halin na faɗa da kowa.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 5*
~Har dare suna zaune shiru ba karamin haushi sukaji ba da babban yaya ya ɓata wannan cake da shagalin, batool wacce take karfin hali sabida ba lafiyane da ita ba, tace musu "kunga muneeb ba wanda zaku rinƙa yiwa gwaninta bane, shi mutum ne wanda yake a juye ba zaku taɓa gane inane alkiblanshi ba, kada ku kara mishi surprise"
sameer yace "amma ai shi yana mana"
tace "dashi daku ba daya ba, kunfi kowa sanin halin yayanku"
shiru sukayi Azad banda tsaki ba abinda yake yi, jabeer tsaban haushi ya kasa cewa komai, kawai yace "ni zan tafi school ba zan tsaya haushi ya kasheni ba"
shiga ɗaki yayi ya ɗauko katon jakanshi na baya ya rataya ya rike laptop ya kalli sameer da yake kallonshi yace "zaka je ne ko na tafi?"
tashi yayi yace "bara na ɗauko jakata nima"
ɗauka yayi ya fito yana jan zip ɗin, sukace "Azad ka kula da unty batool sai dare zamu dawo"
yace "sai kun dawo"
fita sukayi suka shiga zazzafar motarsu driver ya jasu da guards suka bi bayansu, tsaki jabeer yaja yace "wallahi babban yaya mugun ɗan iska ne"
sameer yace "ai yafi karfin ɗan iska ma saide ɗan guguwa"
dariya jabeer yayi, wayanshi ne yayi kara da sauri ya duba yaga babban yaya ɗauka yayi jikinshi na rawa yace "hello"
cikin rashin fara'a yace "nono zaku siyamin na fridge ɗina ya kare banda me...me..tsami"
yace "to babban yaya"
kallon sameer yayi yace "mu juya mu tafi kasuwa"
yace "me kuma?"
"wai nono yake so nashi ya kare"
da sauri suka cewa driver ya juya zuwa kasuwa, a inda suka saba siya mishi suka siyo babu tsami ko kaɗan, ansa musu a babban leda sameer yana rike dashi jabeer kuma yana rike da wayarshi, sameer yana juyawa yayi karo da mutum, najwa wacce nonon yake kanta faɗuwa yayi ya wanke mata fuska da jikinta, waro ido sameer yayi ya tsaya yana kallonta, wani irin huci take yi tana kallonshi da dara daran idanunta, ya kasa magana ita kuma tana tafasa jin baice mata ko sannu ba saima kallonta da yake, cikin masifa tace "bakaga abinda kamin ba?"
yace "sorry"
wani tukukin bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya jin da turanci ma yake mata magana, ta ɗau nonon dake gefenta batasan ko na waye ba ta watsa mishi shima jikinshi ya ɓaci, waro ido jabeer yayi da sauri yazo yace "ke bakida hankali ne? zaki watsa mishi nono?"
tace "shi hankalin ne dashi daya bige nawa?"
hayaniya suka fara guards nasu sukazo da sauri, ɗaya ya daka mata tsawa itama a fitsare ta juya zata mayar mishi taga bindiga a hanunshi, tsit tayi bata kara cewa komai ba sai rawan da jikinta yake yi, da sauri ta kalli sameer tace "dan Allah kayi hakuri kace ya ɗauke wannan bindigan daga kaina"
sameer yayi mishi alaman ya ɗauke, ɗaukewa yayi kawai ya ɗauki na ledan yaja hanun jabeer suka tafi, ajiyan zuciya ta sauke ganin sun tafi tace "wayyo najwah yau da an harbeki ya inna zatayi? Allah ne ya yiki da nisan kwana"
juyawa tayi zata tafi da sabida babu nonon da zata siyar, baya tayi zatayi ihu ganin sameer tsaye yana kallonta, hanu yasa a aljihu ya ciro kuɗi sabbi dal ya bata, kallonshi take da mamaki, tace "na me?"
yace "na wanda nayi miki asaranshi, kiyi hakuri bada sanina bane"
jikinta yayi sanyi, tace "karka damu idan nono ne muna dashi dayawa duk ruganmu babu wanda ya kai babana yawan shanu, ko sau goma zaka ɓarar zan tatso wanda ya fishi"
murmushi yayi yace "kiyi hakuri ki karɓa sabida nasa mun dawo ne domin na baki"
tace "karka damu, inna idan taga wannan kuɗin zata ce aina na samu, kuɗin sun min yawa gaskiya dama dubu ɗaya ce zan karɓa"
yace "dan Allah ki karɓa"
karɓa tayi ta cire dubu ɗaya kawai sannan tasa mishi a aljihu tace "na gode"
barinshi tayi a wajen ta tafi, binta yayi da kallo har ta shiga mashin ta tafi.
jabeer daya jima da zuwa yace "sai muje ai tunda ta tafi"
binshi yayi suka koma mota suka tafi.
zaune yake akan sofa me alfarma dake cikin gidanshi wanda gidan yake na sirri ne, babu wanda ya sanshi da gidan sai shi sai azeez da guards nashi, sai kuma wanda idan an kawo gidan, saide da zaran ka shiga gidan fitanka da rai saide idan Allah ne ya yika da tsananin nisan kwana, gida ɗaya ne tal a cikin daji, ga masu tsaron gidan da mugayen makamai, bindigun dake hanunsu ko manyan sojoji basa rikewa, duk wani abin more rayuwa akwaishi a gidan, saide wannan gidan sunanshi gidan mutuwa, duk wasu yara da za'a sace a garin tofa dasa hanun muneer, wani lokaci da kanshi yake zuwa yayi satan, kallon laptop ɗin yayi yana sanye da kayan shan iska, farin riga ne ya buɗe boturan rigan kirjinshi me ɗauke da kwantaccen gashi a waje, gajeren wando ne fari mara nauyi a jikinshi ya ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya wannan shine zaman daya saba a koda yaushe, crossing leg yake yi, laptop ya zubawa ido yana kallon jaridan daya buga da kanshi na sace yara hamsin da akayi a cikin kwana uku, a hankali ya taɓa wajen share yayi sharing ta yadda duk duniya zasu gani, muneeb yanada tarin mabiya a shafukanshi na sada zumunta, harkan magani yake hakan yasa ya zama babban dealer ɗin magani wanda yayi kaurin suna a ko ina, mutane suna bibiyanshi a social media sabida yadda yake ɗaukan mutane aiki, murmushin gefen baki yayi lokacin da yaga labarin ya fara watsuwa a duniya, kanshi ya jingina da jikin sofan yana kallon yadda ake share na labarin daya posting a second ɗaya, wine ɗin dake cikin glass cup na gabanshi ya ɗauka yayi sipping kaɗan ya mayar, knocking akayi yace "yes"
azeez ne ya shigo yace "boss an samo yara goma"
murmushi yayi yace "a cire duk kayansu a kona a basu uniform susa sannan a tabbatar an rufe fuskansu da baƙin kyalle ta yadda ba zasu gane inda aka kawosu ba koda sun gudu"
yace "okay boss"
tashi yayi zai tafi
yace "az....azeez"
yace "yes boss"
tashi yayi daga zaunen yazo gabanshi yace "ka..ka...kasan haɗarin aikinmu, abi a hankali"
yace "na sani boss"
waya ya ɗauka ya kira numbern da yayi saving da Alhaji sahabi, karawa yayi a kunne yace "ha...ha...hallo, an samu....yara... guda...goma sabbi"
shiru yayi sai kuma yace "da...da...safe a zubar da gawansu cikin gari"
katse wayan yayi yace "duk waɗanda...aka...kai.ba.a dace ba, dole a kai wasu....da safe....jirginsu zai tashi a basu uniform....su...zama cikin shiri"
yace "okay boss"
fita yayi yaja yaran da suke ɗaure da bakin kyalle a ido suna kuka da ihu, bindiga ya ciro yayi harbi yace "idan bakuyi shiru ba zan kasheku da wannan bindigan"
shiru sukayi ya shiga dasu ɗakin da wasu suke kwance a ciki, ya cire musu kyallen sannan ya kira matan dake aiki yasa suka canja musu kaya daga nan aka ɗauresu a wajen fita yayi bayan yace a basu abinci.
yana zaune yana kallon duk abinda yake faruwa a ɗakin, kwanciya yayi akan sofan ya lumshe ido, a hankali bacci ya ɗaukeshi bai farka ba sai azahar, shiga ciki yayi yayi wanka sannan yasa kayan daya cire ya fito yana waya, da hanu yawa security's alaman zasu tafi, mota aka buɗe mishi ya shiga, da kanshi zaiyi driving hakan yasa shi kaɗai ne a motar, fita sukayi suna binshi a baya da zasu motar, company ya nufa domin yanada baƙi, an shirya musu zama, yana zuwa kawai ya wuce inda zasuyi zaman, a high table ya zauna sannan ya fara musu bayanin yadda samun maganin ciwon hanta da za'a fara aiki dashi zai kasance, sun fahimta domin shi ɗin kwararre ne yanada ilimi sosai yasan kuma duk abinda zaiyi domin ya amfanar da marasa lafiya da maganin daya kawo, sun gama zama lafiya ya tashi ya koma office domin duba meke tafiya a cikin company, yana tsaka da dube dube a laptop yaga komai normal, knocking akayi yace "yes"
shigowa akayi me kawo mishi coffee ne sanye da uniform amma babban mutum ne, da cup ɗin a hanunshi ya durkusa yace "yallaɓai ga coffee"
kallonshi yayi kallon daya saba da raini da rashin sanin darajan kowa da kuma wulakanci, ya karɓi coffee ɗin ya kai baki, wani irin zafi ne ya ziyarci bakinshi da sauri ya zubar dana bakinshi, cikin tsoro mutumin yace "yallaɓai kayi hakuri wallahi....."
watsa mishi yayi a fuska, cikin jin raɗaɗi ya fara goge fuskanshi ya nuna mishi hanyan waje yace "f..f...fita"
tashi yayi yana jin azaban zafi a fuskanshi yaje wajen ruwa yana wanke fuskan, har fuskan ya ɗaye, yana kuka sosai wata daga cikin masu aikin tazo tace "baba meya sameka?"
yace "yallaɓai ne ya watsamin coffee a fuska"
rufe ido tayi ganin fuskan ya ɗaye tace "Innalillahi sannu baba gaskiya yallaɓai baida imani Allah ya saka maka"
yace "ameen".
muneeb cigaba yayi da abinda yake gabanshi, waya ya kira yace a tara duk masu aikin su jirashi a hall na meeting, cikin mintuna kaɗan suka hallara gaba ɗaya masu aikin, kowa ya zauna a kujerun da aka tanada domin meeting, sun surutu tsakaninsu kowa yana addu'a Allah yasa ba laifi sukayi ba, cikin tafiyan isa da izza, babu alaman fara'a ko kaɗan ya shigo, tsit sukayi babu wanda ya kara ko numfashi me nauyi bale tari, tsayawa yayi ya goya hanu a baya yana binsu da kallo, da kakkausan muryanshi yace "waye cleaner?"
da sauri cleaner tace "gani yallaɓai"
yace "i....i...ina ɗayar?"
tace "batada lafiya bata zoba"
yace "na..na..koreta a aiki ke kuma kizo nan"
gabanta yana faɗuwa tazo ta ɗan durkusa tace "gani yallaɓai"
ya nuna mata waje da hanunshi yace "ɗa..ɗa..ɗauko wancan roban"
fita tayi da sauri taje waje can da nisa ta ɗauko roban da suke mopping dashi, tazo dashi tace "gashi nan yallaɓai"
ya karɓa yace "da..dama ba ɓaci roban yayi ba yau kika kasa mopping...me kyau?"
jikinta yana rawa tace "am sorry yallaɓai"
hanu ya zuba a aljihu yace "jeki saman... stair"
waro ido tayi zatayi magana yace "jeki...mana"
da sauri ta fita taje saman stir ta tsaya, yace "diro"
ba ita kaɗai ba har sauran mutanen saida cikinsu ya ɗuri ruwa, duk idanunsu a waje ganin yadda yayi maganan ba wasa, kuka ta fara tace "na tuba yallaɓai wallahi ba zan kara ba na tuba"
yace "i..idan..baki diro ba na koreki"
tace "ina tareda kannena marayu da wannan aikin nake kula dasu, idan na bar wannan aikin ban san yadda zanyi dasu ba"
yace "ina ruwana?"
tana kuka tace "yallaɓai na tuba"
tsaki yaja ya kalli sauran mutanen yace "daga..yau..duk wanda bai aikinshi daidai ya bar aikin anan"
tafiya yayi ya barsu, hamdala tayi tana godewa Allah.
bacci yayi sosai a cikin office baima san lokaci yaja har anyi sallan Isha ba, kallon agogo yayi yana yamutsa fuska, da sauri ya tashi ya shiga yayi alwala yayi salla sannan ya fito ya rufe office ɗin, duk masu aikin suna nan, domin idan bai tashi ba babu wanda ya isa ya tafi, duk jimawan da sukayi babu wanda ya isa ya shigo haka suka hakura suna zaune koda kwana zaiyi to saide suma su kwana wannan dokan muneeb ne, suna ganinshi sukayi hamdala bai kulasu ba ya wuce wajen mota domin tafiya gida, suna ganin ya tafi suka tashi kowa ya kama hanyan tafiya, yana zuwa gida ya kalli falo yaga babu kowa, kallon dinning yayi yaga sunci abinci, zama yayi yaci abinci shima sosai kafin ya tashi, har zai wuce ɗakinsu sai kuma ya dawo da baya, ji yayi suna hira Azad na basu labari, buɗe kofan yayi ya shiga, kowa ya kwanta suka rufe ido kamar masu bacci, murmushi yayi ya maida kofan rufe, tafiya ɗakinshi yayi, azad ne ya buɗe ido yace "ya tafi"
duk suka tashi kowa yaci gaba da hiranshi, batool tana ɗaki tasha maganinta amma fa tana jin ciwon yana damunta sosai yau, ta daure sosai sabida batason ɗaga hankalin kannenta saide duk yadda taso ciwon yaci karfinta, numfashi take ja da kyar tana birgima, waya take kokarin ɗauka ta kasa, hawaye ta fara na azaba cikin ciwo tace "Azad? Azada? sameer? najeeb?"
birgima take, Azad dake kwance ya ɗaura kanshi a kafar sameer yana kallon laptop na sameer ɗin ya tashi da sauri yace "na manta ban duba unty batool ba, bara naje"
sauka yayi daga gadon, jallabiya ne me taushi a jikinshi, sameer yace "to na hanun daman unty batool baka minti biyu baka ganta ba sai kaji kamar akan kaya kake"
dariya yayi yace "eh mana ya sameer ai ni kalen hanjinta ne"
fita yayi ya shiga ɗakin da sallama, kunna wutan yayi yace "unty batool banzo na dubaki...."
da gudu ya karasa ya riketa domin saura kiris ta zube a gadon, wani irin ihu yayi ya kira sunan najeeb da sameer, bubbugata yake ganin ta suma ya fara kuka yana kiran sunanta, muneeb dake shirin kwanciya bacci yaji ihun azad, babu takalmi ya fita da gudu, ɗakin batool ya nufa ganin su sameer sun shiga, bai tsaya wata wata ba ya ɗauketa cak, yace "ki buɗe ido"
bai kula da wandon jikinshi gajere da armless ba ya fita babu ko takalmi tana rungume a kirjinshi, a mota ya sata sannan suma suka shiga, da gudu ya fita da ita, guards suka shiga motarsu suka rufa musu baya, kamar kullum tsaida komai na asibitin akayi domin kula da batool makawa wacce aka buɗe asibitin sabida ita, emergency aka shiga da ita, atake masu tsaronsu suka zagaye asibitin babu me shiga babu me fita.
safa da marwa yake yana kallon kofar ɗakin, su Azad suna gefe suna addu'a, har Dr ya fito muneeb yace "ya jikin?"
girgiza kai yayi yace "babu komai karka damu zata samu sauki"
shiru sukayi, har dr ya tafi babu wanda ya kara magana.
*Jiddah Ce...✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 6*
~Najwah ce zaune a kusada Adda meerah, cikine babba a jikin adda meerah haihuwa yau ko gobe, yanzu najwah ta daina zuwa tallan nono saboda kula da adda meerah wacce bata samun kulawa sam sam a wajen kannen mijin da surukarta, ɗaure take da guntun zani ta ɗaura ɗankwali siriri, gashinta da kullum yake a kitse guda biyu ya sauka har bayanta, wuta take hurawa hayaki ya dameta sosai sai tsaki take ja kamar tayi kuka, Ameerah dake zaune akan kujera tana kallonta tace "boɗɗi kibar wannan wutan kawai idan zai dameki"
tace "a,a Adda ya zama dole ne na hura dan banso ki rinƙa shan ruwan sanyi zai saki mura"
murmushi tayi tace "to boɗɗi na gode, gani nayi wai hayaki yana damar min ke"
tace "ba komai"
da kyar wutan ya kama ta girka tukunyar ruwa kafin ta fara share cikin gidan, kallonta kawai Ameerah take, a hankali ta juyo domin zubar da shara ido suka haɗa, Ameerah tayi murmushi, tace "adda wai meyasa kike yawan kallona ne a kwanannan?"
tace "ba komai najwah kawai bana miki fatan kiyi aure a wannan rugan, ina miki fatan ki samu miji me hankali me kuɗi wanda ba zai wulakantaki ba, Inaso kiyi karatu ki zama wani abu a rayuwa, kar kiyi aure ki karashe rayuwarki cikin wahala irin wanda nake ciki yanzu"
murmushi tayi tace "adda kenan"
daga nan bata kara cewa komai ba, amma can kasan zuciyanta wani irin tausayin ameera take ji, da kuma haushin mazan kauyen da tsanansu ciki harda baba, har ruwan yayi zafi kafin ta ɗauko flask ta juye a ciki, shiga ɗakin tayi ta aje kana ta ɗauko cup ta zuba mata kaɗan ta kai mata, karɓa tayi tana sha Arɗo yayi sallama, ɗauke kai najwa tayi tana cigaba da aikin gabanta, kallonta yayi sai kuma ya kalli ameera yace "ina abincina?"
tace "yanzu najwa zata girka"
tsaki yaja yace "ni ba zanci abincin da zata girka ba sabida kece matata ke nakeso ki girka idan kuma kin barmin ita yau ta zama matata to saiki bamu ɗaki ki koma cikin gida"
najwah dake rike da tukunya batasan lokacin da tukunyan ya faɗi ba jin maganan banza da arɗo yake yi, bata kulashi ba kawai taje tasa takalminta ta gyara mayafinta tace "adda na tafi"
tafiya tayi har taje bakin kofa taji ihun adda, da gudu ta dawo dan ganin meke faruwa, gani tayi yana janta a kasa zuwa bakin murhu, rufe ido tayi tace "Arɗo ka saketa bakaga ciki a jikinta ba?"
cigaba da janta yayi tace "Arɗo ka saketa nace"
ganin ba zai saketa ba taje da gudu ta fara janshi, cikin zafin rai ya juyo zai mareta ta rike hanun gam, tace "wallahi idan ka kara taɓa adda meerah zanyi maka abinda ba zaka taɓa mantawa ba"
Ameerah tace "najwa ki tafi"
sakin hanunshi tayi kawai ta fita daga gidan, ranta yana suya, wani irin baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, batasan lokacin data fashe da kuka ba, har ta isa gida kuka take, a kofa ta tsaya ta share hawayenta sannan tayi sallama ta shiga, inna tana kan tabarma tayi tagumi sabida yanzu baba ya gama zagin iyayenta, tana ganin najwah tace "kin dawo? ya kika baro Addanki?"
a hankali ta zauna kusa da inna tace "tana lafiya"
kwanciya tayi akan tabarman ta ɗaura kanta akan kafar innan tace "inna bana farin cikin zaman adda ameera a gidan arɗo meyasa bakwa buɗe baki kuyi magana ku kwaci ƴancinku? nifa ko za'a kaaheni ba zanyi aure a wannan rugan ba"
shiru inna tayi itama bata fatan najwah tayi aure a wannan rugan, shiru sukayi kowa yana tunani a ranshi.
cikin dare Ameerah ta fara naƙuda duk yadda tayi arɗo ya kira mata mutane su taimaka mata yaki, tsaki ma yaja yace "sauran matan da suke haihuwa da kansu su kaɗai ba mutane bane?"
kuka take yi sosai tace "arɗo dan Allah ka kiramin innata ko najwah dan Allah kaji?"
pillow yaja ya kara gyara kwanciyarshi yana bacci, bayanta sarawa yake sosai ga wani irin azaban ishin ruwa da take ji, tana birgima a wajen tana cewa "cikina wayyo bayana, wayyo Allah zan mutu jama'a ku taimakeni, najwah? najwah? najwah?"
ta galabaita sosai kafin ta samu ta haihu batama san ko mace ko namiji ta haifa ba sabida tsananin duhun dake ɗakin Ita dai tana jin sautin kukan jariri sama sama domin bata san inda take ba.
najwah dake kwance akan gadon inna bacci take inna na gefenta itama tana bacci, a firgice ta tashi tace "Adda Ameerah?"
kallon cikin ɗakinsu dake ɗauke da duhu tayi, taɓa goshinta tayi taji zufa sosai ya wanke mata fuska, dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un adda meerah?"
inna dake bacci ta buɗe ido a hankali tana kallon najwah cikin duhun ɗakin, tashi tayi ta ɗauko fitila ta kunna nan take haske ya gauraye ɗakin, ganin najwah dafe da goshi cikin razana tazo da sauri ta riketa, rungumeta najwah tayi, inna tace "mummunan mafarki kikayi ko?"
tace "inna nayi mafarkin dada tazo ta ɗauki adda ameera sun tafi wani waje kuma basu kara dawowa ba"
Dada itace ta haifi inna kuma ta jima da rasuwa, inna gabanta yayi mummunan faɗuwa jikinta yana rawa tace "karki damu insha Allah babu abinda zai samu Ameerah"
tace "inna amma ance idan kayi mafarkin mamaci ya ɗauki wani to mutuwa za'ayi"
shiru inna tayi, da sauri najwah ta saketa, dira tayi daga kan gadon babu ko tsayawa neman mayafi tayi hanyan waje da fitilan a hanunta, inna tace "ina zaki najwah?"
tace "zanje gidan adda meerah"
tace "najwah karfe ukun dare fa ya kusa"
tace "inna bazan iya zama ba koda na zauna hankalina ba zai zauna ba"
buɗe kofan tayi tasa takalmi, tana jin baba yana cewa "waye? waye?"
bata kulashi ba ta fita daga gidan, cikin duhun daren take tafiya tanasa kafanta a duk inda fitila ya haska, da haka har ta isa gidan adda, da sallama ta shiga cikin sanɗa take tafiya, kowa yana bacci a wajen hakan yasa ta nufi ɗakinsu adda, a hankali ta tura kofan tasa kanta tana lekawa, da sauri ta haske fitila a inda take ganin mutum kwance, shiga ciki tayi, idanunta kamar zasu fito lokacin da taji ta taka mutum, hasakawa tayi taga adda meerah kwance a jariri yana gefenta shima a kwance, jikinta ne ya fara rawa kasa yin komai tayi, fitilan dake hanunta ya faɗi kasa, idanunta sun kara girma, da kyar ta daure ta durkusa kasa ta bubbuga ameerah a hankali tace "adda meerah? Adda meerah?"
jin shiru ta fara bubbugata da karfi tana cewa "Adda meerah? dan Allah ki tashi bamuyi haka dake ba, ki tashi bamuyi haka dake ba adda, kar kimin haka"
jaririn ne yayi kuka, ido ta kai kan jaririn jin yana tsala ihu ta ɗaukeshi cikin jinin ta rungumeshi, wani irin ihu tayi saida duk mutanen gidan suka tashi, kofan ɗakin suka zo domin ganin abinda ke faruwa, arɗo dake bacci ya tashi da sauri jin ihu yace "wani shegen ne yake mana ihu a tsakar dare haka?"
mamanshi rike take da fitila haskawa tayi taga Ameerah kwance cikin jini bata motsi ga najwah rungume da jariri yana ihu, salati suka fara, tace "meya sameta?"
kasa amsawa najwa tayi banda ihu babu abinda take yi sai kara kanƙame jaririn take, a cikin daren aka tara mutanen unguwa ciki harda inna wacce har rugansu akaje kiransu, tace "dan Allah kar ku cemin abinda najwah tayi mafarki ya faru, bamuyi haka da ameera ba dan Allah"
tana zuwa ta tarar da Ameerah kwance an rufeta da zani har fuskanta, ga najwa kanƙame da jariri ta zama kamar a zauce, shiru inna tayi tazo ta buɗe fuskan taga Ameerah ido rufe fuska ɗauke da murmushi, tace "Ameera haka mukayi dake? haka mukayi dake Ameerah zaki tafi ki barni? zaki tafi ki barni Ameera?"
kuka ta fashe dashi ta ɗaura kanta akan Ameerah tana kuka me cin rai, har gari yayi haske babu wanda ya runtsa arɗo sai rarraba ido yake mamanshi kuma tasa mayafi ta zauna daram a kasa.
inna da kanta ta yiwa Ameerah wanka aka shiryata domin kaita gidan gaskiya, najwah wurgi tayi da jaririn inna ce ta rikeshi lokacin da zai faɗi, rike Ameera tayi ta hanasu fita da ita, da kyar aka taru aka riketa suka fita da ita, silalewa tayi kasa ta faɗi a sume, ruwa aka ɗiba aka shafa mata a fuska, ba ita ta farka ba saida masu jana'iza suka dawo, tana zaune a wajen inna tayi shiru idonta akan jaririn da ba'a mishi wanka ba har yanzu, inna taki bata jaririn sabida a zatonta najwah ta samu taɓin hankali duba da yadda take bin mutane da kallo da yadda take yin abu kamar ba daidai take ba, arɗo ne ya shigo ya durkusa kasa mamanshi ce tace yaje ya gaishesu sabida kada ayi zarginshi, kamar da gaske ya fara kuka yace "inna ya hakuri?"
shiru inna tayi mishi, yace "najwah ya hakuri?"
shiru tayi tana kallonshi, yace "duk abinda ya faru Allah ne ya tsara...."
wani irin kukan kura da tayi ta damko riganta da iya karfin da Allah ya bata, cizo ta fara kai mishi daga nan ya fara kwatan kanshi, sakinshi tayi ta ɗauko katon kataton dake gefe ta rinƙa kwala mishi, mutanen dake wajen kowa ya tsorata suka fara ja baya sabida sunyi zaton mahaukaciya ce, inna ta kwantar da jariri a kasa tazo tana jan najwah, fizgan jikinta take tana kuka da hawaye tana dukanshi da katakon, kanwarshi dake zaune tace "ya isheki haka taya zaki rinƙa dukanshi shiya kasheta ne?"
juyo dara daran idanunta tayi, sun rikiɗe sun koma jajur, fuskanta ma ya koma jajur daga yellow, batasan lokacin data janyo kanwar tashi suka fara dambe ba, ranta yana tafasa ji take zata iya komai a yanzu, inna tana cewa "najwa kiyi hakuri ki bari, najwah ki kyalesu"
kin barinsu tayi katakon ta ɗaga zata maka mata jaririn ya fara kuka, ajewa tayi da sauri taje inda yake ta ɗaukeshi ta rungumeshi, kallon inna tayi tace "mu tafi"
da sauri inna ta ɗauko mata takalminta kin sawa tayi tsaban zafin zuciya kawai ta fita da yaron a rungume babu takalmi, duk cikinsu babu wanda ya iya hanata tafiya da jaririn suna tsoron yi mata magana ma, share hawaye tayi a hanya tana jin son yaron yana ratsa jiki da jininta, inna tayi shiru