Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
inda yake, hanunta ameera ta rike tace "duk abinda zakiyi ki tuna shi ya haifemu" cikin ɗacin rai da tsananin tsananshi tace "sabida shiya haifemu saimu bari ya kasheta?" fizge hanunta tayi taje da gudu ta rike kafanta, janyo inna tayi ta rungumeta, ganin haka ya zaro itacen dake gefenshi ya fara dukan inna, najwah rungumeta tayi itacen yana sauka a bayanta, tana runtse ido amma duk yadda za'ayi bata bari ya samu inna, ameera kuma ta rakuɓe a gefe cikin tsoronta tana kuka tana kallonsu har ya gaji ya wurgar da itacen ya ɗau ledan dake cike da tsire ya shiga ɗaki, a hankali najwah ta zame inna daga jikinta tayi shiru kawai ta tashi daga wajen, inna ta share hawaye cikin karfin hali tace "bari na gama muku abincin kunji?" juya baya najwah tayi tana share hawaye, a kullum sai inna tasha tsinannen duk a wajen baba, tun suna kanana har izuwa yanzu da suka girma bai daina dukanta ba, tasha wahala fiye da yadda ake tsammani, ya wulakantata kuma yana kan wulakantata sabida yaga batada iyaye, iyayenta sun rasu kuma batada tsayayyun ƴan uwa, a hankali suka zauna kan tabarman sukayi shiru inda sabo sun saba amma kullum abin yana damunsu, ameerah ganin najwa tayi shiru ta matso kusa da ita, tace "kawo na kwance miki kanki na kara miki sabon kitso wannan ya fara tsufa" shiru tayi har ta fara kwance mata kan, saida ta gama ta leƙo fuskanta tace "wani irin style kikeso?" babu dariya akan fuskanta tace "kowanne" jikin ameera a sanyaye ta fara mata kitson, bata son ganin najwa a wannan halin na rashin dariya, sabida a kullum najwa itace kawarta abokiyar hiranta, basa rabuwa ko wajen tallan nono watarana watarana ne najwa bata zuwa amma kullum suna tare. *Jiddah Ce....✍️* 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *NI DA MUNEEB* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 2* ~Suna zaune a asibiti babu wanda yayi bacci, duk suna ganin idan sun rufe ido zasu rasa yayarsu, gani suke zata mutu da zaran sun rufe idonsu, Azad ne ya fara gyangyaɗi domin baya jure wahala, kanshi ya ɗaura a kafaɗan jabeer ya rungumeshi zai fara bacci jabeer yace "kaga zaka fara ɗauramin nauyinka ko? zaka fara baccinka da baka tashi da wuri" hamma yayi yace "ya jabeer please" daga nan yaci gaba da baccin, ture kanshi jabeer yayi yace "ka matsa min, wannan cin da kake dashi shiyasa kake nauyi, jibi duk kafi kowa kiba anan" tsaki yaja ya kalli unty batool dake kallonsu tana lumshe ido tana murmushi tashi yayi yaje inda take yace "unty batool ki ɗan matsa na kwanta a gafenki" a hankali ta matsa mishi ya kwanta ya rungumeta, harara muneeb yake mishi amma ya rufe ido dan wallahi yana jin bacci, cikin mintuna kaɗan bacci ya ɗaukeshi, ido ta zuba mishi hawaye yana wanke mata fuska duk tafi jin tausayinshi shine karami duk da ya kai 20years amma tana tausayinshi sabida bai samu gatan mahaifiya ba, shafa kanshi tayi kana tayi mishi peck a goshi sannan ta juya itama ta rufe ido zata fara bacci, wayan dake aljihun jallabiyan muneeb ya fara ringing, da sauri ya ɗauka yana dubawa, tashi yayi ya fita suka bishi da kallo ciki harda unty batool data rufe ido, kallonta sameer yayi tayi mishi alama ya bishi, gyaɗa kai yayi sannan ya tashi cikin sanɗa yabi bayan muneeb, saida yayi nesa da kowa kafin ya amsa call ɗin, cikin kasa da murya ta yadda ba za'a jishi sosai ba yace "ka..ka...ka isa?" sai kuma yayi shiru yana saurara, yace "to..to...ka karka kuskura a samu matsala, idan.. idan...idan aka samu matsala kafi kowa sanin abinda...zaiii.faru" daga nan ya katse wayan ya juya yaga babu me kallonshi, sameer da sauri ya mannu da jikin bango har muneeb ya wuce ya koma ciki kafin shima ya fito, saida ya ɓata lokaci kafin ya koma ciki, kallonshi muneeb yayi kallon daga ina kake? kanshi kasa yace "naje dubaka ne" a fusace yace "ni yaro ne? zan..zan...ɓata ne?" girgiza kai yayi yace "sorry" tsaki yaja, duk sukayi shiru suna zaune har gari ya waye basu samu isasshen bacci ba, duk sukayi alwala a cikin masallacin asibitin sukayi salla, da Azad da sameer da jabeer tare suka shigo, ta tashi ta zauna tana ganinsu ta fara murmushi zama Azad yayi a gefenta ya rike hanunta yace "good morning unty batool" tace "ya kake, baby Azad?" yace "am fine ya jikin?" tace "da sauki baby Azad" sameer da yake hamma yace "good morning unty" tace "ya kake?" yace "fine" jabeer ma ya gaisheta, tana amsawa sukaji sallaman muneeb kasa kasa, amsawa sukayi da basketa a hanunshi da katon flask a ciki, ajewa yayi da flask na tea yace "ga breakfast" tun kafin suyi magana ya fita, Azad ne ya sauko ya janyo basket ɗin, plate ya jejjera a ciki guda huɗu ya cire sannan ya buɗe abincin, kamshi ne ya karaɗe ɗakin, jallof rice ne wanda yaji vegetables da pepper chicken, serving spoon ɗin ya ɗauko ya fara ya fara zubawa kowa, tashi yayi ya bawa sameer da jabeer nasu, shi kuma yasa nashi dana batool a plate ɗaya, bata ya fara a baki a hankali take ci badan tana jin daɗinshi ba sai dan bataso suga rashin samun saukinta, shima yana ci haka har suka gama, maida plate yayi a cikin basket ɗin, batool tace "ku kaini gida banason zaman asibiti" duk suka amsa da "to" riketa sukayi ba tareda sun tambayi Dr ba sabida dama basa zama a asibitin sosai, tana tsaye amma bata iya mikewa, tafiya take a hankali suka fita, security suna ganinsu suka buɗe musu mota shiga sukayi, suma duk masu gadinsu suka shiga motarsu tare suka fita daga hospital ɗin, hakan yasa asibitin ya zama free yanzu sabida family ɗin makawa sun tafi, koda suka isa gida ma riketa sameer da jabeer sukayi Azad kuma ya ɗauko basket ɗin yana binsu a baya, masu aiki suka zo da gudu cikin girmamawa suka karɓi basket ɗin daga hanunshi, a falo suka yada zango, ta kwanta akan sofa su kuma suka shiga ciki domin yin wanka, koda sukayi wanka fitowa sukayi Azad yayi kyau cikin gajeren wando da rigan armless, zama yayi ya kunna tv ya kamo tashan cartoon ya fara kallo, jabeer kuma ya kwanta shima sanye da kayan shan iska yana latsa waya, kallon sameer tayi sannan tayi mishi alaman yazo kusa da ita, tashi yayi ya koma kusa da ita, kasa da murya tayi tace "ya ake ciki?" yace "gaskiya ban gano komai ba har yanzu, sabida yayi nesa kafin yayi wayan banji komai ba, a ankare yake gaskiya" dafa goshi tayi tace "oh my god sameer tabbas akwai gagarumin abinda muneeb yake aikatawa kuma ina zargin ba abu me kyau bane, sameer aina muneeb yake samun waɗannan maƙudan kuɗin? iyayenmu masu kuɗi ne tun kafin su mutu to amma sameer munfi kowa sanin muneeb yanada kuɗin daya wuce misali kuma duk mun san ba'a wannan company yake samu ba, wallahi sameer na jima ina zargin muneeb anya ba tsa...." rufe bakinta yayi yace "dan girman Allah unty batool karki furta wannan kalman, zuciyata ba zata jure jin wannan kalman akan babban yaya ba, eh nima na yadda akwai abinda yake yi a ɓoye amma inada tabbacin ba wannan mummunan abin bane" ido ta zuba mishi na tsawon mintuna kafin tace "sameer ina tsoron wani abu yazo ya sameku bayan na mutu sameer ina tsoron muneeb wallahi ina tsoronshi" shiru yayi kanshi kasa yace "unty batool addu'a zamu dage dashi babu abinda zai...." turo kofan da akayi yasa yayi tsit bai kara ko tari ba, ita kuma batool ta rufe ido kamar me bacci, shigowa yayi fuska a murtuƙe sanye yake da farin shadda yayi bala'in kyau, ga wani kamshi da yake yi me daɗi, agogon rolex me tsadan ne ɗaure a hanunshi sannan yasa hula akan tulin gashinshi dake sheƙi kamar na mata, sajenshi a gyare idan ba magana yayi akaji harshenshi ba zaka rantse balarabe ne, idanunshi masu rikita mutum ya zubawa sameer sannan ya kalli Azad da jabeer wanda hankalinsu baya kanshi yayi gyaran murya, duk suka gyara zamansu suka nutsu, kallon batool yayi wacce ta buɗe ido yace "zan fita me zan kawo miki?" murmushi tayi mishi sannan tace "koma me zaka kawomin Indai na halak ne Inaso" ido ya zuba mata itama tasa idonta a nashi tana kallonshi, da sauri ya ɗauke kai kawai ya fita daga ɗakin, kallonta Azad yayi yace "unty batool meyasa kike yiwa babban yaya haka?" shiru tayi bata bashi amsa ba, da alama shima jabeer baiji daɗi ba kawai yaci gaba da pressing wayarshi, tsadadden motarshi g-wagon fari dal ya shiga sannan ya kalli bodyguards nashi kosassu masu murɗaɗɗen jiki irin na ƴa wrestling, sai kuma yaga security's ɗinshi wanda suke sanye da baƙaƙen coat da hanu yayi musu alaman su shiga mota akwai inda zasu je, shiga motan sukayi yana zaune a baya aka buɗe gate nasu na alfarma, convoy sukayi har suka hau titi saida kowane mota ya tsaya suka wuce, haka dama kullum idan sunyi convoy to babu motan da zai kara wucewa sai motocin gidan makawa sun gama wucewa, sunyi tafiya me nisa kamar zasu bar garin wani daji suka shiga banda bishiyoyi babu abinda suke wucewa har suka isa tsakiyan dajin wani gida ɗaya a tsakar dajin me tsananin masifan kyau suka tsaya a kofan, buɗe mishi kofa akayi ya fito fuska ba annuri ya kalli security dake zagaye dashi yayi musu alaman su zagaye kofan da yatsu biyu kawai yayi musu alaman, shiga ciki yayi yasa bakin glasses a idonshi sannan yasa facemask ta yadda babu me iya ganeshi, masu aikin gidan duk suna sanye da uniform kala ɗaya pink na yadi ne riga da wando, maza ne yawanci masu aikin sai mata kaɗan basu da yawa, kana ganin matan zaka san suna cikin baƙar wahala domin duk fuskansu yayi baƙi ƙirin ga datti da suke fama dashi, suna ganinshi suka far durkusawa kasa basa tashi har sai ya wucesu, wani ɗaki ya nufa wanda yake nesa da gidan, tun daga bakin kofa yake jiyo kukan wasu kananan yara, toshe kunne yayi jikinshi ya fara rawa, jingina yayi da jikin bango sannan ya rufe ido yana so yayi relax kafin ya ɗan samu nutsuwa shiga ciki yayi ya ciro makulli a aljihunshi sannan ya buɗe kofan ɗakin da aka rufe harda chain, shiga yayi ya goya hannayenshi a baya, subhanallahi ƙananan yara ne a wajen suna ɗaɗɗaure da chain a hannayensu, wasu suna kwance a gefe kamar basa da rai, yunwa da alama yana ɗawainiya dasu, ga wani irin wari da ɗakin yake yi, kallonsu yake ta cikin glasses ɗin, wani yaro da ba zai wuce 12years ba yana kwance cikin wahala bakinshi ya bushe yana kuka yace "yaya dan Allah ka fitar damu daga nan, yaya kayi hakuri idan laifi mukayi maka ka yafe mana" shiru yayi yana kallon yaron, sai kuma yayi murmushi ya ciro waya daga aljihu, cikin sanyin murya yace "ka..ka...kawo abinci" katse wayan yayi, babu jimawa akayi knocking buɗewa yayi da kanshi, wani matashi wanda yake sa'a dashi dan ba zai wuce 31years ba ya shigo da wasu mata suma da uniform a jikinsu, hanunsu rike da manya manyan kulolin abinci suka shigo dashi suka aje a gabanshi, yayi musu alama da hanu, jikinsu yana rawa suka fara sa abincin akan plate, bawa yaran suka fara sannan yace "ru...ruwa fa" jikin babban matar yana rawa ta tashi da sauri taje suka shigo da ruwan gora, fara bawa yaran sukayi kamar sunyi shekara basuci komai ba haka suke karɓan abincin wasu harda wanda ya zube a kasa suke ɗiba suna ci, saida ya tabbatar sun gama basu kafin ya juya zai tafi yaji an rike ƙafarshi, bai juyo ba kuma bai janye kafar ba, wata kyakkyawar yarinya ce fara sal tace "yaya nifa kaga banida lafiya kullum sai mamana ta bani magani amma yau kwana goma bansha ba kuma banje school ba, kuma abbana yace idan na girma zama doctor sabida nice kaɗai suka haifa, to yanzu ina nan yaya kenan ba zan kara ganin mamana da abbana ba?" janye ƙafarshi yayi bai kalleta ba ya fita daga wajen yana jinta tana cewa "yaya ka cewa mamana zan dawo na zama likita" shiru yayi ya kulle kofan yasa chain sannan ya kalli wanda ya kawo abincin yace "Azeez gobe za'a fita da kaya, wanda suke can an gama ka zama cikin shiri" yace "an gama boss" tafiya yayi ya fita daga gidan gaba ɗaya, shiga motarshi yayi sannan ya zauna, duk bodyguards ɗin suka shiga motar suka kara yin convoy suka tafi, wannan karon a cikin gari suka nufi wani katafaren waje me matukar kyau da ɗaukan ido, da alama wannan shine c.e.o ɗin company domin gateman yana ganinsu yayi gudun buɗe gate, fitowa yayi bayan ya cire facemask ɗin sannan yasa glasses ɗin ya fara tafiya, cikin isa da izza da nuna shi ɗin daga family ɗin makawa yake tafiya, masu aiki uniform nasu suit ne bakake da riga fari ta ciki, harda matan duka sanye suke da suit bakake, office nashi da yafi aljannan duniya kyau ya shiga, zama yayi akan tamfatsetsen kujeranshi, cire hulan yayi yana jin sanyin ac yana ratsa shi, kanshi ya ɗaga sama ya fara juyi da kujeran, knocking akayi bai amsa ba yana ji ana knocking saida yaga dama kafin yace "yes" ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya shigo cikin girmamawa yace "oga an tura kaya kasar paris yau sannan custom sunsa hanu kaya ya wuce" kallonshi yayi da tsumammun idanunshi kafin yace "ba..ba..babu custom daya...isa ya tare kayana" cikin girmamawa yace "hakane oga amma fa hankalinmu ya tashi sabida munsa koken a kasan kayan kuma tabbas zamu samu ƙazamin riba" murmushi yayi ai kuwa murmushi ya mishi kyau da ace yana yinshi a koda yaushe da yafi haka kyau, yace "good" tashi yayi yace "ga takaddun" nuna mishi inda zai aje yayi sannan ya cigaba da juyinshi akan kujeran, ajewa yayi ya fita, wayarshi ne ta fara ringing ya kalli sunan yaga baby Azad, amsawa yayi yace "ina...ina...jinka" ya faɗi hakane sabida shirun da yaji baby Azad ɗin yayi, ji yayi Azad ɗin yana magana kasa kasa yace "sameer kayi magana" sameer ɗin yace "A,a jabeer ne zaiyi magana" musu suke a tsakaninsu ya daka musu tsawan da yasa suka nutsu a take, Azad wanda su sameer suka gudu suka barshi rike da wayan kamar zaiyi kuka yace "dama babban yaya kuɗin hanunmu ne ya kare kuma munason zuwa shopping" tsaki yaja kana ya kashe wayan, transfer na kuɗi yayi musu a account ɗin Azad, ganin alart ya shigo na makudan kuɗi Azad ya waro manyan idanunshi yace "1 billion?" wani irin tsalle ya daka sannan ya fita da gudu ya sauka kasa, har sun dawo falo suna game sun ma manta sun barshi a masifa eh masifa mana babban yaya ai masifa ne, rungumesu yayi da karfi yace "babban yaya ya tura mana billion ɗaya" duk suka kalli alart ɗin, tsalle suka fara a ɗakin, batool data fito tana tafiya a hankali daga bacci ta tashi hakan yasa batada karfi ko kaɗan, dafe da bango ta karaso inda suke, Azad ne yazo da gudu ya rungumeta, ciza baki tayi cikin ciwo itama ta rungumeshi tace "baby Azad murnan me kuke?" yace "babban yaya ya turo mana 1 billion zamuje shopping" da mamaki ta kalli sameer shima kallonta yayi sai kuma tace "masha Allah sai kuyi mishi godiya" Azad cikin jin daɗi ya saketa yace "bari naje na shirya yanzu zamu tafi" jabeer ma yace "nima yanzu zan shirya yau akwai wash" yabi bayan Azad, sameer ya juya zai bisu ta rike hanunshi, tsayawa yayi yana kallonta itama kallonshi take, tace "sameer a kullum kai kaɗai nake faɗawa abu sabida kaine babba kafi su Azad hankali da tunani, sameer mu kara sa ido akan muneeb" cikin mutuwan jiki yace "unty batool wallahi duk wani sa ido daya kamata nayi, saida na yiwa ya muneeb to amma har yanzu na kasa gano komai may be he's innocent shiyasa bamu ga komai ba" girgiza kai tayi ta zauna akan sofa tace "zuciyata taki yadda da muneeb innocent ne, na kasa yadda sameer, a kullum ina rokon Allah ya ciremin shaƙƙu akan muneeb amma har yanzu na kasa dainawa sameer gaskiya ina tsoron mutuwa na barku tare dashi, muneeb ɗan uwanane na jini kamar ku, amma ina tsoron barinku a hanunshi haka kawai na kasa yadda dashi, sannan nasan dole zan mutu domin ciwon cancer a ciki baya sauki" durkusawa yayi a gabanta ya riko hannayenta yayi mata kiss a hanu sannan yace "insha Allah ba zaki mutu ki barmu ba muna tare dake, babu abinda zai rabamu" murmushi tayi mishi, shafa fuskanshi tayi tace "ina fatan koda na mutu zaka kula da kannenka harma dashi muneeb ɗin" yace "insha Allah ba zan karya alkawari ba" Azad wanda yaci gayu kamar ba gobe ya sauko daga stair, wani bala'in kyau yayi cikin riga red da wando black, yasa black facing cap, agogon da ya muneeb ya bashi ranan birthday ɗinshi tsadadde yasa black, kamshi yake sosai, a gaban batool ya tsaya yace "ya? nayi kyau?" murmushi tayi me sauti sannan tace "kayi kyau baby Azad kamar wanda zaije wajen budurwa" rufe fuskanshi yayi da tafin hanunshi cikin kunya yace "kai unty" jabeer ne ya fito shima yayi kyau cikin yadi milk color yasa hula milk yayi kyau sosai yana kamshi yazo yana gyara zaman agogon hanunshi, yace "sameer idan bakaje ka shirya ka fito da wuri ba wallahi zamu tafi mu barka" harara sameer ya aika mishi sannan yace "kaida ka gagara tambayan kuɗin saida baby Azad ya tambaya shine zaka zo kana gayamin maganan banza?" yace "kaima ai ka gagara tambaya duk ɗaya muke" ganin sun fara musu Azad ya nuna musu atm yace "wallahi zan tafi na barku ku duka sabida kun san nine da magana akan kuɗin" sanin halinshi sukace "Allah baka hakuri" sameer ne ya shiga domin shiri Azad ya zauna gefen batool yace "me dame dame kikeso mu kawo miki?" tace "koma mai inaso" yace "karki damu yau saina huce haushina aka chocolate" dariya sukayi, sameer ne ya fito yayi matukar kyau cikin riga orange da hula orange sai bakin wando, kamasu da muneeb ya fito sosai, ganin suna kallonshi yace "ya akayi?" jabeer yace "gaskiya ban yadda ba duk kun fini kyau wallahi sai naje na canja kaya" ganin da gaske yake suka kama hanyan tafiya yasan halinsu badan yaso ba kawai ya bisu yana ɓata rai, dariya batool tayi suna fita kuma dariyan ya koma kuka, masu gadinsu suna ganin sun fito suka tashi buɗe musu mota akayi suka shiga, binsu a baya sukayi domin basu tsaro na musamman, basa taɓa fita babu masu tsaro tun basa so har sun saba, tsadaddun motoci ne kuma kowane da sunan family ɗinsu akai wato makawa, duk wani motan da yake wucewa idan motocin gidansu sunzo wucewa tsayawa suke, hakan kuwa akayi yauma motocin sun tsaya a gefe, Azad ne yace "nifa gaskiya na tsani wannan ɗabi'an babban yaya wai sai kowa ya jira mun wuce kafin ya wuce? to idan sunada uzuri fa? wani fa sauri yake zai kai matarshi ko ƴarshi asibiti meyasa za'a tsayar dasu?" sameer dake karanta jarida yace "to ai kasan ba zamu iya karya wannan dokan ba dole haka zamu hakura" jabeer kam danna wayarshi yake bai kulasu ba, da haka har suka isa mall ɗin, babban mall ne parking sukayi suka fito a tare suke tafiya masu tsaronsu suna binsu a baya, kowanne rike da bindigan kariya da kuma bakin kaya a jikinsu, duk masu siyayya aka fitar dasu waje domin makawa's zasuyi siyayya ba'a bari kowa ya zauna a mall ɗin, Azad cikin jin haushin fita da mutane sukeyi idan zasuyi shopping yayi tsaki kawai yasan koda yayi magana umarnin babban yaya ne a cewarshi babu abinda yafi mishi kannenshi muhimmanci shiyasa yake basu masu tsaro kwararru na musamman, duk abinda suke so ɗauka suke suna sawa a basket, da haka har suka gama aka ɗauka har mota aka kai musu, Azad ne rike da karamin leda a hanu suna tafiya suna hira, biyan kuɗin sukayi kana suka koma mota, sai a lokacin aka kyale mutane suka shiga. lokacin da suka hau titi kowane mota tsayawa yayi, wani driver da yake sabo ya kalli motocin da suka wuce sannan yace "wai meyasa a kullum idan waɗannan sunzo wucewa sai ace kowa ya tsaya su ɗin su waye ne?" murmushi na kusa dashi yayi sannan yace "waɗannan sune family ɗin makawa, yayansu muneeb makawa attajirin me kuɗi ne yana ɗaya daga cikin manyan mutane uku masu kuɗi na nigeria, ance su marayu ne babu uwa babu uba shi yasa yake son kannenshi kamar ranshi, da abu ya samu kannenshi ya gwammace ya sameshi koda wani irin masifa ne, hakan yasa duk inda zasu je suna tare da masu basu tsaro, bai yadda da kowa ba shiyasa yake basu tsaro na musamman" driver yace "gaskiya alamu sun nuna yana sansu irin wannan kulawa haka?" yace "kaɗan ka gani daga cikin soyayyan da yake nuna musu, saima kaje siyan abu idan sunzo dole ka hakura sai an gama dasu kafin a juyo kanka" yace "to Allah ya kyauta" a tsakiyan falo suka barbaza kayan kowa yana zaɓan bashi, batool wacce take kuka tunda suka tafi har saida taji dawowansu kafin ta share hawaye tana kallonsu suna raba kayan. Najwah durkushe take a gaban shanu tana tatsan nono, sanye take da kayan fulani fari tayi adonsu me kyau ta fenta bakinta da bakin kwalli, gashinta da Adda meera ta kitse mata ta barshi babu ɗankwali sai adon data kame gashin dashi kamar ribbon, murmushi take yi tana waƙa da harshen fulatanci tana cikin nishaɗi a duk lokacin da zata tatsi nono, adda meerah ce ta karaso wajen hanunta rike da samira itama tayi kyau sosai cikin riga da zani na atamfa, da ado sosai a fuskanta ta ɗaga murya tace "najwa kizo muci abinci kin gaji saiki huta ni zanyi sauran" jin an ambaci abinci tayi saurin tashi domin bata jure yunwa, da sauri taje ta zauna karkashin bishiyan da Adda meera ta zauna, abincin ta buɗe shinkafa da wake ne yaji man shanu da barkono, murmushi tayi tace "wayyo Allah kamar inna ta san abinda nake so a raina" tace "ba inna bace nice na dafa sabida nasan kinfi so" murmushi tayi tace "gaskiya naji daɗi" wanke hanunta tayi tasa suka fara cin abincin, daɗi yake mata sai murmushi take, meerah tace "najwah?" tace "na'am adda meera" tace "kin san duk duniya babu wacce nake so kamar ke ko?" ta jijjiga kai tana cigaba da cin abincin, tace "to Inaso kiji duk maganan da zan miki kin san dai ba zan cutar dake ba" tace "um" tace "najwa ki koyi hakuri, dan Allah kada ki kara faɗa da kowa a wannan rugan, najwa ki daina biyewa mutane kina faɗa da mata da maza" haɗiye abincin tayi sannan tace "ai bana faɗa da mata duka nake yiwa duk macen fata tsokaneni kuma kinfi kowa sanin ƴan rugannan basu da kunya kuma ni bana neman tsokana kin sani, saide duk wanda ya tsokaneni ko shine me garinmu saina rama" kullum idan tana mata nasiha bata yadda hakan yasa tayi shiru kawai tasan da gaske bata neman tsokana amma batada hakuri, da haka har suka cinye abincin ta koma ta gama tatse nonon kafin ta ɗaura katon kwaryan a kanta tace "mu tafi adda meerah zanje wanki a bakin kogi" ɗaukan samiran tayi sannan ta ɗau goran ruwan da sandanta ta rike suka jera suna tafiya suna hira kamar kawaye da haka har suka isa gida, najwa ce ta shiga ɗaki ta ɗauko tulin wankin da suka tara tace "na tafi bakin kogi" inna dake banɗaki tayi saurin fitowa tace * "najwah banda faɗa, kiwa Allah kiwa Annabi kada kiyi faɗa da kowa, najwah kinfi kowa sanin yadda nake shan zagi a garinnan a kanki cewa ake kun kasa auruwa sabida rashin kunyarki har yayarki ana tsoron auranta, gori iri iri babu wanda ba'a yimin amma ni nasan lokacinku ne baiyi ba, dan Allah najwah ki barni da abinda yake damuna har babanku bai daina zagina akanku ba yace kun kasa aure dan Allah ki fita harkan kowa" tace "to inna naji" kundura tasa fari sannan ta ɗaura wankin a kanta ta ɗau baho da omo tace "adda ameera idan kin gama yiwa inna kitson zaki

Chapter 2 of 11