace "you look so much like your father today, kayi kyau sosai, Allah ya maka albarka kaji" dan lusme ido yayi yana danne abinda yakeji a zuciyan shi yace "Ameen" purse din data shigo dakin dashi ta ijiye agefenta tadauka tabude taciro rapas nayan dollars guda biyu tamikamai tace "gashi kama y'ata manni dasu" karban kudin yayi ahankali dan baiso yaki karba taji haushi, rungume shi tayi ahankali taredamai kiss akumatu tace "stop being sad, I love you son, kaci abinci kuwa?" juyawa da sauri Arham yayi yafita daga dakin ya shiga mota Waleed din yay zamanshi a mazaunin direba, he just wish inama shine Waleed, kome zaiyi iyayen shi basa tabamai fada komin girman abun, unlike him da kullum abu kadan Umma fada takemai, abu dan kankani sai fada, Waleed ko abinci ma abaki ake bashi, bodyguard ma saida sukai fada da Ammi sosai dan anso kusan 10 sudinga binshi da kyar ya karbi daya wanda yadawo direban shi, bama abari yasha wahalan neman mataba aka samomai yar gidan masu kudi, graduate lawyer fa dudda dai bai taba ganinta ba aka bashi, just look at suit din da uncle dinshi ya kawo mai daga Ukraine, suit din ermenegildo yana costing about 22 to 28000 dollars, suit din jikinshi kadai worth a fortune dan yakai almost 8.8million naira a kudin Nigeria, takalmin kafanshi na Testoni kusan 3m ne shima, gata da dadi is beyond tunanin kowa ko shima inda bai gani da idanunshi ba dabazai taba yarda ana bama yaro gata irin gatan da ake bama Waleed ba, why was he born from the poor home? Maisa Umma ta auri Abban shi wani Malam Muhammad Bala, malamin islamiyya? Yataso ko gidan kansu basuda shi sai gidan haya, gidan dakuna ashirin da biyu da bayi guda biyu daya na kashi daya na fitsari, daga baya kuma yazo yarasu ya barsu cikin talauci, Waleed ne ya shigo rayuwan shi ya chanza mai komi..... Bude motan da akayi yadawo dashi daga daga dogon tunanin dayaje Ammi ne tabude ma Waleed din kofar motan tana kallon Arham tace "son ina gajiya" cikeda kunya dan yafi sakewa da Mom sabida ita tanada raha sosai while Ammi batada raha tanada fada, bata cika wasa da yaraba, aduniya in tana tareda Waleed ne kawai zaka dinga ganin dariyanta da murmushi ta abanza, da farkoma ya dauka bata sonshi ne sai daga baya ya lura haka Allah yayi ta ita kawai bamai yawan wasa da sakema yara fuska bane, cikeda girmamawa ya sauke fuskanshi yace "ina yini Ammi, ya taro" tana kokarin saka Waleed dake mata wani shegen shagwaba a mota tace "Alhamdulillah Arham, ai tuntuni muna tareda mahaifiyarka ma wlh, mamanka akwai kirki, kaga Arham gashinan drive him safe please, saikun dawo, bye Son, have fun okay, if u need anything ka kirani zan aikoma dashi" ta shafa kan Waleed din dake tura mata baki tana murmushi, kunna motar Arham yayi yaja Ammi na daga musu hannu tana murmushi, saida sukadan yi nisa ahanya sanan ya kalli Arham din dayaga yay shiru kuma ba halin shi bane yamika mai rapas din dollars din da Ammi tabashi duka biyun yace "use this" da sauri Arham ya kallai saikuma ya maida kanshi kan tukin yace "a'a, abinda Ammi tabaka zan karba" murmushi yayi kafin ahankali yace "take it inada wanda zanyi amfani dashi already" "shikenan" Arham yafadi ahankali kafin yace "thanks blood" murmushi Waleed yamai baice komiba, ahaka har suka karasa event centre babu wanda yakara magana cikinsu, daman yawanci in suna tare Arham ne mai kawo hira shi Waleed iya kanshi um a'a kokuma yan maganganu kadan, parking yayi yace "ka zauna aciki, I need to confirm in Amarya ta iso dan tare zaku shiga Hall din" bai jira amsanshi ba yamaida kofan yarufe yay wurin entrance din daidai zai shiga Abdul suna saukowa daga elevator tareda Salima suna hira shiru sukayi ganin Arham, Salima tace "you must be Arham ko? Best friend na ango" dan murmushi Arham yayi yana binta da kallo tana sanye cikin asshobi kawayen Amarya pitch yace "yeah nice to meet you Mss Salima" murmushi Salima tayi tana kallonshi ganinshi shima kyakkyawa sosai saidai dudda kyanshi baikai kyawun Dr ba, kuma Dr yafishi kaurin jiki da cikama mutum ido, ganin kallonshi take yasa ya katse shirun yace "ina Amarya? Cus they're going in together" "eh tana wani daki asama where is Dr?" juyawa yayi yace "lemme get him" har wajen motan yaje yabude motan ya kalli Waleed dake dandanna waya yace "let's go ango" ballamai harara Waleed yasakeyi hakan yasa Arham yace "sorry mana ai kuma gaskiya nafadi kai angon ne" ahankali Waleed yafito yana gyara suit din jikinshi su karan kansu su Abdul da Salima kallonshi suke yawani irin yin mugun kyau cikin white suit din dasukai mugun fitting dinshi maida kofar Arham yayi yana kallonshi yace "muje" ahankali suke tafiya har zuwa gaban entrance din Salima takasa daina kallonshi, dan kallonta yayi sanan ya kalli Abdul batare dayace musu komiba, anatse Abdul yace "sannu da zuwa Ya Waleed" bai kallesu ba yacema Arham dake kusadashi "let's go" wucewa sukayi dukansu suka shiga lift din yakaisu 4th floor, wani daki Salima tabude tana kallon Arham dan Waleed mugun cika mata ido yake tace "ku shigo tana nan" shiga ciki tayi suka hada ido da Ilham datasha uban gayu anmata makeup tasaka wani gown white daya mata fitinannen kyau ita kadai zaune kan wani Royal chair tai kyau sosai, cikin tafiyan nan nashi mai daukan ido daidai ya sawo kanshi cikin dakin Arham biyeda shi abaya, ahankali ta mike tsaye tana kallonshi hada ido sukayi hakan yasa ya tsaya chak shima, wani irin dadi ne ya lullubeta batasan lokacin data saki murmushi ba da sauri tazo wajenshi batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi, ihu dakin ya dauka Arham ya shigo dakin da kyau yana kallonsu yana murmushi, da sauri Salima taciro wayarta tafara musu hotuna, ahankali yadaga hannayenshi ya rungume ta back, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta shige jikinshi sosai tana shakan kamshin dayakeyi, kaman ta jawo gobe takeji ayi a daura musu aure tayi ta dawo matar this ajebota handsome rich kid, "wai anan zamu kwana ne" Abdul yafada yana dariya, ahankali tasake shi cikeda jin kunya hakan yasa shima ya saketa, juyawa tayi suka hada ido da Arham da tundazu yake kallon bayanta Allah Allah yake yaga fuskarta, dan murmushi tayi sanan tajuya ta kalli Waleed din, dan lumshe ido yayi yabude kaman mai rada yace "my best friend, my brother, my blood, Arham" wani irin murmushi tayi ta juya ta kalli Arham tace "the great Arham nasha jin labarin ka tun abakin Ammi, my husband best friend childhood friend, so nice to meet you" dan murmushi Arham yayi yakasa daina kallonta yace "yes your husband is my blood we've been together since childhood, and he means the world to me, so ki kula min da abokina dakyau" dan dagakai tayi ta kalli Waleed kafin ahankali takama hannunshi tarike gam tana kallon face dinshi tace "I was born to do that, I love you so much Doctor na" ganin akwai mutane awajen yasa ahankali yace "thanks" wani iri Arham yaji he just feel inama shine yake da wanan soyayyan, Waleed is the definition of yaran da ake haifa da silver spoon abakin su, Waleed is just surrounded with love ne ta ko'ina, just look at yanda wanan hadaddiyar classic graduate lawyer yarinyar nan kesonshi tama mutu akanshi but yana yanga, infact baima sonta, baima son auren ko kadan, yarinya ga shegen kyau, itama yar masu kudi but yake yanga, he just wish zai sami yarinya haka dazata dinga mutunmai dinan, Salima ne ta katse silent din tace "I think we should go anfara event fa tundazu" fitowa sukayi duka atare, bayan an sanar da isowansu a hall aka kunna music suka shiga cikin kasa ita sai hotuna ake musu, sosai akai event kala kala duk in Ilham zata dagokai saita hada ido da Arham dake kallonta saidai ta sakanmai murmushi ta maida hankalinta kan Waleed, anso sai asuba za'a tashi 1 nayi Waleed kaman zaiyi kuka yakira Arham awaya bai dauka ba, ganin duk yay wani iri yasa Ilham tace "me kakeso baby?" batare daya kalleta ba murya chan kasa yace "nagaji i think atashi" ayanda yay maganan saida yasa har wani lumshe idanu tayi, Waleed is handsome gawasu mayun pink lips dayake dashi dake shinning kaman ka lashe, she can't wait to have a taste of them, kasa cemishi komi tayi sai binshi take da kallo, ganin kiss call dinshi yasa Arham yazo gayamai yayi atashi yagaji bacci yakeji, Arham baimai musu ba ya sanar da dj a kunne, yan abubuwa kadan akayi aka tashi, dudda yanda Waleed keso yaje gida Arham yace mai ba haka akeba shizai raka Amarya gida sanan saisu tafi, yanaji yana gani Arham yasa aka saka Amarya a bayan motansu yasa Waleed din kusada ita sanan yakoma gaba ya shiga ya tukasu, sun danyi nisa da tafiya Ilham ta matsa kusadashi ahankali tareda saka hannunta kan nashi ta kama gam, shiru yamata yana dan lumshe ido kafin daga baya bacci yay nasa ran kwasheshi ya daura kanshi kan kafadarta, wani irin dadine ya kasheta tai dan murmushi tace "haka abokinka keda saurin bacci?" ta glass din gaban motan ya kallesu yay dan murmushi yace "ai zakisha shagwaba, haka Allah ya yishi, mijinki shagwababbe ne" murmushi tayi ta shafa fuskarshi bata sake cewa komiba shima Arham haka har suka kai gaban gidansu, ahankali ta gyaramai kai tareda pecking nashi ta kalli Arham daya bude mata mota tace "good night our blood" murmushi yayi yace "good night our wife" gyadamai kai tayi tawuce yamaida kofan yarufe yana dan satan kallon bayanta, ta shiga gidan su, dakinta tawuce direct inda Salima da wata kawarta suke zaune harsun chanza kaya dansu tun dazu suka iso itakuma dayake ahankali Arham ke gudu saisa basu iso dawuri ba.
[11/1, 11:44 PM] Re@lš¤ K@usy š: š« _TWO DIFFERENT WORLD_ š«
āļø M SHAKUR
6ļøā£
_*This novel is for free. Wanda mu Kungiyan FREE HAUSA NOVELS WATO BANZA *ASSOCIATIONS* muka dauki nauyin kawo maku.
Page 6
*_MOHAMMED V INTERNATIONAL AIRPORT, MORROCO._*
Karfe shida na safe daidai jirgin British Airways ya sauka a airport din Mohammed VI, sai kataniyar saukowa passinger suke daga cikin jirgin kana ganinsu kasan they're all stressed out sun gaji iya gajiya, saida kusan kowa yagama saukowa daga cikin jirgin sanan ahankali wata yar doguwan matashiya tasawo kanta tawajejen kofan zata fito tana goye da jakar makaranta abayanta tarike igiyoyin gefen jakan gam da hannunta, farace sol yarinyar tana sanye da wata bakar doguwan riga mara kwalliya ko daya ajiki jallabiya, sai gyalen ta datai rolling aka sai abin yay kaman hijabi dudda hakan bai hana bakin suman gaban goshinta bayyana ba sun mugun kwanta sunyi lublub kaman na yar jaririyan da aka haifo yau, tanada manyan idanuwa fararen fat da brown kwaiduwan ido dan ko kadan nata ba bakake bane brown nesu light brown, giran ta full da gashi baki mai shining kaman ta sakamai relaxer, gawani siririn dogon hanci daya ratsa tsakiyan fuskanta ya bala'in karamata kyau, lips dinta pink yirr yan fele fele kananu kaman na yaron da aka haifa yanzu yanzun nan. Sake rike igiyan jakan datake goyedashi tayi gam, ahankali ta lumshe ido iskan garinsu yawani kada mata fuska tasaki murmushi daya lotsar da dimples dinta na both sides, dama da haggu sun lume chan ciki sosai kaman rijiya tai wani irin kyau da ba'a iya misaltawa sanan tabude idanun ahankali kafin tadaga yar kafarta tafara saukowa daga kan matattakalan jirgin tana kallon ko'ina ganin bataga yan gidansu ba daidai da mutum dayaba yasa taji wasu hawaye sun taho mata masu dumi, ahankali takai hannunta kan fuskarta zata share hawayen kaman daga sama taji an kwalamata kira. "Widad! Widad!" wani irin juyawa tayi da saurinta, wata mata tagani ita kadai tadan manyan ta sosai dan akalla zatafi 70 yar tsohuwa ce tana sanye da doguwan riga itama da hijabi daya tsaya mata aciki tana tahowa da dan sandanta a hannu, wani irin tsalle yarinyan tayi hawayen suka karasa zubowa cikeda murna cikin harshen larabci tsohuwan tace "ahlan wa sahlan wa marhababik Widad" cikin wani irin muryan kuka yarinyar da tsohuwar takira da Widad tace "Assalamu Alaykum Amah" holding shoulders nata taohuwan tayi sanan tai kissing left cheek nata sanan tamata ana dama tana murmushi cikin tsantsan farin ciki da tsantsan so takara mata another peck a forehead tace "waallaykumus salam Widad, kaif? (how are you)" juyawa tayi tana kallon ko'ina na filin Airport din kaman mai neman wani abu tace "Alhamdulillah Amah" ganin yanda take kalle kalle yasa tsohuwar tai murmushi sosai batare datace mata komiba tabarta tacigaba da kalle kallenta, tana cikin kalle kallen kaman mai neman wani abu taji anrike mata hannu gam wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta tsayar da kanta chak kafin ahankali lebbbenta suka furta "Ab.....Aby" dawani irin sauri ta juyo kaman amafarki, wani magidanci ne tsaye a bayanta yana rikeda hannunta yana sanye da jallabiya fari fat, kafanshi sanye da skos na maza, sai kanshi daure da rawanin larabawa sai farin gilas a idanunshi da daga gani kasan na kara karfin ganin idanune, kana ganinshi kaga tsantsan balaraben morroco kyakkyawa ajin farko, wani irin fashewa da kuka tayi haka Allah yayi ta tanada saurin kuka, very emotional mutum ce ita, sanan duk duniya batada wanda takeso kaman babanta saisa kodaga nesa takanji a jikinta yana kusada ita, fashewa da kuka sosai tayi tace "Abyyyy" anatse magidanci yasakin mata wani kyakkyawan murmushi yakai fararen hannunshi yadaura kan fuskarta ya share hawayen datake tass kafin yarungumeta ahankali yana bubbuga bayanta anatse irin na manya dinan cikin muryanshi na dattawa yace "marhababik, marhababik" sunkai kusan 5min tana jikinshi har lokacin tana sheshekan kuka sanan yadago ta, hannayenshi yasa akan fuskarshi yay cupping face dinta cikin tsantsan so yace "kidayra? (how are you)" ahankali tace "Alhamdulillah Aby" gyadamata kai yayi yace "masha Allah" yanuna mata mutanen dake tareda shi alamun ta gaidasu, ita sai a lokacin nema ta lurada su dazu mahaifinta kawai idanuwanta suka gane mata, yangidansu ne dan gidansu family house ne babban gaske, wata balarabiya dake kusada mahaifinta ta gaida ta hanyar cewa "Assalamu Alaykum Um" sanan ta kalli sauran tacemusu "Assalamu Alaykum" amsata sukayi ko wanne da murmushi kan fuskarshi banda matar dake kusada mahaifinta dako amsata batayiba, cikin harshen larabci mahaifin nata yace "mutafi gida" kasancewan ansan koshi waye agarin saisama aka bari suka shigo har filin jirgin yasa suna zuwa akaimata clearing komi suka shiga wasu manya manyan jeep farare sukai gida, itadai tana cikin na mahaifinta kusada shi sai matar data kirada Amah gefen ta, mahaifinta kuma na gaba da direba, sukabar airport din.
Agaban wani babban tangamemen gida sukai parking, irin gidan nan da aka ginashi na usulin culture larabawa, an zagaye gaban gidan da flowers iri iri daban daban kalolinsu kaman kazo ka kwasa ka gudu, tun kafin tafito daga cikin mota takejin sautin ganga na mandiri ana bugawa ana wake, murmushi tayi ta kalli mahaifinta cikeda so duk lokacin dazata dawo daga school sai Aby yahada mata walima na kayatarwa daban mamaki dan tarbanta kadai, bude kofa tayi tafito sanan tamikama kakanta hannu tafito daga motan Aby yafito yana kallonsu, kowa ya sassauko daga cikin motar akai cikin gidan, babban compound ne da girman tsakar gidan zaiyi girman primary school ana raye raye ana wake ana, ana rawa, ganin Widad din da iyayen ta sun shigo yasa mawakin yataho gabansu da yan amshin shi suna buga mandiri suna rera wake yace "kaifa Anti? Wa kaifa ji'iti? Marbabiki Ya Widad binti Othman Benjalloun" wani irin murmushi tayi ta washe fararen hakoranta tana kallonsu tana kara rike igiyan jakan makarantan ta abubuwa like this nabata peace sosai yanasa tana tunawa da mahaifiyar ta, ahankali mahaifinta ya kalli fuskarta murmushin dayagani kwance kan fuskar yasa yaji hankalin shi ya kwanta sosai, flowers ya karba a hannun daya daga cikin ma'aikatan gidan sanan yazo ta gabanta yabude flower ya sanya mata flower a wuyanta cikin harshen turenci dakeda Arabic intonation yace "wercome bark homer Widad" rungume mahaifinta tayi tana murmushi sosai tama kasa magana, ganin abun nasu bamai karewa bane yasa Amah cikin harshen larabci tace "to mayyar mahaifinta tadawo fa yanzu mun shigesu, saki ubanki muje daki kiyi wanka kizo ki chanza kayan nan kizo kici abinci ki kwanta kiyi bacci" Amah tai maganan tanajan hannunta, binta tayi tajuyo tama mahaifinta waving hannu sukai cikin gida, dan murmushi mahaifinta yayi yajuyo ya kalli matarshi datai kini kini darai cikin harshen larabci yace "kawomin shayi dakina" yay maganan tareda wucewa yashiga wani wakacecen falo irin traditional falon larabawan nan namasu kudin gaske, babu kujeru adakin sai wasu irin filulluka hadaddu set set da ake kishigada akansu gawani wargajejen hadadden carpet daya zagaye ko'ina a falon sai uban laushi kaman da fatar jarirai akayi sai shisha pot asalin pot din na larabawa, dan daidaikun asalin gidan rikakkun balarabe ne zakaje da bazaka ga shisha pot a dakunan su ba.
Othman Benjalloun dattijo ne dakeda shekaru 62 aduniya, bala'in mai kudine agarin morroco, agabaki dayan garin ance bayan Mohammed VI wanda yake number 1 mai kudin garin, Othman shine the second richest person in the whole morroco, yana harkan banking insurance, yanada bankuna yanada kasuwanci da dama, matayenshi uku aduniya, Mahaifiyar Widad itace ta farko wanda a yanzu ta rasu, sai matarshi da biyu wacce Widad takira da Umm, sai ta ukun wacce yasaka sabida cutar da Widad datasoyi Allah ya tona mata asiri, yarshi daya aduniyan nan tal Widad, Allah baitaba bashi haihuwaba sai akanta, itama din harya cire rai dan yaga yay mata uku duk shiru yace halan daga shine sai kwatsam ga mahaifiyar Widad da ciki, yakusan karaman hausa a lokacin daya gane tanada ciki saisa da aka haifamai mace saiya radamata suna WIDAD ma'ana love, yana bala'in son yarinyar so mai zafi, gashi kana ganin yarinyar kaganshi kaman yay kaki, ko office zashi da yarshi da mahaifiyar ta yake zuwa sabida yadinga sata a ido kodayaushe, indan tafiyan fitanshi daga gari ce ta taso saidai yadauki mahaifiyar ta da ita dan bazai iya nisa da itaba saisa itama yarinyar ta taso tana bala'in son mahaifinta, tanada shekaru 18 mahaifiyar ta tarasu daga ciwon kwana daya tal, Widad takusan hauka take mahaifin nata yafita da ita da kyar aka samu taji sauki aka dawo da ita gida tadinga kuka daga karshe taroki mahaifinta tunda tagama sakandire yakaita wata kasar tai University intana gida tunawa da mahaifiyar ta take sosai, da kyar da kyar saima dayaga ta kwanta tana ciwo sanan ya yarda yakaita Egypt yamata komi yasaman mata admission in datake karanta mass communication.
Wani hadadden babban daki suka shiga itada Amah dake upstairs, dakin wakacece ne babba dayasha carpet tako ina mai bala'in kyau dan duk wanda yasan morroco yasansu da sana'ar kera carpet su sayar, gadaje biyune hadaddun gaske masu rumfa da aka zagaye da labulaye farare masu kyau acikin dakin babba da karamin gado, tun bayan mahaifiyarta ta rasu tadawo dakin kakanta da zama kakanta ne kadai takejin dadin zama da ita dan tana sonta kaman ne, jakanta tacire ta ijiye akasa sanan ta taka zuwa gaban wardrobe din dakin dan neman kayan dazata saka, Amah kuma ta ijiye sandarta agefe ta zauna ahankali kan gadonta tanabin bayan Widad din da kallo, shekara daya kacal dabata ganta ba amman saitaga ta chanza mata a ido sosai, dan murmushi tasaki tana tunanin Widad da aka haifa jiyane ta girma haka, batare da Widad tajuyo ta kalleta ba cikin harshen larabci tace "Amahh why are you smiling? Tunanin me kike?" tai maganan tareda juyowa hannunta rikeda wata jan kaftan dayasha ado kaman irin dogayen rigunan India, hararan ta Amah tayi tace "wuce kije kiyi wanka, favourite dinki nasa aka dafa tagine, rice da herbs saikuma flat bread" washe baki tayi ta yarda rigan hannunta kan gado da gudu tai bayi, kyalkyacewa da dariya Amah tayi tadauki sandarta tawuce tafita dan tabbatar da yan aikin sun jera komi a tsakiyan falon barinma wanda tasan yar jikallenta tafiso. Dan aikin datagani awurin yana ijiye plate dake dauke da dry fruits tacema "ina flat breads din danasa ku gasama Widad?" cikeda girmamawa yace "yanzun nan jibril zai karasa baking dinsu yafito dasu" zata sake magana taga Aby na saukowa daga sama shima da hannu tama dan aikin alamu daya wuce yabata wuri, da sauri yawuce bayan ya gaida Aby, saukowa daga benen Aby yayi yazo gabanta mahaifiyar tashi yace "Assalamu Alaykum Amah" "waallaikumus salam" ta amsashi tana zama, ahankali shima ya zauna gefenta yadau inibi daya yajefa abaki yanadan bin wakan da akeyi awaje cikin kwanciyan hankali, ganin yanda yake farin ciki yasa mahaifiyar shi takira sunan shi. "Othman" anatse yajuyo ya kalleta tareda ijiye inibin daya so jefawa cikin baki kan faranti, dan gyara zama Amah tayi da kyau kaman yanda shima ya natsu yana jiran yaji mezatace mai, cikin muryanta na tsofaffi tace "wace shawara ka yanke akan maganan damukai dakai jiya?" fuzar da iska yayi fuskarshi ya dan nuna damuwa yace "I don't know Amah, all I know for sure is bazata koma wanan makarantan babu aure akanta ba, ai nai mata kokari dana iya nabar y'ata wacce ita
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 20