jan ƙaramin tsaki yana kawar da kansa gefe guda, kai tsaye wajen jiga_jigan motoci na Alfarmar da aka shirya masa ya nufa tare da shiga ɗaya daga cikin cars ɗin hakimcewa yai a Back sit yana duba watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa tare da ɗan ciza lips nasa wanda ya zame masa Al'ada
kai tsaye Masauratar Handaash su ka yiwa tsinke wan da a duk daƙiƙa ɗaya zuciyar ke masa wani irin bugu wan da bai san dalilinsa ba,
*KULU*
ni kuwa tun lokacin da na shiga wajen uwargidan sarki nake Allah yasa na fito lafiya ba tare da nayi laifi ba sai dai Addu'a ta bata ci ba domin kafin na fito sai da nasha tafikan uwargidan sarkin har biyu akan ta kamani wai ina kallonta, sannan ta bani aiki mai tsanani akan na dawo ɓangaren ta nice zan dinga gyara ko ina da duk wani abinci tare wai da kular mata da Babban ɗan ta wato Prince ABIODUN lokacin da tace hakan hantar cikina ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba, dan harga Allah ban son abinda zai haɗa ni da mugun ɗan ta kamar yanda naji ana faɗa, bata barni haka ba sai da ta sakani nai aikin da na jigata ba kaɗan
tunda na shigo ɗakin nake ta huttai da nishi tsabar gajiya ga sallolin dake kaina, ga babban tashin hankalina mutane na a ɗakin domin a ɗakin Bayin gidan aka
Maido mu mu kusa 8 ne a ciki wanda kowa a takure yake bacci, a boye na yi Arwallah na fita daga Bayan ɗakin inda na tabbatar da ba za' a kamani ba na yi Sallolin before na dawo ɗakin , ina rarraba idanuwana don naga Bintu ganinta a kwance ya sakani tunkarar inda take ina ɗaka mata duka a baya tare da ƴar dariya Are you tired? hararana ƙasa _ƙasa tai tana cewa "ke Hegiya Alqur'ani kin san ba jin harhen nasaran nan nake ba ki man harhena kawai ni ban iya harhen kahurai ba a to" ta faɗa tamkar mai raɗa ƴar dariya nai ina kwanciya tare da furta " Bintu kin gaji ne" hawayen dake maƙale a idanuwanta ta samu tana matsowa tare da furta "wallahi KULU masarautar nan akwai zalunci da yawa ko kin san......." sai kuma tai shiru kuka yaci ƙarfin ta ƙasa ƙasa, gani idanun mutanen ɗakin ya fara dawowa ɗakin ya sakani kama hannunta ina miƙar da ita zuciyana a cunkushe da damuwa ganin hawayen Bintu wanda nake ji har a cikin raina, fita mu kayi na zaunar da ita ina kafeta da idanuna ni kaina ji nake da zan iya kukan babu abin da zai hanani fashewa dashi ," haba Bintu ki yi shiru da huƙurin cinye jarabawar mu, haka Allah ke son ganimmu ba Wai don bai sommu ba, don ita ƙaddara zanen zabo ce duk wayonka baka isa ka tsallake ta ba, Bintu kiyi duba dani wace rayuwar ce ban gani ba?ni ɗin nan ko ɗumin Mahaifiyata ban ji ba, ban san asalin wace ni ba shin ni ƴar waye ban sani ba , shin Ƴar shege ko Ƴar sunan? ban sani ba Bintu, naga kyara da tsanana cikin Al:umma naga ƙuncin rayuwa wacce ban san iya adadin ta ba, Allah ya jarabceni ta hanyoyi da dama" na faɗa wasu ƙwallar takaicin rayuwa na zubar min
shiru Bintu tayi tana share hawayenta tace "Kulu tabbas kinga rayuwa,na haƙura na karɓi ƙaddarar da Ubangiji ya ɗora man"
Murmushin karfin hali na sakar mata ina faɗin "faɗa min abinda ke damunki da har kika kasa faɗa man"
"KULU ina cikin matsananciyar damuwa ana so a keta man Haddi a masarautar nan daga mazan har matan wallahi da idona jiya naga wani abu ita waccan ochuchuwa take kowa? suna iskanci da wani mugun bafaden nan Ayomide kin sannin ban iya rufi tsinannan katsalanda na ya jawo min, hine na jira suka gama, nai masu maganar Ƙurame akan cewar na ga suna iskanci kuma sai na faɗa, to hine suka kama man dariya, Ayomide harda taɓa ƙirjina ya tsotsi bakina ta ƙarfi, sannan Ochuchuwa ta dinga taɓa man ƙirji har na gaza ƙwatar kai na, suka gama tattaɓeni,nayi kuka ban faɗa miki ba, to hine yau Ochuchuwa ta gayyato qawayenta suka riƙeni suna tattaɓa ni, dan har kayana suka cire man haihuwar uwata suka ganni za suyi man fyaɗe Allah ya bani sa'a na kuɓuce musu" ta ƙarashe zancen cikin kuka da ƙunar rai
ɗan jim nayi ina rintse idanuwana,gabana na faɗuwa jin furucin Bintu, haƙuri na bata tare da rarrashinta sannan ta ƙara jajircewa wajen riƙe mutuncinta , wan da sosai na girgiza da lamarin gidan Sarautar, sannan na tsunduma Tunanin DIYANA wacce na rabu da ganinta ban san dalilin ƙin ziyartana ba, hawaye naji sun ƙara cika mun ido na tabbatar da Diyana ma na rasata "ba nida kowa yanzu?" na tambayi kaina wan da ban san maganar ta fito ba sai da naji Bintu na faɗin "KULU kina dani mana, kamar yanda ban da kowa sai ke haka kema bakida kowa sai ni, mu haɗu mu rungumi ƙaddarar mu" ta faɗa da ɗan murmushin karfin hali
murmushi nai mata ina miƙewa muka shiga ɗakin, tun da muka shigo na lura da kalar kallon da Ochuchuwa ke bina dashi don idan ba gizo idanuwana su kai man ba har lashe leɓe take, hakan ya sa nace Bintu ta kwanta tai baccinta cikin salama babu abinda zan bari ya faru da ita, baccin dai a ɗaɗɗare ta yisa ina jin yanda take faman sauke ajiyar zuciya, nima kwanciyar nayi amma sam na gaza yin Bacci wanda na tabbatar kowa yai bacci, ajiyar zuciya na sauke wanda nima baccin ya ɗan fara ɗaukana
Washe gari tun da safe ko wane ya nufi ɓangaren aikinsa, ni kam raina cike fal da damuwa da zullumi na nufi sashe Uwargidan sarki
Tunda na shiga Babban Falon zuciyana ke ƙara hauhawa da bugawa ina jero sunayen Ubangiji, gefe naja na tsaya ganin sai bayi ke hada hada a Falon da gyare gyare, wata ce ta dafa ni tana furta ""you are KULU" yeah na furta ina dubanta "ok Follow me" kamar yanda tace haka na bita muna shiga wani coridor da ya kaimu stairs mai mugun tsayi da yasha floor Cafet ,a hankali muka nufi babbar ƙofar ɗakin wan da a kaf ɓangaren gidan nan ban taɓa cin karo da kalarta ba bcox yanayin girmanta da kyawunta, security door , handle ɗin ƙofar ma Automatic digital biometric lock ne irin na zamani wanda ba kowa ne ke shiga cikinta ba
Da kanta matar ta buɗe man tana furta na shiga na gyara ɗakin kaf, da to na amsa ina kutsa kaina a cikin ban san lokacin dana ƙara murtsike idanuwana ba ina jijjiga kai, tare da ƙara mamakin daman a gidan duniya da akwai kalar waɗannan kayan Alatu da more rayuwa, wllhy ko a mafarki ban taɓa cin karo da kalar wannan haɗaɗɗen wajen ba, a hankali na kara ware idanuwana da nufin ƙara basu abinci sai dai karaf idanuwana suka sauka ya zuwa wani tangameman photon Wanda na kafe da ido ina kallon fuskar kyakkyawan mutumin dake cikinta , ya sha Suit baƙaƙe ga manyan kitson kansa da ya zubo har dokin wuya , babu abinda yafi jan hankalina sama da murmushin da ya saki har gefen kumatunsa ya lotsa, ga manyan dara daran idanuwansa da ya qara warowa wanda ya bada wani fatsion na daban, ko tantama ban yi wannan shine mamallakin ɗakin kuma Prince ABIODUN ɗin da ake nufi jarumin gwarzon masarautar
[10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU*
*BY RIAMCOOL*
*Mikiya writer's Asso.....*
Bismillahirrahamanirrahim
P.17&18
A hankali nake bin Stairs ɗin ina sauka hannuwana riƙe da kwankwasona wanda tsabar gajiya ce ta sakani riƙewa wanda a hakan ma wai ban idar da aiki ba, "wash" na furta a hankali time ɗin dana sauka daga shegiyar Stairs ɗin mai tsayi,kallona Baiwar tayi tana faɗin"You're going to cook now" cike da gajiya na amsa da ok tare da furta "a ina ne kichen ɗin?" na faɗa da harshen turanci ba tare da tace man komai ta nuna man hanyar da zan bi ya zuwa kichen ɗin,
Tun kafin na ida isa ƙamshin girki ya fara ziyartana wanda har wani lumshe ido nake ina ƙara baza hancina , a hankali na kurɗa kaina a haɗaɗɗen kichen ɗin ina mai bin kuku's ɗin da kallo wanda dukkansu maza ne ni kaɗai ce mace kasancewar basu Sanni ba ya sakani gabatar da kaina, sanin cewar ban iya kalar girkinsu ba ya saka duk wani abun yankawa na yanka masu, haɗaɗɗen Yamnita and vegetables stew suka girka da fish fillets and liver Wanda a cewarsu sune favorite food ɗin ABIODUN shi ya saka aka girka masa ,kasancewar yana hanyar isowa masarautar, cikin haɗaɗɗun warmer masu masifar kyau aka zuba masa, wani Kuku Mosis ne ya umarceni dana shirya Abincin tsab a Dining, sannan kafin na shiga na tabbatar na tsabtacce jikina har turare na saka sbd ABIODUN nada tsauri da kuma ƙyama idan har ya ganni a haka zai iya amai, wani yawun takaici na haɗiye ina ɗaga kaina na fice
ba wani ɓata lokaci nai wanka tare da sauya wasu kayan suma dai irin na bayin ne sanin cewa ban da turare ya sakani ficewa kaina tsaye ina faɗa wa Mosis ɗin cewar ban da turare, turarensa ya bani na shafa, sannan na ɗauki Abinci naje na fara jerawa wanda na iske Abinciccika da dama da juice duk an shirya wanda nake mamaki na tabbatar ko mutum Talatin ba lallai su cinye abincin dake shaƙe akan dining ɗin ba ,
*ABIODUN*
Ko da suka iso Masarautar kai tsaye sashen Mahaifiyarsa ya wuce, Hakimce take a bisa ɗaya daga cikin kujerun Falon Hadimai na hidimta mata, wanda ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana shan ƙamshi,Ahankali ya saka ƙafafuwansa ya zuwa Falon ba tare da yayi magana ba, sai dai ɗan gyaran murya wanda ya ankarar da Maman nashi, murmushi ta saki tana miƙewa ya zuwa gunsa tai hugging nasa tana shafa fuskarsa tare da faɗin "Welcome to my son how are you?"
ɗan murmushin da ba lallai ka gane yana yinsa ba yai mata tare da sumbatar goshinta yana faɗin "fine awujo" (umma) da yake haka yake kiranta
murmushi ta saki tana sakinsa tare da furta kọkọ lọ lati wẹ ( ka fara zuwa kai wanka)
"Ok Awujo" ya furta yana wucewa ya zuwa part nasa,A hankali ya shiga ɗakin yana mai lumshe idanuwansa jin wani daddaɗan ƙamshi ya ziyarcesa bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba, yana buɗe idanuwansa ya sauke akan Babban Falon nasa wanda aka canzawa tsari yasha gyara da ado na musamman, shafa kitson nasa yai yana ɗan taune lips nasa, Bedroom nasa ya shiga inda ya samu mata Bayi a ciki ko wace kanta a ƙasa yayin da suke jiransa ya shigo ,ƙara haɗe kyakkyawar fuskarsa yai yana shiga Toilet har ruwan wanka da turarukan jiki duk sun haɗa masa, kai tsaye wanka yayi sosai sannan yai na ruwan turare, Towel kawai ya ɗora ya fito
Nufosa su kayi da nufin yi masa shafa sai dai cikin tsantsar ɓacin rai ya furta "even if that one of you goes out, don't let the one that ends up with me Before I count three, leave because I don't want to see your ugly face" ya furta a masifance
Tuni jikinsu ya hau kyarma ko wace nason rigan ƴar uwarta fita sbd suka tsaya tsab zai iya kashe su tsabar masifarsa , ƙaramin tsaki yaja yana ganin duk laifin Awujonsa ce da take mayar dashi ƙaramin yaro idan banda abinta miye na wani bashi Hadimai mata masu masa shafa dukda kasancewarsu Dattijai ne, da baiyi tsaye ba ya tabbatar har wanka za su iya masa ma "Just abastard" (Ƴan iska kawai) ya faɗa a ƙufule
cikin ƙanƙanin lokaci ya gama shirinsa tsaf jikinsa sanye da dakakkiyar shaddar wacce taji haɗaɗɗen ɗinkin Yoruba wuyansa saƙale da murjanai masu masifar kyau da tsada, haka zalika kansa sanye da hularsu mai tsada ta yoruba wacce ta ɓoye kitson da yai,sosai yake baza uban ƙamshi kai kace Company turare ne a jikin nasa, ƙafafunsa sanye da loafters cover shoe
cikin taƙama da isa ya fito daga ɗakin yana sauka down stairs wacce za ta kaisa wajen Awujonsa, babu kowa a Falon nata duk ta sallami Hadiman nata, tana ganinsa ta kama hannunsa tana furta "let's go eat food"
*KULU*
Ni kuwa tun lokacin dana ajiye Abincin nake tsaye kasancewar duk in ka ajiye Abinci ba zaka bar wajen ba har sai anzo an kammala ci sannan, sosai na gaji da tsayuwar,Ƙamshin turaren da naji na dumfaro inda nake ya sakani ɗago da idanuwana sai dai karaf suka sauka akan Mutumen da naga photonsa wanda nake da tabbacin shine ABIODUN sosai na shagala da kallonsa sai nake ga duk kyawunsa da na gani a photo ashe ba kyau bane ganinsa a zahiri yafi, zungurar man ƙafa da wata baiwa tayi ya saka hankalina dawowa ya zuwa gangar jikina,sai naji kunya na kuma gode Allah da yada Uuwargidan sarkin can bata gani ba wacce nake da tabbacin ita ce Maman ABIODUN sbd ga kamanni nan sun bayyana a tsakaninsu
Zama yai yana ɗan ƙara haɗe rai, kallommu da ɗai ɗai Maman ABIODUN ɗin tayi tana sallamar bayin da muke tare ya rage ni kaɗai ce hakan ya saka ni tsurewa waje guda ina zare idanun tsoro da wani tsinannan kallo ta bini tana daka man tsa tare faɗi Ubanki ne zai yi serving nasa kika zura mana idanu" ta faɗa a harshen turanci
jikina na ɓari na tunkaro inda warmers ɗin suke na fara serving nasa dukkan wani abu da aka shirya masa sai da na zuba masa, ina ja baya na tsaya tare da duƙar da kaina ina shanye hawayen dake son zubo man,ita kuwa ta fice tana faɗin yaci Abincin sosai da kafin ta dawo
ba tare da ABIODUN ya kalleni ba ya fara cin Abincinsa musamman ma Yamnita Nd Vegetable stew ɗin yana gamawa ya miƙe da nufin barin wajen sai dai cikin rashin sa'ar kauce masa muka haɗa jiki dashi wanda ya saka shi ɗago da Manyan idanuwansa ya zuba su a kanta da nufin yi mata masifa, da cin mutunci, tuni jikina ta fara kyarma na rintse idanuwa bakina na karkarwa idanuwana na ambaliyar ruwan hawaye wanda na tabbatar Mari ne zai sauka a kuncina, kallonta yake a karon farko kenan da har ya tsaya yana ƙarewa mace kallo yana kallon ɗan mitsilin bakinta dake son furta wani abun, ganin yanda jikinta ke karkarwa ya saka shi murmusawa yana ɗan ƙara zuba mata narkakkun idanuwansa "Open your eyes" na tsinkayi muryarsa wan da ni nai tunanin saukar lafiyayyen mari a fuskana
A hankali nake ware manyan idanuwan nawa wa ƴanda suke cike tab da ruwan hawaye, sosai gabansa ya faɗi yan zubawa idanuwan nata kallo yana karantar wani abun cikinsu, bai san lokacin da ya janye ba yana ɗan kuma haɗe ransa tare da furta "you can go" cikin tsoro na furta "ok sir" ina haɗa hanya na wuce
bayanta yabi da kallo tare da murmusawa yana faɗi "A cowardly girl"................
RIAMCOOL ce.........
[10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU*
*BY RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSO.....*
*Bismillahirrahamanirrahim*
*P.19&20*
Yana gama faɗin haka ya fice ya zuwa sashen BOLUWATIFE,wanda tun lkcn da ya fito ya zuwa Babbar Farfajiyar Masarautar ya zuba ma waje guda idanuwa yana ɗan lumshe Manyan idanuwansa, jin kirarin da fadawa suke yayinda suke a zube ƙasa, ɗan haɗe ransa yayi yana ɗaga musu hannu Alamar su bari kai tsaye sashen BOLUWATIFE ya nufa
*Boluwatife*
Tun daren da taji Oba Adewale Femi ya faɗi ABIODUN zai dawo ta shirya Babban tuggun da take gani haƙarta za ta cimma ruwa, tun a daren ranar da zai dawo ta nufi gun Boka Olesegun
Kamar yanda ta saba a koda yaushe yauma ɗin tsaye take tana faman karanta wasu ɗalasimai waɗanda ba ganesu kake ba dan na yau sunfi na koda yaushe muni, baiwarta Febo dake tsaye sosai ta tsure waje guda tana jin tsoro duk da ba yau ne ganinta na farko ba, kafin suyi wani ƙwaƙƙwararan motsi duka suka fara jin brain nasu na juyawa tsikar jikinsu na tashi,kunnuwansu na musu wani kalar sauti Dummmmmmmmm, sauyin iskan da suka ji ne ya saka su buɗe idanuwansu, akan Boka Olesegun dake murmushi mai bayyanar da zaƙwaƙwurin muninsa da razani
"Boluwatife me ke tafe dake ne?" ya faɗa da razananniyar muryarsa, bakinta ta buɗe ta fara magana cikin ƙunar rai "haba Boka Olesegun na gaji fa da ganin ABIODUN a masarautar to ga dama ta zo min tabbas jinin JOHAAN ya bayyana a Masauratar nan tunda Oba Adewale Femi (Sarki Adewale Femi) ya furta da bakinsa, ya bayyana cewar yana son ABIODUN ya bar masarautar nan a farkon zancensa, amma daga bisani kuma ya fara kokwanton hakan, ka taimakeni ya zartar da hukunci daya yanke a farko nice nake son cikin dake jikina ya zamto yariman Masarautar Handaash" ta idasa da zubar wasu hawayen takaici da tsanar ABIODUN dake ranta
Dariya ya fara yi wacce kai kace ba zai taɓa dakatawa da ita ba, daga bisani kuma ya haɗe rai tamkar baƙin hadarin da zai zubar da ruwan halakarwa, "Boluwatife na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, mafitarki biyu ce ko kibi Addini ABIODUN sbd Dodonsa bautarsa yafi naki ƙarfi idan kina haka ba zaki galaba akansa ba, na biyu ko dai kiyi sadaukarwa da cikin dake jikinki shine za ki iya nasara akansa"
da rinannun idanuwanta take kallon Bokan nata tana furta "Babu wata mafitar ban da wannan domin ɗaya daga cikinsu banji ina iya bi ba"
"Boluwatife ba kya da zaɓi ban da wannan, amma zan fara baki wani maganin da za kiyi ammfani dashi ki ciyar dashi zai fara galaba akansa"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki tana mai mashi godiya bayan ya bata maganin da yanda za tayi amfani dashi
Washe gari jin da kanta tai masa girki da magungunan da Boka Olesegun ya bata, bayan ta gama shirya komai ta Hakimce a kujeran Falon tana jiran shigowarsa
Ƙamshin turarensa ya sanar mata da shigowar ABIODUN cikin wani kalar farinciki da ya fito tsantsa a fuskarta ta miƙe tana faɗi"Welcome my beloved son"
Murmushin ganinta yayi yana mai ware hannayensa ya rungume ta tare da faɗin "thanks" ya faɗa tamkar wanda bai son magana
A fuska kawai wannan murmushin da annurin fuskarta ke fita amma a ƙarƙashin zuciyarta ƙuna take, kukan zuci ne fal a cikinta ƙiyayyarsa tai mata ninkaya ta dabaibaye dukkan wani loko nata, rugumarsa da tai ji take ƙara acce garwashin wuta ne ta taɓa da da hali tabbas babu abinda zai hanata ɗaukar rayuwar Abiodun ta yadda gawarsa ma ba zatai kyan gani ba
Cire jikinta daga nashi tai tana ƙara ƙaƙalo masa murmushin da dauriyar yinsa kawai take, tsabar iya makircinta, ya saka ba zaka taɓa cewa ba a zuciyarta yake ba
hannayensa ta kama ta zaunar dashi tana ta masa maraba, a zuciyar ABIODUN kuwa sosai yake jinjina girman ƙaunar da Boluwatife ke masa yana mamakin yanda Awujonsa ke son rabashi da ita
Maganar ta ce ta
katsesa tana furta masa da yaci abinci girgiza mata kai yayi alamar ba zai ci ba cikin dmw tace " My son, what do you mean you don't eat food I prepared this food with my own hands" ta faɗa da dmw
Murmushi yayi yana faɗin "I ate food in Awujo, that's why my stomach was full and I couldn't put any food in it"
Ba don taso ba ta kyalesa amma a zuciyarta ta ayyana dolensa yaci Abincinan "tohm shikenan amma ka tabbatar girkin dare a wurina za kaci tun da kaci na wajen Awujenka"
ɗaga mata kai yayi alamar to, yana tattaro dukkan nutsuwarsa ya mayar da ita a gunta tare da faɗin "Mama Bolu,wani abun ne ke faruwa da masarautar nan ne da har Daddy ya gaza faɗa Mani, sannan naga tsantsar tashin hankali a wajensa wan da ban samu damar tattaunawa dashi ba, amma nasan dukkan wata damuwa na Daddy ke kin sani ki faɗa mani babban dalilinsa na cewar na baro London nasan ba lafiya ba" ya faɗa cikin harshen turanci
murmushi tayi tana mayar da hankalinta gunshi tare da shimfiɗa damuwa a fuskarta tana faɗin "Son tabbas dan dmw da akwai ta a masarautar nan abin da Mahaifinka ke gudu a tsayin shekaru yau gashi yana shirin faruwa a masarautar nan sbd jinin JOHAAN na a cikin masarautar nan"
Sosai maganar ta dake shi amma yai ta maza ba tare da ya iya mgn ba, miƙewa yayi ya fita zuciyarsa sam babu daɗi
Kai tsaye sashensa ya nufa yana kwanciya yi tare da lumshe idanuwansa Oba Adewale Femi kawai yake jira ya dawo daga fada domin ya ƙara jin ba'asin zancen
Da ƙyar ya samu baccin gajiya na ɗaukar sa, wan da ya daɗe yana before ya farka wanka ya sake yi yana son nufar Mahaifinsa wanda ya tabbatar a yanzu ya dawo daga fada
Zaune yake yana sauke numfashi jin mahaifinsa ya gama kora masa jawabi tamkar yanda Boluwatife ta faɗa masa, "wane shiri yanzu ake ciki" ABIODUN ya faɗa
shiru Oba Adewale Femi yai yana
kallon itama Mahaifiyar ABIODUN ɗin wacce take sauraronsu, "ABIODUN a iyakar bincikena tun kafin abun ya faru an sanar damu ba wata mafita mafita ɗaya ce mai tsauri ita ce barinka a Masarautar HANDAASH"
Daga shi har Maman nashi kallon Oba Adewale Femi suke cikin tsantsar mamaki da zallar razani bakinsa na rawa ABIODUN ke furta
Dad, you know what you're talking about" ABIODUN ya faɗa cikin kodai mahaifin nasa ba a hayyacinsa yake ba sai dai maganar da yaji ya furta ne ya saka shi gazgata lallai yana hayyacinsa "ABIODUN, I am aware of what I am saying that you should leave this kingdom" ya faɗa da hawayen dake biyo kuncinsa wanda tun da suke basu taɓa ganin koda ɗigon hawaye a idanuwansa ba sai yau da ya furta ABIODUN yabar masarautar sa da bakinsa akan wani dalilin da ba lallai ya faru ba hasashe ne kawai cikin masifa da tujara Maman ABIODUN ta fara faɗin "ABIODUN has nowhere to go, he will never leave this kingdom, on what is an illusion, there is no war about it."
hannu ya Adewale Femi ya ɗaga mata yana mai mata kallon takaici da rashin hankali ƙofa ya nuna mata ta fita, wan da cikin fushi ta fita tana mai zazzaga masifar ɗanta ba zai bar masaurar nan ba
ABIODUN kuwa ya gaza furta komai wanda numfarfashi kawai yake fitarwa ,
*KINGDOM OF JOHAAN*
Wani kalar zafi da huci ke fitowa daga jikinta sosai take mayar da numfarfashin azabar da take ji a duk lokacin da zata haihu sai dai na wannan karin daban yake , Azababben zafi ne ke ratsata tun daga kanta har izuwa tafin ƙafarta dalilin haka ya haifar mata da karkarwa tamkar wacce taji kiɗan gangi wanda haka ne ya haifar mata da gumin dake tsatstsafowa daga ko wane loko na jikinta
A hankali ta ƙara lumshe Manyan dara daran idanuwanta tana ambata Jesus a hankali wan da a fatar bakinta ne kaɗai za ka gane, Gimbiya Josmie dake tsaye kanta tuni idanuwanta suka cicciko da ruwan hawaye tana faɗin "Ki daure za ki iya da amincewar Jesus" ta faɗa da harshen turanci
cikin dakiya da jajircewa Matar dake naƙudar ta buɗe idanuwanta tana kallon Josmie tare da buɗe busasshen leɓenta tana girgiza kai hawaye na biyo kuncinta ...............
*RIAMCOOL ce*
Writer of
RUSHEWAR RAYUWA
BAYAN WUYA
ANYA UBA NE
AND NOW
*KULU*
[10/23, 9:03 PM] CUTIE~RIAM: *KULU*
*BY RIAMCOOL*
*Mikiya writer's Asso.....*
*Bismillahirrahamanirrahim*
P.21&22
"Josmie ba zan iya ba na tabbatar a wannan karon ma Abinda zan haifa ba lallai ya tsira ba, shima halakar man dashi za ayi, na roƙi Yesu Jesus da in har za a halakar man da wannan yaron na cikina to