Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
da uwanda aka kawo bayana sun haihu,ɗakin haihuwar ni ɗaya ce kamar mayya. Sai tsakar dare can na ƙara jin wata naƙudar ta fita hankali,ihu na fara ina kiran sunan Aliyu .Likitoci su ka rufa kaina aka fara bani taimako,kafin wani lokaci kukan baby ya cika ɗakin. "Masha Allah an samu ɗiya mace dakyar!" Cewar wata nurse ta na mai ɗora min ita kan ƙirji.Ido na lumshe hawaye na zubo min,sai da aka gyara ni sannan aka kai ni ɗakin hutu. Aliyu ya ɗauki Babyn ya yi mata huɗuba,ni kuwa cike da so na kallonsu kafin bacci ya ɗauke ni. Washegari,kukan Baby ya tashe ni.Nurs ɗin nan ita ta koyar da ni yadda zan shayar da baby,duk da azabar da na ke ji bai hana ni ci gaba da bata abincinta ba. Abun da ya bani mamaki shine yadda jaririyar ke kallona tarrr cikin ido tamkar ta san ni.Aliyu na duba na ce "zo ka yarinyar nan yadda ta ke kallona" Aliyu ya matso ya na murmushi ya ce "so ne ta ke ta fara tantance Uwarta saboda wannan da alama sai ta yi ƙiwa" ido kawai Babyn ta ke juyawa ta na shan mama.Tun ina tunanin ta saki har na kai na cire mata nan kuma ta hau kuka doli na mayar mata a baki. Kafin a sallamo mu daga asibiti shayarwar da na yi ma Baby ya kusa hamsin kuma sai an yi dagaske ta saki.Ganin haka na ce ma Aliyu ya sawo madarar gwangwani don gaskiya ba zan iya ba,likitoci ma sun yi amanna da hakan. Ƴan unguwa uwanda suka san ni tuni sun fara shigowa yin barka,abu guda na lura da shi duk matar da ta zo da Ɗanta da zarar ya kalli baby sai ya yi ta kuka. Ban baiwa hakan wani muhimmanci ba,na bar shi kan cewa kawai ƙila tsoron jariri ne su ke. Mun yi waya da ƴan gida Umma ta ce sai jibi Anty Murja za ta zo, ɓangaren Aliyu kuwa Hajiya ta ce ita za ta yi tsaron biƙi. Da dare na kaɗa madara cikin biberon🍼 na fara baiwa Baby,zubdo madarar ta rinƙa yi ta na kuka.Aliyu da ke zaune kusa da ni ya na kallon mu ya ce "ki bata mama tunda ba ta shan madarar" cikin gajiya na ce "babu komi duk ta shanyeta tasss yanzu haka yunwa na ke ji,dubi yadda na rame lokaci guda" cikin jin haushi ya taso ya ɗauki Babyn tare da jan rigata sama kun san wani abun mamaki? Caraf baby ta yi ta fara tsotsata wanda na ke jinsa har cikin zuciyata,jin kamar numfashina zai tsaya na ƙwaci kaina. Aliyu ya ƙara yin fushi ni kuwa na ce "wlh ba zan zauna ta yi ta jana ba alhalin babu komi ciki,ka bari na ci abinci.Ga madara nan ta sha in ba ta sha kuma ita ta sani" bai tanka ni ba ya fara bata madarar. Tamkar mage haka ta shanye madara ɗaya da 🍼 shi kansa Aliyun sai da ya yi mamaki.Ganin ta na shan madarar yasa na ƙi bata mama duk nacin da za ta yi,don haka kawai na ji ban nonon ya fita raina.Wata tsohuwa mai suna Iyani, maƙwabciya ta wacce ke yi min wankan biƙi ita ke bani haƙuri tare da huɗubar wai a sannu zan saba. Ina zaune ina kaɗa madarar baby yayin da Iyani ke wanki kaya,baby tuni ta fara kuka ganin yadda ta ke kukan yasa na ɗora mata mama ai kuwa ta rinƙa jansa zuuuu babu tsayawa.Dariya abun ya bani na ce "ah an ji yunwa ashe bari na yi sauri na haɗa miki madarar ki" na ɗauko marfin bijiron sai na lura da tétine ɗin(ƴar robar nan wacce yaro ke baiwa yaro damar jan madara) duk an tattaune ta.Shiru na yi ina nazari ta yaya jariri da bai da haƙora zai taune roba? Ido na ƙura ma Babyn da kyau ina kallonta kun san mi na hango? Kamanin Hajiya sak a tattare da ita banbancin ta da Hajiya shekaru ne kawai,zan yi cewa wannan small Hajiya ce muƙut na haɗiye wasu yawu...... Mu haɗe a PAID GROUP💃🏻💃🏻duk mai son cigaba da karatu zai biya 200 ne na saka shi group ɗin da na ke Posting. WhatsApp +22795045822 NB: daga lokacin da book ya kammala complete 500 ne. [31/10 à 09:53] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Littafin kuɗi ban yarda ki karanta shi ba tare da kin biya kuɗin karatu ba,duk wacce ta karanta shi ta sani ina biyarta 200 ko gobe.Sannan da wacce ta fitar,da wadda ta gani a wani groupe ita ma ta tura kuma duk ina biyarku kuɗin iya adadin mutanen da suka karanta. Duk mai so 200 ne kacal ta turo da katin ta WhatsApp +22795045822 *PAID PAGE* 9 Ina tsaka da duba feeling Aliyu ya shigo,nuna masa na yi yadda duk ta tattaune ƴar robar.Ya karɓa da mamakina sai na ga ya na dariya "haba Bahijja ta yaya Baby za ta tauna robar alhalin ba ta da haƙora? Kawai yara ne masu shigowa nan su ne suka tauna shi.Ko kuma Maman Babyn " ya kashe ido ɗaya ya na zolaya ta. Na sauke ajiyar zuciya na ce "ƙila ba! Dama wasu in sun gani sai su ce sai sun sha.Wai yaushe Hajiya za ta zo?" Aliyu ya canza fuska ya ce " wlh tunda aka yi haihuwar nan Hajiya ke fama da cutar bacci,Ya Yusuf ya ce in ta rufe kanta a ɗaki wani sa'in sai dare ta fito,amman in shaa Allah gobe zan je na ɗaukota.Ita Anty Murja ba za ta zo ba ne?" "Za ta zo yau tun jiya mu ka yi waya da ita,yanzu haka ta na kan hanya" "Ok to babu damuwa bani Babyn na gani na yi mata addu'a" Aliyu ko gama rufe bakinsa bai yi ba ta shiga tsala kuka. Na fara ririgata ko ta yi shiru,kukan ya rage Aliyu na ɗaukarta ta ƙara fashewa da wanda ya fi na farko sai kace wacce aka jona ga lantarki.Doli na karɓe ta ,madara na fara bata da cokali kamar mai maƙoshin roba haka ta ke zuƙe madarar ko magul- magul irin na jarirai ba ta yi. "Ki saka ma feeding sabuwar roba mana zai fi a cokalin" cewar Aliyu ,na amsa da "to miƙo min ya na can cikin kayanta" Aliyu ya ɗauko ya canza ma feeding roba bayan ya yi ƴar huda inda madarar za ta rinƙa fitowa. Sai da na cika feeding da madara na fara bata,tass ta shanye sa ta fara kukan shegantaka."Ki ɗorata da abincinta kin san madara ba ta riƙe ciki kamar nono" ba dan na so ba na ɗaga riga,tuni Baby ta fara gyaran baki ina ɗora mata ta fara zuƙata kamar za ta janye ni.Aliyu na fita na cire kayana tare da sa yatsa manuniya na ɗan dungure goshinta na ce "sai baƙar zalamar tsiya wannan in ki ka fara girma mun shiga uku buhun shinkafa na san sati guda zai mana" Wani irin kallo ta ke yi min,duk da ta na Jaririya bai hana ni jin shakka ba.Saboda kallon da ta ke yi min irin wannan ne kamar za ki gani. Kwantar da ita na yi,na tashi na ɗauko kunu da madara na fara sha.Ina zaune na ga abin mamaki Baby ta canza kwanciyarta,da ta ga kamar na lura da haka sai ta mirgina ta zatse kanta kafin ta fara kuka. Ƴan magana su na cewa Uwa da Ɗa sai Allah,to kukan da ta ke sai ya mantar da ni komi na yi saurin ɗaukar ta .Ina yi mata ƴar waƙa "yi shiru yi shiru an Babyna ,wa ya taɓa min an Babyna " lamo ta yi kan kafaɗata ta na sauke ajiyar zuciya kamar wata babba. Ina ƙoƙarin sauketa Anty Murja ta yi sallama,da murna ta shigo.Baby wacce ta fara bacci na miƙa mata,nan ta shiga yi mata hotuna kafin mu fara hirar yaushe rabo. Wani abun al'ajabi wunin ranar Baby bacci ta wuni wanda shi ne karon farko da hakan ta faru tun da na haifeta.Don wani sa'in har cewa nake an ce jarirai na bacci amman banda Baby sai Aliyu ya ce dama wasu sai bayan suna suke. "Yau na ga ƴar ɓurrr! Duk ba ki tashi yin bacci ba sai yau da Uwar ki ta zo? Haba ku tashe ta" Iyani ke faɗa ta na shafar kumatun Baby, Anty Murja ta ce "a'a ku barta ta yi baccinta ai ina nan sai an yi buki" ni dai ban ce komi ba. ★KWALO Hajiya ce zaune cikin ɗaki ta na meeting ita da ƴan uwanta matsafa. "Ai wlh ba ƙaramin burge ni ki ka yi ba da ki ka ɗauki suffar Ƴarta,kin ga ta wannan hanyar ce kawai za ki azabtar da ita" "Ai tun farko ni na bada shawarar mu je mu ɗauke Babyn ta yadda za mu raine shi, wannan ya saka Hajiya ba ta sha wahala ba wajen shiga cikin jikin Babyn " "Ai hakan shi ne daidai,ki yi mata azaba mai raɗaɗi yadda za ta gane eh ke ɗin *BOKANYA* ce kamar yadda ta ke zargi" "Yadda ta zame miki ƙarfen ƙafa ta amshe martabar ki wajen Aliyu ke ma ki watsa gidan ki hana su zaman lafiya" Zantukan abokan Hajiya kenan wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,har yanzu ita ba ta yi magana ba kallonsu kawai ta ke. Zuwa can ta ɗaga masu hannu ta ce " har yanzu babu wacce ta yi min tambayar mine ne dalilin dawowata na bar jikin Baby,tun ɗazu sai shirme ku ke faɗa akan abin da kun san duk ƙaramin aikina ne" gamun baki suka yi wajen tambayarta " to mine ne dalilin dawowar ta ki?" Hajiya ta gyara zama ta ce "kun san akwai wata Yayar Bahijja wacce ta ke bamu matsala,to ita ce ta zo.Na sani sarai da zarar ta gan ni za ta gane ni duk da ina cikin jikin Baby, wannan yasa na fita na dawo nan domin neman shawar ku" duk shiru suka yi kafin zuwa can su sauya yare zuwa na ƁOYAYYAR DUNIYA (NEXT BOOK ƊINA) dariyar cin nasara su ka yi dukan su kafin su watse. Tsakar gida Hajiya ta fito,duk surukanta su ka shiga gaisheta cike da girmamawa.Kai kawai ta jinjina kafin ta wuce garken Akuyar ta wacce ta sake,sai dai wannan ƴar Jaririya ce. Kan Akuyar ta ke shafawa ta na wani mimimi da baki kamar mai addu'a,tsawon lokaci kafin ta tashi ta koma ɗaki. Kayan bokancinta ta fiddo,ta girgiza wata kwalba wacce ke ɗauke da ruwa kaloli kafin Hajiya ta zama ƴar ƙarama kamar tsutsa ta shige kwalbar. Gama shigarta ke da wuya kwalbar ta girgiza da kanta kafin ta ɓace. ★NIAMEY Baby ba ta farka ba har sai da ta ji ta cikin ruwan zafi,bari na faɗa maku wani abu kukan Baby na yau ya banbanta da na kullum.Ka na jin rauni irin na jarirai a cikinsa,kukan kuma ya yi siriri kamar yau aka fiddota a ciki. "Baiwar Allah ina ga jikinta ciwo yake saboda yawan ɗauka duba ki ga yadda ta ke kuka" Iyani ta faɗa ta na gasa mata jikin. Yadda Baby ke kuka har can ƙasan zuciyata na ke jin shi,ana gama mata wanka aka naɗe ta da towel.Iyani ta miƙo min ita ta na cewa "ki ba ta abincinta ta sha" Cike da tausayi na ke goge mata gashi kafin na ɗora mata nono,kasa sha ta yi sai dakyar ta kama.Kamar mai koyo haka ta ke ɗan jan shi kafin ya kubce mata sai na sake gyara mata. A yau a daidai wannan lokacin ne na fara jin soyayyar nan da uwa kan jin in ta na shayarwa.Na dubi Anty Murja na ce "wlh ji na ke kamar yau ne na fara bata nono,sai na ga kamar an sauyata" Anty Murja ta ce " kin ji ki da wani zance wai an sauyata" "Eh wlh Anty,tun da na haifeta kullum daram ta ke sai yau ne na ga wannan raunin na jarinta" Anty Murja ta ce "yanzu Bahijja a gabana ki ke cewa kin haihu?" Iyani ta karɓe zancen "eh yaran zamani kenan babu ta ido" nan fa suka fara yi min tsiya. Anty Murja na baiwa Baby,fuskar Babyn ta duba sannan ta ɗago ta kalle ni ta ce "Bahijja Baby da ke ta ke kama sak" na yi ƴar dariya na dubi Babyn ai kuwa yau sai na ga kamanin mu sak. Na ce "da farko wlh da Hajiyar Aliyu ta ke kama" Iyani ta ce "kin san jariri rikiɗa yake" anty Murja ta ce"Allah kiyaye da ta yi kama da Hajiya ina dalili ta je ta kwaso baƙin halinta" ni dai ban ce komi ba,anty Murja ta buɗe baki kamar rariya ta fara baiwa Iyani labarin Hajiya nan Iyanin ta kama mata su na ta zagin Hajiya . Da dare mu na kwance Iyani ta fara ƙunnai,sai ciwon ciki Zuwa toilet wanda ya yi bai da iyaka,magani na bata amman ga banza.Kafin wani lokaci ni ma ɗan yatsana ya fara zugi, Anty Murja ce kawai ke daram. Washegari ko da na tashi ɗan yatsana ya kumbura ya yi suntum, Iyani da dama zawon ya tsaya sai dai jikinta babu ƙwari. "Anty Murja don Allah ki je ki samo min maganin ciwon hannu Allah ya fara matsa min"na faɗa kamar zan yi kuka,ta dube ni ta ce "wlh Bahijja kaina ke mugun ciwo ba zan iya fita ba" Mu nan jingum sai ga Aliyu hankali tashe na tambaye sa lafiya? Ya bani amsa da "Hajiya ce ta ɓata tun jiya ba a ganta ba kuma ƴan gida sun ce ba su ga lokacin da ta fita ba,ga ɗakinta kuma a buɗe an bincika ba ta nan"..... [31/10 à 15:42] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Littafin kuɗi ban yarda ki karanta shi ba tare da kin biya kuɗin karatu ba,duk wacce ta karanta shi ta sani ina biyarta 200 ko gobe.Sannan da wacce ta fitar,da wadda ta gani a wani groupe ita ma ta tura kuma duk ina biyarku kuɗin iya adadin mutanen da suka karanta. Duk mai so 200 ne kacal ta turo da katin ta WhatsApp +22795045822 *PAID PAGE* 10 Alio bai ida rufe bakinsa ba muryar Hajiya ta bayyana a tsakar gida.Da murna ya fita ya tarbota kafin su shigo ciki, gaisheta duk mu ka yi har da Iyani da ke tsohuwa.Biris Hajiya ta yi da mu kamar ba ta ji ba kafin ta fara cewa "ina takwarata Habsu" Aliyu ya yi dariya ya ce "Hajiya ina laifin ki ce Hafsy ko kuma Baby? Amma ai wannan suna na tsofi ne" ya yi maganar ya na mai ɗaukar Baby ya miƙa ma Hajiya . Kan capet ta zube kafin ta fara yi mata wasa ta na cewa "ko wa ya taɓa Habsu sai ya kwana dare angaje! Kaiii! shi da bacci hannun riga domin Habsu ba kanwar lasa ba! Yeeee! Ka ga JIkar Habsu! Weee! Babyn Autan Hajiya! Kamo ta nan,wannan baki sai ya yi cin abinci irin wannan mimimi da baki kamar shinkafar Tillabery" tunda ta fara waƙe-waƙenta na fara ɗora su kan sikelin hankali. Ba zargin Hajiya nake ba,amma tabbas a yadda ta yi kukan kurciyar nan ta tabbatar min da ciwon cikin jiya da Iyani ta yi da sa hannunta haka ma ciwon kan Anty Murja. To ni kuma ciwon yatsan da nake fa? Shine na kasa samo amsar shi tunda dai jiya da su na gulmar Hajiya da zaginta ban tanka ba.Wata zuciyar ta bani amsa ƙila dan kin dungure goshin Baby. Ina ɗago kai mu ka haɗa ido da Hajiya ,wani irin baƙin kallo ne ta ke yi mini wanda na kasa tantance na miye.Haka kawai na ji ina shakkar ta ,da sauri na sunne kai,ita kuma ta ci gaba da yi ma Baby wasa. Abincin da ruwa aka kawo mata ,ta ƙasan ido na ke kallon yadda Hajiya ke yamutsa fuska kafin ta ce "ba na cin abinci ai" cikin gyatse Iyani ta ce "sai mi? " "Madara zan sha ko kuma jan lemu" Iyani ta ce "ai kuwa sai in madarar takwarar ki za a baki don wacce Bahijja ke sha ta ƙare" "Eh a bani ai dama kishiyata ce! Mi ya kai mai biƙi da shan madara? Ko babu hatsin yin kunu ne?" Cewar Hajiyar. "Akwai kin san yaran zamani doli sai mai daɗi" Iyani ta faɗa. "Laifin Aliyun ne da ya sawo mata madarar,mai biƙi ba ta shan kunu ina za ta samu ruwan nono? Shi yasa na ga Takwara wata ƴar figit ashe ba ta ƙoshi" nan fa Hajiya ta fara zazzaga masifa har Aliyu da ya shiga bedroom sai da ya fito. "Ai na sawo wata madara ta na mota bari na ɗauko,wlh Hajiya baby kwana dare take shan madara sam nono bai isar ta hakan yasa ita ma Bahijjar in za ta sha kunu sai ta ƙara da madara" Aliyu ke faɗa cikin son kwantar da hankalin Hajiya.Da sauri ya fita ya kwaso kaya niƙi-niƙi,Hajiya ta haɗiye ɓacin ranta amma ka na iya hango shi a fuskarta. Ko minti biyar ba ta ƙara ba ta ce za ta tafiya gidan wata abokiyarta.Aliyu ya kaita a mota,har bakin ƙofar gidan.Da za ta fita ta ce "Auta ka son ciwon kan ka ba komi ake saya ma mace ba,yanzu mine ne na zuba madara cikin kunu salon Takwara ta yi ta zawo ko?" Aliyu ya yi dariya ya ce "to Hajiya in shaa Allah daga wannan ta ƙare ba zan sake sawo wata ba" Hajiya ta washe baki "Yauwa jira ni a nan har na fito" ta faɗa kafin ta shiga gidan ƙawarta. Karime shi ne sunan ƙawar Hajiya ,ta na ganinta ta taso suka rungume juna cike da murna. "Ai na zata kin manta da ni irin wannan shekaru da aka ɗauka ba ki zo gidana ba sai dai ni na je" Karime ta faɗa. Hajiya ta ce "ke ma ai neman magani ke kai ba wai gani na ba,yanzu dai gani zo ki bani labari in sha" "Hajiya ina wuni" Suby ta faɗa wacce ta ci kwalliya kamar ƴar sarki. Hajiya ta waro ido ta ce "Wai Suweiba ce ta zama budurwa haka? Tun ta na ƴar ƙwaila rabona da ita.Lafiya lau ina zuwa?" Suby ta shagwaɓe fuska ta ce "zan tafi salon gyaran gashi ne" Wani murmushi Hajiya ta yi na cin nasara kafin ta ce "faɗuwa ta zo daidai da zama,mu je na sa Aliyu ya kai a mota " Suby ƴar kuri ta na jin haka ta yi tsalle. Aliyu na zaune a mota Hajiya ta umarce shi da ya kai Suby salon,ba don ya so ba ya ce "ok ta shigo mu tafi" Hajiya ta ce "Yauwa Auta sannan ka biya kuɗin gyaran,shiga ƴata" ta buɗe ma Suby gidan gaba ,har sai da suka bar layin kafin Hajiya ta koma ciki. ★Ciwon kan Anty Murja ya matsa sosai duk da ta sha magani amma ga banza, wannan ya saka ta kira Umma ta ce ta aiko mata maganin Hausa . Mu na zaune ne suka yi wayar ko minti goma ba a yi ba Anty Murja ta tashi ta fita sai ga ta da ledar magani. Wannan lamari ya ɗaure min kai sosai amma na ƙyale,ta na shan magani ai kuwa ta samu lafiya mu ka ci gaba da hidimar mu. Da dare Aliyu ya shigo,yanayinsa kawai na duba na san da matsala.Na tashi na bi bayan shi,ina shigowa ya yi raf da ni.Na ɗan ja da baya na ce "Ali..." Ban ida ba ya haɗe bakinmu ya fara yi min kiss. Can ya tsagaita ya ce "Bahijja gaya min sai yaushe za ki samu tsarki?" cikin mutuwar jiki na ce "nan da kwana 36" ya rumtse ido tare da ranƙwafowa saman jikina cikin cool voice ya ce "ba zan iya jurewa ba my Bahij Allah ji nake kamar zan mutu,ban taɓa tsintar kaina cikin irin wannan mugun feeling ɗin ba" mi jikina zai yi banda rawa? Tamkar na hau mazari haka na fara zanzana ƙafafuna ma sun fara gazawa,kuka,kuka fa Aliyu ke nan ga yi mini saboda ya na son kasancewa da ni amma ba hali. Ya ƙara jawo ni ya manna a ƙirjinsa ya matse ni gam,a tare mu ka sauke ajiyar zuciya.Yadda yake fitar da huci kamar kumurcin zaki kawai ya isa ya ƙara jefa ni cikin cakwakwalin damuwa da tashin hankali. Daga can falo kuwa ina jin Anty Murja na cewa "shirunsu ya yi yawa fa, Iyani ya kamata ki shiga ki dubo" "a'a ita da mijinta! Ai yanzu an bar irin wannan sakarcin,na san dai ba zai nemeta ta na jinin biƙi ba sai dai romence ku ke cewa ko mi" Anty Murja ta gagaɓe da dariya. Kukan Baby na fara ji sama-sama,na yi niyya zamewa daga jikinsa da sauri ya sake riƙe ni.A hankali na ɗago kaina wanda ke ɓoye a ƙirjinsa,gabana ya yi mugun faɗuwa ganin yadda idonsa su ka yi ja. Na lumshe ido ba tare da na shirya ba jin damshin yawunsa kan laɓana,sumba yake min cikin fitar hankali wacce ta kai mu da yin kwance kan bed. Mun ɗauki lokaci a haka ya na rungume da ni kafin na fara jin saukar numfashinsa.Na ja ajiyar zuciya ina jin salama tunda har ya samu bacci,falo na fito inda Baby ke ta yin kuka Iyani na bata madara. "Anty Murja ki na ganin Baby na kuka ko ki amshe ta" na faɗa ina turo baki,ba ta tanka ni ba ta ci gaba da latsa wayarta. Ina ɗaukar ta na ji yanayinta ya sauya ba kamar jiya ba,sai ta dawo sak Babyn farko mai kama da Hajiya .Ba zan ɓoye maku ba har wani kallo na ga ta na yi min kamar ta na jin haushi na...... MRS SADAUKI 💫✍🏻🫶🏻 [01/11 à 15:07] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️* ```gajeren labari``` *MRS SADAUKI 💫✍🏻* SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪 FCWA☀️ Littafin kuɗi ban yarda ki karanta shi ba tare da kin biya kuɗin karatu ba,duk wacce ta karanta shi ta sani ina biyarta 200 ko gobe.Sannan da wacce ta fitar,da wadda ta gani a wani groupe ita ma ta tura kuma duk ina biyarku kuɗin iya adadin mutanen da suka karanta. Duk mai so 200 ne kacal ta turo da katin ta WhatsApp +22795045822 *PAID PAGE* 11 Shimfiɗe Baby na yi don ba zan juri kallon nan ba,ina nufar ɗaki don dubo Aliyu Baby ta canyara kuka.Bakina na ja na ce "wannan yarinya na kasa gane kan ki wlh,kamar wata hawainiya sai rikiɗa ta ke .Yanzu mine ne na kuka?" Na faɗa ina mai dawowa na ɗauke ta. Iyani ta ce "ta saba da hannu ne shi yasa,ku iyaye in aka ce ku rinƙa ajiye yara sai ku ga an takura ku to ai ga irin ta nan.Bahijja tunda aka sako ku daga asibiti anya kin taɓa ajiye Baby?" Na turo baki ina gunguni kafin na wuce ɗaki. Bawan Allah Aliyu sai bacci yake, ka na ganinsa za ka san na wahala ne.Da mamakina ita ma Baby shi take kallo har wani juya ido take gabanin ta maido da idon gare ni ta tsayar da su ƙyam cikin nawa . Gabana ya yi wata irin muguwar faɗuwa,da sauri na nufi falo .Bisa kan ƙafafuwan Anty Murja na ajiyeta,kuka ta fara ta na wani motsa jiki kamar wacce aka ɗora kan garwashin wuta. Anty Murja ta ce "mine ne wai ke damun yarinyar nan?" Na bata amsa da "ki duba cikin idonta ki gani" da sauri Baby ta rufe idon har wani matse su ta ke.Anty Murja ta kece da dariya ta ce "Bahijjar Ƴar nan taki da abun mamaki take dubi yadda ta ke jimƙe ido,ɗauko kwalli a saka mata" ko motsawa ban yi ba ina nan ina kallon Baby a gaban idona wani abu mai kamar haƙi kamar baƙin zare ya fita ta hancinta. Kuka ta fara mai cike da rauni ta na buɗe idonta uwanda tuni sun yi jawur.Anty Murja ta yi mata addu'a kafin ta bani na ɗorata ga nono,sha ta fara har ta na ƙwarewa.Baiwar Allah ta ji yunwa sosai,a wannan ranar daidai wannan lokacin na ɗan fahimci wani abu amma wautar da na yi shine na bar ma kaina sani tare da ɗaukar aniyar sai na bi didigin Baby. ★A can ɓangaren Hajiya kuwa duk jikinta ƙaiƙayi yake yi mata,Karime da ke gefenta wacce Hajiyar duk ta bata lambarin komi ta ce "Hajiya da barin yaran nan ki ka yi suka yi zaman aurensu tunda dai shi Aliyun bai rage ki da komi ba,dubi yanzu wajen ki cutar da Bahijjar ga sakamakon da ki ka dawo da shi" "Ki bari Karime

Chapter 4 of 5