Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"to oga" buɗe furan kawai yayi bai kara kallonshi ba ya fara sha, wani irin daɗi nonon yake mishi ga kamshin madara da yake kuma a tsaftace. da sauri yaje inda take yace "gashi wannan inji oga" kallon kuɗin tayi sai kuma ta kalleshi, karɓa tayi ta cire iya kuɗin nonon data dama ta bashi sauran tace "kai mishi ni iya kuɗin abinda na siyar nake karɓa" da mamaki ya waro ido ya kalli kuɗin sannan ya kalleta yace "malama kin san nawane kuɗin kuwa?" tace "ban sani ba tunda bani na bayar ba ka mayar mishi" shiru yayi yana kallonta ɗauke kai tayi tana zubawa wani da yazo siya, ganin da gaske take ba zata karɓa ba ya juya jiki a mace ya koma office ɗin, ya jima yana knocking kafin ya amsa, shiga yayi yazo ya ɗan russuna kafin yace "oga yarinyar taki karɓan kuɗin tace iya kuɗin abinda ta siyar zata karɓa" a fusace ya juyo da kujeran tunda yake a duniya bai taɓa yiwa wani kyauta akayi rejecting ba, this is the first time daya bada kyauta aka mayar mishi, cikin zafin rai yace "who the hell think she is? wacece ita da muneeb makawa zai bata kuɗi taki amsa? waye babanta a garinnan?" yayi maganan yana tada jijiyan wuya, a tsorace yace "wallahi oga ban sani ba amma da ganinta ƴar talakawa ce domin babu alaman kuɗi a jikinta sai kyau kamar macijiya....." ganin yadda yake hararanshi yasa yayi shiru, cikin fushin daya saba a koda yaushe yace "ka...ka..ka...ka" rufe ido yayi jin maganan yaki fita sai huci yake, da kyar yace "kace ta bar nan daga yau kakkakkkarta kara zuwa" yace "okay sir" tafiya yayi zai buɗe kofa sai yayi wani tunani yau kaɗai da baisha nonon ba har wani kala yake ji, idan ta tafi aina zai rinka siya?" da sauri yace "wait" tsayawa yayi, yace "forget about her" yace "okay sir" kasan zuciyarshi haushi yake ji yaji ya tsani halinta. tana gama saida nonon ta tattara ta shiga mashin domin ɗaukan habib a school, an jima da tashi musu tun daga nesa take hangoshi ya zauna yayi shiru yana kallon yaran da suke tafiya, ya rungume jakanshi, tausayi taji ya bata dan habib yanada ruwan shiru shiru a duk sanda ta ganshi saita tuna yayarta ameerah wacce ta kula da ita sosai, hakan yasa take jin son yaron a ranta kullum yana karuwa, bataso taga yana kuka a hankali ta sauka a mashin ɗin tun daga nesa ta fara cewa "habibi? habibi?" yana ganinta yayi wani kyakkyawan smiling da gudu ya tashi yaje ya faɗa jikinta, sama ta ɗagashi tana juyi dashi, cikin so da kaunarshi tace "habibi yi hakuri banzo da wuri ba ko?" yace "mama ai kuɗi kikaje nema sabida ki biyamin kuɗin makaranta kuma ki siyamin indomie" murmushi tayi tace "habibin mama me wayo" saukeshi tayi ta rike hanunshi suka shiga mashin ɗin, tafiya suka fara yace "mama yau kin san me akayi?" tace "a,a habibi saika faɗa" yace "karatu akasa nayi kuma na karanta ban ɓata ba shine malamanmu ta bani biscuit harma na rage miki naki" buɗe jakanshi yayi ya ciro mata ragowan biscuit guda biyu yace "ga naki" karɓa tayi tace "habibi na gode amma wannan biscuit ɗin ai yayi kaɗan na bar maka ka cinye" ya shagwaɓe fuska kamar zaiyi kuka yace "wa ke fa na ragewa" tace "to na gode" cinyewa tayi yace "good mama" da mamaki tace "har ka fara koyan turanci?" gyaɗa kai yayi irin na yara yace "harda karatu malama tace nafi su hanin ilimi" tace "Allah maka albarka yasa ka zama me ilimi sosai" yace "ameen" har suka isa gida suna hira sosai, wanka tayi mishi tasa mishi jallabiya baki na yara sabo dal ta siya mishi, subhanallah harshenshi ne kaɗai yake nuna shi ba balarabe bane amma sak ɗan larabawa ya zama, tace "kayi kyau" inna tace "wannan angon nawa kowane kaya kyau yake mishi" yace "inna nifa ba zan aureki ba" ta rike haɓa tace "iye to wa zaka aura?" yace "mama zan aura" yayi magana yana nuna najwa dake juye taliya daga kan wuta, tace "sabida me zaka aureta?" yace "sabida ina sonta" share hawaye najwa tayi ba tareda ta bari sun gani ba, a hankali ta mike ta ɗau plate zata zuba musu taga manja ya kare, rike kwankwaso tayi tace "hande min boni lalashewa" inna tace "ɗume?" cikin gajiya tace "manja timmi fa inna" inna tace "laaa ai na manta babu ko kaɗan?" cikin iya fulatancin ta kuma cewa "wala ko seɗɗa" tayi maganan tana juya roban manjan, shiga ɗaki tayi ta ɗauko kuɗi tazo tace "habibi jeka maƙotanmu ka siyo manja" ya karɓi kuɗin yace "to mama" fita yayi ta zauna akan turmin data daka yaji, gashinta daya addabeta ta kameshi waje ɗaya ta dumbuza a cikin hula, inna tana ganinta tana tura baki sabida ta tsani kitso ko tsifa yanzu wannan kan yafi wata biyu a kitse, tun suna jiran habib har ta gaji tace "wai dan Allah meyasa idan na aiki habibi makota siyan abu bai dawowa da wuri ne?" inna tace "ai baya jin magana ne kullum saina mishi faɗa baya ji zai dawo ya sameni ne ai saina mareshi" ɓata rai tayi domin ta tsani ace za'a mishi faɗa bale mari, murmushi inna tayi domin da gangan ta faɗi hakan, tace "inna me yayi na faɗa da har zaki ce zaki mareshi watakila mutane dayawa sukaje siyan abu shiyasa bai dawo da wuri ba" shiru kawai tayi mata, shigowa yayi yana shesheƙan kuka, da kallo ta bishi direct wajenta yazo ya faɗa kanta yana kuka, tace "meya sameka?" yace "halima ce ta mareni" tashi tayi wuf tace "ta mareka?" hijabi ta zaro daga kan igiyan tasa babu ko takalmi a kafarta ta rike hanunshi zasu fita inna tace "najwah? najwah? ki dakata ki tambayeshi me yayi mata ta mareshi?" cikin masifa tana tafiya kamar zata kife tace "koma me yayi meyasa zata mareshi?" kafin inna tayi magana ta fita, babu sallama ta shiga gidan, maman halima na zaune tana kulla kuɓewa taga mutum a kanta, da sauri tace "subhanallah baiwar Allah ya zaki shigo mana gida babu sallama?" tace "wacece halima?" halima ta fito daga ɗaki budurwa ce tace "nice halima me ya faru?" nuna habib dake ɓuya a bayanta yana share hawaye tayi, tace "me yayi miki kika mareshi?" tace "ki tambayeshi mana shi da ya kai miki kara" tace "habibi me kayi mata?" yace "ban mata komai ba" ta kalleta da idanunda da suka kara girma tace "yace bai miki komai ba, meyasa kika mareshi" ganin sun fara tashin hankali matar tace "baiwar Allah manja ya fasa mata" tace "shiyasa zata mareshi sabida ya fasa manja? bata san tsautsayi bane? wallahi idan ta kara taɓashi koda laifinshi ne saina koya mata hankali" cikin tsiwa halima tace "wallahi saina mareshi naga abinda kika isa kiyi, idan kinaji kinada ɗanyen kai to wallahi inada yaya ɗan taurin kai ne kamar ke" hijabin jikinta ta cire ta ɗaura a kwankwaso taja hanun habib tace "habibi tsaya anan" tsayawa yayi, tace "idan ba zina akayi aka haifeki ba ki taɓashi" "dan girman Allah kiyi hakuri baiwar Allah" cewar maman halima, najwah tace "a,a mama bari dai ta gwada rashin kunyarta ni najwah zan nuna mata karamin hauka take dashi" halima tazo ta ɗaureshi da mari, rike kunci yayi yace "wayyo fuskata" najwah data janyo halima zaka rantse itace ta haifeta, maman halima tana ihu ganin najwah akan ruwan cikin ƴarta tana duka kamar an aikota, tuni makota suka fara taruwa jin hayaniya da ihu a cikin gidan, inna babu shiri tazo, jan najwah suka fara, ranta tafasa yake so take ta lahanta halima ko ranta zaiyi sanyi, sallama akayi wani mashayi ya shigo gidan yace "wai me yake faruwa yau a gidanmu aka taru?" maman halima tace "yauwa audu kazo ka taimaki ƴar uwarka wannan yarinyar batada kunya" a fusace yazo zai mari najwah, hanunshi ta rike da karfi tana kallonshi tace "babu abinda ya saka" yace "kanwata kika daka? yau zan kasheki a gidannan" ganin zai fara dukanta inna tace "dan Allah kayi hakuri bawan Allah wallahi..." kafin ta karasa najwa ta kwasheshi da dambe, matan wajen duk sun tsorata ganin tana rama duk dukan da yayi mata jan kafafunshi tayi ya zube kasa tim, duka take kai mishi, habib yazo yana janta yana cewa "mama ki barsu mu tafi" inna tace "najwah ɗanki fa ke miki magana ba zakiji magananshi ki hakura ba?" tace "kin manta da nasihan Ameerah?" cak ta tsaya daga faɗan, hanun habib ta rike suka fita daga gidan, inna ta rinƙa basu hakuri musamman mamansu ta basu hakuri sosai saida sukace sun hakura kafin ta fita, matan unguwa sai mamakin karfin najwah suke, tana zuwa gida tace "habibi jirani naje na siyo mana manja" yace "to mama amma karki kara zuwa faɗa dasu" tace "insha Allah ba zan kara ba" hijabin tasa zata fita yace "mama wacece ameerah?" tsayawa tayi ta kasa tafiyan, a hankali ta juyo tace "yayata ce amma ta rasu" yace "Allah yaji kanta" tace "ameen" fita zatayi inna tace "koma koma koma nace" komawa tayi, tace "bafa can zanje ba inna manja zanje siyowa a kasuwa" tace "kawo kuɗin ki zauna a gida ni zanje na siyo" zatayi magana inna tace "kimin shiru ki koma ki zauna ko kofa kika fita ban yafe ba, har sai naje na dawo mara hakuri kawai" kuɗin ta karɓa tasa takalmi ta tafi domin babu takalmi ma taje raba faɗan, komawa tayi ta zauna tace "habibi kawo takaddunka muyi karatu" ɗaki ya shiga ya kawo takaddun suka fara karatu, inna ta dawo da manja kafin sukaci abinci, har dare babu inda taje, kayan habib ta cire mishi sannan tasa mishi vest da gajeren wando na yara, ita kuma tasa kayan da take bacci dashi mara nauyi ta hau katifan inna ta jima da bacci, habibi ya rungumeta sabida haka ya saba bacci, addu'a tayi mishi ta shafa mishi sannan ta shafa suka fara bacci. ya tashi daga aiki yau da wuri, su Azad suna falo suna aikin kallo, ya hararesu duk a nitse suke yace "ina unty batool?" tare sukace "tana ɗaki" ya mikawa Azad ledan yace "kai mata" da sauri ya tashi ya karɓa, ɗaki ya shiga yayi freshup kafin ya fito yasa kaya mara nauyi ya ɗau laptop ya fito, Azad ya kai sakon harma ya dawo domin kallon film ɗin da yake so akeyi, zamanshi keda wuya suka jiyo sautin tafiyan babban yaya, kallon juna sukayi, yazo ya zauna a ɗaya daga cikin sofan ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yasa glasses kafin ya fara duba laptop ɗin, tsit suka zauna ko tari babu me yi a cikinsu suna kallon ma basa gane me akeyi a tv, kallonsu yayi ɗaya bayan ɗaya kafin ya kara cigaba da aikinshi, azad ne ya tashi a hankali yace "bari naje na duba abu" gyaran murya muneeb yayi yace "dawo" dawowa yayi, yace "zauna babu inda zakaje" yana magana ne kamar zaki, a hankali ya zauna, sameer yana kunshe dariya a ɓoye, azad ya ɓata rai, unty batool wacce take zaune akan gado, kamar ta san meke faruwa a kasa, ta tashi tasa karamin hijabi akan riga da wandon jikinta, wayarta a hanu ta fito tana dudduba wayan, zama tayi a kusa da Azad ta kalleshi tace "baby Azad kana lafiya?" a ranshi yace "ina lafiya wannan mugun na nan" a fili kuma yace "kaina ke ɗan ciwo Inaso nasha magani" da sauri tace "ciwon kai? yaushe? meyasa bakasha magani ba?" yayi shiru, ta kalli muneeb da yake kallo tace "tashi kaje kasha magani" wuf ya tashi yana kallon sameer, da sauri ya nufi sama ɗakinsu ya shige ya ɗau wayarshi ya fara duba chart da akayi a group nasu, kanshi ya ɗaura akan pillow ya ɗau sweet nashi yana sha, batool tace "muneeb inaso muyi magana kuma so nake ka bani duk hankalinka" aje laptop yayi ya juyo yana kallonta yace "i..ina jinki" tace "muneeb ya kamata kayi aure, lokaci yana kurewa muneeb, bai kamata muyi ta zama haka a gidannan babu ci gaba ba, ya kamata ace kayi aure ka haifi ƴaƴa muma mu kara yawa a family ɗinmu, ka san dai ni bazan iya aure ba muneeb banida isashen lafiya nan gaba kaɗan zan nemi taimako sabida jikina ba sauki nake samu ba kara ciwo nake ji, ya kamata ka samu mace me hankali wacce zata kula da kai, idan nayi sa'a ka samu me hankali nima zata kula dani da sauran kannenmu amma baka tunanin aure ma muneeb baka damu ba naga bakada niya, iyeyenmu nasa raye kaine yanzu babanmu kaine zamu bawa darajan mahaifi duk da na girmeka amma wannan kannenka ne muneeb kayi aure" ta karashe maganan tana kuka, ido ya zuba mata tunda ta fara maganan har ta gama bai ɗauke ido ba, tace "ina tausayinsu sameer musamman Azad banaso ya rasa kulawa" shifa ba wai auren ne ba zaiyi ba, raini ne bayaso kana auren mace zata fara rainaka shi kuma shine abinda baya so, ga mata dayawa suna kawo mishi hari ɗauke kai yake daga kansu sabida bai shirya karɓan raini ba, ganin tana kuka yace "to...me....abin kuka?" tace "dole nayi kuka muneeb baka san me yake damuna a rai ba" yace "na..naji...zanyi auren" tace "muneeb yaushe zaka yi? kaida ko budurwa baka yi baka kula mata, anan nana makociyarmu ta fara nuna tana sanka amma ka rinƙa yiwa yarinya shariya ko kallo bata isheka ba gashi har tayi aure" tashi yayi yana hamma yazo ya share mata hawayen yayi mata peck a forehead yace "ki...ki...daina kuka bakida lafiya...idan lokaci yayi zanyi auren" zatayi magana ya rufe mata baki yace "shiiii ya isa" maganinta ya ɗauko ya ɗau goran ruwa yazo ya durkusa a gabanta yace "take" karɓa tayi tasha ya rike hanunta yace "oya time for sleep" kashe tv yayi su sameer da suke zaune kamar akan kaya suka tashi da sauri suka tafi, hanunta ya rike har zuwa ɗakinta, kallonshi take duk yadda taso tayi magana ya hanata, cire mata karamin hijabin yayi yace "sleep" kwanciya tayi ya rufata da blanket yace "g...good night" kashe mata wuta yayi ya fita, ɗakinshi yaje kasancewar ya gaji bai amsa kiran da azeez yake mishi ba ya kashe wayan ya kwanta, idan yana son hutawa baya barin waya a buɗe kuma baya sa komai a ranshi cire komai yake ya kwanta. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *NI DA MUNEEB* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 10* ~Cikin bacci najwah sai zufa take tana girgiza kai, damƙe bedsheet ɗin tayi da mugun karfi a firgice ta tashi tace "A,aaaaaaaa" inna tace "subhanallah" jin ihun da najwah tayi yasa ta tashi daga baccin da take, kallon najwah wacce ta dafa kirji sai zufa take, tace "menene?" tana share zufa tace "inna wani mummunan mafarki nayi, inna wasu yara kanana na gani suna kuka a ɗauresu sannan aka rufesu a wani ɗaki me tsananin duhu, sai kuma wani mutum tsaye da baƙin kaya ya rufe fuskanshi da facemask suna rokanshi ya fitar dasu a wajen inna yana tsaye yana kallonsu yana dariya, sai Adda meerah tace naje ta ceci yaran kada na bari ya cutar dasu tana kuka take cewa najwah kije ki taimakesu na san zaki iya najwah" inna tayi shiru ganin hankalin najwan a mugun tashe yake tace "Allah sarki watakila kinsa satan yara da ake a garinnan ne a ranki tunda kullum ina faɗa miki naji a rediyo" ta girgiza kai tace "inna ban taɓa sawa a raina ba" habib dake bacci yace "mama zansha ruwa" kasa tashi tayi ta ɗibo mishi ruwan tsaban tsoron da mafarkin ya bata, inna ce ta ɗibo mishi ruwan bayan yasha ta bawa najwah tace "kisha ruwa" karɓa tayi ta shanye tas kafin tace "na gode" zama tayi ta kasa komawa baccin inna tace "kiyi addu'a ki kwanta insha Allah ba zaki kara mummunan mafarkin ba" tana toshe kunne tace "inna kukan yara nake ji a kunnuwana" inna tace "najwa mafarki fa ba gaskiya bane ki kwanta kiyi bacci" tace "wallahi inna kukan yara nake ji" inna addu'a ta fara mata tana tofa mata har ta samu nutsuwa ta kwanta saide bacci yaki ɗaukanta haka ta kwana ido biyu, har gari ya waye bata runtsa ba, abincin karyawa tayi musu sannan ta tashi habib tace yayi salla sallan yayi tayi mishi wanka ta shiryashi cikin uniform, yace "mama meyasa idonki a kumbure? kuka kiyayi?" tana mamakin habib wani lokaci idan yayi tambaya kamar ba yaro ba, tace "kukan me zanyi habibi tunda kana tare dani?" yayi murmushi yace "yawwa mama batayi kuka ba" tana gama shiryashi tasa kaya itama ta fito suka yiwa inna sallama, har kofan school ta ajeshi kafin suka tafi, yau tazo da wuri, suna ganinta me gadi yace "kyakkyawa kin karaso yau da wuri" murmushi tayi tace "eh baba sabida yau na kai habibi makaranta da wuri ne" yace "Allah sarki" shiga ciki tayi, tana zama babu jimawa motocin muneeb suka shigo, sai yau ta ganshi tunda ta fara saida nono anan bata taɓa ganinshi ba, yadda yake tafiya kamar bayason taka kasa yasa taji bata sanshi, ga wani botsarewa da yake yana shan kamshi sai taji ya kara bata haushi, bata kara tsananshi ba saida taga yana bin kowa da kallon raini da isa, duk yadda suke durkusawa suna gaisheshi bai amsa na ko mutum ɗaya ba, ɗauke kai tayi lokacin da zasu haɗa ido, saida ya juyo kafin tabi bayanshi da kallo, gwada tafiyanshi tayi yadda yake bubbuɗa hanu tace "takama kamar karuna ko dan yanada kyau da kuɗi ne yasa yake wannan cika yana batsewan, tsaki taja taci gaba da abinda yake gabanta, jim kaɗan akazo karɓan nashi zuma mishi tayi ta dama da ludayin dama sannan ta zuba madara akai kamar yadda ta saba, mika mishi tayi tace "gashi" karɓa yayi ya kai mishi ya dawo da daidai kuɗinta ya bata, karɓa tayi har ta gama siyarwa bata burin ta kara ganinshi, makarantan su habibi taje ta ɗaukeshi, yau da suka koma gida ta shiryashi itama ta shirya cikin riga da skirt me kyau, kwalli tasa tayi masifan kyau tasa mayafi green irin kayan, takalmi tasa flat wanda ta siya a kasuwa ta riko hanun habib da yayi kyau jikin jinx na yara da riga red an rubuta MY HOPE a jikin rigan, ta kalli inna dake daka tace "inna bara na kaishi yau yasha ice cream ɗinnan da kullum yake damuna da sunanshi" tace "to najwah Allah ya tsare hanya" tace "ameen" farin ciki ƙarara a fuskan habib jin an kira ice cream, inna tace "ka dawomin da nawa fa megida" yace "to inna amma guda rabi zan kawo miki" tace "ni dai ka kawomin" zasu fita inna tace "najwah" tsayawa tayi bata juyo ba sai tura baki take, tasan zata fara wannan nasihan nata ne, tace "banda faɗa, najwa ki zama me hakuri banda faɗa najwa" tace "to inna naji" fita sukayi suna tafiya a hankali tana bashi labarin kogi, yace "to mama addanki bata zuwa ne ita?" tace "tana zuwa amma bata fiye zuwa ba sabida ana yawan faɗa acan, kuma ita bata son faɗa kamar kai take" yace "Ayya da na santa da tare zan kaiku makka" tace "addu'a zakayi mata kace Allah yaji kanta yayi mata rahama" yace "Allah yaji kanta yayi mata rahama" tace "ameen" mashin suka shiga aka kaisu wajen shan ice cream, sai kallon mutanen wajen take kowa da yaranshi wajen abin ban sha'awa, murmushi take tana tunani inama ace adda meerah tana raye da tare zasu zo nan, ice cream ta siya musu da habibi suka zauna suna sha, yace zai hau lilo ta ɗaurashi tana turashi, yara suna ball yace zaije suyi tana tsaye tana kallonshi yaje suna ball da yaran, murmushi take ganin habibi yana farin ciki sai taji babu abinda take kara nema a wannan duniyan, wurga ball ɗin yayi sama faɗawa ball ɗin yayi a jikin wani dake zuwa, waro ido tayi a tsorace ganin ball ya taɓa mutum, saukewa yayi yana kallonsu cikin sakin fuska ya karaso ya durkusa ya bawa habib dake tsorace yana binshi da kallo, yace "habibi ka iya ball ne?" a hankali yace "inayi a school" yace "good boy, waya kawoka nan?" nuna najwah dake tsaye ta harɗe hanu a kirji yayi, yace "mamana" murmushi tayi mishi ganin yaja hanun habib zuwa wajenta, yace "ina wuni maman habibi" tace "lafiya ƙalau yayan habibi" yayi dariya kaɗan jin sunan data kirashi yaji daɗi, yace "nima nazo siyawa kanina Azad ice cream sabida baida lafiya" tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya" yace "ameen" yana rike da hanun habib yaje ya siya ice cream ɗin dayawa ya kara siyawa habib, tace "amma ai yayi yawa" yace "karki damu nasan habibi na son ice cream" dariya tayi kaɗan tace "gaskiya mun gode yana so sosai" fita sukayi tare suna hira habib na tsakiyansu hanunshi rike dana sameer, yace "ku shiga mana na kaiku gida tunda ba sauri nake ba" tace "a,a karka damu zamu shiga mashin" duk yadda yayi da ita taki yadda yace "to shikenan bara mu tari mashin ɗin tare" tace "kar dai mu gajiyar da kai" yace "babu komai wallahi" saida ya tarar musu mashin ya biya kuɗin kafin ya karawa habib taso taki saida ya ɓata rai kafin tace habibi ya karɓa, idan ba itace tace ya karɓa ba baya karɓan kyauta a hanun kowa, tayi mishi godiya kafin suka tafi, shiga motarshi yayi yaga miss calls ɗin jabeer, kira yayi jabeer yace "dan Allah kayi sauri wannan Azad ɗin wallahi ya fiye shagwaɓa wai kuka yake idan baisha ice cream ba zai mutu" tsaki yaja yace "bashi wayan" bashi yayi cikin murya kaɗan yace "ya sameer zan mutu bansha ice cream ɗin ba" cikin masifa yake so yayi magana sai kuma yace "ba zaka mutu ba Azad yanzu zan kawo maka ka rinƙa daure rashin lafiya kaji?" yace "to yaya" katse wayan yayi yace "Azad Allah ya shiryeka" yaja motan ya tafi, yana zuwa ya bawa Azad da yake zaune ya rike pillow ya zama kalan tausayi dan dama shi haka yake idan baida lafiya. unty batool tayi mishi alaman yazo sunada magana, saida ta tafi ya bita, ɗakinta ya shiga tana zaune akan sofa yace "gani unty batool" ta nuna mishi gefenta tace "zauna" zama yayi tayi shiru shima yayi shiru, sun jima a haka kafin tace "sameer ya kamata mu gano wani abin zuwa yanzu sameer ban yadda da muneeb....." yace "dakata dan Allah unty batool" tashi yayi ya tsaya ranshi a ɓace yace "ko sau ɗaya, ko sau ɗaya ba zakiyi tunanin meyasa Allah bai nuna mana komai akan ya muneeb ba? unty batool ya muneeb is innocent baya aikata komai mara kyau, haka Allah ya halicceshi baida son dariya kuma baya shiga harkan mutane hakan ba zaisa mu rinƙa zarginshi ba, mun jima muna zarginshi amma har yau mun kasa gano abu koda ɗaya ne wanda ya aikata mara kyau, meyasa ba zamu hakura ba? can't you trust your brother koda sau ɗaya ne? tunda fa iyayenmu suka mutu shi yake kula damu, duk da baya sake mana fuska muna matukar tsoronshi amma babu abinda baya mana, matukar ya gane muna son abu shi yake zuwa ya siya mana da kanshi, kin kula damu kamar mahaifiya shi kuma ya kula damu kamar mahaifi, haramun mu rinƙa zarginshi, ba zai taɓa yafe mana ba idan yasa muna bibiyanshi sabida muga ko yana aikata wani abu a ɓoye ba zaiji daɗi ba, zai shiga tsananin damu zai fara tunanin mu na kusa dashi muna zarginshi ina ga mutanen nesa?" tunda ya fara magana take kallonshi har ya gama, a hankali tace "sameer...." hanu biyu ya haɗa yace "dan Allah unty batool mu rufe wannan maganan anan, daga yau idan maganan zargin babban yaya zaki min dan girman Allah kada ki sake kirana, ni bazan iya zama ina zarginshi ba" tace "sameer nima na fara wannan tunanin wallahi nima kunya nake ji ace wai nice nake zargin kanina da aikata ba daidai ba, nima banason hakan yanzu sameer" yace "da hakan yafi unty batool" tace "to ka saki fuska mana" sakin fuska yayi tace "mu koma falo" tafiya sukayi kamar babu maganan da sukayi, jabeer yace Azad fa lafiyansa lau banda ciye ciye babu abinda yake yi" cikin kakkausan muryanshi ya shigo sanye da bakin suit, yayi masifan kyau kamar balarabe yace "wa...wawwaye ba lafiya?" Azad yace "nine" da sauri yace "kaga Dr?" yace "no yaya yanzu na samu lafiya...." kafin ya karasa ya ciro waya ya kira dr mansoor, yace yazo akwai mara lafiya, rarraba ido Azad ya fara domin harga Allah ya warke rigima ne kawai da rashin son zuwa school da babban yaya yace zai fara, jabeer yace "yawwa idan akayi maka allura zaka warke" kamar zaiyi fitsari a wando jin allura, jabeer juyar da kai yayi yana dariya kamar zai mutu, har dr mansoor ya shigo ya fara dubashi allura ya ciro tana hawaye yace "wallahi

Chapter 8 of 11