bude press taga Badiyya ta kwashe kayanta, Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ke yaushe kika lura bata nan?" Mayraah da gabanta ya fadi don bata son Ammi tasan ba a dakin ta kwana ba tace "Kawai ina tashi naga bata nan, ni na zata tana parlor ne at first" Ammi ta fice daga dakin ta koma nata dakin, wayarta ta dauko tayi dialing number Badiyyah taji a kashe, ta rasa yanda zata yi kawai ta kira Hajja, Hajja na dagawa bayan sun gaisa Ammi tace "Hajja Badiyyah ta je gidanki ne?" Hajja tace "Wacece kuma Badiyyah?" Ammi ta kasa cewa komai, nan taji dama bata kira Hajja ba, amma to duk ta rude, Hajja tace "Ban gane Badiyyar da kike nufi ba, bayan warce ke gidanki dama akwai wata Badiyya ne?" Ammi tace "To zan kiraki Hajja" Bata tsaya sauraron Hajja ba ta katse wayar ta ajiye kan gado ta fita da sauri zuwa dakin Maheer, ganin baya dakin ta tafi dakin Usman, Maheer da har ya ci gaba da baccinsa ya bude ido saboda irin kiran sunansa da Ammi take, ya mike zaune yana kallonta, hankali tashe Ammi tace "Maheer Badiyyah bata gidan nan fa" Maheer yace "Toh Ammi jaririya ce ita Badiyyar nan?" Rai bace Ammi tace "Wani irin magana kake gaya min haka, an tashi babu yarinya a gida kace min jaririya ce" Maheer yace "To nima haka na samu labari, kilan gidan kakarta ta tafi ba an mata fada jiya kan ta dawo da daddare ba" Ammi tace "To na kira Hajja kuma daga yanda take amsa min Badiyyah bata je gidanta ba" Maheer yace "Bichi ta tafi kenan" Da damuwa Ammi tace "Wayarta fa a kashe Maheer" Maheer yace "Don Allah kar ki wani damu kanki Ammi, Badiyya fa ba yarinya bace, inda baza a mata fada ba zata yi abinda ta ga dama ta tafi" Ammi ta kasa cewa komai, can ta juya ta fita daga dakin, Maheer ya koma ya kwanta...
Wata dattijuwa ce tsaye kofar gidanta da wani bugujejen riga dake ta zamewa daga shoulder dinta, ga wani uban dankwali ta kima a kai hannunta rike da tsintsiya, fada take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cikin daga murya take cewa "Sannan a karshe sae dae ince Allah ya isa tsakanina da ku, Allah ya saka min wannan cutata da sa ni magana da kuke ba dangin iya ba na baba, kuma ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba bishiyar nan ta girmi iyayen kakanninku, wllhi ban yafe ba har karshen duniya...." Wata mata dake wucewa da kayanta dukundukun tace "Baaba Ladi ina kwana, wani barnar aka maki halan" Mama Ladi ta juya tace "Sai ma kin tambaya?? yaran da kowa yasan Allah ya riga ya tsine masu albarka tun a nan duniya, yanzu don Allah ke a ina kika taɓa ganin an sha rake a karkashin bishiya Delu? Ba fa iyayensu masu zaman kashe wando a kauyen nan suka dasa bishiyar ba, nima gadonsa nayi gun mijina shi ma kuma gun iyayensa da suka gada wajen nasu iyayen ya gada, kinga kuwa ae ba banza bishiyar take ba, tun fa asuba nake aikin share wajen nan sae yanzu na gama, ai kinga an cuceni an ci amanata, sai cikin dare ko wani mahaluki ya tafi ya kwanta ya bai ma hakarkarinsa hakkinsu sai shaidanun yaran su hada daba karkashin bishiyata suna shan rake suna cin gyada, kuma in sha Allahu ƙara zan sa a zagaye min bishiyar da shi, sai in ga ta inda 'ya yan banza za su zauna karkashin bishiyar" Matar dake tsaye tana sosa kanta tana sauraron Mama Ladi tace "Ai ko kawai yanda kika ce ya kamata ayi, abi duk a zagaye wajen kawai da kara, sai dai fa wannan zai ci damin ƙara ba kadan ba tunda bishiyar tsamiyar kin ga ai tana da girma, kina yin haka kuwa kin yi maganinsu, kin ma huta da masu bi maki kofar gida kullum" Machine ne ya tsaya kofar gidan aka sauko rike da akwati, Mama Ladi tayi shiru tayi mitsi mitsi da ido tana kallon warce ta sauko daga saman machine din, can dai tace "Wacece wannan?" Warce ta sakko bata ko kalleta ba ta ja akwatin zuwa cikin er tsakar gidan, Matar dake tsaye tare da Mama Ladi ta washe rubabbun hakoranta tace "Baƙi aka yi daga birni kenan Baaba Ladi" Mama Ladi ta kalleta tace "Ke dai tseguminki yawa ne da shi Delu, nan kika gama bani shawaran banza wai in zagaye bishiya da ƙara kamar don ni kadai aka halitto bishiyar, to ai mugun halina bai kai haka ba da zan ki bari a zauna a sha iska in samu lada a karkashin bishiyata, kawai mata kiyi ta yawo kina doyi kina shiga hakkin jama'a, ke baki jin warin jikinki ne baiwar Allah, ke wari mijinki wari, aa to Allah ya mana tsari... Tafi ki ban waje munafuka" da sauri Delu ta yi gaba, Mama Ladi ta shige gidanta, haɓa ta rike tace "Wa ya maki kwatancen nan Badiyya?" Badiyya da har ta tube kaya ta watsar kasa tace "Nan din ne bazan gane ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Ai ko gaki nan kin kawo kanki tubarkallah, naga baki taɓa zuwa ke kadai bane sai da Hajja kuma kuna zuwa baki wuce awa daya kike wucewa ki bar Hajja tunda ita har sati tana iya yi a kauyen nan, ke sae kice baxa ki iya ba" Badiyya tace "Yanzu dai wanka nake so inyi, wannan garin naku zafi kamar oven...." Mama Ladi tace "To Hegen almajirin me debo min ruwan a rafi bai zo ba, amma akwai ruwan da na adana bari in kai maki kiyi wankan" Daga haka ta fita daga bukkar, Badiyya ta bi ta da kallo, katon drum da ta sa ma kwado ta bude ta dau bokiti ta cika da ruwa tace "Banda ke ma wa ya isa yasa in bude wannan ajiyar tawa, ruwan nan yafi wata shidda komin rashin ruwan da nake bana taɓa sa, sai dae rashin ruwan ya kasheni babu ruwana, nasan wataran zai min amfani, to yau ga amfaninsa" Badiyya ta fito da sosonta da Sabulu ta wuce ɗan karamin bandakin dake tsakar gidan bayan Mama Ladi ta kai mata ruwan, Mama Ladi tace "Allahu Akbar, wllh sak marigayiya, bana mantawa haka take zuwa ta min sati a garin nan tun ma bata yi aure ba, ita kadai ce bata kyamatar inda nake sae er uwata Hajja kaka, Allah dai ya ji ƙan Rukayyah, shi yasa komi na samu er ta Badiyya nake ajiye ma idan na samu me shiga kano in basa amana ya kai mata" Badiyya na fitowa daga wanka ta tarar Mama Ladi ta ajiye mata kunu da kosai, ta ɗan yi shafe shafenta sannan ta fara cin abinci don karfe biyu na rana ake nema, Mama Ladi har da shimfida mata sabon zanin gado a kan gadon karfenta, Mama Ladi ta dawo ta zauna gefenta tace "Ban ji kince er uwata Hajja tace ki gaisheni ba" Badiyya ta fashe da kuka kamar jira take, a gigice Mama Ladi ta saki kara tace "Wayyo Allahna, mutuwa Hajjan tayi? Na shiga uku na lalace, ta mutu ne?" Cikin kuka Badiyyah tace "Tana nan Mama Ladi ba abinda ya sameta, kawai dama na zo in gaya maki abinda ake min ne saboda an ga bani da kowa, anga Abbana da Ummata basu da rai" ta kare maganar tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Subhanallahi me ake maki Badiyya, su fa mutane har yanzu basu gane rikon maraya akwai tsarkakkiya ba shi yasa da yawan jama'a wuta za su, wa yace masu ana ma marainiya haka? Yanzu basu san ta dalilinki duk sai su shiga wuta ba" Nan Badiyya ta gyara zama ta labarta ma Mama Ladi duk abinda ke faruwa, na karya da na gaskiya, wanda na karyar ma yafi yawa, Mama Ladi tayi shiru tana kallonta baki bude, can ta gyada kai a hankali tace "Tabbas Hajja ta kirani ta sanar min da wannan biki har nace idan Allah ya nufa in zo to zan zo, don gaskiya naci alwashin sai bikinki zan je garin kano don kece tawa, Ita kanta Ammin ta kirani ta sanar min da batun bikin na mata Allah ya sanya alkhairi kawai, ko ba komai hakan ma zan samu lada, to da naji har da na Mashir ne ma yasa na canza shawaran zanje bikin don Mashir nawa ne, ashe kwace suka maki suka makala ma ita meran, ikon Allah, mutane sun zama abinda suka zama a harkan rashin tsoron Allah... Amma Ammi ta bani mamaki ainun, wllh ta ban mamaki, ita Hajja dama bazan kullaceta ba tunda nasan Ammin ce ke juyata yanda ta so, Hajja bata jin maganar kowa sai ita ko don tana kulla mata shinkafa a leda ta kai mata ne oho, amma banda haka ko ita da bazata amince da wannan abu da aka maki ba, me aka yi akayi Mera kuma Allah na tuba? Ana nufin Mera ta fi ki matsayi wajen Ammi ko Hajja kenan? To ko dai cutar mantuwa ce ta kama su, kina er kanwarta uwa daya uba daya a maki haka akan Mera?" Badiyya dake ta kallon Mama Ladi tace "Ko dai baki gane wacce Mayraahn nake nufi ba?" Mama Ladi tace "Ni ko na gane warce kike nufi, ko ba er wajen Ammi ba? Ko ba wannan tsigalalliyar fara doguwa da hanci zarere kamar biro" Badiyya ta hade rai tace "Ita mana... Ita ce ta kwace saurayina za a masu aure yanzu haka saura wata daya" Murmushi Mama Ladi tayi ta rike haɓa tace "Ikon Allah, dama ance in da ranka zaka ga abubuwa iri iri, to gashi ko na ga wannan"
07087865788✍🏻
WhatsApp only.
[5/31, 4:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
6......
Babu wanda ya kai Ammi shiga tashin hankalin disappearance din Badiyyah, Maheer dama ko a jikinsa ya shirya ya fita aiki wajen karfe tara, Mayraah ma shi ya sa ta tafi lectures, don ita ma hankalinta ya tashi ganin yanda Ammi ta damu sosai, gashi Ammi ta kasa gaya ma Abba abinda ke faruwa har dai ya fita wajen karfe goma, dama kafin ya fita ta nemi izinin zuwa wajen Hajja, yana fita kuwa ta bi bayansa zuwa gidan Mahaifiyarta... Hajja dai ta bi ta da kallo har ta nemi waje ta zauna sannan tace "Ke baki da aiki sae daga ma kanki hankali akan abinda bai kai ya kawo ba matar nan, waye bai san halin Badiyyah ba, yarinyar da nima ta sha min haka in tashi da sassafe in ga babu ita a gida, nace maki ki kwantar da hankalinki kin ki" Da damuwa Ammi tace "To Hajja naga na kira Bichi sunce bata je ba, ga shi har yanzu wayarta a kashe kinga kuwa dole in damu ai" Hajja tace "Yanzu haka tana wajen kawayen nan nata da basa gaya mata gaskiya, sai can yamma nasan zata tafi Bichin, haka nan take sai dai in mantawa kika yi, don haka ki kwantar da hankalinki kawai, in dai Badiyya ce zata aikata abinda yafi haka ma" Har kusan la'asar Ammi bata bar gidan Hajja ba, lokaci lokaci kuma take kiran layin Badiyya still sai ta ji a kashe, a takaice dai ranan ta kira Badiyya ya fi sau Hamsin, Hajja tace "Kin ga ki tashi ki koma gida yamma ya gabato" Ammi "Me zan girka maki kafin in tafi?" Hajja tace "Ga dai sauran girkin da kika yi da rana ai ya isheni har ma zan ba almajiri a ciki" Hajja bata rufe baki ba wayarta ya fara ring, ta dauka tana nuna ma Ammi screen din tace "Waye?" Lokaci daya Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya ganin Badiyya ce ke kiran Hajja, Ammi tace "Ita ce" Hajja tace "Ahaf, taga daman kunna wayar kenan, Allah dai ya shirya mana ita kawai"' Hajja ta daga kiran tare da saka handsfree tayi sallama, daga daya bangaren Badiyya tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau Badiyya, ina kika je duk kika bi kika daga ma mutane hankali haka?" Badiyya tace "Kawai na tafi Bichi, kuma zan yi sati zuwa kwana goma a nan kafin in dawo" Hajja ta buda baki tace "Makarantar fa Badiyya? Ba naji ance a matakin karshe ku ke ba? Wa zai maki jarabawan?" Badiyya tace "Kwana goma fa kawai zanyi in dawo ai" Hajja tace "To me yasa kika tafi babu ko sallama duk kowa ya bi ya damu, ko Ammin taki fa baki sanar ma tafiyarki ba duk ta daga hankali" Badiyya tace "Kawai ni Hajja bazan iya zaman gidan ba ana nuna min wariyar launin fata saboda iyayena sun mutu, Shi Maheer yayi ta min fada yana min tsawa kamar wani ubana kuma ko fuska baya sake min alamar dai bai ji dadin zuwana gidan su ba, ita kuma Mayraah saboda ni taki zaman dakinta ta kwashe duk wani abun amfaninta ta fita, kwata kwata ma ta daina kwana dakin kuma ko magana bata min tun da naje wllh, kawai dai alamar babu wanda yayi farin ciki da dawowata gidan, shi sa kawai na taho Bichi idan nayi kwana goma a nan na huta zan dawo gidanki, sauran kayana dake can gidan dama ki aika a kwaso min a ajiye nan gidanki" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To shikenan sai kin dawo, ina gaida mutan gidan gaba daya" Badiyya tace "Za su ji" Daga haka ta katse wayar, Mama Ladi dake dama fura tace "To kin ga haka ae ya fi kar tashin hankali yasa er uwata ta shiga wani hali in shiga uku" Badiyya dae bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta ta koma ta jingina da gadon karfe tana kallon Mama ladi, Mama ladi tace "Wai ya naga duk kin dawo wani iri" Badiyya dai bata ce komai ba, amma fa kana ganinta kasan she looks confuse.... Ammi kam tayi jigum tana kallon Hajja bayan ta ajiye wayar hannunta, ta ma kasa cewa komai maganganun Badiyya kawai ke mata yawo a kai, Hajja ta kyabe baki tace "Ki tashi kawai ki tafi gida, Allah ya sauwake, amma Mayraah bata kyauta abinda tayi mata ba, da bata yi mata haka ba, Su dama 'ya yan nan naki maza ni nasan ba son Badiyyah suke ba tun asali, dubi abinda Usman yayi mata ranan kamar wata mara galihu, kawai an maidata baren karfi da yaji, haka ae babu dadi, in su basu hada komai da ita ke kam ai dolenki ce..." Lokaci daya hawaye ya kawo idon Ammi jikinta yayi sanyi, Hajja tace "Ni ba kuka za ki min ba, ki tashi ki tafi sae anjima, amma ki gargadi Mayraah abinda tayi sam bata kyauta ba..." A hankali Ammi ta girgiza kai tana hawaye tace "Ni ban isa in canza maki tunaninki akan abubuwan nan dake faruwa a kwanakin nan ba Hajja, nasan akwai abubuwa da yawa a ranki da baza ki iya fadi ba, sannan nasan duk abinda zance maki bazai sauya tunaninki na cewar ina fifita Mayraah akan Badiyya ba, kuma ina ta kokarin gudun hakan amma abun ya ci tura, dai dai da second daya ban taɓa fifita Mayraah akan Badiyya ba Allah shine shaida...." Hajja ta dakatar da ita da sauri tace "Ke kin fi kowa sanin ba haka nake ba, Allah ya sauwake kuma in zama haka, ni babu komai ƙasan raina sai Alkhairi, ai ɗa na kowa ne bawa sai me shi, Allah dai ya rufa mana asiri duniya da lahira, in ma akwai wani zargi da kike yi a ranki da har yake damunki yau da kullum to ki gogesa, ba komai ke hanaki sukuni da aikin koke koke ba illa abinda kika dasa a ranki yake nukurkusan ki, ni ai ba yarinya bace, don haka ki tashi ki tafi gida kawai, yara kuma gaba dayansu Allah yayi masu albarka, duk daya suke a wajena babu banbanci har ga Allah" Har Ammi ta bar gidan Hajja jikinta a sanyaye yake, why is all this happening all of a sudden, duk kwanan nan bata samun nutsuwa ta rasa dalili, ta saƙa wancan ta warware duk ita kadai a ranta, tun dai da aka kawo kudin auren Mayraah, Ko da ta koma gida maimakon tayi scolding Mayraah kan abinda Badiyyah tace a kanta bata yi hakan ba, sai ma kara jan abarta da tayi a jiki tana kuma jin ta har cikin ranta.... Throughout satin tare Mayraah suka dinga zuwa kasuwa da very close frnds din Ammi guda biyu, kaya na gani na fada suka dinga siya mata na lefe masu tsada da quality, within period din kuma Dr Musharraf ya tura mata sauran 3M din, Ammi tayi ta mata fada me yasa zata bari ya kara turo kudi, wannan ai rashin godiyar Allah ne da kai kai inda Allah bai kai mutum ba, kafin sunday suka gama hada komai na lefe, Abaya da akwatuna ne sai jewelries kawai ba a siya ba.... Ranan litinin da yamma Musharraf ya tura driver dinsu ya je daukan kayan don a zuba su cikin akwati, bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs sanye da hijab har kasa, Ammi ce zaune parlon da Usman, Mayraah ta karasa kusa da Ammi ta durkusa kasa tace "Ammi yana jirana a waje" Ammi na kallonta tace "To amma kar ki dade" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta kalli Usman dake kallonta sannan ta mike, Usman yace "Me yasa shi bazai zo ido na ganin ido ba" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, Ammi ta kallesa tace "Ai bai ma fiye zuwa da daddare ba" Mayraah ta juya ta nufi kofa kamar munafuka, Usman yace "Saura ayi isha kina waje" juyawa tayi ta kallesa, Ammi ta hararesa tace "Yi tafiyarki ki rabu da shi, wani ya hanasa dinga zuwa zancen shi ma..." Mayraah ta ɗan yi murmushi ta fita daga parlon. slowly take tafiya har ta isa kofar gidan, ta jingina da motarsa tana jiran ya sauko, sauke glass yayi lkci daya turarensa ya gauraya wajen, yana kallonta yace "I am not staying long, ki shigo mu yi magana...." Ba musu ta bude motar ta shiga sannan ta kulle ta jinginar da kanta da kujeran motar cikin sanyin murya tace "Good evening sir" Yana kallonta yace "Me yasa baki je school ba yau?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I was having headache" Ya dinga kallonta, can yayi kasa da murya yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa suka hada ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa yace "Tell me... menene yake damunki? for almost a week u are moody, What's happening wifey?" Tana kallonsa da manyan idonta tace "Ba abinda yake damuna fa" Yace "Ur test scores were poor..." Mayraah ta dinga kallonsa tana nazarin wani test ma suka yi, sai kuma tace "Na Dr Garba?" Yace "Test nawa ku ka yi last week?" A hankali tace "Uku" Yace "You didn't perform well in all" Kasa cewa komai tayi, and at the same time she look disturb and sad, Ganin yanayin da ta shiga yace "Tell me, baki yi karatu bane?" Ta langwabar da kanta a hankali tace "Wallahi nayi" Yace "Kinga it's ur final semester Mayraah, u need to add in more effort... Idan akwai abinda yake damunki ki gaya min yanzu, feel free to tell me Baby" Cikin sanyin murya tace "Pls sir baza a iya barin bikin sai bayan na gama final exams ba?" Shiru yayi yana kallonta for almost 40 seconds, jin yayi shiru ta ɗan kallesa suka hada ido, kamo hannunta yayi ta janye da sauri tare da turo baki, yace "Me yasa kike son a bar bikin sai bayan final exams?" Tace "So i can concentrateq fully" Yace "No Mayraah, in 2 weeks time za ayi bikinmu in sha Allah, i know u are in ur final semester i will give u the whole time, I won't stress u, zan fi kowa son ganin kin fito da first class dinki, i promise bazan takura ki ba, naga kuma nema kike ki dawo 2.1, your performance is dropping terribly..." Mayraah dai bata dago kanta ba, yace "Idan ma kina son ki zauna gidanku bayan anyi bikin har zuwa sanda za ku gama exams din it's okay by me" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh ka bari in zauna gidan namu har in gama exams din" yace "Consider that done" Ta sauke kanta tace "Thank you so much" Ya sakar mata Murmushinsa me kyau underneath his breath yace "My pleasure" Tace "Yaushe za mu yi test dinka?" Yace "Gobe" ta dago da sauri tana kallonsa duk da ta san gobe ne amma tunaninta zae ɗaga masu, yace "I know u can do it Dear" Ta marairaice tace "Plss sir ka bar shi on Wednesday mana" yace "Ae bana zuwa Wednesday, beside i will be going to Abuja that day" tayi shiru tana kallonsa, ya shafa beard dinsa yace "Zan tura maki AOC, and u can forward to ur colleagues a group dinku na WhatsApp, kinga su ma sun ci albarkacinki kenan" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "To mun gode Sir" Yace "Sai bayan biki zaki daina ce min Sir din nan?" Ta ɗan saci kallonsa amma taki cewa komai, Ya lumshe ido ya bude, yace "Kinsan Friday za a kawo lefen ki?" Mayraah da sai da gabanta ya fadi tayi shiru bata basa amsa ba, yace "Yeah, on sunday sae in kaiki ki gaida Mamina with her sisters, they are all around" Mayraah dai ta kasa cewa komai, yace "We have just this week, daga next week bazan samu lokacin kai ki ba" Jin she is quiet yace "You are not saying anything Wife" Ta yi gathering courage tace "Allah ya kai mu lafiya" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "It's almost time for isha, zan tafi yanzu"
Washegari Mayraah na zaune class tare da sauran Coursemates dinta ko wanne da sheet of paper a gabansa da question paper, ita dai sai juya pen din hannunta take, she looks so confuse cause ta yi karatu jiya da daddare don sai da ta kai kusan karfe daya kafin ta kwanta, but ji tayi kamar bata bude handout din ba kwata kwata, ga wani ciwon kai da ya sa ta gaba, ta daga kai ta kalli Dr Musharraf dake tsaye hall din wearing a sparkling white shirt, baƙin glasses ne a idonsa so she can't tell where he is looking in particular, ta ɗan bi hall din da kallo, Zaune taga Badiyya tare da clique dinta ta dage sai kwafan na Amira take da gefen ido, tun last week rabonta da school sai yau, bayan kusan minti talatin Mayraah ta mike kawai ta linke takardanta, Hamida sai kallonta take da mamaki ganin fa bata ga tayi rubutu ba, ta dinga mata alamar ta tsaya kar taje tayi submitting amma tuni Mayraah ta nufi inda Dr Musharraf ke tsaye, tana kallonsa tace "Where can i submit sir?" Ya mika mata hannu ta basa takardan, zata juya ta bar wajen as if in a whisper yace "Wait" ta tsaya ba tare da ta kalli fuskarsa ba, bude takardan yayi yaga sunanta kawai ta rubuta sai course da code, ya dinga kallonta kafin ya mayar mata da takardan yace "Go back and sit my friend" Ta amshi takardan ta juya a hankali ta koma, Badiyya dake kallonsu ta wani tabe baki ta ci gaba da satan answers din Amira da gefen ido, kusan sai da duk yan class din suka yi submit suka fita har Badiyya da clique dinta, ajin ya rage few students sai Mayraah dake ta juya pen dinta, zuwa sannan dai ta samu ta tuna solution din second question din kuma ta rubuta, yana cewa 5 minutes more amsan number 1 ya dira kanta in full speed, within that 5 minutes ta amsa question din ta kusa cika fullscap, dama questions hudu ne, to ta samu ta amsa biyu, zuwa sannan su hudu ne kawai a ajin da basu gama ba, ta mike ta tafi ta basa takardan ta ya amsa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14