Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
na fi son mutuwa taxo ta ɗaukeni ba zan tashi ba kawai" wanda duk wannan maganar da take ta nayi ne cikin ƙarfin hali ba fita take sosai ba, iya fatar bakinta dake motsi kawai za ka gane abinda take cewa girgiza kai Josmie tayi ruwan hawaye na ƙara ambaliya a kwarmin idanuwanta, "Za ki tashi da yardar Jesus sannan ki reni yaronki da hannunki a wannan karin babu abinda zai faru da yaron cikinki" dukda azabar da take ji hakan bai hanata mayarwa Josmie amsa ba, "da gaske wannan karin ba za a halakar man ya yaro ba, kamar yanda aka halakar man da ƴaƴana ba ɗaga mata kai Josmie tayi tana mai murmushi wan da yake haɗe da kukan tausayi, yayinda da lkc guda kuma tai wani nishi mai ƙarfi daya haddasa fitowar jariri wan da ya canyara kuka a lkc ɗaya, lamo tayi tana mai lumshe idanuwanta tana jin wani bacci bacci na niyyar fixgarta sai dai tai ƙoƙarin hana kanta sbd wannan baccin dake fixgarta shine sanadin duk halakar ƴaƴanta, a wannan karin ba zata bari hakan ya faru ba, don haka tayi ƙoƙarin ware manyan idanuwanta masu matuƙar kyau akan yaron dake hannun Josmie yana canyara Kuka Murmushi mai haɗe da sautin kuka ta saki "Josmie yau nice na ware idanuwana akan abinda na haifa wan da hakan bai taɓa faruwa ba" iya ɗaga mata kai kawai Josmie tayi tana murmushin farinciki, cikin lkc ƙanƙani Masarautar JOHAAN ta san da cewar Gimbiya ARUSH ta haihu sannan ɗa Namiji Tun lokaci da. Mai martaba ya shigo ya zuwa ɗakin da ARUSH ɗin take ya kafeta da idanuwa yayinda shima hawayen farinciki ke fita "na haihu a wannan karon ba tare da banga fuskar abinda na haifa ba, nayi farinciki da godiya ga Yesu domin shi ne ya bani damar ganin wannan yaron ina son ku tabbatar man da cewar tabbas zan rayu da yarona, ku bashi kariya daga halakakkun gidan sarautar nan, ku tsare shi daga makircin maƙiya" ta faɗa da ƙwalla cike taf a idanuwanta wanda murmushi da annurin ke akan bisa kyakkyawar fuskarta shima murmushin ya saki yana kama hannayenta duka tare da saka idanuwansa akan nata "ARUSH I can assure you that this time our child will not perish" murmushi mai haɗe da dariya ta saki tana rungume sa, wanda duk abinda suke Gimbiya Josmie na kallo tana sakin murmushin farinciki yayin da ta kaiwa mai martaba Yaron sosai ya riƙesa yana kallonsa wan da murna ce fal a ransa ganin ya samu Magajin masarautar Handaash, a daren ranar sosai akai shagali yayin da farinciki ya ninkaya a masarautar Handaash yayinda a gefe ɗaya na munafukai da kuma maƙiya ba haka suka so ba, baƙi ciki ne fal cike da zuciyoyinsu, sosai take haki da furzar da iska mai zafi tana mai sake jan wani numfashin tana fitar dashi yayinda idanuwanta sun kada sun yi ja kai kace gauta, "ina ina da hakan ya faru me ya saka a wannan karin Yaron ARUSH ya tsira?? tun bisanin shekara Ashirin nice ke galaba akanta mi yasa a wannan karin banyi galaba ba akanta, ga shi abinda nafi tsana ne shine samuwar wani ɗa Namiji a gidan sarautar nan kayi duk yanda za ayi kaga ka halakar da yaron nan" ta faɗa da dakakkiyar murya ta tsofi wacce har kyarma take Mutumin da tsawon shekaru yake tare da ita but har a wannan lkcn bai taɓa ganin fuskarta ba idan banda yamishashsun idanuwanta wan da tsabar tsufa ya saka su yamushewa, itama a nata ɓangaren bata nuna masa cewar ta ganesa ba, duk da kalar ɓadda kamar da yake hakan ba zai hanata ganewa bcox makira mace ce mai haɗarin gaske Jijjiga kansa yai yana shaƙe murya"in dan wannan karki damu ki saka a ranki tamkar anyi an gama ne duk da na dan ba mu kaɗai bane masu harar yaron nan ba" dariya mai nuna zallar jin daɗi tayi tana furta "nayi Alqawarin ARUSH ba ke babu jin daɗin haihuwa haka zan ci gaba da ɓatar miki da yara" sosai suka tattauna yan da ɓatar da yaron zai kasance a ɓangaren ARUSH kuwa duk da kalar tsaron da aka bata amma sam taƙi ta kwantar da hankalinta tai bacci gani take idan har tayi bacci a wannan karon ma zata rasa yaronta tamkar yanda take rasawa, har yanzun tana jin ɗaci da kuma raɗaɗin abinda ke faruwa da ita *KINGDOM OF HANDAASH (Masarautan Handaash)* Tun lkcn da KULU dana bar wajen ABIODUN zuciyarna ke mani dukan Uku uku ban nutsu ba har sai da naga n abar sashen na koma ya zuwa namu, ni kaɗai ce a cikin ɗakin namu yayin da kowa ya kama gabansa, a hankali na fara ganin wulgawar haske wanda ya sakani rufe idanuwana ana fatan Allah ya sa Abinda zuciyans ke raya mani gsky ne Ina buɗe idanuwana hasashena ya faɗa mani gsky domin kuwa Diyana ce a gabana fuskarta ɗauke da murmushi, faɗin kalar yanayin farincikin da na shiga ba zai musultu ba,jikinta na faɗa ina mai fashewa da kukan farinciki tare da faɗin "Diyana a ina kika shiga? kika barni ba kya son ziyartana" Kaina ta shafa yayin da take kafeni da idanuwanta wanda tsabar kaifinsu sam bana iya saka nawa a cikinsu, "KULU masarautar nan shigowarta da aiki ni kaina ban shigo ba sai da na shirya, akwai haɗarurruka da dama a cikinta,da dalilin shigowana a ciki" "Diyana ban gane ba ki fahimtar dani yanda zan gane" na faɗa da tsoron dake raina fal Murmushi ta saki tana furta "a halin yanzu ba zaki gane ba amma nan gaba kaɗan za ki fahimci abinda nake son sanar dake,a halin yanzu na fara sani wacece ke a sanadin masarautar nan da kika shigo na san Ahalinki a halin yanzu" da mamaki shimfiɗe a fuskana nake dubanta "Diyana kin san wace ni? shin su waye iyayena , kina nufin duk kin san wannan???" na jero mata tambayoyi gefe ɗaya ta kalla tana furta "eh duk na sani" "na tabbatar kina da hanyar sadani dasu kuma ke mai taimako ce a koda yaushe ina mai roƙonki ki taimaka ki fitar dani a masarautar nan wllhy ina ji a jikina na zauna a cikinta da akwai abinda zai faru dani" "KULU hakan ba zai taɓa faruwa ba a halin yanzun sbd babu bawan da ya isa ya shallake qaddararsa dole ne ki fuskanceta ƙadaddararki na ata ko ina ba lallai ko kin koma a mahaifarki su karɓe ki ba, ki fahimta da akwai qaddara mai ƙarfi da zata haɗaki dasu" tana gama faɗin hakan ta ɓacewa ganina yayin da ta barni cikin tunani mai zurfi da kuma zubar hawaye waɗanda na rasa na miye yayinda maganganuta ke ƙara kai kawo a brain nawa "me ce qaddarar da zata faru dani a masarautar nan har ta haɗani dasu?" Naiwa kaina wanna tambayar wacce bani da mai bani amsa Kuka sosai naci harna gode Allah a ranar sbd tsabar kukan dana sha kaina sai da yai ciwo abinci kanshi dan Bintu ta takura min da naci na ɗan tsakura *ABIODUN* Tun lkcn daya gama sauraren ɗanyen hukuncin da Mahaifin nasa ya furta ya rasa kalmomin da zai yi amfani wajen mgn jikinsa a sanyaye ya miƙe yana mai ganin jirin da har ya kusa yar dashi a ƙasa ba don mai martaba Adewale Femi ya riƙesa ba da tuni yasha ƙasa da rinannun idanuwansa da suka jiƙu da ruwan hawaye Adewale Femi ke kallon Yaron nasa "ABIODUN did not say anything" "There is nothing I can say to leave me in this emirate, it is the end of my life." ABIODUN ya faɗa with tears in his eyes Riƙo hannayensa Mai martaba yai yana kallon idanuwan ABIODUN "kar kace haka mana ba zaka rasa rayuwarka ba akan ka bar masarautar nan ni kaina tamkar numfashina zai fita haka nake ji, sai dai idan za kayi man Arqawali ni kuma zan Barka a masarautar nan" ɗan jimmm ABIODUN yai yana ɗaga kansa alamar ya amince "ABIODUN na san da cewar a halin yanzu mace bata gabanka balle kuma soyayya, ina son Kai man Arqawali ba zaka so wata ƴa mace a masarautar nan, dukda kai ɗin mai na tabbatar mai aji ne sai dai ance ka guji makiri duk inda yake na tabbatar ko wace ita tana nan tana bibiyarka domin ka faɗa komarta ban son haɗa jini da maƙiyammu" ɗaga kansa ya sake yi a karo na biyu yayin da ya rungume mahaifin nasa yana mai tabbatar masa ya ɗaukar masa Arqawali lkcn da ya bar sashen Mahaifinsa ya shiga ya zuwa nasa ɗakin wan yanda ya barsa haka yake alamun ba a sake gyara masa ba, a ƙufule ya fita inda yaci karo da securities nasa maza ɗaya daga ciki ya kira ya gyara masa komai da komai Kuku's suka shirya masa abinci, kaɗan ya ɗan tsakura ya kwanta don ya samu relief ni kuwa washe gari tun da Asuba na tashi mukai sallar mu a ɓoye tamkar yanda muka saba , sai da gari ya ɗan fara haske before na nufin sashen Uwargidan sarki domin gyarawa Yaronta sashensa da kuma yi masa girki, a lkcn bani kaɗai bace dan haka na shiga sahun kingin Bayin muka gyara ko ina tsab, lkcn ƙarfe takwas na safe na shiga kichen inda muka fara yiwa Uwargidan sarki abinci ta da kingin yaranta, sannan mukai wa Prince ABIODUN nashi daban shima inda muka girka masa Rice stew and vegetables stew + pawpaw Yayin da duk aikin da muke Kuku Mosis na mini fira wani nayi murmushi wani nayi dariya Wani kalar Cinyan Dabba naga ya ɗauko mai tsoka da mai wan da sam ban taɓa ganin da akwai mai kal ar naman ba a Akuya rago da sauran naman mu na musulmai "what meat" zaro idanu yai yana furta "You mean you don't know Pork meat" ɗan sosa kaina nayi ina yatsina fuska cikin wayancewa nace "Awww I know" ok ya furta yana murmushi A zuciyana kuwa cike yake da ƙyamar da ƙyar na shiga taya shi wanke naman muka gyarasa sosai farfesunsa mu kayi yayinda sai ƙamshi yake zubawa tsab muka kammala, muka jera a Dinning cikin gajiya da aiki na nufin ɗakin ABIODUN zuciyana fal da tsoro A buɗe ɗakin na sameshi hakan ya bani damar turawa ina tura kaina a ciki tare da gyaran murya shiru naji hakan ya sa na fara gyara parlourn tsab ko ina sai ƙamshi ke tashi cike da gajiya na shiga fara leƙa bedroom nasa sai dai sam babu kowa a ciki ajiyar zuciya na sauke ina shiga tsab shima n gyara na wanke Toilet Da ɗan sarsarfa yake hawan step ɗin benen jikinsa sanye Da Kayan game, cikin kuzari ya tura ɗakin nashi yana mai lumshe idanuwansa jin ƙamshi ya dokar masa hanci buɗe idanuwansa yai yaga ko ina tsaf alamun an gyara motsi yaji a bedroom nashi hakan ya saka shi tunkarar ciki,motsin mutum naji a bayana wanda ya sani juyowa a hanzarce gabana na dukan ukku ukku ganin wanda nake tsaye gabanshi............... *Ma sha Allah my Habibties 💖 😻 Ina matuƙar gdy da addu'o'inku gareni much love Habibties 💖* *RIAMCOOL ce* *Writer of* RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:03 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u *A lover from the beginning You can follow my channel* *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso....* *Bismillahirrahamanirrahim* *Assalamu alaikum ina gdy ga waƴanda ke mun addu'a , sannan masu biyoni pc suna min complain ɗin bana musu Update da wuri waye da miye, na faɗa muku fa ban da lafiya, ne tun da nake Novel ban taɓa tsaitsayawa ba ba tare da dalili ba, akwai wacce tamin mgnr da banji daɗinta ba, gsky mutane ku san kalar mgnr da za ku faɗa dan Allah, Allah ya kyauta* P.23&24 Shi kuwa ba tare da ya kalli inda take ba ya raɓa ta gefenta yana wucewa tare da ɗan ƙara haɗa rai yana wucewa ta gefena, nannauyar ajiyar zuciya na saki ina hamdala ganin dukkan aikin daya kamata nai masa, Abinci kaɗai nake jira yaci, ida fitowa nayi daga bedroom ɗin na tsaya a falo ina jiran fitowarsa Shi kuwa tun lkcn da ya shige kai tsaye Toilet ya nufa da nufin yin wanka ko ina fes but ruwan wanka ne bata haɗa masa ba, da kanshi ya haɗa abinda sam bai taɓa yi ba, kuma bai damu da sai ya kira ta haɗa masa ba, ko da ya gama wanka shiryawarshi tsaf yai cikin kayan pajames yana zuba uban ƙamshi, jin cikisa na kukan yunwa ya saka shi tunkarar Falon, tsaye ƙiƙam ya ganta haka zalika idanuwanta na a ƙasa, jikinta na ɗan kyarma kawar da kanshi yai daga kallonta yana nufar dining ɗin, A hankali na fara ɗaga ƙafafuwana da suka min nauyi, haka zalika jikina naji ya fara kyarma tamkar wacce aka kaɗa wa kiɗan gangi, da ambaton Allah a bakina na nufi dining ɗin wanda da ƙyar nai serving nashi ina ja da baya tare da mayar da wani wahalallen numfashi, haka zuciyana na ƙara bugawa, hannu na saka ina dafeta bakina na jeranta sunayen Ubangiji, dukkan wani motsinta yana gani da yanayin yacce take abu, shi sai yake ganin tamkar marar gsky, bai san lkcn da ya ja ɗan siririn tsaki ba, Abinci kaɗan ya ɗan tsakura ya umarceni na kwashe kayayyakin daya gama cin Abinci, saida na sake gyara ko ina, "Come back here, I sent you to go out" ya faɗa a kausashe lkcn da nazo fita Girgiza kaina nayi ina faɗin srry a hankali cikin shakka da tsoro,siririn tsaki yaja yana ci gaba da danna wayarsa daga bisani kuma ya ajiye wayar yana ƙara kallonta tun daga ƙasa har sama, "Is it true that your body is always in pain?" Ya faɗa da ɗan yatsina fuska, girgiza masa kai kawai na iya ina mayar da kaina ƙasa Sake kallonta yake da rinannun idanuwansa wanda sam a wannan karin ya gaza sarrafa kanshi, so yake ya dinga kallonta a haka, tun ranar da idanuwansa su kayi masa tozali da KULU brain ɗinsa ta rasa samun nutsuwa, haka zalika zuciyarsa bata daina buga masa ba ,"Lift your face" ya faɗa da son jefa idanuwansa a cikin nata ɗago da idanuwana nayi waɗanda suka tara ruwan hawaye ina kallonsa a karo na farko kenan da na jefa idanuwana a cikin nashi, sosai yake ƙare mata kallo,idanuwan nata suka fara fizgarsa da yanayin yanda suke cike tab da hawaye, shi sam ba ma'abocin mgn bane ko tambaya amma a kan Baiwar da bai san asalin ta ba sai ya tsinci kansa da son jeranta mata tarin tambayoyi "your eyes never tire of tears" ya sake tambayarta share hawayen nai Ina girgiza kaina tare da kallonsa nace "I have an eye problem" ƙara taɓe baki yai yana faɗin "you can go" Ok na furta ina russunawa ƙasa na fice, wani wahalallen ajiyar zuciya ya saki yana taune lips nashi na ƙasa, sam ya gaza fahimtar al'amarin da akwai tarin ƙaddarori da dama dake tunkarosa shi ya san da haka, bai san lkcn da wasu tarin hawaye Masu raɗadi suka zubo masa ba wan da shi kaɗai ne yasan dalilin zubarsu Tun lkcn dana fita nake sauri sauri ina sauka daga Stairs ɗin,kaina na Sara min tamkar zai tsage gida biyu, ga wani zazzaɓi da nake jin yana son rufeni, na tabbatar bai rasa nasaba da yunwar dake ƙwaƙular hanjin cikina, Kai tsaye inda muke karɓan Abincimmu na nufa ina bin layi har yazo kaina, Flat na miƙa aka zuba min Teba da miyar kuɓewa wacce sam ba sonta nake ba amma tsabar yunwar dake addabana zai sakani naci Wuri ɗaya na samu ina zama tare da zubawa Flat ɗin Abincin ido ruwan hawaye na ambaliya a kwarmin idanuwa wllhy ko a mafarki ban taɓa tunanin zanyi rayuwa kalar wannan ba, na tabbatar da qaddara zanen zabo ce, haka zalika ina ji a jikina yanzu ne Alƙalamin ƙaddarata ya soma rubuta ƙaddararriyar rayuwana, yau she ne zan cinye jarabtar da Ubangiji ya ɗora min? wannan ne ban sani ba, Allah da ya jarabceni da hakan shi zai yaye man damuwata, na tabbatar da Ubangiji ba wai baya sona bane da har yayi ni haka ya mayar dani ƙasƙantacciya, wacce na zamto baiwa mai bautawa wasu tun ban san wace ni ba ban mallaki hankalina ba, "yanzu haka zan ƙare wane zai auri baiwa?? na samu nima rayuwar ƴanci na tabbatar a haka rayuwata zata qare cikin azaba da bautatawa ba tare dana raya sunnar ma'aiki ba," na ƙarshe mgn a hankali tare da sake zubar wasu siraran hawaye waɗanda ban san ranar daina zubarsu ba ba don raina yaso ba haka naɗan tsatstsakura naci ba tare da ina jin daɗin Abincin ba, Kwanaki na tafiya makwanni na shuɗewa sam babu wani canji haka koda yaushe nake azabtuwa da ayyuka waɗanda suka lillinku,sosai na fara ƴar rama tsabar damuwa dana fara sakawa kaina, wani lkcn nakan sha kuka ba adadi, ban da mai rarrashina sai Bintu wani lkcn kuma sai dai na rarrashi kaina, A hankali nake bin bishiyoyin cikin masarautar da kallo ina mai lumshe idanuwana wannan shi ne karo na farko da nai tafiya mai tsayi a masarautar nan harya kawoni ya zuwa wajen daya wadatu da korayen bishiyu, ga wani sassanyan ni'ima da iska dake ratsa jikina ban san lokacin dana saki murmushi ba ina nufar babbar ceɗiyar da ta wadatu da ganyayyaki harta saki wadatacciyar inuwa mai sanyi,zamewa wajen nayi ina mai sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da duban gefena wan da nake jin sautin tafiya, saurin janye idanuwana nayi ganin wan da ke tunkaroni fuskarsa ɗauke da wadataccen murmushi wan da yake fallasa man abubuwa da dama, "Prince ABIODUN " na ambata a hankali zuciyana na sake man dukan ukku ukku duk tako ɗaya da zai yi A hankali ya fara yawo da idanuwansa ya zuwa fuskarta yana mai sake sakin murmushin daya ƙara fallasa sirrin kyawunsa, "JOSINA" ya ambata a hankali wan da wannan sunan da shine yake kirana,sakamakon ce masa da nai sunana ne a haka ba tare da na ɗago da fuskana ba na amsa da "Yes Sir" ina mai sake makure jikina waje ɗaya, ɗan ɓata fuska yai yana furta "Stop calling me Sir" ya faɗa a shagwaɓe shiru nai ba tare da na bashi amsa ba ina mai wasa da yatsun hannayena "you can be a friend from today" naji saukar muryarsa wacce tai man ámsa kuwa sanna na daina jin wani gamsasshen iska na ratsa jikina, lkc guda na tsinci kaina da zuba masa idanuwa waɗanda lkc guda suka tara ruwan hawaye, "wllhy sam ban dace da kamar ka Mutum mai daraja da ƙima a idon duniya za kayi Abota da ƙasƙantacciyar baiwa kamarni ba, na tabbatar na amince ban yiwa maka adalci ba,kayi haƙuri na zauna a iya matsayin da nake" na ƙarshe zance da sauke idanuwana a ƙasa Shi kanshi ya san da cewar tabbas gsky ta faɗa amma sai dai sam zuciyarsa taƙi bashi damar gazgata hakan,sannan bai taɓa jin cewar zai iya cika Alqawarin Mahaifinsa KULU ita ce sanadin dukkan juyawar rayuwarsa da buɗe masa shafin kundin ƙaddararsa A hankali ya sauke idanuwansa a kanta yana mai furta "ke sam ba baiwa bace kar kiyi tunanin ko ban san asalin ki ba, ki sani tun kafin shigowarki a masarautar nan na san da cewar ƙaddarata zata gibta a tsakanina dake,tun ganin farko da nai maki Alƙalamin ƙaddarata ya sauya, nasan asalinki nasan jininki, a wannan karin KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara, sai yanxu na idar da gazgata zancen mahaifina cewar ba hasashena bane" wan da duk wannan zancen da yake yana yi ne da harshen turanci wanda idanuwansa sun kaɗa sunyi, ja lkc ɗaya jijiyoyin kansa sukai ruɗu ruɗu, yana miƙewa ya bar wajen Kallo na bisa dashi wan da sam na kasa gane zancen da yake man "ko dai ya zare" na furta a hankali "na san jininki a wannan karon KINGDOM OF JOHAAN" na maimaita mgnr ƙarshensa a hankali wacce ita ce tafi tsaya man,sosai na shiga tunanuka da dama da kuma ruɗu, da damuwa *ABIODUN* Tun lkcn da ya bar wajen KULU ya samu wata bishiya yana zamewa a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka fara wanke masa fuska ya gaza sarrafa kansa a ta wannan ɓangaren wace ƙaddara ce ke gabatoshi da son haɗa jini da maƙiyansa, tun tasowarsa babu wani abin da yafi tsana sama da KINGDOM OF JOHAAN, sai dai jarabta da ƙaddarar ce zata kasance a haka KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara a wannan karon ba zai iya tsallake tarkonsu Ya faɗa komar son KULU son da ba zai iya ciresa ba son da yake ji koda yankan naman jikinsa take ba zai iya rabuwa da idata ba, a da bai gazgata cewar ita ɗin jinin JOHAAN bace sai da bincikensa ya tabbatar masa haka zalika idanuwanta sun tabbatar masa da ita ɗin wacece ................ *RIAMCOOL ce* *Writer of* RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:04 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u *Masu so daga farko kuyi fllwng wannan channel ɗin* *KULU* *BY RIAMCOOL* *MIKIYA WRITER'S ASSO......* *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM* P.25&26 A hankali siririn hawaye suka soma zarya a kumatunsa, wan da bai san da zubarsu ba sai dai yaji ɗuminsa, kenan hasashen tsayin shekaru da bincike zai tabbata, sosai ya daɗe a bakin bishiyar yana mai jin zuciyarsa da tamkar ba a ƙirjinsa take ba Ganin kansa ya fara sara masa ya saka shi miƙewa yana fitowa in da ya bar fadawansa nan ya samesu ba tare da yai magana ba ya fara tafiya tamkar wan da aka zarewa lakka, kai tsaye sashensa ya nufa domin bai san wata hayaniya, yana so ne ya keɓe shi kaɗai ya samu nutsuwa da damar yanke mafita Ruwa ya samu ya ɗan ƙara watsawa yana kwanciya zaɓi ɗaya gareshi ko dai yabi mafitar da Mahaifinsa ya yanke na barin masarautar ko kuma ya faɗa wa Mahaifinsa wacece KULU 'sai dai a ɓangare ɗaya na zuciyarsa bai jin shawara ta biyun za ta yiyu muddin Mahaifinsa ya gano wace ita a Masarautar nan to tabbas kuwa mummunan hukunci ne zai yanke a kanta wan da bai fatan tabbatuwar hakan, sosai yai nisa a dogon tunani wan da sai dai yaji hannu na yawo a fuskarshi, buɗe idanuwan nasa yai yana saukesa akan Awujonsa wacce itama ta kafesa da idanuwa tana mai karantar yanayinsa "Think about what you are" ta tambayesa cikin kulawa da ƴar damuwa, yatsina fuska yai yana furta "nothing I have a headache" da damuwa fal a ranta ta furta " let me call you Family Doctor" "No I will drink medicine, tea I need to drink" ya furta a ɗan shagwaɓe murmushi tai tana shafa kanshi tare da miƙewa sawa tai aka haɗa masa wanda da kanta ta bashi yasha sannan ta bashi maganin sai da taga yai bacci sannan ta bar ɗakin *KULU* ni kuwa sosai na daɗe a wajen ba tare dana gano kalma ɗaya da yake nufi ba, ganin ba zan gano ba ya sakani miƙewa ina nufar sashen Bayi ban sami kowa ba sai Bintu wacce ke kwance itama a lokacin zazzaɓi ne ya rufeta, zama nai ina mai taɓa jikin nata naji da sauƙi domin babu zafi, "kin sha magani?" na tambaye ta a hankali girgiza kai tayi hawaye na fita a idanuwanta "a a ban sha ba, ban san inda ake karɓowa bane" shiru nayi ina share mata hawayen daga bisani nima na haɗe kaina da guiwa ina mai sake jin matsatsin rayuwa, Washe gari tun da na tashi na gabatar da aikina tsaf komai na haɗa masa sai sannan na tafi dan sam ba nison haɗuwata dashi, nufina idan ya gama nazo na kwashe wuraren da yaci abinci Bayan an ɗan jima na koma sai dai yanda na kawo Abincin haka na iske shi da alamar ma ko taɓawa ba ayi ba, Bedroom ɗin na shiga sai dai ƙarar ruwan da naji ya tabbatar min da cewar yana Toilet , Wani wahalallen numfashi na sauke "kenan haƙata bata cimma ruwa ba?" na tambayi kaina Ina tsaye a wajen ya fito ba tare da na kalles ba na furta

Chapter 5 of 8