Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
bisa jikin ƴar iskar Antynta ta ɗora ruhina tsabar mugunta,amma zan rama nan da kwana uku komi zai je daidai kamar yadda mu ka tsara" "Ki na ganin Aliyu zai yarda ya auri Suby?" Karime ta tambaya. "Mi zai hana? In ma bai yi don Allah ba zai yi don tsiya,tun jiya na so ya kawar da budurcin Suby amma yaron nan mai taurin kai ya tafi gidan shi" "Ni zan so su yi komi bayan aure kar mu je ayi biyu babu,ba ta ga Aliyun ga shi kuma ta rasa budurcinta" cewar Karime . "Hum! Sai kace ba ki san ni ba? Ko ko kin manta ni ne? To ki tsaya ki ji auren Aliyu da Suby ki ƙaddara ma har an yi shi" Hajiya ta faɗa ta na susar bayanta. "To Hajiya bari na je na kwanta sai da safe" Karime na gama faɗa ta bar Hajiya ita ɗaya. Kamar jira suke abokanta suka bayyana cikin ɗakin, meeting suka fara kafin ɗaya daga cikin su ta baiwa Hajiya wani garin magani "ki karɓi wannan ki tabbatar kin sa ma Yayar Bahijja shi cikin kayanta na jiki da zarar kin yi haka doli za ta barin gidan" Hajiya ta karɓa ta na cewa "gobe zan koma gidan ai,ku na iya tafiya amma kar ku manta ranar biki ku zo na gayyace ku a suffar mutum za ku zo" "Ina jin tsoro Hajiya kar asirinmu ya tonu " "Matsalata da ke kenan,mugwar siffarki ki aje ta gida ko ba a koya miki yadda ake yi ba?" "An koya min amma ban taɓa gwada wa ba saboda ina gudun a samu matsala" "Mtsw ba ki ga lokacin da zan tafi neman auren Aliyu ba sai da na ajiye duk wata muguwar siffa ba? To ke ma kiyi haka" ★Washegari Ina zaune gefen gado Aliyu ke shiryawa cikin wani farin yadi.Na dube shi a karo na ba adadi na ce "Aliyu jiya mine ne ka sha da ya saukar ma da mugun feeling?" Da mamaki ya dube ni ya ce "feeling ? Ni? Mi ki ka gani?" Shiru na yi ban ƙara cewa komi ba. Ya na gama shiryawa ya zo inda nake a zaune ya yi min sumba kafin ya fita,addu'a na bisa da ita kafin na fito falo. Ina shirin zama Hajiya ta shigo babu ko sallama sai ƙamshin turare ke tashi irin na ƴan bori .Gaisheta na yi,ta amsa ciki-ciki kafin ta ce ma Iyani" yau kuma ku biyu ne gidan?" "A'a Murja na toilet ta na wanka" ba ta sake cewa komi ba ta shiga ɗayan ɗakin,sam ban yi tunanin wani abu za ta yi ba kawai na barsa ƙila kayanta na riƙe da hannu za ta aje. Ko minti biyar ba yi ba ta fito,kan kujera ta kwanta ta lumshe ido. Cike da mugunta Hajiya ke kallon Bahijja da Iyani ta ƙasan ido,so take ta nuna masu kamar ta na bacci. Murja ta fito daga wanka hankali a ɗan tashe kafin ta shiga ɗaki ta ɗauko jakar kayanta."Bahijja zan tafi na dawo" ta ce min ta na mai ficewa ba tare da ta ko tsaya ta ji amsa ta ba. Fitar Anty Murja da kamar minti goma Hajiya ta fara nasarin bacci yayin da kuma Baby ta fara wani irin kuka kamar ranta zai fita.Duk ruɗewa na yi saboda ta ƙi shan madara,an yi mata wanka an cire kayan jikinta amma ta ƙi yin shiru. "Ki bata ta sha ƙila za ta yi shiru" cewar Iyani,na karɓi Baby.Jikina tuni ya bani wannan Baby ta biyu ce amma na daure na ɗora mata abincinta,sha ta fara ta na kuka ƙasa-ƙasa kafin ta yi shiru. Zut! Zut! Zuuuuuu haka nake ji kafin na farga ta tsotse duk madarar da ke ciki,kamar an yi min doli haka na maidata ga ɗayan mamar nan ne na ga ikon Rabbi.Tamkar ana jan raina haka na fara ji,ban san ta yaya ba naji na fizgo kalmar "ya rahamane!!" Ina mai cire mamar a bakinta,in ba idona suka gane min ba daidai ba tabbas jini na gani ya na ɗiga a mamadin madara. Na sa hannu na laƙuto sai kuma ya koma fari ƙal kamar rufa ido, Baby na kalla wacce ta ke wani min fari da ido. "Ban san mi ke damun ki ba,haka ban san mine ne tattare da ke ba amma haka kawai nake jin ke ba alkhairi ba ce a rayuwata.Zan bar shayar da ke daga yau tun da dai akwai madara,gobe zan sa Aliyu ya ƙaro miki wata" Cikin sakwani biyu Baby ta canza wanda ya yi daidai da tashin Hajiya . "Ban gane ba za ki ƙara shayar da ita ba? Gaya min dalili?" Shine tambayar da Hajiya ta yi min .Sosai na yi mamakin yadda aka yi mai bacci ya ji maganar da nayi duk da ƙasa-ƙasa na yi ta. Wani murmushi na yi wanda ni kaina ban san na mine ne ba na ce "eh Hajiya saboda babu ruwan nono madara za ta rinƙa sha" ai kuwa Hajiya ta hau ni da masifa "sai in ke za ki sawo madarar amma ba dai Aliyu ba" "sai yunwa ta kashe ta kowa ya huta amma ba zan sake shayar da ita ba" kamar wacce ta sha wani abu haka na koma ranar har sai da Hajiya ta yi mamaki,a ƙarshe dai ta bar gidan bayan ta gaya min kalma " za ki gani" Ko da Aliyu ya dawo bai tambaye ni Hajiya ba haka ni ma ban yi masa ba.Matsalata guda a yanzu shine ina Anty Murja ta shiga tunda na kirata wayarta ba ta shiga, Umma kuma ta ce har yanzu ba ta je can ba. Yau ma Aliyu sai da na rage masa zafi mugun feeling yake fama da shi,ita kuma Baby kukan duniya ta yi shi amma na ƙi shayar da ita a doli ta sha madara. Cikin juyayin sauyin rayuwa da kuma ɓatan Anty Murja aka yi zanen suna,ranar buki Umma ta zo sai na ga duk yanayin ta ya sauya. Na yi niyyar tambayarta dalili amma ta ƙi bani fuskar haka,ana tsaka da buki ta ja ni gefe. "Bahijja daga yau ina so ki koma wankan da ruwan kunnuwan magarya,sannan ki rinƙa karanta surorin ukun ƙarshe da ayatul ƙursiyu da kuma amanar rasulu ki na sha hakan zai warkar da ke da ciwon duk wani sihiri" Umma ta faɗa min tare da yi min nasiha mai ratsa jiki "duk tsanani kar ki mijin ki ya gundire ki,kar ki gaji balle ki ɗauki aniyar barinsa." "To Umma in shaa Allah zan yi duk yadda ki ka ce.Shikenan anty Murja har yanzu ba ta dawo gida ba?" Na tambayi Umma. Baki kawai ta ja ta sauke ajiyar zuciya kafin ta yi min sallama. ★Bayan buki Yau kwana na arba'in har da kwana biyu a sama amma jinin biƙi bai da niyyar tsayawa,a kullum sake bulbulo min yake.Tun ina jin kunya har na yi ma Umma maganar,addu'a kawai ta ce na ci gaba da yi.Ɓangaren Baby kuma har yau ba ta sauya zane ba,duk da Aliyu ya yi nacin duniya amma fafur na ƙi shayar da ita. "Bahijja ban san mi ki ka ɗauke ni ba, kin hana ma Ƴata abincinta haka ni ma kin ƙi karɓata a kullum sai ki ce jinin bai ɗauke ba.Wai ko zina ki ke so na fara yi?" Aliyu ke faɗar haka cikin ɗaga murya kamar zai dake ni. "Ta ya zan shayar da yarinya da duk sati sai an canza mata robar feeding? So kake ta tattaune min mama? Ka na fa gani yarinya kamar ɗiyar aljannu gwangwanin madara bai yi mata kwana uku ta shanye shi" cikin masifa ya katse ni da "Ni kuma mi yasa har yanzu kin ƙi bani haƙina? Ko ko ni ma renon Aljannun ne tsoro ki ke ji na zazzage miki abu?" Na ce "tunda *BOKANYA* ta yi ƙulle-ƙullenta ta yaya jinin zai tsaya? Ai wlh ko da na ga Hajiya ta na sa ma wannan ɗan banzan feeling ɗin na riga na gano nufin...." Ban ida kai ƙarshen kalmar ba Aliyu ya ɗauke ni da mari,yayin da Baby ta fara dariya har da ƙyarƙyatwa. Wannan karon ba ni ba hatta Aliyu sai da ya firgita,a tare mu ka kalli inda Baby ke kwance kafin mu kalli juna. Da sauri na ce "Aliyu ka ga abinda na ke gaya ma ko? Ina ce dai ka ji dariyar da jariri ƴar wata biyu ta yi?" Shiru ya yi ya na kallon Baby. "Ki kwantar da hankalin ki Bahijjana,ko ma su uban waye suka shiga jikin ƴata za su fita a yau,ɗauko hijabin ki mu tafi" Aliyu ya faɗa ya na sungumar Baby. A mota na tarar da shi kafin wuce,gidan wani malami ne mu ka je. Albora shine sunan shi, Baby ya karɓa wacce ta rumtse ido,ya yi murmushi kafin ya saka ta cikin wasu ruwa a doli ta buɗe idon ta na kuka. "Aljannu sun yi ma ƴar nan illa sun mayar da ita kamar wata shago su shiga su fita duk lokacin da suka ga dama" cewar malamin ya na mai yi mata karatu, Baby sai kuka take wanda ka na jinsa za ka gane babban mutum ne ba Jaririya ba. "Ga wannan ruwan ku rinƙa yi mata wanka da su kullum,sannan ku shafa mata man zaitun" Malam Albora ya faɗa ya na mai miƙa ma Aliyu. Mu na fitowa Aliyu ya ɗauki hanyar Kwalo,duk yadda na nuna rashin amincewa bai saurare ni ba. Mu na isa mu ka tarar da wani tashin hankali,kaf iyalan gidan sai koke-koke suke.Hankali tashe Aliyu ya ce "mi ke faruwa?" Ya Yusuf ya bashi amsa da "Hajiya ce ta rasu".... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5