Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sukabi ta gefensu suka fita daga dakin, wani irin juyowa Ammi tayi cikeda wutan bala'i, da kunan rai da tsantsan bakin ciki ta kalli Mom sanan tanuna mata Waleed dake kwance kan gado da hannu tace "kinga abinda Arham yama d'ana ko? Kinga abinda Arham yama d'ana ko, kina gani daiko, yaron da dama kece tun day one kikai approving friendship dinshi da yaron, left to me yarona ya rayu ahaka baida aboki I his mother can be his best friend and his everthing aman kika nace saina barsu sunyi abota, dan haka karma naji kinhanani dauka hukunci dan wlh wlh bazan yarda ba" tai maganan tana dauko wayanta daga cikin jaka da sauri Mom tace "Adda kinga calm down yanda kike tafarfasan nan bai kamata kidau hukunci ba, dan Allah kiyakuri Adda" da wayan hannunta tanuna Mom tace "Zainab ki shiga taitayin ki, na rantse miki da Allah yanda Arham ya jima d'ana rauni ko kwana baza'ai ba shima sai anjimai, wlh saiyasan ya buganmini d'a, shidan ubanshi ubanwa yataba dukanshi haka? Waleed dakoni bantaba daga hannu na daka bane wani kato zai dokanmin wlh wlh saina ramamai, wlh kuwa kinji na rantse miki" Ammi tai maganan tana bude kofa tafita daga dakin tana dailing number Maman Arham. Ringing daya Mama tai picking call din ganin kira daga Ammin Waleed, kafin ma Ammi tai magana cikeda fara'a tace "Assalamu Alaykum, barka da yamma Hajiya" ko amsa sallamarta Ammi batayi ba cikeda bacin rai tace " please kome kikeyi kibarshi kisamemu a orphanage na Waleed yanzun nan kizo, ina jiranki yanzun nan" tana kaiwa nan ta katse wayan jikinta na vibrating, Mom ma takasa cewa komi tazama yar kallo matsalan yayarta kenan intai fushi batada hankali, kuma bataji bata gani barin ma when it comes to Waleed matter. Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake. Hijabi kawai ta dauka ta zira akan kayan dake jikinta, ta kwalama diyar kanwanta kira tace "nafita yar albarka saina dawo, ki daura abincin dare" daga ciki yarinyar ta amsa da "saikin dawo Mama" fita tayi daga dakin ta kwalama driban ta kira yafito, mota ta shiga tace yakaita orphanage dinsu Waleed ya amsa mata da to, yatada motar yafita daga gidan. Ko cikakken 15min direban bai daukaba yakaita orphanage din, tana fadin mahaifiyar Arham ce ita aka barta ta shiga dan ta taba zuwa sau daya suka shiga ciki, kirjinta bai kara faduwaba sai dataga ma'aikatan orphanage din carko carko a tsaitsaye ana tattaunawa agaban clinic, parking direba yayi tabude kofa tafito daga motar kirjinta na bugawa, wayarta dake hannunta taciro tanemo layin Arham ta hau kiranshi danta tambayeshi maiya faru, wani abu yafaru ne amman har wayan ya katse bai dauka ba, hakan yasa tai dialing number Ammi, ringing daya Ammi ta dauka, ahankali Mama tace "Hajiya na iso" cikin muryan Ammi dabata fita sosai tace "kishigo asibitin muna emergency" shine kawai abunda Ammi tafadi mata ta katse wayan, sosai Mama taji kirjinta na bugawa yanda Ammi kemata magana, hakan yasa ta daga kafarta tana kallon mutane ta shiga tafiya harta karasa gaban asibitin tasa hannu ta bude kofar ta shiga ciki, kasan cewan emergency din asibiti bata boyuwa yasa tana ganin dakin tagane batare datama tambayi nurses din dake wurin ba tai wajen kofan, ahankali ta murza hannun kofan dakin tashiga ciki, Ammi da Mom tagani zazzaune, Mom kan kujera Ammi kuma kan gado gefen kafar Waleed, Waleed kuma kwance kan gadon asibiti, ansa mishi drip, fuskarshi tai jajir ta kumbura wuyanshi ma haka, hannunshi adaure daurewan irin na karaya dinan, wani irin mummunan faduwa gabanta yayi karfin hali tayi tadaga kafarta ta karaso cikin dakin ta tsaya gefen Waleed, bakinta har rawa yake tace "Ha....Hajiya meya sami Waleed? Meya faru? Meyasame shi"? muryanta na breaking sosai tayi maganar hankalinta a mugun tashe, dagokai Ammi tayi tazuba mata jajayen idanunta sanan ta tashi daga kan gadon tace "biyoni" da sauri Mom ta tashi tana girgiza ma yayarta kai amman Ammi ta dauke kai kaman bata ganta ba tabude kofa tafita Mama biyeda ita, itama Mom tabisu wajen, tsayawa sukayi a reception premises din cikin fushi Ammi tamata pointing dakin da Waleed yake ciki tace "wlh mutuncin ki danake ganine yasa nakiraki dan kizo kiga abinda yafaru da idanun ki, kinga Waleed dina, kinga yanda yake akwance agadon asibiti, kinga yanda yadawo, dan iskan danki ne ya mishi haka, Arham ne yama Waleed dina haka, jibi yanda yama d'ana dukan dakoni dana tsugunna na haifeshi bantaba mai irinshi ba, kitayani tambayan Arham da ina labo yazo yatayani nakudar d'ana ne dazai kamamin shi ya daddaka haka"? mamaki ne ya mugun cika Mama kaman wacce ke koyan magana tadafa kirjinta tace "Arham! " tana kwalalo idanunta waje tsabagen mamaki, cikeda masifa Ammi tace "duk abunda Waleed yama Arham da abunda zai saka mishi kenan, Waleed ko agogo nasaimai bayi karba saina sayo biyu nashi dana Arham, komi shida Arham, amman yau Arham ne zai kamashi yama wanan shegen dukan toh wallahi bazan yarda ba, wlh, bazanji kunyarki na cuci kaina ba, wlh wlh bazan yarda ba yanda yama yaron nan shegen dukan nan sai shima anmai irin ta, mai rabani da Arham sai Allah don saina yagashi, saina sa anmishi x10 abunda yama Waleed wallahi wallahi bazan yarda ba" Mom dai batace komai ba kuma batayi yunkurin hana Ammi fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham. ā¤ā¤ā¤ [11/1, 11:47 PM] Re@lšŸ–¤ K@usy šŸ”: šŸ’« _TWO DIFFERENT WORLD_ šŸ’« šŸ’«šŸ’« _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_šŸ’« šŸ’« āœļø M SHAKUR 2ļøāƒ£6ļøāƒ£ & 2ļøāƒ£7ļøāƒ£ FREE PAGE Komawa falo sukayi duk suka zauna Anty Hussai da Yakolo sukahau hira banda Anty Hassu datai shiru tana tunani ko kadan bata yarda da Ilham ba, but still batason tama Ilham tunanin datake yi, duka duka yaushe Ilham ta girma hartai wayon da da aurenta zata dingabin wasu mazan, ta tambayi kanta saikuma tai shiru, duka duka yaushe akai auren Ilham dake mugun son Waleed kaman zatai haukane zatabi wani namijin? Ajiyan zuciya ta sauke tana kokarin kawar da tunanin daga zuciyanta dan bamata fatan abinda take tunani shike faruwa. Wuraren 4 na yamma ya shigo gidan marayun yay parking motarshi yana tattaro wasu uban takardu daya ijiyesu a kujeran gefen direba ya kwasa dayawa yarike sanan yabude motan yafito daidai Waleed yakaraso wajen dan daga masallaci yake, wani iri Arham yaji dayaga Waleed kaman zai maida takardun cikin motarshi saikuma yarike hannunshi, karasawa wurin shi Waleed yayi hannunshi zube cikin aljihu yace "kadawo blood" gyadamai kai Arham yayi yace "yes nadawo blood, Mama ta iya saka mutum aiki, iyaye sai ahankali" zaro hannu Waleed yayi daga aljihu yamika Arham din yana kallon uban papers din hannunshi yace "what are those blood mugani" Da sauri Arham ya kalli papers din gabanshi nafaduwa Saikuma yakara linkesu yana lankwdhesu da kyau gudun karyaga mainene su yace "they're not mine, nawani dan anguwan mu" saikuma yabude mota da sauri ya zubasu ciki sanan yamaida kofar motar yarufe yajuyo ya kalli Waleed dahar lokacin kallonshi yake, sanan yace "muje daman akwai maganan danake so namaka" juyawa Waleed yayi yace "am going to the clinic now to check my patient nafito mayi maganan" ganin kaman ran Waleed din yabaci yasa yace "muje to naraka ka clinic din" yabi bayan Waleed din, clinic din suka shiga da basuda much patient that are on admission saidai out patient wayanda kawai zasuzo suyi complain kazakaza na damunsu adubasu abasu magani sutafi, dakin da Widad take direct Waleed yayi Arham biyeda shi suka ya shiga, tana kwance akan gadon an lullubeta da bargo fuskarta ne kawai awaje da gashinta da akai parking tana bacci, idanunta har wani nama nama sukayi tsabagen bacci, karasawa gaban gadon yayi Arham biyeda shi, Arham yace "for the past 3month now kullum yarinyar nan nazo dakin nan bacci take saikace wacce take a coma" stethoscope yadauka yana makalawa a kunne yace "she's not in a coma, babu ranan duniyan dabata tashi, yawanci sau daya take tashi, amata brush abata abinci suma duk tanaci tana gyangyadi tasha magungunan ta, I was the one that increase her dose, duk wanda yakeda damage a brain need absolute rest, yesterday nakara mata MRI da CT scan I was happy with the result, fluid din yaragu sosai wanda yarage baifi an atom size ba, yanzu shi nabashi 4days, dazaran kwanakin sun cika zan sake running test din inhar babu saina godema Allah, tagama da magungunan zan mata transfer zatabar hospital takoma hostel, dudda haka I will be monitoring her ina bata magungunan that help with the memory lost" yay maganan yana zare, stethoscope din daya daura kan kirjinta duk Arham na kallonshi, dan tabe baki yayi yace "tamayi kokari kusan watan ta 9 akan gadon asibiti, sai yanzu ma nake dana sani daban karanci medicine ba nima nadawo likita kaman kai nawani kama ina karanta engineering, kumako kasan inda na karanta medicine dafa nafika kwarewa" yay maganan ahankali hankalin shi nakan wayanshi dayake dannawa yana kokarin turawa Ilham message kartace baikara nemanta ba, dan juyowa Waleed yayi ya kallai jin maganan yamai wani iri aka, ganin wayama Arham din ke dannawa yasa yagyara mata bargon yace "let's go" yay gaba shikuma Arham yamaida wayan aljihunshi da sauri yabishi suka fita, office din Waleed suka shiga, Arham yaja kujera ya zauna Waleed ma yazauna yana gyara zaman takardun kan table dinshi sanan yace "yes ina jinka kace akwai maganan da kakeso kamin blood" Ahankali Arham yasake jawo kujeranshi gaban table din sosai yasauke ijiyan zuciya ahankali sanan yace "I need a favour blood, kaima kasan you've been my ride, my backbone my everything, u are my only friend I come to you in every situation" yadanyi shiru sanan yace "I need money blood, I need money sosai" ahankali Waleed yace "for what?" ahankali yace "kaga na farko, Maman su yarinyar nan da Mama tace na aura, kanwar Mama gidansu ya rushe, ruwa yamusu gyara, sanan inaso nasaya ma mijinta shanu da gona su dinga sana'a, sanan inaso nakaisu Umara harda Mama and many other thing, please kabani 10m blood" yakarshe maganan ahankali shiru Waleed yayi yana kallonshi, arayuwanshi baida mutum daya keso kaman Arham, saisa kome zaimai baya taba sa ido koyaga mezaiyi da kudin kowani abu baruwan shi, in yabashi kudi yabashi ne so badamuwarshi bane abinda zaiyi da itaba, baitaba cire kudinshi yasai kaya ma shi kadaiba bazaima iyabane inhar shi zai cire kudi yasai sitira to nashi dana Arham zaisaya, duk wani abu dazaisa ajikinshi inhar Arham baidashi to iyayen shi ne ko uncle dinshi suka siyamai, yana bama Arham kudi sosai excluding kudin albashin shi, lokacin bikinshi yabashi dollars da Ammi tabashi baimasan yawansu ba, ko last 2weeks saida yamai kyautan 3M cikin kudaden sa gwamnati takawo ma gidan marayu tallafi dan he don't really needs government money kafin su kawo yay amfani da kudinshi yayi abinda ya kamata, abincin Mama da supplement dinta yana kanshi kowani wata saiya saya yakaimata yabata kudin kashewa amatsayinta na maman abokinshi, yabada kudin man motan ta dakudin man generator na gida, banda inverter dayasa aka saka agida saisa 247 duk lokacin dazaka gidan Mama nada wuta, Arham baya komi danta ko'ina ya tare mai wata dawainiyar shi to'ina yake kai kudin shi? Abin yadade yana damunshi bawai dan sa ido kowani abuba just amatsayin shi na abokinshi na gaskiya zaiso yasan inda yake kai kudaden shi karyazo yana wulakanta kudinshi koyana saka kudinshi awani abu na haram ne, yariga yasaimai dankareren gida a anguwan da gidanshi yake da Ilham keciki, incase inya tashi aure yasa matanshi ciki ballema yace gini yake da kudin ina Arham yake kai kudi, kowani bad abu yake da kudi? No hakkinshi ne amatsayin shi na abokinshi na gaskiya ya tambayeshi yaji. "X-man kayi shiru kobaza kabani bane?" Arham yatambaye shi, dan nisawa Waleed yayi yace "no bahaka bane, actually I've been wanting to ask you this question also, I think today is the right day, Arham" Waleed yakirashi anatse, zubamai idanu Arham yayi irin ina jinka dinan batare daya amsaba, ahankali Waleed yace "Arham banso kamin karya, tell me please mekake yi da kudi"? Dawani irin sauri har yana neman taran numfashin shi yace "kaman ya menake yi da kudi" dan jim Waleed yayi yana kallonshi saikuma yace "okay lemme do it like this kafahimce ni, blood duk wata dawainiya dazata sa ka kashe kudinka na dauke makashi yet kullum bakada kudi, me kakeyi da kudi"? Wani irin zabura Arham yayi yamike tsaye daga kan kujeran dayake kai yana kallon Waleed din yace "mekake nufi da duk wata dawainiyar dazata sa na kashe kudi ka daukemin ita yet kullum banida kudi, Waleed gori kakemin sabida kana siyama mahaifiyata yar buhun shinkafa duk wata kana kaimata"? Waleed was still seated akan kujeran shi ya girgiza kai yace "uhm'uhn that's not wat I meant Arham, calm down and sit let's talk please, banga abin zafin nanb......" wani irin buga table dinshi Arham yayi da hannu yay kara yace "don't fucking tell me to calm down, on what account zaka dinga tambayana menake da kudi sabida ka daukemin dawainiyar kaina kana saima mamana yar buhun shinkafa da wake, Waleed ni kakema gori sabida kaga Allah bai horemana kaman kuba eh? Ni kake ma gori Waleed, am talking to you kamin shiru are you stupid"? Arham yadakama Waleed tsawa dayasa Waleed yaji ranshi yabaci dan ba'amai tsawa koda yana yaro baima sababa, tashi kawai yayi dan baiso yabiye mai suyi fada yay wajen hanger dayake makala suit dinshi yaja yadauka zai saka, wani irin shan gabanshi Arham yayi da jajayen idanunshi ya kalli Waleed yanuna kanshi da hannu yace "ni kakema gori Waleed, sanan inamaka magana kamin banza ni kake ma gori"? Kasa saka jacket dinma Waleed yayi sabida ihun Arham dayake mai a kunne kaman zai fasamai dodon kunne yamaida jacket din yarike a hannu sanan ya kalli Arham yace "since you are too dumb to understand a simple question dana tambayeka then take it anyhow you wish to take it" yana gama maganan yadau wayanshi daga kan table zai juya yay kofan fita Arham yasha gabanshi yace "ni kakema gori"? cikeda mugun bacin rai da kulewa da maganar Waleed yace "nayi, kai duk abinda kaga dama" kaman amafarki Arham bai wata wata ba ya daurama Waleed wata lafiyayyen mari ata gefen ido dan marin har yadan taba idanunshi na side din dama jikake kau! Idan Waleed yace he was expecting a slap from Arham he is lying, jin saukan mari yayi kawai daga sama baisan lokacin daya saki wayanshi da jacket din dake hannunshi akasa ba suka fadi, wani irin fincikanshi Arham yayi ya bugada bango bayanshi yabada bam, Arham ya shakemai wuya, cikin kunfan baki da mugun tsana yace "sabida rashi da talauci yasa am working under you, yaro dakai u are just 28 inada 35yrs na girmeka da shekaru shidda zaka tsaya kana gayamin magana yanda kaso, daman hausawa sunce yaro da kudi babba yake dawowa, this can not work with me, yau saina koyama hankali, I will teach you a lesson, fight me back now, fight me back" har alokacin Waleed was shocked yama kasa yarda Arham dinshi ke fada dashi haka, ya shakeshi yana neman kashe shi idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi sun fito, fuakanshi tai jajir abunku da farin mutum, ahankali ya iya yataba hannun Arham dake wuyanshi muryanshi bata fita sosai yace "u.....are....hurt.....ing me blood.....am....am.....my....my.....breath" yay maganan about to die amman Arham baida alamun sakinshi saima kara shakeshi dayayi yace "I said fight me, fight me mana, I want you to fight me dan Allah inka isa, kai fada dani kaga yanda zan baka kashi, na farfashe maka wanan bakin dakake min gori dashi kan kasayama Mahaifiyata wanan shegen tsukukun gidan kaman gidan kiwon kyankyasai, da shegiyar akurkan motar nan, inda don Allah kakeyi da tikeken gida zaka saya mata irin naku mansion, mota mai numfashi bata manoma ba, yau saina nuna maka kudin ka bazai iya taimakonka a hannunna ba, I will deal with you yau Waleed, wlh saikai fada dani zan kyaleka na rantse maka" daidai lokacin akai knocking kofar office dinshi, sake shakeshi yayi to the extend this time idanunshi sun soma juyawa gashi yakimai komi dan he can't raise his hand on his friend or hurt him in anyway ba, da kyar hannunshi ya iya komawa baya dashi yatataba flower verse din dake kan table dinshi ya kabar dashi kasa yay kara akasa sabida wanda ke waje ke knocking kofarshi yaji ya shigo, jin karan flower verse yasa Mama Iyami tace "subhallahi karan menene wanan" ta murza handle din kofan kawai ta shigo ciki, ganin yanda Arham ya shake Waleed yasa da sauri tai kansu yace "Mr Arham innalillahi wa innailaihi raji'un, wats happening here? Meke faruwa haka? Kaida abokin ka, let him go, sakkashi kaga" ta shiga kokarin fincike hannun Arham daga wuyan Waleed, cikin fushi Arham yace "wlh bazan sakeshi ba saiyay fada dani, sainaga uban karfin dayike dashi dayake juyani yanda yakeso sabida yaga yanada kudi dan ubanshi" ganin yanda Arham ya harzuka Waleed na neman mutuwa a hannunshi yasa tafita daga office din da gudu ta kurma uban ihu. "jama'a kuzo kutaima keni, Dr Waleed Warbai and Mr Arham are fighting, please helppppp" ihunta gabaki daya yadauki gidan marayun, da gudu wasu staff din Waleed da yaran gidan marayun damasu shara, gardeners da waye da waye aka shigo office dinshi da gudu, Nura dawasu maza hudune suka fizge Arham, suka jashi baya Waleed kuma yay baya zai zube wasu ma'aikatan suka tareshi, da gudu Iyami tafashe da kuka tace "innalillahi is sir alive jama'a?" wani ma'aikaci ne mai suna Auwal yace "he's alive but sai ankaishi asibiti" da sauri suka fita dashi daga office din, Mama Iyami tajuya ta kalli Arham dake huci yana tsaye ya fizge kanshi daga rikon da akamai tace "Mr Arham meya hadaka fada da abokin ka eh, dan uwanka fa, blood naji kuna kiran junanku, Mr Arham meya hadaku dashi" cikin wani irin fushi Arham yace "kije ki tambaye shi mana, dayake shi ogan kine bazaki iyaba shine yabaki aiki, yana baki na abinci bazaki iya tambayanshi ba, amman dayake ni kin rainani dole kitasani agaba kina tambaya, matsiyatan mutane, masuyin boyi boyi dan abasu kudi, fatararru kawai" yay maganan fuuu yafita daga office din ma'aikatan kowa yabishi da kallo ana mamakin tome yahada su tsawon shekaru nawa ba'a tabajin kansu ba saiyau, motarshi ya shige yaja motar yawuce yabar orphanage din. Staff, ma'aikata, yaran gidan marayun aka fiffito aka taru awaje, daman ance bad news yafi yanda wuri nanda nan aka cika ko'ina, aka cika gaban clinic da saida Dr Kemi da Dr Ayo suka kira security gate biyu sukazo, akasa kowa yakoma various places dinsu, Baba Mani ne kawai da Mama Iyami aka bari suka shiga asibitin har zuwa dakin da aka kwantar dashi likitoci akanshi ba'a bari sun shiga ciki ba, fuskarshi tai mugun jan da saita baka tsoro, gefen idanunshi na dama ya kumbura dan hardan tsagewa yayi jini yadan fito, kasa daurewa Mama Iyami tayi ta fashe da kuka a rayuwa tanason Waleed, bata taba haihuwa ba, mijinta yarasu, an koreta gidan haya yazo batada inda take kwana, abakin titi takoma tana bara tana tara kudin datake samu danta kama haya, wata rana tana cikin baranta taga anyi parking, Waleed yafito kai tsaye yace mata mesa kike bara Mama, tace banda kowa, mijina yarasu, banda y'aya Allah baitaba bani haihuwa ba, ankoreni agidan haya, bara nake natara kudi nasami matsugunni, budan bakinshi bazaki kara baraba, sanan yajuya yay wajen motarshi yace zomuje, gabanta nafaduwa amman hakanan taji zuciyarta nacemata tabishi, motar ta shiga, yana zaune agefenta ga basket da alamun abinci ne aka dafamai agida, dauka yayi duka basket din yabata yace kici, budewa tayi ta shigaci kaman bata tabacin abinci, yakaita gidan marayun shi, yakaita asibitin shi yasa tai wanka, aka kawo mata kayan asibiti tasaka yadubata tsaf bata dawani ciwo sai maleria yay treating nata, sanan dakanshi yakaita girls hostel yabata daki na musamman dake dauke da komi sanan yace "aikinta kawai ta dinga kulamai da activities din yaran nan, she's in charge anan section din, zai dinga biyanta duk wata, sanan yasa akayo mata dinkunan kaya masu kyau aka kawo mata, tundaga ranan kulada ita yake to the extend har Ammi tasani tanada number ta, Ammi data ambata aranta yasa taciro wayarta ta shiga neman number Ammi tana kuka sosai, kaman wayan zata katse sanan Ammi ta dauki wayan, cikin kuka Mama Iyami tace "Allah yataimaki Hajiya amin afuwa hala ban kira alokacin daya kamata ba, amman dolece tasa nakira" takara wani irin rushewa da kuka dayasa gaban Ammi ya shiga dukan uku uku tama kasa magana tsabagen faduwan gaba dan tanada hawan jini, Mama Iyami cikin kuka tace "Hajiya kome kikeyi kibarshi kizo ba'asan ko karshen ne yazo ba, wayyo Allah na Hajiya" takara kecewa da kuka dayasa Ammi bakinta yafara motsi tana kokarin furta magana takasa dakyar tana wani irin nishi tace "k.....kar.....shen wane.... Iya.....mi"? Cikin wani irin mahaukacin kuka kaman wacce akama mutuwa Mama Iyami tace "karshen Dr Waleed Hajiya, Mr Arham yama Dr Waleed shegen duka, yanzu haka Dr Waleed baisan inda kanshi yakeba, likitocin mu gabaki daya na kanshi baisan inda kanshi yakeba ana kokarin ceto rayuwanshi, saisa nace kizo idan ma cikanwan ce yacika agaban ki, ai Mr Arham bai kyauta ba da kyar muka kwaci Dr Waleed a hannunshi Hajiya, dan Allah kizo yanzu koda karshen ce yayi ta a hannunki, wayyo Allah na Dr Waleed" tarushe dawani rikitaccen kuka tana katse wayan, majina shabe shabe. Wani irin baya Ammi tayi zata zube akasa daidai lokacin mai aikinta tafito daga kitchen dauke da katuwan kulan abinci, wani irin sakin kulan tayi akasa tai kan Ammi da gudu kafin Ammi ta zube ta tareta tareda ihu tace "Hajiyaaa!" duk masifar Ammi tana bala'in sonta dan tayi aiki a gidaje da dama bata tabayin aiki agidan dataji dadi irin na Ammi ba, ganin Ammi ta sume yasa ta kuma ihu. "Mai gadi, direba, duk wanda yake awaje ya shigo ku taimake ni, Hajiya ta suma" da gudu ma'aikatan gidan suka shigo, su mai gadi naganin Hajiya assume sukai kitchen suka fitoda ruwa agora yayyafa mata ruwa sukayi tawani irin sauke ajiyan zuciya tare da bude idanunta, ahankali take kallonsu one by one, kafin ahankali tace "ku kaini wurin Waleed gida a orphanage, dan Allah ku kaini wurin Waleed dina a orphanage". [11/1, 11:47 PM] Re@lšŸ–¤ K@usy šŸ”: šŸ’« _TWO DIFFERENT WORLD_ šŸ’« āœļø M SHAKUR 2ļøāƒ£9ļøāƒ£ FREE PAGE Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji

Chapter 17 of 20