Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
shiga ɗakin Hajiya wani irin hayaƙi ne ya turniƙe kai kace madafa,tari na fara yi babu tsayawa ina shirin fita na ganta tsaye ƙiƙam a gabana ta cika wajen kai kace Basamudiya. Wuyana ta kamo ta matse gam da manyan aikaifunta sai kuma ta yi saurin sake ni. Na yi baya na faɗi ina jin jiri,ɗakin na juya mini. Ban san abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni a gadon asibiti,hannuna an rataya mini salkar jini.Aliyu ya shafi kaina ya ce "Ban san mi yasa ki ka sha maganin zubar da ciki ba,ga shi ya yi miki illa sosai duk da cikin ya zube kin zubda jini sosai" Na waro ido jin furucinsa,yaushe na samu cikin har na sha magani ya zube? Ban kai ga samo amsa ba na ji muryar Hajiya daga can waje ta na cewa "ai doli Aliyu ya rabu da ita wannan mai farar ƙafar,tun da ta shigo gidanmu ahalina ke fuskantar matsala" "Kar ki damu da zancen Hajiya don ba zan iya sakin ki ba,ke rayuwata ce" Aliyu ke faɗa ya na mai ci gaba da shafar gashina. Ido na lumshe ina tunanin abin da ya faru da ni kafin hankalina ya gushe,tabbas Hajiya ce silar komi na kasa gane dalilinta na yin haka. Sati guda na yi cur a asibiti kafin na dawo gida,tun kwanciyata Hajiya kullum sai ta je asibiti a siffar mage ta na bani tsoro.Kar ku tambaye ni ta yaya na san haka saboda ni kaina ban sani ba abin da na sani shine ina tattare da wani sirri na daban wanda ya ke ci ma Hajiya tuwo a ƙwarya. A sannu a hankali lokaci ke tafiya,kullum in na yi waya da Umma sai ta bani shawarar na ci gaba da yin addu'a. Na zame ma Hajiya ƙadangaren bakin tulu,ƙarara ta ke gwada mini ƙiyayya a gaban idon Aliyu kuma kamar za ta goya ni. Kun san tafiyar saƙa? To haka mu ke ni da Hajiya.A yau na zauna na yi tunani sosai,abin da na yanke shine barin gidan nan. Aliyu na zaune ya na kallo na zo na haye masa ƙafafu,duk hankalinsa ya tattaro ya maido kaina.Baki na turo a shagwaɓe na ce "My Haidar na gaji da zama ni ɗaya a nan duba fa ka gani kullum sai ka shiga gari saboda aikin ka sannan ka dawo a gajiye,mi zai hana mu koma can da zama kawai" sai da ya haɗiye wasu yawu sannan ya ce "haka kike so?" Na gyaɗa masa kai ya ce "dama tun farko haka na tsara to Hajiya ce ta tsara lalle a nan za ki zauna" kukan sangarta na sakar masa,ban bar sa ba har sai da na tabbatar na ci galaba a kansa . Washegari tun da safe zage-zagen Hajiya ya tashe mu daga bacci.Shegiyar akuyarta sai kuka ta ke,duk fitowa mu ka yi.Yayun Aliyu sai haƙuri su ke bata yayin da shi kuma ya sunne kai. "Tun da ya zama mijin ta ce ai shikenan sai ku yi ta tafiya"Hajiya na gama faɗar haka ta shige ɗakinta. Ban zo da komi ba sai kayan jiki wannan ya saka su kawai na ɗauka,bayan na yi ma ƴan gida ban kwana zan juya na nufi ƙofar fita nan fah wani al'amari ya faru akuyar Hajiya ta kubce tare da nufo ni a tsiyace...... Please share [28/10 à 11:52] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Page 4 Na waro ido tare da yin tsaye ƙiƙam har sai da akuyar ta zo gat da ni ta saka ƙawonninta za ta tinne ni,ai kuwa na yi mata wata bangaza tsiya har sai da ta faɗi. Shegiyar Akuwayar nan ta miƙe ta ƙara ƙoƙarin kai mini karo nan ma na ci galaba kanta,kunnuwanta na riƙe da dukan ƙarfina.Ban san inda na samo ƙarfin ɗaga ta ba kawai sai gani na yi na fara garata tamkar majaujawa na yi cilli da shegiya ta bugi ƙaton icce da ke tsakar gidan. Tamkar wacce ta yi tsere haka na fara sauke ajiyar zuciya,yayin da matan gidan da yaransu su ke tsaye su na kallon ikon Rabbi. Rahila sam ta kasa ɓoye farin cikin da ta ke,da murnarta ta ƙaraso guna ta na cewa "Bahijja fatan ba ki ji ciwo ba? Masha Allah ai gwara da ki ka yi magan..." Maganarta ce ta yanke lokacin da wasu dattija mata biyu su ka shigo. Wani abun da ya bani mamaki gun akuyar suka nufa su na shafarta "Bahijja ke fa na ke jira tun ɗazu" Aliyu ya faɗa daga bayana.Hakan yasa Rahila ta saki hannuna ta na yi min fatan sauka lafiya. Hanyar Niamey mu ka ɗauka ni da Aliyu ,ba mu yi awanni uku ba mu ka shigo garin.Gidan da ya ɗauka haya wanda ya ke rayuwa tun tuni mu ka sauka.Gidan ciki biyu ne da babban falo sai toilet, kitchen kuma na can daga waje.Tsarin gidan ya burge ni sosai,wanka na shiga yayin da Aliyu ya ce mini zai tafi nemo mana abin da za mu ci. Har sai da na shirya na canza kaya sannan ya dawo.Dambun shinkafa da soyayen kifi ne ,sai da mu ka ci mu ka ƙoshi kafin mu zauna ya na yi mini hira dangane da garin Niamey . Sauraren shi kawai na ke,amma hankalina na can Kwalo.Sam tunanin abin da ya faru ya kasa fita kwanyata,sannan matan nan biyu da ban san su waye ba na hangi wani lamari a tattare da su. "Ya dai?" Aliyu ya faɗa tare da bubuga kumatuna,na ja ajiyar zuciya kafin na ce "Ni kuwa Aliyu miyasa Hajiya ke Bokanci?" Tamkar saukar aradu haka tambayar tawa ta ratsa Aliyu ,na fahimci haka ne duba da yadda ya zabura da kuma yadda ya ke jifana da wani mugun kallo. "Ban gane Bokanci ba,wace Hajiyar dai tukunna?" Ya yi tambayar ya na tamke fuska. "Hajiyar ku mana,ko kai ba ka da labarin abin da ta ke?" "Mine ta ke? Bahijja ki na cikin hankalin ki kuwa? Bari ganin ina yi miki mugun so yasa duk maganar da ta fito bakinki ki rinƙa yaɓa min ita ,sam ba zan lamunci haka ba" ya na gama faɗa ya fice ya bar min gidan. Na taɓe baki na ɗauki wayarsa na kira Anty Murja,bayan mun gaisa ta bani Umma.Tambayar farko da Umma ta yi mini ita ce "Bahijja a ina ki ka jawo magana? Mi ya kai ki shiga hurumin da ba na ki ba? Kin san illar Akuyar da ki ka yi faɗa da ita?" Shiru na yi ina nazari ta ya aka yi Umma ta san haka? Koko dai uwar tawa ce *BOKANYA* banda labari? Umma ta katse min tunani "ki na ji na ko Bahijja? Ki ƙara dagewa da addu'a kar ki yi sake! Sannan gobe ki tashi da azumi ki wuni cikin zikirori kin ji?" Da "to Umma" na amsa ita kuma ta ci gaba da cewa "kar ki saki ki yarda da mutane saboda ana haɗa kai da uwanda ka aminta da su wajen cutar da kai,abu na gaba da zan faɗa miki shine ki so mijinki ki yi masa biyayya kar ki sake yi masa maganar da za ta ɓata ransa wacce za ta kai shi da yin fushi da ke!" Zanrukan Umma sun ƙara saka ni cikin duhu sai ya zan yi? Doli na yi biyayya akan abin da ta ce. Aliyu ya shigo ya na kallona,na turo baki ina kashe waya na miƙa masa abarsa.Hannnuna da wayar duk ya haɗa ya riƙe gam kafin ya fizgo ni,a doli na miƙe tsaye.Ƙara jawo ni ya yi ya haɗe da ƙirjinsa,da sauri na rufe ido saboda a duk lokacin da yake mini irin wannan kallon na kan tsinci kaina cikin shauƙi. Ban yi zato ba na ji bakinsa kan laɓana,tun ina kakauce masa har na haƙura na bada kai bori ya hau.Dariya ya shiga yi mini,cikin jin haushi na fara dukan ƙirjinsa haɗi da ture sa."Allah zan cije ka,kuma sai ka san wa ka yi ma dariya " na faɗa kamar zan yi kuka.Aliyu ƙarshen ɗan duniya ne,maimaikon ya rabu da ni sai ya kama haɓata ya fara cizawa a hankali ta yadda ba zan ji zafi ba. Tamkar fitar iska haka idona ya yi tozali da wani baƙin hayaƙi,ya na fita ta window.Na zabura na ci karo da ƙirjin Aliyu ,da sauri ya janye daga jikina ya tashi zaune haɗi da jawo ni "mine ne uhum?" Kai na girgiza masa. Ya ja dogon hancina ya sake cewa "shine kuma ki ka firgita?" Na marairaice fuska na ce "wanka zan yi" ya ɗaga min gira ɗaya ya ce "ko na yi miki?" Kafaɗa na maƙe kafin na je na yi wankan gabanin shi. Da dare ma abinci waje mu ka ci tun da har yanzu ban gama tsara komi ba.Aliyu na zaune a falo ya na kallon tv na fito cikin riga da wando na bacci,aza ƙafata cikin falon ke da wuya wata baƙar mage ta shigo ɗakin ta na kuka. Aliyu ya ce "ina sauran abincin nan ?" "Mi za ka yi da shi?" Na tambaye shi."Mage zan ba ni shaf na manta da ita,kullum nan ta ke cin abinci" har zan yi magana sai kuma na tuna da nasihar Umma. Sauran abinci na ɗauko,ga mamakina sai na ga ya fita waje ya ɗauko wani tsohon plate ya zuba mata abinci.Ci ta fara yi ni kuma ina kallonta,kusa da Aliyu na zauna ina kallon Film ɗin da ya ke kallo. "Yanzu duk wannan bom ɗin da ke tashi ba gaskiya ba ne?" Na tambayesa ina kallon yadda wuta ke tashi cikin tv.Ya jawo ni ya ɗora kan cinyarsa ya ce "duk cikin ɗabi'un ki ƙurciyarki da wautarki sun fi komi burge ni!" Na turo baki ina gunguni saboda babu abin da na tsana irin a raina min shekaru. "Haba ƴar ƙwaila ta wannan fushin fa?" Aliyu ya tambaya,cikin son ƙara nuna masa ina fushi na juya masa baya nan idona ya yi baƙin gani. Idanuwa shidda na gani jere ras ta jikin window sai dai babu fuska,da ɗan yatsa na yi wa Aliyu nuni ko kafin na furta wata kalma sun ɓace ɓat.Na miƙe tsaye ina sake kallon windown amma babu komi,shiru na yi ina nazari duk tambayar duniyar da Aliyu ke yi mini ban basa amsa ba. "Kira mini Umma dan Allah" na faɗa kamar zan yi kuka,zai yi magana na fara dire-diren ƙafafu doli ya kira min ita. Bedroom na shiga na labarta ma Umma komi "Yauwa yanzu abin da za ki yi ki samu ruwa masu kyau ki tofa addu'a sai zuba su a duk wani bango na ɗakin" Umma na gama faɗa mini haka na kashe wayar na yi kamar yadda ta ce. Aliyu dai sai kallona ya ke.Sai da na gama na ce "ban san mi na yi ma wannan matar ba ta ke biya ta da sharri ! " "Wace matar?" Aliyu ya tambaye ni,yi na yi kamar ban ji sa ba na shige ɗaki na yi kwanciyata. Washegari ina kitchen ina soya wainar ƙwai Aliyu ya fito rataye da jaka,fuskarsa ba walwala.Ko kafin na kai ga tambayarsa ya ce "yanzu Ya Yusuf ya kira ni wai Hajiya ba lafiya jikinta ya matsa" "Allah bata lafiya!" Shi kawai na furta. "Amen! Ki kula da kan ki zan je ban sani ba ko can zan kwana" Na waro ido na ce "ina za ka tafi? Wai ba dai Kwalo ba?" Ya tamke fuska ya ce "Bahijja wace irin tambaya ce haka kuma?Ba ki ji na ce Hajiya ba ta lafiya ba?" "Allah tsare hanya" na faɗa ina mai ci gaba da aikina,"na aje ƙaramar wayata bisa table ki ɗauka ki fara amfani da ita kafin na sayo miki wata"Aliyu ya faɗa kafin ya fice. Cikin ɗaki na koma na ɗauki wayar Umma na kira ko gaisheta ban yi ba na ce "Umma gida zan dawo na gaji da wannan lamari,makircin matar nan ya yi yawa wai kin ji ba ta lafiya kawai daga zuwan mu jiya shine har ya kwasa ya koma.Amma lokacin da mu ke can..." Umma ta katse ni da "Bahijja irin tarbiyyar da na baki kenan? Uwar mijin na ki ce makira? Kul! Kar na sake ji kin faɗi haka,ko ba komi Ɗanta ki ke aure.Ya ya kin ɗauki azumin?" Na waro ido na ce "Umma shaf na manta wlh ,kin ga fah yanzu na gama haɗa abincin kumallo" "In dai ba ki ci komi ba tun tashin ki to ki miƙe da azumi sannan ki yi Azkhar ɗin da na ce" "To Umma in shaa Allah ! Ina Anty Murja?" Na tambaya , Umma ta bani amsa da "ta yi baƙi ne" "yanzu da safiyar nan?" "Hum! Bahijja ba za ki gane ba,masu neman magani" ban fahimci maganarta ba haka mu ka yi sallama. Almajiri na baiwa abincin kafin na zo na zauna na fara zikirori da addu'a,haka na wuni aikin nan har marice ya yi.Ina tunanin inda zan samu ƙanƙara wacce zan sha in an kira sallar magrib Aliyu ya shigo,na miƙe da murna zan tarbesa idona ya sauka cikin na Hajiya wacce ke biye da shi a baya....... Please share [29/10 à 10:08] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Page 5 Wata juriya da dakiya na aro ma kaina,yi na yi tamkar ban gan ta ba na yi tsalle na laƙanƙame Aliyu "Masha Allah barka da zuwa mijina ya jikin Hajiya da sauƙi?" Na tambayesa ina mai ƙara riƙesa. Dakyar ya sauke ni a ƙasa ya ɗan sosa ƙeya ya ce "tare fah mu ke da Hajiya!Ba ki gan ta ba ne ko mi?" Ya kauce ta yadda zan ganinta da kyau.Na waro ido na ce "laaa! Ai na zata gizo ta ke min kamar yadda ta saba! Hajiya ya jiki? "Na yi tambayar ina sakar mata wani murmushi. A cikin idon Hajiya na hango zallar takaici da baƙin ciki,sai da Aliyu ya ce "Hajiya ba ki ji ta na miki ya jiki ba?" Sannan ne Hajiya ta ce "au! Daga nan tsaye zan amsa ba za a bani gun zama ba?" "Wace ni Hajiya!? Ke da gidanki wa isa ya yi hakan? Bari na ɗauko miki kujera" na faɗa ina shirin wucewa in ɗauko mata kujera kawai sai ji na yi Hajiya ta bangaje ni.Ki gizau ban yi ba sai dai na ji wani mugun shock ya ratsa ni tamkar wuta ta raɓo ni sai dai dai ko 30s ba a yi ba ya fita daga jikina.Yadda mu ke kallon juna cikin ido na ke hango tsantsar mamaki a tattare da ita,ƙila ganin babu abin da ya same ni. Aliyu ya ja hannunta su ka shiga ɗaki,ni kuwa tsaye na yi ina tunanin miye nufin Hajiya? Na maida lamarin gefe na leƙa waje.Wani shago na hango nan kusa da gidanmu,na ga har da frigo/frigine da sauri na fita na sawo ƙanƙara.Tuni an fara kiraye-kirayen sallah,a tsakar gida na tarar da Aliyu na alwala a yadda ya haɗe rai ya tabbatar min fushi yake da ni.Ban kula shi ba na shiga ɗaki,a zaune na tarar da Hajiya ta yi ɗaiɗaya kan kujera.Waje na samu mai kyau na kwankwatsa ƙanƙarar sannan na zauna bayan na matso da kayan buɗe baki. "Ya Rabbil alamen ka tsarkake min zuciyata da dukan wani saɓon Allah,ka kare ni daga sharrin masu sharri, Ya Allah ina neman tsari daga sharrin aljanu da mabiyansu,da duk masu mugun nufi akanmu.Ya Allah yadda na shigo wannan gidan da aure Allah ka sa mutuwa ce silar fitata daga gare shi! Ya Allah ka azurta mu da zuri'a ɗayiba maza da mata masu farar zuciya.A ƙarshe ya Rabbi ka sa mu zame ma maƙiyanmu ciwon ido amen!" Ina gama jero addu'o'ina na yi addu'ar shan ruwa. Bayan na gama na je na yi sallah,daga inda na ke a can bedroom ina jin shashekar kukan Hajiya yayin da Aliyu ke faman tambayar ta lafiya. Na shafa addu'a na fito ina cewa "subahanallah Hajiya lafiya ko jikin ne?" Ba ta bani amsa ba sai harara da ta banko min. "Auta ka tashi ka mayar da ni garinmu tun da matar ka ta ce ba ta son zamana" Hajiya ta na gama faɗar haka Aliyu ya yo cikina da faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Nasihar Umma ta sake faɗo min hakan yasa na duƙa har ƙasa na ce "don Allah Hajiya ki yi haƙuri in na ɓata miki rai,Aliyu wlh na fi kowa murnar Hajiya ta zauna nan ƙila dai ba ta fahimta ba ne.Yanzu gaya min duk abin da ki ke so" Aliyu ya sauke ajiyar zuciya ya ce "tashi Bahijja sai dai don Allah kar ki sake,kin ga Hajiya ta tsufa ta na buƙatar kulawarmu sannan ba wata isassar lafiya gare ta ba" na gyaɗa kai na ce "to in shaa Allah mijina duk abin da ka ce haka za a yi,bari na je na gyara mata gun da za ta kwanta" ina gama faɗa na je na gyara ma Hajiya ɗaya ɗakin har da saka mata turare. Abinci na zuba mata da ruwa da komi tamkar basarakiya,ta na ci ta na ɓata fuska kamar an yi mata doli.Na kira Umma tun kafin na kai ga gaya mata Hajiya ta zo ta ce mini "ki kula da kyau ki yi taka tsantsan da matar nan saboda ta yi mugun shiri ita da ƙawayenta,ki ƙara addu'a gobe ma ki tashi da azumi" na ja ajiyar zuciya na ce "to Umma zan yi,amma ni gaskiya ban so ta ci gaba da zama nan" "Kar ki ce haka saboda da zarar kin nuna ba ki so to ta ci galaba kan ki.Kar ki nuna mata komi ki zama doluwa tamkar ba ki san komi ba,in shaa Allah zan tura miki maganin wanka da wanda za ki rinƙa shafawa" na yi ma Umma godiya na kashe waya. Da dare mu na kwance da Aliyu na ke shaida masa gobe zan tashi da azumi,yi ya yi kamar bai ji ni ba har sai da na sake maimaitawa."Yanzu saboda Allah Bahijja azumin mine ne ki ka tsiri yi? To ko ma dai mi za ki yi kar ki manta sai kin yi girkin safe da na rana da kuma dare.Babu wanda zai sani fita ina sayo abinci kamar wani gwabro" Na rungumesa ina mai cewa "zan yi mana ko saboda Hajiya! Gaya min abubuwan da ta fi so sai na rinƙa girkawa ina son yi mata surprise ka ga za ta ji daɗi sosai" Aliyu ya dube ni cikin ido ya sakar min murmushi kafin ya fara sumbatata. Addu'ar da ya saba yi kullum in za mu kasance ya fara karantowa ba tare da ya kashe hasken ɗaki ba,ido huɗu mu ka yi ni da wasu idanu uwanda ba su da fuska da sauri na janye daga garesa na kashe hasken ɗakin. Washegari na so tashi da azumi sai dai yadda idona suka matsa min da ciwo ya sa na ajiyesa dan doli. Duk yadda za ku iya ƙiyasta yadda nake ji to ya zarce haka,sam ko idona ban iya buɗe wa.Wani irin raɗaɗi haɗi da tsikara suke min,Aliyu shi kansa ya yi mamaki. Ina zaune kan kujera ta fito hannunta na ji ga haɓata yayin da Aliyu ke ƙoƙarin buɗe min ido,da sauri na jimƙe su gam."Ki buɗe Hajiya ta saka miki magani " cewar Aliyu ,na girgiza kai hawaye na min zuba na ce "a'a ban so ka kira min Umma" "mi yasa ki ke da taurin kai Bahijja? Wannan maganin ya na yi sosai tun ina yaro Hajiya ta taɓa saka min irin sa" Na fashe da kuka ina kiran sunan Umma,a can cikin madubin idona abubuwan ban tsoro ne iri-iri ake wano min sai dai na gwammaci haka kan Hajiya ta zuba min maganin da ba san na mine ne ba. Ta yaya? Ya aka yi? Ban sani ba,muryar Anty Murja ce ta ratsa falon.Ina jin haka na tashi zumbur,ina jin ta na gaishe su Aliyu kawai ya amsa yayin da na ji takun sawun ƙafafun Hajiya haɗi da ƙyaci. Anty Murja ta jawo ni a jikinta ta rungume,ban sani ba ta hanyar tsafi ne ko siddabaru kawai dai na ji idona sun daina ciwo kamar ɗaukewar ruwa. Na ware su kan fuskar ƴar uwata ɗaya tilo,cikin idonta na ke kallo inda a nan take wani haske ya fito daga garesu ya shiga cikin nawa.Har wani Flou na gani kafin na dawo ras,kun san wani abin mamaki? Hum! Hajiya ce ta fito da jakar kayanta wai Kwalo za ta koma. Aliyu na faman ba ta haƙuri amman ta ƙi a doli suka fita tare,Anty Murja ta saki murmushi kafin ta shafi kumatuna ta ce "zan koma kar ta ga na jima" kafin na kai ga tambayarta ta juya baya ta fice. Da sauri na fito amman wayam,har ƙofar gida na leƙa amma ban ga anty Murja ba.Wayata na ɗauka domin kira sai dai babu kuɗi,ina nan zaune jingum dabarar cin bashi ya faɗo min.Wayar Umma na kira sai dai har ta gama ringing ba ta ɗauka ba,haka ma ta anty Murja. Tun da Hajiya ta tafi ita da Aliyu ba su sake dawowa ba,shi ma ɗin ya na can garin wai ciwon Hajiya ya ƙara rikicewa.Ban wani damu ba saboda sam matar ba ta yi min ba, ɓangaren su Umma kuwa da na gaya masu abin da ya faru sai suka yi saurin kawar da zancen. Ina kwance ina game a waya na fara jin tashin zuciya,haka na fara daurewa can kuma sai amai.Maricen ranar sai ga Aliyu,da ya kai ni asibiti gwajin farko aka tabbatar ina da ciki. Tsabar murna Aliyu sai da ya rungume ni,haka mu ka dawo gida nan ya fara nuna min tsantsar kulawa.A kullum sai ya kira Hajiya da ya tambayeta jiki sai ta ce babu sauƙi a ƙarshe ta fara yi masa kuka da magiyar ya dawo kusa gare ta. "Aliyu ba fa zan koma Kwalo da zama ba,in ka gaji da ni to kai ni gidanmu.Ba zan je garin da ake firgita ni ba,to wai ma in mu ka je mu za mu bata lafiya?" "Bahijja in ke ba za ki je ba ni zan je! Saboda Hajiya uwata ce ni ta haifa ba ke ba ko ma *BOKANYA* ce ina son aba ta" "Au ! Yanzu ka yarda da maganar Bokancin? To madallah tun da har ka gane.Lokacin da ina Kwalo babu irin abin..." Ban kai ƙarshe ba ya sharara min mari ya na huci tare da nuna ni da yatsa "Bahijja duk yadda na ke guje miki sai kin san yadda ki ka yi kin ɓata min rai.To daga yau ki rubuta ki ajiye ni Aliyu ban sonki ban ƙaunar ki kuma wlh yau sai kin tafi gidan ku sakin ki zan yi" ya yi maganar ya na mai ɗauko takarda da abin rubutu. Wata muguwar dariya na ɗauka tamkar mahaukaciya kafin na kama wuyan Aliyu na shaƙe na ce "ku kun yi kaɗan akan ku sa Aliyu ya sake ni,wacce ta aiko ku ma ta kasa ne to ku je ku ce mata ta sake sabon shiri wannan bai yi ba" wani baƙin hayaƙi ya fita daga bakin Aliyu nan ya fara yin tari. Kallona ya yi ya ce " mi aka yi Bahijja wannan kallon na mine ne?" Shiru na yi ,sai kuma na basar na ɗauki madubi da zumar shafa hoda don na rantse da Allah yau sai na tafi Tillabery gun Umma. Da sauri na saki madubin jikina na rawa,kun san mi na gani? Fuskar Anty Murja kan fuskata....... Ga masu ra'ayi book ɗin nan 200 ne kacal duk wacce ta shirya biyan kuɗin karatu ta yi min magana ta WhatsApp +22795045822 [29/10 à 17:41] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Page 6 Aliyu ya matso ya ce "Bahijja ke ma kin ga abin da na gani cikin idonki ko? Wlh har sai da na ji tsoro" guntun madubin na ɗauko na sake dubawa a karo na biyu. Wannan karon fuskata na gani sai dai can cikin ƙwayar idona wani birbuɗin launin kore ke ɓacewa a sannu tamkar hayaƙi.Na lumshe ido zuciyata na ɗan bugawa Das!Das tamkar wacce ta yi arba da mutuwarta. "Bahijjana ???" Aliyu ya faɗa ya na rungumo ni,cikin ƙirjinsa na shige ina sauke wanin gwaron numfashi kafin na ce " Please ka kai ni gida gun Umma ina son yin magana da ita mai muhimmancin sannan don Allah mu tashi daga wannan gidan tsoro ake bani" bayana ya shiga bubugawa tamkar

Chapter 2 of 5