kashe kudi a yan kwanakin nan, kayi hakuri ka ji" Maheer dake ta kallon Ammi dama ya innata abinda ya sa ta kirasa kenan shine ta fara kame kamen wai ya nemo mata irin Gold din a kasuwa, yasan ba dalilin kiran ba kenan tunda dai tasan shi ba kasuwa yake shiga ba, she just beat about the bush kafin taje main point dinta, ko kadan Maheer bai son duk abinda zai daga hankalin Mahaifiyar tasu, yace "Shikenan Ammi zan tura maku in sha Allah, Allah ya rufa asiri" Ammi tace "Ameen, Allah maka albarka Maheer, Allah ya sa 'ya yanka su maka biyayya yanda kake min, Allah ya kara maka budi" Bai wani jima a dakin ba ya fita...
Washegari Thursday karfe tara da rabi Maheer ya fita gida zuwa gidansu Haseenah don kai ta su siya kayan dinner dinta tunda na farkon tace masa bata so, jiran kusan minti ashirin yayi mata a mota sai ga ta ta fito ta shiga front seat tana masa wani kallo tana blushing tace "Good morning Sweedy" Ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yace "Nace maki akwai inda zan je amma kika bata min lokaci Madam" Ta wani karyar da kai tace "Ita fa amarya bata laifi Baby, ko ka manta ne?" Tada motar yayi suka bar layin, waje me shegen tsada ta kai sa za ta siya ready made din dinner wear din wanda tun a IG ta sa suka turo mata ta zabi wanda take so, kawai yanzu zuwa zata yi ta gwada in akwai ɗan wani adjustment da za ayi sai a mata nan take, shi dai bai ce mata komai ba har suka shiga Lounge din wajen, bayan some minutes aka yi attending masu, wani ubansun dress ya ga an dauko mata wanda ko ba a fada maka ba kasan sai aljihu ya girgiza, ta amsa tana wani murmushi aka yi leading dinta zuwa inda zata je ta gwada, Maheer ya sauke wani ajiyar zuciya a ransa yace ai ko za su yi bala'i da ita don in har kayan nan ya wuce 200 zuwa 250 to sai dai a fasa siya, ya dau ruwan da aka ajiye masu yayi sipping yana jiran jin price din kayan, wayar Haseenah dake cikin jakarta ne ya fara vibrate, ya kalli jakar dake gefensa sannan ya dauke kai, har dai kiran ya katse, sake kira aka yi nan ma dai bai yi attempting ya ga me kiran nata ba, sai da aka yi kira kusan sau hudu, sannan ya sake kallon jakar da mamaki, jawosa yayi kusa da shi ya bude ya ciro wayar, yana cirowa kuwa yaga wata babban sarka sai daukan ido yake can kasar jakan, ya sa hannu ya ciro sarkan yaga hade yake da dankunnensa da zobe, da ɗan mamaki yake jujjuya sarkan, wayar Haseenah da ke daya hannunsa ya fara vibrate, yana dubawa yaga Badiyya ce, sake kallon sarkan yayi kamar me observing din wani abu, da sauri ya ajiye wayarta ya dau nasa ya shiga WhatsApp ya shiga chat dinsa da Ammi yayi downloading image da ta turo masa jiya don dama bai yi downloading ba, he was sooo shocked ganin exactly sarka da dankunnen hannunsa ne a picture din, ya dinga kallon hoton gold din wayar tasa da na hannunsa, banbancin kawai wanda Ammi ta tura masa a case dinsa yake, wannan kuma ba cikin case yake ba, kamar wanda ya tuna abu yayi saurin mayar da wayarta cikin jakarta ya ajiye jakar inda ta bar sa, ya fara tunanin yanda zai yi da sarka da dankunnen hannunsa, da sauri ya zura a aljihun wandonsa, and it was very obvious zata iya lura da aljihun nasa, can ya mike ya kai wayarsa kunne kamar yana waya ya fita daga Lounge din ya fito harabar wajen, motarsa ya nufa still pretending he is making call ya bude motar ya boye Gold din a ciki sannan yayi maza ya koma ya zauna inda yake zaune, bayan few minutes sai ga Haseenah ta fito tana wani murmushi tace "Baby transfer the 600k for them mu tafi, masu lalle nasan suna can suna jirana dama nace sai ana gobe daurin aure zan yi so that it will remain clean har a kai ni gidanka" Ya sakar mata murmushi yace "That is thoughtful of you, dress din ya maki dai ko?" Ta zauna kusa da shi tace "Sure dear, i love it soo much" Nan take yayi transfer din, bayan sun yi confirming payment din aka bata package din kayan suka fito tare da shi tana sakale da jakarta.... Direct gida ya maida ta yace sauri yake ana jiransa daga haka yayi reverse ya bar layin, Haseenah ta ciro wayarta bayan ta shiga gate din gidan ta zaro ido ganin miss call din Badiyya har biyar, dialing din number me siyar da Gold tayi tace "Haba Hamisu tun daxu fa kai nake jira wllh" yace "Ehh Hajjaju gani a hanya ai" tace "Toh sae ka Karaso" Ta kira Badiyya tace "Dadina dake takura wllh, gashi nan yanzun nan na kirasa yana hanya, kinsan basa fitowa kasuwa da wuri ne yau, don Allah kiyi calm down ya a isowa zan kira ki" Badiyya tace "Gaskiya ni dai yayi sauri Haseenah, wllh akwai wanda zan ba 200k ne duk ya addabi rayuwata yana neman min tonon asiri" Haseenah tace "Nan da minti kadan yana isowa bayan ya auna zaki ji alert abinda kin turo min acc dinki kawai be patient Baddiee" A haka suka rabu Haseenah ta shiga cikin gidan tana sauri ta je ta nuna ma kawayenta classy and unique dinner dress din da zata saka, amma fa tayi mamaki da lokaci daya Maheer yayi payment din bai ce kudin yayi yawa ba don shi kam ba mai son fake life bane, a ranta tayi concluding yasan abinda yake jira eagerly ai dole ya biya kudin dress sharp sharp babu musu. Haseenah bata bari an fara mata lallin ba saboda Hamisu dake hanya, wajen karfe sha biyu ya kirata yace yana waje, ta dau jakarta ta lallaba ta fice daga gidan babu wanda ya lura da ita, tana zuwa inda tace ya tsaya ya jirata ta bude jaka tana kokarin fiddo gold taga wayam, da farko ta zata idonta ne ya nuna mata haka, ta kikkifta idon ta sake wangale jakar still taga wayammm, wani azababbun zufa ne suka hau keto mata tana gwale ido tace "Hamisu, duba min jakar nan ka ciro Gwal din a ciki ni na kasa cirowa" tana fadin haka ta manna masa jakar a hannu tana zare ido, Hamisu ya mayar mata jakar da sauri yace "Ke me jakar baki gani ba sai ni Hajiya" Zazzage komai na cikin jakar ta hau yi a kan titi a rikice amma babu gold bBu alamar Gold, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku da Badiyya" Hamisu yace "Gaskiya Hajiya kin bata min lokaci ne kawai, ai da kin fara dubawa kafin ki kirani.... Gashi customers can na ta jirana na bar su na yo nan wajen ga Unguwan nisa, kawai ni bari in tafi kasuwa yanda ake ciki sai ki kirani" Yana fadin haka ya buga machine dinsa ya kara gaba. Kiris ya rage Haseenah ta saki fitsari a titin, ko ina na jikinta rawa yake tsabar tashin hankali, ta dai samu ta ruga cikin gida ta shige visitors toilet dake cikin compound tayi fitsarin, tana fitowa ta tafi can backyard din gidansu ta zauna zufa wani na bin wani a goshinta, ita ba abun tayi raising alarm ba asirinta ya tonu Mummy ta gano abinda ke faruwa, dazu fa kafin ta fita da Maheer sai da ta duba jakar yana ciki kuma tunda suka dawo bata ajiye jakar nesa da ita ba balle tace a dakinta aka dauke, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ko dai wajen siyan kayan ne aka mata sata da taje gwadawa?? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace me zan ce ma Badiiya"
Ammi ta kasa motsawa daga inda take zaune tana kallon abinda Maheer ya ajiye masu saman gado ita da Aunty Mariya, Aunty Mariya ta mike a gigice tace "Ina ka samo wannan Maheer?" Shi dai bai ce komai ba ya koma gefe daya ya rungume hannunsa yana bin su da ido, Ammi ta kallesa tace "Maheer wannan daga ina? Ko sabo ka siyo ne?" Yace "Babu wani sabo, tsohon da ku ka sani ne dai" Ammi ta buda ido with shock tace "Daga ina??" Maheer ya ɗan yi shiru yana tunanin abinda zai ce masu don bai son fara painting Haseenah black wajen Ammi, he just have to cover her up in other not to create doubt tsakaninta da iyayensa, Aunty Mariya ta hade rai tace "Dallah ka mana magana ka yi wani shiru, where did u find this?" Ya shafa kansa yace "Ita warce Ammi bata son laifinta ta kai ma Haseenah ajiya, shine Haseenan ta bani dazu da naje gidan, Badiyya ta kai ma Haseenah sarkan ta ajiye mata" Ammi ta dafe kanta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya kam buda baki tayi hangangan tsabar mamaki, Maheer ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta fara hawaye tana girgiza kai ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta dau Gold din ta adana shi inda babu wanda hankalinsa zae kai wajen a dakin Ammi ita ma ta fita daga dakin.
Mami ce zaune parlonta a sama tare da yan uwan mijinta maza su biyar, Kawu Mansur yace "Maryam da girmanki da hankalinki bai kamata kina biye Halima kuna maida maganganu haka ba, shi sa muka ja ki muka dawo nan sama dake ayi magana ta fahimta...." Mami dai wani direction din daban take kallo kawai zuciyarta na tafarfasa, Kawu Mansur yace "Tsakaninki da Allah Maryam me kika sani game da gidan nan da Abdallah yake neman aure?" Mami tace "Au ashe ma yan uwana ne kenan da har zan san wani abu game da gidan, ka ga fa Yaya Mansur yanda ku ka samu wannan labari sama ta ka to nima haka nan ya riskeni, yanda duk aka bi ku da Envelope nima haka aka kawo min nan, sannan ina ganin ai ba wani zai zauna ma Musharraf da yarinyar nan ba, ko ma menene tunda yace yaji ya gani yana so ina ga a bar yaron kawai, he is old enough to make decisions for himself, shi ma ai an basa takardan kafin ma a kai maku and he wasn't bothered about it...." Kawu Faisal na kallonta kasa kasa yace "Tunda auren wasan yara ne da har zai bude baki yace yaji ya gani ba? Mu kuma gamu a banza, To abinda ke da shi baku sani ba shine, bai isa ya yanke ma kansa decision kansa tsaye as far as mu iyayensa muna raye, don haka ba shi da wani say a wannan lamari sai abinda mu manya muka ce, in kuma bashi da manyan ne sai ki gaya mana yanzu mu ji...." Mami ta masa wani kallo kafin ta kai ga cewa komai Kawu Mansur yace "Yanzu dai duk ba wannan ba, wannan lamarin da ake ta cukuikuyawa abu ne me sauki wllh, mu fa muka kai kudin nan ba wasu suka kai mana ba, mafi sauki shine mu sake komawa gidan don a warware mana abinda ya shige mana duhu daga bakin iyayen yarinyar nan da suka amshi kudi hannunmu, ai ba sai an tsaya ana cece ku ce ba, ga best alternative kawai na kawo" Mami tace "Ohh da an san da haka za a zo nan a daga min hankali saboda an raina ni? To wallahi ku ja ma Halima da Rumaisa kunne idan basu fita harkata ba ina me tabbatar maku hukuma ce zasu min iyaka da su, nan ba da dadewa ba kuwa" mikewa Kawu Saleh yayi ya fita daga parlon sauran ma duk suka mike suka bi bayansa parlon ya rage Kawu Mansur kawai, Kawu Mansur yace "Yanzu dai kiyi hakuri Hajiya, duk abinda ake ciki za ki ji kira anjima, ko kuma in zo da kai na" Daga haka ya mike ya fita daga parlon.... Abbansu Maheer na Bedroom dinsu yana duba wasu takardu, dawowarsa kenan daga Abuja saboda daurin auren 'ya yan nasa da za ayi gobe, Ammi ta shigo dakin tace "Yallabai wai kayi baki fa" Abba ya kalleta yace "Daga ina?" Ammi tace "Maheer yace kamar dangin yaron nan ne Musharraf, yace su suka kawo kudi" Abba ya ajiye takardun hannunsa yace "Toh lafiya, Allah sa dai ba cewa za su yi a daga bikin ba" Ammi tace "In hakan shine mafi alkhairi ai babu yanda aka iya" Abba ya dau wayarsa ya fito daga dakin ya fito compound don a nan parlon baƙin yake, yana shiga parlon duk aka gaggaisa, Maheer ya shigo ya ajiye masu carton din ruwa da lemo, Abba yace "Ya shirye shiryenmu?" Duk suka amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah" Abba yace "To Madallah" Kawu Mansur yace "Dama wata magana ce ke tafe da mu Alhaji, sai dai za mu so kayi mana uziri kuma ka fahimce mu, don ko kaine a shoes dinmu iyaka hakan kai ma zaka yi" Abba da yayi jim, can yace "Ikon Allah, to ina sauraronku Alhaji, Allah sa dai lafiya" Maheer dake kokarin fita daga parlon jin abinda Uncle din Musharraf yace sai ya kasa fita lkci daya jikinsa ya basa all is not alright, Alhaji Faisal ya ciro takardan aljihunsa ya mika ma Abba, Alhaji Mansur ma ya ciro ya mika masa, Alhaji Sale shima yayi haka Abba dae sae amsan takardun yake yana bin su da kallo cike da mamaki yace "Na menene wannan din?" Alhaji Mansur yace "Mu ma duk haka suka iso gidajenmu a yammacin jiya, ka duba ka gani Alhaji" Abba ya maida dubansa kan takardun baya ko kiftawa amma ya kasa duba ko daya ya karanta, Maheer ya karaso kusa da Abba zai amshi takardun Abba ya daga masa hannu, calmly yace "Zan duba" Yana fadin haka ya shiga duba content dinsu gaba daya, daya bayan daya yabi har ya gama karanta su, a hankali ya linke su duk ya ajiye gefensa yana kallon Uncles din Musharraf da suka zuba masa ido gaba dayansu, Abba ya ɗan kwantar da kansa jikin kujeran da yake zaune, trying all possible best to be calm yana kallonsu yace "Haka ne.... Duk abinda ke rubuce jikin takardun nan gaskiya ne amma banda abu daya zuwa biyu ..." Yana kai wa nan yayi shiru, Alhaji Faisal yace "To Alhamdulillah, sai dai fa Alhaji abu dayan nan zuwa biyu da kace is of no importance to us right now, don tun asali baka bi ka'idar da ya kamata ka bi ba while giving out the girls hand in marriage tunda kasan da wnn babban issue din a kasa, in other words an yaudaremu an kuma yi playing with our intelligence an mayar damu kananun mutane, sannan an cuci ɗan mu, a lamari na aure babu amfanin shigowa da rashin gaskiya cikinta saboda gudun abinda zai je ya dawo, domin haka muke son sanar da kai cewa a yanzu mun janye daga wannan auren da muka nema ma ɗan mu ake kokarin daura sa gobe, sadakinmu da duk wani abu da aka kawo gidan nan za mu aiko a amsar mana in sha Allah, gatan da ko wani uba zai yi ma ɗan sa kenan a issue irin wannan, mun bar ka lafiya Alhaji" Abba was speechless, har duk suka mike suka fara fita daga parlon, Maheer da gaba daya ya dinga jin maganganun Uncle din Musharraf kamar a mafarki yayi saurin daukan takardun da Abba ya ajiye a gefensa yana dubasu daya bayan daya, kallon Abba yayi, lkci daya ya duka nan gabansa hankali a tashe yace "Abba ban gane ba, what is all this? Me yake faruwa??" Abba ya kasa ce masa komai don yayi nisa tunanin da ya tafi, Maheer that is getting impatient don har wani zafi yake ji duk da AC dake kunne parlon yace "Don Allah kace min wani abu Abba, i am loosing my self, I can't stand this anymore, me ke faruwa?" Abba ya sauke ido ya kallesa, bayan few seconds ya fara magana Calmly yace "Haka ne.... Mayraah isn't my biological daughter Maheer, ba ni da Ammi muka haifi Mayraah ba, bamu san ta yaya ma aka sameta ba, mu dai kawai...." Kasa ci gaba Abba yayi, Maheer that was dumbfounded and shock ya dinga kallon Abba kamar ranan ya fara ganinsa it felt like mafarki yake kawai, bayan shirun kusan minti uku tsakaninsu, Maheer yayi karfin halin mikewa with breaking voice yace "Ni da Usman kuma su waye iyayenmu? If Mayraah isn't ur child then mu ma ba yaranku bane" Yana kai wa nan ya fice daga parlon Abba ya kasa ce masa komai...
Mayraah ta mike zaune tana kallonsu Hamida dake ta harkan gabansu a dakinta, waya ne kare kunnenta suna magana da Musharraf da ya kirata ko minti biyu ba ayi ba yanzu, a hankali tace "I will call u back, i am not alone" tana fadin haka ta katse wayar ta fita zuwa corridor din dakunan, sake dialing numbersa tayi yana dagawa ta marairaice tace "But sir kasan bazan iya fitowa yanzu ba ai, they are people everywhere a gidan, i will be noticed idan zan fita" Musharraf yace "Plss Mayraah find a way da zaki samu ki fito it's urgent plss" She couldn't resist because of the urge in his voice, cike da damuwa tace "But are you okay sir?" Yace "No i am not" Tace "Ohk, yanzu kana farkon shigowa layinmu kace?" Yace "Eh" Tace "Toh i will be coming right away" Katse wayar tayi ta fara tunanin ta yaya zata fita gidan nan without being noticed, daga karshe dai she successfully found her self outside ba tare da an lura ita bace don Nikab ta saka, ko su Hamida basu son ta fita daga gidan ba, inda yace mata yayi parking ta nufa, taga Motarsa ta karasa ta bude front seat din ta shiga tana kallonsa da damuwa, kafin ta ce komai taga ya fara driving motar, da mamaki tace "Sir ina kuma za mu je?"
Payments before end of free pages, to avoid going for break...
07087865788✍🏻
WhatsApp only, no phone calls pls
[6/6, 4:38 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga one and only Maman Khadee me sabon kasuwar dutse😁 (Aunty Zahrah) da Er ta Deejah me lamurje a ɗa kafin ta fara siyar da namijin goro yanzu, sai kuma me cikin shekara uku da taki haihuwa har yau har gobe (Matar Babana Ummu Nabila🙄) khaleesat Haiydar na maku fatan alkhairi a ko da yaushe😁
This page goes to you Zainurah Yazeed Ahmad, u are one of the die hard fan i am opportune to meet, Allah Ubangiji ya raya maki zuri'a, and i do appreciate u now and always dear, Allah ya biya maki bukatunki na alkhairi....
Sauran fans da suka yi patronizing dina even before in gama free pages wllh i really appreciate u people, ina maku fatan alkhairi duniya da lahira, Allah ya raya maku zuri'a, ya kara ma iyayenku lafiya da tsawon rai me amfani, Ameen.
12....
Mami was speechless, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi, banda kallon Alhaji Mansur babu abinda take, Alhaji Mansur ya ci gaba yace "Don haka mun sanar masa za aje karbo mana duk wani kaya da aka kai gidan da sunan aure, kudin da muka kai kuma Faisal zai koma ya amso su" Mami ta girgiza kai cike da damuwa tace "Ba sai an amso komai ba Alhaji, mu bar masu ko don...." Ya wani hade rai ya dakatar da ita a fusace yana kallonta yace "Akan me zaki ce ba sai an amso komai ba? Mu bar masu saboda muna tsoronsu? Mutanen da basu san mutunci ba, mutanen da suka yaudaremu suka maida mu yan iska, ai basu cancanci ko tsinke a bar masu ba wlh, komai sai sun fito da shi idan ba haka ba hukuma ta rabamu da su" Mami dake masa wani kallo ta kasa jurewa tace "Ku ko ina sai kun nuna wannan halin naku na karanta? Idan shi wanda ya siya kayayyakin da kudinsa yace a bar masu fa?" Alhaji Mansur ya mike yace "Shi wanda ya siya kayan ya ci kaza kazansa, ai ba shi ke da iko da kansa ba, Kuma wallahi wallahi kin ji rantsuwan musulmi ko? To sai an amso kayan nan gaba daya, yanzun nan za a tura su Halima tunda dama su suka kai, don haka su za su koma su amso, aikin banza kawai" Yana kai wa nan ya fice daga parlon yana muzurai, tashin hankalin Mami ya kashi biyu yanzu ta ma rasa wani tunanin zata yi in particular, babban damuwarta na farko Musharraf, she don't know how he will take this and cope don ta ga yana son yarinyar, na biyu kuma ita a rayuwarta bata son taga an ci ma mutum mutunci, she detest that, babu tantama tasan an tara jama'a gidansu yarinyar nan, a haka su Halima za su je su gwada halinsu na rashin tarbiyya da rashin mutunci cikin taron jama'a, mikewa tayi ta dauko wayarta tayi dialing din number Alhaji Saminu wanda shine babba a family din and he resides in kaduna, kuma duk suna shakkarsa suna jin maganarsa, yana picking bayan sun gaisa ta fara masa bayanin abinda ke faruwa, ya katse ta yace "Duk na san da batun nan an kirani an gaya min komai, ashe kananun mutane ne makaryata, kinga kuma baza mu bari ɗan mu ya auro warce bata da asali ba, dama an san su waye iyayen nata ne to da sauki, kinga kuwa ai baza mu yarda a kawo mana irin wannan cikin zuri'ar mu ba" A hankali Mami tace "Haka ne, amma yanzu Alhaji Mansur ya bar nan wai za a tura su Hajiya Halima su je can gidansu yarinyar su amso kayan aure da aka kai, ni kuma naga hakan bai kamata ba tunda nasan wacece Hajiya Halima nasan kuma me zata je ta aikata a gidan, kasan cin mutunci bashi da dadi Alhaji" Alhaji Saminu yace "Shikenan shi Faisal da zai koma amso kudin auren sai ya karbo har akwatunan, zan kirasu in sanar masu kada a tura kowa in ba shi Faisal din ba" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, Mami ta ɗan ji hankalinta ya kwanta don baza ta so a walakanta kowa ba a kan Musharraf, kara kiran layin Musharraf tayi for the countless time amma still a kashe, she felt so disturb and worried for him, ta zauna saman kujera ta dafe kanta.... Ammi ta kasa nutsuwa tun bayan da ta shigo parlon baƙi ta dalilin kiran da Abba yayi mata a waya, Abba ya bi ta da ido har ta nemi waje ta zauna tana kallonsa ita ma, da kyar tayi karfin halin cewa "Lafiya dai ko Yallabai?" Abba ya kasa ce mata komai ya dauke idonsa daga kallonta, nan taji hankalinta yayi mugun tashi don kana ganin Abba kasan he is not himself, Ammi ta kasa jurewa tace "Don Allah ka gaya min abinda yake faruwa Yallabai ko yaron cewa yayi ya fasa auren ne??" Abba ya kasa bata amsa don a duniya baya son duk wani abu da zai daga mata hankali sanin condition dinta, but he have no choice dole zata sani, Ganin yanda Ammi ta rikice masa yayi ta maza yace "Haka ne" Ammi was shock, ta dinga kallon Abba ko kiftawa babu, lokaci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Kana nufin ya fasa auren?" Abba ya gyada mata kai, Ta fashe da kuka tace "Meye dalilinsu Yallabai? Sai ana gobe daurin aure an tara jama'a za su zo yau su ce sun fasa, me aka masu haka?" Kuka take sosai tana kallon Abba da ya kasa cewa komai don zuciyarsa ya gama karaya, he is
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14