Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
wata Baby. Cikin so ya yi min magana wacce na ji ta har tsakar kwanyata "in shaa Allah Babyta duk abin da ki ke so shi za a yi,bari na kai ki gun Umma kafin ki dawo zan kama wani gida dama na sa ayi mana sabbin kayan ɗaki.Gaya min sai mi kuma ki ke so?" Na ɗan janye daga jikinsa ina zagaye cikinsa,ido cikin ido mu ke kallon juna.Ban sani ba ko na fara son Aliyu ne ko mi,kawai dai na ji wani shauƙi ya fizge ni.Ɗigirgire na yi ta yadda zan ƙara tsayi na sumbaci laɓansa,a yadda ya ke dubana ya tabbatar min abin ya zo masa a ba zata. Tattausan murmushi ya sakar min haɗi da jawo ni ya haɗe bakinmu.Sumba mai tsayawa a zuciya ya yi min kafin ya ja ni zuwa mota,sai da ya saya mini snack sannan mu ka kama hanya. Yau ji na nake wata sabuwar halitta,tsakanin Niamey da Tillabery babu wani nisa sosai hakan yasa mu ka isa cikin ɗan lokaci.Da mamakin matan da na tarar tsakar gida birjit na shiga ɗaki ina sallama, Umma ta fito ta na bayyana murnar ganina a fili. Bayan na gaisheta na je na yi ma Aliyu iso,cikin falo mu ka zauna Umma ta kawo mana ruwan sanyi. "Umma su uwancan matan mi su ke yi? Ko biki ake?" Na tambaya. "Masu neman magani ne kin Murja ta fara bada taimako,to wasu ma can ƙila ba za su samun damar ganinta ba" Dariya na yi irin ta in abu ya baka mamaki "Anty Murjar ce ke bayar da magani? Hhh! Don Allah Umma bari bani dariya.To wane karatu ta yi da har za ta zama likita?" Maimakon Umma ta bani amsa sai ta mayar da hankalinta kan Aliyu su ka fara hira,tashi na yi na fita. Wata ƴar buka na gani ta zana,sai da na yi dariya kafin na nufi ɗakin na shiga.Anty Murja ce a zaune ta kama kan wani yaro sai buga masa wutsiyar doki take,tsaye na yi ina kallon ikon Allah. Kuka yaron ya fara kafin aljanin jikinsa ya yi magana,a ƙarshe dai Murja ta baiwa uwarsa magani su ka fita. Ta dube ni ta ce "sai yanzu ki ka ga damar zuwa? Ina shi Aliyun?" "Anty Murja yaushe ki ka zama *BOKANYA* ban da labari? Ita wannan wutsiyar ta mice ce?" Na tambayeta ina mai kai hannu zan ɗauka wata irin wuta ta fito fatseee. Na zabura na yi baya ina waro ido,"kar ki take mata Ɗa" cewar Anty Murja ta na mai nuna bayana.Ihu na yi don kuwa ni ban ga kowa ba,dariya ta shiga yi min kafin ta nuna min waje na zauna. Bayan na yi zaune ne ta ce mini "Bahijja ita rayuwa da ki ke gani wani sa'in doli ce ke sa mutane yin abin da ba daidai ba.Ni magani na ke bayarwa ba na duba sai in ya zama doli,kuma aikina na yi kyau shiyasa ma ki ka ga mutane na rububina" Kai kawai na jinjina amma fah ban yarda ba, Anty Murja ta saki murmushi ta ce "leƙo ki gani" ta yi min nuni da ƙwarya gabanta wacce ke ɗauke da fararen ruwa. Na duƙa na kai fuskata ina kallo,na ɗan waro ido ganin Hajiya ta bayyana,kamar ranar farko yau ma da fararen kaya sai dai wannan karon a bakin wani kogi ta ke a tsaye. Idonta a rufe,ta riƙe baƙin Zakara kafin ta guntule masa kai jini ya fara zuba ya na tsarta cikin kogi .Abu kamar almara haka na ke kallonta kafin Anty Murja ta shafi ruwan duk komi ya ɓace.Murya na ɗan rawa na ce "Antyna don Allah mine ne Hajiya ke yi a nan? Allah sa dai ba raba ni da mijina za ta yi ba" wani kallon ƙasa-ƙasa Anty Murja ta ke yi min ba ta ce komi ba sai miƙewa ma da ta yi. Baya ta juya min sannan ta ce "Bahijja soyayyar da Aliyu ke yi miki ce ta fi ƙarfin tunani,ba dan a gabana aka yi komi ba da na ce asiri ki ka yi masa.Kaf ɗiyan Hajiya ita ta ke juyasu su da matansu,ke ce ki ka gagareta.Ta bayar da ruhinta ga aljannu,sun gindiya mata sharaɗin har abada ba za a haifi namiji ba cikin zuri'arta domin a cewarsu duk ranar da aka haifesa to ita a ranar za ta mutu.Kar ki yi tunani mutuwa irin waga ta duniyar a'a mutuwar duniyar matsafa wato duniyar da babu wanda ya san da ita sai matsafi,Mayu da dai sauransu.Bayan soyayyar da Aliyu yake yi miki mai ƙarfi to alƙalamin ƙaddara ya nuna tabbas ke ce ɗaya macen da za ta iya haihuwar namiji muddin ba ki rabu da Aliyu ba.Tun a ranar farko ta zuba magani a abincin da ki ka ci,manufar maganin shine ƙone duk wani ƙwan haihuwarki sai dai kash! Akuyar tsafinta ba ta karɓa ba wanda hakan ya nuna da matsala gwara ta baki makari" Anty Murja na zowa nan a zancenta ta juyo ta kalle ni da kyau kafin ta ce "ko ba ta baki magani wanda ya saka ki amai ba?" Kai na gyaɗa mata alamun eh ta bani. "Da kuma ki ka sha shine ki ka yi aman bala'in da ta zuba miki na san kin ga abubuwa dayawa tun dai ke ma ki na da aljannun gado " cewar Anty Murja.Jikina ya ɗauki rawa,tsoro nake ji a yanzun ita kuwa murmushi ta sakar min ta ce "na san doli ta shafa miki lafiya duk da hakan zai yi wuya amma faɗan da ya fi ƙarfinka ai sai ka mayar da shi wasa" "Anty Murja yau kuma wani lamari ya faru tsakanina da Aliyu,kuma....kuma da na duba madubi sai na ga fuskar ki a ciki mi hakan ke nufi ?" "Koma ciki Bahijja ina da patients a waje zan yi miki bayani daga baya" cewar Anty Murja ta na buga wata ƴar ƙarar rawa,nan wata mata ta shigo ni kuma na fita. Aliyu ya dube ni ya ce "Ni fa wucewa zan yi tun ɗazu ake jirana" na ja baki na ce "to ka kula da kanka sannan please ka yi addu'a sosai" murmushi ya sakar min kafin ya miƙe. Har mota na raka sa kafin na dawo ciki,abinci Umma ta zuba min na ci ba a wani jima ba na maidosa sai kuma zazzaɓi.Ƴan jiƙe-jiƙe ta yi na magani ta bani na sha na yi wanka daram na dawo garas,ita kuwa Umma ina lura da ita yadda ta ke kallon cikina.Wata kunya na ji ta kama ni,a doli na yi kwance ina tunanin rayuwa. Na lumshe ido da zumar yin tunani amman fuskar bokanyar matar nan ta zo ta yi min tsaye ƙiƙam,tamkar a gaske haka na ke ganinta fuskarta kicin-kicin ba annuri. A doli na buɗe idona na zuba su ga Umma wacce ke min wani kallo kamar mai son tantance wani abu."Bahijja ni kuwa mi yasa imaninki ya yi rauni? Dube ki har tunanin zuciyar ki ina gani saɓanin da duk yadda na so na bincike ki ban samun ƙofa" shiru na yi ina tunani can na ce "ya aka yi ki ka gane to? Mi ke sa imani yin rauni?" Ta ƙi bani amsa ta farko sai ta ce "daga lokacin da ka fara tunanin wani zai iya cutar da kai wanda ba Allah ba imani ya ragu,yarda da maganar masu duba ko wani abu da ya yi kama da haka" "To Umma ke ya aka yi...." Ban kai ƙarshe ba ta tashi ta bar gun ta bar ni cikin zullumi.Kaina ya sake ƙullewa na fara jero tambayoyi,ko ko dai haka ne da gaske saboda ina tunanin Hajiya za ta cutar da ni imanin nawa ya rage? To shin abin da Anty Murja ta nuna min shi ma duba ne? A bayyane na furta "lalle da buƙatar na shiga makarantar addini ta yadda zan samu ilimi sosai" da wannan tunanin bacci ya ɗauke ni. ★Sati na biyu a gidan Umma kafin na koma Niamey tare da rakiyar Anty Murja.Sosai Umma ta yi min sayayyar da ba ta samu ta yi min ba ta aure,duk wani abu da amarya za ta buƙata na same shi a yanzu. Sabon gidan da Aliyu ya kama mai kyau ne sosai don har da shubke-shubke sannan ya fi girma. Kayan ɗaki da komi na kitchen suma sun haɗu,a falo ya saka min ƴar ƙaramar frigine .A ranar da na zo tamkar wata amarya haka mu ka kula da junanmu. Washegari Laraba,wacce ta na cikin ranakun da ba zan taɓa mantawa ba. Tun da safiyar ta waye na ke jin shauƙi tare da ra'ayin samun nishaɗi.Tv na kunna na ƙure dukkan volume ina sauraren waƙa haɗi da rawa,na yi nisa sosai cikin shauƙi kafin a fara buga min gida kamar za a cire ƙofar. Tsuki na ja kafin na nufi ƙofa,ba tare da tambayar wane ne ba na buɗe gidan.Wata tsohuwar ƴar kimanin shekaru sama da ɗari ta faɗo min a jiki,hannunta ta ɗora kan kwankwasona tamkar wasu masoya.Ido na firfito ina ƙoƙarin jayeta sai dai taushin fatarta mai kama da dafafen nama sam babu daɗin taɓa wa .Dakyar na tureta ta ɗago kai a hasale bakinta da hannuwanta duk jini,kafin na yi wani yunƙuri sai ganinta na yi har ta kai ƙofar ɗakina ta na wangale baki ta shige.Ihu na ƙurma haɗi da kururuwa kafin ka ce wani abu mutane uwanda ke kusa sun cika gidan,ɗakina na fara nuna masu da yatsa sai dai a bincike babu kowa. Ƙin shiga na yi ɗakin har sai da Aliyu ya shigo,ina kuka na yi masa bayani.Baki kawai ya ja alamun bai yarda ba,ya ja hannuna zuwa ciki.Sawun matar na gani ɓaro-ɓaro amman da na nuna ma Aliyu sai cewa ya yi bai ga komi ba.Daga bayana na ji ana dariya irin ta tsofi da sauri na waiga,ido huɗu mu ka yi da ita ta na washe min baki daga inda ta ke a tsaye jikin labule....... Littafin kuɗi ne 200 kacal mai son biyan kuɗin karatu ya tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822 [30/10 à 09:00] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Masu cewa gajeren labarin ne na kuɗi? Kar ku manta mallakina ne,ni zan yanke hukuncin yadda zai kasance.Lokacin da na yi CIKIN ALJAN ganin damata na baku shi a free,kuma yadda kuka bani haɗin kai na ji daɗi sosai.Yanzu don ya na PAID ne kuke ganin ban kyauta ba? Kar ku min haka mana domin yanzu na fara gajerun labarai in kun nuna min haka ku na tunanin zan ci gaba ne? A'a sai na koma wancan salon nawa wato na soyayya. Page 7 Jiri ya fara ɗibana yayin da na fara jin Ɗan cikina na motsawa da ƙarfi,da hannu na yi ma Aliyu nuni ya kai dubansa.Kamar walƙiya haka ta ɓace sai dariyarta da na fara ji ta na ambaton "Jinin jinjiri! Jinin jinjiri!" In na ce kalaman ta ba su tsoratar da ni ba na yi ƙarya. Wani zazzaɓi ya taso min nan take,a doli Aliyu ya ɗauke ni zuwa asibiti.Yadda jikina ya yi tsanani sosai yasa suka riƙe mu tare da bamu gado,ina nan kwance an sa min ƙarin ruwa.Bacci na ke mai kamar ido biyu,yadda tsofin matan ke tunkaro gadona gadan-gadan yasa na yi yunƙuri zan tashi sai dai tamkar mai ciwon ɓarin jiki haka na zama ko motsin kirki na kasa. Kun san yadda ake yin cs a ciro baby? To haka matan suka kewaye ni biyu kusan kaina,ɗaya kusan ƙafafu,ɗayar kuma ita ce ke shafa cikina. Raɗaɗi na ji har cikin kwanyata,ina kallonta ta buɗe wata ƴar kwalba ta shafi cikina sannan ta fara magana kamar haka "da sunan duk wani ibilisi da mabiya bayansa yau zan cire Ɗan cikin nan na tafi da shi zuwa duniyarmu,daga yau ya zama na mu za mu raine shi har zuwa lokacin haihuwarsa" a gaban idona wani dunƙulalen abu ya fito daga cikina ya shiga kwalbar ta kuwa rufeta ruf. Ranƙwashi aka yi min a kai tare da cewa "shegiyar yarinyar nan ta addabi duniyarmu da har da yi ma Akuyar gado duka ke ma sai kin yi kuka kamar yadda mu ka yi" wani ranƙwashi aka sake yi min "ki bar munafuka ta kama gidanta ta saka masa matakan tsaro ko ka shiga babu abin da za ka iya yi,ai na yi zaton har asibitin ba za ki bari mu shigo b...." Kukan wata yarinya ce ya karaɗe ɗakin,duk mu ka mayar da hankalin mu kanta ,ba san sani ba ko abin da na canka daidai ne amma yarinyar tamkar ita ma ta na ganin abin da na ke gani. Fuskar wacce ta ci Ɗan cikina ta tunzura ta zama yalo,daga inda ta ke a tsaye ta zira hannu ta zaƙulo kurwa/ruhi yarinyar wanda ya ƙara kukanta."Ku yi sauri mu tafi mu raba wannan" ta faɗa kafin su fita,ina ganin yarona na cikin kwalba na yin motsi. Washegari Koke-koken mutane ya tashe ni daga nauyayen baccina,uwar yarin nan na ji ta na cewa "tun jiya aka so a sallame mu amma kuma na ce a bari har zuwa yau ashe ajalin yarinyar na nan asibiti" shiru na yi ina tunani. Abin da ya faru jiya ya dawo min a kai,gabana ya faɗi har izuwa yanzu dai ban ce komi ba. Wata mata kuma wacce na ke tunanin Yar wacce ta rasa Ƴa ce ita ma ta ɗora da "ki duba fah ki ga kafin safe yarinya ta koma fari fal kamar wacce aka tsotse ma jini" Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo min,Aliyu ya shigo ya na duba na . "Daga masallaci nake,ya ne ya jikin naki?" Kai na girgiza ina mai fashewa da kuka,"subahanallah! Kuka kuma Bahijja? Mi ya faru?" Ya jero min tambayoyin ya na mai taɓa jikina. Dr ya kira sai dai tambayoyin duniya sun yi min na ƙi amsawa a ƙarshe ne na nuna cikina.Ɗakin scanning aka kai ni,Aliyu na daga gefena.Ta cikin ƴar ƙaramar tvn na ke hango Ɗan cikina ,Dr ya ce "Yaronki ya na cikin ƙoshin lafiya,ke mine ne ki ke ji?" Wani murmushi ya kubce min ina jin daɗi har cikin raina daga nan kuma na watsar da lamarin jiya na barsa a matsayin mafarki. Dr ya sallame mu,da zuwan mu gida na tarar da kiran Umma ya fi ɗari haka ma a wayar Aliyu .Kiranta na yi ta na ɗagawa ta ce "Bahijja lafiya na yi ta kiran ki ba ki ɗauka ba?" "Eh jiya ne na ɗan samu zazzaɓi amma yanzu na warke fatan kun tashi lafiya?" "Ina wata lafiya Bahijja? Rayuwar ki na gani cikin duhu duk iya yina na kasa gane taƙamaimai ko mi ke damun ki ko zai faru da ke" Umma ta faɗa . Na ce "don Allah Umma ki bar irin wannan zantukan Allah sai ki sa tunanina ya je gun da ban fatan ya zama haka ne! Ni lafiya ta lau babu abin da ya same ni" "To na ji tunda haka ki ka ce" Umma ta faɗa amma alamu sun nuna ba ta yarda ba. Toilet na shiga na yi wanka sannan na yi sallah,a falo na fito na tarar da Aliyu na waya. "Yauwa ga ta nan ma" ya faɗa tare da kara min wayar a kunne. "Bahijja ashe jikin ki ya ƙiya miki? To Allah baki lafiya yasa kaffara ce.Dama in mutum na da juna biyu sai haƙuri Allah dai ya sa ku rabu lafiya" muryar Hajiya ce,yau cikin sanyi ta ke min magana tare da tausayawa.Har zuciyata na ji daɗin addu'o'inta na kuwa amsa da "amen Hajiya ,fatan kun tashi lafiya? " Ta ce "lafiya lau alhamdullah! Yanzu na ke tambayar Aliyu ko kun zo birthday ɗina kin san gobe ne kuma ko wace shekara sai an yi ɗan ƙaramin buki.To da na ji ba ki lafiya na ce kawai ku bari ba sai kun zo ba" karon farko da na yi murmushi don ina tare da Hajiya "a'a za mu zo in shaa Allah ai na ji sauƙi ma" Hajiya ta ce "a'a Bahijja in kin ji ba ki iyawa don Allah ki yi zaman ki,kar a wahalar min da takwarata " Hajiya ta faɗa cikin raha na ce "to shikenan Hajiya " da sauri kuma ta ce "to Bahijja sai in kun zo bani Aliyun " Kitchen na shiga na bar shi su na waya,a yau Aliyu farin ciki yake sosai da na tambaye shi sai ce min ya yi "saboda kun shirya ke da Hajiya ga shi har za ki je birthday ɗinta" hacinsa na ja ina dariya na ce "ya kamata mu ma mu kai gudunmuwa" "eh ai har na gama tsara komi" ★Ranar birthday ɗin Hajiya duk wasu jikokinta da Ƴaƴanta da matansu sun hallara. Ko da mu ka isa mutane sun kusa cika gidan tamkar ana buki,har da maƙwabta. Rahila na ganina ta rungume ni cikin murna,gaisawa mu ka fara kafin na wuce gun Hajiya wacce ta ke tsakiyar wasu dattijan mata wai ƙawayenta ne. Gaishe su na yi duka kafin na bata wata doguwar riga ja ta kanti mai kyau,sosai ta yi murna kafin ta shiga ɗaki ta canza. Jikoki aka fara tsokanarta wai ta dawo kamar ƴar budurwa,buɗar bakin Hajiya sai cewa ta yi "ai budurwar ce ko in ce ƴar Baby ku jira lokaci..." Dariya duk aka shiga yi banda ƙawayenta wanda suke wani murmushi su na kallona. Aliyu shi ne Auta wannan yasa shi ya kama mata wajen yanka cake,ga mamakin kowa Hajiya ni ta fara baiwa ta na cewa "Auta tunda yau ga ma matarka kai sai ka haƙura" na ci cake ɗin ina yi ma Aliyu gwalo. Tamkar magie haka na ji Ɗan cikina ya juya da mugun sauri,kafin cikina ya fara yin zafi kamar garwashi.Sam ban kawo komi ba a raina,Hajiya na ankare da ni ashe mu na haɗa ido ta sakar min murmushi a doli na mayar mata da martani. Shagali aka fara har da kiɗa,na kuwa cashe saboda a yanzu music na min mugun daɗi a kunne.Abinci aka fara zubawa kowa na ci amma banda ni da ke faman shan ruwa,da haka dai har aka yi komi aka gama kowa ya watse. Aliyu ya so mu koma gida tun yau amma na nuna na fi son mu kwana. Tsohon ɗakin mu wanda yake a gyare mu ka kwanta ,can cikin dare na fara jin ana kiran sunana cikin wata irin murya mai jan hankali da shiga ɓargon zuciya. Ban buɗe idona ba kawai samun kaina na yi tsaye kan ƙafafuna tare da buɗe ɗaki.Sanyi hunturu ya bugu fatar jikina yayin da murna ke ci gaba da kirana "zooo! Zo! Zo! " Haka na fara jefa ƙafafu ido rufe har na zo daf da muryar. Garken Akuyar nan na samu ruhina a ciki,mata da maza ne birjit a gun sai hidima ake kowa da kofi a hannunsa.Akuyar Hajiya tsaye kan ƙafafunta,ban ji tsoro ba ko kuma na ce ruhina bai ji tsoro ba haka na duƙa na gaisheta ga mamakina sai ta ƙi amsawa can kuma Hajiya ta ƙaraso ta na cewa "ki bata haƙuri akan abin da ki ka yi mata" ƙememe ruhina ya ƙi baiwa Akuya haƙuri. Ganin haka ta Akuya ta yi min wani tinni a goshi na fasa ihu tsabar azaba,daga gefena na ji Aliyu na cewa "Bahijja? Lafiyar ki kuwa?" Zumbur na miƙe ina jin goshina na yi min ciwo. Mafarkin da na yi ya faɗo min a rai,sauka na yi daga kan gado Aliyu ya jefo min tambayar"ina za ki je?" Ban bashi amsa ba na buɗe ɗakin tare da fita direct garken Akuyar na nufa....... Littafina na kuɗi ne ki biya 200 kacal na karatu na saka ki group wacce ta shirya ta tuntuɓe Ni ta WhatsApp +22795045822 [30/10 à 15:18] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Last free page Page 8 Ina shirin kai hannu ga Akuyar sai na ga tamkar an yi ma garkenta gushi ta matsa can gaba kaɗan,ni ma na matsa ina kallon idonta masu fitar da wani mugun haske yalo da ja. Ƙugu na riƙe na ce "wato duk abin da na yi miki bai ishe ki ba har sai kin biyo ni cikin bacci ki na bani tsoro ko? Sai na cire miki wannan shegen ƙahon gobe in kin ga uwarki sai ki tinneta da shi" na faɗa ina dube-dube,can na hango wata gatari na tafi da ɗan sauri na ɗauko shi. Ban yi wani jinkiri ba na sare dogon ƙahonta,ta yi kururuwa wacce ta sa ƙasa girgiza,daidai nan Aliyu ya fito . "Bahijja mi ki ke yi a nan cikin wannan tsohon daren? Wuce mu koma ciki" Ko kafin na yi magana Akuyar nan ta fara yin wani gurnani kafin ta faɗi kwacaaa. Aliyu ya zo ya ja ni da ƙarfi mu ka koma ɗaki,tsaye ya yi ya na kallona na wani lokaci kafin ya sako min wata tambaya "Bahijja don Allah mi ke damun ki? Wannan canjin da idanun ki suke yi na mine ne? Wlh kin fara bani tsoro a yi mutum kamar jinsin aljan?" Atishewa na fara yi kafin na ji kaina na sarawa haɗi da juyawa. Kukan Hajiya ya tashe ni daga bacci,na ware idona kanta a inda ta ke tsaye ƙiƙam Aliyu na faman ba ta haƙuri. "Kin kashe min Akuyar da uwata ta bar min gado sai ki huta amma ki sani yadda ki ka gulala min sai na ninka miki baƙin ciki fiye da haka" na waro ido ina sake kallon Hajiya wacce ta ke balbalin bala'i. Ta na fita Aliyu ya ce na shirya za mu koma Niamey. A tsakar gida kuwa duk matan gidan ne suka yi jingum su na kallon gawar Akuyar,baki na ɗan taɓe kafin na nufi ɗakin Hajiya . A kwance na tarar da ita su Aliyu da sauran yayunsa sun kewaye ta .Ciwonta ne ya tashi kamar yadda na fahimta,lokaci guda kuma ta rame. Dakyar dai Aliyu ya barta mu ka koma Niamey,sai dai kuma a ranar ya sake komawa ganin haka ni ma na tafi gidan mu. ★Anty Murja ta kwantar da ni ta na yi min wanka da ruwan magani, Umma na gefe ta na sharar ƙwalla.Na ɗago na dube ta na ce "Umma wai kukan mine ne ki ke?" Anty Murja ta bani amsar tambayar" Bahijja a zahirin gaskiya Ɗan cikinki bai tare da ke ya na can ƁOYAYYAR DUNIYA(Next book ɗina in shaa Allah) duk iya bincikenmu mun kasa gano inda suka ajiye shi.Yanzu mafita ɗaya ce shine ki rabu da Aliyu" da sauri Umma ta ce "har abada ba za ta rabu da shi ba,Ɗan cikinta kuma doli za su maido shi ." Ran Anty Murja ya ɓace ta ce "Umma kin fi kowa sanin matar nan a yanzu ta fi ƙarfin mu doli mu zubda makamai" "in tafi ƙarfin mu ai ba ta fi Allah ba ko?" Anty Murja ta ja baki ta ce " Umma da dai...." Sai kuma ta yi shiru ta na kallona. Sam na kasa ɓoye mamakina, zantukansu ya yi sak da na bokaye uwanda su kaɗai ne za su iya sanin abin da bai faru ba a duniyarmu.Tashi na yi zaune,abin da na fahimta har yanzu su na yi min ɗaukar ƙaramar yarinya wacce ba ta da wayo. Tun zuwana gidan su ke ta ɗura min magani yau ne suka shirya duba ni ko kuma tantance halin da na ke ciki. Na dubi Umma na ce "zan koma gidana ba zan iya zama a nan ba a na tayar min da hankali,ina kuka taɓa ganin an sace yaron da ke cikin mahaifiyarsa? Ta ya ma haka zai yiyu alhalin likita ya tabbatar min ɗana na cikin ƙoshin lafiya?" "To ke Murja ɗaukar ta ku je asibitin a dubo ta sai ku kawo min sakamakon" Umma ta faɗa, Anty Murja ta min jagora zuwa wata ƴar ƙaramar clinic inda aka yi min scanning aka kuma sake tabbatar Ɗan cikina na nan lafiyarsa lau. Da mu ka dawo gida Umma ta yi mamaki sosai haka ma Anty Murja. Da wannan na koma gidana can Niamey na ci gaba da rainon cikina,duk wata ina zuwa awo. Aliyu kusan zamansa ya koma can Kwalo saboda har yanzu jikin Hajiya ya ƙiya. ★Ranar gumurzu,ranar banbance ɗan duma da kabewa.Bayan watannin da cikina ya yi ,yau ga shi na tashi da naƙuda kamar raina zai fita haka na ke ji.Sauƙina guda tal Aliyu na nan shi ke ƙarfafa min gwiwa,kayan haihuwar ya saka a bayan mota mu ka nufi asibiti. Tun ƙarfe goma sha ɗayan rana har bayan sallar isha'i haihuwa ta gagara.Duk matan da na tardo

Chapter 3 of 5