Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi "KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU, sosai muka ci uwar tafiya kafin mu fita daga cikin garimmu a lokacin mun jigata sosai da tafiya ga ƙishi ga yunwa, a haka har muka isa inda aka jejjera amalanke, kayammu muka zuba a ɗaya daga ciki sannan muka shiga, kallona BINTU tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska tana ɗora hannayenta bisa kai ta kurma ihu tana faɗin "na higesu ni BINTU mutuwa ba ki man rana ba kin rabani da uwata da ubana yau gahi an hiyar dani" ni kaina hawayen naji suna neman zubar min amma sai dai dole nai ƙoƙarin shanyesu ina taune leɓena na ƙasa, tare da furta sunayen Allah Muna ji muna gani haka muka dinga tafiya har Allah ya iso damu cikin birni a lokacin ne Shu'aibu ya siya mana Abinci wanda da ƙyar muke tura shi ,daga nan mota muka hau wacce za ta kaimu har garin OYO tafiya bata wasa muka yi ba, dan Sallah ce kaɗai ke tsayar damu, sosai na jigata naji cikina ya juye na fara zazzaga Amai tamkar zan amayar da hanjin cikina, da tausayi Bintu ta dinga yi man sannu ɗaga kaina kawai na iya yi, wani dogon tsaki Shu'aibu ya ja yana furta "dan uwar ki lashe aman da kikayi kin wani ɓatawa mutane mota, ki lashe ko na yi miki lilis a motar nan" hawaye tuni suka ƙara jiƙa man fuska ina furta "kayi haƙuri idan an fita zan gyara motan amma bazan iya lashewa ba" ƙwafa kawai yaja yana juyawa, ba da jimawa ba muka sauka in da Bintu ce ta gyara inda nayi Wa amai, lkcn dare har yayi, hakan yasa Shu'aibu cewar mu biyo shi,zuciyata cike da ɗar ɗar muka bisa tare da hawan adai daita ya kaimu wani guri, ɗan ƙaramin gida ne Shu'aibu ya kaimu wan da cikinsa ɗaki ɗaya ne kacal, gashi ana tsuga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, shiga mu kayi ɗakin muna muzurai dan tsoro, wani kalar kallo Shu'aibu ya bimu dashi yana murmushin gefen baki, a hankali ya ƙara so gabanmu yana saka hannunsa yana shashafa mu tare da lumshe idanuwa, "Innalillahi miye haka ka daina dan Allah babu kyau" na faɗa ina girgiza masa kai hawaye na zuba "Zan ci uwar ki kika sake magana, wllhy dole ne na taste ɗinku kafin na kaiku gidan arnaye waɗanda basa dungura goshinsu a gabas na tabbatar duk sai sun dinga kashe dare daku, to nima yau zan kashe arna daku" ya faɗa yana washe baki, ganin yana taɓa dukiyar Fulani su, kuka Kulu da Bintu suka saka yayin da sukai ƙoƙarin ƙwatar kansu amma sam sun gaza, wani kalar ihu suka ji Shu'aibu ya fasa yana ja da baya, nan take idanuwansa suka fara kakkafewa ya faɗi, wani kalar ajiyar zuciya na saki ina murmushi tare da furta "Diyana" banji an amsa ba hakan ya sakani sulalewa ƙasa ina kwanciya bacci na ɗibata, sai da gari ya ɗan fara haske sannan na buɗe idanuwana bakina ɗauke addu'a Bintu na tayar muka fita sai dai babu ruwa hakan ya saka muka ɗauki ruwan roba mu kayi arwallah, har muka ƙarashe sallah Shu'aibu bai tashi ba, nan take gabana ya faɗi na fara tunanin karfa ace Diyana tayi halin nata ina cikin tunani haka muka ji yana tari tare da miƙewa, yana hamma, ruwan ya ɗauka yana fita ya wanke fuska da baki, kallomu yai yandaa faɗin "idan za mu fita ya zama wajibinku ku cire hijabbanku, sannan inda zan kaiku ku kiyaye wani ya gano cewar ku musulmai ne, idan aka gano tabbas kun kaɗe," shiru mu kayi yana faɗin mu tashi mu fita, Hijjabin muka cire wasu hawaye Masu zafi na biyo kuncina "ya Allah" na furta a hankali tare da tunanin wane shafin kundin ƙaddarar zan buɗe a yanzu, baya ga cikakken littafin ƙaddarar dana ƙarasar a baya, tamkar wacce aka zarewa lakka haka na bi bayansa muna fita wata motar muka sake hawa wacce kwana mu ɗaya da yini sannan muka sauka, muna sauka, muka hau a dai daita ya kaimu wani waje, inda ga mutane nan da dama ko wane a dudduƙe wan da mafi akasari su duk ƴam mata ne, layi Shu'aibu yabi tare da umartar mu durƙusa mu duƙar da kawunnanmu, layi ne yazo kan Shu'aibu nan take aka gama cinikummu ya tafi, dukkamu durƙushe muke ga wata uwar rana da ake yi wanda tuni muka fara gumi zufa na tsiyayya mun sha baƙar wahala kafin azo da wata ƙatuwar mota ta Alfarma wacce tun da nake ban taɓa ganin kalarta ba, cikin ta aka zuzzuba mu muka fara ɗaukar hanya, manmanyan gidaje muka dinga ketawa wan da a iya rayuwata ban taɓa tunani da akwai kalar su a duniya, nan na shafa'a wajen kallo, wani danƙareran get muka ga an shiga ciki wan da nan take zufa ta fara yanko man gabana ya tsananta faɗuwa ,..................... *RIAMCOOL ce* Writer of *RUSHEWAR RAYUWA* *BAYAN WUYA* *ANYA UBA NE* And now *KULU* [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso...* *Bismillahirrahamanirrahim* *P.11&12* Sunayen Allah na fara jerowa da nufin zuciyata ta samu salama daga bugun data fara man, ban ida razana ba sai da naga wani baban get ɗin masarautar mai tambarin wani baƙar halitta da ƙaho nan take gabana ya ƙara yankewa yana faɗuwa, sosai nake jin tamkar na taɓa rayuwa a masarautar nan, nake ga wasu munanan abubuwan na dawo mani, wan da tun a wancan ƙarnin ya faru, Wata muguwar tsanar masarautar ce tai man dirar mikiya , nayi nisa a cikin tunani naji ana faɗin "Iwọ jẹ obinrin dudu" (ke baƙar baiwa fito) naji an faɗa da wata ƙatuwar murya wacce ta saka jikina kyarma sbd tsoro, jikina a mace na fito nabi layi muna tafiya, tamkar wasu dabbobi maras galihu haka aka mayar damu, sbd duka Kafin mu ƙarasa ya zuwa get ɗin ƙarshe, sosai na jigata sbd bulalar da aka shaɗa man, wajen ya fashe ga zafin rana, numfarfashi kawai nake mayarwa ina jera sunayen Ubangiji Muna kaiwa ƙarshen get ɗin aka umarce mu da mu zube a ƙasa, zubewa mu kayi ko wane kansa a ƙasa, mun fi ƙarfi 2 hours before a fara kirawo mu ko wane ana kaisa ya zuwa inda zai zauna, waje guda aka haɗamu nida Bintu, daga nan ma haka muka ci uwar tafiya kafin mu isa sashen bayi, wajen uwar bayi aka kaimu, wacce ta kasance itama yare ɗin ce, kasancewar ina jin yarensu da kuma turanci shi yasa abin bai man wahalar gane zancen ta ba, kan cewar za ta ƙara ni a cikin hadiman uwargidan sarki, wanka muka fara yi sannan muka ci Abinci, ganin marece yayi sosai ya tabbatar man da cewar la'asar ta wuce sosai hakan ya bani damar ɗauro Arwallah, ɗakin da muke ciki muka kulle sannan muka samu muka fara ramuwar sallar dake kanmu, a daren ma haka mu ka kulle muka yi sallar, kasancewar mun kwaso uwar gajiya ya saka mu kwanciya da wuri, baccin wahala na ɗaukar mu Washe gari tunda sassafe muka ji bugun ƙofa tamkar za a ɓallata, tashi nai na buɗe ina kallon Uwar bayi dake faɗin "wash your face and follow me" da ok mah na amsa ina shiga Toilet ɗin na ɗauro Arwallah sai dai ganin Uwar bayi a wajen ya saka jikina yin sanyi ganin ba zan samu damar yin sallar ba Kaya ta bani, Riga ja zane baƙi tace na saka daga yanzu su zamto cewar sune kayan Sakawata Juyawa nayi zan shige Toilet na saka naji tana faɗin "where are you going with the things in your hand" "I'll wear it". na faɗa, zaro ido waje tai tana faɗin "It's a change of clothes and you have to go Toilet"shiru nayi ina zare ido kar ta gano ni bahaushiya ce, dan Shu'aibu sai da ya gargaɗemu akan mu nuna musu mu ba hausawa ba ne "Which tribe are you, the ozo or ogboni tribe" na tsinkayi muryarta wacce gabana ya faɗin, yawun tsoro na haɗiye ina furta Ogboni girgiza kai tayi tana taɓe baki, a kunyace na sauya kayan a gabanta, fita tayi na bita a baya wanda naga muna ƙara tinkarar get Wanda nabi da kallo tsabar kyansa tamkar wata sokuwa, "da gani da zallar gold aka ƙera shi" na faɗa a zuciyata jigajigan securities, ne ke gadinshi kasancewar sun san uwar bayi shi yasa bamu samu wahalar shiga, ba , daskarewa waje guda nayi ganin wani hamshaƙin waje daya bayyana, har tuntuɓe na kusa yi, tsabar kallo, ban ida tsurewa ba sai da muka shiga wani hamshaƙin wuri daya saka brain ɗina dakatawa da aiki, ganin zallar gwala-gwalai ne ke walwali a wajen, taɓani uwar bayi tayi hakan ya saka tunanina dawowa, tamkar raƙumi da akala haka na dinga bin uwar bayi harya zuwa wani babban Falo wanda ya fi na can da haɗuwa kamar wata sokuwa haka na zama wajen kallo kafaɗata da uwar bayi ta buga ne ya saka hayyacina dawowa ya zuwa gangar jikina, wani yawu na haɗiye ganin yadda uwar bayin ta zube a ƙasa tana mai taɓa wata matashiyar budurwa wacce a ƙalla ba zata wuci 23 yrs ba, tsawar da naji uwar bayi ta doka man akan ban zube a ƙasa ba ya sakani zubewa kamar yanda tayi jikina na karkarwa, ba tare da matashiyar budurwar nan tayi mgn ba ta ɗora ƙafafuwan ta ya zuwa gadon bayammu tana karkaɗasu, tamkar na fasa ihu tsabar takaici, hawayen da naji na ƙoƙarin zubo man na danne, sbd na tabbatar a haka zan ƙarashe rayuwata cikin ƙunci da takaicin duniya, tafi ƙarfin 15 minute sannan ta sauke tana kallommu a yatsine, Tashi mu kayi sannan tai mani nuni da hannu alamar na taso, miƙewa na matsa kusa da ita hannayena ta ɗora ya zuwa kafaɗunta alamar nai mata tausa, banbaranƙwai naji abu na fara mata a hankali tana lumshe idanu, duk yanda nai ƙoƙarin danne hawayen dake ƙoƙarin zubo man sai da na kasa, ba tare da na bari wani ya gani ba na sharesu na ci gaba da aikina, kallona uwar bayi tayi tana faɗin "Alamu sun nuna ki zauna a baiwar gimbiya Sontum ,daga yau duk wani hidima kece za kina yi mata, sannan ki faɗa mana sunanki" cikin ɗan razani na faɗa musu Josina amma ana kirana da KULU,ba tare da wani yace ƙala ba Uwar bayi ta wuce, ni kuwa bayan na gama mata tausa ne ta haɗani da wata baiwa wacce tai man bayanin abubuwan da zan dinga mata, hankalina bai tashi sai da naji wai har kaya nice zan saka mata, a lkcn ihu ne kaɗai ban fasa ba, haka naja na tsaya a bayanta duk idan ta buƙaci wani abun nice ke yi mata,a yinin ranar sosai nasha baƙar azaba wacce ko maƙiyina bana yiwa fata [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso* *Bsmllhrhmrhm* *P.13&14* Tamkar na fasa ihu tsabar zullumi haka nake ji Addu'a ta bata wuci Allah ya sa tace na tsaya daga bakin ƙofar shiga, sai dai Addu'a tawa bata karɓu ba, haka na shiga wan da babu abinda ke tashi a Baban Falon idan banda ƙamshi ga wani lallausan Cafet da nake jin ƙafafuwana luntsume ciki, ina son ɗago da idanuwana, na basu abinci amma babu dama tsabar kar nayi laifi, jiki a ɗaɗɗare na faɗi nayi gaisuwa wan da babu wanda ya kulani "What are you doing here?if you don't come and work as a slave" naji furucin wata dakakkiyar murya ta mace wacce ta sakani haɗiye wani yawu ina kallonta da Alamu dai itama Baiwar ce sai dai amma tana da iko a kan Bayi dubana nakai gun Sontum sai dai naga sam bata a wajen wannan ya nuna cewar ta shige ya zuwa ciki ajiyar zuciya na saki ganin ban shiga ba, dama sam ban sa haɗuwa da mutanen ciki musamman mai zuciyar fir'auna ABIODUN da naji suna faɗi don nidai harga Allah tun kafin na saka sa a idona tsoronsa ya cika man zuciya da fargabar haɗuwa dashi duk gyaran da Babban Falon yasha sai da ta sakani sake masa wani gyaran, Fruit ta sakani yankawa Ina gamawa na kai mata "go inside and reach the King's Lady " naji furucinta wan da ya sakani zaro idanuwa ina ɗaukar Fruit ɗin ya zuwa ciki a hankali na kutsa kaina ina duƙar da kaina ƙasa wan da tun daga bakin ƙofar shiga ya kasance duk barrori ne, masu hidima yanayin da naji bugun zuciyata na hauhawa da kuma ficewar tsoron da yai man ƙawanya azuci ya sakani ɗago da manyan idanuwana na saukesu ya zuwa wata babbar mace wacce taci ado na ban mamaki haɗaɗɗiyar bayeraba mai madarar Izza cike da mulki , kallo guda za kai mata ka tabbatar ita ce matar sarki Sontum ce liƙe a jikinta wan da zaka tabbatar ita ce Mahaifiyarta a hankali na faɗi nayi gaisuwa na ajiye mata Fruit ɗin a gabanta, *Ɓangare guda kuwa* Tun lokacin da ABIODUN ya dawo ya zuwa Masauratarsa dukkan wani sirri na masarautar JOHAAN ya kawo wa Masauratarsa da kuma shirya Babban tuggu na gani sun rushe masarautar JOHAAN da dawo da mulkin ya zuwa gare su, Babbar Fada ce ta Alfarma wacce ta gaji da haɗuwa tsabar kyau sai dai duba ɗaya za kayi wa Mutanen cikinta ka tabbatar da akwai damuwa data shimfiɗu akan fuskokinsu musamman ma Sarki Adewale femi , zufar data tsatstsafo mishi ya share yana faɗin “Ìyọnu àjálù wo ni yóò ṣẹlẹ̀ ní ìjọba Handash,(wace musiba ce ke tunkaro Handaash) na tabbatar jinin JOHAAN na a cikin masarautar nan tun ranar da Bugun zuciyana ya sauya numfashina ke cikin gargada na tsoron faruwar abinda Soluwole ya faɗa, Mo n sa fun isẹlẹ naa, ABIODUN gbọdọ kuro ni Ijọba yii (ina gudun faruwar abun ya zama dole ne ABIODUN ya bar masarautar nan") dukkan mutanen cikinta sosai suka girgiza da Kalaman sarkin Adewale femi Eyin Oba wa Adewale, e jeki a so pato nipa ipo ti e ba n kuro ni ABIODUN lo si ijoba yii, e ranti ABIODUN ni ohun ija wa pataki, ti olori ilu Handaash si dabi Abin Buta Soluwole. (Ya Sarkimmu Adewale Femi ka ƙara jiɓantar lamarin kana ganin barin ABIODUN a masarautar nan mafita ce, ka tuna cewar ABIODUN shine makamin masarautar JOHAAN ,kuma jigo a gare ta shi ɗin tamkar Abin Bauta Soluwole muke ganinsa" wazirinsa ya faɗa tare da duƙar da kansa ƙasa Shiru yai yana nazartar maganar waxirin nasa tabbas gaskiya ya faɗa Tun faɗowar ABIODUN ya zuwa doron duniya ya tabbata dashi ɗin jigo ne ga masarautar sa, ko kaɗan bai son ƙaddarar ABIODUN ta juye ya zuwa yadda aka faɗa masa kuma tabbas ya san da zata faru ɗin amma koda rayuwarsa zai rasa ba zai taɓa bari hakan ya faru akan ABIODUN ba, tabbas bokansa ya faɗa masa cewar Jinin Handaash na a cikin masarautar nan, sosai idanuwansa sukai ja sannan shatin jijiyoyin kansu su kayi ruɗu ruɗu tsabar tashin hankalin da yake ciki Jin kansa na neman tarwatsewa ya saka sa sallamar mutanen fadar, tun lokacin da ya shiga sosai abubuwa ke dawo masa, wanda yake jin babbar muguwar tsanar masarautar JOHAAN na masa ƙawanya a zuci shigowar Boluwatife ya saka shi mayar da hankalinsa ya zuwa kanta wacce ta gaji da kyau tsabar haɗuwa, a hankali ta zauna kusa dashi tana masa murmushin da tasan na kashe masa zuciya sannan ya bayyanar mata da sirrin dake ransa, bayan wasu ƴan Mintuna ta ɗago da manyan idanuwanta tana kallonsa wanda take son gano wani abun cikin yarensu take faɗin "Ya shugaba majiɓancin lammuran Masarautar JOHAAN Baba ga yarima ABIODUN majiɓancin lamurran Handaash tabbas da akwai damuwa a ranka, sannan zan so ka bayyanar man da ita, inji idan da akwai mafita" ta faɗa cikin sigar ladabi da daddaɗar murya mai kwantar da ran Sarki Adewale Femi tamkar wanda ke son dama a tayar da zancen haka ya miƙe yana saka idanuwan nasa a cikin na matar tasa, "Boluwatife tabbas ina cikin damuwa sannan dake kaɗai zan iya shawara a cikin lumana ki samar man da mafita, da akwai babbar musiba a Masarautana ko kin san da cewar da Akwai Jinin Handaash a masarautar nan,a da na yanke Shawarar ABIODUN ya bar masarautar nan na tsawon wasu shekaru masu tarin yawa gudun faruwar abinda aka faɗa a wancan ƙarnin" ya faɗa da tsantsar damuwar dake cin ransa Wani shaiɗanin murmushi ta saki wanda bai fito a bayyane ba sai ma tarin damuwar data shimfiɗa a kan fuskar nata tana faɗin " tabbas ka kawo Shawara sai dai da akwai......" bata idasa ba sakamakon maganar daya fara yi " na sani Boluwatife ABIODUN ɗina shine jigon masarautar nan bai cancanci ya barta ba ABIODUN ɗina shine cikar kamalar Masarautar Handaash sannan makami Babban Jigo, dole mu canza shawara" murmushi ta saki dukda ba hakan taso ba, ta ɗan jima before ta miƙe ta fita barorinta na take mata baya har izuwa Sashen ta, tun da ta shiga ta faɗa a babban gadon nata tana lumshe idanuwanta tare da shafa cikin jikinta daya bayyana Me ya za har yanzu ta gaza cimma ƙudirinta a wannan karin ba za tayi ƙasa a guiwa ba ya zama dole tai ƙoƙarin ƙara cusawa Oba Adewale Femi son fitar da ABIODUN a masarautar nan wannan ce damar ta , *LONDON* *ABIODUN* Kwance yake a bakin Swimming pool Ya lumshe Manyan idanuwansa ya kai a ƙalla ten minutes before ya waresu a hankali yana mai ɗan yatsina fuska ganin kallon da wata Baturiya ke wa haɗaɗɗiyar Baƙar fatarsa wanda tsabar kyau har wani sheƙi take tana walwali from his navel or wherever a murmuɗe ganin tana ƙara bin His broad chest and eyes are wide open ya saka sa jan Dogon tsaki yana faɗin "Witch" Tamkar hadarin gabas haka ya saƙe ɗaure fuskarsa yana miƙewa nan take cikakkiyar ƙirarsa ta bayyana, dogon kitson daya sha ya zubo a dokin wuyansa, Headphone nasa ya ɗauka yana liƙawa a kunne ya fara tafiya cikin gadara da cikakkiyar Izza interesting what to look at, tamkar haɗin Baki Ƴam matan turawan suka haɗa baki wajen furta "wow, handsome man" Ba tare da ya juyo ya kalli ɗaya daga cikinsu bcox shi sam ma bai san da su sbd Headphone ne a kunnesa yana jin waqar Naira Marley................. *RIAMCOOL ce* Love U all my Habibties💖😻 [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *By RIAMCOOL* Mikiya writer's Asso....... P.15&16 Haɗaɗɗen masaukinsa ya nufa yana zama bisa ɗaya daga cikin kukerun Falon tare da lumshe Manyan idanuwansa yana ɗan kaɗa ƙafa before ya cire Headphones ɗin yana ware idanuwansa akan phone din dake ringing, hannu yakai yana ɗauka a hankali yai picking duba ɗaya za kayi masa ka san tabbas kiran mai muhimmanci ne duba da yadda ya tattara nutsuwarsa da kuma yalwataccen murmushin dake ɗauke a kyakkyawar fuskarsa har yai sanadiyyar lotsawar kumatunsa wan da ba ƙaramin sihirtaccen kyau yai ba "Hello" ya faɗa to drown wani ajiyan zuciya mai martaba Adewale Femi ya saki daga ɗayan ɓangaren yana mai lumshe idanuwansa jin muryan Yaron nasa "ABIODUN how are you? hope you are in good health," ya faɗa da murmushin karfin hali dake ɗauke a fuskarsa "Yes, Daddy, I hope you are safe, but I heard your voice in worry, I hope there is nothing wrong with you" ABIODUN ya faɗa da ɗan damuwa,murmushi mai sauti ya saki yana faɗin "Yes, ABIODUN, I just want you to leave LONDON and come, there is something important, like this help" Oba Adewale Femi ya faɗa da ɗan damuwa da kuma rashin son maganar ABIODUN yace "Daddy I will come but tell him your worries (Daddy zanzo amma ka faɗa man damuwarka") "nothing ABIODUN" Oba Adewale Femi ya faɗa da ƙarfin hali tare da katse kiran yana sauke ajiyar zuciya wasu hawaye Masu raɗaɗi na zubo masa, na tunawa da shawarar da ya yanke na fitar da ABIODUN a cikin Masarautar sa A ɓangaren ABIODUN ma haka ya shiga cikin damuwar yana tunanin ko wani abu ya faru da masarautar nasu da har Mahaifin nasa ya gaza furta masa, nan take yaji zuciyarsa ta gaza nutsuwa , kamar ya kira Mahaifiyarsa sai kuma ya fasa ganin ko ya kira ba Lallai ace ta san sirrin Oba Adewale Femi ba,kyawawan lips nasa na ƙasa ya jiza yana shafa manyan kitson kansa tare da lumshe Manyan idanuwansa he went into thinking abubuwa da dama, da ƙyar ya samu ya rintsa a daren washe gari tun da safe ya sa aka shirya masa private jet,ya zuwa Nigeria garin OYO, A hankali yake bin matattakalar jirgin yana saukowa cikin nutsuwa da jarumta, da kuma cikakkiyar Izza mai yawo a jininsa,wan da idanuwan Mutane suka fara yawo kansa Musamman ganin prince ABIODUN, ganin yanda idanuwan mutanen ke yawo a kansa ya saka shi

Chapter 3 of 8