Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana so tace ta sassauta rikon data yiwa yaron tana jin tsoro domin har ita yau tana tsoron najwah, suna shiga gida tana rike dashi taje bakin murhu ta hura wuta ta girka ruwan zafi, saida yayi zafi sosai kafin ta juye a baho, shiga ɗaki tayi da ruwan ta ɗauko klin da soso, gyara ɗaurin zanin tayi sannan ta yanke cibiyan ta fara mishi wanka, yana kuka tana cewa "ka daina kuka kaji insha Allah ba zaka taɓa kuka ba matukar ina raye" saida ta gama mishi wanka ta sashi a sabon zaninta ta rungumeshi, kuka yake yi sosai, ta gane yunwa yake ji, goyashi tayi ta fita, wajen shanunsu taje ta fara tatsan madara, saida ta tatsi dayawa kafin ta koma gida, saukeshi tayi ta fara bashi madaran, sha ya fara tana kallonshi kamar tana kallon meerah kama suke sosai da meerah, saida ya koshi kafin yayi shiru bacci ya ɗaukeshi, akan gadon inna ta kwantar dashi sannan ta kwanta a gefenshi ta kasa koda kyafta ido ne kallonshi kawai take tana tuna tun lokacin da suke yara da Adda meerah har zuwa yanzu da take mafarkin ta mutu domin har yanzu bata yadda da gaske adda meerah bata raye ba, inna ce tayi sallama da abinci a hannu, ajewa tayi a hankali tace "najwah sauko kici abinci kinga tun jiya rabinki da abinci" girgiza kai tayi, tana jin ciwon kai tace "a'a inna bana jin yunwa" shiru inna tayi, ta zauna kawai a kasa, baba ne ya banko kofar gidan ya shigo, ɗaga murya yayi yana kiran sunan inna, a hankali ta fito daga ɗakin ta durkusa, da yatsa ya nunata yace "Allah ya isa tsakanina dake safiya Allah ya isa ban yafe ba, kuma kije sai Allah ya saka min" kallonshi tayi da mamaki tace "me nayi maka?" yace "safiya Allah ya isa ban yafe ba, safiya abinda kika koyawa yarannan kenan? Ashe zina kike koya musu safiya? yanzu har ameera da take da aure bata daina zina ba, gashi nan arɗo ya irgamin komai yace tunda ya aureta bai taɓata ba, to aina ta samu cikin wannan jaririn da kuka shigomin gida dashi?" dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un arɗo ba zaiga Annabi ba, arɗo sai Allah ya tsine mishi tunda ya yiwa gawa sharri" yace "kece Allah zai tsine miki, safiya Allah ya tsine miki albarka keda yaran da kika haifa da wacce ta mutu da wacce take raye dama yaron da aka haifa duk Allah kwashe muku albarka" najwah dake ɗaki tayi shiru tana jin wani abu me nauyi a kirjinta, duk maganan da baba yake faɗa sai taji kamar an ɗaura mata dutse mafi nauyi a kirji, sai hawaye take, inna tashi tayi zata tafi yace "dakata safiya, kin san ba zan zauna da ɗan zina ba, ba zan reni shege ba, sannan yarannan na fara zargin ba yarana bane, musamman najwah harma da ita Ameeran, sabida haka na sakeki saki uku" hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tace "usman tunda nake ban taɓa zina ba, sannan ƴaƴana basu taɓa zina ba, idan har na taɓa zina Allah ya saka maka da Alkhairi, idan kuma ban taɓa yiba Allah ya sakamin da Alkhairi ya fara nuna maka sakayya tun a duniya, Allah yabi min haƙƙina dana ƴaƴana, ƴata ta rasu usman shine zaka sakamin da wannan mugayen kalaman? ina bukatan rarrashi da hutun zuciya ina jin zafin mutuwan ƴata shine zaki bini da wannan sharrin? ban yafe ba" shiga ɗaki tayi ta kwanta akan gadon tana kuka, najwah wacce taji komai tace "inna zama a garinnan bai kamamu ba, tashi zakiyi mu shirya mu bar garinnan" inna tace "na yadda najwah na yadda mu bar garinnan wallahi nima ba zan iya zama ba" tashi tayi ta fara shirya kayansu a boro, inna ta tattara duk wani abu me amfani ta zuba a katon ghana most go, najwah ta ɗaga bakin tabarma ta ciro kuɗi masu yawa sannan tace "ga wannan na tallana ne da nake ɓoyewa" karɓa inna tayi tace "Allah miki albarka amma yanzu ki jirani zanje gidan rabi dilalliya tazo ta faɗi nawa zata siya sauran kayan ɗakin duka" tace "to inna" mayafi inna tasa sannan ta fita zuwa gidan dilalliya, baba ya shigo ɗakin ya kalli najwa wacce taki kallon inda yake, takadda ya wurga mata yace "ga takaddan sakin uwarku sai kuje kuyi ta bin maza kuna zina kuna samun kuɗi idan kunga dama ku tara duniya da abinda ke cikinta idan kunga dama kubi mazan duniya haka dai zaku kare a wahale a tsiyace" fita yayi daga ɗakin ta kalli takaddan da larabci aka rubuta hakan yasa ta gane me a ciki, sawa tayi a jakan inna sannan ta kalli yaron dake bacci, murmushi tayi, inna suka shigo da dilalliya ta duba kayan duka sannan tace "to gaskiya safiya kayanki basuda wani kyau, kinga tsofin yayi ne amma naga halin da kuke ciki zan siya da daraja" inna tace "na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi" tace "ameen" kuɗi ta ciro masu ɗan kauri ta irga ta bata, karɓa tayi da godiya, bayan ta tafi inna ta kalli najwah tace "wani suna zamu sawa yaron?" shiru najwa tayi da ace macece da zasu sa mata ameerah, inna tace "ko nasa sunan babana?" tace "eh inna" a hankali ta fara raɗa mishi suna yadda akeyi, murmushi tayi tace "sunanshi HABIB" najwah ta kalleshi tace "a wajena kuma sunanshi HABIBI" inna tace "Allah ya raya habib da albarka yasa ya zama ɗa na gari" tace "ameen inna" goyashi tayi a bayanta tasa mayafi sannan inna ma ta tattara kayansu ta rike suka fita, kuka ya fara tana girgizashi tace "habibi yi hakuri yi shiru habibi" tafiya sukayi najwah bata kara juya baya ta kalli gidan ba, haka kuwa tayi lokacin da sukazo barin garin bata kara kallon garin ba, mashin suka hau aka tafi dasu can cikin gari nesa da garinsu sosai, murmushi tayi lokacin da suka shigo cikin birni ta kalli inna wacce bata saba da birni ba, tace "karki damu inna komai zai zama da sauki" tace "to najwah" tace "me mashin taimako nake nema" yace "ina jinki" tace "dan Allah ina zamu samu gidan haya? wanda babu mutane?" yace "babu damuwa zan muku jagora na kaiku unguwa me kyau ma wanda babu hayaniya" tace "to mun gode" wani unguwa ya kaisu madaidaici na masu rufin asiri a kofar wani gida me kyau kaɗan na daidai zaman mutum ɗaya da iyalanshi yace "nan haya ne wannan shine gidan me bada hayan" ya nuna musu gidan, zai tafi najwa tace "dan Allah tsaya mana" ya tsaya tace "ba haya muke so ba siyan gidan mukeso muyi" inna ta waro ido tace "ke najwah ina mukaga kuɗin siyan gida?" tasa hanu a hulan kanta ta ciro kuɗi masu yawa tace "wannan kuɗin shanun baba ne na siyar bai sani ba sabida na siyasa adda meerah kaji da kayan suna idan ta haihu" shiru inna tayi, me mashin ya shiga har gidan mutumin yayi musu jagora, ya siyar musu kuma ya ɗanka musu takaddan gidan, shiga gidan sukayi najwah tana bin ko ina da kallo, kayansu da sukazo dashi suka shigar ɗaki ɗaya da yake gidan saide akwai bedroom a ciki, aje kayan sukayi sannan suka shimfiɗa tabarma tace "idan mun huta zanje na siyo mana katifa sabida habibi karya kwanta a kasa sanyi zai shiga jikinshi" inna tace "to" zama tayi suka huta kafin ta goya habibi a bayanta ta fita, kasuwa taje ta siyo musu abubuwan buƙata ciki harda kayan abinci da katifa da kuma sabbin kaya wa habibi, kuɗin hanunta saura kaɗan ta adana sabida gobe. *Jiddah Ce....✍️* 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *NI DA MUNEEB* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 7* ~Kwance yake akan gado ya rufu da blanket yana bacci cikin nutsuwa kamar wanda baida komai a kanshi, kyakkyawan fuskanshi ya kara yin kyau domin yana daga cikin waɗanda bacci yake yiwa kyau, cikin sanɗa Azad ya shigo ɗakin ya kunna tocin wayarshi ya haska yaga yana bacci, murmushi yayi yace "thank god" a hankali ya fara buɗe side drower ɗinshi yana dube dube, ganin babu abinda ya kawoshi ya ɓata rai kamar zaiyi kuka yana cigaba da nema, can ya hango bakin leda da sauri ya ɗauka ya buɗe, gani yayi hotuna ne dayawa da yara wasu sanye da kayan makaranta wasu kuma da personal, kallon hoton ya fara sai kuma ya taɓe baki ya maida laidan yaci gaba da neman abinda yake nema, murmushi yayi lokacin da yaci karo da tsadadden agogon daya kawoshi ɗakin, sawa yayi a aljihu ya ɓoye a hankali ya maida drower ya rufe, kallon muneeb dake kwance yana bacci yayi, sannan yace "babban yaya bai san yau na mishi babban sata ba, zanje wajen party ɗin abokina dashi nasan kowa saiya kalli hanuna a wajen" ɗan durkusawa yayi ya mannawa muneeb ɗin kiss a goshi sannan yace "i love you babban yaya" cikin sanɗa ya fara tafiya ya buɗe kofan yasa kafa ɗaya a waje zaisa ɗayan yaji muryan babban yaya yace "dawo" waro ido yayi ya runtse ido irin yadda yara keyi idan an kamasu suna aikata laifi, buɗe wutan ɗakin yayi a hankali ya juyo fuska abin tausayi yace "good morning babban yaya" wani irin kallo yayi mishi babu dariya akan fuskanshi yace "zo nan" zuwa yayi kanshi a kasa yace "me..me..me..kazo yi?" yace "na..na..na" hararan daya mishi saida yaji fitsari yana shirin sauko mishi, yace "kwaikwayon m..maganana kake?" da sauri yace "wallahi a,a ya muneeb" yace "to me kazo yi?" da sauri yace "nazo na maka kiss ne" kallonshi yayi da sauri yace "ina nufin nazo nayi maka peck a baki" ganin kallon da yake mishi a ruɗe yace "a kumatu, no a forehead" ganin jikinshi yana rawa yace "fita" har kamar zai faɗi wajen sauri, yana fita ya jingina da kofan ya dafa kirji ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yace "ya Allah na gode maka daka tseratar dani daga mugun babban yaya" dakinsu yaje yaga jabeer yana bacci, marinshi yayi da karfi yace "tashi ka gani" tashi yayi yana murza ido yace "meyasa zaka tasheni?" ya ciro agogon yace "ya ka gani?" waro ido yayi yace "agogon babban yaya?" signal yayi mishi yace "yes an gaya maka ni ɗin wasa ne? ai zuwa nayi ja sace ba nace maka zan iya ba kace ba zan iya ba?" sameer dake zaune akan gadon ya ɗaura laptop a kafarshi yana dannawa, kallon Azad ɗin yayi yace "amma kana neman rigima Azad, meyasa zaka ɗauki agogon babban yaya kasan idan ya gane ba zakaji daɗi ba ko?" tsaki yaja yace "kaifa matsoraci ne nifa da kake ganina bana da tsoro jarumi ne ni sabida kasan soja zan zama" sameer yace "Allah dai ya rufa maka asiri" ɗalewa gadon yayi ya ɗaura kanshi a kafar jabeer yana kallon agogon yace "wayyo Allah sauri nake gobe yayi naje wajen birthday ɗinnan nasan nine most expensive guy na wajen, sabida zan zama me tsada" jabeer yace "kabi dai a hankali karka bari ko kuɗa ya taɓa agogon babban yaya" yace "na san me nakeyi ai" muneeb komawa yayi ya kwanta yayi shiru, murmushi yayi tunawa da abinda Azad ɗin yace wai nazo nayi maka peck, son kannenshi daban yake ji a ranshi, musamman Azad da yake shine karami, a hankali ya rufe ido yana so bacci ya ɗaukeshi, kasa baccin yayi kawai ya tashi ya ɗau wayarshi ya buɗe data zubawa wayan ido yayi yana kallon sakonnin da suke shigowa, saida suka gama shiga kafin ya fara dubawa, duk akan business nashi ne hakan yasa yayi reply, da wanda zasu turawa kaya da waɗanda an riga an tura musu kayan, azeez ya gani a online, yace "me kake bakayi bacci ba?" buɗewa yayi sai kuma ya turo mishi "am with my beb" tsaki yaja yasan azeez mayen mata ne sosai, shi kuma ya tsani abinda ya alakanci mata, bai kara mishi reply ba kawai ya rufe datan ya sauka daga gadon, falo ya koma ya zauna akan sofa yayi shiru yana kallon cikin ɗakin, cikinshi ya shafa a hankali yana runtse ido, ciwo yake ji cikin yana mishi, tsaki yaja ya tsani wannan ciwon cikin da yake taƙura mishi rayuwa, komawa ciki yayi yana duba pills nashi bai gani ba, tsaki ya kuma ja ya kwanta, bacci yaki ɗaukanshi ya koma falo ya kwanta akan sofa, nan ma baccin yaki ɗaukanshi sauka kasa yayi ya kwanta akan tile, ganin ciwon ya dameshi ya rasa yadda zaiyi kawai ya ɗaga waya ya kira sameer, sameer dake duba laptop ya kalli wayanshi dake ringing yana mamakin waye me kiranshi a wannan tsohon daren?" ganin babban yaya yayi saurin ɗauka, yace "hello ya muneeb" murya kasa kasa yace "kazo ɗakina" da sauri ya aje wayan ya rufe laptop ɗin ya fita" knocking yayi, yace "shigo" a hankali ya tura kofan ya shiga, ganinshi a kasa ya karaso da gudu yace "meya sameka?" a hankali yace "cikina" sameer yasan abu sosai akan lafiyan ɗan adam domin likitanci yake karanta, yace "yaushe ya fara maka?" "tun ɗazu" ya amsa a takaice, kallonshi yayi sosai sannan ya tashi yace "ina zuwa" ɗakinsu yaje ya buɗe first-aid-box ya fara duba magungunan ciki, can yace "yawwa" ya ɗauka sannan yaje fridge ya ciwo ruwan gora, ɗakin ya koma ya ɗagashi ya taimaka mishi ya zauna akan sofa, har yana zufa duk da Ac na aiki, maganin ya bashi, yatsina fuska yayi sabida bai son magani ya karɓa da kyar ya haɗiye yasha ruwan dayawa kafin ya kwanta, shiru sameer yayi ya zauna kusa dashi, ya rufe ido a hankali yana jin ciwon yana sauka, da haka har bacci ya ɗaukeshi, sameer tashi yayi yaje ya ɗauko bargo yazo ya shimfiɗa a kasa kusa dashi, kwanciya yayi shima ya fara bacci a wajen. Asuba ta gari, shi ya fara buɗe ido ya sauke su akan sameer dake bacci a kasa, a hankali ya lumshe idon ya kara buɗewa, murmushi yayi wanda baima san yayi ba, sai kuma ya murtuƙe fuska ya sauka daga sofan ya shiga ciki, wanka yayi sannan ya ɗaura towel ya fito, jallabiya yasa sannan yayi sallah, fita yayi har yanzu sameer yana bacci, ganin sanyin asuba gashi bai rufu ba ya koma ɗaki ya ɗauko blanket nashi ya dawo ya rufashi kafin ya fita, ɗakinsu Azad ya leka yaga suna bacci, kitchen yaje ya fara musu girki kamar yadda ya saba, cikin kwarewa ya gama komai, ya koma ɗakinsu Azad yayi knocking da karfi alaman su tashi, babu wanda ya tashi a cikinsu, shiga ciki yayi ya rike waist yana kallonsu yadda suka rungume juna kamar wasu wawaye suna bacci, tsaki yaja yace "kai A...a...Azad ku tashi kuyi...salla" shiru sukayi saima kara jan bargo da jabeer yayi, ya kara cewa "ja..ja...jabeer tashi kuyi salla" jabeer ma bai tashi ba sai cewa yayi "umm" fita yayi ranshi a ɓace yaje fridge ya buɗe, ruwan gora da suka fara daskarewa ya ɗauka ya juye a wani babban bowl, naɗe hanun jallabiyanshi yayi ya ɗauka ya shiga dashi ɗakin, ganin suna bacci har yanzu ya juye musu ruwan a jikinsu, Azad da yaji wani masifaffen sanyi ya shiga jikinshi yayi ihu ya tashi shima jabeer tashi yayi a firgice, Azad yace "wani mara imanin....." shiru yayi da sukayi ido huɗu da babban yaya, bai kara magana ba sai rawan sanyi da yake, domin yanzu ba karamin sanyi ake ba, jabeer da yaji yayi freezing ya kasa yin komai sai kallon Azad, fita yayi daga ɗakin baice musu uffan ba, jabeer yana rawan ɗari yace "Azad ciremin kayan jikina sanyi" Azad ne yayi dauriya ya cire mishi kayan, tsaban sanyi duk suna rawan sanyi, hakoran jabeer har suna haɗuwa da juna, bargon da bai jike ba Azad ya ɗauka ya rufa mishi jikinshi dashi yace "kaje toilet ka watsa ruwan zafi" a hankali ya sauka yaje toilet ya haɗa ruwan zafi sosai ya shiga, saida yaji sauki kafin yayi alwala ya fito, salla sukayi jabeer ya kwanta akan sallaya yana baccin wahala, atake zazzaɓi ya rufeshi, Azad ya bashi paracetamol yasha kafin ya kwanta jikin yayi sauki, sameer ya jima da tashi salla yayi yaje ɗakin batool, ta zauna ta jingina baya da jikin gadon tana kallonshi yana ɓalle maganinta, tace "sameer ina fatan Allah ya bani nisan kwana na zauna tare daku amma na san hakan ba zai taɓa faruwa ba" ya mika mata maganin baiyi magana ba, karɓa tayi tasha, hanunta ya rike yace "muje breakfast" sauka tayi a gadon, tana sanye da bakin kaya roba roba ta zama kamar balarabiya gashinta ya rufe mata da mayafi siriri yana rike da hanunta suka fito, muneeb yana zaune akan kujera yana cin abinci, saida suka zauna ta kalleshi tace "ya jiki?" a takaice ya amsa "da sauki" daga nan bai kara cewa komai ba sai cin abinshi da yake" suma babu wanda yayi magana abinci suka, ci suka fara, Azad da jabeer suka fito suma suka zauna, suka fara breakfast babu wanda ya yiwa ɗan uwanshi magana har suka gama, sameer da unty batool suka zauna a falo shi kuma jabeer ya koma ɗaki ya ɗauko blanket yazo ya kwanta a gefen sameer ya rufu ya fara bacci, Azad yana tsaye a bakin kofa yana jiran tafiyan ya muneeb sabida so yake ya tafi shima amma baison yaga agogon da zai ɗaura, murmushinshi me kyau yayi lokacin da yaga muneeb ya fito sanye da bakin kaya riga da wando yayi bala'in kyau, ya gyara gashinshi da sajenshi kamar ka saceshi ka gudu, yana waya har ya wuce bai kula dashi ba, ya sauka kasa yana cigaba da waya bai kula kowa ba ya fita, hamdala Azad yayi ya shige ɗaki da gudu, wanka ya faɗa bayan ya gama ya fito, tsadaddun kayan daya shirya ba birthday ɗin abokinshi yasa, shadda ne baƙi yasa da takalmi baki sai sarƙa irin na yarabawa (igbo tribe) agogon daya sato yasa sannan ya taje gashinshi ya kalli kanshi a madubi yace "wow Azad ka haɗu iya haɗuwa" murmushi ya yiwa kanshi kafin ya ɗau turaren babban yaya shima ya satowa yayi da jimawa ya fesa, sanda me ado ya rike subhanallah wani bala'in kyau yayi, wayarshi ya daga yace "gani nan zuwa yanzu" fitowa yayi daga ɗakin yana taku kamar baya son taka kasa, tun daga nesa suka jiyo kamshin turaren kuma sun san wannan turaren babban yaya ne yake aiki dashi, ido suka zuba mishi su duka suna kallonshi yana takowa yana wani irin smiling, murmushi unty batool tayi lokacin daya karaso yace "ya kika ganni unty?" tace "looking masha Allah" sameer yace "kai Azad aradu kayi kyau sosai bari nayi maka hoto nasa a status" tsayawa yayi da kyau sameer yayi mishi hotuna masu kyau, kallon hoton yayi yace "sunyi kyau" ganin ana kiranshi a waya yace "bari na tafi kada nayi late" jabeer yace "karka kuskura ya muneeb ya rigaka dawowa" yace "hauka nake da zan tsaya ya rigani dawowa?" kuɗin da suke sabbi dal yasa a aljihu kafin ya fita, motarsu jeep baki da tinted glass, security ya yiwa magana suka zo da sauri, shiga motar yayi suka shiga nasu driver ya jashi, suka haɗa convoy kamar yadda suka saba, suna hawan titi ya fara murmushi a ranshi yana ji yau sai yafi kowa kyau a wajen, hakan kuwa akayi zuwanshi ya tada wajen da tafi, sai sannu ake mishi, ya zauna a v.i.p daga nan aka fara yanka cake dama shi kaɗi ake jira, shida abokanshi sunyi ankon bakin shaddan sunyi bala'in kyau sunata hotona ana yaɗawa a social media domin shi kanshi hamid me birthday ɗin ba ɗan kananan mutane bane, ƴammata da manya da kanana idonsu akan baby Azad, shi kuma yanada sakin fuska hakan yasa yake shiri da abokanshi sosai, spray ya fara da kuɗin da yazo dashi, nan take aka fara hyping nashi domin saida kowa ya san wannan daga makawa's ya fito. Muneeb ya ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya yana kallon jaridan da aka fitar wanda shine ya bada rahoto sannan ya faɗa musu yawan adadin yara da aka sace a cikin kwana ukun nan, murmushi yake yana ganin wawancinsu da basu tambaya aina yake samun labarin ba, saide wani zuciyan ya tabbatar mishi sabida yanada kuɗi ne basu tambayanshi, a ranshi yace "matukar kanada kuɗi babu abinda ba zaka samu ba, kuma babu abinda zaifi karfinka" murmushi yayi ya ɗau wine dake gefe ya buɗe da kwalban yake sha, har suka isa company, buɗe mishi marfin mota akayi ya fito cike da izza yake takawa har zuwa office nashi, zama yayi wasu manyan mutane sukayi knocking ya san da zuwansu shiyasa ya basu daman shigowa, shiga sukayi su biyar duka da manyan kaya a jikinsu, kana ganinsu kasan basu haɗa hanya da talauci ba, waje ya nuna musu yace "ku...ku..ku zauna" huɗu daga cikinsu suka zauna ɗaya yaki zama yace "ba zama ne ya kawomu ba" murmushin gefen baki yayi yace "me..me..meya kawo ku?" yace "gargaɗi muka zo muyi maka, muneeb makawa kayi kaɗan ka shiga mana hanci, har yanzu kai yaro ne a wajenmu kai karamin alhaki ne domin ko yanzu mukaga dama zamu iya kashe ka kuma babu abinda ya isa ya faru damu domin mu nan mun rigaka shiga harkan saida mugayen kwayoyi kuma ka shigo kanaso kayi mana tawaye bayan mu muka koya maka komai da komai kuma kafi kowa sanin me yake tsakanin mu da kai" tashi yayi daga zaunen da yake ya goya hanu a baya yaje bakin kofa ya rufe da makulli, ya dawo ya wurga makullin akan desk ya ciro bindiga daga cikin aljihunshi ya ciro safan hanu yazo ya riko hanun mutumin yasa mishi safan hanun kafin ya danka mishi bindigan ya ware hannayenshi cikin in ina yace "gani kasheni, me kake jira da bazaka kasheni ba Alhaji lawan? ka kasheni mana" ganin ba zai harbeshi ba ya riko hanunshi me bindigan ya saita kirjinshi yace "harba mana ko an gaya maka muneeb yanada burin zama ne a duniya kamar yadda kuke buri? ka sani yau idan kuka kasheni za'ayi asaran rayuwaka fiye da ɗari kuma wallahi asirinku a tone yake" buga kujera ɗayan yayi ya nunashi da yatsa yace "to ka tona mana asirin mana sai me? an gaya maka bamu san kaine kasurgumin ɓarawon yara na garinnan ba? an gaya maka bamuda masaniya akan satan yara da kake yi?" murmushin gefen baki ya kuma yi sannan ya ciro wayarshi yace "satan yara kaɗai kuka sanni dashi?" cikin in ina yake maganan, ya nuna musu wani video ɗin yara da suke a kwance a wani ɗaki a galabaice, yace "wannan gidana ne a tsakar daji bayan ni sai security's ɗina da masu aikin gidan kaɗai muka san da wannan gidan, sai kuma ku da nake faɗa muku a yanzu, bayan na saci yara kun san ina nake kaisu?" dariya ya kwashe dashi harda rike ciki, kallon juna suka fara zuwa yanzu sun fara tsorata, yace "to ai kaisu nake kasar waje ana fita dasu a kaisu asibiti a cire ƙodansu, daga nan wasu suyi rai wasu kuma su mutu, basa dawowa da rai da tsakar dare nake zuwa ina zubar da gawansu, idan kuna ganin karya ne bari na nuna muku" waya ya kira video call, wani dake cikin jirgi ya ɗauka fuskanshi rufe da facemask yace "boss mun tashi ai" murmushi yayi yace "yara nawa?" yace "su 20 mun bar 30 sai kuma" yace "nuna minsu na gani" nuna mishi yaran dake kwance kamar gawa a cikin jirgin yayi duk suna sanye da uniform kala ɗaya, yace "good job" kashe wayan yayi ya kalli su Alhaji lawan da suke kallon kallo, da sauri Alhaji sale yace "me ka taka muneeb da kake gaya mana wannan abin?" dariya yayi sosai ganin sun tsorata yace "me na taka?" matso Alhaji salen yayi da sauri yayi baya, yace "ba abinda zan maka.." ya haɗa fuska kamar bai taɓa dariya ba yace "kai Alhaji saleh kanada yara biyar s school ɗin mm academic nursery school, yaranka kanana ne basu girma ba babbansu shine sadik sai Atika me sunan mamanka sai kuma yasir da abeed da kuma deen" waro ido yayi, yace "relax ba abinda ya samesu" ya kalli ɗayan yace "kai kuma Alhaji lawan wannan yaron daka sashi a rai sabida shi kaɗai Allah ya baka yana can yana zaune a cikin makaranta yayi shiru yana tunanin kowa yanada mama amma shi bayi dashi, kuma bai san kaine ka kashe mamanshi sabida ka samu kuɗi ba, sunanshi Ishaq ko?" idanunshi a waje yake kallon muneeb, murmushi yayi yace "relax kaima babu abinda zan mishi" sun tsaya basu iya cewa

Chapter 6 of 11