da ta irga taga banyi ɓatan ko biyar ba sannan ta barni na wuce ɗaki, ina shiga na taras da ba kowa ajiyar zuciya na saki ina fito da Awaran na buɗe na fara ci ina lumshe idanu saboda daɗin da tayi man, ina cikin ci ne na ji an bankaɗo labulen ɗakin "iyeeee wato ke ba za kici abinda aka girka ba sai dai kici Awara sannu ƴar ƙwai nasan Baba ya siya miki to wllhy ba za kici ba sai kin kawo ta nan tun da ba Ubanki bane tsintacciya" Zainabu ta faɗa tana fizgar ledan Awaran dake gabana
Shiru nayi ban ce mata ƙala ba haka zalika ban ɗago idanuwana na kalleta ba,har ta ƙarashe man zagin cin mutunci sannan ta fita,jingina nayi da bangon ɗakin ina mayar da numfashi hawaye na zarya a kuncina, a daren ranar ma da ƙyar nai bacci zuciyata fal da tunanin abin da zan kuma gani sai dai har nai baccin ban kuma ganin komai ba.
A haka rayuwata taci gaba da tafiya babu wani sauyi ƙalubalen gidammu na ƙara gaba yayin da wajen Baba kaɗai nake samu na raɓa naji sanyi, sannan yake takawa su Mama Khubrah birki ga wani abin da suke Mani
A hankali nake jin hayaniya na tashi a tsakar gidan da kuma Kukan su Mama Khubrah dake tashi cikin gidan, da sauri ta fito "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un mota ta take Malam ya mutu ya barni ashe Ajali ne ke kiransa harya fita na shiga ukku ni Khubrah" na tsinkayi Muryan Mama Khubrah wacce ban fahimta ba sai da naji ana faɗin "ku shigo da gawar sa" wani Mutum ya faɗa Ban ida gazgatawa ba sai da naga an shigo da gawar Baba wan da jikinsa ke sharkaf da jini, ban san sadda na fasa wata uwar ƙara da kururuwa ba ina faɗuwa nan ƙasa sumammiya
ban ida sani inda kaina yake ba sai da na tashi naga ana min firfita da kuma koke koken dake tashi a gidan , da gudu na miƙe ina nufar inda naga an saka gawar a mankara "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un Baba bai Mutu ba wllhy ku dawo man dashi, shi kaɗai gareni duk duniya mai sona idan ya tafi wurin waye zan raɓa naji sanyi,fitar da yai a ɗazun ashe fita ce ta har abada babu rabon ya dawo ,yanzu Baba ka tafi tafiya ta har abada wacce babu dawowa, ban san ya zanyi da rayuwata ba ni Kulu ku taimakeni" na faɗa tamkar wata zautacciya yayin da na fashe da wani matsanancin kuka,
Dukammu gaza Magana mu kayi sai kuka tsakanin ni da su Mama Khubrah yayin da su sun sami dangin su masu rarrashinsu ni kuwa babu wan da yabi ta kaina balle har naji sauƙin abinda nake ji a zuciyata,rirriƙe gawar mu kayi yayin da za a ɗaukesa wan da da ƙyar aka ɓanɓaremu nida Zainabu,ina ji ina gani aka fita da gawar Baba Bayan kwanaki sha biyar Mutuwar Baba ba ƙaramin tashin hankali ta jefani ba wan da azabar gidan namu ta ƙara ninkuwa
*Masarautar HANDAASH*
Da rinannun idanuwanta Boluwatife ke kallon Boka Olusegun tana faɗin "Olusegun ba zan taɓa bin Addinin Abiodun ba, dan na yarda da kaine shi ne dalilin da ya saka na baka yarda na a kanka, Ina son ka samo wata mafitar ban da wannan
dariya Olusegun ya fashe da ita yana faɗin "Boluwatife !!!! Mafita ɗaya ce wanda Dodon Bauta ya bani amma zan ƙara roƙon Alfarma a wajensa na tabbatar ba zai kunyatar dani ba, amma kafin nan ina da buƙatar da ki bayar da jinjirin cikin jikinki wan da Abin bauta na tabbatar ba zai ƙasa a guiwa ba wajen cikar muradinki
Duk da tashin hankalin da take ciki bai hanta sake shiga cikin wani ba wan da ya sakata wata zabura tana kallon Boka Olusegun.............
Ayi manage banda charge 🥺nex page zan yi mai yawa in Sha Allah
Love yhu All my Habibties😘
[7/23, 12:27 PM] RIAMCOOL: *KULU*
*BY: RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION*
*Bismillahirrahamanirahim*
*P.7&8*
*Jiya nayi mistake ɗin Number page,page 5&6 zan saka na saka 4&5*
Sosai Boluwatife ke kallon Boka Olusegun yayin da mamakinta ya gaza ɓoyuwa da yarensu na Yarbawa take faɗin "Olusegun kana nufin cikin da na daɗe ina so sai da ƙyar abin bauta ya ƙaddara mani samuwarsa,gsky ba zan iya bayar da cikin jikina ba zan san nayi" ta faɗa zuciyarta da alamu karyewa
dariya ya saki yana faɗin "kije kiyi tunani Boluwatife"
Ba tare da ta sake kallon Olusegun ba ta fice a ɗakin, ta ɗan yi tafiya mai nisa before ta isa inda bararonta suke, sai yanzu na ƙare mata kallo dakekiyar macece Choculate color mai manyan idanuwa fuskarta a haɗe,yayin da jikinta ke sanye da dakakken leshi da murjani a wuyanta, tamkar hadarin gabas haka fuskarta ke ɗaure tamau yayin da take tafiyar Barorinta na take mata baya, a haka harta isa inda Motocin Abiodun suke yayinda ake ta miƙo mata gaisuwa da kirari amma sam hankalinta ba anan yake ba ya karkata ne ya zuwa ta ga Abiodun ɗin yadda ya koma, A hankali takai dubanta gun Mahaifiyar Abiodun wacce itama fuskarta ke ɗauke da maɗaukakin farinciki yayin da shi kanshi Sarkin fuskarsa ke fitar da Annuri wan da jikinsa ke sanye da wani dakakken Farin leshi ƴar ciki da babbar riga sai wuyansa dake sanye da murjanan shima yayin da hannayensa ke riƙe da sandar azurfa,
Ajiyar zuciya ta saki tana kai dubanta ga Motocin yayin da ta zuba idanuwa taga fitowar Abiodun,a dai_dai lokacin ne aka buɗe murfin Motar bai fito ba illa ƙafarsa ɗaya daya fara fitowa da ita ya ɗan ɗauki kusan Five minutes before ya ida fito da ɗayar ƙafar ihun da yaji Mutane nayi na farincikin ganinsa shi ya bashi damar ida fitowa Yayin da sai da Boluwatife ta dafe ƙirji ganin cikakken Namiji Abiodun Mahaifansa da ƴan uwansa kuwa bakunansu sun gaza rufuwa sbd farincin ganinsa cikin ƙoshin lafiya,
Yana isowa inda Mahaifin nasa yake ya faɗi ƙasa yana kai masa gaisuwa,ɗagosa Mahaifin nasa yayi yana rungumesa, tare da faɗin
"Kaabo ọmọ-alade mi, Abinabawa tẹsiwaju lati daabobo ori rẹ" nan take busa da kaɗe_kaɗe suka fara tashi,gun Mahaifiyarsa yake yana rungumeta wacce itama ta rungumesa tana faɗin"Kaabo, Alade, O ṣeun, Ọlọrun, ti o dabobo ọ lati awọn ibi ti ijọba yii."(Barka da dawowa Yarima Nagode Abin bauta da har ya cigaba da kare ka daga sharrin Matsafan Masarautar nan) ta faɗa tana jefawa Boluwatife kallo
dukkansu ɗunguma sukai ya zuwa Babban Falon gidan,wanka Abiodun ya shiga yayi, fitowa yai daga Toilet ɗin jikinsa ɗaure da Towel ƙirar nan ta jikinsa tamkar ta doki koda ya fito hadimansa Mata na tsaye na jiran fitowarsa, kansa suka fara taje masa suka ɗaure masa baƙin dogon gashin kansa, sannan suka fara shafa masa haɗaɗdun lotion masu daɗin ƙamshi da tsada, sosai suka shirya sa cikin kayan su na Yoruba masu tsada da jinin sarauta,haka zalika ɓoyayyen kyawun Abiodun ya fito
koda ya fito dukkansu suka ɗunguma ya zuwa Baban wajen da Da aka ɗiba a cikin masarautar yayin da yasha Kaya na Alatu da more rayuwa a ciki,sosai aka haɗa babbar liyafa yayin da wurin ke ɗauke da Abinci kala da kala
*KULU*
Zaune nake a tsakar gidammu yayin da hankalina ya karkata ya zuwa aikin da nake wato tsince shinkafa, sallamar da naji ita ce ta sakani ɗagowa ina kallon Talatuwa wacce ta dubeni tana faɗin " Khubrah na ciki kuwa"
gaisar da ita nayi ina furta "eh tana ciki" wucewa tayi tana shiga cikin ɗakin ni kuwa na mayar da hankalina akan aikin da nake
Tunda Talatuwa ta shiga suka gaisa da Khubrah ta dubeta tana faɗin "Khubrah nazo miki da wata magana ne dama idan har za ki amince"
kallonta Mama Khubrah tayi tana faɗin "faɗi ko wace magana ce in Sha Allah zan amince"
gyara zamanta Talatuwa tayi tana faɗin "nake ga Khubrah tunda ba kece kika haifi Kulu ba sana hasali ma ba ku san asalinta ba mi zai hana ki Kaita masarautar Kudu wacce ake cinikayyar Bayi wanda nima zan kai BINTU a can, wallahi KHUBRAH maƙuddan kuɗaɗe ake samu ni kaina an bani maƙuddan kuɗaɗen BINTU kin gansu anan" ta faɗa tana zaro maƙuddan kuɗaɗen dake cikin kwagirinta
zaro ido Khubrah tayi tana kallon kuɗin tare da faɗin "Haba Talatuwa ai babu abinda zai hanani kai KULU kuwa can ban san da wane baki zan gode miki ba,na kawo man wannan maganar daman gashi kuwa ina cikin halin na rashi,yanzu wa zan bawa KULU ya bani kuɗaɗen"
na tsinkayi maganarta wan da dai_dai nazo shiga a ɗakin, baya naja ina furta Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un, mi Mama Khubrah ke nufi, shin siyar dani za tayi dan Baba bashi da rai ko dan na kasance ƴar tsintuwa marar galibi??? Nai wa kaina waɗannan tambayoyin hawaye na zuba a idanuwana da son ƙara jin zancen nasu na kai kunnena aɗakin ina sauraronsu yayin da Talatuwa ke faɗin "kin ga ki bar komai a hannuna goben nan zan yiwa Shu'aibu magana komai za ayi yi, jibi ki shiryata a Kaita inda za ki karɓo kuɗin"
Sosai Mamah Khubrah ke godiya,jin motsin tahowarsu ya sakani barin bakin ƙofar ɗakin
Bayan ban ɗaki na gewaya ina wanke fuskana don kar a gano wani abun
duk yanda naso ɓoye damuwana ya gagara dole sai da fuskana ya nuna har sai da Mamah Khubrah ta gane man, tsoron ta kar ace na san abinda suka ƙulla ita da Khubrah ya saka ta tambayeni amma sai na ce mata kaina ne ke ciwo,
Kwance nake na ƙurawa kwanon ɗakin idanu inata juye juye yayin da damuwa ce fal cike a raina
Wacece KULU
kulu dai tun tana Ƴar jinjira Malam Hadi ya tsinceta a gona wan da ya ɗauke ta ya kawo ta fadar mai gari tare da neman Alfarma ya riƙe ta duk da ya san mawuyacin abu ne Matarsa Khubrah ta riƙe ta saboda rashin Mutuncinta
Da ƙyar da rarrashi ta amsheta wan da ba wata kulawa da take bata, sai dai rainon Ubangiji da taimakon Aljana Diyana da take tare da ita wacce ita ke ciyar da ita tun tana jinjira, tun tana ƙarama ta buɗi ido ta ganta da Diyana,
Lokacin data fara girma Malam ya sakata makaranta Boko da islamiyya wanda take da ƙoƙari sosai sai da abinda ke damunta bai wuci gorin da take fuskanta gun yaran Khubrah da ita kanta Mama Khubrah na cewar ita ƴar tsintuwa ce, ga ƙarin damuwar ta bai wuci yadda Mutane ke nuna mata kyara da hantara ba,ko cikin yara bata da ikon yin wasa saboda hantara,tun tana kuka harta daina shiga cikin yaran hakan ya sakata tasowa cikin kaɗaici sai dai Diyana ce mai ɗebe mata kewa wacce takewa kallon Mahaifiya
Tun tana shekara goma asalin kyawunta ya fara fitowa wacce ta kasance ita ba fara ba sannan ba baƙa ba wato irin fatar nan ce mai tsada Choculate color sai manyan idanuwanta masu jefa me kallonsu a wani yanayi,bakinta ɗan madai_daici, sai dogon gashin kanta da kuma wanda ya kwanta mata luf luf a gaban goshi, sannan ya fitar mata da kwantaccen sajenta, tun tana karamar ta kasance sam bata da hayaniya, ka ƙoƙari don tana aji biyar ta iya karatun Hausa da turanci wan da yake da nasaba da koyawar da Diyana ke mata sannan hada ƙarin wasu yaririka tana jinsu har larabci tana ji,hakan ya saka Baba ke matuƙar ji da ita sosai yake nuna mata so fiye da yaransa wannan ya sa su Zainabu da Mahaifiyarsu ke nuna mata ƙiyayya
A.lokacin da take shekara sha biyar lokacin ne kuma ta fara gane ganen abubuwa masu ban mamaki wan da take shiga cikin damuwa, sannan a duk lokacin da wani ya ɓata mata rai sai yaji a jikinsa ko kuma yayi ta rayuwarsa lura da hakan dasu Mama Khubrah su kayi suke mata kirari da Mayya har cikin gari shi yasa ko kaɗan bata da wani namiji mai cewa yana sonta duk da kyawunta kuwa,hakan be dameta ba duk da babu ranar da zata zo ta koma ga Ubangiji ba tare da ta zubar da hawaye ba, har ya zuwa yanzu..
More comments more Typing
*Riamcool ce*
[7/28, 7:05 PM] RIAMCOOL: *KULU*
*By: RIAMCOOL*
*Mikiya writter's Association*
*Bismillahirrahamanirahim*
*P.9&10*
Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana
Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man
Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi
Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi
"KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna
Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki
kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU
[10/23, 8:52 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n
*KULU*
*By: RIAMCOOL*
*Mikiya writter's Association*
*Bismillahirrahamanirahim*
*P.9&10*
Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana
Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man
Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi
Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi
"KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna
Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki
kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU, sosai muka ci uwar tafiya kafin mu fita daga cikin garimmu a lokacin mun jigata sosai da tafiya ga ƙishi ga yunwa, a haka har muka isa inda aka jejjera amalanke, kayammu muka zuba a ɗaya daga ciki sannan muka shiga, kallona BINTU tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska tana ɗora hannayenta bisa kai ta kurma ihu tana faɗin "na higesu ni BINTU mutuwa ba ki man rana ba kin rabani da uwata da ubana yau gahi an hiyar dani"
ni kaina hawayen naji suna neman zubar min amma sai dai dole nai ƙoƙarin shanyesu ina taune leɓena na ƙasa, tare da furta sunayen Allah
Muna ji muna gani haka muka dinga tafiya har Allah ya iso damu cikin birni a lokacin ne Shu'aibu ya siya mana Abinci wanda da ƙyar muke tura shi ,daga nan mota muka hau wacce za ta kaimu har garin OYO tafiya bata wasa muka yi ba, dan Sallah ce kaɗai ke tsayar damu, sosai na jigata naji cikina ya juye na fara zazzaga Amai tamkar zan amayar da hanjin cikina, da tausayi Bintu ta dinga yi man sannu ɗaga kaina kawai na iya yi, wani dogon tsaki Shu'aibu ya ja yana furta "dan uwar ki lashe aman da kikayi kin wani ɓatawa mutane mota, ki lashe ko na yi miki lilis a motar nan"
hawaye tuni suka ƙara jiƙa man fuska ina furta "kayi haƙuri idan an fita zan gyara motan amma bazan iya lashewa ba"
ƙwafa kawai yaja yana juyawa, ba da jimawa ba muka sauka in da Bintu ce ta gyara inda nayi Wa amai, lkcn dare har yayi, hakan yasa Shu'aibu cewar mu biyo shi,zuciyata cike da ɗar ɗar muka bisa tare da hawan adai daita ya kaimu wani guri, ɗan ƙaramin gida ne Shu'aibu ya kaimu wan da cikinsa ɗaki ɗaya ne kacal, gashi ana tsuga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, shiga mu kayi ɗakin muna muzurai dan tsoro, wani kalar kallo Shu'aibu ya bimu dashi yana murmushin gefen baki, a hankali ya ƙara so gabanmu yana saka hannunsa yana shashafa mu tare da lumshe idanuwa, "Innalillahi miye haka ka daina dan Allah babu kyau" na faɗa ina girgiza masa kai hawaye na zuba
"Zan ci uwar ki kika sake magana, wllhy dole ne na taste ɗinku kafin na kaiku gidan arnaye waɗanda basa dungura goshinsu a gabas na tabbatar duk sai sun dinga kashe dare daku, to nima yau zan kashe arna daku" ya faɗa yana washe baki, ganin yana taɓa dukiyar Fulani su, kuka Kulu da Bintu suka saka yayin da sukai ƙoƙarin ƙwatar kansu amma sam sun gaza, wani kalar ihu suka ji Shu'aibu ya fasa yana ja da baya, nan take idanuwansa suka fara kakkafewa ya faɗi, wani kalar ajiyar zuciya na saki ina murmushi tare da furta "Diyana"
banji an amsa ba hakan ya sakani sulalewa ƙasa ina kwanciya bacci na ɗibata, sai da gari ya ɗan fara haske sannan na buɗe idanuwana bakina ɗauke addu'a Bintu na tayar muka fita sai dai babu ruwa hakan ya saka muka ɗauki ruwan roba mu kayi arwallah, har muka ƙarashe sallah Shu'aibu bai tashi ba, nan take gabana ya faɗi na fara tunanin karfa ace Diyana tayi halin nata
ina cikin tunani haka muka ji yana tari tare da miƙewa, yana hamma, ruwan ya ɗauka yana fita ya wanke fuska da baki, kallomu yai yandaa faɗin "idan za mu fita ya zama wajibinku ku cire hijabbanku, sannan inda zan kaiku ku kiyaye wani ya gano cewar ku musulmai ne, idan aka gano tabbas kun kaɗe,"
shiru mu kayi yana faɗin mu tashi mu fita, Hijjabin muka cire wasu hawaye Masu zafi na biyo kuncina "ya Allah" na furta a hankali tare da tunanin wane shafin kundin ƙaddarar zan buɗe a yanzu, baya ga cikakken littafin ƙaddarar dana ƙarasar a baya,
tamkar wacce aka zarewa lakka haka na bi bayansa muna fita wata motar muka sake hawa wacce kwana mu ɗaya da yini sannan muka sauka, muna sauka, muka hau a dai daita ya kaimu wani waje, inda ga mutane nan da dama ko wane a dudduƙe wan da mafi akasari su duk ƴam mata ne, layi Shu'aibu yabi tare da umartar mu durƙusa mu duƙar da kawunnanmu, layi ne yazo kan Shu'aibu nan take aka gama cinikummu ya tafi, dukkamu durƙushe muke ga wata uwar rana da ake yi wanda tuni muka fara gumi zufa na tsiyayya mun sha baƙar wahala kafin azo da wata ƙatuwar mota ta Alfarma wacce tun da nake ban taɓa ganin kalarta ba, cikin ta aka zuzzuba mu muka fara ɗaukar hanya, manmanyan gidaje muka dinga ketawa wan da a iya rayuwata ban taɓa tunani da akwai kalar su a duniya, nan na shafa'a wajen kallo,
wani danƙareran get muka ga an shiga ciki wan da nan take zufa ta fara yanko man gabana ya tsananta faɗuwa ,.....................
*RIAMCOOL ce*
Writer of
*RUSHEWAR RAYUWA*
*BAYAN WUYA*
*ANYA UBA NE*
And now
*KULU*
[10/23, 9:00 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n
*KULU*
*By: RIAMCOOL*
*Mikiya writter's Association*
*Bismillahirrahamanirahim*
*P.9&10*
Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin